Kenza eBookz

Ganin ido complete - Chapter 6

Ganin ido complete - Chapter 6

Ganin ido complete Chapter 6: Ganin ido complete Chapter 6. Misalin ƙarfe biyar na yammar ranar juma'a Mummy ta fito cikin kyakkyawan ado ita da Humaida da…

3,375 words

Misalin ƙarfe biyar na yammar ranar juma'a Mummy ta fito cikin kyakkyawan ado ita da Humaida da alama fita za su yi.

Wuri ta samu ta zauna domin jiran Daddy wanda shi ma yana ciki yana shiryawa yayinda Humaida ta fice zuwa ƙasa.

Sallama Biba ta yi a hankali ta shigo parlourn. Wata uwar harara Mummy ta shiga jefa mata har ta ƙaraso ta durƙusa a gaban ta.

"Lafiya?"

Murya a ƙasa sosai ta miƙa mata wayar da ke hannunta ta ce.

"Daman Humaida ce ta ce na kawo miki wayar ki Aunty Aysha ta kira..."

Da ƙarfi ta warce wayar tana faɗin.

"Don kin kawo mini waya dole sai kin wani zo kin durƙusa a gabana? Shegiyar munafuka!..."

"Yi haƙuri Mummy..."

"Dan Allah tashi ki bani wuri.....ke tsaya dai!"

"Ko kin ɗaga kiran Ayshar ne kin yi munafurcin da ki ka saba?"

Da sauri ta girgiza kanta ta ce.

"Wallahi na rantse da Allah Mummy ban ɗaga ba. Ai tun da ki ka yi faɗa na daina ɗagawa."

"Ta shi ki bani wuri."

Tun da Aysha ta fara kiran wayar Mummyn bata daina ba har yanzu. Sai da ta ga dama sannan daga ƙarshe ta ɗaga wayar sama-sama ta ce.

"Ya akayi?"

Cikin murya mai sarƙe da kuka daga ɓangaren Ayshar ta ce.

"Mummy Barka da wuni!"

"Barka.."

Shiru ne ya ratsa tsakanin su na tsawon lokaci wanda babu abin da ke tashi daga cikin wayar sai sautin muryar kukan Aysha tamkar za ta ɗauke numfashi tsabar damuwa da tsananin ruɗanin da take ciki.

"Wai lafiya kike nema ki kashe mini dodon kunne?"

"Mum.. Mu.. Mummy!"

"Mts! Fita zan yi fa, kina ɓata mini lokaci."

Cikin wani irin raɗaɗi ta ce.

"Ina kewarki Mummy, ina kewar Twins da Humaida."

"Na ji..."

"Mummy Baffa ma yana gaida ku."

Taɓe baki ta yi tace.

"Na ji sai an jima... Ni wallahi dama daina kirana kikayi da ya fiye mini alheri Aysha mts! Na tsani na ci wallahi. Shi dai mutum gashinan bashi da zuciya. Da wata ce ke tsawon lokacin nan yakamata ace kin ma manta da ni...."

"Mu...mmy! Kin taɓa ganin 'ƴar da ta yi zuciya da mahaifiyarta?..."

"Nawa akayi?"

Da ƙarfi ta runtse idanuwanta tana girgiza kai tamkar tana a gabanta ta ce.

"Ni kam ba zan iya ba...Ba zan iya ba Mummy!"

Katse wayar ta yi ganin Daddy ya fito ta ɗauki Jakarta Hankalinta kwance suka fi ce zuwa shan Ice-cream ɗin su da suka shirya.

***

Sai da muka sake share sati tara a asibitin wanda yanzu Alhamdulillah, Ammie ta samu sauƙi sosai fiye da baya tare da taimakon Dr. Basheer da sauran ma'aikatan da ke wurin har muka kai ga samun takardar sallamarmu, domin a yanzu, hannunta ya warke tare da duk wasu raunukan da suka sameta. Ƙwaƙwalwarta komai ya yi fiye da za to wannan karon wanda har Dr. Basheer ya bamu tabacci cewa idan har ta ci gaba a haka in sha Allahu komai zai koma dai-dai tamkar ba'a yi ba. Sai dai kuma, an sake shimfiɗa mana sabbin dokoki fiye da na baya ma akan yanda zamu ci gaba da kulawa da ita da kuma kula da shan maganinta yanda ya kamata. Sannan follow-up ɗinmu zai dawo every four weeks a nan FMC gusau kamar yanda na nemi alfarma idan zai yi yu,kuma sai gashi sun amince mana domin sauƙaƙawa garemu tun da yanzu babu wani matallafi.

A wannan karon gidan sa ya kaimu har da Ammie bayan an bamu sallamar yace muyi wanki mu shirya kayanmu da kyau sannan mu koma gida.

A lokacin da zamu baro asibitin har kuka na yi domin ta riga ta kasance tamkar gida a gareni mai bani farin da yaye mini damuwata fiye da gidanmu dake Gusau. Sai dai kuma, a wannan karon in sha Allahu zan ƙara jajircewa da taka-tsan-tsan da duk wani abu da zai zamto barazana ko shamaki ga lafiyar Ammiena. Daddy ma, na jima da yanke hukuncin daina neman sa har abada duk wuya duk daɗi.

Da dare bayan matar Dr. Basheer ta shigo. Mai kirki da ita, ta saka aka kawo mana abinci mai rai da lafiya sannan ta ce mu ba su wuri zata yi magana da Ammie. Bayan mun fita suka zauna tsawon lokaci suna tattaunawa sannan daga ƙarshe ta yi mata sai da safe ta wuce.

Kallon Ammie na yi wacce ke zaune akan sallaya tana lazimi na ce.

"Ammie.. Mata mai kirki ko?"

Jinjina kai ta yi ta ce.

"Ai ba matar ba Beenafah, har mijin na ta mutumin kirki ne. Ki duba yanda ya yi ta faɗi tashi akanmu tamkar wa su danginsa. Kai! Ai wallahi ba zan daina saka wannan mutumin a addu'a ba Beenafah, domin ya cika ɗan kirki..."

Cike da murmushi na ce.

"Ammie kamar Yaya Ashiru ko?"

Gyaɗa kanta tayi ta ce.

"Sosai kuwa."

"Idan muka koma zamu iya tafiya gidan su Ammie?"

"sosai. In Sha Allahu babu abin da zai hanamu zuwa gidan su Ashiru domin ya yi mana halacci..."

Kallon Bahrain na yi wanda ya duƙufa sosai akan waya yana ta dannarta ba ji ba gani na ce.

"Wai kai miye kake yi da wayar nan tun ɗa zu? Please ka ajiye ka zo muci abinci..."

Sai yanzu ya taso da wayar a hannun sa ya na wani simi-simi tamkar an tsoma Kaza a ruwan zafi ya miƙo mini yana faɗin.

"Aunty Beena kalla yanda wayan nan ya yi..."

Da sauri na fisge wayan ina faɗin.

"Miye wayan ya yi Bahrain?"

Shiru ya yi mini kurum yana bina da ido.

"Oh my God!... Ammie wallahi ya rufe simcard ɗinnan dole sai an saka wasu code zai buɗe."

"Subhanallah! Garin ya ya haka Bahrain?"

Hawaye ne suka gangaro daga idonsa yana mai ƙureni da kallo ya ce.

"Dan Allah ki yi haƙuri aunty Beenafah wallahi ni ma ban san lokacin da na danna hakan ba."

Ajiyar zuciya na sauke sannan na jinjina kaina na ce.

"Ba komai. Kawai dai damuwata ɗaya ce akan Yaya Ashiru, idan ya kira bai samu ba zai ji haushi. Amma thank God tun da gobe zamu koma..."

Kallona Ammie ta yi ta ce.

"OK yasan cewa gobe zamu koma ɗin?"

Girgiza kaina na yi na ce.

"Ya dai san cewa cikin satin nan ko zuwa next week za'a bamu sallama amma bai san cewa yau ne ba domin kinga abin kamar daga sama ne tunda ko mu bamuyi expecting ba, kuma tun jiya da ya kirani bai sake kira ba,daman kuma da wayan Umma ne ya kirani yace mini wayarshi ta faɗi ta ci screen tana wurin mai gyara, to ina ga bai samu ya amso wayar ba har yanzu."

Daga nan ba wanda ya sake cewa komai har muka gama cin abinci muka yi shirin kwanciya bacci.

Washegari, da wuri ya kaimu tasha ya saka mu a mota cike da tarin alkairan da baki ma ba zai iya furta kalaman godiya ba sai dai muyita yi masa addu'a har ƙarshen rayuwarmu.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa*

*FREE-BOOK*

*PAGE 9*

Muna tafe a hanya muna ƙara tattauna rayuwa ni da Ammie har muka iso garin Gusau. A wannan karon Ammie ta samu horo iri-iri daga ƙungiyoyi daban-daban ma su kula da masu kalar ciwonta wanda a yanzu in sha Allahu duk abinda zai zo mata muna da yaƙini da saka rai cewa za ta iya adopting dai-dai gwargwado.

Kalle-kalle na fara bayan mun sauka a motar wai ko zan ga Yaya Ashiru a tawa wautar, amma har muka samu Napep muka hawo ban ga ko mai kama da shi ba.

Muna isowa ƙofar gida muka sauke kayanmu na shiga gaba na tura gidan sai dai kuma ga mamakina a rufe yake ta ciki.

Cike da mamaki na ƙara tura ƙofar amma kuma a rufe take. Idan zan tuna ranar da zamu tafi wani igiya na samu na zarge ƙofar kawai muka yi ta tafiyarmu.

Kallona Ammie ta yi ta ce.

"Beenafah lafiya?"

"Ammie gidan kamar a rufe yake."

"To ki ƙwan-ƙwasa mu ji."

Zuciyata cike da fargaba na hau ƙwanƙwasawa kamar yanda Ammie ta ce. Sai da muka yi kusan minti biyar muna jira sannan sai ga wani mutum ya buɗe ƙofar ya fito.

Kallon mu ya yi cikin nuna rashin sani ya ce.

"Malamai daga ina?"

Shiru mukayi, daga ni har Ammie ba'a samu mai tanka masa ba tsabar mamaki wanda sai Bahrain ne daga ƙarshe ya ce.

"Gidanmu ne mana, mun dawo daga asibiti, ka buɗe mu shiga."

Kallon Bahrain ya yi yana wani murmushi ya jinjina kansa ya ce.

"Gidan ku ne ko Yaro?"

Bakin gaskiyar Bahrain ya ce.

"Eh mana."

"To, ni dai gadi aka ɗauke ni kuma masu ainahin gidan suna Abuja, sai ƙanin matar mai gidan da yake ciki wanda ya yi aure wata ɗaya da suka wuce, bayan su ban san wasu ma su zama a nan ba..."

A gigice na ɗora hannuna a kai na buga wani irin gigitaccen ihu na ce.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Mun shiga Uku Ammie mun lalace...Yanzu mu ina zamu nufa,..."

Itama Ammie dafe gefen zuciyarta ta yi tare da runtse idanuwanta gam a hankali ta shiga furta.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allahuma ajirni fiy-musibati wa Akhlufni khairan minha...."

Addu'ar da ta yi ta nanatawa kenan har sai da ta ji nutsuwa sosai a ranta, kanta na wani irin sara mata ta janyoni zuwa jikinta ta na faɗin.

"Ya isa Beenafah.. Ya isa. Kema ki maimaita wannan addu'ar da nayi in sha Allahu Ubangiji zai musanya mana da mafi alheri.."

Tana kan faɗar haka sai ga wani ya buɗe gidan ya fito.

Cikin mamaki na kalle shi na ce.

"Uncle Isma'il?"

Uncle Isma'il ƙanin Mummy Zaliha ne uwar su ɗaya uban su ɗaya. Tun da suka koma Abuja shi kuma ya shiga neman alfarma cewa dan Allah su bashi gidan ya saka amaryar sa idan lokacin auren sa ya yi. Da farko har Daddy ya amince amma mummy ta ce ita sam bata amince ba domin watarana idan sun shigo garin ai dole suna da buƙatar wurin zama saboda haka bata amince ba. Yana na nan yana ta neman mafita sai gashi ya zo gidan wata ranar Alhamis ya tarar gidan buɗe babu kowa duk an bi an cire AC ɗinda suke gidan, an sace kayan babban generator dama duk wa su sauran kayan da suke waje. Hakan yasa ba shiri ya ɗauki waya ya kira Mummy Zaliha, nan take suka yi meeting daga ƙarshe suka kira Isma'il ɗin suka ce ya gyara ɓangarensu Beenafah ya saka amaryar tasa a ciki. Part ne mai ɗauke da Babban parlour wanda yake da dining area ɗan matsakaici da kitchen, sai ɗakin bacci ɗaya sai toilet a ciki. Idan ka fito akwai verander kewayayya da kuma toilet ɗin waje sai aka zagaye Part ɗin aka saka babbar ƙofa wacce ake iya rufe gidan idan an so. Bayan an yi bikin ne Daddy ya turo musu sabon mai gadi domin tsaron gidansa.

Wani irin ɓata rai ya yi tamkar bai taɓa sanin yan da ake dariya ba ya ce.

"Ya akayi?"

Haɓa na rawa na ce.

"Uncle Isma'il ba ka ganemu ba ne? Mu ne familyn Dr. Bello Wazeer ƙanin mijin Mummy Zaliha.."

Wani kallon sama ƙasa ya yi mana sannan ya ce.

"Na gane mana, Mulaifa ce da Beenafah da kuma Bahrain...."

Cikin jin wani sanyi a raina na nuna mutumin da ya tare mana ƙofar na ce.

"Wannan mutumin ne ya ce wai ba zamu shiga ba. Dan Allah ka ce ya barmu mu shiga..."

Girgiza kan shi ya yi ya ce.

"Ba zaku shiga wannan gidan ba domin ba ku da matsugunni a ciki?"

Cikin wani irin kuka jikina na wata irin tsuma na ce.

"Dan Allah Uncle Isma'il ka rufa mana asiri dan Allah ka barmu mu shiga, gidanmu ne fa. Gidan Daddy ne Yayan Mahaifinmu wanda bamu da wani bayan shi a duniyar nan..."

"To ni ina ruwana, ai ba Laifina ba ne ni..."

"Don Allah Uncle Isma'il, don darajar iyayen ka kada ka kore mu daga nan..."

Hannu na ga ya saka cikin aljihu ya ciro waya ya lallatsa ya kara a kunnen sa wanda ba ɓata lokaci naji yana magana daga ƙarshe ya miƙo mini wayar, hannu na rawa na karɓa na joganata a kunnen tare da fashewa da wani irin sabon kuka mai tsuma zuciya na ce.

" Daddyyy! dan Allah kada ka kore mu daddy, daddy Idan ka koremu ina zamu nufa?"

Daga can ɓangaren Daddyn cikin masifa ya fara magana da cewa.

"Zama zan yi ku riƙa yi mini wasa da dukiya ina kallon ku? Kun tafi kun bar gida a buɗe sakaka saboda bakusan zafin kuɗi ba duk an shiga an yi mini sata sannan ki ce kuma in bar gida ku ci gaba da yin yanda kuka ga dama? To na rantse da Allah hakan ba zai yi yu ba, nasan yau da gobe tun ana ɗaukar abun da yake waje watarana cikin gidan za'a shiga a yayeni. saboda haka na rantse da Allah zamanku a gidan nan ya ƙare har abada..."

A hankali Mummy ta miƙo hannu ta karɓi wayar daga hannuna ta kara a kunnenta tana zubar da hawayen baƙin ciki domin duk abinda yake faɗa tana jin sa daman wayar a hands free take ta ce.

" Ka ji tsoron Allah Alhaji Mudassir! Ka ji tsoron Allah. Ka tuna waɗannan yaran ba su da wani wanda za su kira na su bayan kai.... "

" Ke dan Allah ni bana magana da mahaukaciya,sai dai ina miki addu'ar Allah ya baki lafiya...Isma'ila ka amshi wayar ka ji mi zan gayamaka."

Durƙushewa na yi zuwa ƙasa ina wani irin kuka tamkar wacce akace uwarta ta mutu.

Ammie ma haka ta ja Bahrain ta rungumesa jikinta tana ta addu'a wacce ita ce makami a gareta, ga kanta sai ciwo yake tamkar zai tsage gida biyu.

Bayan ya gama wayarsa ya juyo ya kallemu ya ce.

"Ku shiga ku tattara kayanku ku saka a mota ina jiranku."

Tamkar wata mai koyon tata haka na daddafa na shiga ni kaɗai yayin da Ammie ta togace bakin gate. Sai da na gama bincika ko'ina ban samu kayan ba sai daga ƙarshe na tarar dasu ɗakinda Generator yake, an rabke su wuri ɗaya tamkar wasu kayan bola-bola.

Ganin ina neman ɓata masa lokaci ya saka mai gadin ya kwashe kayan ya saka a cikin Hilux ɗinda na gani nan a harabar gidan da alama ita ce motar tasa domin ni can baya dana san shi ban san shi da mota ba.

Wani babban wulaƙanci ma da ba zan taɓa mantawa da shi ba shine wai mu shiga baya tare da kayan, shi ba zamu shigar masa gaban mota ba. Hmm! Duniya kenan.

A hankali yake tafiya har muka baro GRA ɗin zuwa wata unguwa da bamu taɓa sanin tana Existing ba a rayuwa. Yara ne gasu nan suna ta wasa abin su, mutane gasu nan ko ta ina.

A bakin wani matsakaicin gida ya yi parking ya fito ya buɗe ƙofar gidan. Yara ya kira suka saukar mana da kayan sannan ya ciro makullai guda uku na kubaka ya damƙa mini a hannuna tare da faɗin.

"Ku gode Allah ma saida na gama gyara gidan sannan akace na baku ku zauna. Kuma wallahi ku saurara ku ji gargaɗina; ko da wasa kada na sake ganin ƙafarku a ƙofar gidan can , koda wasa kada na ji wai kunje neman wani abu wallahi rashin mutunci zan yi muku wanda ko kare ba zai ci ba. Kuma shima kunga wannan gidan? Zamanku a ciki temporary ne, kada ku yarda ku ɓata mini gidana kunji na gaya muku."

Har ya ƙarasa maganar sa ya tattara ya tafi daga ni har Ammie babu wanda ya ce masa uffan. Muna nan a tsaye ina ta kuka da ni da Bahrain Ammie ta kira wani yaro cikin yaranda suka tsaya suna kallon mu ta ce.

" Ya sunan wannan unguwar ne?"

" Nan Shi ne Hayin Malam Ibrahim."

Jinjina kai ta yi ta ce.

"Na gode."

Kallona tayi ta ce.

"Ku zo muyi addu'a mu shiga. Ba komai kuyi haƙuri, duk yanda rayuwa ta zo wa bawa to dole ya yi haƙuri ya godewa Allah..."

Ganin ta dafe gefen kanta tana neman zubewa ƙasa yasa na ƙwallara wata irin razananninyar ƙara da gudu na je gareta na ce.

"Ammie mine ne? Miye ya same ki?"

Murmushi ta yi ta ce.

"Bakomai Beenafah, kai na nike jin yana ciwo sosai.."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..Ammie muje ciki kisha magani, lokacin shan maganin ki ya yi ma tun ɗazu. Mummy dan Allah ki ƙwarara kanki kin ji Ammie na."

Cikin gidan muka shiga da bismillah ɗauke a bakinmu. Na samu wuri na zaunar da ita cikin verander.

Gidan a gyare yake fes kamar yanda yace, ko'ina an fenteshi da kalar zuma, ga breaking tiles an baza ko ina a filin gidan har bakin ƙofar fita. Ɗakunan nabi na leƙa. Ciki da parlour ne guda ɗaya, sai ɗaki ɗaya daban a waje, kitchen da kuma toilet, sai kuma rijiya da aka yi ta da ɗan tsayi sannan aka rufe bakinta da murfi itama a jikinta duk tiles ne har sama. Gidan gwanin sha'awa, da hakan Ammie sai ta ji hankalinta ya ɗan kwanta kaɗan.

"Beenafah zo ki bani maganin nasha mana."

Da sauri na zo na ɗauko mata tasha da kanta sannan na mayar.

"Ammie ni ina jin yunwa."

Kulolin da muka zo da su ne tun daga gidan Dr. Basheer wanda ya saka aka shirya mana abinci kafin mu gama shiryawa. Wai shi yasan idan muka iso ba zamu samu damar ɗora girki ba domin akwai gajiya da kuma buƙatar shirya wuri.

Plate na ɗauko na zuba masa,lafiyayyar shinkafa da miya ne da nama. zaunawa ya yi yaci, bayan ya kambala ya ɗora kansa akan cinyar Ammie dake zaune murya cike da rauni yana hawaye kaɗan-kaɗan ya ce.

"Bana son Daddy Ammie... I hate him, I hate Mummy Zaliha har Humaida ma.."

Da sauri ta sanya hannunta ta rufe masa baki tana girgiza kai ta ce.

"Kul! Kada na ƙara ji kaji ko Bahrain..Komai na duniya haƙuri ake. Tashi ka yi sallah ka ɗauki ga tabarma can ka shimfiɗa daga can ka kwanta ka yi bacci."

Lokaci ɗaya muka tashi muka yi sallar sannan ta ce mini.

"Beenafah mu ci abincin nan mu zo mu shirya kayan nan da wuri."

Gyaɗa kaina na yi na ce.

"To Ammie."

Abincin na ɗauko na zuba mana a tare muka zauna muna ci. Ganin yanda nake ta juya cokalin yasa ta kalleni a hankali ta ce.

"Ki yi haƙuri da duk yanda rayuwa ta zo miki."

Komai bance ba har muka kambala sannan na ce ta kwanta ta huta ni zan gyara komai da kaina tunda lokacin hutawarta ya yi. Daman ba wani kaya ba ne. Katifa ce wacce muke kwanciya ni da Ammie sai katifar Bahrain. Single room ɗinda ke wajen kawai na gyara mana domin shi ma yana da faɗi sosai,kuma ya ishe mu bama buƙatar ciki da parlourn. Sai kayan tarkacen kayan aiki su ma da ba wasu masu yawa bane na saka a kitchen ɗin. Sai kayan sawarmu dana kai parlourn na jere a lungu ɗaya da kayan siyayyar abincin da muka zo da shi daga can.

****

Tun da Mummy ta ji Daddy yana waya da su Beenafah ta zo ta tsaya a kan shi bayan ya kammala ta kalle shi ta ce.

"Yanzu kai saya musu gidan za ka yi ko ya ya?"

Ɗan taɓe baki ya yi ya ce.

"Eh to. Idan Shi Isma'ilan ya ce zai siyar sai a saya musu..."

Cike da mamaki ta ce.

"Ka siya musu Alhaji? A'a, ni gaskiya ban yarda ba. Idan kace ka siya musu kuɗi ne zaka kashe ma su yawa, sannan shi kan shi Isma'il ɗin idan ka siye gidansa zai ɗauke shi matsayin hujjar da zai ci gaba da zama gidanmu wanda ko da watarana muna so ya tashi ba zai tashi ba. Saboda haka ka barshi a haka dai, su zauna, duk ranar da wata buƙata ta so kowa zai iya kama abinda yake da shi."

Jinjina kai Daddy ya yi cike da gamsuwa da maganarta ya ce.

" Kuma fa zancen ki haka yake wallahi..."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull