Kenza eBookz

Ganin ido complete - Chapter 37

Ganin ido complete - Chapter 37

Ganin ido complete Chapter 37: Ganin ido complete Chapter 37. " Wannan gidan...lokacinda aka gama ƙerashi....mun shigo cikinsa muna farin ciki aka saka…

3,371 words

" Wannan gidan...lokacinda aka gama ƙerashi....mun shigo cikinsa muna farin ciki aka saka kaya lokacin da aka saka rai da auren sa da Hanifah, ƙarshe da auren bai yiyu ba, haka aka rufe shi cike da baƙin ciki na tsawon lokaci, babu wanda ya sake takowa cikinsa ko sau ɗaya sai yanxu da aka yi nasarar samun wacce za ta shigo cikinsa....Amma! Saboda son zuciya irin na ki, ko yau ga shi ba'a yi nasara ba domin haka za'a sake rufe shi cikin baƙin ciki kamar can baya."

Daga hakan itama ta fi ce ta koma ɓangaren Hajiyar, su Nadee na ganin ta fi ce suka miƙe a tare suka bi bayanta. Ta ɗauki tsawon lokaci zaune a inda suka barta tana ta kuka yayin da zuciyarta ta sarƙafe da wata irin nadama wacce ta ji ina ma tun farko ba ta fara aikata wannan aika-aikar ba. Ta yi ta tunanin lokaci makamancin wannan, amma kuma da yake shaiɗan ya nutsa zuciyarta sosai har ta yi nisan da ba ta jin kira sai taci gaba tana ganin za ta iya yin nasara musamman da ta ji ya ce ya bar ƙasa har Abada saboda ba zai iya zama babu Raudah ba....Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ina ma ace za ta iya dawowa da hannun agogo baya? Ina ma ace tun farko ba ta amince da wannan bahaguwar shawarar ba? Da yanzu mutuncin ta bai zube a gaban 'ƴa' ƴanta ba. Idan wannan abun kunyar ya fita ina za ta tsoma ranta ta ji sanyi?... "

A hankali ta ji takun takalmi a bayanta, hakan yasa ta waigo da sauri tare da miƙewa tsaye.

Hairiyyah ta gani tsaye tana ta kuka tana girgiza kai. Da gudu ta zo ta Rungumeta tare da fashewa da wani kukan tana faɗin.

" Hajiyaa! Haƙiƙa kin aikata babban kuskure mai muni da mafi girman kunya a duniya...Amma ni ban san kowa ba ban san komai ba idan ba ke ba Mahaifiyarta, da kuma Yayana Muhammad da sauran 'ƴan uwana. Kun bani tarbiyya yanda ya kamata musamman ke ɗin nan! A yanzu Ke ce wadda kika ɓata komai, amma ina roƙonki ki yi tunani mai kyau, kada ki sare....Ubangiji mai yafiya ne muddin bawa ya yi tuba na gaskiya...Ke ce kika ɓata, saboda haka ke ce za ki san yanda za ki gyara. Kin fi kowa sanin waye Ya Mohaa..."

Murya a raunane ta ce.

" Hairiyya wallahi sharrin shaiɗain ne dan Allah ku yafe mini.. "

" Ba komai...Allah yasa mu dace yasa kuma mu fi ƙarfin zukatanmu."

Tana kambala faɗar haka ta ja hannun Hajiyar tana faɗin.

" Mu je... Mu je gida ki huta."

*******

Tun da ya daka mini wannan tsawar na sha jinin jikina na lafe wuri ɗaya a hankali ina ci gaba da raira kuka ba tare da sauti ba....Tsoro ne fal a ƙasan raina amma kuma ban san yanda zan yi ba. Abun da na yarda da shi shi ne har abada na san ba zai iya cutar da ni ba. Babu tunanin da bai zo mini ba musamman na su Aunty Labiba da Hajiya.....ina yi ina lissafi har bacci ɓarawo ya yi nasarar sa ce ni.

Ban san cewa na yi bacci mai nauyi ba sai da na motsa a hankali kwatsam na ji ni cikin jikin mutum ga wani irin ƙamshinsa da ya cika mini ƙofofin hancina, ina buɗe idona naga hannunsa ɗaya kewaye dani ina kwance kan ƙirjinsa ya ƙanƙameni sosai sannan ɗayan hannun kuma yana riƙe da waya a kunnen sa yana magana.

Janyewa na yi da sauri na matsa baya ina wani muzurai gabaɗaya jin yanda kunyarsa ta gama kamani. Shi kam Ko kallona bai yi ba ballantana ya nuna alamar cewa ya fahimci ma farkawar tawa,wayar sa kawai ya ci gaba da yi wanda yana yi yana kallon gefen windown da yake zaune tamkar bai san da wanzuwata a wurin ba. Nima windown da ke gefena na ware ido ina kallon waje kamar yanda yake kallo. Duk da cewa rufe take ruf da duhu an sanya mata tinted ko'ina, hakan bai hanani fahimtar cewa garin ya gama yin haske ba. Ma'ana kenan tunda muka fito muke tsula gudu bamu tsaya ko'ina ba har gari ya fara haske. 'Sallah fa?' na furta a zuciyata domin tabbas ba mu yi sallar asuba ba.....shiru ni dai na yi ina ta istigfari a raina domin ba ni da laifi shi ne mai laifin, ko zunubi ne shi a za'a rubutawa ba ni ba. Hakan yasa na ƙara jinginawa jikin car seat ɗin tare da lumshe idanuwana kawai ina tunanin Ammiena ba tare da sanin inda muka dosa ba.

Lakeview Crescent, Asokoro, F.C.T., Abuja, Nigeria.

A hankali motar farko dake gaba mai ɗauke da jami'an Secret Tactical Guides da suka shahara wajen bada kariya da tsaro a wurin manyan mutane masu ƙumbar susa suka shiga sarrafuwa domin sun iso madakatar mai gidan na su. Motar ƙirar Range Rover sentinel ce ta Ƙarya corner in a slow motion ta shiga titin unguwar da gidansa yake. Sai mota ta biyu Mercedes-Maybach S680 Guard Edition wadda ita ce motar da muke ciki. Sai kuma A bayanmu, wa su G-Wagon Brabus ne guda biyu masu ɗauke da bodyguards ɗinsa waɗanda ke sanye da black tactical suits, earbud da kuma bulletproof vests.

"Eagle One approaching Asokoro zone, switch to Silent Protocol.....Repeat, silent mode activated."

Ɗaya daga cikin jami'an ya faɗa ta hanyar sadarwar da suke tafiyar da aikin su (wannan wani yare ne na masu tsaro wanda suke amfani da shi a sirrince wanda da wuya mutum ya iya fahimtar abin da hakan ke nufi idan ba kana aiki tare da su ba ne. Ma'ana suna nufin Engineer Muhammad Attahiru Araam ya iso.)

Lokaci guda motar lead escort ɗin ta kashe na'urar tare da ƙara rage gudu fiye da na baya ta sulale cikin lakeview Crescent. Babbar unguwace mai gate-gate ɗinda ba ka isa ka wuce ba sai an tantance da zuwanka.

Muna isa, ƙofar gate ɗin katafaren gidan da ta kasance automatic ce sai ta buɗe kanta cike da wani irin sauti mai nuna alamar tsaro.

Muna shiga cikin zafin nama suka sauko suka buɗe masa ya fito. A hankali ya zago inda nake zaune ya buɗe da kansa ya riƙa hannuna a hankali ya fito dani. Ina haɗa ido da su na ji wani irin matsanancin tsoro ya kamani tamkar kace ƙyat! Na zura da gudu. Sai yanzu na ƙara godewa wannan veil ɗin da yake kaina, domin da ace babu shi da yanzu haka za su riƙa kallona kamar wata Stella. Ina ganin suna wani gaisheni na ƙara janyo veil ɗin na rufe fuskata domin bana ƙaunar ma haɗa idanu da su tsabar yan da suke firgitani.

Wani robotic sound na ji daga jikin bangon ƙofar yana faɗin.

"Security Level: Maximum....Intrusion mode:Activated"

A hankali cikin takunsa na zaratan Maza ya fara jana cike da nutsuwa ba kamar jiya da ya janyoni da ƙarfi ba muka taka muka shige gidan wanda yake upstairs ne mai hawa uku na ji da gani.

Muna shiga a main parlour muka tarar da masu aiki maza da mata sun yi cirko-cirko suna ta faman miƙa mana gaisuwa.

Bai ko tsaya tanka su ba muka zarce a hawa na biyu muka yada zango a tsakiyar parlour inda a nan ne ya buɗe wani ɗakin da kansa muka shiga. Kallona ya yi a karon farka idanunmu suka sarƙe ya wani lumshe a hankali ya buɗe in a calm voice ya ce.

"Ki yi sallah a nan."

Daga haka ya juya ya fi ce.

Tashi na yi na zazzaga ɗakin wanda sosai na ji ya ƙayatar dani, sannan na wuce banɗakinda ya yi mini tamkar wani ɗakin bacci akan faɗin sa da tsaruwarsa. Hankali kwance na cire kayan jikina na gama duk buƙata ta sannan na yi wanka na yi alwala na ɗoro veil ɗina na fito.

Ina zuwa kan makeken gadon ɗakin na tarar da wasu shopping bag an zubesu a nan. Janyowa na yi na buɗe wanda ba komai a cikinsu sai kayan amfanina da alama yanzu aka siyo su. Shiryawa na yi shaf-shaf cikin wata haɗaɗɗiyar Abaya peach colour na zuba hijabi na gabatar da sallah Asuba. Bayan na kambala ina nan a zaune tsawon lokaci ban ji ɗuriyar kowa ba wanda hakan yasa na miƙe a hankali na buɗe ƙofar na fito.

Zaune na gansa a kan 3seater ya tallafe gefe-gefen kumatunsa yana kuka wiwiwi tamkar wani ƙaramin yaron goye. A gigice na isa garesa ina faɗin.

"Subhanallah! Ya Mohaa mi ka ke yi haka? Ka yi haƙuri dan Allah..."

Janyoni ya yi jikin sa har sai da na ji na tsorata ya ƙanƙameni gam tare da manna fuskarsa akan ƙirjina wanda har ina jin saukar ruwan hawayensa akan skin ɗina, ga kuma kwantaccen Sajensa da ke ƙara sa tsikar jikina tana ta shi yana wani gugar jikin nawa. Sosai jikina ya ɗauki ɓari amma kuma ganin yanda yake kuka ba ƙaramin tausayi ya bani ba. Haƙiƙa na san zafin cin amana fiye da kowa a duniyar nan, Hakan yasa duk da ina a tsoracen na saka hannayena na zagaye wuyansa cike da tausayinsa ni ma na fara hawaye ina faɗin.

"Ka yi haƙuri... Allah yana sane da kai...!!!"

Ya jima sosai yana kwararar da ruwan hawaye wanda sai da ya gaji don kansa sannan daga ƙarshe a hankali ya sassauta tare da janye jikinsa ya buɗe idanunsa da suka rine sosai suka canja launi ya kalleni cike da ƙwarin gwiwa ya jinjina kai ya ce.

" Thank you... Thank you for saving me..."

Daga haka ya janyo wata ƙaramar wayarsa ya daddana a hankali ya kai wayar saitin kunnena kurum ba tare da ya ce komai ba.

Jin muryar Ammie na yi tana mai yin sallama a cikin wayar. Cikin farin cikin jin sautin muryar ta ta na ce.

" Halo Ammie... Ammie ina kwana!"

"Lafiya lau Beenafah. Ya gajiya ya kuma tashin mai gidanki? Ina fata yana lafiya?"

Kallonsa na yi kamar yanda shima ɗin yake kallona ko ƙyaftawa babu, ɗan murmusawa na yi na ce.

"Lafiya lau muke Ammie, ga shi nan a zaune yana gaishe dake. Ina Bahrain, ina Abbu ina su Mama??"

Murmushi ta yi wanda har ina iya jiyo sautinta sannan ta ce.

"Beenafah kenan! Kowa yana nan lafiya, Bahrain bai tashi bacci ba kin san shi da samun wuri."

"To Ammie idan ya tashi ki gaishe sa da Abbu."

"Za Su ji In Sha Allahu... Su Aysha ma har sun ta so.."

Cike da mamaki na ce.

"Ammie tun yau za su koma kamar ana korar su??"

"To Beenafah, ke da suka je domin ki amma kuma tafiyar uzurin mijin ki tasa kin tafi kin bar su mi za su tsaya jira??"

Sake ɗago kaina na yi daga wasa da yatsun hannuna da nake na kallesa wanda har yanzu ya kasa ɗauke idonsa a kaina cike da mamakinsa na jinjina kaina kawai na ce.

" Uhm! Haka ne kuma. To Allah ya tsare. "

" Amin. Sai an jima na gode."

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....

*PAGE 35*

A hankali ya zamar dani gefen sa saman kujerar ya tashi ya sauka ya fi ce daga parlourn. ina nan zaune na yi shiru ina rarraba ido kusan 15minute sai ga shi ya dawo ɗauke da trayn abinci a hannun sa. Ɗan ƙaramin Wood table dake gefe ya janyo ya ɗora tray ɗin sannan ya zauna a kusa dani ya ɗauke mug ɗin Tea mai zafi-zafi ya kai hannun sa zuwa bakina.

Zaro ido na yi tare da ɗan matsawa baya kaɗan ina girgiza kaina. Hannuna ya janyo ba tare da ya ce komai ba ya bani cup ɗin sannan ya buɗe plate mai ɗauke da wainar ƙwai da Irish ya saka fork a ciki ya ɗan ƙara turomin zuwa gabana sannan ya miƙe ya fi ce.

Kaɗan na sha Tea ɗin ba wani mai yawa ba sannan na janyo plate ɗin shi ma dai na ɗan tsakura kaɗan na rufe na ajiye.

Ina nan har misalin sha biyu na rana sai ga shi ya sake haurowa ya shigo. Ƙasa na yi da kaina a hankali bayan mun haɗa ido da shi ina jin yanayin sautin bugun zuciyata na ƙaruwa a hankali wanda ban san dalili ba.

Zaunawa ya yi can gefen ɗayar kujerar da nake zaune ya yi shiru ba tare da ya ce mini komai ba. Nima ganin hakan yasa na shiga murza yatsun hannuna waɗanda suka ji jan ƙunshi suka yi kyau kamar su tabbata a haka. Duk da bana kallon sa, hankali na da idanuwana suna kansa, a ƙasa-ƙasa nake kallon duk motsin da ya yi kamar yanda shi ma yake kallona a kaikaice. Daga ƙarshe dai bayan mun gama zaman kuramenmu ya tashi ya kunna makeken TVn da yake jikin bangon parlourn. Zee world ya kamo mini sannan ya tako a hankali ya ajiye mini remote ɗin a gefena. Ya sake ficewa.

*********

Gefen su Aunty Labiba kuwa, gari na wayewa bayan su Aunty Aysha sun wuce, ta tattara su Adeel ta wuce gida ba tare da ma ta yiwa Hajiya sallama ba.

'ƴan buki kowa sai ɗokin zuwa ganin idon amaryar Mohaa yake daman sun ce jiya ba su ganta da kyau ba. Da dabara da komai suka sanar da su cewa uzurin gaggawa ne ya taso wa Mohaan shiyasa ya yi asuba suka wuce. To sanin cewa shi ɗin ba mazauni ba ne sai hakan bai ba su mamaki ba.

Nadeeyah ma misalin ƙarfe goma na safe ta fito ita da yaranta su uku ta isko Hajiya a bedroom ɗinta tana zaune ta jikina a pillow still da ruwan hawaye a kan fuskarta ta ɗago jiki a sanyaye ta kalli Nadeeyah a hankali ta saukar idonta.

"Hajiya ni zan tafi. Allah ya bamu alheri."

Daga haka ta juya ta fito inda ta tarar da su Dija zaune suna jiran kakar tasu ta fito.

"Mummy ina Grandma? Ba za ta fito muyi sallama ba?"

Hawayen idonta ta share a kaikaice sannan ta jinjina kai tana murmushi ta ce.

"Hajiya tana da baƙuwa a ciki, and daddynku ya ce dole mu hanzarta yana jiran mu sai mun koma zai yi tafiya a yau ɗinnan."

"OK! To sai mu yi waya."

Tare suka iso har bakin mota da Hairi wacce ita kam ko kaɗan ta kasa ɓoye hawayenta tun jiya har zuwa yau. Ta nan har suka gama shiga motar drivern ya ja su suka fice sannan ta juyo ta dawo gida ta shige ɗakin ta ta kulle tare da faɗawa kan gado ta sake rushewa da kuka.

Aunty Labiba ma tunda ta koma gida take neman Layin Yayan na ta amma ba ta samesa ba, hakan ba ƙaramin sake ɗaga mata hankali ya yi ba domin a tarihi wannan shi ne karo na farko wai ta kira duk Layukansa ace mata a kashe suke. Ganin har kusan yamma ta kasa reaching ɗin shi yasa ta shiga neman Layin na hannun damansa a cikin Guides ɗinsa Sharath da Haroun wanda su ma dai duk ɗaya ne wayoyin basa shiga. Ta yi iya ƙoƙarin ta wurin ganin cewa ta samesa amma kuma hakan yaci tura, dole ta zauna ta rubuta masa text ta tura masa wanda take fatan koda ya buge wayar daga baya ya karanta ya kuma saurari maganarta.

Ziza ma tun misalin bakwai na safe Emraan ya shiga zanzamarta akan cewa yana jiran ta su wuce wurin aikinsa yana da buƙatar ya isa kafin lokacin ya cika domin ya shirya abubuwa.

Tun da gari ya waye gabaɗaya ta kasa gane kan mutanen gidan, daman jiya ta yi ta jiran Emraan ya dawo daga rakiyar ango amma har ta kai ga yin bacci bai dawo ba.

Yau ma ta kasa samun fuska a wurin kowa wanda ta rasa sanin dalilin hakan. Ko hajiya ma da ta so gani tun ɗazu ta kasa ganinta har ta gama shiri ta fito. Tana tsaye riƙe da hannun Abeer Munira ta zo da leda ta miƙa mata tana faɗin.

"Aunty Ziza ga Wayar da Ya Emraan ya sayawa Beenafah ta barta a nan..."

Karɓar ledar ta yi a zafafe ba tare da ta buɗe ba ta yi wurgi da ita tana faɗin.

"Bana son iskancin banza da renin wayau Munira kin ji ko? Do I look like stupid to you? Ko kuma kina tunanin ni abokiyar wasan ki ce? Ni na saya mata wayar da za ki zo min da maganar banza??"

"Ki yi haƙuri Aunty Ziza ban san ya zan yi da wayar ba ne tun da ta riga ta tafi ta barta a nan...."

Wani irin tsaki ta buga tare da jan hannun Abeer ta wuce ta shiga mota ta wuce.

Ziza dai tunda ta ya yaji tana Kebbi ta yi fushi sosai kamar yan da shima Emraan ɗin ya yi. Bayan Hajiya ta tabbatar cewa babu zancen Beenafah da Emraan yasa ta kira Iyayenta ta basu haƙuri. Daman kuma already iyayenta zaune kawai take gidan ba don suna so ba sai dai don tace ita babu in da za ta je. Hajiya na kira su ta basu hak'uri still tace idan Emraan bai zo ba za ta koma ba, hakan yasa Musamman Mummynta ta rantse ta ce sai ta koma. A ranar Wednesdayn da suka iso Gusau tun a ranar Mohaa ya ɗauki Emraan da kanshi suka ɗauki hanya suka wuce Kebbi state dan kanshi ya bayar da haƙuri hatta Ziza sai da ya bata hak'uri sannan the next day suka juyo tare suka dawo da ita.

Tana shiga gida ta wani kalle shi ko zaunawa ba ta yi ba ta ce.

"Munira ta bani saƙon wayar da ka saya mini ka ce ta bani, kuma na gode..."

Cikin tsananin ɓacin rai ya kalleta a zafafe ya ce.

"Ina cikin tsananin fushi saboda haka kada ki nemi ƙara fusatani Ziza!!!"

Taɓe baki ta yi kawai tare da kawar da kai gefe domin can cikin ranta ba ƙaramin tsorata da yanayin sa ta yi ba, domin ba ta taɓa ganin sa a wannan yanayin ba. Idan za ta iya tunawa ko a ranar da suka yi rikici akan zancen Beenafah ran shi bai yi ƙololuwar ɓaci haka ba.

Miƙewa ya yi tare da jan Hannun Abeer ɗinda ke ta masa surutu ya ce.

"ina jiran ki a mota yanzu....kada ki ɓata mini lokaci."

Ta shi ta yi a gaggauce ta shiga ta ɗauko duk wani abin da take buƙata sannan ta fito ta sallami masu aikinta kamar yanda ta saba idan za ta yi tafiya sannan ta rufe ko'ina ta fito ba ɓata lokaci ya ɗauki hanya.

*******

Su Aunty Aysha kuwa, koda ƙarfe uku na rana ta buga sun isa Sokoto. Bayan sun gama cin abinci sun huta Mummy Sameera ta shigo ɗakin da suke zaune da Ammie ta kalli Aunty Aysha ta ce.

"To malama sai ki tashi mu tafi ko??"

Wani kallon Aunty Aysha ta yi wa Mummy Sameerar sannan ta fashe da dariya ta ce.

"Haba Aunty Sameera? Ke yanxu dan Allah ko na ce miki zan biki na bar Ammiena za ki yarda da wannan maganar?"

Dariya suka kwashe da ita sannan ta ce.

"Ah, to ai dai a gidana kike, ko gidansu Hajiyar su Ahlan kika je bakya iya kwana sai kin dawo gidana..."

"To Aunty Sameera gidansu Hajiyar Ahlan kika ce, nan kuma gidan uwata ne."

Ammie da ta fito daga toilet ɗauke da Baffa ne ta ajiye shi akan gadonta bayan ta gama mishi wanka ta ɗauko man shafawa ba tare da ta kalli Mummy Sameera ba ta ce.

"Hajiya Sameera fa sai dai ki yi haƙuri, amma Aysha kam tana nan tare dani sai idan ta tashi tafiya ta je ta miki sallama...idan kuma nan za ki ci gaba da zama to..."

Waro ido ta yi tana dariya ta ce.

"Yanzu Aunty Mulaifa ni za ki ce wai na zauna a gidanki alhali da gidan mijina? Na kwana bana gidan sannan ki ce wai na ci gaba da zama a gidanki..."

Dariya ta yi tana murzawa Baffa man a jikin shi ta ce.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull