Ganin ido complete - Chapter 62
Ganin ido complete Chapter 62: Ganin ido complete Chapter 62. Ƙara juyowa ta yi tana fuskantata da kyau cike da kulawa ta ce.
3,361 words
Ƙara juyowa ta yi tana fuskantata da kyau cike da kulawa ta ce.
"Beenafah!"
Buɗe Idanuwana na yi waɗanda suke a rufe tunɗazu na kalle ta na ce.
"Na'am Ammie.."
"Miye abin da yake damunki?"
Gabana ne ya faɗi jin wata tambayarda kwata-kwata ban tsammace ta a yanzu ba. Murmushi na yi ina ƙoƙarin sai ta kaina na ce.
"Lafiya Lau Ammie..mi kika gani?"
Cikin rashin yarda da maganata ta ce.
"Naga fuskar ki tayi fayau, kuma duk kin susuce bakya cikin yanayin ki....ga idanunki ma duk sun zurma..."
Murmushi Hairi ta yi ta ce.
"Da wani irin Amai mai tsanani ta farka, kuma ba ta ci wani abinci ba, Tea Kawai ta sha muka fito...."
A ruɗe ta ce.
"Subhanallah! To kin je wurin likita kuwa?"
A tausashe na ce.
"Ammie ki kwantar da hankalinki please...ba wani abun da ke damuna, kawai kwana biyun nan ina jin yanayin amai ne, musamman idan naji wani kalar ƙamshin da bai gamshe ni ba."
Jinjina kai ta yi tana faɗin.
"OK! Allah ya ba ki lafiya."
Wayarta ta ɗauko ta kira Su Aunty Aysha da kuma su Maman Fakiha ta faɗa musu cewa tafiya zan yi. Na san ta faɗa musu haka ne domin idan na koma gida ba lallai su samu ganina muyi sallama ba, duk da cewa tafiyar ina jinta tana mini wani iri a zuciyata tamkar na fasa haka nake ji. A yanda na ke ji a yanzu...tabbas komai na iya faruwa.
A nan muka wuni har magriba, bayan mun sha fira da su Aunty Aysha su Fakiha sannan muka koma gida. Muna shiga na shige ɗakin Aunty Ziza domin na samu damuwata ta ɗan ƙara ragewa wanda na lura idan ina ni kaɗai abun yafi damuna sosai. Bayan mun gama fira sai misalin sha ɗaya muka koma ɗakina ni da Hairi. A yau kam ban isa na hanata kwana a nan ba domin na san ko nace ta tafi ba tafiya za ta yi ba.
Ina nan naga text ɗin Ya Mohaa ya shigo kamar haka.
"Salam Bibina...na rasa laifin da na yi haka da har kika ɗauki wannan tsattsauran hukunci a kaina...please ki sasauta min domin ya yi mini nauyi da yawa,... Sam ko Ruwa na kasa haɗiyewa, duk da cewa ban san laifina ba, please ina fata da ki sauko da wuri dan Allah...Duk yanda na so na kasa isowa yau, ina Abuja dole sai gobe zan iso. Ina ƙaunarki sosai...ina kuma jin tsananin kewar ki tamkar zan yi hauka haka na ke ji..."
Taɓe baki na yi ina mai kawar da wayar a gefe, duk da cewa nima ina jin kewarsa kamar yanda yace shi ma yana kewata. To amma ni Sam ban wani jisa har can ƙololuwar kai na domin yanxu na gane cewa duk abin da yake faɗa mini na yaudara ne kawai ba don yakai har zuciyarsa ba.
Washegari ma, ganin mun samu rarar lokaci muna gama karyawa na cewa Hairi mu tafi gidan Aunty Labiba domin na yi mata bankwana, idan har na koma ban je gidanta ba hakan ba zai mata daɗi ba ko da kuwa bata faɗamin ba.
A bakin gate muka ci karo da kishiyarta Hajiya Marwa tana tsaye tare da driver da kaya a gaban shi da alama saƙo ne take so ta aike shi da shi.
"Ina wuni?"
Kusan iya kalmomin da muka furta a gareta kenan, wanda a wurin Hairi ko arzikin kallo ba ta samu ba.
A mamakance ta wani kalle ni tamkar idanun ta za su zazzago ta ce.
"Wace ce wannan kamar Beenafah?"
Sai yanzu Hairi ta waigo ta yi mata wani kallon sannan ta ja ta togace ta ce.
"Ita ce! Ya aka yi?..."
Aunty Labiba da fitowarta kenan muka ji tana faɗin.
"Ya kuka tsaya a can? Ku shigo mana."
Kamar yanda take neman ƙarin haske haka itama Hairi ta ke ta tarin maganganu a cikin bakinta wanda ta so baje mata su kamar me, sai ga Aunty Labibar ta fito hakan yasa muka yi gaba muka shige ciki.
Muna man misalin karfe uku na rana sai ga text ɗin unsave number ya shigo wayata. Da sauri na ɗauka, hannayena har wani shaking suke tsabar yanda na ruɗe ganin numbern Ya Jafaru.
"Na ji ance gobe ne za ki tafi, kuma bamu samu mun ƙara tattaunawa ba, na san cewa kina cikin gidan Labiba a yanzu, please idan ba damuwa za ki iya fitowa mu haɗu mu tattauna, ina nan waje ina jiran ki..."
Ajiye wayar na yi ina mai jin wani iri a raina, na jima ina ta saƙawa da warwarewa tsawon lokaci wanda daga ƙarshe na bi shawarar zuciyata da ƙwaƙwalwata cewa kada na tafi wurin sa, domin har yanzu ban gama farfaɗowa daga shock ɗinda ya bani ba, har yanxu ban gama fayyace maganganunsa ba na shekaranjiya ba, bitarsu na ke daki-daki wanda har yanzu ban kai ko rabin shafi na maganganun nasa ba, so nake na baje su da kyau na yi musu fassara ta fahimta domin neman mafita. Idan na ce yanxu na sake saurarensa tabbas kaina da zuciyata tarwatsewa za su yi.
Haka muka ci gaba da fira sukuku dani tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Muna nan misalin ƙarfe huɗu na yamma muna shirin tafiya gida sai wayar Hajiya ta kira tana shaida mana cewa wai daga nan gidana zamu wuce domin Ya Mohaa ya faɗawa Emraan cewa na wuce gida yana gab da isowa.
Addu'a ta biyoni da ita har bakin gate, bayan mun shiga mota ta kamo hannuna cike da soyayya ta ce.
"Beenafah! A kullum son ki ƙara ninkuwa yake a zuciyata, kin zame mana alheri Beenafah bayan kin shigo rayuwarmu. Kin sanya Daddy farin ciki wanda shi ne silar sauyawar ƙaddararsa. Ina alfahari da ke. Allah ubangiji ya ba ki lafiya, ya kuma sauke ki lafiya. Ki kula sosai, kuma ki riƙe duk shawarwarin da na baki kin ji ko? Allah ya kai ku lafiya."
Murmushi na yi ina mai jin wani sanyi a raina na ce.
" Amin yah Allah. Na gode sosai Aunty Labiba,Allah ya saka da alheri."
Muna fita na fara waige-waigen inda zan gansa tamkar wata Mahaukaciya, sai dai, har muka isa gidan ko alamar sa babu. Muna shiga na tarar har Biba ta dawo ta shige kitchen baiwar Allah tana ta fafutukar haɗa abincin tarbar Ya mohaa.
Sam ni ban ji wani ɗoki ba, duk yanda Hairi ke ta surutunta wanda mafi yawa duk akan zancen aurenta ne da Suhaib gabaɗaya ni hankalina baya wurin. Tunanin Ya Jafaru ne ya yi mini kane-kane a zuciyata, ji nake tabbas ina so in ji minene abin da yake so ya sake sanar mini. Kenan bibiyata yake ko me? Ta ya ya yasan cewa na je gidan Aunty Labiba?
*******
Jafaru kuwa, tun daga ranar da suka baro gidan su Hafsa ya shiga bibiyarta ba dare ba rana. Ko kaɗan ya hana kansa sukuni. Tunda ya lashi takobin sai ya ga bayan wannan auren na Beenafah ya rasa nutsuwarsa.
Tunda ya kira ta ya ji cewa tabbas kalamansa sun yi tasiri a kanta yake cikin tsananin farin ciki. Take ya fara sabon lissafi domin ya ƙiyasta ba jimawa za ta fito ta bar gidan Mohaa, shi kuma daga zaran ta fito a wannan lokacin...zai tayar da ƙayar baya kamar yanda Baba Kali ya bashi shawara wanda dole su Baba su goya mishi baya kuma su bar shi ya aureta.
Koda ta je gidan Ammie akan idonsa har ta gama wuninta ta koma gida. Hankalinsa ne ya tashi sosai jin cewa wai tafiya za ta yi ta koma Dubai.
Haka yasa ya biyo ta har gidan Labiba, da hope ɗin cewa zai haɗu da ita ya ƙara jaddada mata kalamansa, sai dai kuma, haƙar sa ba ta cim ma ruwa ba,domin taƙi ba da haɗin kai.
Hakan yasa ya biyo ta gida, wani irin farin ciki ya ji ganin ta dawo gidanta, kuma ya tabbatar cewa mijin na ta bai dawo ba, domin da ace ya dawo tabbas ba zai taɓa bari wani driver ya tuƙata ita kaɗai ba tare da shi ba. Sai da ya bari aka gama sallar magriba sannan ya je kai tsaye zai shiga gidan. Masu gadi na tare shi yace shi ɗin ɗan uwanta ne ya zo ne yi mata sallama domin ya ji ance gobe za ta koma.
Ganin ɗaya daga cikin security ɗin ya gane shi domin a tare suka zo har da zu Ammie a ranar, sai bai sha wata wahala ba suka bar shi ya shige.
Yana shiga ya tsaya nesa da gidan tare da tunanin abin da ya kamata ya yi. Idan ya shiga gidan mi zai ce mata? An ya ma za ta saurare shi kuwa?
Yana nan yana shawara kawai ya ji ƙarar motoci, na'urori sai amsawa suke har aka gama wangale gate ɗin.
A gigice ya faɗa tsakankanin flowers ya kwanta tsabar yanda ya gigice lokaci ɗaya. Bai ƙara ruɗewa ba sai da ya hango sa ya fito daga mota cikin nutsuwarsa, ga shigar nan ta manyan kaya wacce ke ƙara masa ƙima da ƙwarjini...Kishi ne kawai ke sa yana kiran sa da tsoho, amma ko makaho ya shafa yasan cewa wan can sam bai kai a kira shi da wannan kalmar ta tsoho ba duk da cewa shekaru sun ja, domin jikin sa ƙyanƙyan yake tamkar wani ɗan 35yrs. Ga sajen nan baƙi wulik wanda yake ƙara fito masa da kyaunsa uwa uba ga hutu da jindaɗi.
Bai ƙara ruɗewa ba sai da ya hango yanda securities ɗinsa wanda suke da kusan kalar Kaki uku suka ɗauki saiti tare da samun kowane lungu da saƙon da ke gidan suka ƙame domin bada kariya da gidan da kuma lafiyar mutanen gidan.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Wannan ita ce kalmar da ya shiga furtawa ba ƙaƙƙautawa yana mai ƙara lafewa cikin flowers ɗin ganin irin bala'in da yake gabansa. Shi yanzu ya zai yi kenan? Ya zai yi ya fice daga gidan nan? Dama ace tun farko da suka shigo ya wuce direct cikin gidan wata ƙila ya samu mafita idan ya ce bankwana ya zo mata. To amma wannan wace haukar ce ta hau kan shi da har zai ɓoye haka kamar wani ɓarawo?
*******
Ya mohaa kuwa, yana shigowa Hairi da ke zaune tare da Biba ta maƙalƙaleshi tana mishi sannu da zuwa. Bayan sun gama gaisawa Biba ta gaishe shi sannan ya wuto direct ɗakinda nake.
Zaune nake akan Sallaya wacce tunda na kambala sallar magrib ɗin na kasa matsawa ko'ina, sabon aikin da Ya Jafaru ya samar mini shi na zauna ina yi wato tunani wanda ko cikakken Azhkhar ban samu na yi ba.
Ina ganin ya shigo na miƙe tsaye da sauri ina kallon sa.
Wani irin kallo ya bi ni da shi mai cike da zallar karaya kamar yanda nima nake yi, mun shafe kusan minti biyu a haka sannan daga ƙarshe ya ware hannayensa cikin sagewar gwiwa, alamar na zo.
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 52*
Yau da zuciyata take cikin mugun yanayi, sai naga ya koma min wani mutum na daban. Ƙwarjininsa da kuma nauyinsa da nake ji, sai na ji sun ƙara nauyi sosai a Idona. Ban sani ba ko don akan shi kaɗai na fara sanin mine ne soyayya, maimakon na ji haushinsa na ji cewa ya fice mini a rai, sai na ji ma tamkar wata sabuwar soyayyar ce aka sake dunƙulawa aka naɗe ƙirjina da ita, tsananin kishin sa sai na ji na ninku a raina fiye da yanda na ke a 'ƴan kwanakin nan. Wata zuciyar ingi zani take da cewa na tafi garesa yayin da wani ɓangaren ke bina da mugun gargaɗin cewa kada na yarda na yi wannan gangancin, domin idan har komai da yake mini duk na ƙarya ne ba da gaske yake ba...mi zai sa nima na riƙa mutuwa akansa ina jin tamkar shi ne ɗan autan Maza? 'He's just using you and He's just pretending...Har abada ba zai taɓa son ki ba saboda matsayinsa da na ki ba ɗaya...lokaci kaɗai yake jira, da ya samu yanda yake so zai auro wata wadda tafi komai, ke kuma a lokacin saki zai biyo na wulaƙanci.
Waɗannan su ne kalmomin Ya Jafaru da na tuna wanda lokaci ɗaya na juya masa baya ina mai jin wani irin raɗaɗi a zuciyata na shiga girgiza kaina alamar ba zan iya zuwa gare shi ba, kawai sai na fashe da kuka.
Mohaa ya shiga cikin wani tsananin tashin hankali da gigitar da bai san ma lokacin da ya watsar da duk abin da yake hannun sa ba, wata irin super ya yi ya iso gareni tare da janyoni jikin sa tamkar zai fashe da kuka ya ɗago fuskata tare da zuba mini idanu kawai yana kallona, ban kalle sa ba, domin ban san ta ya ya zan fara kallon idonsa ba, duk da cewa ban kallesa ɗin ba, na lura da yadda duk ilahirin jikinsa ya ɗauki ƙyarma tamkar wanda ake wa azabar ƙanƙara.
A wasu ɗabi'unsa da na laƙanta;yana da wahala idan wani abu ya faru na rashin daɗi ya iya buɗe bakin sa ya yi magana kai tsaye, a duk lokacin da wani abu zai zo mana, sai da ya sanyani cikin jikinsa ya rungumeni na tsawon lokaci, sannan daga baya ya nemi jin abin da yake faruwa, wanda ya yi imani da cewa, a duk lokacin da wanda kake ƙauna ya shiga wani hali to abun na farko shi ne ka fara bashi kulawa ta hanyar musayar saƙon zuciya da kuma body language, matuƙar kuɗin masoyane na haƙiƙa...to tabbas kaso casa'in na daga cikin azabar da kake ji da nauyi a ƙirjinka za su ragu.
Ganin da gaske na ƙi bashi haɗin kai yasa ya nemi ya rungumeni domin ya bani lokaci,sai dai kuma, yanda na ture shi ne ya ƙara mugun ɗaga masa hankali a gigice ya ce.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Beenafah! Mine ne yake faruwa haka? Mi nai miki da zafi haka?....kinga..Dan Allah kada..."
Cikin wasu irin zafafan hawaye na ɗago idona na kalle shi, sosai na ji wani irin tsoro ya kamani ganin yanda idanunsa suka kaɗa sosai suka canja launi tsabar tashin hankali da damuwar da suka cim mi shi a lokacin da bai yi aune ba. A hankali na shiga ja baya ina faɗin.
"Kada ka zo kusa dani,..domin.."
Maganar tawa ce ta maƙale, ganin irin kallon ya kafeni da shi wanda ko ƙyaftawa babu shi ne ya sanyani haɗiye sauran maganata...Zan iya rantsewa cewa tun da nake da tsawon lokaci ban taɓa karo da shi a irin wannan yanayin da yake ciki ba, kuma ko a mafarki akace zan gansa da irin wannan ɓacin ran da damuwa tabbas zan ƙaryata. Gabaɗaya cikin kalmomin da na tana da zan furta masa ni karan kaina na tabbatar babu ɗaya wacce za ta kasance alheri daga ciki...
A raunane ya buɗe bakinsa zai yi magana kwatsam sai muka ji wata ƙara daga kusuwar ɗakin ta shiga amsawa alamar security alert. Wata ƙaramar hologram security device ce ta fito tamkar an yi amfani remote control wurin fito da ita, a hankali red light ta shiga ɓillawa tare da sakin wata murya irinta robot tana faɗin.
"Intruder detected...i repeat intruder detected! We have discovered an unknown thief inside the house, can we proceed with immediate action or await further instructions.? I repeat intruder detected."
Cike da rashin kuzari ya juya ya fita still hankalinsa tashe, a ransa faɗi yake Wane irin ɓarawo daga magaribar fari haka? Da ace cikin dare ne da tabbas ko waje ba zai leƙo ba zai ba su umarnin yin maganin sa yanda ya dace, to amma shigowarsa kenan ace ɓarawo? Sai dai idan akwai wani abin.
Sulalewa na yi zuwa ƙasa abin duniya duk ya bi ya isheni, wannan wace irin rayuwa ce. Ni yanzu dan Allah mi ya kamata na yi? Shi ɗin fa ba yaro ba ne, at least ya kamata duk abinda zanyi na kwatanta ko? Miƙewa na yi a zafafe jin wani irin mugun tunani da ya ɗarsu a ƙwaƙwalwata lokaci ɗaya, tunawa da sanarwar security alert.
"To idan Ya Jafaru ne ya yi haukar shigowa gidan nan fa? Innalillahi wa inna ilaihi!"
Na furta da ƙarfi ina mai jin yanda kai na ke wani irin sarawa, lokaci ɗaya na ji kamar kaina na juyawa, tamkar na kife haka na ke ji...duk da haka ban sare ba, hakan yasa da gudu na runtoma na yo waje.
Duk wani haske da ke gidan ya canja launi zuwa Red alamar danger mode
Daga inda nake tsaye bana iya hango komai da kyau kasancewar naga yanda securities ɗin suka zagaye wuri ɗaya da bindigogi a hannunsu, sai Ya Mohaa da Hairi waɗanda ke tsaye dab da su da alama magana yake musu.
Da gudu na ƙara so wurin domin na ƙara tabbatarwa da mike faruwa.
Durƙushe yake akan ƙafafunsa, securities ɗin sun kewaye shi an rufe masa fuska an kuma ɗaure hannayensa ta baya.
Duk da cewa banga fuskarsa ba, jikina ya gama bani cewa Ya Jafaru ne...tabbas shi ne domin na san shi farin sani da wannan rigar ta en ƙwallo. Wani irin bugawa zuciyata ta yi tsabar yanda na tsorata, bakina na rawa na ce.
"Kuk..ku cire masa wannan ƙyallen na fuskarsa yanzu!"
Ganin yanda hankalina ya tashi sosai yasa Hairi matsowa inda nake ta kama hannuna a tsorace tace.
"Please Mummy calm down...kin san condition ɗin ki dan Allah ki yi a hankali."
Da sauri suka cire masa ƙyallin. Da gaske kuwa Ya Jafarun ne. Da sauri na soma juya idanuna alamar tsantsar mamaki na ce.
“JAFARU!!!”
Ganin yanda wani daga cikin securities ɗin ya zage ya zabga masa mari ne ya sake ɗaga hankalina a gigice na ɗaga masa hannu na ce.
“Ka daina dukansa! Ku sake shi yanzu-yanzu!”
Cike da mamaki suke kallona sannan wani ya ce.
"Ma'am...this man..."
"I said you should let him go...matuƙar kuna son aikinku ya ɗore, to lallai ku sake shi ya tafi. Shi ɗin ba ɓarowa ba ne, Yayana ne."
Na ƙarasa maganar cike da faɗa yayin da idanuna ke cike da hawaye tsabar tashin hankali.
Jinjina kai Ya mohaa ya yi yana kallona, cikin wani irin sabon mamakina murya a ƙasa sosai ya ce.
" Bibi...ki bari abi komai a hankali..."
Duk da cewa a tsorace nake, hakan bai hanani ɗaga murya ba ina faɗin.
"Tell them to let him go please...Kada ka bari su yi masa illa, wallahy shi ɗin ba ɓarawo ba ne."
Umarni ya yi musu da cewa su sake shi tunda hakan na zaɓa. Ina nan tsaye har sai da suka kwance shi ya tashi kai tsaye ya fice daga gidan.
Ina ganin ficewarsa na sauke wata irin ɓoyayyiyar ajiyar zuciya sannan kai tsaye na saka kai na shige ba tare da na ƙara kallon inda suke tsaye ba.
Na jima a kwance akan gado shiru ina ta nazari akan wannan abun da ya faru. Ban san lokacin da na miƙe zaune ba jin wani sabon tunanin again da ya nemi ya zautar da ƙwaƙwalwata.
"Tabbas Hairi ta taɓa ganin Ya Jafaru, domin a gabanta shekaranjiya yace yana son magana dani a keɓance....so what of Idan ta sanarwa Ya Mohaa fa? Ko kuma ita kanta dame za ta fassara abun? Ya zo ranar, sannan yauma ga shi ya biyoni gida...Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Da gudu na diro daga kan gado wanda hatta Ƙasan marata sai da naji ya amsa ba daɗi. Tamkar wata taɓaɓɓiya haka na fito ina rarraba idona ko Allah zai sa in gan su suna tattauna maganar. Wayyo Allah na ni Beenafah! Wallahy haukacewa zan yi! Ni na ma rasa miye abin da yake damuna a yanzu. Tabbas dole na bayyana mata komai domin gudun zargi, to idan ta faɗawa Ya Mohaa ta wace fuska zai kalleni kenan? Cewa ina tare da wani a waje? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wayyo Allah ni Beenafah mi na aikata haka? Ya shigo gida tamkar ɓarawo kuma na tsaya kai da fata na ce dole sai an sake sa ya tafi? Miyasa zan kare sa? Wace hujja nake da ita akan hakan?