Kenza eBookz

Farrah complete Novel - Chapter 12

Farrah complete Novel - Chapter 12

Farrah complete Novel Chapter 12: Farrah complete Novel Chapter 12. Tunda tashiga motan tai shiru, komi na zaman mata kaman mafarki haryau takasa manta…

3,965 words

Tunda tashiga motan tai shiru, komi na zaman mata kaman mafarki haryau takasa manta rayuwanta just like a week ago, tun tana Yar yarinyar ta takeshan wahala agabanta aka kashe yar uwanta, dakin datake kwana na wajen tumakan gidansu, abinci saita sata idan su Inna basa nan, Shafa ita kadai ke sonta aduka garinsu, Shafa na yawan gayamata watarana sai labari wataranan ne yazo yanzu, wanan da rana daya kawai tafita taga za’a kashe mutum ta ceceshi gashi yanzu iyayen mutumin sun zamarda ita yarsu gashi yau zataje makaranta, girgiza kai tayi tareda murmushin kuka hawaye yazubo mata sharr dasauri tasa hannu tashare hawayen, hanya ta kalla tanason gidan nan babu kaman Mami dake koyamata karatu, ta shiryata ko da maman su na raye tana sonsu amman kullum fita take saida nono dakuma idan anyi karaya akirata Mamanta kullum wahala take danta kawomusu abinci basu taba ganin Baban su ba koma waye mahaifinta bazata taba yafemai ba dan mahaifiyar ta rasu da wahala hakama yar uwarta, koba komi zata dage tai karatu tanaso tazama likita kaman Mami sabida ta taimaki mutane da mata dayawa bataso mata sudinga mutuwa sabida rashin samin likita dazai lurada su. Kankame jakan makarantan ta tayi akirji tareda lumshe idanu ita tana tunanin zuci, parking dataji anyi yasa dasauri tabude idanunta tana kallon wajen, gaban wani hadadden school sukai parking, ganin motoci tayi kala kala ana parking ana sauke student maza na sanye da dogon wando, da shirt da jacket da necktie, mata kuma na sanye da skirt daya tsayamusu a guiwa da shirt da jacket da nectie sai hula na beret, da fararen safuna akafafunsu da farin safa kowa na shiga cikin school din, kana ganin school din kaga school na yan gayu, tana zaune ahaka lost in thought tana kalle kalle bodyguard yabude mata kofan motan, adan firgice ta kalli bodyguard din sanan tafito ahankali tana kankame da jakanta a hannu kaman irin mutanen nan da aka dauko daga kauye ana shirin kwace musu jakansu, zagayowa ta inda take Zayn yayi yana tafiya ahankali yana gyara zaman farin glasses na idanunshi dan satan kallonshi tayi da sauri tadauke kai wuceta yayi hakan yasa tabishi da sauri suka shiga cikin school din student na kallon Farrah duk inda sukayi sabida yanda ta kankame jakan makarantan ta a kirji tan tafiya kaman wacce ke shirin sata, ganin yanda ake kallon Farrah some student na pointing nata ana dariya yasa Zayn ya tsaya chak batare daya juyoba yanda take kalle kalle tana biyedashi yasa bamata lura ya tsaya ba kawai karo taji taci dashi students sai dariya, juyowa Zayn yayi yakalleta itama kallonshi tayi jikinta har bari yake baki ta tabe zatai kuka idanunta sun cika da kwalla sosai girgiza mata kai yayi tareda kai hannunshi ahankali ya karbe jakan data kankame akirjinta, zagayowa yayi ta bayanta ya tsaya yakama hannunshi da kanta yasaka mata jikinta na rawa sanan yazo ta gefenta yakama hannunta sukai wajen lift ya shiga da ita sanan yasa 5th floor yarufe kofan, jin abu na sama yasa kuka data rike da kyar tasakeshi hannunshi takama da sauri takalli fuskanshi cikin muryan kuka tace “Ya Zayn dan Allah kamaidani kauyen mu ni banson makarantan nafasa” baitaba jin abu yabashi dariya ba sai yau.💫 FARRAH 💫

✍🏻M SHAKUR

THIS BOOK IS NOT FREE❌ Wanan littafin FARRAH 500 ne kacal. Don magana dani M SHAKUR chat me up directly by clicking on this link; wa.me/+2347012181461

EPISODE 2️⃣5️⃣ Gimtse dariyan yayi yadan daure fuska baisan ya akayi ba kawai ji yayi yace “dama kinada tsoro”? Gyadamai kai tayi kaman wata Yar little baby tace “za’a dingamin dariya idan ban iya abu ba” yatsine fuska yayi kaman baiso yay maganan sai kuma ahankali yace “I will teach you” dan kwalalo mai manyan idanunta dake jikeda hawaye tayi alamun bata ganeba ahankali yace “zan koyamiki anything dabaki iya ba, babu wanda zai miki dariya” gyadamai kai tayi tasauke kanta kasa har lokacin jikinta na bari tana wasa da yatsunta, yatsun ya kalla saikuma yadauke kai yace “kidaina jin tsoro babu abinda zai faru” gyadamai kai tayi daidai kofa yabude yafice tana biyedashi tana kalle kalle har office din headmistress din school din, suna shiga office din Babban matan dake ciki wanda kana ganinta kasan itane headmistress din tace “ohh Zayn welcome, sannunku da zuwa have a sit” zama sukayi tana kallon Farrah tace “hello pretty lady” Farrah tasan hello hakan yasa ta kakalo murmushi ahankali tace “ina kwana” murmushi matan tayi tace “lafiya kalau” sanan takalli Zayn cikin harahen turenci tace “your Mom told me everything about her, zamu mata papers na primary school, yanzu abinda zai faru I will test her inga daga wani class zata iya farawa” wani textbook na English na SS1 matan tabata tabude mata wani passage ta tura mata gabanta tace “read this Farrah” tanuna mata wajen dan kallon matan Farrah tayi dudda bataji turencin ba tagane cewa karanta duka rubutun wajen akace tayi, ahankali ta gyadama matan kai, Zayn takalla ahankali shima kallonta yake raurau tayi da idanu baisan mesaba ji yayi kaman shima yace yafasa sakata a school din yatafi da ita sabida yanda tayi dauke kanshi yayi da sauri yaciro wayanshi yafara dandannawa headmistress din tace “uhum ina jinki Farrah fara” Gyadamata kai Farrah tayi dasauri kafin ahankali tace “kam…..fri…hen…..shon(comprehension), da…..man…..sta…..tree(the monster tree)” dan murmushi headmistress din tayi ganin daga asalin farkon page na textbook din tafara bama passage din take karantawa ba, dudda haka tayi kokari, dama the main challenge da ita da Mami suke tsoro shine yazo bata iya hada baki ba amman tunda yanzu ta iya hada baki kawai ahausance take karatun turencin she will pick up fast, wani takarda da maths question ke ciki aka bata wanda mainly addition subtraction da multiplication ne aciki, sai kuma numbers raise to power 2, pen tabata tace “yimin lissafin nan nagani” karban pen din tayi tayi talla hakan yasa ta iya lissafi kuma tun a primary school datayi tasan addition subtraction multiplication sign da square and power sign nan da nan tayi taba headmistress din dubawa headmistress din tayi with so much excitement tace “good job Farrah” dudda Farrah batasan metace ba but yanda tai maganan tasan ance tai daidai ne tai kokari washe cute white teeth nata tayi ta screen na wayanshi yake kallon face dinta, murmushi yadanyi ganin this is her first smile tunda tazo school dinan, tashi headmistress tayi tace “muje nakaiki class naki SS1, Zayn wait for me here u will fill out the forms” tashi Farrah tayi ahankali tana kallon Zayn ganin yanda ta tsaya yasa headmistress tace “Zayn baraka bimu ba” dan dago kanshi yayi yakalleta tashi yayi ahankali yafice tabishi dasauri har class nasu anan sama shiga class din headmistress tayi da ita shikuma ya tsaya abakin kofa teacher na ciki duka ajin tashi akayi aka gaidata murmushi tayi tace “settle down student, this is your new class mate, everyone welcome Farrah Muhammad Ganuwa with Atama clap, ATAMA 👏 ATAMA👏 LABAKO👏 LABAKO👏 LAMARINAAAAAAAA👏👏👏👏” yanda suke tafi headmistress namusu wakan Atama saida yasa Farrah taidan murmushi tana kallon yan ajin, dan tabe baki Zayn dake kallonta yayi yace “silly girl” headmistress tace “can I hear you all say welcome Farrah” atare duka yan ajin sukai ihu “welcome Farrahhhh” washe baki Farrah tayi sanan Headmistress tabata wani sit dake gaba gaba tace “once yayanki yagama cike komi zansa akawo miki all books and textbooks naki” Gyadamata kai Farrah tayi sanan headmistress tajuya tafice Farrah na binta da kallo, leka wajen tayi ganin bataga Zayn abakin kofan class din nasu dayake da ba, kalle kalle tashigayi ta window chan saigashi yazo zai wuce yana maida waya aljihu kaman waya yayi kallo ajin yayi dasauri tadagamai hannu alamun bye dauke kai yayi kaman bai Santa ba hakan yasa ta harareshi. “Focus Farrah” malaman dake ajin tai magana da sauri Farrah takalli gaban allo gabanta nafaduwa.

Komawa office sukayi kudin komi Zayn yabiya tundaga kan takalmin makarantan su, socks, sport wears, uniform, books, textbooks, babu single abu na school din dabai biyamata ba sanan ya ciremata all the forms tass kusan 1hr yayi a school din sanan yagama komi, headmistress tayi tace “ko waye direba nata dazai dibga zuwa daukanta idan an tashi needs to go to our security office yay register sabida asan dashi, we don’t release our students to just anybody for safety purpose” kallonta Zayn yayi kaman bazaice komiba sai chan yace “for now I will be the one coming” murmushi headmistress tayi tace “indai kaine ba matsala” tashi yayi yace “lemme get going” gyadamai kai headmistress tayi tace “regards to your Mom” ficewa daga office din Zayn yayi headmistress na binshi da kallo saida yafice ta girgiza kai ahankali tace “yaran yanzu, Allah dai ya gyara mana jibi yanda ya maida gemunshi jama’a, wai Wanan ne gayu awajen su” secretary nata ta kwalama kira tana shigowa note and textbooks na Farrah da Zayn yabiya tanuna mata tace “kaima Farrah SS1 Science” kwasa tayi tafice.

The Wellness by Oriflame routine is designed to support your intake of protein, dietary fibre and micronutrients, in the right proportions, every day.

A = ACTIVATE Set the foundation of your routine with vitamins, minerals and omega-3 fatty acids. These are needed every day to fill the nutritional gaps in your daily diet. You find them in our Wellness Multivitamin and mineral.

B = BUILD Boost your defence system, and even build it over time, with the amazing Astaxanthin, together with bilberry extract and protein. Antioxidants are your active defense against environmental pollutants and help your body cope with a hectic lifestyle. Proteins help your body build new cells. You can find these in our Wellness Shakes.

C = CUSTOMISE We all have individual needs depending on our age, lifestyle and general wellbeing. That’s why you should top up your routine with additional nutrition to feel and look your best. This includes using products like our Wellness soups and bars.

Meanwhile lemme all introduce you to supplement da I think we be solution to all problems na jikinmu.

Dukanmu nan munsan ORIFLAME is a reputable brand da aka sansu wajen wallafa abu mai kyau yanzu sunyi Supplement mai suna WELLNESS by ORIFLAME. Kowa dakuka gani mata da maza muna bukatan some mineral, vitamins da sauransu dazai helping jikinmu da system namu, supplement dazai karama defense mechanism namu karfi to protect us from ciwake ciwake, sanan dazai taimakawa organs dinmu yin aiki da kyau.

Idan kina shan wellness zaki kyau, zai karamiki lafiya, zai taimakawa organs naki sosai, akwai so many reviews, wata tace tunda tasha wellness tafara samin ruwa gaba, wata tace skin nata yay fresh, wata tace gashinta daya karairaye yadawo, wata tace nonon ta yakara cikowa, banda haka wellness na bada kariya against cancer.

Wellness is the best supplement da ake dashi right now wanda kasashen duniya da dama sukasha kuma suke recommending ma mutane.

I have good news! Supplier wellness dinan tace namuku albishir duk wanda yasaya akwai FREE DELIVERY to duk inda kake a Nigeria. You will never regret buying wellness, zaki saya sanan kisaima maigida nshi shima. Don sayan wellness contact her by clicking on this link; wa.me/+2349133427208💫 FARRAH 💫

✍🏻M SHAKUR

THIS BOOK IS NOT FREE❌ Wanan littafin FARRAH 500 ne kacal. Don magana dani M SHAKUR chat me up directly by clicking on this link; wa.me/+2347012181461 DUK WACCE TAKARANTA MIN HOOK BATARE DATA BIYABA BAN YAFEBA.

EPISODE 2️⃣6️⃣ Sosai take concentrating a karatun da ake koyamusu her only problem shine rashin iya turenci, ranan gabaki daya maths da further math kadai tasan tagane shima sabida lissafi ne amman sauran abubuwan dasukayi bata ganeba sabida rashin iya turenci.

Break aka kada, kowa na ajin tashi yayi yafice banda ita dake zaune kaman an dasata awajen bude jakanta tayi sanan tadauko water bottle da Mami tasaka mata aciki dawani kula tabude, fries ne aciki da pepper chicken da sausage, sai fork murmushi tayi ahankali tasa fork tafaraci shigowa ajin akayi wata yarinya data dan dare Farrah tsayi da kadan tashigo ciki tana rike da cups biyu na parfait ta taho inda Farrah take kujeran dake facing Farrah ta zauna akai tana kallon Farrah da itama ke kallonta, dan murmushi tayi tamikama Farrah parfait daya tace “my name is Maryam, kowa call me Miemie agidan mu, I am a baker, na iya bakin cakes and so many many other thing kefa” abinda take bata Farrah takalla sanan ahankali tasa hannu ta karba dan kartaga kaman tamata wulakanci but bamata iyacin abinba, ahankali Farrah tace “sunana Farrah, ni ban iya yin cake ba but Mami tace zata koyamin” murmushi yarinyar tayi tace “ohh that’s nice, tun ina yarinya Mom tafara koyamin baking, yanzu is officially my business you can search me on Instagram @alfasimcakes, I really like you Farrah tunda kika shigo nake kallonki, you are so pretty” murmushi Farrah tayi batace komiba, ganin kaman batagane abinda take fadi yasa Maryam tamika mata hannu tace “friends? Muzama kawaye?” Shiru Farrah tayi tana kallonta batare daya mikamata hannunta ba, murmushi Maryam tayi tace “don’t be scared nima just last week aka sani a school dinan, a Saudi muke zama, sabida Yayan mu Ya Habeeb anturoshi yayi wani project anan Nigeria more like a course for 3yrs shine fa dukanmu muka dawo nan, Mom da Dad wai bazasu iya barin yaronsu yazo Nigeria yana wahala shi kadaiba babu mai girka mishi abinci ba, Dad dina is a Doctor, shima anan Nigeria aka haifeshi but he works at Saudi, the whole thing is so annoying nafison Saudi kan nan garin, tunda nazo banda any friends tundazu da aka shigo dake nake kallonki, kinga tsayinmu daya, though nafiki kadan, kuma kaman we are age mate, sanan bakida hayaniya, and you are very very very pretty, ni banma taba ganin someone as pretty as you are a school dinan ba sai yau kaman ke, so will you be my best friend, Babban kawata my Besty eh Farrah, I want us to be best friends forever BFF, ko baki sona” tunda take surutun Farrah ke kallonta saita tuna mata da Shafa, haka Shafa ke zuba gatada hayaniya, hannu Farrah tabata hakan yasa Maryam tai ihu. “Yeeeeee we are BFF” ahankali Farrah tace “Beef” dasauri Maryam tace “BFF” ahankali Farrah tace “BFF” “yauwa haka, menene baki gane ba” English Farrah tanuna mata da sauri tace “wanan” Gyadamata kai Maryam tayi tace “gamacin abinci zamuje library anjima muyi karatun tare we will be doing everything together tare daga yanzu” Gyadamata kai Farrah tayi tanadan murmushi dan Maryam is free spirited person hakama Shafa take.

3 aka tashi daga school parking books nata Farrah tayi tasa ajakanta, Maryam data gama hada komi nata takaraso wajen kujeran Farrah tana goya jakanta tace “muje headmistress office ki amshi uniform naki datace ki amsa idan an tashi” goya jakanta Farrah tayi tace “ok” murmushi Maryam tamata yakama hannunta tarike tace “let’s go Besty” fita sukayi daga ajin yan ajin na kallonsu yanda suka zama kawaye Maryam last week tazo bata taba kula kowa ba sai yau dataga Farrah toko tasan Farrah ne daga wani waje, office din headmistress suka shiga, tana ganin Farrah tace “good Farrah kin tuna kinzo, I was about nada secretary na ma takiramin ke kafin kitafi baki dauki uniform naki ba, here we go” headmistress tabata wani katon jaka na uniform nata kala kala da sport wears karba tayi ahankali tace “thank you” murmushi headmistress tamata tace “har kinye making friend Good job Maryam” washe baki Maryam tayi sanan suka wuce suka fita, lift suka shiga suka sauka kasa sanan sukai gate, tun kafin sukai gate Maryam tamata pointing wani mahaukacin jeep tace “ga motan gidan mu chan, me Ya Habeeb yazo wani daukana yau ni bazanje ba munyi fada” ta tsaya daga cikin school din, dan zaro idanu Farrah tayi tana kallonta tace “da yayanki kike fada Maryam”? Dan lumshe idanu Tayi tabude su sanan tace “Muryanki dadi Farrah gashi dan karami baya fita da kyau, by the way kinga ko tunda muka dawo Naija nake fushi da Ya Habeeb, driver ke zuwa daukana ni mezanyi da motanshi, da namazo da wayana dana kira Mom nace mata bazan shiga motan shi ba” dariya Farrah tayi dan Maryam is so funny, tana tunamata da Shafa sosai, kama hannunta tayi tace “kinga ko babu kyau ana fushi da dan uwa, kije hala ma yazo yace miki kiyakuri ne wuce kitafi” Farrah tai maganan tanajan hannunta suka fito gate, ganin motan Ya Zayn a pake ga bodyguard gaban motan yasa Farrah tasaki hannun Maryam dasauri tace “nima anzo dauka na bye Miemie” tadagama Maryam hannu, hannu itama Maryam tadaga mata tanadan dariya jin tacemata Miemie tace “bye Fairy🧚‍♂️ ” budemata bayan motan bodyguard yayi ahankali tashige cikin motan tana leken Maryam da itama tabude gaban motansu tashiga tana leken Farrah tana murmushi tamaida kofan tarufe.

The Wellness by Oriflame routine is designed to support your intake of protein, dietary fibre and micronutrients, in the right proportions, every day.

A = ACTIVATE Set the foundation of your routine with vitamins, minerals and omega-3 fatty acids. These are needed every day to fill the nutritional gaps in your daily diet. You find them in our Wellness Multivitamin and mineral.

B = BUILD Boost your defence system, and even build it over time, with the amazing Astaxanthin, together with bilberry extract and protein. Antioxidants are your active defense against environmental pollutants and help your body cope with a hectic lifestyle. Proteins help your body build new cells. You can find these in our Wellness Shakes.

C = CUSTOMISE We all have individual needs depending on our age, lifestyle and general wellbeing. That’s why you should top up your routine with additional nutrition to feel and look your best. This includes using products like our Wellness soups and bars.

Meanwhile lemme all introduce you to supplement da I think we be solution to all problems na jikinmu.

Dukanmu nan munsan ORIFLAME is a reputable brand da aka sansu wajen wallafa abu mai kyau yanzu sunyi Supplement mai suna WELLNESS by ORIFLAME. Kowa dakuka gani mata da maza muna bukatan some mineral, vitamins da sauransu dazai helping jikinmu da system namu, supplement dazai karama defense mechanism namu karfi to protect us from ciwake ciwake, sanan dazai taimakawa organs dinmu yin aiki da kyau.

Idan kina shan wellness zaki kyau, zai karamiki lafiya, zai taimakawa organs naki sosai, akwai so many reviews, wata tace tunda tasha wellness tafara samin ruwa gaba, wata tace skin nata yay fresh, wata tace gashinta daya karairaye yadawo, wata tace nonon ta yakara cikowa, banda haka wellness na bada kariya against cancer.

Wellness is the best supplement da ake dashi right now wanda kasashen duniya da dama sukasha kuma suke recommending ma mutane.

I have good news! Supplier wellness dinan tace namuku albishir duk wanda yasaya akwai FREE DELIVERY to duk inda kake a Nigeria. You will never regret buying wellness, zaki saya sanan kisaima maigida nshi shima. Don sayan wellness contact her by clicking on this link; wa.me/+2349133427208 ***************************

Wani farin guy ne sol kaman balarabe zaune a driver seat yana sanye da suit brown hannunshi rikeda wani file hankalinshi gabaki daya na wajen yana karanta abin ciki, batare daya dagokai ba balle ya kalleta ba yace “who is she”? Kaman daga sama Miemie taji tambayan da Ya Habeeb yamata kuma tasan yamata tambayan ne sabida today is the first day tun last week data fara zuwa school dinan tajero tafito waje tareda wata tana murmushi, washe baki tayi jin tambayan da Ya Habeeb yamata tace “Ya Habeeb she’s my new friend her name is Farrah Muhammad Ganuwa, I call her Fairy, cus she’s as beautiful as all this fairies danike gani a cartoons” dan tabe baki Ya Habeeb yayi ya maida file din dayake karantawa ya rufe sanan ya ijiye yadago kanshi yazuba mata manya manyan idanunshi. Wow! Yanada wani kalan kyau kaman shi yayi kanshi, gashin kanshi baki sidik sun kwanta, yanada gashin gira dakeda cikan gaske baki kirin dashi yana wani kyalli, ga dogon hancinshi kaman shiya makala ma kanshi, wani dan karamin baki yakedashi dakenan ja, yanada saje mai kyau dakenan a kwance yazo yahade da dan gajeren black gemunshi, kamanninshi daya sak da Miemie saima haske dayaso yafita sosai, dan karamin bakinshi yabude yana kallon fuskanta yace “be careful with the kind of friends you make Miemie, you know I don’t like it” yay maganan yana maida hankalinshi kan motan dayake kokarin kunnawa, dan daure fuska tayi ashagwabe tace “I like Farrah Ya Habeeb a lot, she’s just definition of the kind of friend danake so, she’s cool, calm, batada surutu and tanada kirki sosai” dan juyowa yayi yakalleta ganin yanda take yaban wacce yau tafara ganinta sai kawai ya girgizakai batare dayace mata komi ba ganin ta gama zarewa, wani babban estate sukaje agaban wani babban gida yau horn aka budemusu gate suka shiga, parking yayi dasauri tafito tai gaba batare data jirashi ba.

Wani Babban falo tashiga, wata Babban mata ce dabazata wuce sa’an Mami ba zaune tareda wata mata suna magana, tana shiga da gudu tai wajen matan tace “oyoyo Mom” murmushi matan tayi tace “oyoyooo Miemie ya school” tashi tayi zaune tace “Mom I’ve finally made a friend today for the first time tunda muka dawo Nigeria” dan ware idanu Mom tayi tana kama baki tace “that girl must be special yanda kike da selecting abu dinan” Gyadamata kai tayi dasauri tace “sunanta Farrah Mom, tanada kirki, Mom she’s so beautiful Fulani ne su, Mom kinga gashinta kuwa gata da hank……” hadiye maganan tayi sabida Ya Habeeb daya bude kofan dakin yashigo wani mugun kallo yamata ahankali ta dudda kanta kasa sanan tadan kalli Matan dake zaune kusada Mom Yar Aiken Mom ne tasan kan Abuja Mom na ai kanta kasuwa da sauransu haka ahankali tace “ina yini Anty Lami” hararanta Anty Lami tayi tace “yanzu kika ganni” zatai magana Ya Habeeb yace “go upstairs and change kidawo kasa kici abinci” gyadamai kai tayi ahankali sanan ta tashi tana turo baki tai sama hararanshi Mom tayi tace “ka kiyayan mini yarinya fa Habeeb, yanda kake miskili haka kakeso ka maidamin da yarinya miskila, ga abincin ka a dinning” tashi yayi yace “I am not hungry Mom later” Anty Lami tace “matan Habeeb zatai fama baya iyacin abinci ko kadan” girgiza kai Mom tayi tace “ni harna gaji wlh Lami, dagashi har Miemie basa iyacin abinci wani zubin sainayi dagaske natasasu agaba nakasa na tsare sanan zan samu suci abinci, ita Miemie nata baya damuna sosai Dan ta iya kwadayi shiko kwata kwata Habeeb bayama son zaki bansan waya biyo ba dani da Baban shi munacin abinci” dariya Anty Lami tayi tace “Allah sarki Dakta, Allah dai yabiyashi ya rayamai yaranshi Habeeb da Miemie, ni babu abinda zan iya saka miki dashi Hajiya sai addu’a kawai nagode bari naje na karbo miki sakon” Gyadamata kai Mom tayi tace “kije da direba, bari nadubo Miemie najita shiru” dariya Anty Lami tayi tana bude kofa tace “yawuce tai bacci” sama Mom tayi zuwa dakin Miemie, bude kofan dakin tayi ahankali, Miemie na kwance kan gado daga ita sai white singlet da skirt din uniform dinta tana bacci hannunta rikeda pen ta rubuta sunan Farrah yakusan cika page din book dake kan gadon, hannu Mom tasaka ahankali ta dauki book din tareda karbe pen din, sunan Farrah ta kalla kafin ahankali tace “who are you Farrah? Diyata na sonki sosai” dan murmushi tayi ta maida book din tarufe sanan ta ijiye mata kan side drawer kafin taja bargo tarufa mata sanan tawuce tafita daga dakin.💫 FARRAH💫

✍🏻M SHAKUR

THIS BOOK IS NOT FREE❌ Wanan littafin FARRAH 500 ne kacal. Don magana dani M SHAKUR chat me up directly by clicking on this link; wa.me/+2347012181461 DUK WANDA/WACCE TAKARANTA MIN LITTAFI BATARE DATA BIYABA BAN YAFEBA

EPISODE 2️⃣7️⃣

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull