Kenza eBookz

Ganin ido complete - Chapter 66

Ganin ido complete - Chapter 66

Ganin ido complete Chapter 66: Ganin ido complete Chapter 66. Yana ganin ta fita shi ma ya fice zuwa wurin Uncle Mu'aƙƙib. Wannan shi ne karo na farko da…

3,296 words

Yana ganin ta fita shi ma ya fice zuwa wurin Uncle Mu'aƙƙib. Wannan shi ne karo na farko da ya shigo ainahin gidan nasa wanda ya haɗu sosai ba kaɗan ba.

Hoton Suhaib ya kalla dake bango ya yi murmushi sannan ya kalli Uncle ɗin ya ce.

"Yaron kirki...tabbas kin rai ne da kyau da tarbiyya. Tsarin sa yana burgeni sosai, shiyasa idan saura zan tuna...sai na ji cewa ko kaɗan bana nadamar aura masa Hairiyya da zan yi."

Jinjina kai Uncle Mu'aƙƙib ya yi shima da murmushin a fuskarsa ya ce.

"Tarin dukiya da babban matsayi ba su da dalilin saka yaro ya lalace sai idan an samu giɓin rayuwa, wanda ko dai daga iyaye...ko kuma daga su yaran karan kansu."

Wuri ya samu ya zauna suna fuskantar juna da kyau ya ce.

"To Uncle baka jin hakan ɗinma da yake faruwa, akwai taimako sosai wurin haɗin kai da soyayya tsakanin Iyaye guda biyu wurin ganin sun gina yaran ta hanyar da ta dace? Amm! Misali, yanzu kai ɗin nan mata nawa kake da su?"

Kai tsaye Uncle Mu'aƙƙib ya ce.

" Ɗaya."

Jinjina kansa ya yi ya ce.

" Uncle Amyn fa?"

" Shima ɗaya. "

" Jaddi Fa?"

Yanzu kam pausing ya yi yana kallon shi da alamar tambaya a fuskar sa ya ce.

" Ɗaya."

Ɗan ƙara gyara zamansa yayi yana mai jinjina kai ya ce.

"Uncle, duk mata ɗaya-ɗaya kuke da su...duk da cewa nasan akwai masu biyu-biyu uku-uku a cikin ku har masu huɗu ma....but na zaɓi in lissafoka ku da kuke mata ɗaɗɗaya domin bayanin da zan yi maka ya tafi daidai....gidanku babban familyn ne guda, mai tarin 'ƴa' ƴa. Jikoki da farin ciki, ga dukiya ga komai na more rayuwa,uwa uba ga haɗin kai...wannan family ne wanda mutane suke sha'awa da burin su ma ace na su ya zamo haka. Duk kuna farin ciki ne da walwala da mataye ɗaya-ɗaya da kuke da su. Ga shi dai har ka kawo yanzu wanda na san dai babu wani zancen ƙara aure a gabanka har abada, Uncle Amyn,...Jaddi..wanda shi ba'a ma magana. A hakan farin ciki kuke, kuma babu abinda kuka rasa daga matayen na ku...Kaga da wannan dalilin Uncle? Nake roƙonku da ku janye zance na da Noura, I'm not that type too...na auren mata fiye da ɗaya, idan Kunga ƙanina ya yi ra'ayi, ni ba lallai ina da wannan ra'ayin ba. Allah ma ba ɗaurawa kowane namiji cewa sai ya yi mata fiye da ɗaya ba, idan ka auri ɗaya har ƙarshen rayuwarka baka da zunubi, idan ma kuma ka auri biyu, uku, huɗu, har ƙarshen rayuwarka shi ma baka da wani laifi a wurin Allah. Idan ma zaunawa za ka yi a duniyar har ka koma gareshi ba tare da ka taɓa yin auren ba shima ba ka da zunubi akan hakan matuƙar dai za ka kiyaye da dokokin Allah. Da wannan nike roƙonku akan kada ku tilasta, kada ku kai ni bango in ji cewa ba ku damu da damuwa ta ba. Ba lallai sai ni ba, akwai mazaje da yawa waɗanda za ta aura ta ma fi farin ciki fiye da idan tana tare dani....Uncle Mu'aƙƙib! Kun yi kukan rashina tsawon shekaru tunanin cewa na mutu bana duniyar nan...amma a yanzu...zai fi muku ciwo da raɗaɗi fiye da yan da kuka ji a baya, domin zan kasance ina raye amma bana tare da ku. Ina roƙo da ku fahimci damuwata, ba wai zan bijire muku ne domin nuna cewa baku isa dani ba, auren ne bana so bana ra'ayi, mata ta ta ishe ni rayuwa. Ciki ne da ita a yanzu, bana so sam abun da zai riƙa ɗaga hankalinta."

Yana gama faɗar haka ya miƙe ya wuce ya koma gidansa direct ya shige ta kulle. Ya jima a toilet tsawon lokaci yana sakarwa kansa ruwa, sannan daga ƙarshe ya fito ya shirya cikin riga da wando masu sauƙi.

Ya yi mata alƙawarin cewa kada ta yi bacci zai kira ta, amma kuma damar hakan ba ta samu ba, saboda gabaɗaya baya hayyacinsa, tunani da kuma lissafe-lissafe su ne abin da suka shige masa gaba.

Yana nan zaune wuri ɗaya a parlour tamkar wani ɗan maye tsawon lokaci, sannan daga ƙarshe ya janyo wayarsa ya duba agogo. 1:22am, abin da agogon ya nuna masa kenan. Miƙewa ya yi ya fito ya haye Rooftop ɗin gidan nasa wanda ya tarar an ƙawata shi sosai an gyara shi kamar yanda na su Jadda yake, daman ya ji Suhaib na tsokanar Beenafah yana cewa Jaddi ya saka an gyara mata Rooftop ɗin gidanta wanda ko da ta zo watarana, tunda har ya fahimci tana ƙaunar wurin ba sai taje kwarakar gidan wasu ba.

Tsaye ya yi tare da ɗora hannayensa akan zagayayyen ƙarfen da ke wurin ya shiga kallon garin wanda ya haska cikin fitilu masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali.

Motsin da ya jiya daga gefensa ne ya saka shi ɗan Waigowa kaɗan ya kalli gun. Jaddi ya gani a tsaye yana masa murmushi, cike da farin cikin ganinsa ya rungumesa na ɗan wani lokaci sannan ya janye yana murmushin shi ma, ya ce.

"Barka da zuwa, da fatan an dawo lafiya?"

Murmushi Jaddi ya yi yana mai jinjina kansa ya ce.

"Lafiya ƙalau na iso. Da fatan kai ma ka zo lafiya?"

"Lafiya ƙalau, Alhamdulillah!.."

Ɗan ƙara gyara tsayuwarsa ya yi yana mai fuskantar sa da kyau ya ce.

"Tafiyar kasuwanci? Ko kuma siyasa?"

"Tafiyar siyasa ce,...kai ma fa da kake da sauran lokaci, naga ka nemo yara ka saka a cikin kasuwancinka, to ballantana ni, idan nace har yanzu ina tafiyar kasuwanci da kai na, ai ko kai za ka mini faɗa ko?"

Jinjina kansa ya yi yana dariya ya ce.

"Hatta wannan harkar Siyasar ya kamata ka daina ta haka Grandpa. Alhamdulillah! An ci ma manyan nasarorin da sai dai godiya ga Ubangiji...Kaga za ka samu ka zauna wuri ɗaya ka ci gaba da bautawa Allah wanda ya halliceka domin bauta masa kaɗai."

"Haka ne Hammodi...Ina alfahari da kai...matuƙar alfahari. Ahm! Magana ta gaba kuma. Batun auren ka da Noura, mun tattauna da Kakar ka da kuma sauran Iyayenka..."

A hankali ya ɗaga kan shi yana kallon sararin samaniya, yan sa taurari suka jera suke ta ƙyalli hakan abun burgewa ne da ɗaukar hankali. Numfashi ya ja sannan ya sauke a hankali yana mai jinjina kansa ya ce.

" Grandpa! Ban san tarihin soyayyarku da kai da Jadda ba...but amma a yanda still na fahimceku da ganin yanda kuke gabatar da abubuwanku...zan iya cewa kun gina alaƙar soyayyar da kyau da kuma amana tun farkon rayuwarku..Duk da cewa kun tsufa sosai, kuna da 'ƴa' ƴa da jikoki..har yanxu kuna ƙaunar junanku, har yanzu kuna girmama juna da girmama ra'ayoyin junanku. Kana matuƙar son abun da take so, har yanzu da shawarwarinta kake amfani.."

Juyawa ya yi yana facing ɗinsa, cikin wani irin yanayi ya ce.

" Grandpa...ban taso tare da iyayena gabaɗaya, amma daga yanda Mahaifina yake bani tarihin zamansu da mahaifiyata...shi ya tabbatar min da cewa Mahaifina ya gamsu da duk abun da mahaifiyata take masa wanda bai yi yunƙurin ƙarin wani auren ba sai da ta mutu ta bar shi a duniyar....To kamar haka ne Ni da Beenafah. Ta yi min komai a duniya, ta ce to rayuwata, ta amince da aurena ba tare da tasan ni wane kalar mutum ba ne, ta amince dani wanda bata sani ba, shin ni ɗin, kurma ne, makaho ne, kuturu ne ko kuma gurgu marar ƙafa, shekaru ma haka, bata tsaya ta yi tunanin cewa ni sa'ar auren ta ba ne ko a'a, kawai abun da kyakkyawar zuciyarta ke yi mata nuni da shi...shi ne ceton rai. Bayan mahaifiyata da sauran iyayena...Beenafah ta fiye min kowace irin Mace a duniya Grandpa. Ina ƙaunar ta sosai, ƙaunar da ba zan iya haɗa ta da wata macen ba. Please ku gafarceni..ba wai don na bijire muku ba, ba don ina ƙin Nourar ba, ra'ayin ƙarin auren ne bani da shi, idan kuka matsa kuma...dukkanmu mu ukun zamu cutu sosai."

Kamar yanda jikin Uncle Mu'aƙƙib ya yi sanyi a ɗaxu...shi ma dai Jaddi tamkar an tsoma shi a ruwan ƙanƙara haka yake ji tsabar yanda maganganunsa suka shiga zuciyarshi.

Kafaɗar shi ya dafa tare da jinjina masa kai a hankali yana mai jin yanda idonsa ya cika da ruwan hawaye ya ce.

" Mun riga mun fahimce Hammodi. An soke zancen wannan auren...da mu rasaka har abada alhali kana raye...gwanda mun haƙura tunda baka so...da mun ɗauka cewa idan mun aura maka Noura...za ka fi kasancewa a tare damu da kuma ɗaukar matsalolinmu a matsayin naka...sai ga shi hasashen namu ba haka yake ba, domin ka bamu muhimmanci sosai tare da bin umurninmu, ga Suhaib ka ɗauka ka ɗora shi kai tsaye a wuri mafi haɗari wanda ko tunanin ya cutar da kai ba baka yi. Komai namu ka mayar da shi haka, haka kuma komai naka ka mayar da shi namu. Allah ubangiji ya ƙara muku zaman lafiya da farin ciki mai ɗorewa, Allah ya sauke ta lafiya."

Bai san lokacin da ya rungume kakan nasa ba tsabar yanda ya ji farin ciki ya kamashi, saboda yanda suke ta giɗaɗa maganar nan ya za ta sai ya sha baƙar wahala kafin su iya fahimtar sa ballantana ma su yarda ya janye maganar.

" Kai...dare ya yi sosai, ka samu ka je ka huta..."

Murmushi ya yi yana kallonsa ya ce.

"Kai ne ya kamata ka huta Grandpa."

Har ya juya zai tafi, sai kuma ya wai go yana faɗin.

"Firar da mukayi a Rooftop ɗin gidanka a wancan lokacin ka tuna...Kai ne nan wanda ka rakoni gidana, saboda haka yau ni ne wanda zan rakaka..."

Dariya suka yi dukkan su sannan Jaddin ya jinjina kai ya ce.

"Ka yi gaskiya. Mu tafi ɗin to..na san cewa mata ta tana can ta yi fushi yanzu, saboda na kai uku na dare a waje..."

Da mamaki ya kalli kakan nasa ya ce.

"Kana nufin wai ba ta yi bacci ba?"

Girgiza kai ya yi sannan ya ce.

"Wani lokacin ta kan zauna komi tsayin dare ta jirani, wani lokacin kuma koda zan koma tayi baccin ta. Yau ma dai tunda tasan ina tare da jikinta, to tana can ta kwanta yana bacci cikin kwanciyar hankali..."

Hannun shi ya ɗora akan kafadarshi suka ci gaba da saukowa a hankali yana faɗin.

" Kana ji ko Hammodi..Matayenmu su ne farin cikinmu, kuma su ne kwanciyar hankalinmu. Idan ka samu mace ta gari, sai Kaga rayuwarka ta yi kyau sosai ta yi albarka, idan kuma ka samu matar kirki ba, haka za ka yi ta ƙare wa kullum kamar kuɗin cefane tsabar yanda matsaloli za su yi ta kunno maka kai. Manzon Allah (S.A.W) mafi ƙololuwar jin daɗin duniya...Shi ne mace ta gari. Idan har ka yi dace da wannan, to kaima sai kayi ƙoƙari ka zamo miji na gari a gareta...a wasu lokutan fa, mace kuɗinka ba su ne a gabanta ba, kawai lokacin ka take buƙata ka kasance a tare da ita, idan tayi magana ka saurareta, ka yaba mata, duk fannin da take burgeka da shi a cikin zamantakewar auren ku...ka yi ta yaba mata a kai...."

Sun jima a tsaye bakin Main door ɗin su Jaddan, sannan daga ƙarshe suka yi sallama ya shige shi kuma ya koma gida.

******* Washe gari ya jima bai fito ba, saboda kamar dai ma ido biyu ya kwana har gari ya waye. Hakan yasa bayan ya dawo daga masallaci, suna magana da Beenafah ya kwanta bacci.

Sosai ya ji wani iri a ransa a lokacin da suka haɗa ido da Jadda. Sai da ga mamakinsa, itama ko kaɗan bata nuna masa komai ba. Sai ma kiran masu aikinta da ta shiga yi tana faɗin su haɗo masa abincin karyawa, wannan da aka ajiye tun ɗazu ya yi sanyi.

Wuri ya samu a gefenta ya zauna ya gaisheta sannan ya ce.

"Daman ina so in baki haƙuri ne...dan Allah ki yi haƙuri. Ba don ina ƙinta ba ne yasa..."

Jinjina kanta ta yi tana murmushi ta ce.

"Ba komai Hammodi...wannan duk ya wuce in sha Allah. Ko ba komai ai kuɗin en uwa ne. Allah yasa hakan shi ne mafi alheri. Ni ce ya kamata ace na baka haƙuri akan uzzurawa rayuwarka da na yi."

"Haba ba komai. Na gode sosai Jadda.."

Shigowar Noura da wata tsohuwa wacce sosai suka yi kama da Jaddan shi ne abinda ya ja hankalinsa. Ji yayi Jadda na faɗin.

"Au! Wai har ta fito kenan tun yanzu?"

"Wallahy kuwa, kin san halin mutumin ai, tun da asuba yake ta uzzurawa..."

"Allah ya tsare hanya kin ji ko. Allah ya zaɓa miki mafi alheri."

Wayar shi ta yi ringing, hakan yasa ya tattara daga sunan amsa kira ya fece daga gidan wanda bai dawo ba sai misalin ƙarfe huɗu na yamma.

Kallon shi ta yi tana faɗin.

"Tun safe kana ina haka?"

Wuri ya samu ya zauna sannan ya ce.

"Mun fita da Jaddi...And yanzu ma haka tafiya zan yi."

Wani kallon ta mi shi na mamaki sannan ta ce.

"Tafiya zuwa ina? Jiya-jiyan nan fa ka zo."

Murmushi ya yi mata yace.

"Haka ne...da yake na ɗan baro wani uxuri ne shi yasa..."

"Uhmm! To ba laifi. Ka ce gefen mahafinka za ka tsaya ba a nan ba. To ina neman alfarma dan Allah ka bar Beenafah ta zo nan inda muke. Kaga idan akayi hidimar nan babu ku duka biyun abun zai yi wani iri..."

Cikin rashin yarda da maganar ya ce.

"Jadda! Kin san da juna biyu ne da ita, and kasancewarta a wani wurin idan bana nan, gaskiya kamar abun zai yi wani iri.."

Cikin nuna rashin jin daɗi ta ce.

"Haba Hammodi! Yanzu nan gidan shi ne wani wuri? Don na buƙaci ta zo cikin dangin mahaifiyarka shi ne za ka ce wai abun zai yi wani iri.."

"No please! Ki yi haƙuri. Ba haka nake nufi ba...amma tunda kin ce. Zan tambayi view ɗinta mu ji..."

"Kenan ba za ka zartar da komai ba sai abin da ita ta yanke maka Hammodi?"

"No...ba haka bane..."

"Kana ji Hammodi? Auren Suwara da Suhaib zai tara mutanen da muka jima bamu tara ba. Rashin ka a nan Sam bai mana daɗi ba, dan Allah kada ka ƙi amincewa da zuwan ta domin ko ita muka gani zamu ji daɗi....nan ɗin fa gida ne,gidanku Hammodi, kamar yanda ka ke taƙama da dangin Mahaifinka nan ɗinma duk ɗaya ne"

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya ce.

"Shi kenan Jadda, In Sha Allahu za ta zo."

"Tou Masha Allahu. Allah ya kai mu rai da lafiya."

"Amin."

Daga haka ya fito suka shiga mota tare da su Sharath wanda su shi ne zuwansu na farko. Har Airport Jaddi ya rakoshi, a nan ya tambaye sa cewa.

"Grandpa why Noura ba za ta zauna har a kambala wannan hidiman ba. Ya ake ta uzzura tafiyanta?"

"Saboda Kakanta yana da wani irin tsatstsauran ra'ayi. Shi wani irin mutum ne na daban Hammodi. Labari ne mai tsawo, ka bari duk sanda ka sake dawowa muka samu lokaci zan sanar maka."

"Ok..na barka lafiya farin tsoho Kakan Hammodi."

Dariya suka yi dukkan su sannan daga ƙarshe suka yi sallama.

*******

Gefen Jafaru kuwa, Beenafah na komawa shima ya juya ya koma makaranta. Sai dai gabaɗaya rayuwarsa ta yi matuƙar sauyawa ba kamar yanda ake a da ba.

Rayuwarsa da tunanin sa a yanzu sun ta'alaqqa ne akan Beenafah. Shi bai taɓa ma jin sonta can baya ba kafin ta yi aure kamar yanzu ba. Yanzu ne yake jin yana masifar ƙaunar ta wanda ji yake kamar ma zai yi hauka.

Duk abokan karatunsa sun yi ta bashi shawara akan cewa shaiɗan ne ke ƙawata mishi matar auren mutane ya yi haƙuri ya dage da ibada in sha Allah zai manta da ita. Sai dai ina! Ya riga ya zurma sosai domin har mafarkin yake yana tarayya da ita.

Har ɗaki yaje ya cim ma wani abokinsa Qatada ya zauna ya faɗa masa irin halin da ya sake tsundumawa a ciki.

Kallonsa ya yi cike da tausayi ya ce.

"Abokina magana ta gaskiya kana cikin masifa. Don wannan da masifa zan kira shi. Shawarata ɗaya ce a gareka, ka watsar da lamarin yarinyar nan ka koma ga Allah, ka manta da ita. Wallahy tallahy wannan ba komai ba ne face aikin shaiɗan da yake ƙawata maka ita zuciya, kuma daga zaran ya gama halakar da kai zai koma gefe ya bar ka da kayan da ka ɗaukarwa kanka. Ka manta da ita ka mayar da hankali ga karatunta In Sha Allahu, Allah zai baka wata wacce ta fita alheri..."

Wani irin tsaki ya buga tare da yi masa wani kallon a kaikaice ya ce.

" Gaskiya Qatada baka da hankali!"

" Saboda na gaya maka gaskiya Jafar?"

" Eh to ba dole na ce haka ba. Yarinyar nan fa budurwa ta ce tsawon shekaru kawai wannan ƙaton banza don kawai yana taƙama da kuɗi ya rabani da ita. Shi ne za ka ce wai sharrin shaiɗan ne..in da tun farko ban haɗa sabga da ita ba, ace kawai rana ɗaya na taɓa ganinta kuma da aurenta na ce ina so, to Kaga idan har na aikata haka shi ne zaka ce mini sharrin shaiɗan ne..."

Miƙewa Qatadan ya yi tare da ɗaukar litattafan karatunsa yana wani irin murmushi ya ce.

" Ni dai ina taya ka da addu'a, ubangiji Allah ya ye maka wannan masifa ya shiryar da kai. Ni na tafi wurin abinda yake gabana, kuma exams tana ƙaratowa, ina baka shawara ka kama karatunda ya kawo ka.."

Yana gama faɗar haka ya fice wurin karatu. Wani room mate ɗin Qatadan ne wanda ake kira Ukasha suna ce Masa Uka ya taso daga kan shimfiɗar sa ya zauna a kusa da shi ya ce.

"Wallahy abokina daga jin wannan labarin soyayyar naka akwai sammu da baƙin ciki a ciki..."

Wani irin waigowa yayi yana mai dugunzuma masa hankalinsa ya ce.

"Allah abokina?"

Jinjina kai ya yi yace.

"Sosai ma kuwa? Ai tunda kace wai yarinyar tana masifar sonka wanda ba ta iya komai ma idan ba tare da kai ba na gano bakin zaren..."

Cike da alamar magiya a kalamansa ya ce.

"To don Allah ka faɗamin yanda zan yi?"

"Ai wannan komai a fayyace yake. Iyayenka su ne farkon en baƙin cikin ka, domin su ne suka zama shamaki tsakanin aurenka sa ita. Sannan na biyu wannan tsohon ba haka ya barta, dole billahillazy asiri ya mata. Asiri ne! Kai ma ka auna da ƙwaƙwalwarka ka gani. Da ka fara fahimtar da ita har ta fara ɗaukar haske, sai kuma daga baya abubuwa suka ƙara lalacewa, saboda haka asiri yay mata, ka yarda kawai asiri yay mata."

Nutsuwa ya yi sosai alamar nazari sannan daga ƙarshe ya jinjina kai yace.

" Tabbas wannan magana taka haka take Uka...lallai Biri yay kama da mutum."

"To, tunda har Allah yasa ka fahimta, kai ma yanzu baka ga ta zama ba. Tashi za ka yi ka haɗa en kuɗaɗenka mu tafi can cikin gari akwai wani babban malami wanda aikinsa kenan, dawowa da saurayi budurwarshi da ya rasa ko kuma dawowa budurwa saurayinta da ta rasa...."

"Da kake Uka?"

"Allah wallahy! Ai iyaka ka nemi kuɗi...miye ma kace sunanta?"

"Bbb..Beenafah."

"To ka sanya a ranka Beenafah ta dawo gareka an gama. Da kanta ina gaya ma abokina za ta zo har Campus ɗinnan wurin neman ka. Bari na sulala ƙanzo yanzu ina zuwa,daga zaran na gama sai mu tafi."

Wani irin farin cikin da ya kama Jafaru ji yayi tamkar ya goya Ukasha ya yi ta tiƙa rawa da shi tsabar yanda ya faranta masa.

Da haka suka yi sallama inda yace shima bari yaje ya shirya kafin ya kambala.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull