Ganin ido complete - Chapter 24
Ganin ido complete Chapter 24: Ganin ido complete Chapter 24. " A duk lokacin da aka kira sunan wanda kike so to tabbas sai zuciyarki amsa fiye da yadda…
3,338 words
" A duk lokacin da aka kira sunan wanda kike so to tabbas sai zuciyarki amsa fiye da yadda kike ji idan an ambaci wani daban, ko kuma idan kinji sautin muryar sa koda a waya ne za ki ji numfashinki ya ɗan tsaya, sai ki yi ta murmushi ba tare da wani dalili ba. Idan kika yi fushi da shi sai ki ji gaba ɗaya duniyarki ta ƙuntata, da zaran kuma ya furta miki kalmar ban haƙuri, sai ki ji zuciyar ki ta huce tamkar ruwan sanyi. Idan kika ga yana magana da wata ko kuma shi yaga wani wanda ba shi ba yana magana dake, sai ya ji wani abu ya motsa a ƙirjinsa na tsananin ki shi tamkar ana hura masa huta,amma kuma da zaran ya kalli kyakkyawar fuskarki mai lallausan murmushi sai ya ji ya wuce."
Shiru na yi ina mai ƙure ta da idanuwana yayin da ƙwaƙwalwata ta shiga cikin tsananin ruɗani da neman ƙarin haske, domin babu abinda nake hange da tunanowa sai Yaya Ashiru, idan haka ne tabbas ina cikin ruɗani. hakan yasa ban yi nauyin baki ba tambayeta cewa.
" Munira yanzu kina nufin waɗannan abubuwan duk alamomin soyayya ne?"
Jinjina kanta ta yi ta ce.
"Eh Beenafah. Wannan shi ne so wanda ba dole sai an furta shi da baki ba. A kullum za ki ga yana neman abubuwan da zai yi don kawai ya ganki a farin ciki, kullum yana so ya ji muryar ki, da supporting ɗinki ga dukkan abin da kika sakawa gaba."
Hannu na saka a gefen zuciyata na ɗan lokaci sannan na sake kallonta na ce.
"To idan haka ne, miyasa mutum baya iya fitowa ya furta kenan?"
"Saboda soyayya ba ta neman izini Beenafah! Ita ɗin tamkar iska ce mai shigowa sannu a hankali har tayi nasarar mamaye zuciya daga ƙarshe,ta gama nannaɗeki da farin ciki,baƙin ciki, damuwa, kewa, kishi ba tare da kin fahimta ba."
Kaina na sunkuyar ƙasa ina mai wasa da yatsun hannuna lokaci ɗaya kuma ina jin wani abu na daban a ƙirji na ce mata.
"To idan har ni waɗannan abubuwan sun nuna alamar na kamu da soyayya to shi kuma fa?"
Miƙewa ta yi tsaye tare da jinginawa jikin wardrobe idanunta cikin nawa ta ce.
"Sun ma fiki kamuwa Beenafah. Ashiru da Jafaru dukkan su suna tsananin ƙaunar ki. Na jima wannan al'amarin yana dukan zuciyata, sannan kuma, ban san mi zai faru zuwa gaba,amma dai ki kula, domin soyayya kamar wuta ce wadda idan har kika kuskure, to tabbas za ta ƙone ki ƙurmus, idan kuma kika yi nasara a cikinta;tana iya zama hasken da zai haskaka maki hanyar rayuwa har ƙarshen numfashinki......"
Mun jima Munira na mini wankin ƙwaƙwalwa wanda na kwashe tsawon lokaci ban ɗauki haske akai ba sannan daga ƙarshe suka fice wurin aiki suka barni nan.
Kwantawa na yi a ƙasa na yi lamo! tamkar ruwa sun cinye ni domin na kasa yin wani kataɓus. Babu abinda nake ji da gani idan ba mutum biyu ba. Mutum biyun da suka tsaya mini matsayin inuwa da garkuwa. su ɗin mutane ne masu matuƙar muhimmanci da nake tunanin su ɗin yayyune a gare ni, ashe duk wannan soyayya ce.?? Wani irin zabura na ƙara yi na miƙe zaune ina wani girgiza kaina jin yanda wasu hirarrakinmu da kuma wasu actions ɗin su both Ya Jafaru da kuma Yaya Ashiru suka shiga dawo mini beat by beat waɗanda a yanzu suke alamta mini cewa tabbas suna nufin soyayya a gare ni. Zuciyata ce ta ƙara tsinkewa har ban san lokacin da wasu zafafan hawaye suka silalo mini ba musamman dana tuna cewa wai Yaya Ashiru yace yana so ya sanar dani wata magana. To wace magana ce wannan yake so ya faɗa mini wacce ba zai iya jira har zuwa dare ba??
Ina nan kwance tsawon lokaci sannan daga baya Haula ta shigo ta kalleni ta ce.
"Beenafah! Ko kinyi bacci ne?"
A hankali na yunƙura na miƙe zaune ina ma kallonta da idanuna waɗanda suka canza launi tsabar ruɗanin da nake ciki murya a ƙasa na girgiza kaina na ce.
"Ba bacci nake ba. Ya akayi?"
"Yanzu Aunty Labiba ta kirani tace akwai baƙin da za su zo yau ɗinnan, saboda haka dole muna da buƙatar yin girke-girke kamar yanda ta buƙata. Sannan kuma ta ce Uncle Ishaq wai shima yana hanya ya ta so daga Sokoto, yace dan Allah a yi masa girki shaf-shaf domin yau yake so ya wuce Katsina. To shine nake so ki je ki yi na Uncle Ishaq ɗin tunda ba mai yawa ba ne mu kuma sai muji da wannan ɗin na baƙin Hajiya."
"Waye Uncle Ishaq??"
Maimakon ta bani amsa kai tsaye, ba ta yi hakan ba, kawai dariya na ji ta sheƙe da ita sannan daga baya ta tsahirta ta ce.
"Hajiyar gidan nan, to ƙaninta ne ɗan autan su. Mugun ɗan renin hankali ne na ƙarshe."
Jinjina kaina na yi sannan na ce.
"To mi zan dafa masa?"
Juyawa ta yi ta nufi ƙofa tana faɗin.
"Duk abin da kika ji za ki iya tunda shaf-shaf ya ce."
Ko bayan fitar ta, na kusa minti biyar sannan daga baya na tashi na shiga toilet na yi fitsari sannan na wanko fuskata na fito na ɗauki wayar na wuce kitchen na fara aiki.
Karon farko tsumayi nake na jiran kiran Yaya Ashiru, amma kuma a yanzu; fargaba nake ji ta rashin sanin dalilin kiran.
******
Lieutenant Commander Emraan Attahiru Araam. Shi ɗin Naval Officer ne (Sojan Ruwa). Yana aiki ne a Nigerian Navy Logistics Command, Kaduna state Nigeria. Yana daga cikin masu jagorantar rukunin sojoji, kula da kayayyaki, tsaro da kuma gudanar da ayyuka na musamman.
Tun da ya fara aiki, a nan Kadunar yake tsawon shekaru, sai yanzu da ya samu transfer zuwa jihar Rivers State a kudancin Nigeria.
Bayan ya samu takardar transfer sai kuma a ka haɗa mishi da takardar hutu na wata ɗaya domin samun lokaci da iyalin shi sannan kuma ya samu damar shirye-shirye na komawa sabon wurin aikinsa.
Da wannan ya tattaro a daren jiya ya dawo Gusau, sai dai kuma; ta wata fuskar bai ga amfanin hutun da ya samu ba, domin Hajiya bata nan haka zalika Ziza itama bata ƙasar. Shiyasa ya ji abin yayi masa wani iri, duk da cewar Ziza ta tabbatar masa da cewa nan da sati biyu za ta dawo In Sha Allahu.
Yana sauka gidan sa ko wanka bai tsaya ya yi ba, yana gama ajiye kayayyakinsa ya tattaro kawai ya dawo gidan Hajiyarsa wanda bai shigo gidan ba sai kusan sha biyu na dare. Hakan yasa babu wanda yasan cewa yana gidan har su Munira.
Tun da ya dawo masallacin asuba ya koma bacci bai sake farkawa ba sai misalin sha biyu saura na rana. Yana tashi ya janyo wayarsa inda a nan yaga kiran Ziza kusan 5miss calls,sannan kiran Blood sis (Aunty Labiba) 2miss calls da kuma kiran Hajiyarsa shima 2miss calls.
Ajiye wayar ya yi ya sauka daga kan lallausan gadonsa wanda tun na samartakarsa ne ya shige toilet ya wanke bakinsa da fuskarsa sannan ya fito ya saka wasu simple nic and shirt ya fito zuwa kitchen. Idan zai iya tunawa tun abincin da yaci a gidansa na Kaduna bai ƙara cin wani ba,saboda haka he need something to eat kafin Ziza ta ji ya zauna da yunwa ta fara mishi kuka.
Tun da ya ƙara so ƙofar Kitchen ɗin ya ji sautin Muryarta mai cike da nutsuwa a hankali tana magana da alama akwai maganar da take mai muhimmanci.
Ɗan ƙara stepping ya yi gaba kaɗan ya tsaya jikin ƙofar ba tare da ta sani ba ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa ya tsurawa bayanta kallo wanda ita gaba ɗaya hankalinta ya ɗauku ga aiki da kuma magana a waya.
Tun da na shigo Kitchen ɗin na fara aiki Yaya Ashiru bai kirani ba sai gab da ina batun kambala aikina. Sai da ya kira kusan sau uku sannan a na huɗu na yi picking a darare ina mai sakata a amsa kuwwa domin kada maganar ta hanani ƙarasa aikina cikin lokaci daman ga Haula sai zanzamata take wai Aunty Labiba ta ƙara kira.
A yanda ya ji yanayina, sai hakan ya sage mishi gwiwa tare da zare mishi duk wani kuzarin da ya zo da shi domin bai taɓa ji na a haka ba.
Juyin duniya ya yi dani akan in faɗa masa miye abin da yake damuna na ce mishi ba komai.
Jin na kafe kai da fata ina faɗin ba komai yasa shi sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Ko in bar ki zuwa an jima idan kin shirya sai muyi maganar?"
Girgiza kaina na yi tamkar yana a gabana na ce.
"A'a! Kawai ni dai dan Allah idan ka yi niyyar faɗa mini kawai ka faɗa bana son jan rai, ba zan iya jira har daren ya yi ba."
Jin irin amsata ya sa shi sadaƙarwa ya ce.
"Ko na yi niyyar faɗa miki Beenafah sai inji gabana yana faɗuwa...dan Allah kada ki yi mini mummunar fahimta.."
"In sha Allahu matuƙar dai ba ka kauce hanya ba ba zan yi maka mummunar fahimta ba, ballantana ma nasan halin ka nasan abin da za ka iya da wanda ba za ka iya ba.."
Wani murmushi ya saki mai sauti wanda har ina iya jiyosa sannan ya ce.
"Kin taɓa jin wani abu akaina kamar yanda ni ma nake ji Bee..."
Da shigowarsa Kitchen ɗin da fisgo wayar daga inda na ajiye ta ya rotsa a ƙasa duk ba'a yi second talatin ba.
Tamkar wacce ta yi mummunan gamo, haka na shiga ja baya hankalina a matuƙar tashe, jikina sai wani ciccira yake domin ban san da wanzuwarsa ba a wurin.
Shi kuma cikin wani irin hargagin da bai san ya iya shi ba ya watso mini idanunsa waɗanda suka kaɗa lokaci ɗaya suka canja launi ya ce.
"Daman abin da kike yi kenan? I... I were thought cewa you are too small for all this that's why na nisanta kaina da ke har zuwa lokacin da ya kamata....I thought yanda kike baya-baya kina yin kamar kina tsoron mutane lokaci kike buƙata domin ki gama sanin miye rayuwa?.....but ashe ni kika mayar sauna ko!!!"
Ban san lokacin da na fashe da wani irin kuka ba, a firgice na faɗa jikin gini tare da runtse idanuwana domin tsawar da ya daka mini ba ƙaramin tsoratani ya yi ba.....
Ban ƙara tsorata ba, sai da ya jimƙo tsintsiyar hannuna ya wani fisgoni gab da gab ya ce.
"Buɗe idanunki ki kalleni... Buɗe idanunki ki kalleni na ce!!!"
Cikin tsananin tsoro da ruɗani na yi saurin buɗe idanun nawa ina kallon shi still ina kuka na ce.
"Nannn....na kalle ka! Ka yi haƙuri wallahi na kalle kaaa!"
Lumshe idanunsa ya yi a hankali ya sake buɗesu a cikin nawa ya ce.
"Ni Emraan! Tun a ranar farko ban yi kuskuren kiran ki da mata ta ba, domin ni ne nan wanda zan aure ki. Ban ja baya don Labiba ta shata mini layi ba... Na yi baya ne don jiran lokacin da ya da ce."
Yana gama faɗin haka ya yarfar da hannuna kawai ya juya ya yi tafiyar sa.
Ganin da gaske ɗin ya tafi, yasa a gigice na ruga na koma ɗakinmu tare da duƙunƙunewa sosai na shiga raira wani sabon kuka.
Ƙwaƙwalwata ta rikirkice a halin yanzu. Tambayar kaina na fara, cewa; Shin wannan ɗinma da gaske ne yake faruwa ko kuma ƙwaƙwalwata ce ta fara samun matsala? Emraan! Emraan ni Beenafah zai ce wai ni zai aura? To ta ya ya ma??? Yah Allah ina roƙon ka, idan ma bacci nake ka farkar dani daga wannan mummunan mafarki da na tsinci kaina a ciki. Wace ce ni da har Emraan zai yi wannan furuci a gare ni? Aunty Zi...Ziza!!! Ji na yi hankalina ya sake yin wani irin ƙololuwar tashi tunawa da Aunty Ziza da na yi. Ya ilahiy! Rabbi kasa wannan ya zamto mafarki a gare ni, domin haƙiƙa na fahimci so yake ya katse mini hanyar neman abinci na wanda wallahi sam ban shirya ma hakan ba.
Ina nan a kwance na ji shigowar Su Munira suna faɗin in tashi in shirya abincin a table Idan na kambala, sai dai kuma;shiru ba amsa domin ba zan iya kallon su ina cikin wannan yanayin ba. Haula, ganin yan da Aunty Labiba ta matsa mata da kira, dole hakan yasa ta nufi kitchen ɗin da kanta yayinda Munira ta tsaya a kaina tana tuhuma wai ko akan firarmu ta ɗazu ce yasa na shiga damuwa wanda ni dai ƙala ban ce mata ba.
Haulatu na shiga Kitchen ɗin turus ta ja ta tsaya ganin waya tarwatse a ƙasa ta yi ɗai-ɗai-ɗai. Duƙawa ta yi da sauri ta ɗauko wayar ta shiga dubawa.
"Tabbas wannan wayar Beenafah ce da ta zo da ita. To ya akayi haka ta faɗo ta tarwatse? Gaskiya kam dole ta yi kuka, ashe abinda ya faru kenan. Ko ya akayi har ta yi wannan irin mummunar faɗuwa?"
Daga haka ta tattara ta ajiye a gefen drawer sannan ta yi sauri ta shirya abincin tunda daman already na kambala kaɗan ne ya rage.
Bayan ta kai abinci sai ta koma kitchen ɗin ta ɗauko wayar ta dawo ɗaki cike da alhini tana nunawa Munira. A tare suka shiga janjantamin tare da bakin cewa in yi haƙuri ƙaddarori ne.
Ni dai ƙara lafewa na yi kawai ina mai yin godiya ga Allah wanda yasa fashewar wayar ta zama dalili a tsakanina da su, domin kuwa, ko kwana za su yi suna tambayata wallahi ba zan iya faɗa musu wannan abun da ya faru ba.
Da ƙyar na samu na rarrafa na yi sallah sanadiyyar wani irin tsananin ciwon da kaina ke yi ta dalilin wannan kwamacalar da na tsinci kaina a ciki. Bayan na gama na sake komawa na kwanta ban farka ba sai kusan ƙarfe huɗu saura. Da wani irin zazzaɓi mai zafi na farka har sai da su Munira suka bani magani na sha sannan na samu na lallaɓa na tafi gida cikin wata kalar sabuwar fargabar da ban san mi zan cewa Ammie ba game da wayar.
******
Gidan Daddy ya kacame da farin ciki da guɗa na mashahurin lefen da aka kawo na su Hassana, lefe ne abin da ake kira lefe. Farin cikin Mummy ya kasa ɓoyuwa domin yau ne ta ƙara tabbatarwa cewa lallai auren nan yinsa za'a yi because an riga an saka date nan da wata biyu.
Kuma an riga an tsara cewa Idan auren ya rage saura sati biyu to za su ɗunguma su koma gida Zamfara both familyn Daddy da na Alhaji Mansur Anka duk da cewa ita Mummyn ba haka ta so ba, domin ta ci burin yin bukin ta anan Abuja, buki wanda sai guda-guda ne suka taɓa gudanar da irinsa kaf a faɗin ƙasar. Sai dai kuma wannan burin nata ba zai cika ba domin Alhaji Mansur ya nuna musu yin hidima a gida tafi sauƙi da kuma ƙarfafa zumunci, hakan shi ne ke bayar da duk wata dama ga danginka su samu halarta da kuma yin participating yanda ya kamata. Idan kuma suka ce su za su bukin su a Abuja su kuma suna Zamfara abun ba zai yi daɗi ba.
A wannan matsayar suka amince dukkan su wanda Mummy ta shiga yin shirye-shirye babu kama hannun yaro. Kuɗi ta shiga narkawa ba ƙanana ba tun daga kan kayan ɗaki, kayan buki da komai da komai.
Duk budurin nan da ake Hassana Sam bata cikin farin ciki domin a yanzu ne ma take ƙara jin tsanar Ameer fiye da can baya. Tun suna yin abin su tsakanin ta da 'ƴar uwar ta har Husaina ta kai ga sanar da Aunty Aysha domin su samu su shawo kan Hassana ta yarda ta amince. A yanda su ka ga Mummy ta ɗauki al'amarin auren nan na su da girma tabbas idan Hassana ta ce ba za ta amince ba komai na iya faruwa da Mummy. Hakan yasa suka tsaya a kanta ba dare ba rana amma kuma fir! Ta shafawa idonta toka ba ta ji bata gani. Bata ƙara shiga tsananin tashin hankali ba sai da taga jiya an kawo lefen nan an saka rana. Hakan yasa ko abinci ta kasa ci, babu abinda take idan ba kuka ba.
Tana kwance akan gadonta Biba ta shigo ɗauke da kayan Breakfast ta ajiye a saman wani glass table ta ce.
"Hassana ga abincin nan Husaina ta ce na kawo mik..."
Wani irin ihu ta daka mata tare da miƙewa zaune tana mai ƙara fashewa da kuka ta ce.
"Ba zanci ba Biba!......Ki ɗauke ki fitar da shi yanzu.."
Da sauri Biba ta ɗauke trayn ta juya ta koma kitchen inda ta tarar da Husaina ta faɗa mata yanda suka yi da ita.
Da kanta ta amso abincin ta dawo ɗakin ta ajiye sannan ta zaune gefenta a hankali ta dafa kafaɗarta ta ce.
" Ki yi haƙuri mana dan Allah Hassy, rabon ki fa da abinci tun jiya..."
Cikin wani gunjin kuka ta wai go ta kalleta cike da karyewar zuciya ta ce.
"Hussy na rantse miki da Allah idan har ban auri Salman ba komai zai iya faruwa dani.... Sannan matuƙar aka aura mini Ameer kuwa! To tabbas sai na kashe kaina!"
Wani irin zabura Husaina ta yi jin wata kalmar da ta girmewa tunaninta na cewa wai za ta kashe kanta. Baki na rawa cikin tsananin tsoro ta maimaita kalmar a matuƙar razane da cewa.
" Ki kashe kanki Hassana? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Daga haka ta fito da gudu ta faɗo parlourn da su Mummy ke zaune suna breakfast ita da Daddy da Humaida ta shiga girgiza kanta ido cike da ruwan hawaye ta ce.
"Mummy! Daddy! Dan Allah dan girman Allah kada ku aurawa Hassana Ameer wallahi tallahi bata son sa....duk tsayin lokacin nan, daidai da rana ɗaya ba ta taɓa jin so da ƙaunar sa ba a ranta...Ba shi take so ba, ba shi take muradi ba...Salman ne wanda take so, shi ne wanda take so ta Aura ba Ameer ba... Ta ɓoye hakan ne kaɗai saboda ke Mummy....yanzu kuma ta kai matakin da ba za ta iya controlling kanta ba, ta ce idan akayi kokarin tilasta mata tabbas za ta kashe kanta..."
Wata irin zabura Mummyn tayi tare da saka hannu ta ture gabaɗaya kayan abincin ke gabanta a saman table ɗin suka watse lokaci ɗaya suka tarwatse. Cike da ɓacin rai ta wani daka mata tsawa da faɗin.
"Ina Hassanar take???"
Da gudu Husaina ta koma ɗakin ta janyo hannunta suka dawo suka dire a tsakiyar parlourn suna masu fashewa da kuka a tare.
Gabanta Mummy ta ƙara so cike da tsananin ruɗani da tashin hankali ta ɗago haɓar ta suna kallon juna da ita cikin kakkausar murya ta ce.
"Na ji saƙonki Hassana, kuma na gode da irin sakayyar da za ki yi mini..."
Girgiza kanta ta shiga yi tare da runtse idanuwanta ta ce.
"Ba haka bane Mummy! Ba haka bane! Na yi ta ƙoƙarin ganin na cika wannan umarnin na ki, amma kuma na kasaahhh! Ki yi haƙuri Mummy..."
Wani irin gigitaccen mari ne ta kifa mata sai da ta hantsila gefe tana mai ganin wasu taurari suna shawagi akan gilashin idanuwanta.
Cikin zafin nama Daddy ya miƙe ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya kalli Mummy cike da ɓacin rai ya ce.
" Haba Hajiya Zaliha! Miye ya yi zafi haka? Yarinyar nan fa ba Allah ta saɓawa ba...."
Cikin nuna isa da ƙafafa ta kalle shi a zafafe tana mai jinjina kanta ta ce.
"Tabbas ba Allah ta saɓawa ba, amma kuma ni mahaifiyarta ina da haƙƙi da ita, tunda ta saɓa mini wallahi dole ta karɓi hukunci, kuma wallahi tallahi na rantse da Allah, matuƙar dai ban mutu ba itama kuma bata mutu ba to dole sai ta auri Ameer ɗan gidan Alhaji Mansur Anka...."
Janye jikinta ta yi ta dawo inda suke fuskantar juna ita da Hassanar ta ce.