Ganin ido complete - Chapter 11
Ganin ido complete Chapter 11: Ganin ido complete Chapter 11. "Please ka daina bi na haka bana so. Idan kana da wata magana dani to ka cim mini a gida…
3,355 words
"Please ka daina bi na haka bana so. Idan kana da wata magana dani to ka cim mini a gida kamar yanda ka saba, Ammie ta faɗa mini bata son hakan please daga yau ka daina."
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"In Sha Allah ba za'a koma ba. Kinga ma na tsaya daga nan....Allah ya tsare hanya."
"Amin. Sai na dawo."
Ina zuwa na tarar da Adeel da ƙur'ani a gabansa yana karantawa. Dariya ce ta suɓuce mini ƙasa-ƙasa na ce.
"Adeel hala har da yau ɗinma azumi kake?"
Jinjina kan shi ya yi ba tare da ma ya kalleni ba, alamar irin boss ɗin nan wanda mai kashe shi sai ya shirya.
Jinjina kaina na yi na ce.
"Masha Allah. Allah ya nuna mana..."
"uhm! Kafin an jima ka fara mana kuka ba."
Cewar Aunty Hajjo tana mai ƙarasowa cikin parlourn.
Dariya na yi muka gaisa sannan kowa yaje ya kama aikinsa. Bayan munyi sallar azahar muna kitchen misalin ƙarfe uku saura sai ga Adeel ya shigo fuskar nan a turbune ya ce.
" Ni fa wallahi Aunty Beenafah cikina zafi yake mini.."
Taɓe baki nayi ina mai ɓoye dariya ta na ce.
"Allah ko!"
"Shikenan kawai an kai Hanan gidansu Hajiya ni an barni a nan kuma ita can ɗin bata azumi..."
Ruwan zafi na ɗebo na haɗa masa Tea nan take na miƙa masa sai gashi ya karɓa. Jinjina kaina na yi na ce.
" Amma dai kam ya kamata ka riƙa yin lissafi Adeel. Bahrain fa azuminsa goma sha uku, kai kuma shida kawai, haba! Bana son mutum ya zama mai raki da yawa. Kana namiji ya kamata ka riƙa zama mai juriya."
"To kiyi haƙuri,in sha Allahu gobe zan yi..."
"Ai kullum haka kake cewa.."
"Ki yi haƙuri zan yi gobe. Amma dan Allah za ki kawo mini Bahrain in gan shi?"
"Eh..."
"Yaushe kenan?"
Kallon shi Aunty Hajjo ta yi ta ce.
"Dan Allah kada ka ishemu da tambayoyin nan naka na 'ƴan Jarida, a bikin Sallah In Sha Allahu za ta kawo maka shi."
A yanda na lura ba su cika shiri da Aunty Hajjo ba, domin ita bata cika shiga al'amarin yara ba, ban sani ba ko su Adeel ɗin ne bata doguwar alaƙa da su ko kuma haka dai take a rayuwa.
Madara ya buɗe ya ƙara sannan ya ɗauki gorar ruwa ɗaya ya fice kawai ba tare da ya ƙara cewa komai ba.
Tsaki ta ja tana mai ci gaba da mita tana faɗin.
"Allah Beenafah na tsani rashin sanin ciwon kai a rayuwa. Mafi yawan yaran masu kuɗin nan sai a hankali, sakuwa da shiririta ya yi musu yawa, kana zaune 24 hours a A.C baka aikin fari baka na baƙi amma azumi ya gagareka....wai nan har don ma Mummyn ta su tana yi masa jan ido, shiyasa Hanan ta fishi daɗin sha'ani, ga shegen surutun tsiya, idan ya fara maka tambaya tamkar wani jikan Aku.."
Ni dai ƙala bance ba kawai na ci gaba da dariya, in dai fagen tambaya ne ni dai ina da Oga Bahrain saboda haka ba zance komai ba.
****
Tun ana sallah saura kwana uku muka fara aikace-aikace masu matuƙar yawa da kuma wahala, idan akayi wannan ayi wannan, sannan ga Aunty Labiba ba ta son tarkacen mutane, mu ɗin dai mu kaɗai ne sai ita cikon ta uku. Na ga wasu en mata su biyu sun zo da alama Sallah suka zo, amma kullum suna ɗaki ban taɓa ganin sun zo kitchen ba. Ana saura kwana biyu salla ta kiramu bayan mun kambala aiki, ta bani kaji guda biyu na turawa da aka gyara ta bai wa Aunty Hajjo biyar, magi, shinkafa, Mai, komai haka ta raba mana shi wanda komai na Aunty Hajjo yafi nawa yawa wata ƙila kam sun fi mu yawa ne shiyasa ko kuma don ta fini daɗewa da ita. Wani ƙarin farin cikin ma Leshi ɗan ubansu ta ƙara mana da Atamfa tace mana daga gidan iyayenta aka raba shi ne ta karɓo mana namu. Wallahi Allah ya sani ina ƙaunar Aunty Labiba domin tasan girma da darajar ɗan adam. Duk abin da Biba ta faɗa mini dangane da ita ashe somin taɓi ne sai yanzu da na zauna da ita na ƙara sanin haƙiƙanin wacece ita.
Cike da uzuri na gama shirya kayana na ɗauka nabi ta ƙofar baya na kai bakin gate sannan na dawo parlournta ana yi mata zanen lalle mai kyau na ce.
"Aunty Labiba na tafi sai da safe..."
"A'a! Ba inda zaki je sai an miki lalle Beenafah."
Ɗan gwalo idona na yi ina mai dubin agogon bangon parlourn na ta na ce.
"Aunty Labiba biyar ta gota sosai..."
Gyaɗa kanta ta yi ta ce.
"Na sani. Yau ɗin already dare ya yi, gobe kuma daren sallah sannan kuma sai kin zo nan ɗin still, to idan ba'a miki yau ba shikenan a haka za ki yi sallar?"
"Aunty Labiba..."
"Sai fa an miki lalle Beenafah. Ki gayawa Maman taku cewa ni ce na tsayar dake."
Zaunawa na yi daman already an gama mata za'a farawa cikin baƙinta ne ta ce su yi mini alfarma a mini. Da ƙyar na lallaba ta yarda aka mini kaɗan wanda daga yatsu sai bayan hannu da tafi shima ɗan mitsini, maganin dai ba'a yi ba. Ƙafar ma haka, ba wani mai yawa ba amma yayi matuƙar yin kyau kamar ka lashe.
Ina nan sai da aka fara kiran sallar Isha bayan ya bushe naje na wanke sannan na fito a gaggauce ina ta mata godiya. Ni da baƙinta dai ido ne, bayan gaisuwa babu abinda yake haɗamu da su, to ko zaman lallen nan sai dai in ɗago in ga suna kallona daga zaran mun haɗa ido sai su kauce.
Ina isowa inda na ajiye kayana muka yi kiciɓis da Muhsin da kuma Adeel wanda da alama masallaci za su tafi. kallon inda na ɗaga ledar naman Muhsin ya yi yaga ruwan naman duk sun ɓata floor ɗin ya wani buga tsaki ya ce.
"Dan Allah ƙazamar banza ki zo ki wankewa mutane wuri kin ji ko..."
Cikin shakku Adeel ya waro ido ya kalleni sannan ya kalle shi ya ce.
"Ya Muhsin Aunty Beenafah ce fa..."
"And so! Miye ruwana da kowace banza ce ita. Ki wuce ki ɗebo ruwa ki zo ki wankewa mutane wuri....kuma kai idan na ji ka ƙara kiranta da Aunty wallahi sai na fasa maka baki..."
Lumshe idanuwana na yi jin yanda kalamansa suka dakar mini zuciya har ban san lokacin da wa su zafafan hawaye suka wanke mini fuskata ba. Wai wannan yaron! Idan har ban girmeshi ba shima ba zai girme mini ba, sai dai kuma idan mu zo ɗaya da shi ne a shekarun amma shi ne ya tsaya a gabana yana ci mana fuska son ran sa. Hmm!
Duƙawa na yi na kwashe ledojina domin wallahi ba zan goge wurin ba, duk abin da zai yi ya daɗe bai yi ba ina jiransa. Ban yi aune ba kawai na ji an ja hijabina baya da ƙarfi har saida ya yage. Jikina na wani irin mazari na waigo tare da yi masa wani mugun kallo na ce.
"Sake mini hijabita Muhsin!"
"Idan ba'a sake ba mi za ki yi?"
"Ya Muhsin ka sake mata hijabinta...ka daina Ya Muhsin.."
Cewar Adeel hankalinsa a matuƙar tashe.
Hannayena guda biyu na saka na fisge da ƙarfi sannan na sake duƙawa na ɗauki kayana na kama hanyar gate na fice zuwa gida.
Ina shiga na tarar da Ammie, Bahrain da kuma Fakiha. Bahrain ɗin yana fifita wa Fakiha lallenta ga hasken Nepa fal ko'ina ya haska tamkar farin wata. Tuni na ji duk wani ɓacin ran da na zo da shi ya tafiyar sa.
Cike da jin zallar farin ciki na ce.
"Wayyo Allah Nepa! Ammie Nepa? Waye ya saka mana Nepa?"
Dukkan su dariya suka shiga yi ganin yanda duk na ruɗe na cika da farin ciki.
Kallona Bahrain ya yi ya ce.
"Ya Jafaru ne ɗa zu yazo da wani abokinsa ɗin nan mai aikin Nepa ya saka mana..."
"Innalillahi! Wayyo Allah Nepa, shikenan mun huta da duhu...Mun gode mun gode Allah ya saka masa da alheri."
Daga haka na fito da gudu daga gidanmu na shige na su gidan sai ga shi kuwa na ci sa'a yana zaune a saman benci yana cin abinci.
"Ya Jafaru mun gode sosai, mun gode Allah ya saka da alheri, Allah ya biya maka buƙatocinka na alheri duniya da lahira."
Cikin nuna jindaɗin addu'a ta yace. "Amin Beenafah. Kin dawo?"
"Eh na dawo, Ina zuwa naga gidanmu ko ina haske,wallahi na ji daɗi sosai....miye kake ci haka?"
Kallon cikin plate ɗin ya yi sannan ya kalleni ya ce.
"Indomie ce na sa Fakiha ta soyamini..."
Kafin ya iyarda rufe bakin sa har na zauna na kaɗa hannuna muka ci gaba da ci.
Kallon lallen hannuna ya yi ya ce.
"Kai! Amma dai wannan lallen ya yi kyau."
Dariya na yi na ce.
"Da gaske?"
"Da gaske nake, waye ya yi?"
"Gidan aikina. Aunty Labiba ta saka aka mini."
"Gaskiya ta kyauta. Mun gode, Allah ya biya."
"hmm! Ya Jafaru Aunty Labiba tana da kirki. Ta fa ƙara mana kala biyu ni da Aunty Hajjo, sannan har da hijabai guda biyu da kayan kwalliya da gyale..."
Nan na yi ta bashi labari Maman su na ta aikinta tana saurarenmu har muka kambala na fita na wuce gida.
Kallona Fakiha ta yi ta ce.
" Wai ke kin wani je kin yi zamanki. Mai lalle tunɗazu tana ta can tana jiran ki.. "
Hannayena da ƙafata kawai na nuna mata ba tare da na ce komai ba sai aikin murmushi.
"Au! Ashe ma kin yo lallenki daga can? To an huta, daman Ya Jafaru ne ya bamu dubu huɗu kowa dubu biyu ya ce muyi lalle da kitso..."
"Kitso tun kwana biyar da suka wuce Aunty Hajjo ta dunƙule mini abina...saboda haka a bani kuɗina."
Wata uwar harara Fakihar ta maka mini sannan ta ce.
"Wai ma! Nikam wallahi na riga na sayi kayan lalle da nau da naki na kai mata, har kuɗi na biya ta don ban san cewa daga can zaki yo ba...."
"To ta yiwa wata da su sai ta bata kuɗinta mana."
Cewar Yaya Hamza dake shigowa gidan yanzu.
Jinjina kaina na yi na ce.
"Ah to! Kina karɓowa ki mayar masa da kuɗin sa tunda an samu sauƙi. Ya Hamza ka goge mana kayanmu mana dan Allah..."
"Ba zan yi ba..."
"Kai Ya Hamza dan Allah?"
"Gaskiya aiki ya yi mini yawa ba zan iya ba..."
"Eh, amma idan kana son wani abu ka iya sakani wahala, shi ne nasiha ɗaya ba zaka mini ba. Da Ya Jafaru ne da yanzu ya amsa. Wallahi Ya Jafaru da abinda na ce da ma wanda bance ba komai yi mini yake."
Dariya ya yi ya ce.
"To Ya Jafaru kika ce Beenafah. Ya Jafaru daban Ya Hamza daban..."
"Beenafah!"
Ammie dake ɗaki na ji ta kira sunana, hakan yasa na shige ɗakin na bar su a nan.
****
Washe gari ma ban dawo gida ba sai tara na dare. Cikin daren nan bayan na dawo na shiga haɗa mana Miyar stew da sauran aika-aikacen da ke jirana wanda ban kwanta ba har asuba.
Muna cikin shiryawa zuwa filin Idi Ya Jafaru ya shigo mini da ɗunkunan da Ammie ta bashi shekarajinya wai har ya ɗinke su.
Daman na riga su shiryawa cikin Atamfa ta sabuwa da sabon hijabina da takalmi. Ina jin sallamarsa na fito ina murmushi na ce.
"Kai Ya Jafaru gaskiya ka wanku...ka yi kyau, wannan shaddar ta maka kyau."
Murmushi ya sakar mini yana jinjina kansa ya ce.
"Ke ma kin yi kyau sosai... Zo mu yi hoto."
Matsowa na yi muka yi ta ɗaukar hoto da wayarsa da ni da shi. Bayan mun gama ya yi ta ɗaukata ni ka ɗai har sai da Ammie suka fito ita da Bahrain ɗin sannan muka fito muka nufi babban masallacin Idi tare da su Fakiha da maman su,cike da farin ciki.
Bayan an kambala muka dawo gida muka zauna zaman cin abin ci da sha muna ta yiwa juna barka da shan ruwa.
Muna nan zaune a gida munata firarmu, sai misalin sha biyu na rana na na cewa Ammie.
"Ammie bari na tashi naje gidan Aunty Labiba, tace mana yau ne kaɗai take gida daga gobe gidan su za ta riƙa tafiya sai dare ta dawo."
"To ba damuwa, ki gaisheta sosai..."
"Eyyah Ammie na so mu tafi dake da Bahrain."
Girgiza kanta ta yi ta ce.
"A'a Beenafah.. Ke dai ki tafi.."
"To dan Allah ki bari muje da Bahrain na yiwa Adeel alƙawarin kawo masa Bahrain."
"Wannan ba damuwa, Allah ya tsare, ku gaishe da su... Ungo ga dubu biyu ki kai musu shi da Hanan ɗin kice nace barka da sallah ne."
Cikin farin ciki na amshi kuɗin muka shirya muka kama hanya muna tafe muna labari har muka isa.
Muna shiga harabar gidan muka tarar da yaran gidan gaba ɗayansu suna tsaye jikin motar babansu da alama fita za su yi. Wasu manya-manyan kulilo ne masu azabar kyau na ga an ajiye a bakin booth ɗin motar.
Adeel da Hanan na ganina suka rugo da gudu suka rungumeni. Kallon su na yi sun sha gayu sosai cikin tsadaddin kayansu na ce.
"Wow..Masha Allah! Sai ina haka?"
"Gidansu Hajiya zamuje tudun wada."
"Ina ne gidansu Hajiya?"
"Gidansu Hajiyar Daddynmu ce."
"Oh..ok. To sai kun dawo. Ga Bahrain na cika maka alƙawari na kawo maka.."
Dariya ya yi sannan ya miƙa mishi hannu ya ce.
"Bahrain ɗin Aunty Beenafah mu gaisa..."
Har muka gama duk maganganun da zamuyi Muhsin da ƙannensa suna tsaye suna kallonmu, sannan daga ƙarshe muka nufi cikin gidan. Kafin mu ƙarasa kawai na jiyo kukan Hanan sosai tana ɗaga murya tana ihu. Ba shiri na juyo na dawo inda suke. Raina ne ya ɓaci sosai ganin Tima ta kamata sai dukanta take ga Muhsin babban banza da Muhsina tsaye suna kallonta tana cutar ta. Da sauri na fisge Hanan ɗin daga hannunta ina kallon Adeel na ce.
"Ba ka da hankali ne? Ba ka ga yanda take dukanta ba?"
"To Ya Muhsin ya ce kowa ya ƙyale su...."
"Kai sakaran ina ne ana dukan ƙanwar ka kana tsaye,.... Ke Tima miyasa kike yin haka? Ban ƙanwar ki ba ce? An kinga bata kai ki girma ba..."
Kafin na ƙarasa rufe bakina kawai na ji Muhsin ya wani turani da ƙarfi sai da na faɗi ƙasa tim! Tasowa na yi da tsantsar mamaki a fuskata da baƙin ciki na wanke shi da mari. A gaban Bahrain da Adeel zai tureni? Yaran da suke ganin girmana ya zubar mini da mutunci a gaban su, ai wallahi ba zai yiyu ba.
Dukkan su wurin babu wanda bai yi mamakin marin da na sauke mishi ba. Ba ma kamar Muhsin ɗin da ya yi wani suman tsaye domin ko a mafarki bai yi expecting ba. Da gudu Adeel ya shiga gida sai gashi sun fito tare da Aunty Labiba da ma wasu baƙi da tayi sun kai su biyar.
Cike da mamaki Aunty Labiba ta zo ta shiga tsakaninmu wanda ya na huci nima ina yi tamkar na shaƙeshi haka nake ji.
"Ke Beenafah miye haka? Subhanallah!"
Hawayenda suka silalo mini ne na share da bayan hannuna na ce.
"Aunty Labiba ki tambaye shi miye matsalata da shi a gidannan...?"
Yana ganin Maman su ta fito kawai ya fashe da kuka ko kunya bai ji ba.
Cike da masifa da tsantsar wulaƙanci ta ƙara so wurin kawai ta kifa mini mari, za ta sake na biyu ne Aunty Labiba ta riƙe mata hannu ta ce.
" Akan wane dalili Hajiya Marwa?.....Na ce akan wani dalili za ki mareta? Idan ma wani abu ne ai sai ki jira abi abu daki-daki...."
"Labiba ni za ki hana na mari 'ƴar aiki?' ƴar aikin da ta mari Ɗa na ta zubar masa da mutuncinsa a gaban ƙannensa!"
"Shin kin san abin da ya yi mata da har ya saka ta mareshi??"
"Miye zai yi mata! 'ƴar iskar yarinya marar mutunci! Ai duk irin abin da take masa babu wanda ban sani ba, lokaci ne daman nake jira irin wannan. Ko ni nan sau nawa nake haɗuwa da ita a cikin gidan nan? Amma sai ta yi tamkar za ta tureni ta wuce, gida kamar gidan ubanta..."
Girgiza kai Aunty Labiba ta yi ta ce.
" A'a wallahi! Ba dai Beenafah ba, ko Lailah (cewa da ƙanwar mijin su) da nake ganinta marar son mutane sai da ta yabi nutsuwa da halin kirkin Beenafah.. "
" Wai Labiba akan 'ƴar aiki za ki tara mana jama'a?? To wallahi tallahi sai na ɗauki mataki akan wannan' ƴar iskar yarinyar..."
"Ni kaina Hajiya Marwa na yi mamakin tsayuwata a nan, to amma Beenafah a ƙarƙashina take dole kuma in kare mata da mutuncinta.....Ke Beenafah miye ya faru tsakaninki da Muhsin?"
Duk yanda Aunty Labiba ta so in yi bayani Hajiya Marwa ta hana, sai faman bala'i take tamkar wacce akace na kashe mata Muhsin ɗin.
Ganin taƙi bari ma na yi magana yasa Aunty Labiba ta ja hannuna da nufin mubar wurin sai ga Daddyn su Adeel ya fito daga ɓangaren ita Hajiya Marwar.
Cike da mamakin ganinmu haka ya ce.
"Lafiya kuwa? Miye yake faruwa?"
"Miye ma bai faru ba! Kawai 'ƴar iska da ita ƙazama ta zo ta ɗauki hannu ta marar mini Ɗa na, to wallahi tallahi ba zan yarda. Banga yanda za'a yi muna zaune lafiya ba amma ' ƴar aiki ta zo tana shiga tsakanin yaranmu tana so ta haɗasu faɗa ta kunna ƙiyayya da gaba a tsakaninsu. Idan ba shi ba ina ruwanta da faɗan Tima da Hanan da har za ta ja Tima ta wanka mata mari akan Hanan, sannan don Muhsin yayi magana shima ta wanka masa mari, kuma ta dawo cewa Adeel wai ya zauna nan a kashe masa ƙanwa ba zai rama ba..."
Cike da ɓacin rai Daddyn na su ya waro ido ya kalleni wanda ban san lokacin da na fashe da wani irin kuka ba ina girgiza kai na alamar ba haka akayi ba.
Wani uban tsaki Hajiya Marwar ta sake bugawa sannan ta ce.
" Munafurcin banza munafurcin wofi! Duk abin da kike musu ai ina sane ƙyale ki kawai na yi, to na rantse da Allah dole ka ɗauki mataki da kanka ko kuma ni na ɗauka idan ba haka ba sai ta raba maka kan yara.."
Kallon Aunty Labiba ya yi wacce ta cika ta batse akan wani irin baƙin cikin Hajiya Marwa da ya rufeta ya ce.
" Labiba ba ki ce komai ba..."
Lumshe idanunta ta yi a hankali waɗanda suka canja launi ta kalle shi murya a ƙasa sosai ta ce.
" Mi zance Barrister? Bana son rigima, ka sani sarai bana son rigima. Na tabbata idan an bi kadin duk waɗan nan maganganun na ta ba haka suke ba. Beenafah ba za ta yi haka ba wallahi..."
"Labiba! Shin duk miye ya kawo wannan? Kuma duk akan wa ake wannan rigimar? Akan Wannan yarinyar ko? Ita ɗin ba dangin ki ba ce, ba dangina ba ce, In dai don saboda ita ake wannan, to daga yau kada ta sake shigowa gidan nan,ki sallameta taje ta nemi wani gidan..."
"Amma Barrister..."
Ɗaga mata hannu ya yi alamar bai son jin komai ya ce.
"Labiba! Tun ba yau ba Hajiya Marwa ke ta damuna da complain ɗin yarinyar nan. Sannan ai akwai Hajjo, don mi yasa ita ba su yi complain a kanta ba? Labiba ni na san ki da bin umarnina, sannan matuƙar dai akayi wannan na san ba Allah na saɓawa ba kawai neman maslaha muke, saboda haka ki yi haƙuri ki sallami yarinyar nan bana so ta ƙara shigowa gidannan. Dan Allah ki yi haƙuri. Idan ma wata zaki nemo ni ba zan hana ba."
Daga haka ya juya ya buɗe motar ya shigar da Kuulolin sannan ya shige motar sa ya yi shiru kawai tare da ɗora kansa akan starrying motar.
Taɓe baki Hajiya Marwa tayi sannan ta ja tsaki ta ce.