Kenza eBookz

Farhatul qalbi complete - Chapter 16

Farhatul qalbi complete - Chapter 16

Farhatul qalbi complete Chapter 16: Farhatul qalbi complete Chapter 16. Zama tayi akan kujera tanata murmushi

4,486 words

Zama tayi akan kujera tanata murmushi

"Ina wunin ku??. Ummimi na, Maa da Aunty Ai..."

Suka amsa. Ya yinda ta juya ta kalli Umma Hadiza.

"Ina wuni?"

"Lapia kalau amarya."

Can dai sunata zaune jugum. Waheedah ta miqe ta shiga kitchen din. Ta shiga dakko trays da plates da cokula da serving spoons.

Ta koma ta dakko warmers na abincin ta ajiye musu akan dinning dake gefen parlorn.

Ta sake bude freezer ta debo musu ruwa da lemo ta ajiye.

"Ahh .. Har na manta ma... Sannu sis." Waheedah ta fada.

Haj Hameedah na hankalce da su. Ta dubi Zayn da ke gefe, Kan sa akan tv. Ya yin da Ahlam ke danne danne a wayarta.

"Maa ga abincin can kar ya huce."

"Toh Waheedah sannu da aiki kinji?"

"Yauwa..."

Miqewa sukayi suka nufi dinning din. Ita dai Umma Hadiza bata tashi ba.

"Zo mana Hadiza.."

"Hajia nan din ma yayi .." ta amsa ta cikin ladabi.

Kan dinning table suka nufa. Suka ja kujeru suka zazzauna.

Ahlam tayi serving dukkanin su abincin.

"Waheedah zo ki zuba... Ki zubawa Umman ku ma"

"Tohm."

Karasawa tayi dinning din. Ta janyo plate babba ta zuba musu abincin ita da Umman ta.

"Ki kara muku mana..."

"Ya ishe mu haka...."

Ta koma can inda Umman tasu ke a zaune ta ajiye plate din abincin a gaban Umman .

"Sakko muci Umma..."

"Tohm Waheedah..."

Kasan carpet suka zauna. Abincin na tsakiyar su. Su kayi basmala suka fara ci.

Zayn na kan kujera ya kurawa tv kallo.

"Ah ina naka abincin? Zuba ma sa yaci Ahlam."

"Na koshi Ummimi."

"Dan Allah ka karba ka ci ka ji?"

Zai sake cewa wani abun . Haj Hameedah ta masa kallon kar ya yi haka. Ya dan kakaro yake yace,

"Toh.."

"Yauwa... Sannu Ahlam da aiki. Abinci yayi dadi." Ummimi ta fada tana mai sake yanko loma ta saka a bakinta.

Ahlam din ta danyi yake. kafin tace,

"Ai bama ni nayi ba Ummimi."

"Ai ho to... Na wajen sayarda abinci ne?"

"Ah'ah Waheedah ce ta yi komai..." Ta karasa fada hadi da sa ka hannu ta nuna Waheedah da yatsanta.

"Ah masha Allahu... Lalle tayi kokari."

"Sosai ma. " Cewar Hajia Aisha.

Ita dai Haj Hameedah murmushi kawai ta ke.

Ahlam ta zuba abincin a plate ta kai gaban Zayn. Yana daga zaune ta tsaya akan sa kerere. Da plate din abincin tamkar zata dora akan sa

"Gashi...." Hannunta daya na kan wayarta . Dayan kuma tana miqa masa abincin saura kadan ya bare.

Ya sa ka hannu ya karbi abincin ya ajiye a gefe. Kallon abincin ya tsaya yi. Gashi dai komai tsaf tsaf. Kamshin abincin na ta dukan kofofin hancin sa.

Amma tsantsamin sa da kuma aqidar sa ta qin cin abincin da ba na Maa ba yasa ya kauda fuska kawai yana jan kasan leben sa.

Ahlam ta koma ta zauna akan kujera tanata scrolling pages a Instagram. Sai bude videos take yi tana kalla.

Waheedah ta tattare inda suka ci abincin ta kai kitchen. Su Maa na karasa ci ta gyara wajen ta kai kwanukan kitchen tana dauraye wa.

"Wai baka ci abincin ba ka barshi yanata sandarewa?"

'Zan ci....." Ya fada ahankali yana mai kallon idanun Haj Hameedah mahaifiyar su.

Cokalin ya dauka ya saka acikin abincin. Sai yamutsa fuska yake. Amman tunda ya fara taunawa sai yaji wani dadi da gardi na fita na abincin.

Ya samu kan sa da sake ciko loma ya saka a bakin sa. Tabbas gaskia ne ba mafarki yake ba. Bai taba cin abincin mutane me dadi irin wannan ba idan har ka tsame na mahaifiyar su Haj Hameedah.

Ya shiga zura loma bayan loma yanata ci. Yana korawa da lemo. Sai daya cinye tas tukun sannan ya ajiye plate din yana goge bakin sa da tissue.

"Alhamdulillah..." Ya fada yana sake shan ruwa.

Waheedah ta sake fitowa daga kitchen tanata dauke kwanukan da bata dauka ba dazu. Ta hada da wanda ke agaban Zayn . Kitchen ta kai su ta wanke su tas. Tatattare kitchen din . Ko'ina tsaf. Sai da ta tabbatar ta gyara komai sannan ta koma dakin nan ta shiga bandaki ta watsa ruwa.

Ta mayar da kayan makarantar ta. Rigar Kuma ta ninke ta dauka ta fita daga kitchen dakin ta koma parlorn. Daga gefe ta tsugunna.

"Mu tafi ko...?" Ummimi ta fada tana kallon Haj Hameedah.

"Tohm Ummimi yadda kika ce."

Mikewa suka yi baki daya. Ciki harda Waheedah dake gyara zaman rigar hannun ta.

"Sis ga kayan. Nagode."

"Wane kaya?"

"Rigar da kika bani na saka nayi aiki da ita.."

"Oh . Ni ba aro na baki ba Waheedah... Kyauta na ba ki.. kinji ko?"

"Eh. Nagode Allah ya saka da alkhairi ya kara miki arziki mai tarin albarka Amin. "

"Amin..."

Zayn yana sauraron maganganun da su ke. Yanata mamakin adduoin da Waheedah ke yi.

Ya danyi murmushi kawai kansa akan tv.

Waheedah ta matsa wajen Haj Hameedah tana gaya mata alkhairi da Ahlam ta mata na bar mata kayan da tayi.

"Tohm Ahlam godia muke... Waheedah tace na miki godia."

"Kai ba komai Maa. Ai an zama daya."

"Angode kwarai. Allah ya saka da alkhairi." Cewar Umma Hadiza dake yaba kyautar.

"Amin."

Fita sukayi dukkanin su wajen. Direban ya tashi motar. Suka shiga baki dayan su.

Ya yin da Ahlam da Zayn ke ta waje a tsaye suna musu sallama . Har suka fice daga gidan tukun sannan Ahlam ta juya ta shiga ciki.

Zayn ya bita a baya shi ma. Ko da ya shiga bata parlorn. Ba kuma ta kasan baki daya.

Saman ya haye da sassarfa. Ya bude dakin ta ya leka. Tana kwance akan gado kamar ruwa.

Tayi dai dai da ita. Hijabin na gefe. Ita kuma ta sake barrarrajewa akan gadon bayan ta tukwikwiye jikin ta da bargo.

Rufo mata kofar dakin yayi. Ya koma kasa ya zauna akan kujera. Tv nata yi. Idanun sa na kan tv. Amman zuciyar sa ta tafi duniyar tunani. .....

_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ πŸ’ž _NA_

_NANA HAFSATU_ _(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_PG:47_

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._

___

*GIDAN MALAM NALADO*

Karar gudar shigowar mutane ce ta sa inna Sa'adatu hanzarin toshe kunnuwanta. Duk a tunanin ta amarya aka kawo a layin bayan su

Cikin bacci karar ta isheta. Ta kuma tabbatarwa kanta tabbas yar iskar rediyon Marka ce ke yi.

Don haka cikin fushi ta mike ta fita daga cikin dakin nata.

Ja tayi ta tsaya a lokacin da dandazon wasu mata suka tunkari dakinta suna sallama.

Ta bisu da idanu tana mamaki. Auren wa akeyi haka?

"Shiga da kafar dama...." Matan su kace da matar da ke lullube cikin mayafi wai ita amarya

Daurewar kai tasa inna Sa'adatu ta basu hanya suka shiga dakin nata. Suka gaysa ita dai tanata binsu da kallon mamaki

"Allah ya baku ikon zama tare da juna, Allah ya kauda fitina a tsakani..."

Cewar wata babbar mata dake tsugunen a bakin kofa.

"Eh wallahi delu batada hayaniya. Da yardar Allah zaku wanye kalau. Amatsayin ki na babba kima matar farko dan Allah kece agabanta. Ki dubi girman Allah idan tayi ba daidai ki tsawata mata..."

"Bangane ba..." Inna Sa'adatu ta tanbaye su cikin karshen gaskiyar ta.

"Wannan din abokiyar zaman ki ce."

"Abokiyar zama....?" Ta sake maimaitawa tana tauna maganar.

"Allah de ya hade kan ku ya kauda fitinah a tsakani ."

"Ah wai wace irin magana ce wannan? Idan batan kai kukayo ku tambaya a nuna muku inda zaku je. "

"Banan ne gidan malam na lado ba?"

"Nan ne...Ya akai?"

"To shine dai aka kawo masa amaryar sa. "

Inna Sa'adatu ta ja tsaki ta fice daga dakin tana mai dokawa sunan Marka kira.

"Marka .. marka... Kina Ina ne wai?"

"Ga ni nan..." Marka ta amsa ta. Tana tsakiyar sauran yan kawo amaryar sunata hira.

"Bangane ba .. waye yayi aure?"

"Mai sunan malam mana..,"

"Kan babban bala'in can .. Au me?"

"Aure ."

"Aure fa kika ce? Malam dinne zai yo aure? Meya ke da shi meya tara da hat zai karo aure.?"

Marka ta ja tsaki tana girgiza kai...

"Zancen dai kenan... Yayi aure."

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun...Muga wacce shegiyar ce ." Ta kwasa a guje tayi cikin dakin ta.

Tsakiyar mutanen taje. Ta yaye mayafin da ke jikin amaryar. Wa zata gani?

Deluwa dai wadda ta kama hayar daki. Ta Kuma ke sayarda abincin sayarwa. Wadda sukayi fada akan buta, Ta zubar mata da kwabin danwake. 🀣

'bangane ba....," Inna Sa'adatu ta fada. Hannunwanta biyu dafe da kirjin ta . Ranta amatikar razane. Duk ta firgice. Wannan shine babu zato ba tsammani.

"Kai ! Kai!i Kai... Wannan ba karamar kasurgumar munafuka ba ce ke.... Kinada hassada da tsantsar mugunta.. Na meye zaki auren miji? Akan wane dalilin?... Iyye? Daman can daya bakin ku daya. Da Markan da shi malam din. Wallahi ni daman na san wannan rawar takashin da Marka keyi akan ki na san da kwai wani abun a kΓ sa. Wohoho. To ta yanke ta gille dai. Ba dai kin shigo gidan ba? Mu zuba mu gani. Wuya tallan turmi."

"Allah ya baki hakuri Yaya..."

"Yaya? Na hada ki da yayar na kwarfe. Kiji Wani sabon salon munafurci. Wai Yaya.? Allah ya Yayaba miki masifa da balai."

Yan dakin suka mata caaaaa. Takaici yasa inna Sa'adatu jan hijabin ta dake jikin kofa ta fice daga gidan.

Ya yinda aka raka Deluwa dakin ta . Sannu ahankali yan uwanta da abokan arzuka suka fara watsewa . Har dai gidah yazama sai yan gidan kawai idan ka tsame inna Sa'adatu da bata nan.

Tana fita ta wuce majalisar su malam na lado. Mutane nata yi mΓ sa Allah ya sanya alheri.

Inna Sa'adatu ta kutsa ta cikin mazan ta ta shiga ta janyo malam na lado daga cikin su . Yanata janye hannun ta dada kama masa aljihu tana jansa.

"Menene hakan wai?"

"Gaskia malam kai bakin munufiki ne."

'haba Sa'adatu. Wanmnan wace itiyar rayuwa ce haka. Zaki wulakanta ni acikin abokai na. Dubi yadda sukayi cirko cirko suna binmu da kallo. Suna kuma sauraron abunda muke fada."

"Kunyar duniya kenan ma. Kafin kaje ka hadu data azabar lahira saboda baqin halin ka da muguntarka. "

'cikani wai menene haka wai?"

"Allah ya kwashe maka albarka malam."

"Sa'adatu wai meye haka eh...?" Ya fada da karfi

Abokan sukayi kansu. Ta daga musu hannu tana nuna shi.

"Munafiki ne. Annamimi ne, Kuma bakin mugu.."

"Assha. Assha. Dan Allah ki dena fadar haka. " Cewar malam Isubu mijin naja.

"Idan ba tsabagen tsagwaren rashin mutunci da tsantsar butulci ba. Me na rage shi da zeyi aure? Kuma ze karo din be fadamun ba. Ina cikin bacci ma jiyo hayaniyar yan kawo amaryar.. Wannan ya dace.?"

"Kiyi hakuri....." Suka shiga bata baki suna bata hakuri.

Tayi kwafa kawai ta juya ta koma gidah. Tana shjga zaure ta hadu da Deluwa.

Ta gogeta zata wuce . Deluwar ta hana ta hanyar riko gyalenta.

"Cika ni...."

"Dan tsaya mana... Yayata."

"Algunguma .."

"Kash Ina ki tsaya kin ki. Bakyacin ribar zance..... Ina kwanaki da mukayi cacar baki da ke akan butar ki da Marka ta kawo?."

"Matsalar ki ce ni sau ni dalla ..."

"Ki saurara .. Idan baki mance ba . Kin kirani da shashasha matsoraciya.. Na ce miki ki jira ramuwa ta... Dan ramuwar gayya tafi ta gayya zafi... Wannan itace ramuwar da na ce ki tsumayi zuwan ta . Na aure miki mjii har gidah.. sirikar ki da mijin duk sun juya miki baya.... Gidah yazama namu gaba daya.... Daga haya na haye igiyar auren me gidan..🀣. Me yafi wannan ramuwar dadi? Uhm.... Yayasko... Yayata mai buta."

Inna Sa'adatu maganganun Deluwa sun tsaya mata a rai. Sun taba mata zuciya. Sun raunata damuwarta. Hawaye ya taho ta danne hade da cijewa tace,

"Miji ne dai ko? Gaki nan ga shi... "

"Miji, uwar miji da gidan baki daya...Ga kuma karin ki amatsayin abokiyar zama na.. Riba uku"

Inna Sa'adatu ta tattare ta fisge mayafin ta da Deluwa ta riqe tayi gaba tashige dakinta tanata mita kasan makoshi.

Baki daya tun daga ranar ta nemi farin cikin zuciyar ta ta rasa. Zuciyar ta ta rubanya da baqi mai ciwo da tsantsar na dama...

To haka rayuwar take.., sai dai fatan Allah ya yayi mana me kyau Amin...

*BAYAN SHUDEWAR WASU LOKUTA*

*Dare* ya zama safiya. Safiya ta zama rana, Ya yinda rana kan zamo yammaci. Kwanakin mu nata shudewa. Lalle Allah buwayi ne gagara misali. Kuma mai kowa da komai .

Cikin ikon sa da qudurar sa hadi da buwayar sa. Waheedah Nalado ta kammala zana jarabawar makarantar kare sakandire. Wato ssce. Wanda ake kira da senior secondary school examinations na waec da neco.

Da rarrafe yaro kan girma. To hakan yake a bangaren na waheedah. Ta zama cikakkiyar budurwa mai jini a jika. Kyawunta ya kara yalwatuwa.

Hakama cikar gashin kan ta. Hasken fatar ta. Dara daran idanun ta. Dan karamun bakin ta. Bugu da kari ta sake tsawo tubarkaAllah.

Duk wanda ya daga kai ya kalli Waheedah a karo na farko. To babu shakka sai ya sake daga idanu ya kara kallon ta a karo na biyu. Sam ba gajiyawa. Tanada shiga rai ga duk wanda ke tare da ita ko ya santa.

Mutane na yabawa da dimbin hankalin ta da nutsuwar ta da kaifin girmamawa da tarbiyyar ta. Ga fara'a da ta wuce duk inda mutum kan tsammata.

Waheedah na da ilimi na boko dana islama. Domin har sun sauke Qurani a tahfiz din su. Hakama ranar asabar da lahadi tana zuwa wata islamiyyar ta matan aure.

Ranar litinin zuwa jumu'ah tana zama da kwana ne awajen gwaggo haule. Yayin da ranakun asabar da lahadi tana kwana ne agidan su na malam na lado....

_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ πŸ’ž _NA_

_NANA HAFSATU_ _(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_PG:48_

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._

__

*GIDAN MALAM NALADO*

*Waheedah* na tsakar gidan su tanata share share. Kawayen ta suka shigo bakunan su dauke da sallama. Tsantsar farin ciki ya bayyana a fuskokin su.

Tana ganin su ta tsaya da sharar. Ya yinda tsintsiyar ke hannun ta na dama. Kallon su take tana son magana ta kasa .

Basira da fanna suka sheke da dariya. Cikin tsantsar farin ciki marar misaltuwa suka rungumeta a tare.

Ta cillar da tsintsiyar hannunta ta kankame su. Cikin muryar zakuwa ta dube su,

"Ya ake ciki...? "

"Kin samu admission Waheedah .. kin samu." Fannah ta fada tana mai sake kankame Waheedah cikin farin ciki.

"Waheedah sunan ki ya fito.kin tsallake...."Basira ta fada tana dariya itama.

Waheedah ta dubi gabas tayi sujjada. Hawaye daya na bin daya na farin ciki

"Allah ka karawa annabi daraja, Aamin. Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillahi da'iman wa Abadan. Allah mungode maka da wannan babbar kyauta.... Ni Waheedah na samu nursing...? Rabbi ka dafa mana ka iya mana..... "

"Aamin . Amin" suka hada baki wajen amsa adduoin ta...

Inna Sa'adatu dake leken su ta window ta tabe baki ta koma ta kwanta akan katifa tana jera tsaki.

Mikewa tayi ta sake rungemu su kafin ta saka kasan rigar ta tana goge hawayen dake zuba. Cikin farin ciki ta sake cewa da su,

"Nawa kawai ku ka fada .... Ku fa? Sai kace ni kadai ce ke neman admission din? " Ta jefe su da hararar wasa.

Fanna ta tuntsire da dariya sannan tace,

"Muma duk mun samu..."

Sake rungume juna sukayi sunata murna. Cikin haka Marka da Deluwa suka shigo.

"Ife ifen menene haka har waje ana jiyo shewar ku?"

"Mun ci jarabawar shiga makarantar school of nursing ..."

"Ah masha Allah.... Allah yasa ku fara a saa " Deluwa ta amsa su tanata murmushi.

Domin babu lefi suna mutunci da Waheedah. Ita kan tayata aikin komai idan tazo kwana. Da sauran hidindimu da ke deluwan ta samu karuwa juye ne batayi ba. Cikin har ya dan tasa. Kuma kullun tana basu abinci har da Najib.

Marka ta ja tsaki tana yamutsa fuska.

"Sai kuyi tayi ai... Boko ko jaraba. Bokon ce agaban ku ba aure ba. Gandama- gandama da ku. Meya kwan ku rufawa junan ku asiri ku tsaida mazaje kuyi aure? Kun gwammace ku yita yawo a titi da sunan karatu. Allah shi kyauta." Ta shige cikin dakin ta tanata doka mita.

"Aunty akwai abunda zan tayaki da shi ?" Waheedah ta tambayi Deluwa.

"A'ah Waheedah... Babu komai"

"Tohm.."

Daki tayi saurin shigewa. Najib yana kwance akan katifar sa. Ya yin da hannun sa daya ke kan kafarsa yana matsawa.

"Sannu Najib..."

"Yauwa Yaya.."

"Kana sauraron mu ko?....." Ta karasa tanbayar sa tana murmushi..

"Yanzu na tashi ..."

"Sannu.... Ya jikin naka?"

"Da sauki.."

"Allah ya kara sauki . Amin"

"Amin..,"

"Na samu admission fa .."

Mikewa yayi daga kwancen da ya ke. Fuskar sa lullube da farin ciki.

"Har na hango ki cikin farin uniform dinnan..."

"Kai de bari Najib... Alhamdulillah."

"Na tayaki murna Yaya... Allah ya cigaba da kara miki nasara. Ya bada sa'ar karatu."

"Amin Aamin .."

"Umma ta sa ni?"

"A'ah yanzu na ke son zuwa na gaya mata... Bansamu naje na dubo ba... Su Basira ne ke sanar mun"

"Masha Allah ... Alhamdulillah."

Kayan ta ta ciro da ke cikin wata leda viva. Ta fice wajen tana,

"Kuyi hakuri kawayen amana.... Bari na sauya kaya "

Dakin su Zainab ta shiga ta sauya kayan. Ta shafe jikinta da mai. Ta goga ruwan alumun a hammatar ta.

Sannan ta shafe jikinta da turaren ruwa. Duk sanda ta shafa ko ta dauki kwalbar sai ta tuno yayan su marigayi Kamal.

Yanzun ma hakan ne ya kasance. Siraran hawaye suka zubo mata kan fuskar ta. Ahankali cikin rawar murya tace,

"Allah ya jikan Yaya Kamal.. Rabbi ka gafarta masa. Ka shayar da shi ruwan alkausara. Rabbi kasa yana aljannatul firdwas madaukakiya da shi da sauran musulmai baki daya, Amin "

Da sauri ta karasa adduoin ta sauya kayan nata zuwa wanda ta dakko. Bata wani tsaya kwalliya ba. Ta dai shafa farar hoda da man lebe.

Ta yi daurin dankwalin channel o. Ta yafa wadataccen mayafin da Umman su ta bar mata.

"Muje..."

"Kawata kina lokaci. ." cewar Basira.

"Kece me yin lokaci tawan..." Waheedah ta fada tana murmushi.

"Gaskia Basira ta fada... Kina kamshi muna bin ki da humra. Kinga yadda kika tsatso kyau tawan? Sai ma a uniform. " Fannah ta fada tana dariya

Ita dai Waheedah murmushi kawai take. Tayi wa Deluwa sallama suka fice bayan ta sake duba jikin Najib.

"Ni fa gida zan wuce ...." Basira ta fada .

"Kai kawata...."

"Allah tafiya .kawata "

"Eh kinsan ni kadai ce basu dawo ba ."

"Eh kuwa."

"Nima dai tafiyar zanyi. Zan tsaya shagon Na'Ateeku na sayo cefanen da Umma ta bani."

"To shikenan... Idan na dawo zaku jini. Godia nake kawayen amana .. Allah ya albarkar ci zumuncin mu. Aamin"

"Aamin Yaa rabbi ."

"Aamin Aamin ."

Mikewa tayi kanta tsaye zuwa hanyar new gra shurah inda gidan aikin Umman su yake.

Ta dade bata je ba . Rabon ta da zuwa tun suna rubuta jarabawar kare sakandire.

Bakinta dauke da adduoi ta karasa shiga layin. Manya manyan motoci suna fa ke a kofar gidajen unguwar. Kanta tsaye ta shiga cikin gidan na The Adams Family....

Taci saa kuwa kofar sashen baa kulle take ba. Wata mai aiki tafuto daga cikin gidan tana tattare kofar.

"Sannu Ina wuni...?"

"Lapia kalau.... "

"Ya aiki?"

"Alhamdulillah..... Ki shiga suna ciki."

"Tohm..." Ta amsata cike da ladabi.

Ta kutsa kai ciki bakinta dauke da sallama.

"Wa'alaykm Salam.... Ahhh wata sabon ga ni..." Nadra tafada tana mikewa tsaye..

Bata da kyama ko ganin kaskancin na kasa da ita.

"Ina wuni sis....?"

"Alhamdulillah...dear sis."

"Maa ga Waheedah... Umma ga Waheedah.."

Daga kitchen suka fito a tare. Haj Hameedah da Umma Hadiza. Fuskokin su fadade da murmushi.

Ta tsugunna har kasa ta gayshe da su. Suka amsa duka fuskokin su a sake.

"Lapia lau...... Waheedah na." Maa ta fada tana murmushi.

"Alhamdulillah....." Umma Hadiza ta amsa ta.

"Je ga abinci can a dinning ki zuba kici." Haj Hameedah tace da ita.

"A koshe naki Maa."

"To kya tafi da shi... Kwana biyu kin manta da mu. Sai yau?"

"Tuba na ke Maa..."

Zama tayi tanata lankwasa hannayenta kafin ta sake cewa,

"Na samu admission a school of nursing.......

_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull