Kenza eBookz

Ganin ido complete Novel - Chapter 12

Ganin ido complete Novel - Chapter 12

Ganin ido complete Novel Chapter 12: Ganin ido complete Novel Chapter 12. " Aikin banza, wato sai ma ka tsaya bata haƙuri da rarrashi ita ga 'ƴar gold kada…

3,324 words

" Aikin banza, wato sai ma ka tsaya bata haƙuri da rarrashi ita ga 'ƴar gold kada ranta ya ɓaci. "

Tsahirtawa ta yi da maganar da take ta kalli Su Muhsin ɗin ta ce.

"Ku je ku shiga motar ku tafi, ku cewa Hajiyar na ce ta ajiye kulolin zan aiko driver ya ɗauka."

Tana nan a tsaye har suka shige suka ɗai sannan ta juya tana wani ɗaɗɗaga shoulder tana feleƙe ta shige gida.

Leƙowa Daddyn na su ya yi ya ce.

"Adeel... Hanan! Ku zo mu tafi mana."

Kallon mummyn ta su Adeel ya yi ya ce.

"Mummy bana son Aunty Beenafah ta daina zuwa dan Allah ki bai wa Daddy haƙuri, wallahi ba abin da ta yi, Aunty Muhsina ce ta je ta faɗa mata Ƙaryar nan..."

Kallon shi ta yi tana wani murmushin ƙarfin hali ta ce.

"Kuje Adeel, ku cewa Hajiya ina gaisheta ina mata barka da shan ruwa sai na zo."

A hankali baƙin ta suka shiga zamewa suna komawa ciki yayin da kowa ke tofa albarkacin bakin sa.

A hankali ta tako inda nake durƙushe akan ƙafafuna ina ta aikin rusga kukan baƙin ciki ta ɗagoni tsaye tana kallon cikin Idona ta ce.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa*

*FREE-BOOK*

*PAGE 15*

"Beenafah! Ki yi haƙuri...Dan Allah ki yi haƙuri! Duk abin da ta faɗa wallahi ni sam ban yarda da ita ba, komai za ta ce nasan baki aikata ba. Ki yi haƙuri ki tafi. Allah ubangiji ya baki inda ya fiye miki nan alheri."

Jinjina kaina kawai na yi ba tare da na furta mata komai ba, domin ji na yi Bakina ya yi mini wani irin nauyi tamkar an saka mini takunkumi. A hankali na janyo hannun Bahrain yayin da naga wani irin duhu ya taso ya mamaye mini lemar idanuna.

Ban waiwayeta ba har muka fito kamar yanda itama ban ji ta kira sunana ba. Da ƙyar na iya ƙarasowa wajen gate ɗin na zube ƙasa warwas ina mai fasgewa da wani irin mugun kuka ina ihun faɗin. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Na shiga uku ni Beenafah.... Ni yau naga baƙar rana..Ina zan saka raina na ji sanyi? Ƙaddara miyasa haka? Miyasa zaki gifto a cikin rayuwarmu da muka sha matuƙar wahala kafin ginata....."

Na faɗa da ƙarfi ina mai saka hannayena na dafe kaina zuciyata tamkar za ta fashe tsabar yanda take wani irin tsananin bugawa tamkar za ta fasa ƙirjina ta fito.

Shi ma Bahrain kukan ya fashe da shi lokaci ɗaya yana mai faɗowa jikina hankalinsa a tashe ganin yan da na gigice ina kuka ya ce.

" Aunty Beena to mu yanzu ya zamu yi?"

Rungumeshi na yi ina girgiza kai na na ce.

"Ban san yanda zamu yi ba Bahrain!!! Ban sani ba! Sai da muka sakankance da cewa baƙin cikinmu da damuwarmu sun riga sun tafi...ashe akwai sauran Rina a kaba... Yau gashi rana tsaka ruwa ya ƙarewa ɗan Kada bai gama wanka ba...Bahrain gaba ɗaya mafarkina ya rushe...Mafarkina ya rushe Bahrain! wayyo Allah na! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."

Muryar mai gadi na ji a kaina wanda daman a gabansa akayi komai yana faɗin.

" Ki yi haƙuri Beenafah ki mayar da lamarinki a wurin Allah in sha Allahu zai miki magani. Wannan kukan da kike a nan bashi da amfani ki yi haƙuri ki tashi ki tafi gida kada ki tarawa kan ki jama'a."

"Aunty Beenafah ta shi mu koma gida wurin Ammie...Ki tashi mu tafi Aunty Beena...Ki yi haƙuri ki tashi mu tafi."

Miƙewa na yi ina mai bin umarnin Bahrain muka kama hanya wanda ikon Allah ne kawai zan ce ya kai ni gida.

Koda muka isa ƙofar gida su Ya Jafaru suna nan zazzaune akan babbar tabarma ƙofar gida suna ta bukin sallah wanda ni lokaci ɗaya tunanina ya juye na manta da wai yau ce ma ranar sallah.

Cikin tsabar ruɗewa Ya Jafaru ya taso ya tare mu yana faɗin.

"Kai Bahrain lafiya kuwa? Miye ya faru take kuka.... Tambayarka nake miye aka yiwa Beenafah take kuka??"

A gaskiya, naga hankalin Bahrain a wannan lokacin domin bai tsaya bai wa Ya Jafaru amsa a tsakiyar mutane ba kamar yanda ya nema wanda shi ma na san tsabar ruɗewa ce ganin yanda muketa kuka a tare. Yana ganin na shige gida shima ya biyo bayana. Ganin hakan yasa Ya Jafarun faɗowa cikin gidanmu shima hankalinsa a tashe.

Ganin yanda muka shigo ya sanya Ammie sakin butar da ke hannunta wacce ta ɗauka da nufin zagayawa banɗaki.

Hannayenta ta saka cikin tashin hankali ta dafe ƙirjinta ta ce.

"Subhanallahi! Beenafah lafiya? Lafiya ina tambayarki? Bahrain miye ya faru?"

"Ammie wai can gidan ne fa suka ce sun kori Aunty Beenafah, wai taje kada ta sake zuwa gidan har abada..."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Miye ya yi zafi haka? Miye kika aikata musu?"

"Wallahi ba abin da ta yi musu Ammie, wata masifaffiyar Mata ce ita da yaranta suka yi mata rashin mutunci kuma sai Babansu ya ce ya koreta, shi ne itama matar tace ta tafi."

Cikin wani irin taratsi Ya Jafaru ya ce.

"Wace Mata ce wannan? Wace Mata ce na ce Bahrain?"

Hannu Ammie ta ɗaga mishi ta ce.

"Ya isa Jafaru. wace Matar kake tambaya? idan ka ganta mi za ka yi mata? su da gidan su. Allah yasa hakan shi ne mafi alheri. Ka yi haƙuri dan Allah ka sanyaya ranka,wannan zafin zuciyar bai da wani amfani."

Zuciyar shi cike da ƙunci ya fice ba tare da ya sake furta uffan ba. Faɗuwa na yi dirshan zaman 'ƴan bori na sake dasa sabon kuka mai cike da tsananin raɗaɗi da ƙona zuciya.

Haka na share kwana uku ba tare da na yiwa kowa magana ba. Na shiga tashin hankalin da baki ma ba zai iya furta shi ba. Tsoro ne ya dunguzuma ya mamaye mini zuciyata. Tambayar kaina na fara 'Shin Idan rasa wannan madafar da mukayi ya sake mayar da Ammie ga turkenta mai caɓo fa? Sannan ina makomar Bahrain akan walimarsa da kuma ƙare makarantarsa? In fact sauran buƙatuwan rayuwar fa.....??'

"Beenafah!"

Ɗago rinannun idanuwana na yi na kalli Ammie wacce ke tsaye a kaina na amsa mata murya a dusashe. Itama cikin tausasawa ta ce.

"Haba Beenafah! Ki yi haƙuri mana. Allah zai yi mana mafita..."

Lokaci ɗaya na ji wasu sabbin hawaye sun shiga zarya daga kwarmin idanuwana na ce.

"Ammie... Komai ya dawo mana sabo. Ta ya ya zan kwantar da hankalina Ammie? Rayuwa za ta yi mana wahalaaa... Za ta yi wahala Ammie. Bana so, ke ko Bahrain ku sake shan wahala makamancin wacce muka shawo a baya.."

Rungumoni ta yi tare da share guntun hawayenta ta ce.

"In sha Allahu ba za mu sake maimaita rayuwa makamanciyar wacce muka yo a baya ba. Allah yana sane damu, shi zai bamu wata mafitar kamar wacce ya bamu a baya, ki sani; ba dabararmu ba ce kuma ba wayonmu ba ne yasa muka fita cikin ƙanginda muka shiga a baya, ikon sa ne da amincewar sa kuma ko a yanzu In Sha Allahu zai bamu mafita..."

"Am..amma Ammie, akwai wahal.."

"Ya isa na ce miki. Kowa ya damu da halin da kike ciki har Jafaru ma ki duba yanda ya shiga damuwa. Ki yi haƙuri ki barwa Allah zaɓi."

Jinjina kaina na yi na ce.

"Shikenan Ammie na daina... Allah ya zaɓa mana mafi alherin."

"Amin. Ta shi kije ga abinci can ki ci, kiyi haƙuri da rayuwa."

****

Aunty Labiba kuwa, tun da Barrister ya kori Beenafah ta kasa samun sukuni. Ko fita wannan; tun da taje gidan iyayenta washe garin Sallah ta dawo ba ta sake fita ko ƙofar gida ba. Beenafah ta tsaya mata a rai, haka ma su Adeel tsawon lokaci babu wata ranar da za ta zo ta wuce ba tare da sun yi maganar ta ba har aka gama bikin sallah yara suka koma makaranta itama ta koma bakin aikinta.

Yau ma, misalin ƙarfe biyar na yamma, ta na zaune a parlournta na ciki cike da gajiya wanda dawowar ta kenan daga aiki, ta zauna shiru tana tunani sai ga Hajjo ta yi nocking ta shaida mata cewar ta yi baƙuwa. Sai da ta jima a tsaye sannan ta amsa mata da cewa tana fitowa yanzu.

Tana shigowa suka yi ido biyu da babbar ƙawarta Jamila Hadi. Murmushi ta sakar mata tare da kama kujera ɗaya ta zauna suna fuskantar juna suka gaisa. Hajjo ta saka ta kawo mata ruwa da abin taɓawa daga baya ta kalle ta ta ce.

"Jamila ina cikin damuwa..damuwa sosai."

A hankali Jamilar ta dire glass cup ɗinda ke hannunta ta ce.

"Subhanallah! Miye matsalar Labiba?"

"Hmm! Jamila 'ƴar aiki ce dani, yarinya mai matuƙar kirki da ladabi, ga shi ta iya aiki sosai tana matuƙar yi mini biyayya da son Yarana, wallahi ko su Adeel ba ki ga yanda suke ƙaunarta ba. Haka kawai Hajiya Marwa da Yaranta suka kafa mata ƙahon zuƙa sai da Barrister ya koreta hankalin su ya kwanta, kora ta wulaƙanci Jamila. Na ji kunyar yarinyar nan fiye da yadda kike za to, saboda irin yanda ya yi humiliating na ta gaban kowa ya kore ta. Ɗan Adam fa daraja ce da shi..."

"Kash! Ko wannan yarinyar da na taɓa tararwa tana wanki?"

Jinjina kanta ta yi ta ce.

"Ita fa! Abin da yafi bani baƙin ciki shi ne; ban san duk irin abin da suka ta yi mata ba sai daga baya bayan Barrister ya koreta ne Adeel yake gaya mini ma wasu abubuwan, to tunda har akayi hakan kinga ban san ma sauran ba. Jamila! Tun da nake da Hajiya Marwa tsawon shekaru sha shida kenan ban taɓa damuwa da ita ba, ban taɓa kawota a kaina ba, sau biyu ina ga a rayuwata na taɓa yin sa'insa da ita ko shi ganin na yi tana nema ta takani domin ba ta da kirki ko kaɗan. Daman target ɗina shi ne in samu wata center in saka ta class ɗin koyon girke-girke kamar yanda na yi wa Hajjo ta koya ta iya,in yaso daga zaran Hajjo ta yi aure sai ta maye gurbin ta kawai tun da aurenta ya kusa. Na ji ciwon wannan abin da ya faru ba kaɗan ba, Marayu ne fa! Daga ita sai ƙaninta sai Mamanta suke rayuwa, kuma duk wata tana neman izinina akan kai Maman ta ta asibiti da alama ba ishashshiyar lafiya ce da ita ba. Jamila ta ya zan iya taimaka mata ba, ina girmama umarnin Barrister don haka dole na haƙura da ita. Kaina ya kulle, ina buƙatar mafita."

Shiru Jamilar ta yi na ɗan lokaci tana nazari sannan daga ƙarshe ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta kalleta ta ce.

" To! Ni dai my advice here is that; tun da har kina so ki taimaka masu, to ki mayar da ita gidansu Hajiyarki..."

Ɗan waro ido Labibar tayi da alamun mamaki a fuskarta amma ba ta yi magana ba, hakan yasa Jamilar ta jinjina kai cike da ƙwarin gwiwa ta ce.

"Yeah! Since you wanted to help, Kawai ki mayar da ita can taci gaba da aiki ƙarƙashin Hajiyarki, kinga daga can za ki riƙa jin labarinta, wane hali take ciki, sannan ma duk lokacin da kika son ganin ta za ki iya zuwa...."

Cikin nuna tsantsar farin ciki ta ce.

" Allah ubangiji ya saka miki da alheri Jamila. Na gode sosai Allah ya bar mana zumuncinmu amin. Ni wallahi kwata-kwata ban kawo wannan a kaina ba, na share tsawon watanni sai shan wahala nake, ta neman mafita."

"Amin amin yah Allahu. Kin ga shikenan komai ya wuce, sannan Allah zai baki lada na niyyarki ta alheri a gare su."

"Haka za'a yi Jamila, bari na kira Hajjo tun yanzu ma na ji ko tasan gidan na su...."

Wani ɗan ƙaramin abu ta ɗauko mai kama da remote ɗin AC ta danna, Hajjo dake kitchen tana hada-hadar haɗa girkin dare kawai ta ji na'urar ta yi ƙara alama kenan uwar gijiyarta na nemanta. Ɗauraye hannayenta ta yi ta zo ta yi sallama ta shiga.

Kallonta Labiba ta yi ta ce.

"Hajjo ko kin san gidan su Beenafah?"

"Wallahi ban san gidan su ba Aunty, amma dai kwanakin baya ta kirani bayan Magrib da wata number muka gaisa da ita, bayan mun gaisa na tambayeta ko Layinta ne sai ta ce mini a'a, wayar Yayanta ce ta kira ni ta tambeyani ya su Adeel...."

"Kin yi saving numbern Hajjo?"

Girgiza kanta ta yi ta ce.

"A'a"

Cikin ɗan ɗaga murya ta ce.

"To don me yasa ba ki yi saving ba?..."

"Calm down mana Labiba...tun da har ta kira ta ai ba'a rasa numbern a call log ɗinta indai ba ta goge ba."

Jinjina kai Labibar ta yi sannan ta ce.

"Ɗauko wayar ki duba mini lambar."

Cikin zafin nama ta miƙe taje ta ɗauko wayar ta zo gaban su ta shiga neman lambar, sai da ta kira kusan number biyu waɗanda ba su da suna sannan ta kira ta uku ta da ce bayan ta tambaye shi cewa dan Allah ko shi ne Yayan Beenafah.

Karɓar wayar Aunty Labiba ta yi bayan ta yi mishi sallama ta ce.

"Sunana Hajiya Labiba, dan Allah ina so ka faɗawa Beenafah cewa; ta sanar da mamanta gobe ta nemi izininta ta zo ta haɗu dani kan corner ta shigowa Layin mu idan an fito daga babban titi misalin sha biyu na rana."

Jinjina kai ya yi tamkar yana a gabanta ya ce.

"In Sha Allahu za a sanar musu."

****

Tun da Daddynsu Hanan ya koreni daga neman halal ɗina duniyata ta ƙuntata. Farin cikin Ammie da Bahrain ya fiye mini komai a duniyar nan domin su ka ɗai ne ahlin da nake da su bayan su ban san kowa ba. Idan rayuwarsu ta gyaru tabbas ta wa ce ta gyaru, idan kuma ta lalace nima rayuwata ta lalace. Na sha baƙar wahala, tun ban gama sanin kaina ba na fara fuskantar wahala da ƙuncin rayuwa wanda ta kai ta kawo sai na yi share-share da goge-goge Mummy za ta bani abinci wanda shi zan kaiwa Ammie da Bahrain da kuma ni kaina, a hakan wani lokacin ko da zan koma ta jiwa kanta ciwo wani zubin har Bahrain ma, haka zan yi ta kokawa da ita wanda har ni kaina bata bari ba. Ba bu mai ceton mu babu matallafi, tunda Mahaifinmu ya mutu shikenan kowa ya juya mana baya, wanda ashe duk soyayyar da kowa yake nuna mana duk ta GANIN IDON mahaifinmu ce.....mts! Bana so ko kaɗan ina tuna bayana domin ji nake tamkar na haɗiye zuciyata na mutu wanda ko maƙiyina bana fata ya yi irin rayuwar da na yi a baya. A yanzu ma 'I'm scared! I'm scared kada abin da ya faru ya sake faruwa. Duk da dai yanzu da sauƙi domin bama ƙarƙashin mulkin kowa sai dai! Wahalar rayuwa ce za ta dawo mana sabuwa. Ni ba namiji ba, ta ina zan fara? Dole na nemi hanyar ci gaba da kulawa da su.....da wannan mafarkin na ji zuciyata ta ƙarfafa tun daga ranar da na haƙura da tunanin komawa gidan Aunty Labiba har zuwa yau da muka rasa madafa.

Kuɗin da muka shiga tarawa domin hidimomin Bahrain dole a hankali muka shiga zaro su da kaɗan-kaɗan muna cin abinci da su da sauran 'ƴan buƙatocin rayuwa.

Duk irin burin da muka ci akan Walimar Bahrain haka ya tashi a banza domin ba wani abun kirki muka taɓuka ba, sai dai kuma! Ina matuƙar alfahari domin ya samu ya sauke alƙur'ani mai girma cike da ingantaccen karatu wanda ya samu kula yanda ya kamata, Alhamdulillah!

Zancen graduation ne dai muka jingine muka ce su barshi zuwa next year mu gani, daman ganin ƙwazonsa ne yasa malaman suka ga cancantarsa akan ya kamata ya zana jarabawar daga primary five amma tunda hakan bai samu ba sai muka ce a barshi ya yi primary six, in sha Allah kafin lokacin muna fatan Allah ya yalwata mana.

Yaya Jafaru shi ne ya tsaya mana akan wasu abubuwan duk da cewa shima ba wata sana'a ce da shi ba ta dindindin domin ɗinke ne kawai yake yi kuma ɗinkin idan ba lokacin Sallah ba sai a fi sati ɗaya ba'a kawo masa kala ɗaya ba. Sai aikin ƙarfin da yake fita idan ya samu aikin siminti da fenti. Amma a haka yake ƙuƙutawa idan ya tarar ba mu ci abinci ba ya samu ya sama mana wani abun, Yaya Hamza ma haka. Sai dai yau da gobe bata bar komai ba. Haka muke rayuwa ba tare da na sare ba, kullum cikin bincikar Maman Fakiha nake idan akwai wani aikin da zan yi don Allah ta sanar mini idan an samu. Wanka kau ma duk an so mana take muna yi domin akwai rijiya a gidan namu kuma tana da ruwa ko da yaushe. Da wuri nake tashin Bahrain ya cika mini manyan robobin aiki kafin ya fita makaranta, idan mun kambala aiki sai mu wanke ni da Ammie, wanda ba laifi, don dubi biyu, dubu ɗaya da ɗari biyar, Ɗari bakwai, duk muna samu.

A haka kuma Maman Fakiha ta samo mini gidan wata Mata wacce kullum aikin kawai shi ne na riƙa zuwa kullum safiya ina yi mata wanke-wanken kwanoni shika ɗai ne aikin. Wai almajirinta baya nan ita kuma ta tsani wanke-wanken kwanuka a rayuwa shiyasa kawai ta ce a nemo mata mai yi duk wata dubu biyu. Kuma kwanukan, ba wani yawa sosai shiyasa da naje ba jimawa nake kammalawa na koma gida.

Hmm! Mutane a duniya kala-kala ne wanda ni dai a duniyata banda kamar Aunty Labiba, kullum kwanan duniya na tuna da ita sai hawayen kewarta sun wanke mini fuskata. Ita wannan sabuwar matar ko da zanje kayan suna nan ta riga ta fito da su waje, iyaka na wanke na bar mata a nan idan ta fito ta shigar da kayanta. A wurin wanke-wanken idan na tarar da abinci na juye idan kuma ban tarar ba na kashe ƙanzo idan akwai in naje gida na shanya a rana. A wannan aikin na yi wata biyu ina yin sa a yanxu na shigo na uku. Mai ƙarami shi ke da babba watarana, dubu biyun nan idan ana tarawa a hankali watarana za ta zamo goma idan an yi haƙuri.

Kayayyakin ƙulle-ƙulle da muke siyarwa ma kullum idan su Ya Jafaru sun fito majalisa ba kunya haka nake fitowa na ajiye gaban ƙofarmu in kira sunan Ya Jafaru ko Ya Hamza in ce su duba mini, da wannan ne muka ƙara samun customer's ɗinmu suka ninku masu shigowa saye har cikin gida.

Tsarin rayuwata da ta Fakiha sun yi hannun riga saboda dalilai da dama. Na farko dai ita ɗin tana da Ya Jafaru, tana da Ya Hamza, tana da Mama tana kuma da Baba dama sauran en uwa, sannan dukkan su ɗauke suke da nauyinta shiyasa duk da su ɗin ba wasu masu ƙarfi ba ne ta fini nesa ba kusa ba, sannan ga ta tana zuwa makaranta both Islamiyya da boko ni kuma ko ɗaya ba na yi, tana da ƙawaye kala-kala wanda ni daga Ammie sai Bahrain sai Ya Ashiru da na rasa da kuma yanzu yayyunta da suka zamo yayyuna, bayan waɗan nan mutanen ba ni da wasu da nake wata hulɗa da su. Duk ranar da bata zuwa makaranta to da yamma za ta fito ta soya awara wanda kuɗin na ta ne mallakinta ne ba na wani ba. Daga lokacin da ta yi wasu baƙin abokan ta da suka zo ta kirani gidan su da sunan mu gaisa suka dinga faɗin wai kalata ba ta aikatau ba ce yasa na ja layi tsakanina da ita. Abubuwa da dama suka saka na ji cewa ita ɗin ba ta dace dani ba. Hakan yasa na ja tungata wanda tun bata fahimceni ba har ta zo ta fahimta daga baya itama ta yi baya-baya da ni.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull