Farhatul qalbi complete - Chapter 14
Farhatul qalbi complete Chapter 14: Farhatul qalbi complete Chapter 14. _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
4,443 words
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
πππππππ
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯° [11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ π _NA_
_NANA HAFSATU_ _(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:42_
_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._
___
*Tana* jiyo sanda mahaifin su ke sanar da rasuwar Yayan na su. Jijiyoyin jikinta suka saki. Ta nemi kwari ta rasa.
Ta zube zaman dabaro. Hannuwanta dafe da bakinta. Wasu hawaye masu dumi suka shiga kwaranya daga fuskarta.
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun..... Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.... Shikenan? Shikenan Yaya ka tafi ka bar mu? Yaya shikenan babu kai? Wayyo Allah na.... Ummanmu. Yayan mu ya rasu. Ya rasu Umma... Na shiga uku..."
Inna Sa'adatu ta leka fuskarta cikin dakin don ganewa idanunta
"Toh.... Allah ya jikan rai... Allahu Akbar." Ta furta tana girgiza kai.
Marka ta koma ta zauna tana daga kai.
"Allah sa karshen wahalar kenan ... Yarannan yadda ake jelar asibiti da su. Gwara ai da Allah ya karbi ran sa. Uwar ta huta itama...." Marka ta fada gatsal ba tare data auna rashin hankalin zancen na ta ba.
Sosai Najib ke kuka... Yanata girgiza Yayan nasu.
"Yaya... Ka tashi Yaya... Baka rasu ba Yaya... Dan Allah ka tashi."
Kuka yake sosai wiwiwi. Jijiyoyin goshin sa sun fito radau. Yanata birgima yana kuka.
Yayin da Waheedah ma ke kukan a kofar dakin Marka .
"Bar birgima yar nan...." Cewar Deluwa matar da ke haya.
Malam Nalado ya fice yanata sauri ya gayawa liman. Liman din ya sanar da rasuwar da lokacin da za'ayi masa sallah a kai shi madakata.
Najan Isubu na jiyowa ta isa gidan tanata salati da sallallami. Tayi kuka sosai tana girgiza kanta.
"Marka ... Yanzu kin kyauta da abunda kikayi? Gashi nan kin raba da da mahaifiyar sa. Bai rasu agabanta. Sati wajen nawa? Basa ganin juna. Sai dai taga gawar ta sa. ? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Kamalu Allah ya jikan ka da rahama. Annabi yasan da zuwan ka. Allah ya shayar da kai ruwan alkausara kamalu... Bakada wani hali na daban fyace na kirki da girmama na gaba da kai... Allah ya dubi biyayyar ka ya saukaka maka tambayar kabari kamalu .. Allah ya kyautata makonci ya jikan dukkanin wadanda suka rigamu da gidan gaskiya. Muma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani .. wannan jinya da ka sha kamalu Allah yasa kankarar zunubai ce . ...Aamin"
Sai data kai karashe. Marka ta ja Wani dogon tsaki. Ta tashi daga zaunen da take a daki ta fito har gaban Najan Isubu. Tamkar zata tsone mata idanu. Haka ta daga yatsa tana mai mata nuni. Cikin dakushewar murya da tsantsar jin haushi ta shiga ce wa,
"Kinga Naja... Kisan ire iren maganganun da zasu dinga fitowa daga bakin ki. Da girman Allah ko Ruwaida kinga dai itace kusan tsarata ko? To ko ita ki tambayeta tayi kadan a gayan magana .. Zaki ce na raba su da Hadiza waye waye .. Kina so ki nuna ni na kashe shi ne ko me? Bayan wannan cutar tasu ance tun suna 'kankana take kashe su. Bayan shi din da yayi dogon zango? ..... Yo wannan da rayuwar sa ai gwara da yake a ma .."
"Dan Allah marka kar ki karasa......"
"Yo ai kece naga kina neman doramun lefi bayan dama can nakasassu ne. Da samun su gwara r..."
"Ko wanne rayayye fa matacce ne watan watarana Marka . Lapia ko akasinta bashi ke sa Allah ya karbi rai ba. Rigar gado ce mutuwa. Wanda kowanne dan adam seya sakata ..Kinga Waheedah an sanarwa Umman ku ne?"
Waheedah dake tsiyayar da hawaye bata samu damar magana ba. Sai jujjuya kai da take kawai . Yayin da hawaye keta kwaranya a kyakkyawar fuskar ta .
Kawai tunano zaman shakuwar su take da Yayan nasu. Yayan su mai fara'a da mutunci. Sam bashida girman kai. Gashi da biyayya da kyautatawa.
Kenan duk shawarar da yake gaya mata da adduuoin da yake yi. Na tafiya ne kenan? Sallama ce yake yi ta haka? Ashe duniyar zai bari baki daya?
Ta sake fashewa da kuka sosai . Har tana shessheka... Najib ma na ta rera kukan sa mai ban tausayi ga duk wanda ya saurara.
Najan isubu ta fice daga gidan tanata sauri.
"Ina wuni aunty ..?" Cewar wani dan adaidata sahu da suke makota.
"Kwana dai ko... Ina kayi dan Allah..?"
"Gangaren durumi.."
"Yauwa muje ka saukeni dan Allah a gidan gwaggo haule ."
"Me kankara?"
"Eh.."
"Toh shigo.... Ance wai yaran nan kamalu ya rasu ko?"
"Ya wuce wai... Ya rasu da gaske. "
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Allah yasa karshen wahalar kenan... Gaskia gayen nan ya jima yana jinya." Ya karasa fada yana girgiza kai
"Aamin..."
Har kofar gidan ya sauketa. Ta janyo nera hamsin ta miqa masa.
"Ah ki basshi... Allah ya kara hakuri..."
"Aamin...." Jikinta asanyaye ta shiga cikin gidan bakinta dauke da sallama..
"Wa'alaykm Salam...."
Suka amsa. Alokacin Umma Hadiza har ta zura hijabinta .zata tafi gidan aikin ta
"Ahh Najan Isubu... Maraba lale..." Cewar gwaggo haule dake zaune akan wata tabarma tana tsintar shinkafa.
"Naam gwaggo..."
"Ahh Najaatu...."
"Naam Hadiza.... Har zaki tafi?"
"Eh wai so na ke na kammala aikina da wuri. Inason zuwa wambai na tsinto rigunan sanyin su kamalu.."
Najaatu ta dan kwakwalo murmushi kawai ta nemi waje ta zauna .
"Wani wajen kika je ne?" Umma Hadiza ta sake tambayar ta.
"A'ah daga gidah na ke...." Tanata jujjuya yadda zata sanar da zancen mutuwar.
"Wani abun ya faru ne Naja?" Gwaggo haule ta tambayeta. Suka zuba mata idanu su duka suna jiran amsar da zata bayar
"Ai daga gidan su Waheedan nake..."
"Toh.... Rashin lapiar ce dai?"
"Kinji ko gwaggo? Daman wallahi baki daya kwanakin nan haka naketa wasu irin mafarkai.."
"Kwarai har kikace zaki sa a kirawo su kamalu ku gaysa ki ga jikin na su . To ya ake ciki najaatu..?"
Najan Isubu ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta kasa cewa komai. Kanta a kΓ sa. Yayin da idanunta suka kawo ruwa.
Umma Hadiza ta zauna a gefen gwaggo haule. Ta hada hannuwanta biyu .
"Waye ya rasu acikin yaran najaatu?"
Najan Isubu ta daga kai ta dubi Umma Hadiza da sauri. Gwaggo haule ma ta kalleta tana mamakin maganar da tayi.
"Rasuwa kuma?" Gwaggo haule ta tambaya.
"Eh gwaggo.... Tabbas cikin yaran ne wani ya rasu... Ko dukan su ne? Kadan daga iko da kudira ta ubangiji..."
"Hakane .... Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.. Naja waye ya rasu?"
Najan Isubu ta daga kai ta kallesu. Hawaye daya na bin daya
"Kamalu ne gwaggo... Allah ya karbi ran kamalu.."
Umma Hadiza ta sauke zuciya. Ta ja salati
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Allah ka jikan kamalu .. Allah kayi masa rahama. Allah ka gafarta masa. Allah ka kyautata makwancin sa. Ka sadashi da annabin rahama... Allah ka bashi nasarar amsa tambayoyin kabari. Allah ka yalwata kabarin sa. Allah kasa aljannar firdwas ce makoma agare shi . Da dukkanin musulmai baki daya... Aamin" Umma Hadiza ta fada. Batayi hawaye ba. Amman idanunta sun kada sunyi cazir. Da alama kukan zuci take yi.
"Aamin Aamin Hadiza..."
"Kiyi hakuri Hadiza ..."
"Hakuri mun godewa Allah Naja'atu. kowa ai dan haka ne... Ko ba jima ko ba dade . Lokacin sa ne yayi..."
"Hakane.. Allah ya gafarta masa. "
"Aamin...."
"Na yafe maka kamalu .. Duk kuwa da babu abunda ka yi mun. A iya sani na da wanda ban sani ba .. Na yafe maka duniya da lahira Kamalu... Allah ya gafarta maka...."
Najan Isubu kawai zuba idanu tayi tana bin Umma hadiza da kallon namijin kokarin da tayi.
Gwaggo haule ta mike ta shiga daki ta dakko hijabi ta zura . Can sai ga mijinta ya shigo yanata sauri shima .
Suka gaysa da Najan Isubu . Ya shiga daki ya dakko hula ya fito..
"Malam kai ma ka ji ne?"
"Eh wallahi .. Jana'iza karfe 10. Allah ya jikan kamalu ya rahama masa. Ya dace da yardar Allah. Don yaran nan sam ba yada matsala. Baya fada da kowa. Ba shi da hayaniya ba rashin kunya. Ba bin yaran banza . Insha Allahu aljanna ce makoma agare shi.. Anata yabon sa"
"Aamin Yaa rabbi .... "
"Allah ya baki hakurin rashi Hadiza..."
"Aamin ..."
Ya fuce da sauri ya bar su. Kafin su ma su tattara komai su barshi. Su fita
"Ni Marka tace kar na soma takawa kofar gidan nan...."
"Mutuwa ce yanzu ai Hadiza. ."
"Ta zama dole ai ... Dole ki je Hadiza.."
Suka gangara suka samu adaidaita suka shiga. Ya kai su har kofar gidan. Mutane sun fara taruwa sosai.
Maza nata alwalar sallar Janaza. Suka shige cikin gidan.
Waheedah na ganin Umman su tatafi ta rungumeta tanata kuka. Umma Hadizan ta sake dakewa bata zubar da hawaye ba. Yayin da labbanta keta kwarara adduar samun ceton rahamar Allah ga kamalu.
"Shigo kuyi sallama Hadiza ... Waheedah kema.. Kai Najib zo."
Umma Hadiza ta shiga ciki. Fuskar Kamal ce kawai a bude. Yayin da dukkanin jikin sa ke a rufe da likkafa ni.
"Allah ya gafarta maka kamalu.. Allah ya yafe maka dukkanin zunuban ka.. Allah yasa aljanna ce makoma agare ka. Allah ya maka rahama. Allah ya maka rahama. Kyawawan halayen ka nagari Allah yasa su bika Kamalu.. " Tana karasa fada ta mike ta koma tsakar gidah kan tabarma ta zauna
Waheedah da Najib kuwa sai da akayi da gaske aka bambare su daga cikin gawar aka fita da ita. Aka sallaceta aka tafi da ita makabarta.
Yan taaziya sai tudadowa sukeyi anata yiwa Umma Hadiza taaziyyah. Masha Allahu ba wanda ke binsa bashi ba kuma wanda yake bi. Ya samu shedu da dama daga bakuna nagari
Yar tsalar da kunun dakyar gwaggo haule ta tasa Najib da Waheedah a gaba suka ci. Sauran akayi sadaka da su .
Nan da nan kuwa mutane keta kawo kayan abincin don samun lada.
Najan Isubu ta kira Indo ta sheda mata halin da ake ciki. Ya yin da indon ta sanarwa the Adams family.
Washegarin rasuwar kuwa Haj Hameedah da Nadra da indon suka zo gidan sukayi musu taaziyyah . Da sadakar buhun shinkafa da carton na taliya da jarkar mai da kuma dubu biyar.
Haka akai ta zaman makoki har na tsawon kwanaki. Kafin aka share makokin kowa ya koma inda ya fito.
Gwaggo haule ta tasa Waheedah agaba tatafi da ita. Najib kadai aka bari anan din.
Amman kullum abincin safe , Rana dana dare duk suna kawo masa. Hakama magungunan sa basa yankewa. Sosai ya kara samun kulawa. Musanman da yanzun shi kadai ne ya rage babu kamalu....
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
πππππππ
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ π _NA_
_NANA HAFSATU_ _(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:43__
_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._
__ A hankali ta shiga bude manyan idanunta. Ta sauke su akan Umma Hadiza dake zaune tana zuba sukari acikin kunu .
"Kin tashi.....?"
"Eh.... Umma." Ta miqe tana salati.
"Na so makara ..."
"Ai da naga kince kina hutu (al'ada) shi ya sa ban tashe ki ba."
"Ai ko na samu bacci . Godia nake Umman mu. Barka da safiya."
"Barka ka dai Waheedah .."
Kwandon sosan wankan su ta dauka da hijabin ta da ke jikin kyauren kofa
"Bari na watsa ruwa ."
"To afito lapia.."
"Aamin Umma."
Ta fice ta shiga cikin bandaki. Bandakin akwai kan famfo da ake amfani da shi. Nan da nan ta tara masa bokiti ya cika ta shiga yin wanka.
Sai data gama tsaf ta janyo auduga ta saka . Kana ta sauya kayan . Daga nan ta sake tara ruwa ta dauraye wanda ta cire. Igiyar da ake shanya a baya taje ta shanya.
"Waheedah..."
"Naam gwaggo .... Ina kwana?" Waheedah ta sunkuya ta gayshe da gwaggo haule da ta futo daga cikin daki.
"Lapia kalau Waheedah . Kin tashi lapia?"
"Alhamdulillah gwaggo..."
"Masha Allah...."
"Gwaggo kin fito....?"
"Eh Hadiza..."
Suka sake gaysawa bayan ta asubah da sukayi. Dakuna hudu ne agidan. Guda daga ciki da ke gefe shine wanda Umma Hadiza da Waheedah suke kwana acikin sa.
"Har kinyi wankan?"
"Eh na dauraye kayan dana cire ma." Cewar Waheedah.. Hannunta dauke da man shafawa na mai gurguwa.
Dan murmushi kawai Umma Hadiza tayi kafin tace.
"Zai sandare fa .." ta fada tana mai mata nuni da kunu da kosanta.
"Ai kuwa bari na zauna..." Ta janyo shi gabanta bayan tayi bismillah. Tashiga hadawa tana ci.
Tana karasa ci ta tattara yan kwanukan ta wanko su tas ta kife. Ta dauki tsintsiya ta share gidan baki daya.
"Sannu yar albarka.... Allah ya miki albarka Waheedah ."
"Aamin gwaggo..."
Turaren shafawar ta ta dakko bayan ta koma daki. Nan da nan ta murje jikinta da shi. Ta tsurawa kwalbar idanu . Yayin da idanunta suka cika taf da hawaye. Yaya Kamal kawai take tunawa.
Shi ne mai saya mata turaren. Da mai sayarda turarukan ya kawo layin su. Inde yanada kudi zai ce ya mata hadi a kwalba rabin shashi.
"Tsayuwar me kike yi ne?" Umma Hadiza ta tambayi Waheedah ganin ta chake a tsaye.
Waheedan tayi hanzarin goge idanunta gudun kar ta karyawa Umman tasu zuciya idan taga tana kukan.
"Ba komai abu na gyara..."
"Ko nayi gaba ne?"
"A'ah gani nan...." Ta fada da sauri hadi da zura hijabin ta .
A tare suka fita daga cikin dakin. Ita zata wuce makaranta. Ya yin da Umman zata tafi gidan aikinta na the Adams family.
"Har kun shirya?" Gwaggo haule ta tanbaye su. Fuskarta kumshe da fara'a.
"Eh gwaggo .."
"Eh...."
"To Allah yasa ku fita a sa'a. Tsautsayi da asara Allah ya kare .."
"Aamin gwaggo ..."
"Aamin.."
Har kofar fita ta bisu tanata addua. Ta Kuma dankawa Waheedah nera hamsin kamar ko da yaushe
"Gwaggo bakya gajiya? Angode Allah ya saka da alkhairi."
"Nagode gwaggo .. Allah ya kara budi "
"Aamin kuyi sauri mana."
Suka tafi sunata doka mata addua. Ita kuma ta koma ciki tana murmushi.
Adaidata suka hau ya kai su har bakin kofar jijjigaggen gate din layin the Adams family.
Suka sauka suka shiga cikin layin . Tsit ba hayaniya sai kukan tsuntsaye da kadawar bishiyu.
"Ki hanzarta Waheedah... Allah yabada saa da nasarar karatu."
"Aamin Umma...."
Ta shiga cikin gidan. Ita kuma Waheedah ta miqe zuwa makaranta.
Da sauri ta shige cikin makarantar tasu. Daga wasu biyu bayanta aka fara tsaron latti. Ta sauke ajiyar zuciya ta karasa ajin su.
*GIDAN MALAM NALADO*
Marka ce a gwaggafe ta saisaye zani tana mai taya Deluwa jifar danwake a kan wuta.
Inna Sa'adatu ta fito daga bandaki kenan. Taa hango sabuwar butar data saya agaban Deluwa . Akan idanunta deluwan ta dauka ta rage wutar itatun gefe .
"Kan babban bala'in can ..." Ta surfa ashariya hannunta akan bakinta
"Menene Sa'adatu ...?" Marka ta tanbaya tana kallon ta.
"Nifa na gaji da cin kashin da ake akai na... Deluwa shara ce kawai tayi ragowa da zaki kwakwaso ki zubata akai na. Ko ki daura kwanon abincin ki bisa kai na ki ci . Wane irin renin hankali ne wannan iyye? Wabillahil lazi sanyi nayi. Ki tambaya kiji. Da mutunci yayi gabas. Yamma nayi "
Deluwa ta tabe baki . Chas bata ce ba. Sai ma karban kudin wani yaro da yazo siyan Dan wake tayi. Tace ya jira ta zuba masa.
"Wato ga sauran kashin baqin duwawun ki ... Ina magana kinyi banza da ni "
"Ah... Wai menene ? Deluwa meke faruwa.?"
"Wallahi Marka bansani ba. Inaga da hannun hagu ta tashi..."
Inna saadatu ta sake bude baki. Ta kalli butar ta maqe maqe a hannun Deluwa sai kace tata. Ta riqeta gam. Hakan ya sake bakanta ran inna Sa'adatu.
Ta cire dankwalin kanta tayi damara dashi a kugu. Kana ta bude baki ta saki kukan kura. Zatayi kan Deluwa Marka tayi hanzarin rikota.
"Ah menene ya same ki ne Sa'adatu? Menene hakan fisabilillahi... ?"
Inna saadatu taja tsaki. Ta shiga kicinyar kwace jikinta daga riqon da Markan tayi mata.
"Ci ka ni Marka .. ci ka ni. Ina ruwan ki?"
"Ina ruwana. ? Haba Sa'adatu "
"Yo ai gaskia ne... Tunda matar nan tazo gidan nan ke da yayan ki kuke shisshige mata saboda tana bar muku kanzon tukwane kuna kankarewa."
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Sa'adatu ni ki ka maishe wa mai maula? Me kike nufi! Kinsan kuwa maganganun da ke fitowa daga bakin ki Sa'adatu?"
"Na sani sarai. .. karya nayi? Ba haka zancen yake ba?"
"La... Zahara'u kina ji?"
Zahara'u dake chuda kan ta da kumfan los batace komai ba. Ta cigaba da abunda take yi .
Inna Sa'adatu ta bangaje riqon da Markan tayi mata. Ta nufi Deluwa gadan gadan . Batayi aune ba jikake tassssss.
Ta wanke fuskar Deluwa da mari. Bata ajiye hannu ba Deluwa ta mayar mata da biyu kwarara tas. Kasss. Zafafa . Wadanda suka sa inna Sa'adatu jiri ta dafe bango tana mai bin Deluwa da kallo.
"Kan babban bala'in can .. Ni kika mara?"
Deluwa taja tsaki. Ta gyara tsayuwar ta tana girgiza kafa.
"Mari na kikayi na rama... Da guzurin sauran dayan . Yana nufin ke ba tsarar cacar baki na bace..... Akan wane dalilin zaki mare ni! Rainin har ya wuce ga baqaqen maganganu ya koma kan mari? Ba kanwar lasa bace ni. Ki bini a sannu.. "
"Haka kikace?" Cewar Inna Sa'adatu. Ta cika tayi fam
"Eh haka na ce... Ko kina da ja?"
"Zaki san kin debo ruwan dafa kan ki .." Inna Sa'adatu ta fada.
Ta duka ta dauki kwabin danwaken da ke gaban Marka ta kwalalar da shi a kΓ sa.
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun..... Ke Sa'adatu." Marka ta fada ganin ta asar da saadatun tayi....
Dariya ta sheqe da ita. Kafin ta juya saitin Deluwa. Ta daga yatsanta tana mai nuni da kwabin danwaken data malalar a kΓ sa. Cikin farin ciki da nuna isa ta shiga cewa,
"Wannan shine tukwicin dana baki...Akan sabuwar buta ta da kika dauka kike rage wuta da ita ..Gobe ma kya kara daukar abunda ba naki ba."
Tana rufe baki Marka ta shiga tafa hannuwan ta tana dafe habarta da dayan hannun.
"Wannan butar fa ni Marka da girman Allah ni na dauka na bawa Deluwa... Wallahi yarinyar nan sam batasan ta waye ba. Ni ce na dauka na bata..."
"A hayye nanaye ... To kinja mata..... Na meye zaki dauka mun buta? Kuma ma ni ba yadda zan ba. Tunda buta dai a hannunta na ganta tana rage cin wuta."
"Amman dai Sa'adatu baki kyauta ba..Asarar nawa kika yi mata akan buta?"
"Kiji ki Marka da wani zance... Ni ansan nawa na sayi tawa butar? Akan wane dalilin zaa dauka mun? Saboda kun hada dadi shine zaki fara wasu zantuka.. Ni ba Hadiza ba ce. Ato."
Tana karasa fada cikin fushi ta sunkuya zata dau butar a kΓ sa. Deluwa ta riqo butar itama. Suka daga kai suna kallon junan su a duqen kafin Deluwa taaaaaa.......
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
πππππππ
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯° [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ π _NA_
_NANA HAFSATU_ _(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:44_
_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._
___ *Ta* riqo butar itama. Suka shiga ja in ja... Sai data bari inna Sa'adatu ta riqe butar da karshen karfin ta. Sai ta saki riqon ita da tayi
Inna saadatun ta bugu da bango. Da sauri ta dafe goshinta da hannu saboda radadin zugin da ya fara mata na zafi.
Deluwa tayi murmushi tana girgiza kai . Cikin fushi inna Sa'adatu tace,
"Baqar muguwa. Aniyar ki ta bi ki."
Chapter notes and social links
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_