Ganin ido complete - Chapter 19
Ganin ido complete Chapter 19: Ganin ido complete Chapter 19. Cewar Munira tana mai sauke ruwan zafi daga wuta tana yi tana ƙara yin mita.
3,375 words
Cewar Munira tana mai sauke ruwan zafi daga wuta tana yi tana ƙara yin mita.
Tsaye na yi shiruuuu! Ina nazari wanda a gaskiya ba zan bari har zuwa wani lokaci ba, tunda har Hajiya ta kada bakinta ta yi mini magana. Da haka na taka na shige ciki kai tsaye na yi nocking,sai da na yi kusan minti uku sannan na ji an ce mini in shiga.
Gabana ne ya yanke ya faɗi ganinta zaune tare da Mijinta jiki da jiki yana rungume da jaririn a hannun sa. Cike da mamaki ta yi mini wani kallon ta ce.
"Lafiya?"
Durƙusawa na yi daga can gefen kujerar farko, murya a sanyaye ganin irin wulaƙantaccen kallon da take jifana da shi, na ce.
"Daman Hajiya ce ta ce in zo in miki barka. Allah ya raya.."
"To na gode."
Ina shirin Miƙewa na ji tana faɗin.
"Ba Za ki ɗauki babyn ba...."
Kasa matsawa na yi kusa da su akan irin wani kallon da take yi mini ta ƙasan ido wanda ba shiri na miƙe na juya ina faɗin.
"Na gan shi, Allah ya raya."
Da gudu na yo waje kamar zan kifa yayin da na ji wani sabon tsoron ta ya ƙara cika mini zuciyata. Tunani ne ya juye zuwa wani bigire na daban. Komai ta yi shi cike da taku ba tare da ya gane ba. Domin tunda na shiga ya kalleni sau ɗaya bai sake kallon inda nake ba har na fito, yana jin kalamanta kamar da gaske a baki amma zuciyarta ba haka bane.
Ina fitowa, Emraan ɗin ya kalli Ziza ya na murmushi ya girgiza kai ya ce.
"Ni wallahi yanayin yanda yarinyar nan ke baya-baya da mutane ne yake bani dariya. Magana ma can ciki kamar wacce akace za'a cinye Namanta ɗanye..."
"Ashe su Mummy Na'ima suna hanyar zuwa? ta yi mini waya ɗa zu."
Ta yi saurin tare numfashinsa da wata maganar don bata so ma yaci gaba da yi mata zancen banza.
Saman jikinta ya ɗaura jaririn ya miƙe yana faɗin.
"Allah ya kawo su lafiya. Hairiyyah ma haka tace mini yau za ta taso... To amma mutanen Kebbi fa?"
Wani kallon ta mi shi sannan ta ce.
"Mutanen Kebbi baga su Mummy Raliya nan ba! Tun jiya fa suka iso..Su Aunty Darajja ne suka ce sai gobe. Sannan su Daddy Ashraf ma ai tun jiya suka iso kuma ka gan su."
Murmushi ya yi ya ce.
"Eyyah! Sorry, wallahi ban lura ba kin san jiya abubuwa sun yi yawa,kuma ba wanda ya sanar mini, amma su Daddy Ashraf kam jiya muna masallaci har aka gama sallar Isha....Bari yanzu na je na gaishe da su Mummy Raliya ɗin."
Ya ƙarashe maganar yana mai nufar ƙofa.
Ita kuma sai wani hararenshi take ƙasa-ƙasa wanda ita kanta bata san dalili ba.
Ni kuma, a parlour na ci karo da su Aunty Labiba,cikin farin ciki na ɗauki Hanan sama ina faɗin.
"Hanan Oyoyo!"
Da murmushi Aunty Labiba ta ce.
"Beenafah. Halan wurin ganin Babyna kika je?"
Gyaɗa kaina na yi ina murmushi na ce.
"Eyh, na ganshi kyakkyawa ne, Allah ya raya."
"Amin...ga Aunty Nadeeyah ki gaishe ta."
Ta yi maganar tana mai kallon wata kyakkyawar mata dake gefen ta ɗauke da yarinya a kafaɗarta wacce tayi bacci,da alama za ta yi shekara biyu zuwa uku.
Duƙawa na yi na ce.
"Ina kwana!"
Da murmushinta ta ce.
"Lafiya, sannun ki?...."
Ihun Munira na ji a bayana da gudu tazo wurin wacce aka ce in gaishe ta ta rungumeta ta ce.
"Oyoyo.. Wayyo Allah Aunty Nadeenmu ta zo..."
Janyewa tayi tana dariya ta ce.
"Dan Allah ƙyaleni kada ki tada mini da yarinya.. Ai tun jinya na zo ina gidan Aunty Labiba abina..."
"Allah sarki! Kai Aunty Nadee! Ina su Dija?"
"Sun shiga Sashen Hajiya Yanzu."
"Tau yayi, sannu da zuwa.."
Harara Aunty Labiba ta maka mata ta ce.
"Wato kin ga uwar ɗakin ki ni kin share ni ko..?"
"Innalillahi! Aunty Labiba sannu da zuwa ina kwana..."
Fitowar Ya Emraan ita ce ta katse mana moment ɗin, wanda a tare suka koma cikin ɗakin Aunty Ziza mu kuma muka wuce waje bayan Munira ta ajiye abin da ya kawo ta.
Zaune nake a bakin famfo ina wanke kayan miya amma kuma abinda Ziza ta yi mini ne ya tsaya a tunanina. Ina cikin tunani naji murya Munira a kaina ta na faɗin.
"Wannan ita ce Aunty Nadeeyah, daga Aunty Labiba sai ita. A Kaduna take aure itama.....ita wannan ɗin ta ma fi Aunty Labiba sanyi da sauƙin kai..."
Wani kallon kin ma rainawa kanki wayau na yi mata sannan na girgiza kaina na ce.
"Wannan zancen banza ne, domin wallahi ko mi za ki ce nasan ba za ta kai Aunty Labiba ba..."
Muna nan bakin famfon muna ta gardama sai ga Aunty Nadeeyah ta zo da kanta. Duk ma'aikatan da ke wurin da sauri suka zube kan ƙafafunsu suna ta famar miƙa gaisuwa.
Bayan sun gama gaisheta ta miƙowa Munira takarda tana faɗin.
" Kin san fa ke wani lokacin kin cika shiririta Munira, Hajiya ta yi ta kiran wayarki amma ba ki ɗaga ba."
Da sauri ta ce.
"Eyyah, tana can kan Window..."
"Yi maza ga Sule can ya kaiki ki amso wannan kayan kasuwa, na ga Haula aiki ya yi musu yawa. Ga baƙi da yawa suna hanya."
"Tau Yanzu kuwa.."
Ɗaki ta koma bayan Aunty Nadeeyar ta wuce ta ɗauko hijabinta wanda ni already da hijabina a jikina ta kalle ni ta ce.
"Ta shi muje mu dawo."
Girgiza kaina na yi na ce.
"A'a. Kije dai ki dawo... Kalli fa yawan kayan miyan nan? Ki je kafin ki dawo na kambala.."
Tsuke fuska ta yi ta ce.
"Kinga ke matsalar ki ko? Koda sun zo sun ga bamu ƙarasa ba ai dole su yi shi da kansu..."
"Ni dai A'a... Kin san da wuri nake wucewa domin makarant..."
Munira wani lokacin haka nake ganinta kamar tana da motsin ƙwaƙwalwa, ina kan magana ta janyo ni daga inda nake zaune ta shiga kabta rantsuwa akan cewa dole sai na rakata,hakan yasa na bita muka tafi ina ta tunzuro bakina.
Kasuwar Tudun Wada ce muka taho, duk inda muka tsaya iyaka ta miƙa a duba a zubo mana kaya, wanda duk zuwan da muke ni dai ban taɓa ganin sun bayar da kuɗi ba, iyaka a karɓo kaya wasu-wasu ne kawai suke bada kuɗi da alama ƙila daga can sama suke tura musu da kuɗinsu.
Muna tsaye ana tuttula cabbage a kwali wanda shi ne abu na ƙarshe kawai na ga mutum ya bayyana a gabana. Yanda ya tsura mini ido yana kallona nima haka na zuba mishi nawa idon yayin da zuciyata ta shiga bugawa da ƙarfi, ƙwaƙwalwata ta shiga hasko mini hoton fuskar sa a ranar da muka rabu na ƙarshe yana ɗaga mini hannu.
Cikin tsananin shock muryar shi har tana harɗewa ya ce.
"BB.. Beenafah!!!"
Rungume shi na yi cike da ruɗanin ƙwaƙwalwa na ce.
"Yaya Ashiru!!!... "
Da ƙarfin tsiya Munira ta janyo ni baya tana zaro ido waje ta ce.
"Ke! Kin haukace ne? Wannan baligin za ki runguma?"
Haɓa na rawa na shiga nuna shi da yatsa yayinda idona ya cika da ruwan hawaye na ce.
"Shi ɗin Yaya na ne..."
Hannuna ya sake raruma ganin abin tamkar a mafarkin sa ya ce.
"Be.. Be.. Beenafah dan Allah ke ce? Ke ce Beenafah? Da gaske ke ce ko? Dan Allah ki faɗamin gaskiya cewa ke ɗin ce ba aljana ba ce Beenafah.."
Da wani irin sabon ɓacin rai Munira ta ƙwace mini hannuna tana mai yi mai wani irin kallo ta ce.
"Wai malam kana da hankali kuwa? Garjeje da kai za ka wani kamata ka riƙe ta. Ka faɗa mata duk abin da za ka faɗa mata da fatar baki mana. Mts!"
Tamkar wasu kuramen da basa gane komai sai yaren junansu haka muka ƙurawa juna ido musamman shi da yake ganin kamar ba ni ba, domin na yi matuƙar canja masa ta fuska da yanayin jiki gaba ɗaya. Idanunsa cike da hawaye ya ce.
" Dan Allah ki faɗa mini cewa da gaske ke ce Beenafah ba mafarki na ke ba..."
Jinjina kaina nayi domin ba shi tabbaci na ce.
"Wallahi ni ce Beenafah a gaske Yaya Ashiru ba mafarki kake ba...."
"To ina kika shiga tsawon lokaci? Rana, dare, sanyi, zafi, damana da iska, waɗannan duk ba su hana mini neman ki ba, ina kika shiga haka?"
Hannayena na saka na share hawayena ina girgiza kaina na ce.
"Gida Muka canza Yaya Ashiru, a ranar da muka dawo daga asibiti muka canja gida.."
"To ina wayarda na baki? Laifin me tayi da kika kashe ta kika hana mini jin labarin ku?"
"Wallahi tallahi ba kashe wayar nan na yi ba Yaya Ashiru, Bahrain ne ya danna ta ta shiga wani wuri sai layin ya rufe,."
"To amma Beenafah ai inda kin cire Layin kin kunna wayar za ki ga number ta ta fito gidan kira ko ba suna...."
Ji na yi Munira taja hannuna tana faɗin.
"Dan Allah ki wuce muje hakanan, wallahi Hajiya bata son irin wannan, idan ta ji za ta yi faɗa..."
Da ƙarfi ya zo ya fisge hannuna rai a ɓace ya kalli Munira ya ce.
"Ke dan Allah Malama ki saketa, kuma ki rufewa mutane wannan bakin naki. Kin san abin da yake tsakanina da ita ne da har zaki zo ki wani tsaya a gabana kina nema ki tunzurani.."
"Ka yi haƙuri Yaya Ashiru, don bata san ka bane kaima kuma baka santa ba..."
Wata uwar hararar ya maka mata sannan ya dawo da kallon sa gareni ya ce.
"Naga tana neman ita dole sai ta rabani dake... Wai har da wani cewa Hajiya ba ta son haka, a'a ba Hajiya ba wallahi makawuya..."
Zaro Ido na yi ina mai dafe ƙirji na ce.
"Dan Allah ka daina Yaya Ashiru ka yi haƙuri..."
Wani irin uban tsaki Munira ta buga tare da galla mishi wata uwar harara sannan taje ta karɓi sauran kayan ta saka a booth ta shiga mota ta zauna.
Kallon shi na yi cikin jin wani irin sabon yana yi, domin yanda ya ga na canza masa shi ma haka naga ya canza mini sosai kamar ba shi ba, ya ƙara ƙiba ya yi kyau. Na ce.
"Yaya Ashiru ni ma na yi ta neman ka, duk inda Napep za ta bi ta wuce sai na yi ta kallonta da saka ran cewa kai ne a cikinta, amma kuma wayam haka zan ga ba kai ɗin ba ne.."
"Allah sarki! Yanzu ki faɗa mini ina ne gidanku, domin waɗannan maganganun duk ba za su yiyu a nan ba,...."
Horn ɗin Oga Sule shine ya ja hankalina na kalli inda motar take sannan da sauri na ce.
"To ka bani numbernka zan kira ka da wayar Ya Jafaru idan na koma gida...Yanzu sauri muke an aikemu."
"To bari na bi ku a baya mana, sai in cim miki a gidan.."
Da sauri na girgiza kaina ina ɗan zaro ido na ce.
"A'a. Can ɗin ba gidanmu ba ne, gidan da nake aiki ne, ka bani numbern zan kira ka idan na koma gida."
Lalabe ya fara ko zai ji biro amma kuma tunda ba'a kasuwa yake ba yasan ba zai samu ba,hakan yasa cike da hanzari ya ciro wayarsa daga aljihu ya sake zare simcard ɗaya ya bani ya ce idan naje na saka zai kira ni zuwa yamma, ko kuma duk sanda na saka simcard ɗin in duba zanga numbern Umma sai in kira.
Daga haka muka rabu, wanda har bakin motar ya zo ya buɗe mini na shiga yana ta ɗaga mini hannu har sai da na daina ganin sa.
Daga ni har Munira babu wanda ya yi magana har muka shiga gidan na wuce ɗaki na kwanta shiru ina ta tunani.
Wani irin jimƙe Simcard ɗin na yi a cikin hannuna tamkar wadda akace za'a ƙwace mata shi.
Sai da muka kambala cin abinci, ina batun tafiya gida Munira ta kalle ni ta ce.
"Waye shi ɗin?"
Kallonta na yi, ina mai jin ba daɗi akan abin da ya faru ɗa zu na ce.
"Ki yi haƙuri."
Ɗan murmusawa ta yi tare da jinjina kanta ta ce.
"Ba komai."
Daga haka na yi musu sallama na tashi na wuce.
****
Da gudu ya juya ya koma gida jiki na rawa ya taradda su Ayya cikin tsananin ɗoki da murna ya ce.
"Ayya! Alhamdulillahi Rabbil Alameen! Allah yau ya bayyanar mini da Beenafah... Wallahi na ganta Ayya... Umma! A kasuwar Tudun Wada na ganta tana siyayya...."
Ido Ayya ta zaro waje tare da saka hannaye ta dafe ƙirjinta ta ce.
"Na shiga ukuna ni Ayyatu ya sake gamo da wannan hatsabibiyar a karo na biyu bayan mun shafe tsawon lokaci muna wahalar nema masa magani.."
Jiki na rawa ya matso gaban Ayya ya ce.
"Wallahi tallahi da gaske nake, ba Aljana ba ce mutum ce. Yanzu haka na bata Layina na ce idan ta saka ta kira Umma...Ayya wai kinga Beenafah yanda ta canza?"
Cikin gatse ta ce mishi.
"Ban ganta ba sai kai..."
Jinjina kansa ya yi yana murmushi ya ce.
"In Sha Allahu kuwa zan kai k..."
Miƙewa ta yi da sauri tana faɗin.
"Allah ubangiji ya tsareni nikam, ai wallahi an yi ɗaya ba za a koma ba."
Daga haka ta shige ɗaki ta bar shi nan tare da sauran mutanenda suka yi shiru suna sauraren su tare da Umma. A hankali Umma ta kalle shi ta ce.
"Shin yanzu ina kayan Jallof ɗinda kace a bari kaje ka siyo?"
Dariya ya fara yana wani sosa bayan kan shi ya ce.
"Umma! wallahi ni nama ruɗe, kwata-kwata na manta da cewa siyayya na je. Amma bari na koma yanzu-yanzu na siyo..."
Har ya kai ƙofa sai kuma ya dawo ya kalli Umma ya ce.
"Umma dan Allah ki ajiye wayarki a kusa, Beenafah za ta kira in sha Allahu..."
Cike da tuhuma Umma ta ce.
"Ka tabbata Beenafah ka gani Ashiru?"
"Wallahi na rantse da Allah ita ce Umma, bari ai dai za ku gani."
****
Ni kuma, Ina zuwa gida na faɗa jikin Ammie ina faɗin.
"Ammie wallahy yau na ga Yaya Ashiru a kasuwar Tudun Wada..."
Zaro ido Ammie ta yi tace.
"Da gaske Beenafah?"
"Wallahi kuwa Ammie. Kawai ban lura ba muna cikin siyayya kawai naga mutum gabana.... Kinga ma wani Layin ya bani ya ce in sa a waya zai kirani, ko kuma in kira lambar Umma akwaita a ciki.."
Na ƙarashe maganar ina mai warwaro simcard ɗin daga cikin hular kaina na nuna mata.
"Alhamdulillah! Haƙiƙa komai nisan dare gari zai waye. Ni ma ina so in gansa da iyayen shi in ƙara musu godiya..."
"Sosai kuwa Ammie. Bari na je idan Ya Jafaru nan ya ara mini wayarsa in saka in kirashi....shin yaushe ma ya ce zai wuce makarantar?"
Tana janyo ledar abincin da na ajiye ta ce.
"Gobe fa zai tafi. Baki sani ba daman?"
Girgiza kaina na yi na ce.
"Na sani. Kawai dai na manta ne tsabar ruɗewa wallahi... Bari naje na ji idan yana nan."
✍️ *OUM-AMEER* ✍️
*GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....
*PAGE 22*
Koda na shiga gidan yana parlourn Mama ya kambala guga yana ta shirye-shiryen kayansa na tafiya gobe.
Gefen akwatinsa na zauna fuskata cike da annuri ina ta dariya na ce.
"wai Ya Jafaru ashe tafiyar ka gobe ne.."
Hannu ya sage yana mai tsahirtawa daga saka kayan a akwati ya kalleni shima yana murmushin ya ce.
"Naga sai wani farin ciki kike, wani alherin ne ya samu haka?"
Bakina har kunne na ce.
"Ya Jafaru yau na haɗu da Yaya Ashiru Allah ya nufa.."
"Masha Allah! A ina kenan?"
"Wallahi a kasuwar tudun wada muka haɗu... Kaga ma simcard ya ƙara bani yace idan na dawo in saka in kira sa.."
Na ƙarashe maganar ina mai buɗe masa tafin hannuna na nuna masa Layin.
Jinjina kai yayi ya ce.
"Masha Allah...Shikenan hankali ya kwanta yau an samu Yaya Ashiru.."
"Wallahi kuwa. Dan Allah ga shi ka saka mini a wayarka, ya ce idan na saka akwai numbern Umma a ciki sai in kira."
Wayar ya miƙo mini yana faɗin.
"Ai kin san password ɗin, sai ki cire Sim2 ki saka a nan."
Ba ɓata lokaci na karɓa na buɗe murfin na cire na saka na sake mayarwa na rufe na kunna. Ƙoƙarin neman numbern Umma na shiga a contact sai gashi kawai ya kira.
Cike da zumuɗi na kara wayar a kunnena na yi masa sallama ina mai jin wani irin daɗi a raina.
Dakatawa ya yi tare da tsuro mini ido yana kallona, jin yadda muryata take sauka cikin nuna kulawa, da yanda nake wani blushing ina masa kwatancen gidanmu ya saka Ya Jafaru murmusawa.
Bayan mun kambala na ajiye masa wayar a gefen sa ina murmushi na ce.
"Wai Ya Jafaru Kaga Yaya Ashiru kuwa? Ya canza sosai kamar ba shi ba, ƙila kuma dai don na ɗauki tsawon lokaci ban gansa ba ne ko?"
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"Uhm!"
Daga haka ya miƙe ya iyarda saka kayan ya koma kimtsa komatsansa a wata Ghana most go.
Ganin hakan yasa na miƙe tare da ɗaukar wayar ina faɗin.
"Tun da aiki kake Ya Jafaru bari na je da wayar in jira zuwansa a can gidan."
Sake jinjina kansa ya yi ya ce.
"OK."
Ina fitowa na shiga gida na cewa Ammie ai na saka sim ɗin kuma har ya kirani yana hanya.
Kallona ta yi ta ce.
"Yau ba za ki je Islamiyya ba ne?"
Dariya na yi ina girgiza kaina na ce.
"Gaskiya Ammie yau ba zan je ba. Yanzun nan fa yace gashi nan zuwa, kuma kin san dole tunda bai san gida ba dole sai na je na zo da sh...."
Ringing ɗinda wayar ta ɗauka yasa na yi saurin duba wayar na ce.
"Yauwa, gashi nan ma ya zo. Cewa na yi ya tsaya daidai makarantar malam Ibrahim."
"Tau jeki ki zo da shi. Bahrain kam ya zo ya wuce kada ya yi latti."
Fitowa na yi cikin zumuɗi na isa wurin, daman bai fi gida biyar ba da yake tsakaninmu da Islamiyyar.
Tsaye yake jikin wani mashin roba-roba ya sha wankan wani yadi milk colour da hulla, ga wani sunglasses da ya ƙara fitowa da shi ya yi kyau sosai, sai wani ƙamshi yake mai daɗi da sanyaya zuciya.
Murmushi ya sakar mini kamar yanda nima na nufo shi da murmushin ina faɗin.
"Yaya Ashiru har ka ƙara so?"
Jinjina kan shi kawai ya yi ba tare da ya furta mini komai ba sai murmushi.
"To zo muje gida."
Gaba na yi wanda sai da na ɗan yi nisa sannan ya hau mashin ɗin ya biyoni a hankali har muka ƙara so.
Bahrain da ya fito cikin shirinsa na Islamiyya da gudu ya ƙara so ya rungume shi yana faɗin.
"Oyoyo Ya Ashirunmu."
Shafa kanshi ya yi yana dariya yace.
"Alaramma Bahrain! Kana lafiya? Ya makaranta?"
"Lafiya ƙalau Ya Ashiru, har na yi sauka an mini walima."
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"Kai masha Allah! Alhamdulillah! Gaskiya na yi murna. Allah Yasa Albarka."
Kallon mashin ɗin ya yi sai kuma ya kalli Yaya Ashirun ya ce.
"Ya Ashiru wannan Mashin ɗinka ne? Ina Napep ɗinka mai daɗi?"
Dariya ya yi masa wanda har ni dake gefe saida na murmusa akan hali irin na Bahrain. Kallon sa Yaya Ashirun ya yi ya ce.
"Napep tuni ta koma kuɗi a aljihu, wannan Mashin ɗin kuwa, na Yayana ne nawa Mashin ɗin yana Kano na baro..."
"To muje kai kaini Islamiyy..."
Wata irin uwar harara na makamasa ina faɗin.
"Banson renin wayau Bahrain! Ka wuce zuwa makarant.."
"Noo! Barshi na ajiye shi mana, Bahrain ɗina ne fa, ba ruwanki jirani yanzu zan dawo."
Daga haka ya sake haye Mashin ɗin sannan ya kalli Bahrain ɗin wanda ya gama ɓata min rai yace ya hau su tafi. Ina nan tsaye a ƙofar gida har yaje ya dawo sannan muka shiga gidan a tare ya zauna akan tabarmar da na shimfiɗa masa.