Farhatul qalbi complete - Chapter 28
Farhatul qalbi complete Chapter 28: Farhatul qalbi complete Chapter 28. "Ahlam.... Dearest wifey na. Ni ya dace nayi fushi da ke fa... Baki mun magana ba…
4,423 words
"Ahlam.... Dearest wifey na. Ni ya dace nayi fushi da ke fa... Baki mun magana ba at all tun a gidan mu. Sannan na dakko ku a mota na kawo ku. Har ya zuwa nan still baki ce mun ci kan ka ba. Na shigo nan wajen ki kika ba banza ajiya na. Na tafi daki na... Please ki dai na jin haushin Waheedah. Wallahi Waheedah bada masaniyar ta aka auramun ita ba. Waheedah batasan ni ne wanda aka aura mata ba sai bayan an kai lefe ranar da aka daura auren... Har ca tayi na same ki ki umarce ni na rabu da ita. Ba zaki gane ba ne duk yadda zan fada. Amman tana ganin kimarki da dattakon ki da girman ki ... Inason ki ajiye a doron zuciyar ki wallahi Waheedah bata ci amanar ki ba. Ahlam na fara kaunar Waheedah tun kafin a daura mana aure da ke. Wannan shine zancena gaskiya. Idan da wanda zaki ji haushi ni ne ba ita ba. Sab..."
"Karka karasa.... Daman na dade da sanin har yanzu babu kauna ta acikin ka...Ka tsane n ...."
Bata karasa ba. Ya hade bakin su waje daya. Duk yadda Ahlam ta so yakice nata. Zayn ya hana. Ta hanyar tallabo fuskar ta da hannun sa. Don bayason yayita bata hakuri ta kalamai. Gwara ya kashe mata jiki gaba daya.
Sai daya ga ji don kan sa tukun sannan ya zare nasa. Yana mayar da numfashi. Hade da sakin murmushi .cikin muryar lallashi yace,
"Uwargidah ran gidah.... Uwargidah sarautar mata. Uwargidah kujerar tsakar gidah... No matter what happens, you will always remain my biggest priority. I promise never to disregard your wishes again. Will you forgive me for what I have done? Ahlam, Wallahi. I never meant to insult you, hurt you, or put you through pain, and I promise to never do this again. I am sorry, please forgive me...Kin yafemun? Uhm? "
Yana magana yana goga hancin sa akan nata karan hancin. Kamshin turaren jikin su nata dukan hancin su. Ya bada wani sanyayyan kamshi mai matukar sanyaya zukatan masoya.
"I love and miss you....." Ahlam ta fada tana mai saka hannu akan fuskar Zayn..
"I love and miss you too ." Ya fada yana mai lakuce mata kumatu.
"Ba wani nan..." Ta fada tana dariya.
"Kin manta favourite buddy na ce ke? Tun kafin ki zama mata agare ni"
Ta danyi murmushi. Zayn ya sake janyota jikin sa. Ya gyara masu kwanciya. Ya saka kanta akan kirjin sa. Ya yinda hannun sa ke shafa kwantaccen gashin ta da ke kamshi.
"Ki amince mu yi tsaftatacciyar soyayya. Domin Ahlam, a duniya babu abun da ya kai samun masoyi dad'i, Buri na yanzu bai wuce na ganin hadewar kan ku da Waheedah ba. Zanyi alfahari da ku a duk inda na kasance..."
Ahlam ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Kafin tace
"Ina kallon Waheedah tamkar Nadra awaje na. Muka sake kusanci ta hanyar dawowar ta gidah na gaba daya. Then all of a sudden ace itace wadda ka auro ? A karkashi na fa ta ke Zayn "
Zuciyar sa ta dan masa zafin kalamanta na karshe. Amman ya danne ya ce da ita,
"Ai na gaya miki ba wai dawowar ta gidan nan na fara kaunar ta ba. Zan iya ce maki ban san so ba sai akan Waheedah... Sannan Waheedah ba'a matsayin yar aiki aka bamu ita ba kema kin sani. Domin ba biyan ta muke ba.... Ahlam ki fuskanci gaskiyar zance. Dan Allah maganar nan ya kamata ki mata duba na tsakani. Ya kamata ace wadannan abubuwan duk an wuce su. Mu rungumi kaddara."
"Amma Zayn k..."
Bata karasa ba ya janye ta daga jikin sa zai tashi. Tayi saurin riko shi tana langabar da kai. Domin ita kanta tasan tsawon lokuta data diba bata tare da shi har jinya tayi awajen Ummimi . Tana matukar kaunar Zayn.
"Shikenan nayi shiru..." Ta fada kanta a kàsa.
Dan murmushi yayi. Ya koma ya kwanta.
"Abunda ya faru haka Allah ya kadarta. Sai fatan Allah ya kara mana zaman lapia da kaunar juna. Hadi da yalwar arziki da wadatar zuci . Ko?"
"Eh...." Ta amsa shi . Tana kallon fuskar sa.
Hannu ya saka ya kashe bedside lamp ya gyara kwanciyar su. Ahlam ta kankame shi sosai tamkar za'a kwace mata shi ..
Daga nan kida ya soma canza salo. Suka shiga bude wasu shafukan na soyayyar su.
Zayn yayi mamakin yadda Ahlam ta ke bashi hadin kai ba tare da kosawa ba kamar a baya.
Nan da nan kuwa suka shiga faranta wa junan su. Zafafan kisses Zayn ya shiga showering jikin Ahlam da su.
Ya kuma ji ta yadda yake muradi. Domin tasha gyara awajen Ummimi. Ta kanas aka dakko mata me gyaran jiki ta gyareta ciki da waje.
Ranar dai saboda tsabar rashin juna da sukayi. Na ramakon kaunar da suka nunawa juna adaren jiya har makarar sallar asubahi suka yi.
××××
Waheedah dakyar ta iya tashi alarm nata dokawa. Taci mamaki da Zayn bai tashe ta ba yau . Allah ya temaka ta seta alarm.
Domin shi ke tashin ta sai kuma ya wuce zuwa masallaci. Amman hakan ya mata dadi gudun tasowar fitna. Kafin Ahlam din taji haushi.
Tanata sauri ta dauro alwala tayi sallah. Ta kwanta akan sallaya bacci ya dan dauketa na yan wasu mintina kafin ta mike ta shige bandaki.
Tayo wanka saboda lectures din safen da zatayi. Ta zura kayanta bayan ta shafa mai. Ta goga hoda sama sama da man lebe bayan ta zizara kwalli
Kitchen ta bude ta shiga. Cikin sauri ta tafasa shayi ta zuba a flask. Ta kai kayan tea din kan dinning area da bread ta ajiye da Nutella/spread.
Tana cikin gyara zaman mayafin ta. Sai ga sakkowar Ahlam din da Zayn a tare. Idanun sa fes akan Waheedah .
Sai sako yake aika mata ta kallon da yake bin ta da shi. Tayi azamar kauda kanta gefe .
"Ina kwanan ku?" Ta gayshe su a tare cikin ladabi
Zayn ya nufeta da sauri yana murmushi. Zai rungume ta ta ja baya da sauri. Ahlam na hankalce da su ta kauda kai gefe
"Zan tafi lectures ne. Ban dade da shiryawa ba. Na kusa makara ne. Ban samu na hada breakfast ba. Sai tea kawai da bread."
"Sannu da kokari, My Baby."
Ita dai ta kakaro murmushi kawai. Tayi hanyar fita,
"Na tafi school."
"Ki jira ni...."
Ya juya wajen Ahlam da ke zaune akan kujera.
"Zan kai ta school ..."
"Alright."
"Daga can zan wuce aiki...."
"Ba zaka dawo ka ci abincin ba?"
Ya dan ja kasan leben sa. Kafin ya daga kai .
"Zan dawo tohm. Bari na kai ta."
Da sauri ya fice har yana tuntube. Waheedah tayi gaba ta fice daga gate din. Bai tsaya jiran baba mai gadi ya tura gate din da kansa ya futar da motar.
Ya sake rufe gate din bayan ya fitar da motar daga cikin gidan. Tana tafiya ahankali tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki.
Ya tashi motar ya tuka har inda take tafiya. Ya zuge glass din.
"Shigo na kai ki ..."
Dan kallon sa tayi ta cigaba da tafiyar ta. Zayn abun ya so bashi dariya. Tun baa je ko'ina ba sun fara garashi kamar taya?
Ya daure ya sake bin ta da motar. Ya faka ya fito daga ciki. Yayi taku uku ya riko damtsen hannun ta.
"Nace ki zo na kai ki.... Meya faru ne?"
"A'ina ? Na kawo maka korafi ne?"
Ya girgiza kai alamar a'ah. Kafin ya riko hannunta ya jata har wajen motar ya bude ya sakata ya rufe. Ya koma wajen mazaunin driver ya zauna ya tashi motar.
Yana tuki yana bin ta da kallo.
"Nasan nayi lefi... Koma menene ni dai kiyi hakuri banason kina fushi da ni."
"Fushi? Meyasa zanyi fushi da kai?"
"Eh to ai ba haka kike mun ba. Baby."
Ta kauda kai kawai tana turo baki gaba. Ya faka motar a gefen titi yana binta da kallo.
"Zan makara fa..." Ta fada cikin muryar shagwaba.
"Mu tafi kenan?"
"Uhm."
Ya danyi murmushi tukun sannan ya tashi motar. Suka dauki hanyar makarantar su..
Hannu ya saka ya kunna speaker din motar. Wakar indila ta love story ce keyi ahankali...
"Wifey...I may not be able to say how much I love you or just how special you are to me, but I can say that my world is full of smiles and happiness whenever you are around. I love you with all my heart... Budemin na shigo kofar ZUCIYAr ki , Da sannu zan zamo dauwamammen FARIN CIKIN da zai bunkasa dukkan wani farin cikin rayuwar ki da mu baki daya.... Ki budemun..."
Dan dariya ce ta kufce mata. Ta yi tana kallon sa.
"Me zan bude?"
"Zuciyar ki.... Zan zamo miki *FARHATAL QALB* da zaki gasgata abun da nake fada.."
Hannun ta ta saka ta kare fuskar ta. Har ga Allah kalaman sa na dulmiyata cikin kunya. Har ta rasa ina yake nemo wadannan manya manyan kalaman na hausa..
"Wai meyasa kike jin kunya ta ne..?? Mijin ki ne fa ni... Ba yayan ki ba "
"Kai Yaya na ne?"
"A'ina na zama Yayan ki?"
"Ya Zayn..."
"Na raba ki da wani Ya Zayn. Ina mjin ki mu gama sharholiyar mu a gidah daya. Daki daya. Gado daya... Ki ce mun Ya Zayn? Noo! Ban karba baa wallahi."
Dariya ta kyalkyale da ita. Daman kuma dariyar yake son sakata. Don haka shi ma ya murmusa kafin ya sake cewa,
"Allah bana so. Ki sama mun pet name haka. Cuz I won't accept Zayn or ya Zayn ever again .. "
"Toh.."
Lakuce mata gefen fuska ya yi. A haka suka karasa cikin makarantar yana ta tsokanar ta.
Ya curo kudin abinci dana handout ya zura mata acikin jaka. Bayan ya bata zazzafar sumba guda daya Tayi masa godiya. Kafin ta sauka ta shige cikin aji
Bayason rigimar Ahlam. Da wajen aiki zai saboda lokaci ya ja Ya koma gidah. Yaci abincin a tsaitsaye .
"Me zaa dafa maka da rana?"
Sai da ya kware don mamaki. Tayi murmushi tana kada kai.
"Kome kika dafa... Less spicy."
"Alright..."
Tashi yayi ya sumbace ta a gefen fuska . Ya mata sallama ya tafi aiki. Yanata mamakin wai Ahlam ce me tambayar abincin da za'a dafa? .
Cike da farin ciki ya nufi mota ya wuce wajen aiki...Yana jin wata nutsuwa na zagaye shi da annushuwa. Hankalin sa a kwance. Yanata adduar Allah ya tabbatar da wannan zama nasu cikin zaman lumana da kaunar juna da kuma yalwar arzuka...
×××
Rayuwa na ta gudu, Haka zaman nasu ya kasance cikin Alhamdulillah,. Dan kowane rayuwar aure yana da ups and downs dinsa. Waheedah na kokarin bawa Ahlam girma. Ta na kuma bin ta da yadda ta so. Hakan ya sa Zayn ganin tamkar ana kwarar Waheedah. Duba da sai yadda Ahlam ta so take bin ta...
Ga tunkaho da nuna mata gadara da karfin iko akan gidan. Tamkar na ta ne ita daya..
Don haka Zayn ya tunkari mahaifan sa da maganar canzawa Waheedah gidah. Ko zaman lapia zai kara wanzuwa dik kuwa da ahakan ma Alhamdulillahi..
Sun amince da maganar sa. Don raba gidan ma wani kwanciyar hankalin ne. Da dai-daita tsakanin su. Domin wata kazantar da ba ka gani ba tsafta ce.
Nan da nan kuwa farfesa Adams ya ba wa Zayn wani gidah bungalow (flat/marar bene.) Kyauta. Mai kyau da shi a layin su Haj Hameedah din amman daga karshe yake shi ta baya.
Zayn ya saka aka fente masa shi. Aka sake gyara shi sosai. Ya zuba masa kaya masu matukar kyau da tsada.
Ya kuma samu Ahlam da zancen tayi murna kwarai da gaske. Domin tafu kaunar ita kadai anata gidan ta bararraje yadda take so..
Zayn bai gayawa Waheedah ba. Sai ana'i satin da zata koma. Suna zaune a parlour su ukun .
Suna kallon film din titanic. Yana shan fruits din dake gaban sa. Suna hira jefi jefi. Ya ce,
"Kun kasance duk abin da na taba so a soyayya. Kun sanya ni jin ana kaunata ta hanyoyin da ba zan iya tsammani ba. Ba zan taba neman karin ba. Ina son ku da ni tare har abada. Daga yanzu har zuwa numfashi na na karshe, zan ci gaba da kaunarku..Ina son ku sosai ..Na rasa yadda zan yi da son ku har ban san kalmomin da suka dace ba don bayyana abin da nake ji game da ku. Babu wata kalma da zata iya misalta kaunata a gare ku! Na kuma ji dadin yadda kuke mu'amala a yanzu sosai... Har cikin rai na nake jin dadin hakan. Allah kuma ya kara mana zaman lapiya Amin ya rabbi..."
"Amin...." Suka amsa baki daya.
"Ke Waheedah baki sani ba. Amman Ahlam ta sani . Na sanar da ita .."
Waheedah ta daga kai ta kalle shi ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa.
"Nan gidan kamar yadda yake da sunan Ahlam .. Kema Allah yayi na sama maki wani matsugunin wanda yake da sunan ki kema... Amma fa wani hanzari ba gudu ba... Ba bene ba ne flat ne.. Sannan kuma ba anan unguwar ba ne... A tasu Maa ne." Ya fada yana tsokanar Waheedah daga karshe.
Wani FARIN CIKI ne ya mamaye ZUCIYAr Waheedah da gauraye . Murmushin fuskarta yaa fadada. Kai kana kallon ta kasan taji dadin zancen sa.
Ba dan Ahlam na wajen ba. Har tukwicin sumba ta so ba shi. Sai ta danne dai . Ta shiga godiya agare shi. Zayn yaji dadin hakan kwarai matuka.
Ahlam ma ta tayata farin ciki. Ana'i washegari zata koma Zayn ya kai su gidan su wajen Haj Hameedah da Haj Aisha. Tun safe har rana. Da rana kuma ya dau Waheedah ya kai ta wajen Umman su gidan gwaggo haule. Acan ta karasa wuni har dare.
Washegari kuma akai mata rakiya gidan ta dake nan layin su The Adams family amman daga karshe.
Tsayawa bayyana yadda gidan ya tsaru ma bata lokaci ne. Komai yaji zam zam.... Sai fatan Allah yasa a tsofe lapia yasa kuma an shiga a sa'a.
Ya kuma kawo musu zuriya dayyiba. Domin har yanzu shiru daga Ahlam din har Waheedah. Gashi tuni har zahara'u yar Marka ta haihu. Ba tazara da ke kwanika ta keyi ko auren ta na baya. Shekara na cika ta sake sullubo wani. Ta shiga renon su su biyu .
*GIDAN MALAM NA LADO*
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ 💞 _NA_
_NANA HAFSATU_ _(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:70_
*_FINALE/END (KARSHE)_*
_______
**Jikin na Marka ya sake saaki. Baki daya sai dai a kwantar a tayar. Sauki daya ta samu ta hanyar maganar ta da ta dawo. Amman itama dakyar maganar ke fita. Cikin wata iriyar murya mai wahalar wa.
Najib kusan kullum yana gidan. Daya dawo daga makarantar boko zai je gidan. Da ke yana ajin karshe na babbar makaranta ta sakandire.
Umma Hadiza na kokarin temakawa da su Marka da yan kudade na daga ribar kasuwancin tah. Tana yi ne kawai saboda Allah da albarkacin yaranta da haifa daga gidan.
Haka ma Deluwa da ke kokarta wa a nata bangaren. Don itama tanada marar lapia acikin yaranta yan biyu.
Zahara'u kuma ta nuna gajiyawa. Ba sosai take zuwa gidan ba ma. Ta kance Na'Ateeku ya hanata. Ko kuma yara ba lafiya.
Malam Nalado ya tsaya tsayin daaka akan rashin lafiyar mahaifiyar sa Marka.
Duk kuwa da ba tsayayyakin aiki ne da shi ba. Da ake biyan sa, Aikin karfi ya saka a gaba ka'in da na'in.
Ya kan je kasuwa ya yi wa yan kasuwa daako su dan bashi na cin abinci. Sai ya soke kudin sa a aljihu. Ya sake gangara wa wajen maagina yayi musu leburanci. Ko na ebo musu ruwa su ko kasa da daukar bulalluka.
Ta hakan ya ke samu ya rufawa kansa asiri da kula da lafiyar Marka. A boye kuma ya kan bawa yaran inna Sa'adatu su kai mata gidan su.
Deluwa kuwa wani lokacin ma ita kan temaka masa. Idan tayi cinikin abincin sayarwar da ta ke.
Su zabba'u kuwa daman ba sa bi takan yiwa Marka wani abun arzikin. Kan su kawai suka sa ni. Su kance a baya ai dama Nalado da zahara'u ta nuna tafu kauna. Don haka su babu ruwan su da harkokin ta.
Su kanzo dai su dubata da dan lemo da ayaba. Wataran kuma su karkade jikin su su tafi. Babu ko sisi.
×××
Marka na tsakar gidah kaman kayan shanya akan tabarma .
Daga gefen wajen dakin girki kuwa Deluwa ce tanata jefa danwake.
Wani yaro dan gidan zahara'u yana wasa da wani kara ya daga shi sama ya cilla. Bai fadi a ko'ina ba sai fuskar Marka .
Ta ke ta kece da kuka. Cikin dashasshiyar muryar ta mai fita a sarke ta ce,
"Shege, Dan iska... Ka ci malafar kan uban ka Adamushe. Matsiyaci. Gayyar masifa."
Gashi ba dama ta saka hannu ta mulmula wajen. Yaron ya kece da dariya.
"Yi hakuri marka .." ya fada yana sake tuntsirewa da dariya .
"Kai mekayi Abbati? Matsa daga nan, Sannu Marka .." cewar Deluwa da sai da ta jiyo maganganun Marka ta gano wani abun abbatin ya aikata.
Dai dai lokacin da malam na lado ya shiga bayan sa kuma wani tsoho ne mai farin gemu yana dogarawa da sanda.
"Assha. SubhanAllahi Marka. Menene kike kuka. Deluwa menene?"
"Yo ka tambayi matsiyaciya.? Ai so ta yi karan ya chake mun idanu nima na dai na gani tamkar yar wajen ta. Wannan mata, wannan mata, Allah dai ya kwashe miki albarka..."
"Assha marka bar cewa haka.... " Malam na lado ya fada. Kafin ya sake cewa,
"Ga malam me carbi na kofar dawanau ya zo duba ki."
"Ayho to .. Sannu malam .."
"Yauwa sannu Marka ... Ina wuni?"
"Alhamdulillah Malam."
"Ya karfin jikin na ki?"
"Da sauki "
"Masha Allahu... Ubangiji Allah ya baki lafiya. Yasa zakkar jiki ce. Allah yasa wannan ciwo na ki kankarar zunubai ce. Allah ya tashi kafadun ki.. Ya sa...
Bai karasa ba zahara'u ta shigo cikin gidan tana koke koke.
"Marka Allah ya isa tsakani na da ke. Wayyo Allah na. Wayyo . Wayyo ..."
Duk suka tsaya suna bin ta da kallo. Malamin ya sake mayarda zaman gilashin kara masa gani cikin idanun sa.
"Assha.... Wacece wannan din?"
"Zahara'u ce autar mu." Malam na lado ya fada yana matsa yatsun sa.
"SubhanAllahi.... Ki ke fadaawa mahaifiyar ki wadannan tsauraran kalamai haka? Assha assha."
Zahara'u ta zube a jikin bango tana mai harba kafafun ta.
"Ya shika ni .... Shi ma ya shika ni. Shika 3 kuma. Yace ba zai iya dawainiya da yara majinyinta har biyu ba. Munje asibiti an gwada su. Suna da ciwon amosanin jini ta sikila (sickle cell..) wayyo Allah na... Marka kin cuce ni.. Kin ha'ince ni. Allah ya isa tsa...
Malam na lado ya samu kansa da faskara mata zafafan maruka har biyu hagu da dama na fuskar ta.
Marka ta sandare da jin bayanin zahara'u. Ciwon amosanin jini yaran zahara'un ke da shi? Maganganun Najan Isubu suka shiga dawo mata na shekarun baya.. Alokacin da zata hada Waheedah da shi. Inda Najan ke ce mata Na'Ateeku fa shima ba lafiyar ce dashi ba. Wani tokararren abu ya tokare mata a makogaro . Sai dai idan Hadiza ce ta kai sunan ta gidan boka.
Dattijon ya dube su duka. Yana wa malam na lado kallon karin bayani. Nan dai Nalado ya sheda masa komai . Tun faruwar neman da Na'Ateeku yayiwa yar wajen sa Waheedah. Da yadda auren ya koma kan zahara'u. Da tarihin ciwon da ke kan Najib da ma marigayi yayan su Waheedah, wato Kamal.
Marka ta kece da kuka... Cikin muryar me cunkushe da damuwa tace,
"Ko kaffara ba zan ba sai dai idan Hadiza ke bibiyar mu da sihiri. Ta jefe rayuwar mu baki daya.... Ya zaai ace. Da fari bayan da nace tabar gidan nan tin da dama auren ya kare tuni. A ranar data tafi Adamushe ya zo ya sau zahara'u saki 3 agaban mu. Yace yara ba nasa bane. Gasunan zube muna zaune da su. Mai sunan Malam ya zo ya auro Deluwa itama gatanan yara biyu du ba lafiya. Waçcen dayar makauniya ce ma tamkar dai diyar Hadiza da ke saka gilashin kara gani to ita wannan yarinyaa ma baki daya bata gani. Akazo ranar daurin auren zainabu yar Sa'adatu a ranar mijin itama ya sauta... Sannan kuma auren zahara'u na biyu dan ana bakin ciki ta haifo har biyu shine Hadiza ta shiga ta fita ta sanyawa yaran irin ciwon yaranta su biyu. Ciwon da ya kashe dan ta na fari kamalu. Gashi Najib yana da shi shi ma. Sannan ace yaran zahara'u na wajen Na'Ateeku suma du su biyun suna da shi? Bayan ciwo ga shika har 3? Ni ma bata bar ni ba. Ta kassarani gashi nan ta lalatamun rayuwa sai dai a kwantar a tayar. Baki daya malam wannan matar ta batamun rayuwa ta da ta iyalina gaba ki dayan mu... "
Malam me carbi na kofar dawanau yayi murmushi kawai. Yana mai girgiza kansa,
"Ki sauri ki ce Astagfirullahi.... Wani bai isa yayi wa wani wani abun ba. Ba tare da Allah ya rubuto haka kaddarar sa zata kasance ba.... Kuma in dai Hadiza dai kike nufi wacce ke wajen haulatu yayar ta. Matar Nalado ta fari. Maganar gaskiya ba zata aikata mugun abu ba... Dukkanin abubuwan da kike fada ya shafeta haka zalika kema ya shafeki Iya. Yaranta sunada ciwon sikila. Diyar ta ya macen kuma bata gani sai da temakon gilashi. Haka zalika ke kika sanyaa Nalado ya rabu da ita..Yaran nan nata jikoki ne agare ki Marka. Ko ba komai itama uwar 'yayan dan cikin ki ce.
"Kada ma ki sake cewa wani ya tozarta miki rayuwa ta hanyar sanya miki ciwo ko gurbata rayuwar ahalin ki. Wannan ba dai dai ba ne. Baki imani da kaddara ba Iya. Babu hutu da kwanciyar hankali ga bawa a wannan rayuwa ta duniya sai yayi imani da qaddarar Allah. Wato ya sakankance cewa duk abinda Allah ya qaddara mai aukuwa ne, kuma abinda be so faruwar sa ba, to haqiqa bazai faru ba. Haka kuma lallai al'umma da zata taru gaba daya domin ta cutar da bawa da wani abu, to ba zasu iya ba sai dai da abinda Allah ya rubuta zai same shi. Hakanan da zasu hadu domin su amfanar dashi, ba zasu iya ba face da abinda Allah ya rubuta.
"Ma’anar Imani da Qaddara: Imani da qaddara na nufin yarda tare da gaskatawa cewa, babu wani alhairi ko sharrai da zai sami dan Adam face bisa qudura da hukunci na Allah Madaukakin Sarki. Sarki ne kuma shi, da yake aikata abin duk da ya so; ba abin da zai iya kasancewa, face da sani, da kuma yardarsa. Babu kuma wani abu a faadin duniyar nan, da yake wajen qarfin ikonsa, Madaukakin sarki ta fuskar samuwa ko rashi; shi yake samarwa da sarrafa shi. Amma, tattare da haka, ya shimfidaa wa bayinsa wasu umarce-umarce da hane-hane, wadanda a cikinsu, ya ba su cikakkiyar damar tsare alfarmarsu ko tozarta ta; babu wanda zai tilasta su. Iyakar abin da yake wurin shi ne, al’amurran za su ci gaba da gudana ne gwargwadon iko da zabin ransu. Amma, yana da kyau a sani cewa, da su bayin nasa, da wannan dama da iko da suke da su, duk Allah Madaukakin Sarki ne ya halicce su. Saboda haka duk wanda ya shiriya daga cikinsu, rahama da jinqai ne, na Allah ya sauka gare shi. Haka kuma duk wanda ya bace, hikimarsa ce Madaukakin Sarki, ta tabbatar da haka. Babu kuma wanda ya isa ya tambaye shi dalili a kan haka. Amma, baya gare shi subhanahu wa ta’alah, kowa abin tambaya ne.