Kenza eBookz

Duba min baya fakon biri - Chapter 8

Duba min baya fakon biri - Chapter 8

Duba min baya fakon biri Chapter 8: Duba min baya fakon biri Chapter 8. Buki kan ya soma don zance tun zuwan mu dai masu gidan basu zauna ba sukan inka…

2,378 words

Buki kan ya soma don zance tun zuwan mu dai masu gidan basu zauna ba sukan inka debe hjy mum dake dan harkokin ta itama don shirin bukin don muna nan aka canza masu set din part dinsu dag daki har falo komai iri daya kalane kawai bambancin kayan. Koshi saida hakan ya dan kawo rikici a tsakaninsu donko hjy malka tace kalan data zaba ke nan tun shego don me hjy mum zata daukeshi. Ita kuma hjy mum tace ai bata san itace ta sayo masu kayan ba dama sai yanzu data fada in haka ba za a bari matsayin ta na babba ta dauka ba saidai baba ya bar kayansa. Nan rikici sosai ya tashi saida Dada ta fito ta tsawata masu a cikin fushi tace ke marka ban gane me kike nufi ba a nan shin ba shigowa kikayi gidan nan kika samu Kubura ba. Ko har kin mantane wai in tuna maki don ni komai yana cikin kaina kamar yanzu akayishi kada ki mayar da mutane wasu bican don kawai shi ya zama shasha kuna juyashi keda diyan ki yadda kuke so. Tirkashi ranan kan naga fadan manya ba dadi don idan kana kusa kunnene kan girmi kaka duk da muna daki hakan bai hana miji komai dake wakana ba wajen. Shi ya dawo daga kasuwa ya kashe wanan wutan daya hada inda yace don ya bata kudi ai basuyi za,a sayo wa yanda kalansu ya bambanta ba tun shago kudin komai iri daya ya basu don haka ta bari hjy kubura da itace babba ta fara zaba. Dole ta dauki kalan milk din ita kuma hjy mum ta dauki ash color din aka zauna lafiya yan company suka jera masu kayan aka fitar da wanda muka sama akai sauyin su zuwa wasu dakunan. Don haka wuni cur mukayi muna wanan aikin na gyaran part din duk da son jikin halkmatu ranan saida ta amfana ga aikin itama aka rutsa da ita. Don bayan mungama na hjy mum kamar yadda mukaji yan gidan nakiranta muma muka kama nabar gwaggon da nake fadi da farko don ko nace gwaggo sai su kama min dariya kawai. Wanan yasa nabar kiranta da gwaggo din nakama hhy mum yadda kowa ke fadi a gidan a yadda ta rikemu dole na mayar da hankali kanta yanzun ma na rage shigowa wajen Dada idan ba aiki muka rarage a part dinta din. Bata da yawan magana haka mukan zauna zugun sai in akwai wuta ta kuna muna kallo wanda kallon ma dai wa,azine su tafi kamowa sai idan zata shige zata kai muna tashan da ake film mu kalla. Zaune muke mun zubawa tv ido ana wa,azi akan sallah nan kan bamu da laifi gaskiya duk mu muna tsare sallah saudai kara fahintar hakki akan sallah din da yanzu muke sauraro a tashan da malamin keyi. Talla sukaje irin na gidajen talabijin lokacin ta dan nisa tace damu yakamata gobe na kaiku wajen gyaran kai a wanke maku kai kuyi kitso har kumshi don idan sun fara shagalin bukin nan baku da lokacin hakan . Daga inda nake kwance na amsa da to tace kawunan ku yana son kitso koba duk sati kuke kitso bane budan ba halimatu sai cewa tayi sai zainab ba ita da mamanta ta iya kitso duk sati take masu. Kefa hjy ta tambaya cikin kallonta tace nikan gaskiya yana kai sati uku huduma banyi kitso ba ta fada tana dariya tace jam kina diya mace kike barin kanki babu gyara haka ko baku san kun girma bane wai ? Muka kalli juna nida halima din tace kunyi sa,a kunzo lokacin kakanin mu sun mutu aida suna nan da yanzu ko wacen ku tana gidan mijinta tana aure. Indai yadda nasan akidar gidan mune na da komu dai primary aka barmu mukayi zamana ikko ne nasamu har nayi secondary a can din ina batun shiga jami,ane Allah ya karbi ran mijina lokacin. Zakice sa,arta muke wani lokaci idan mun zauna muna hira da ita amma saboda cika idonta a fuskan mu bamu iya sakewa da ita muna zance haka dan dama ma halimatu don ko lokacin itace tayi magana. Tace haka Dada ta fada muna Allah ya jikansa ta amsa da amin nima na kara fada tare da dorawa da Allah yasa ya huta aljanna makoma a garesa tace amin . Ban taba tunanem zan kara aure ba a lokacin amma abu ga mai magabata ban jimaba suka kara hadamu aure kuma da babanku nan ashe rabon yayan nan ne dama sai bata karasa ba yadda bahaushe kan fada din suce ya kashe shi. Hjy mum ina suke ne wai bangansu ba mana Dada tace muna kuma kina da yara ai tace suna waje suna karatune dukkansu naso ko karamin abar min nan Alh yaki ya turaahi madina karatu . Tunda ya tafishi har yau ko hutu baizo bama shiyasa yanzu aida nasameku nake jin kamar kada ku tafi wallahi don kuna debe min kewan kadaici sosai wanan zuwan naku. Sai lokacin nayi magana nace wai mukan ai mun kusa komawa school ma hutun mu ya kusa karewa kai mai sunan hjy har ina cewa zanwa babanki magana ya bar min ke nan mu zauna tare. Da sauri nace wai innata bata yarda ai shima baba nasan bai taba yarda da hakan wallahi bai yarda halimatu ta fada a karshe tace ranan fa da Dada tace ya bari ki dawo nan da kwana wajenta cewa yayi ai Dada tayi hakkuri. Duban baya fakon biri sai meshi don Allah Dada tayi hakkuri ta barki a gaban innanku zaifi tunda kina shigowa ai ko wani lokaci. Ninayi mamakima daya yarda kikazo din nan wallahi koda Dada ke fadin ai dake za,azo wallahi ban yarda ba saida kika fada min da bakinki cewa tare dake zamuzo. Dariyan hjy mum din yasa muka kallota don bamu fahinci me takewa dariya a cikin zancen ba tagane me muke nufi tace shi yaya garba din yace DUba min baya fakon biri ? Hakafa yacewa Dada lokacin nakasa fassara wanan maganan nidai na rike kalman kawai a bakina lokacin amma bansan ma,anarsa ba. Aiba wani abu hakan ke nufi ba duba ga zamanin nan da yara basuji suma mutane baka yarda dasu abu a hannunka shine yake abinka ba,a hannun wani ba. Irin hakan da mukan dan zauna tana sake muna fuska yasa muke jin dadi yanzu a gidan bamu ko zancen Dada da sai wani lokaci ma ta kekomu ta samemu zaune ko muna aiki. Washegari din kuwa kamar yadda tace acan muka wuni wurin gyaran kai da kumshi dama ba dabi,ata bace karin gashi don Allah ya hore min suma har gadon bayata da acema ina saka mashi mai da ya sauko min sosai a baya amma kaina yana da santsi don haka shagon mai ya huta dani. Da gashin kaina aka tsantsara min kitson bare bari mai kyau ga wani kamshi dadi na gargajiya mai dadi na tashi a kawunan namu da halimatu dai suka kwasa don tace ita sai ankara mata oulu a kai. Su kuma masu wajen sukace hjy batace ai muna kari ba hakan yasa tayi fushi amma da aka gama kuma sai ta koma murna don sun iya kitso da kumshi kamar tsiya a wajen nasu na bare bari. Hjy mum din tazo ta kwashw mu cikin motarta ni sai kallonta nakeyi ina mamaki don ban taba zaton ko tsamanin ta iya mota ba har tanada shima ashe saida naga ta fito da key munje mun sallami Dada mun fito ta danna key motar tayi kara tun kan mukai waje motar. Yanzu ma din da yamma kuma itace tazo ta kwashemu komawa gida muna faman raba ido ba gida muka nufa gun tella mukaje ya dubamu bai auna muba ya dai ganmu kawai ya tambayi sunan mu ya danyi rubutu a wani littafi muka fito zuwa gida. Mun kamo hanya gidane sai lokacin tayi magana don tunda ta dauko mu kamar ranta yana a bace don yanayinta daya nuna hakan har kana iya ganewa tace. Zaku koma ku samu munyi baki fa don su Addal sun dawo dazun da safe bayan fitar ku duk da nima bansan da zuwansu ba sai ganinsu kawai nayi daga sama kamar anjefosu. Sai ranan na yarda da damuwa nasa babba ya maida yaron dake yawan zama kusa dashi kamar sa,ansa ko amininsa don yadda hjy mum din ke fada muna magana lokacin. Da farko halimatuce tace hjy mum wai Addle kuma tace ba Addale yake ba Addal don yana da sunan baba malam ne mahaifinsu babanku muke kiransa da Addal. Sunan nake maimaitawa a zuciyana na rike sosai can tace akwai dai Allah yanzu don Allah ace an min adalci ke nan duk yaran mamanku malka ankosusu don bukin nan amma ni don son kai dan karamin akawo min shi na ganshi babanku yaki hakan don kuntatawa kawai. A,a,a gaskiya ba,a kyauta ba kan na kallo halima din kafin ta zake nace hjy mum don Allah kiyi hakkuri Allah yasa rashin zuwansu shine alheri su kuma da sukazo Allah ya tsare ya kare ya mayar dasu lafiya tace Amin zainab naji dadin wanan maganan taki sosai wallahi kuma naji zuciyana tayi min sanyi sosai da wanan kalamin naki yanzu. Nace wani lokaci ai mummy zamuga abu muna sonshi amma kuma hakan ba alheri bane tace kwarai tana nisawa zakice wata sa,armuce a lokacin tayi shiru bata kara magana ba har muka shiga gidan nasu tayi packing a inda ta dauki motar da safe. Muka fito zuwa ciki dauke da wasu kaya data miko muna da zamu fito motan nan muka shige ciki wani kamshin dadi part din nata yakeyi kuma yana bude don haka nidake gaba na shigo da sallamata falon. Ciki ciki ya amsa muna yana kwance saman doguwan kujeran falon jikinshi saye da farar jallabiya ta maza mai dogon hannu kafansa farare sun dan baiya ga gashin jikin nan nasa sun kwanta masa lub a kafafun nasa. Ya dan dago yana amsa sallaman tare da fadin mai shiyan bata nan fa saiga hjy mum din ta shigo daga bayan mu tana fadin ki kai min wanan daki halimatu wanan kuma zainab ki aje nan in huta in bude mugani. Mamakine ya kasheni lokaci guda ina kokarin tuno fuskansa in ba karya zanyi ba sune bakin da sukazo katsina wani lokaci har baba yai min bayanin su din nan. Tabbas ma sune shi din ne dai dama dan hjy mum ke nan ake nufi kome ko kuma nan din ma yazone dai kamar yadda yazo muna latsina wani lokaci can lokacin bamu kai hakan ba girma. Halimatu nikan wani suna kika kira dazunne ma ga yayan naku ina sulaiman din ta fada tana kallonshi yace cikin dan dagowa ya fita bansan inda yaje ba sai lokacin nace sannu da zuwa ya dan kalloni. Da sauri nakai kasa ina fadin ina wuni anzo lafiya ya amsa cikin dan kura min ido kafin yace yar gidan baba garba ko ? Itace ashe ka santa ya koma ya kwanta yana fadin wancan zuwan da mukayi katsina na santa kinsan lokacin sun dawo suna katsina tace ehh ai yanzu kam ya dawo gida ke nan . Halima ta fito ta gaidashi itama kafin ta fice da sauri zuwa wajen Dada din dakin mu na shiga nayi sallah ban idar ba nake jin hjy mum din tana kwala min kira ni kuma ina sallah. Saida na idar nazo na sameta ina fadin hjy sallah nakeyi kada lokaci ya shige azahar kawai nasamu nayi a can din dama zance ne ki debowa yayanku abinci ai na debo masa. Na dan rakube ina fadin ayya sallah nakeyi bari naje gun Dada mu gaisa don zuwa yanzu hankalina ya fara komawa gida kan don ban taba tafiya nayi nisa da iyayyena da yan uwana ba sai wanan karon. Da nazo gashi satin mu biyu muka rufe har mun zama yan gida a kano yanzu ko baba na kano ya dawo daga kasuwa baiji duriyan mu ba sai ya tambaya inasu mamana banjisu ba. Wani lokacin idan hjy mun ne kusa dashi zata fada mai abinda muke inko hjy mah ce zata dan basar da tambayan nasa sai yasa murya ya kira wani daga cikin yayansa akiramu. Gashi da halin arziki sai ince sukan haka zariyansu yake da alheri da kuma kula da iyalansu don duk dare baba na kano zai dawo da dan tsarababsa da za,a raba ako wani sashe nagidan. Irinsu yought kilishi limu kaza da gadaden nama mai zafi tare da abin sha kuma sai kowa ya samu a gidan yaci bawai sai wanda yai ra,ayin bawaba kawai zai samu. Tun shigana part din mukaci karo da wanan uwar feleken yar wurin hjy mai nuna kamar tana jin warin mutane idan aka hadu da ita din nan. Nunani tayi da hannu tana fadin wai kece dama ban ganeki ba haka na dauka irin yan classic din nan ne ma a ina kukayi wanan gyaran hakane naga dayan ma yau ta canza sosai. Ban iya bata amsa ba ina kokarin shigewa ga rainin wayau a na magana kina kokarin shige mutum ko ance kada ku fada munane kuma ? Dan murmushin yake nayi mata ina fadin nikan ban dauka dani kike ba ai ku bansan wajen ba wallahi tunda ba garin na sani ba ni andai kaimu an muna hakan na shige dakin da Dada din take. Halima na zaune tana cin abinci nace ke kuma ina can ina jiran kizo muci abinci har na idar da sallah banji ki ashe kina nan kinaci ke ban sani ba Dada tace kyale ja,ira ai na fada mata abincin ku yana can wurin uwarku dama.

ZAINAB IDRIS MAKAWA [1/25, 15:44] Aishatu Aliyu Musa😀🥰: DUBA MIN BAYA FOKON ,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

9️⃣

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull