Ganin ido complete - Chapter 13
Ganin ido complete Chapter 13: Ganin ido complete Chapter 13. Yau ma ko da na wayi gari bana jin daɗi daman kwana biyu Malaria na damuna na, gashi na sha…
3,334 words
Yau ma ko da na wayi gari bana jin daɗi daman kwana biyu Malaria na damuna na, gashi na sha magani duk a banza domin zazzaɓin dai na nan ba inda ya tafi. Hakan yasa da Ya Jafaru ya shigo gidan sai yace na ƙara shan magani kafin yaje wani aiki ya dawo, idan zazzaɓin bai sauka ba sai muje Chemist a mini allura.
Da haka na yi ta lallaɓawa har Yamma. Ina kwance na ɗora kaina akan cinyar Ammie muna fira sai ga Ya Jafaru ya shigo, da ƙwarin gwiwar sa ya kalleni ya ce.
" Beenafah albishirinki!"
Murmushi na yi ina mai jinjina kaina na ce.
"Goro fari Ya Jafaru..."
"Uwar gijiyarki Labiba, ta kirani da kanta ta ce in faɗa miki ke kuma ki faɗawa Ammie gobe tana neman ki ƙarfe sha biyu na rana..."
Wata irin zabura na yi da ƙarfi na miƙe tsaye ina zaro ido na ce.
"Da gaske ka ke Ya Jafaru? Dan Allah da gaske ka ke ko dai zolaya ta ce ka ke?"
"Miyasa zan zolayeki gaki ma kwance kina fama da jiki. Ina wurin aikina ta kirani na ɗauka ta ce mini sunanta Labiba in ce miki tana neman ki..."
Wani uban ihu na buga tare da maƙalƙale Ya Jafaru cike da farin ciki na ce.
"Alhamdulillah Allah!..."
"Ke Beenafah miye haka?"
Cewar Ammie cikin ɗan alamun tsawatarwa wanda hakan yasa ba shiri dole na sake sa na dawo na Rungumeta ina ta farin ciki duk da bansan dalilin kiran ba.
Ajiyar zuciya Ammie ta sauke sannan ta ce.
"Ki daina duk wannan murnar Beenafah domin ban amince kije ba..."
Cikin wata irin razana na ce.
"Miye kika ce Ammie? Aunty Labiba ce fa?..."
"Eh na sani! Mijinta ya kore ki, sannan daman can ba tsayawa akayi neman ba'asi ba, koda ta ce tana son ci gaba da zama dake hakan ba zai yi yu ba domin wannan kishiyar ta ta da 'ƴa' ƴanta ba za su barki ki zauna lafiya ba, domin wulaƙancin da za su yi miki a yanzu sai yafi wanda suka miki a baya... "
Girgiza kai Ya Jafaru ya yi ya ce.
" Bana tunanin haka fa Ammie, domin cewa ta yi tazo ta sameta kan corner ba a gidan su ba, to ina ga wata ƙila dai.... To ban dai sani ba gaskiya amma dai cewa ta yi ta zo ta sameta kan corner. Kinga kenan bamu san dalilin neman ba saboda haka kada ki yanke hukunci cikin rashin sani."
Zuciyata cike da wani irin tsoron kada Ammie ta hanani zuwa ganin Aunty Labiba na shiga kallonta tamkar idanuna za su fito waje. Ni wallahi ko ba zan koma gidan su ba, ganinta kawai ya wadatar dani domin ina jin kewarta a raina daga ita har 'ƴa' ƴanta.
Jinjina kanta ta yi ta ce.
"Shi ke nan! Na amince kije amma kuma ba zan yarda ki koma da yi mata aiki ba."
Cikin jindaɗi na ce.
"To Ammie, In Sha Allahu. Na gode sosai."
Hannu Ya Jafaru ya miƙa cikin aljihunsa ya ciro kuɗi ya miƙo mini yana faɗin.
"Ga wannan....dubu biyu ce, kuyi haƙuri da ita sai ku haɗa da abin da kuke da shi ku lallaɓa."
Kallon shi na yi wanda duk siminti a jikin sa ya gama ɓata shi na ce.
"Mun gode sosai Ya Jafaru, Allah ubangiji ya saka maka da alheri, Allah yabiya maka dukkan buƙatocin ka na alheri."
"Ba komai Beenafah. Allah dai yasa mu dace."
Daga haka ya fice zuwa gidansu. Yana shiga ya ciro dubu uku ya bai wa maman su shi kuma ya soke dubu ɗaya a aljihunsa sannan ya ɗauki bokiti ya janyo ruwa a rijiya yaje ya yi wanka, bayan ya fito ya ɗauki abincin sa ya ci sannan ya shirya ya fice.
****
Ni dai tunda Ya Jafaru ya faɗa mini cewa Aunty Labiba na nemana gaba ɗaya na nemi ciwona na rasa. Har gari ya waye ban yi wani baccin kirki ba domin tunani ne fal ya cika mini zuciyata.
Da wuri na shirya na je gidan maman Abul na yo mata wanke-wankenta na dawo ina yi ina duba lokaci.
Kallona Ammie ta yi wacce ke ɗauke da farantin farin wake wanda za ta ƙulla a leda ta ce.
"Beenafah, ko miye za ta faɗa miki ban yarda ki ci gaba da aiki s gidansu ba."
"In Sha Allahu Ammie ba zan yi ba."
Da haka muka yi sallama na fito na kamo hanya har na iso bakin kan corner inda ta ce na zo na same ta, kuma abin mamaki sai gashi na tarar da motar ta tsaye a wurin. Koda na fito gida ƙarfe goma sha ɗaya da ashirin, hakan ya tabbatar mini cewa tasan muhimmancin lokaci.
Tana ganin na ƙara so ta buɗe motar tace mini na zagayo na shigo gefenta na zauna.
Ina shiga na kalleta cike da kewa na ce.
"Ina wuni Aunty Labiba."
"Lafiya Beenafah. Ya kike ya haƙuri kuma?"
"Alhamdulillah! Ya su Hanan?"
"Su Hanan lafiya ƙalau suke. Kin samu wani gidan aikin ne?"
Gyaɗa mata kai na na yi na ce.
"Eh!"
"A wanne wuri ne?"
"Can ne saman anguwarmu, wurin Islamiyyar Abu-Musa"
"Masha Allah! Nawa ake biyan ki?"
"Wanke-wanke ne kawai nake mata sau ɗaya a rana, duk wata dubu biyu."
"Ok...to daman wata shawara na yanke akan cewa ko za ki koma gidan su Hajiyata ki ci gaba da aikin ki a can..."
Ganin irin kallon da na bi ta da shi yasa ta girgiza kanta ta ce.
"No! Kada ki ɗaga hankalinki Beenafah ba wani abu ne, ba don yana gidanmu ba, mutane ne ma su kirki da daɗin zama, In Sha Allahu za ki ji daɗin zama da su. Ki je ki sanarwa Maman ki yanda muka yi. Can ne gaba damu wurin gidan Yarima ba nisa sosai. Idan ta amince sai ki kirani da wayar wannan Yayan na ki."
" Tau ya yi, In Sha Allahu zan sanar mata, duk yanda muka yi da ita zan kira ki."
Motar ta tayar muka kamo hanya tana yi tana tambayata hanyarmu har muka iso titin da daga shi sai hanyar shiga Layinmu sannan ta saukeni ta ce mini tana jiran feedback.
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *ArewaPen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 16*
A bakin titin da ta ajiyeni a nan na ci karo da Yaya Jafaru, jikin shi butu-butu da siminti da alama daga wurin aiki yake.
Shi kuma cike da nuna kulawa yana murmushi ya ce mini.
"Ah! Da alama dai tattaunawar ba mai jimawa ba ce naga har kin dawo."
Murmushin nima na mayar masa ina mai jinjina masa kaina na ce.
"Wallahi kuwa!"
"Miye tace miki? Allah yasa ba zancen komawa aikin ba ne? Naga Ammie ta ɗauki zafi sosai..."
"Hmm! Kai dai bari Ya Jafaru, wata magana ce kuma ta daban ta zo mini da ita..."
Maganar ta wa ce ta yanke jin wani uban horn da ake ta ruga mana tamkar mai motar zai bi ta kanmu ya wuce, hakan yasa ba shiri cike da hanzari muka yi gefe muna masu ƙure motar da kallo. Wani irin mummunan faɗuwar gaba ne na ji ya riskeni lokaci ɗaya bayan na yi tozali da mammalakin motar.
"Ohh! Wai Beenafah ce? Sannum ki"
Da ƙyar na iya ƙaƙalo kalmar Ina wuni daga can ƙasan maƙogwarona na jefa mishi wacce na san zan ɗauki tsawon lokaci ina jimami da baƙin cikin furta ta gareshi domin bai cancance ta ba.
Shi ma ɗin kallona ya yi da wani kalar murmushin mugunta a fuskar sa ya ce.
"Na ga kina mini wani kallo mai kama da harare ko? To ni dai ina fata baku ɓata mini gidana ba? Ya kamata ma na riƙa zuwa jewaya gaskiya."
Cikin nuna fusata Ya Jafaru ya kalle shi ya ce.
"Kai Malam lafiya? Miye haka?"
Wani kallon ya yi wa Ya Jafaru mai nuna alamun gargaɗi sannan ya ce.
"Kai kuma a suwa? Mts!"
Daga haka ya buga motar sa ya wuce. Kallona Ya Jafaru ya yi fuska cike da alamar tambaya ya ce.
"And shi kuma wannan wane ne shi Beenafah?"
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya na sauke a hankali na lumshe idanuna na buɗe su sannan ce.
"Wannan shi ne wanda ya bamu gidan sa yanzu haka muka muke zaune a kyauta..."
"To amma shi ne zai riƙa miki maganganu na cin fuska da tozarci?"
Murmushi na yi ina mai girgiza masa kaina na ce.
"Ba komai Ya Jafaru, wannan ni ba komai ba ne a wurina kada ka damu..."
"Beenafah!"
Ya Jafaru ya kirana sunana a hankali yana mai bina da ido tamkar yau ne ya fara ganina.
Kallonsa nake, nima idona a cikin nasa na ce.
"Na'am Ya Jafaru."
"Shin zan iya sanin su waye ku?"
Wani guntun murmushi ne ya suɓuce mini ba tare da na shirya ba na jinjina masa kai na na ce.
"Mu ɗin nan fa ba wasu bane Ya Jafaru, mahaifinmu ya rasu shekaru biyar da suka gabata, sai muka dawo hannun Wan mahaifinmu sai kuma daga baya ya koma Abuja ya bar mu a nan, daga nan kuma yasa aka koremu daga gidan nasa, sai wannan Uncle Isma'ilan da ka gani ya bamu gida muka zauna."
Cike da nuna tausayi a kalamansa ya ce.
" Allah sarki! Allah ya kyauta wannan zamanin da muke ciki. Muddin mutum ya rasa majingina shi ya rasa ba ruwan wani. Idan ana ganin idon wanda ake kunya sai a rasa ma ina za a aza da kai idan kuma ƙasa ta rufe mishi ido shikenan ka zama banza wanda bare ma sai ya fika muhimmanci.... "
Hanya na miƙa kawai na ci gaba da tafiya. Duk abin da Ya Jafarun ke faɗi ina ji amma na kasa amsa masa domin shirun shi ne yafiye mini alheri a yanzu. Wani gefen kuma; takaicin Uncle Isma'ila ne ya dabaibaye mini zuciyata, da a lokacin baya ne ko me zai yi ba zan iya buɗe bakina na gaishe da shi ba. To amma yanzu rayuwa ta ƙara yi mini wani karatun da na ɗauki darasi a cikin sa. Ba ko ina fushi yake yin tasiri ba da hawa dokin zuciya. Da ace a wannan ranar na yi haƙuri da abin da Muhsin ya yi mini kamar yanda na saba da yanzu Daddynsu bai kore ni ba, hakan ya koyar dani cewa ba ko'ina rashin haƙuri yake yin tasiri ba domin gashi na ƙare a matsala. Shiyasa na ɗaukarwa kaina alƙawarin zama mai haƙuri kamar yanda Allah da Manzon sa suka koyar cewa mu riƙa yin afuwa da haƙuri. Hakan yasa dole a yanzu na yi kasa da kaina kada na tunzura Uncle Isma'ila har ya kai ga korarmu kuma ba zan so hakan ba domin idan ya koremu ban san inda zamu nufa ba.
Muna kai wa ƙofar gida Ya Jafaru ya ce mini.
"Kinga bamu ko kai ga tattauna maganar da kuka yi da Hajiya Labiba ba wancan banzan ya zo ya ɓata komai."
"Ya Jafaru ba komai zamu yi shawara da Ammie."
"To ba matsala Allah yasa mu dace."
"Amin."
****
Gefen su Mummy kuwa, suna nan zaune suna ta cin duniyar su da tsinke yayin da arzikin bana ya ci uban na shekarun baya.
Aunty Aysha na gidan har yanzu domin ta ce babu inda za ta sai ta yi shekara ɗaya ta cire marmari da kewarsu da ta kwasa na tsawon lokaci. Dole haka Ahlan ya dawo Abuja ya gaishe da su Mummy Sannan ya juya ya koma London shi ka ɗai.
Ƙaninta Hafiz ma da ke karatu a Australia sau biyu yana dawowa gidan yana komawa. Ga abubuwan magana tana ganin su amma ba ta da ikon yi magana. Haka Hassana ke tara samari kala-kala da sunan ma su neman aurenta wanda har ga Allah ba ya yiwa Aunty Aysha daɗi ita da Husaina kawai dai ba su bakin magana.
Yau ma a fusace Daddy ya dawo gidan Ya tara su a parlour har Mummy. Wuri ya samu ya zauna yana kallon Mummyn ya ce.
"Wai Hajiya Zaliha miye matsalar Hafiz ne? Na ce miye matsalar?"
Wani kallon ta yi mai tare da ɗan ƙara muskutawa kan kujerar kaɗan, ta ce.
"Kamar ya kenan?"
"Kin san komai Hajiya Zaliha! Dake da ɗan ki so kuke ku mayar dani shashasha! In ba shi ba karatu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa! Sai kuɗi nake tura masa amma ban san inda ya dosa ba, yaushe rabonsa da tura mini sakamakon jarabawarsu idan an fitar? Ni gaba ɗaya ban san ma a wanne aji yake ba kuma ban san semester ɗinda yake ciki ba..."
"Haba Alhaji! Ka fa san sha'anin karatun nan na zamani komai ya dawo na kuɗi..."
"Eh, ai ban musa miki wannan ba, amma ki tuna nima na yi karatun nan ba wai ban yi ba....Ya mayar dani wani hotiho miliyoyan kuɗi kawai yake karɓa to na mene ne?"
Daga haka ya miƙe yana ta wani huci ya fice ya bar musu parlourn.
Shiru ne ya ratsa tsakanin su tsawon lokaci wanda kowa da abin da yake saƙawa a cikin ransa musamman Mummy da ta yi zugum! Tana mai nutso cikin tunani. Daga ƙarshe dai ajiyar zuciya ta sauke ba tare da ta yi wa kowa magana ba ta ɗauko wayar ta kamo lambar Hafiz ɗin ta kira. Sai da wayar ta yi ringing kusan sauka sannan daga ƙarshe ya ɗaga murya sa a ƙasa sosai ya ce.
"Mummy! Whatsap?"
Cikin nuna tsantsar ɓacin rai ta ce.
"Miye kake yi a yanzu na ji muryarka ta yi ƙasa?"
"Ni ɗin wai? Ba abin da nake sai bacci, bacci nake shiyasa."
Jinjina kai ta yi ta ce.
"OK. Ina so in tambayeka, Miye ka gayawa Alhaji?"
"Miye fa, kawai na tambaye shi 2M ne..."
"Wai Hafiz ina so ka faɗa mini miye kake da kuɗi haka?"
Wata dariyar baki san gari ba ya yi mata sannan daga ƙarshe ya ce.
"Mummy wannan wace kalar tambaya ce? Wanda ke karatu a Nigeria ya nemi kuɗi ballantana ni. Kawai dai kin san rayuwar komai ya dawo sai da kuɗi..."
"Ka shiga taitayinka ka ji na faɗa maka. Yanzu ya zo yana faɗa akan cewa bai san halin da karatunka yake ciki ba, saboda haka; ina so ka kira shi ka faɗa masa shekarar da kake da kuma semester ɗinda kake. Kasan halina Hafiz da abinda zan iya yi ba sai na faɗa maka ba."
Daga haka ta yanke kiran sannan ta mayarda wayarta ta ajiye, a hankali ta rausayar da kanta jikin kujerar tana mai ƙara shiga nazari.
Taɓe baki Hassana ta yi tana wani yatsina ta ce.
" Ni fa Mummy kawai ina ganin Daddy rigima yake ji. Idan ba shi ba miye abin tada jijiyar wuya saboda kawai Ya Hafiz ya tambayi 2M, Kuma dai yafi ƙarfin kuɗin nan ballantana ace..."
Kallonta Husaina ta yi ta ce.
"Hey! Ya kamata Ki fahimci magana kafin ki yi sharhi a kai. Don ya tambayi kuɗi ba laifi ya yi ba amma dai faɗan da shi Daddy yake yi shi ne; Wace Year yake? Sannan a wacce Semester yake."
Miƙewa Aunty Aysha ta yi tana faɗin.
"Allah ubangiji ya kyauta yasa mu dace."
Daga haka ta yi shigewarta ta bar su a nan wanda en biyu ne suka yi ta musayar kalamai yayin da Mummy ta yi musu tamkar ba ta wurin har sai da suka gaji don kansu suka watse suka barta ita kaɗai.
****
Ina shiga gida na tarar da Ammie zaune da kuular abincin Bahrain a gabanta tana zubawa za a kai mishi Islamiyya kasancewar yau Asabar ce.
"Wai har kin dawo?"
"Uhm! Na dawo Ammie.."
Na faɗa ina saƙale hijabina a igiya sannan na samu wuri daga gefen ta na zauna.
"To miye ta faɗa miki? Ina fata lafiya?"
Cike da fargabar rashin sanin amsar da za ta bani na kalle ta na ce.
"Wani zance ne dai makamancin wancan."
"Na me kenan?"
"Cewa ta yi wai na zo ta kai ni gidan iyayenta sai na ci gaba da aiki a can..."
Na ƙarashe maganar ina mai ƙure ta da kallo.
"To idan matar ta ci gaba da bibiyar ki fa? Ko kuma idan Mijinta ya ji ba kwa tunanin matsala? Kada ya zo ya gano watarana yasa a yi miki wulaƙanci..."
"Ammie gidan iyayenta fa na ce miki ba gidan ba.."
"Na sani..."
"Ammie Please kada ki hana dan Allah! Dama ce muka samu kada mu yi wasa da ita. Duk abin da ya faru tsakanina da Muhsin magana ta gaskiya ban taɓa sanar mata ba, na san da ace na faɗa mata tun farkon da ya fara shiga harkata da ta ɗauki mataki. Amma yanzu In Sha Allahu zan kula.. "
" To na ji! Amma su ɗin kin san waɗanne irin mutane ne?"
Girgiza kaina na yi na ce.
" Ban sani ba Ammie, amma dai ina kyautata musu zato. A lokacin da na fara zuwa gidan Aunty Labiba daga ni har ke bamu san wane kalar hali gareta ba, sai gashi ta yi mana kirkin da bamu tsammata ba. To Ammie Mace mai hali irin wannan ya kike tunanin gidan iyayenta ya kasance? Tarbiyya da hali mai kyau fa mafi yawan lokuta daga gidan iyaye yake farawa kamar yanda kika sha faɗa mini."
Matsawa na ƙara yi dab da ita ina mai kamo hannayenta duka biyu na jimƙe a nawa cikin ƙara tausasa murya na ce.
" Ammie! Na ƙara samun wani Ilmi da darasi daga abin da ya faru. In Sha Allahu yanzu zan kiyaye in ƙara yin taka-tsan-tsan fiye da baya."
Ta jima sosai tana nazari sannan daga ƙarshe ta shafe hawayen da suka silalo mata a hankali tana mai jinjina kanta ta ce.
" Ƙwarai kuwa Beenafah, Tarbiyya da hali na gari daga gida yake farawa, duk da cewa ni ban rayu da iyayena ba, ban san ma ya suke ba, ko a ina suke ban sani ba. Amma kuma Alhamdulillah ina alfahari da waɗanda suka raineni har na girma na kawo yanzu. Saboda haka na yarda na kuma amince ki je amma ki kula dan Allah."
" In sha Allahu Ammie. Na gode da yarda dani da kika yi, In Sha Allahu zan kiyaye."
Daga haka na miƙe na haɗa basket ɗin Bahrain na fito gida da nufin kai masa sai ga Yaya Hamza ya zo karɓa yace na koma gida, fita zai yi daga can zai biya ya ba shi.
Yinin ranar gaba ɗaya da tunanin Gidan su Aunty Labiba na yi shi, a raina ina ta saƙe-saƙen ko wane kalar gida ne oho! Har dai Ya Jafaru ya shigo muka ƙara tattaunawa da ni da shi da Ammie daga ƙarshe na ce ya kira mini ita in sanar mata. Ina gama yi mata bayani cikin farin ciki ta ce gobe da safe ƙarfe goma in jira ta in da ta ajiye ni ɗa zu, za ta zo ta ɗauke mu tafi.
Da dare ya yi ma haka na yi ta matse-matsen Ido amma kuma baccin sam ya ƙauracewa Idanuna. Tunani ne ya taru ya yi wa masarrafar tunanina rubdugu. 'Aunty Labiba ta kasance Mace mai matuƙar girma da daraja a gare ni, a gidanta ne na samu 'ƴancin kai wanda zan zauna in yi yanda nake so ba tare da nuna hantara ko ƙyama a gare ni ba, to amma yanzu ina zan dosa? Wane irin gida ne zan je? Su waye zan tarar? Wace kalar rayuwa masu aikatau ke gudanarwa a gidan? Shin akwai 'ƴan ci kamar gidan Aunty Labiba ko kuma gidan mulkin mallaka ne kamar na Mummy Zaliha?'
A haka dai na shafe tsayin dare ina tubka ina warwarewa har kusan Asuba. Da gari ya waye kuma tun da nayi sallah ban sake kwanciya bacci ba. Aikina na yi cikin lokaci kamar yanda na saba, komai sai da na kambala sannan na shirya na cewa Ammie zan shiga gidan Mamansu Fakiha na yi mata bayani sai ta isarwa da maman Abul.
Ina shiga gidan bayan mun gaisa na kalle ta na ce.