Ganin ido complete - Chapter 8
Ganin ido complete Chapter 8: Ganin ido complete Chapter 8. Nan na yi ta zuba ina faɗa mata duk yanda muka yi da mai gadin gidan da kuma bayanin da Aunty…
3,369 words
Nan na yi ta zuba ina faɗa mata duk yanda muka yi da mai gadin gidan da kuma bayanin da Aunty Labibar ta yi mini. Muna nan muna fira sai ga Bahrain ya shigo. Bayan ya gaishemu ya hau rarraba ido yana kallon kyakkyawar kular da ke gabanmu...
"Ka je ka ɗauko plate ka zo in zuba maka Bahrain."
Kyakkyawar Jallop rice ce wacce ta ji wake lafiyayye da koren ganyen da namomi a ciki. Rabonmu da irin wannan kyakkyawan haɗin tunda muka baro Sokoto.
Yanda Bahrain ke cin abinci hakan sai ya sanyani jin hawaye saboda yanda yake yaba daɗin abincin. A tare muka ci da Ammie, sauran da ta rage kuma na rufe masa idan ya dawo daga islamiyya da dare ya ƙarasa cinye saura.
Washe gari da wuri na tashi na nema mana abin kari muka ci Bahrain ya shirya ya wuce makaranta,ni kuma na yi shara da wanke-wanke na shirya na wuce.
Haka na ci gaba da aikina gidan Aunty Labiba. Idan na tafi sha ɗaya na safe kwana biyu bayan kwana biyu kuma in tafi ƙarfe tara na safe.
Yau ma, ina shiga na ci karo da su Adeel sun fito za su je islamiyya kasancewar Asabar ce.
Muhsin wanda shi ne babba cikin su gaba ɗaya da alama zai yi irin shekara sha biyar haka na ji yanata kiran.
"Ke.. Ke.. Ke bakya ji ne?"
"Aunty Beenafah."
Na jiyo muryar Adeel ya kira sunana.
Waigowa na yi na ce.
"Na'am Adeel, ya akayi?"
"Ba Adeel ke kiran ki ba nike kiran ki."
Cike da mamaki na dawo baya na ce.
"Ya akayi?"
Basket ɗin ƙanwar sa Tima ya nuna mini yana faɗin.
"Tea ya zube a basket ɗinta, ki amsa kije ki wanke mata ki gyara ki kawo."
Ba musu na amsa naje na cire kayan ciki a bakin famfon da ke harabar gidan na wanke sannan na ƙara ɗaure bakin bottle ɗin da kyau na saka a ciki na kawo musu suka shiga mota suka wuce.
Ina shiga na tarar da Aunty Labiba zaune a parlournta da kayan break fast a gaban ta da alama yanzu suka ƙarasa karyawa tare da su Adeel ɗin.
Duƙawa na yi na gaisheta kamar yanda na saba a duk lokacin da na tarar da ita gida, saboda tunda na fara aikin nan na kan share kwana biyar ko fiye ma da haka ban sanyata a ido na ba.
Bayan mun gaisa na miƙe da nufin tafiya wurin aikina sai na ji ta kira sunana.
"Beenafah."
Waigowa na yi na ce.
"Na'am Aunty Labiba..."
Please ki zo ki shigar da kayan nan kitchen, sannan dan Allah ina neman alfarma da ki ɗan wanke mini uniform ɗin su Adeel saboda Hajjo bata da lafiya, daman ita ke wanke musu uniform ta goge kasancewar bamu da mai wanki a gida sai dai idan kaya sun taru mu haɗa akai waje.
"Haba Aunty! Miye na neman alfarma. Kawai cewa zaki yi na yi."
Murmushin jindaɗi ta yi tare da jinjina kanta ta ce.
"Allah sarki, to na gode."
"Ki je ki fara karyawa tukun kafin ki fara."
Girgiza kaina na yi na ce.
"Na gode Aunty, amma na ƙoshi."
"Haba Beenafah! Miyasa kike yin haka? Hajjo ta sanar mini duk kika zo gidan nan ko ruwa bakya sha."
"To ai na ƙoshi ne Aunty."
Jinjina kai ta yi ta ce.
"Shikenan! Ta shi kije."
Kayan na kwashe na kai kitchen sannan na fito da kayan na wanke tas! Sannan na hau aikina kamar yanda na saba. Ina cikin yi sai ga Hajjo ta shigo ɗauke da sallama a bakinta. Kallonta na yi na ce.
"Sannu Aunty Hajjo."
"Yauwa Beenafah."
"Ashe ba kiji sarai ba? Allah ya baki lafiya."
"Amin Ya Allah, na gode sosai."
Bayan na gama aikina wuraren ƙarfe ɗaya da wani abu na ɗauko kayan da na wanke na shiga ɗakinda muke zama idan mun zo ni da Hajjo na shimfiɗa guga kamar yanda naga Hajjo tana yi.
Ɗakin Hajjo ta shigo ta kalleni ta ce.
"Ke dai Beenafah shikenan ba ruwan ki da kowa, kullum tamkar wata sabuwar baƙuwa haka kike rayuwa da mu."
Murnushi na yi ina girgiza kaina ce.
"Ba haka bane Aunty Hajjo."
"To yanzu ki ta so ki kaiwa driver abincin su Adeel in ji Aunty Labiba."
"To,yanzu kuwa, In Sha Allahu."
Hijabina na janyo daga inda na sagale na sanya sannan na fito naje kitchen ɗin na ɗauko babban basket wanda aka cika da abin Ci da Sha na kai bakin motar na ajiye wanda a dai-dai lokacin ne itama wata mata ta fito daga ɓangaren hagu ta ajiye basket guda biyu. Cike da nuna isa da ƙasaita ta kalleni ta ce.
"Ke kuma wace ce?"
Cikin ladabi na ɗan rusuna kaɗan na ce.
"Ina wuni?"
"Ba shi na tambaye ki ba, cewa na yi ke wace ce?"
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa*
*FREE-BOOK*
*PAGE 11*
"Ni ɗin mai aikin Aunty Labiba ce."
Taɓe baki kawai ta yi tare da ƙara yi mini wani kallon uku saura kwata sannan ta juya ta koma ciki.
Ina komawa na shiga na ci gaba da yin aikina wanda ban kambala ba sai misalin ƙarfe uku na rana.
Cikin sauri na kai kayan ɗakinsu na shirya cikin wardrobe ɗin su kamar yanda Hajjo ta nuna mini sannan na fito domin nasan Ammie na can na zuba idon ganina.
Ina fitowa daga kitchen muka yi kicibis da Aunty Labiba itama ta fito cikin shirin ta da alama fita za ta yi.
Murmushi na yi na ce.
"Sannu Aunty."
Murmushin itama ta mayar mini sannan ta ce.
"Yauwa Beenafah. Sai yanzu?"
"Eh Aunty."
"To yayi, ɗan jirani ina zuwa yanzu."
Ƙasan kujera na samu na zauna ina jiranta. Bata fi minti goma ba sai gata ta dawo ta miƙo mini kuɗi da wata leda tana faɗin.
"Yau kwana talatin cif da fara aikinki Beenafah. Na gode sosai."
Jimƙe kuɗin na yi a hannuna na hau yi mata godiya da cewa.
"Na gode sosai Aunty Labiba, Allah ya saka da alheri, Allah ya ƙara buɗi ya raya zuriya."
"Amin."
Kallon kuular da ke hannuna ta yi ta ce.
"Buɗe naga abincin da yake ciki Beenafah."
Ba musu na buɗe mata kular ta kalli abincin da ke ciki sannan ta danna wannan na'urar ta kira Hajjo wacce nan take sai gata ta iso wurin.
"Haba Hajjo! Wai miyasa wani lokacin kike abu kamar wata marar wayau? Yanzu dan Allah wannan abincin ko ke kaɗai aka sakawa shi ba za ki cinye ba har ki nemi ƙari?."
Ciki da girmamawa ta ce.
"Ki yi haƙuri Aunty Labiba.."
"Ina so ki canja mata wannan kular daga yau ki ɗauko babba wacce za ta ishe su dan Allah."
"Tau, In Sha Allahu."
Daga haka ta ɗauki abincin ta koma kitchen sai ga shi ta dawo da wata uwar kula wacce zamu iya ci sau biyu ma a rana.
Godiya na yi ta yi mata tamkar zan kifa har ta fi ce tabar parlourn sannan na waigo na kalli Aunty Hajjo na ce.
" Dan Allah Aunty Hajjo baki san wata hanya mai sauƙi ba wacce zan iya bi na koma gida? Wallahi na gaji da kashe kuɗinnan mashin ɗinnan, kullum fa ɗari huɗu."
"Wace Unguwa kuke ne?"
"Hayin Malam Ibrahim."
Dariya Hajjo ta yi tana faɗin.
"Kash! amma dai rashin sani ya fi dare duhu. Ga abu baki da hanci amma kike zaman kashe ɗari huɗu kullum.."
"To ai ban sani ba Aunty Hajjo."
"OK to, daga nan zuwa inda kuke ba wani nisa sosai ko da ƙafa kina iya zuwa kullum ki koma. Idan kin fita ki fara tambayar mai gadi sai ya ɗoraki a hanya daga nan sai ki ci gaba da tambaya."
"To ya yi Aunty Hajjo na gode sosai, Allah ya baki lafiya."
"Amin."
Ina fitowa na tarar har Aunty Labiba ta ja motarta ta fita. Mai gadin na tambaya kamar yanda Aunty Hajjo ta ce ya kuwa nuna mini hanya ina tafe ina tambaya kamar wasa sai wani titin da daga na miƙe sai corner gidanmu.
***
Hatlab Premium Gelato,Nile Outlet. Nile University Campus, F. C. T. Abuja, Nigeria.
Husaina ce zaune ta tasa Daddy a gaba tana ta rusa kuka tsawon lokaci ta kasa ce furta masa komai.
Shi kuma Daddy ganin kukan na ta ba mai ƙarewa ba ne yasa ya kalle ta cikin nuna damuwa ya ce.
"Husaina ni fa ban gane wannan abun ba? Kin turo mini text message kince na zo a cikin sirri ba tare da kowa ya sani ba kina da muhimmiyar magana, yanzu kuma na zo tsawon lokaci kin zauna kina ɓata mini lokaci kuma kina ɓatawa kan ki. Ba ku da lectures ne?"
A hankali ta share hawayen ta da gefen veil ɗinta ta ce.
" Muna da lectures Daddy, amma sai dai kuma; wannan maganar ta fiye mini lectures ɗinda suke gabana a yanzu..."
Ƙara gyara zamansa ya yi yana mai ƙure kallonsa gareta ya ce.
" To, ina jinki Husaina."
"Daddy, har yau dai maganata akan Aunty Aysha ne, na san cewa ban isa na tunkari Mummy da wannan maganar ba, sannan idan ta ji cewa na yi wannan maganar da kai na san tabbas za ta iya ɗaukar kowane irin mataki a kaina...Daddy! Kai kaɗai ne wanda yake da hurumin tsayawa ya yi mata magana kuma ta saurareka...Dan Allah ka gaya mata gaskiya akan Aunty Aysha, abin da takeyi sam ba dai-dai ba ne. Ina jin ciwo sosai ace muna duniya ɗaya amma ace bama iya magana ko kuma ganawa da juna...Daddy ka tuna fa kamar yanda kuke da haƙƙinmu muma haka muna da haƙƙi a kanku..."
Wani kallon ya yi mini sannan ya katse ni da cewar.
" To amma idan shi Ɗan ya yi ƙoƙarin take haƙƙin iyayen nasa ya nuna musu ba su isa da shi ba fa... "
Faɗowa ta yi akan ƙafafunsa tana mai ƙara sautin kukanta sosai ta ce.
" Daddy duk munji! Duk abin da Mummyn ta ce Aunty Aysha taji kuma ta amsa laifinta kuma tana mai tuba da neman gafarar ta Daddy. Dan Allah ka yi magana da Mummy dan Allah ta janye kalamanta hakanan...Daddy ko jiya sai da na kira Alhaji Baba amma ya ce mini babu ruwansa tunda Mummy ta ƙi ta saurare sa. Daddy Aunty Aysha tana cikin damuwa dan Allah Daddy ka yi wa Mummy magana dan Allah...."
Ta ƙarashe maganar ta na mai sake rushe masa da kuka.
Ɗagota ya yi a hankali ta zauna akan kujerar da take zaune akai ya ce.
" In sha Allahu zan yi mata magana... "
" Daddy ka yi mini alƙawarin shawo kanta wannan karon dan Allah.. "
" In sha Allahu na yi alƙawari, zan yi iya yina. Ina Hassana? Ya aka yi kika zo nan ba tare da ta sani ba?"
"Daman kafin mu shiga lecture ɗinne na yi maka text. Yanzu kuma ana cikin karatun na ɗauki excuse na fito."
Miƙewa ya yi yana faɗin.
"To ta shi ki koma, kuma ki mayarda hankali kinji ko. In Sha Allah zan yi mata magana."
"To Daddy na gode sosai, Allah ya taimaka ya ɗoramu akanta."
"Amin. Bye-Bye."
Kafin ta ƙarasa zuwa lecture hall ɗin ta ciro wayarta ta kira Aunty Ayshar, tana ɗagawa cikin rarrashi ta ce.
"Aunty ki kwantar da hankalinki, munyi magana da Daddy In Sha Allahu zai yi mata magana..."
Cike da ɗacin rai Ayshar ta ce.
"Hussy haka Daddy ke cewa kullum zai yi mata magana kuma ba ya yi. Kullum sai Ahlan ya kira shi amma har yau ba wata magana. Ko ɗazu ba jimawa na kira ta yafi sau ashirin ba ta ɗaga ba..."
"Ki yi haƙuri Aunty Aysha, In Sha Allah wannan karon za a da ce...."
Muryar Hassana ta tsinta a bayanta tana faɗin.
"Ohh! Wato munafurcin da kika laɓe kina yi kenan..."
Da sauri ta tsinke kiran kada ma Aunty Ayshar ta jiyo abin ya ƙara girgiza mata zuciya.
Juyawa ta yi tare da yi mata wani kallo ta ce.
"Ni da Yayata Uwa ɗaya Uba ɗaya miye abin munafurci don na yi magana da ita?"
"Munafurci ne mana, kuma kin bijire wa umarnin mahaifiyar ki tun da ta ce kada ki yi magana da ita. Yanzu ki gayamin da Uwar da ta haife da Yayarki wacce ce ta fi matsayi?"
Girgiza kai Husaina ta yi, hawaye na bin kuncinta masu tsananin ɗaci da raɗaɗi ta ce.
" Uhm! Sau dubu idan kika yi wani abin Hassana na kan mutu da mamaki yayin da wani gefe na zuciyata ke cika da tambayoyin wai ke ce kuwa muka kwanta a ciki ɗaya tare da juna ko kuwa musanyaki aka yi? Hassana kin san girman zumunci kuwa? Kin san miye alaƙar jini take nufi kuwa? 'ƴar uwarki! Yayarki uwa ɗaya uba ɗaya tana cikin baƙin ciki da damuwa amma ke ko a jikin ki...Hassana yau fa gareka gobe ga ɗan uwanka..."
Saurin ɗaga mata hannu tayi tana wani mere baki ta ce.
" Dan Allah ya isa haka! Ni umarnin Uwata nake bi ba komai ba, idan ke baki ɗauke ta a bakin komai ba to ni tana da muhimmanci a gare ni....kuma wallahi ki sani! Wannan maganar kamar a kunenta."
Wasu sabbin hawaye ne suka sake wanke mata fuska, cike da jin wani sabon ƙuncin ta ce.
" Matuƙar hakan zai ba ki farin ciki Hassana, to idan kika koma gida yau dan Allah ki ce Mummy ta saka wuƙar sarki ta yankeni."
Daga haka ta bangeta ta wuce Hall ɗin ta bar Hassanar da cizon yatsa.
****
Ina shiga gida na tarar da Ammie da Maman Fakiha suna zaune suna fira. Maman Fakiha maƙociyarmu ce wacce gidansu ke kallon gidanmu a yanzu, mutuniyar kirki ce ita da Mijinta da yaranta su Huɗu. Yaya Jafaru, Yaya Hamza, sai Fakiha wadda a cikin su ita ce kamar muke sa'a ɗaya duk da dai firar shekaru bata taɓa shiga tsakaninmu ba. Sai ƙaramar ƙanwarta Farisa. Suma dai suna da matsakaicin ƙarfin su gwargwado yanda Ubangiji ya tsara musu. Tun da muka zo unguwar ita ce matar da ta fara shigowa gidanmu sannan daga baya wa su daga cikin maƙota suka shishshigo, shikenan suka ci gaba da mutunci da Ammie.
Gaishe su na yi suka amsa sannan na sa kai na shige ɗaki na ajiye kayan da na ɗauko na fito na tafi bayi na yo wanka na fito. Ina kambala shiryawa na tayar da sallar Asr saboda lokaci ya riga ya yi. Bayan na kambala ina zaune ina Addu'a Ammie ta shigo ta yi sallar itama sannan na janyo ledar da kuɗin na ajiye a gabanta na ce.
"Na kambala aikina zan fito ta tsayar dani ta shiga ta ɗauko wannan da kuɗi ta bani ta ce yau kwana talatin cif da fara aikina."
Jinjina kai ta yi ta ce.
"Allah sarki! Wato ba ta manta ba, ba kamar wasu da sai an yi ta tuna musu ba. Nawa ne ta baki?"
"Wallahi ban sani ba, kin san tun farko ba muyi magana ba, yau kuma tana bani na amso na fito."
"To ɗauka ki duba mana."
Hannu na miƙa na ɗauko na ƙirga su. Dubu talatin ne cif.
Kallon Ammie na yi cike da mamaki wadda itama ni ɗin take kallo na ce.
"Ammie! Duba ki gani har dubu talatin."
Cikin jindaɗi Ammie ta ce.
"Alhamdulillah! Ta kyauta kam, mun gode Allah ya saka mata da mafificin alheri...."
"Wannan ledar kuma duba ki gani, sabulun wanki ne a ciki,..." Ina ƙara leƙa ledar da kyau na ce "Da manyan Omo, da sabulan wanka da man shafawa da turare...Kai gaskiya mun gode Ammie. Shikenan ta ɗauke mana nauyin waɗannan a wannan karon...sannan duba ki gani Ammie, kular da tace Aunty Hajjo ta canza, daga yau tace nan za'a dawo zuba mana abinci. Gaskiya matar nan tana da kirki."
Jinjina kai ta yi sannan ta ce.
" Gaskiya na ji daɗi kuma mungode sosai. Mutanen kirki suna nan a inda suke har abada ba a rasa na kirki haka zalika ba a rasa na banza. Amma ina ƙara Jan hankalinki da ki kula ki tsaya matsayinki ki kuma riƙe amana."
"In sha Allahu Ammie zan kula. Kinga jibi akwai zuwa asibiti, dole zan yi mata bayani ta ɗaga mini ƙafa."
"A'a,Ba sai kin faɗa mata ba, munyi magana da Maman Fakiha ita za ta rakani..."
Da sauri na girgiza kaina na ce.
"A'a Ammie, gaskiya ban yarda kowa yaje dake ba ni zan je da kaina..."
"Beenafah..."
Hannayenta na riƙe da sauri nima na ce.
"Ammie! Kece komai tamu ni da Bahrain,ban san komai ba idan ke ba, lafiyarki da kwanciyar hankalinki ya shafe komai. Ban amince da kowa ba, ni dake zamu tafi kamar yanda muka saba."
"To shikenan. Allah ya kai mu."
"Amin Ammie."
Miƙewa tayi ta cire hijabinda tayi salla tana ninkewa ta ce mini.
"Amma dai abincin nan ya yi yawa. Ko gobe yakai ba zamu iya cinyewa ba. Ki ɗiba kikai wa su Farisa."
"Tau Ammie, bari na wanke uniform ɗin Bahrain na gobe tukun."
****
Washe gari ina zuwa ban tarar da kowa a parlour, na wuce na nufi kitchen domin na ajiye Kula sai na tarar da Aunty Labiba tare da Adeel da Hanan suna zaune ita kuma tana haɗa musu breakfast.
"Beenafah! Kin zo?"
"Eh Aunty Labiba ina kwana."
"Lafiya ƙalau, ya maman ku?"
"Lafiya ƙalau, ta ce a gaisheki ta gode sosai."
"Aunty Beenafah ina kwana."
Murmushi na yi na kalle shi na ce.
"Adeel ka tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau."
Aunty Labiba na juya dankali a frying pan ta ce.
"Yau Hajjo ba lafiya, sai misalin takwas ta kirani ta ce mini ba za ta iya fitowa ba jikinta ya matsa. Shiyasa muka yi latti."
"Allah sarki! Allah ya bata lafiya. Da me zan tayaki to a samu muyi sauri?"
"To zo ki soya dankalin ni kuma sai na haɗa Tea ɗin in dafa musu ko spaghetti ce su yi su tafi. Yau kam kuda Islamiyyar nan ƙila sai sha ɗaya. Muna nan mun duƙufa da aikin kwatsam! Muka jiyo gungunin Adeel murya kamar zai fashe da kuka yana faɗin.
"Ni fa Mummy banyi Assignment ɗina ba kuma wallahi idan naje kinsan halin Ustaz dukana zai yi..."
Juyowa Aunty Labiba ta yi tare da sage hannunta tana mishi wani kallo ta ce.
"To yanzu, wannan aikin zan fasa na maka Assignment ko kuma breakfast ɗin zan ci gaba da haɗawa? Ka san kana da home work jiya amma ka zauna kana game har dare? Kuma ina jin Babanku da ya shigo yana tambayarka ko kana da Assignment ka ce a'a..."
Hawaye ya fara hankalinsa a matuƙar tashe ya ce.
"Dan Allah Mummy ki yi haƙuri na manta ne, wallahi Ustaz dukana zai yi. Sai da na ɗauko zan yi amma na kasa yi aikin yana da wahala"
Banza ta yi masa ta juya ta ci gaba da aikinta. Ni kuma jin sa yana ta kuka da gaske yasa na waigo na kallesa na ce.
"Ina Home work ɗin yake?"
Kallona ya yi na ɗan lokaci kamar yadda naga itama Aunty Labibar tayi, sannan ya tashi daga ƙarshe yaje ya ɗauko. Still da ɗan shakku a muryasa ya shiga karanta mini tambayar.
"Cewa akayi in rubuta ma'anar Nun as-sakinah and Tanwin. Sai kuma in kawo rukunin kowanne, guda huɗu-huɗu da misalansu guda uku-uku...."
Murmushi na yi masa sannan na ce.
"Muje to na nuna maka ka yi."
Ba musu ya tashi na bi shi muka je can wani kewayayyen wuri dake cikin babban parlourn na su. Kan table reading ɗin su muka zauna wanda ni a yanda naga yana kallona kawai don bai da wata mafita ne amma da ba zai yarda na taɓa masa littafi ba...
" Aunty Beenafah kin tabbata kin iya?"
Jinjina kaina na yi na ce.
"In sha Allahu ba za ka ci zero gaba ɗaya ba. Ko ya ya ne na ɗan taimaka ai yafi ka tafi hakanan baka yi ba, ko ba haka ba?"
Da sauri ya jinjina kansa ya ce.
"Haka ne, na gode."
Muna farawa ba jimawa mukaji ana ta knocking a main door ɗin.
"Adeel ka je ka duba waye ne..."
Yana rubutun sauri-sauri bai ko ɗago ya kalleni ba ya ce.