Ganin ido complete - Chapter 71
Ganin ido complete Chapter 71: Ganin ido complete Chapter 71. Nan Su Mama Asma'u suka zazzo wurin yi mata murna alherin da ya same ta. Hajiyar Dr. Basheer…
3,359 words
Nan Su Mama Asma'u suka zazzo wurin yi mata murna alherin da ya same ta. Hajiyar Dr. Basheer ma, tun daga Bunza ta shirya ta zo na musamman ta yi mata barka. Daman Allah ya sanya mata ƙaunar Ammie a ranta.
Hamza tamkar zai yi hauka akan farin cikin Ammie ta dawo. Kullum suka yi waya cewa yake wannan makaranta bata kyau ta masa ba, domin ita ce tayi masa cikas da yanxu da shi akayi wannan tafiyar.
Haka ta shiga rarrashinsa akan cewa watarana za ta tafi da shi in sha Allah.
Duk yanda ta yi ta faɗawa Maman Fakiha akan kada ta zo cikin azumi ta jira sai bayan sallah ƙin amincewa ta yi. Haka suka shirya suka zo ita da Baba da su Fakiha suka mata barka suka kwana biyu suka koma gida.
******
Ni kuwa, tunda muka koma gida, aikin Dayaa daga Monday sai friday yake fita office. Rayuwarmu muka shimfiɗa sabuwa wanda kullum yana nan tare dani muna rainon cikinmu.
Waya ce ba dare ba rana kowa kira yake yana jin lafiya ta wanda babu abinda zan cewa Ubangiji sai godiya da wannan ni'ima da yayi mini.
Azumi da akayi, guda goma sha biyu kawai na samu na yi da ƙyar, wanda shi a yanda ya so, na bar azumin sai idan na haihu na rama. Da haka na yi ta lallaɓa shi na samu na yi sha biyu ɗin.
Kullum muna kan zaryar asibiti shi dai a duba lafiyarsa babyn sa, idan an ga da matsala dole na dakatar da azumin.
Sallahr Idi da muka gabatar a Dubai abin ya ƙayatar da ni ba kaɗan ba. Musamman gani ga mijina a masallaci.
Bayan mun dawo muka hau kiraye-kirayen waya musamman vedio call ana ta gaishe-gaishe cike da farin ciki.
Ana gama sallah da sati ɗaya Emraan da Suhaib suka dawo Office. Yayin da zuwan sa office ya dawo only Monday in a week.
A haka rayuwa taci gabar mana da tafiya muna nan muna rainon cikinmu sai da EDD na ya rage two weeks wanda a lokacin sallah babba ya rage a lissafi saura kwana goma sha bakwai.
Ba za to ba tsammani ina tsaye a kitchen after Isha prayer ina haɗa Tea ya shigo Kitchen ɗin ya same ni.
"Bibi! Tea kike haɗawa?"
"Uhm! Welcome."
Na amsa ina mai ajiye spoon ɗin hannuna.
"Ki haɗa dani..."
Dariya na yi na ce.
"Ai fa! Ko miye na sha sai kasha. Maganin da Jaddi ya aiko mini shima idan na haɗa shanyewa ka ke yi, sai ka ce kai ne mai cikin."
Dariya ya yi tare da jinjina kansa yana kallona ya ce.
"Iyyeh! Yau abun na gori ne kenan?"
Dariya na fashe da ita ina girgixa kaina na ce.
"A'a, ai tare muke da shi mu biyu."
"To na ji. Zo mu je in miki wani albishir..."
Cike da zumuɗi na ɗauko tray na ɗora mana kofunan ya ɗauko a hankali yana biye tafiyata har muka isa parlour muka zauna.
Ganin yanda na ƙura masa ido ne yasa yayi dariya yana faɗin.
"Ki sha mana.."
Ɗan ɓata rai na yi tare da shagwaɓe masa na ce.
"Ni dai dan Allah ka fara sanar mini tukun..."
"To miye farashin?"
"Daɗa mini kake so?"
"Kyakkyawan murmushin nan da na bana gajiya da shi..."
Bansan lokacin da na murmusa ɗin ba kuwa, wanda har sai da kyawawan haƙorana suka bayyana sannan ya lumshe idanunsa ya buɗe tare da kamo hannuna ya ce.
"Ammah ta roƙa akan na bari ki je can ki Haihu..."
Murmushi na yi sannan na ce.
"Allah sarki! Ɗazu ma ina sallah sai da ta kirani, sai da na kambala na kira ta."
"To za ki je?"
Girgixa kaina na yi na ce.
"Idan har za ka amince na je wani wuri na haihu, to wurin Ammiena zan je Sokoto."
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"Daman ina da wannan plan ɗin. To sai gashi ɗazu ta kira, ita da Abiyh suka shirya hakan."
"Ba komai, ka ba su Haƙuri, idan Allah ya nuna mana na haihu lafiya sai mu tafi daga baya, amma ni gaskiya na fi son kusa da Ammiena..."
"No...kada ki damu kin ji ko. Abinda kike so ni ma shi nake so. A wannan gaɓar, babu wanda zai takura miki akan ra'ayinki kin ji ko."
"Na gode sosai."
"Ki shirya, ranar friday idan Allah ya kaimu sai mu tafi. Kada ki damu zan yiwa su Abiyh ɗin bayani..."
Daga nan na hau shirye-shirye, ranar friday ɗin na zagayowa muka wuce gida Sokoto.
Ammie ta yi farin ciki sosai wanda har da hawaye tayi, ganin na zo da sunan haihuwa. Kwana ɗaya ya yi a Sokoton ya yi mini sallama ya wuce wanda sai da na yi kuka kamar yanda na saba idan zamu rabu. Har yanzu na kasa sabawa. A duk lokacin da rabuwa ta zo a tsakaninmu sai na ji kamar ba zan iya jurewa ba.
Sosai Ammie da su Mummy Sameerah suka shiga bani kulawa, shirye-shiryen babban sallah suke, amma ni kuma lissafin nake a ranar ina nan na yi kane-kane ina jego. A duk lokacin da na tuna haihuwa, Aunty Ziza ce ka zuwa cikin tunanina, yanda ta ke yi a lokacin da ta haifi Abeer, sai baza mulki take tana ta abinda ta ga dama.
Rayuwar ya Hamza na saka a gaba, tun da na zo gidan duk abinda za'a mini shi nake cewa yayi. Daman na faɗa masa cewa, duk rashin nasihar da ya dinga mini sanda muna Gusau duk sai na fanshe ta a yanzu. Kuma idan ya ce bai zai yi ba in faɗawa mijina.
Yau ma da yake daren sallah, suna Kitchen suna aikin da ya sha masu kai na iske shi ina dariya na ce.
"Ya Hamza!"
Wani kallon ya mini sannan ya ce.
"Ke malama ya dai?"
"Ya Hamza Fara na ke son ci, irin wannan wacce ka siyo mini ranar..."
Wani kallon ya sake mini sannan ya ce.
"Wannan Farar ba siyo ta na yi ba, Mummy Sameera ce ta bani ni kuma na kawo miki..."
"Ni dai ita nake so"
Wayar shi ya janyo ya duba lokaci. Sha ɗaya da minti arba'in da biyu na dare ne yanzu.
"Hmm! In siyo miki Fara a kasuwa, mijin ki ya yi banda ta ko? Dan Allah Beenafah ki rufa min asiri. Ga nama nan a ko'ina na cikin gidan wace fara kuma kike nema...Ammie dan Allah ki yi mata magana mana."
Dariya su Ammie suka kwashe da ita musamman ganin yanda ya marairaice kamar wani maraya yana mini magiya.
Kallona Bahrain ya yi ya ce.
" Yanzu Aunty Beena keda kika ce mini baki da lafiya tun ɗaxu, shi ne kuma kike neman tsokana?"
Ai kuwa, kamar kar Bahrain ɗin ya yi magana na ji wani ciwo ya murɗa mini sai da na runtse idanuna. Da haka na lallaɓa na koma ha tare da na sake yiwa kowa magana ba.
Ina nan ina ta en matse-matse na sai ga Ammie ta shigo misalin sha biyu da rabi tace na tashi mu tafi asibiti.
Tare dani da ita, Abbu da kuma Ya Hamza ne muka je asibitin.
Washegari kowa na can yana shirin bukin sallah ni kuma in Labour room ina gumurzu. Mama Asma'u ce ta zo ta tsaya dani ita da Inna Ladi mai aikin Ammie.
Kowa ba'a sanar wa ba kamar yanda Ammie ta ce domin kada a ɗaga musu hankali. Sai dai Ya Mohaa kam dole aka sanar mai domin kwana ya yi yana kira yana cewa a sadashi da ni, ganin ya ƙi daina kira duk hankalin sa ya tashi ne tayi masa bayanin cewa ina labour room amma komai lafiya ƙalau. Daƙyar ya samu ya gama sallar Idi lafiya domin bai jira komai ba ya kamo hanya.
Misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe bayan gurje-gurje, da yaƙushe-yaƙushe da kuma kiran sunan Dayaa da Ammie Allah ya nufe ni da samun 'ƴan biyu duk Maza.
Ammie ruɗewa ta yi ta gigice jin cewa wai male twins ne. Kafin ka ce mi gabaɗaya dangin Abbu sun cika asibitin sai farin ciki ake.
Bakin Ammie har kunne take ta kira tana sanarwa en uwa da abokan arziki. Bayan an gama shiryani aka ɗauko mini yara biyu Mama Asma'u ta ɗora su akan jikina.
Kallon su na yi da mamaki sai kuma na kalli Midwife ɗin na ce.
"Ya naga yara biyu?"
Murmushi ta yi tace.
"Haba Beenafah! Har kin manta ne kenan, ke ce fa nace miki akwai sauran guda ɗaya amma kika ce na bar shi a ciki..."
Duk yanda na ke ji sai da ta sa na murmusa tuna irin wutar da mukayi dani da ita a ɗaxu. Kuma fa har nuna mini ta yi. To amma ni na ɗauka duk zafin naƙudar ne yasa na ke ganin kamar yara biyu ne.
Da mamaki na ce.
" Nurse, Ultrasound scan fa, Kuma na ƙwararru Baby ɗaya ya nuna, kuma ko satin da zanzo nan ɗin sai da naje na yi wani.."
"ikon Allah kenan Beenafah! Shi ne mai yin yanda ya so. Ya baku kyautar biyu sai ya baku ilmin ɗaya ya ɓoye ɗayan sai yau ya bayyana muku. Alhamdulillah! Allah shi ne abin godiya."
Cewar Mama Asma'u tana mai ƙoƙarin ɗoramin ɗayan akan ƙafata.
"Yaran kuwa suna da buƙatar Nono Beenafah..."
Zaro ido na yi na kalli Nurse ɗin jin wata magana wacce ta saka ƙirjina doka wa. Ganin da gaske take na ce.
"Ba fa komai a ciki."
"In ji waye ya ce miki? Babu zallar madarar da aka saba gani fara, amma akwai madara mai matuƙar muhimmanci ga lafiyar jariri a tsakanin kwanaki uku na haihuwa wacce ake kira da colostrum. Ita wannan madarar tun ciki yana sati goma sha shida Allah yake halitta ta a cikin nonon uwa ta zauna. Wacce idan aka haihu, to amfanin ta na kwana uku ne,za ki ganta yellow-yellow wacce ita ce sinadari na farko mai muhimmanci wurin ƙarawa jariri lafiya da kuma kare shi daga infection. Shiyasa matse ta da wasu ke yi kuskure ne, ko kuma a hana yaro ace wai aci gaba da bashi dabino da zam-zam kafin ruwan nono ya kawo kuskure ne. Gani ake kamar yaro baya shan komai, kalar madarar ba fara ba ce shiyasa ba kowa yake fahimta ba. Tana da matuƙar amfani."
Jin na gamsu da bayanin ta na ce.
" To ba matsala Nurse. Sai a basu ɗin."
Wani Sabon towel ƙarami Mama Asma'u ta ɗauko sannan ta zuba ruwan zafi ta surka tace na sauke rigata.
Runtse idanuna nayi gam ina mai jin kunya sosai, ta saka ta goge nonuwan da kyau sannan ta miƙo mini ɗaya tana faɗin.
" Wannan shi ne Hassan Beenafah, shi ne wanda ya fara zuwa duniyar."
Kallon fuskar shi na yi, sai kuma naji wasu hawaye waɗanda ban san ko na miye ba, sai na rungume shi a ƙirjina na tsawon mintuna ina mishi addu'a sannan na janye a hankali da taimakon Nurse ɗin tana koyar dani har nayi nasarar jona shi ya fara tsotsa.
Shiru kawai na yi tare da runtse idanuna ba don abin yana mini daɗi ba, sai ma zafin da nake ji. Bayan yasha aka bani ɗayan shima na masa addu'a sannan na jona shi.
Ina ganin su Mummy Sameerah na shiga neman abin da zan saka na rufe ƙirjin nawa domin wata kunya ce na ji ta kamani.
Hijabi Mama Asma'u ta jefo mini ganin ina ta kame-kame.
"Mama ba zan iya sakawa ba, dan Allah ki lulluɓa mini kin ji?"
Tasowa tayi daga kan kujera ta lulluɓa mini su kuma sai tsokanata suke. Ni dai shiru na nayi domin gabaɗaya I'm not comfortable da situation ɗin. Ga shi har da ɗin ki aka mini domin sai da ta ƙara ni, yanayina gabaɗaya ba daɗi.
Ina nan sai ga Ammie ta shigo. Kallona take har ta ƙaraso tana mai zubo da ruwan hawayen farin ciki ya ce.
"Barka da arziki farar uwa irin alheri!Sannu Giwata, ɗiyar ƙwarai irin albarka. Kin zama uwa tun baki san miye wannan kalmar take nufi ba, yau kuma ga shi kin zamto ta gaske Beenafah. Allah ubangiji ya yi miki, Allah ya yiwa waɗannan yaran albarka. Allah yasa ki gama da duniya lafiya, Allah ya ƙara baki zaman lafiya da mijinki ya shiryar da waɗannan yaran bisa tafarki madaidaici ya ƙara muku wasu masu albarka. Na gode, na gode da farin cikin da kika sanya ni Beenafah. Yanda kika ji ƙaina kika tausayeni kika wahala dani na tsawon shekaru ba tare da kin gaza ba, ke ma Allah ya ninka miki fiye da abinda kika mini, Allah yasa 'ƴa'ƴanki su tausayeki su ji ƙan ki fiye da yanda kika mini..."
Ban san lokacin da wani irin kuka ƙwace mini ba, jin wata irin addu'a mai tsada a lokaci irin wannan. Jinjina kaina na yi ina faɗin.
" Amin Ammiena na gode sosai Allah ya saka da alheri, duk abinda kike roƙa mini kema haka Ammie, da ke da duk su Mama Asma'u, kowa na gode mishi. Allah ubangiji yasa ku gama da duniya lafiya."
"Amin."
Zaunawa ta yi ta rungume yaran a jikinta tana ta wani irin farin ciki tamkar za ta haɗiyesu a cikinta tsabar yanda take ji.
Kowa da yake ɗakin sai da ya zubo da ƙwallar farin ciki jin kyakkyawan yanayi tsakanin uwa da 'ƴar ta.
Kallona Mummy Sameera tayi tana faɗin.
"Mi za ki ci? A kawo Tea?"
Dariya Mama Asma'u ta yi ta ce.
"Wane Tea? Beenafah kam tun ɗazu ta sheƙe kofuna biyu har da bread in faɗa miki."
"Ah..to Masha Allah, ai haka ake so. Allah ya ƙara lafiya ya raya mana en jikallele."
********
Sai misalin ƙarfe shida na yamma Dayaa ya shigo ɗakin. Zani na ja da sauri na lulluɓe ƙirjina saboda wauta wai shima kunyar sa na ke ji.
Murmushi da hawaye sune abinda ya tarbeni da su tare da hugging ɗina na tsawon lokaci. Janyewa ya yi ya sumbaci goshina wanda lokacin ne na ji saukar ɗumin hawayensa a fuskata.
Koda na buɗe idona, ashe duk wanda yake ɗakin ya sulale ya fece sun barni daga ni sai shi.
Zaunawa ya yi akan kujera ya riƙo ɗayan hannuna yana mini wani irin kallo ya ce.
"Ban san ta yanda zan fara miki bayanin halin farin cikin da nake ciki ba Bibi..."
Murmushi na yi ina mai jin hawaye a idona na ce.
"Na fahimta Dayaa na, kawai ka ce Alhamdulillah!"
"Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Ya Allah kai ne abin godiyata. Allah na gode maka da wannan babbar kyauta da ka mana. Ba wayonmu ba ne ko dabararmu. Allah duk yana daga cikin ni'imominka wanda kuɗi ko wata gadara ba su isa su siye sa ba. Alhamdulillah! Allah ga mata ta nan, yanda ta faranta min, ya Ubangiji ka fini sanin abin da yafi da cewa da ita. Ya Allah ka yi mata albarka, ka bata lafiya mai amfani ka bani tsawon rai da lafiya da ita domin in cika rayuwarta da farin ciki ita da waɗannan yara na mu dama waɗanda za su bayansu. Ya Allah ka tsare ni da yin fariya da juya baya, Allah ka kare ni daga sharrin shaiɗan kada na zamto mai butulcewa a gareka, ubangiji ka ci gaba da tsayar dani da matata akan dugaduganmu na gaskiya da kuma kiyaye dokokin ka har mu koma gareka..."
"Amin. Congratulations! Yau na cika maka mafarkinka Mijina...kalla ka gani? Yara biyu Maza...su ne Allah ya bamu. Alhamdulillah!"
"Alhamdulillah! Na gode sosai Bibi."
Yaran na ɗora masa ya ɗauka yana ta murmushi yana hawayen farin ciki. Muna nan nurse ta shigo dubani, bayan ta gama ta fita ne na kalle shi ina murmushi na ce.
"Midwife ɗin na haihu a hannun ta tana da matuƙar kirki Dayaa, tana da kirki tana kuma da tausayi. Sosai ta yi ta rarrashina tana lallaɓa ni tare da bani kalaman ƙwarara gwiwa har Allah yasa na haihu lafiya."
"Ina take?"
"Su biyu ne gaskiya, da wacce ta yi night shift wacce ita ce aka kawo ni tana nan cikin dare, sai kuma ɗayar ita morning take wacce na haihu a hannunta.
" OK! To mun gode musu sosai Allah ya saka musu da alheri ya taimaka."
Washegari likita na gama dubani aka bamu takardar sallama bayan an tabbatar cewa daga ni har twins ɗina muna lafiya.
A nurses station muka tarar Midwife ɗin na zunduma ihun farin ciki tana ta zuba godiya wanda alama Account ɗinta ne ya jijjiga da alert na ban mamaki duk da cewa ban san nawa ya tura musu ba. Amma gaskiya ta yi farin ciki sosai, sai godiya take tana ta mana addu'a.
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 57*
Tun da na yi wanka na naci abinci na kwanta babu wanda Ammie ta bari ya ƙara shigowa inda nake, sai da yamma da Dayaa ya shigo sannan ta shigo ta tarar da ni a zaune ina breastfeeding na su ta yi murmushi ta ce.
"Kin tashi?"
Murmushin na mayar mata na ce.
"Na tashi Ammie. Na huta sosai gaskiya, na ji jikina ya ɗan fara daɗi kaɗan."
Plate ɗinda ke hannunta miƙo mini tana faɗin.
"Ungo wannan ɗin, pepper soup ɗin en ciki ne, ya yi daɗi sosai. Ni ce na dafa miki da kai na."
Karɓa na yi bayan na ajiye Husain ɗin na yi amfani da Spoon ɗin na fara ci. Sai da na ci fiye da rabi sannan na miƙa mata ina faɗin.
"Ya yi daɗi kam,na gode sosai."
"To mi za a kawo miki?"
Girgiza kaina na yi na ce.
"Water only."
Bottle water ta miƙa min na sha sannan na ce.
"Abbu fa? Tun jiya da muka dawo ban ƙara jin ɗuriyarsa ba."
"Yana asibiti wurin aiki, daga can kuma zai wuce gidan Hajiya Asma'u sai gobe zai dawo nan."
"OK. To Ammie su Aunty Aysha sun ji kuwa? Naga ba wanda ya kirani. Wataƙila kuma sun kira ina bacci ko?"
Jikinta ne ya yi san yi jin na tambayi su Aunty Aysha. Ganin yanda ta yi wani iri ne yasa na ce.
"Ammie lafiya kuwa?"
Girgiza kai ta yi a hankali ta ce.
"Daddynku ne Allah ya mishi rasuwa tun jiya..."
Runtse idanuwana na yi yayin da na ji wani abu ya daki ƙirjina na ce.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Daddy ya rasu Ammie?"
"Ya rasu Beenafah. Sai haƙuri, ki yi haƙuri. Allah ya gafarta mishi ya bashi aljanna maɗaukakiya."
Hawayena na share na ce.
"Amin Ammie. Da yaushe ne ya rasun?"
"Husaina cewa ta yi, koda ake masallacin Idi duk suna asibiti, amma likitocin basu tabbatar musu da rasuwarsa ba sai misalin sha biyu na rana."
"Allah sarki! Na tausaya musu, wallahy na tausayi musu, akwai raɗaɗi da zafi sosai Ammie a cikin rashin mahaifi. Ko ba baka rasa komai na rayuwa ba shi haifi na daban ne..."
Hawayenta ta share sannan ta samu wuri kusa dani ta zauna tana kallona still da wasu hawayen ta jinjina kanta ta ce.
" Rasa Mahaifi da zafi sosai,domin har abada ba za ka taɓa maye gurbinsa ba. Haka zalika Beenafah, rashin miji ma babbar nakasa ce a rayuwa. Wallahy har yanzu ina jin zafi da raɗaɗin rasa Dr. Bello a tare da ni. Kullum idan zan tuna sa sau dubu...to komai sabo yake dawo mini a rayuwa. Tsakanina da Dr. Basheer...tamkar Kaza ce mai 'ƴa'ƴa wacce ta yi musu rumfa a lokacin da ake tsananin keta ruwan sama. Bana jin soyayya...amma ina jin sa da girma da ƙima sosai a idanuna."
"Allah sarki! Allah shi ne mai yanda yaso. Baya barin wani don wani ya ji daɗi, idan muka yi haƙuri, Allah zai saka mana da mafificin alheri. Daman ai duniyar ba gidan zama ba ce. Inda su Abbie suka tafi, watarana muma duk can zamu nufa. Lokaci kawai muke jira. Allah ubangiji ya gafarta musu, mu kuma idan ta mu tazo yasa mu cika da kyau da imani."
"Ameen Beenafah."
Daga haka ta miƙe tana faɗin.
"Mijin ki ya zo tun ɗazu, idan kin shirya sai ki yi masa izinin shigowa."
Duk yanda nake jin cewa na ƙuntata, bayyanar da Ammie ta faɗamin sai da na murmusa har cikin zuciyata.