Ganin ido complete Novel - Chapter 18
Ganin ido complete Novel Chapter 18: Ganin ido complete Novel Chapter 18. Yau, ta kasance Asabar ce wanda kowa yake gida domin hutawa kamar yanda dokar…
3,374 words
Yau, ta kasance Asabar ce wanda kowa yake gida domin hutawa kamar yanda dokar ƙasa ta tanada. Tun da suka wayi gari Mummy take kai kawo ita da 'ƴan aikin gidan domin shirye-shiryen manyan baƙinsu wato Ameer da Ammar waɗanda za su auri su Hassy idan Allah yasa sun samu fahimtar juna kamar yanda Mummy ta ci buri.
Daddy ne ya zo mata da zancen,amma kuma yanzu, tayi uwa ta yi makarɓiya domin ta fi shi son abun wanda har yake matuƙar bai wa su Hassana mamaki.
An gyara babban parlourn baƙin su, bayan an yi dafe-dafen abinci kuma sai da ta sake yin order aka kawo daga waje. Ko kafin ƙarfe huɗu na yamma ta cika, an gama shirya komai da komai.
Ɗinki na musamman ta kawo musu ta ce su saka wanda ya yi matuƙar yi musu kyau tamkar yau ne ranar auren.
Komai na su ya yi iri ɗaya hatta ƙamshin turarensu iri ɗaya. Misalin ƙarfe biyar suka fito zuwa parlourn wanda a nan suka tarar da su Ammar ɗin suna jiran su.
Suna shigowa ɗaya daga ciki ya miƙe yana ta wani blushing ya kalli ɗan uwansa ya ce.
"Ka san dai yanda muka yi da kai? Saboda haka ka jira babba ya fara.."
Murmushi na zaunen ya yi masa tare da gyaɗa masa kansa ya ce.
"To na jira Yaya. Allah ya tabbatar mana da alheri."
Kallon su ya yi ya ce.
"Ni ne Ameer... Ina Ameera? Ina nufin ina Yaya Babba.."
Dariya Husaina ta yi tana nuna Hassana ta ce.
"Ga Ameerar a nan to..."
Washe baki ya yi yana gyaɗa kansa yace.
"Alhamdulillah! Zo ki zauna a kusa dani... Kema ƙanwata kije ga gefen Ammar can ki zauna.."
Yanzu kam na zaunen dariya yayi har ana ɗan jiyo sautinsa sannan ya ce.
"Wai kai dan Allah ko'ina sai ka nuna halinka na son girma?"
"Eh, ai ko'ina akwai babba, inda babu babba wurin banza ne."
Zaunawa suka yi kamar abin arziki suka gaggaisa da juna bayan sun gaisa Ammar dake gefen Husaina ya ce.
"Kamar yanda kika ji tun farko ɗan uwana, abokina kuma aminina ya faɗa, shi ne Hassan ni ne Husaini, wanda ake kiransa da Ameer ni kuma Ammar. Kasuwancinmu ɗaya, wurin aikinmu ɗaya, in fact Komai namu ɗaya ne hatta wurin kwananmu har yanzu ɗaya ne..."
Ɗan taɓe baki Hassana ta yi ta ce.
" Ni kuma abin bai wani burgeni ba, mutum biyu a duniya ɗaya, idan akace komai na su ya zama iri ɗaya abun zai yi wani iri. Ko kai baka lura da hakan ba?"
Jinjina kai Ameer ya yi yana kallonta ya ce.
" while! Daman ba lallai a haɗuwarka da mutum ta farat ɗaya ba kaji tsarinsa ya burgeka. Amma na san in sha Allah, with time za ki ji hakan ya yi miki."
"And don't mind her, Kawai itama tana wasa ne. Ita ce Hassana ni Husaina, kamar yanda kuke, muma haka muke. Komai namu iri ɗaya ake mana tun har yanzu..."
Jinjina kai ya yi ya ce.
"Allah ya tabbatar mana da alheri."
Nan dai suka yi ta tattaunawa wanda duk ƙarfin firar tsakanin su ne da Husaina yayin da Hassana ta kame kan kujera tana ta charting tamkar ba da ita ake zancen ba.
Mummy kuwa, ta jima a jikin windown ɗakinta tana aikin kallon masu ba su tsaron da suka zo da su wato bodyguards. Ga sunan sun kame a cikin kaki sun tsaya tamkar bishiyar kwa-kwa wanda ko giyar wake kake sha baka isa ka kawo musu wargi ba.
Tana cikin kallon su taji motsin shigowar su Hassana sun dawo. Waigowa ta yi cike da zumuɗi ta ce.
"Ya ya?"
Wani irin ɓata rai Hassana ta yi ta ce.
"Mummy ba haske.... Me I don't like the guy... Ni ina zan kai wannan munin na shi da mugun baƙi kamar gawayi, ga guntanci kamar batir, haba! Da me ace akwai bambanci tsakaninsa da ɗan uwansa da zan iya haƙuri hakanan mu juya, to amma duk su ne... Ni gaskiya ba kalar namijin da nake mafarki ba ne Mumm..."
Kafin ma ta ƙarasa rufe bakinta Mummy ta kai mata wata uwar jimƙa a hannu ta ja ta da ƙarfi zuwa jikin windown ta nuna mata da hannu ɗaya ta ce.
" Kalli nan!"
Ta nuna mata jerin gwanon jibga-jibgan motocin su cike da zafin rai ta ce.
" Waɗannan ake bautawa ba soyayya ba.... Wallahi tallahi idan kika ce za ki bijire mini Hassana zan yi matuƙar baki mamaki."
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 20*
Tun ina jin ɗar-ɗar idan ina aiki akan ko zan ƙara ganin sa har na zo na saki jikina domin ban sake ganin sa ba, ko Aunty Ziza karan kanta na daina ganin ta kwana biyu. Hakan yasa na saki jikina na manta da su.
Da Wata ya cika kuwa, dubu hamsin haka Haula ta damƙa mini a hannuna tare da kayayyaki, sannan ga shi duk bayan kwanaki sai sun bani dubu biyu dubu biyar haka su ce mini baƙi akayi suka raba kuɗi. Hakan yasa har yanzu ni na kasa bambancewa akan; shin su en siyasa ne ko kuma dai? Domin yawan mutanen da suke shigowa gidan har sun zarce misali, sai dai mafi yawansu ba kowa ke ƙarasowa har cikin gidan Hajiya ba sai hamshaƙai da mafi yawan dangin su masu zuwa.
Ba ni ba, hatta Ammie ta yi matuƙar jin daɗin wannan sabon albashi da muka samu wanda mun ɗauki manyan buruka mun ɗora akai muna ƙara hasaso gobe mai haske. Ga shi dai bama siyen ko allura a cikin kuɗin, abinci ma kullum na dawo sai an ɗibarwa su Fakiha sannan su Yaya Hamza ma yanzu har Ammie ta saba kullum sai ta aje musu, sabulun wanki, sabulun wanka, kamar dai lokacinda nake gidan Aunty Labiba, sannan a wannan karon na har da sababbin dogayen riguna masu sauƙi a ka ɗinka hardani wanda nawa sun fi na su yawa har da hijabai da undies ma su yawa suka ce mini wai Hajiya ta bayar a ɗinka mana wanda ba ni da abin cewa sai godiya, amma kam Aunty Labiba da Iyayenta sun yi mana abinda Allah kaɗai zai iya biyan su wanda ina musu fatan Aljanna maɗaukakiya.
A ranar da na kawo kuɗin ba ɓata lokaci muka yanke cewa daga zaran na rakata asibiti mun dawo ranar Monday zan je islamiyyar su Bahrain na yi register na ci gaba da zuwa. A yammacin ranar na je na siyo uniform na bai wa Ya Jafaru ya ɗinke mini.
A daren ranar da ƙyar na samu bacci ya yi nasarar ɗaukeni akan ɗokin zuwa makarantar da na yi shekaru ban je ba.
Babu babban abin da nake ƙara godewa Allah a kai face ci gaban da muka ƙara samu na ciwon Ammie, duk muka je asibiti sai mun samu kyakkyawan labarin cewa ciwon ta ya na ƙara sauƙaƙa, haka ma yanzu magani wanda muke siye duk wata bai fi na dubu bakwai ba. Lallai dukkan tsanani yana tare da sauƙi Alhamdulillah.
Bayan mun dawo daga asibitin ma ban wani ci abincin kirki ba saboda ɗoki, ƙarfe biyu da rabi na yi na rana muka bi hanya ni da Bahrain da Ya Jafaru wanda komai zan ce ba zai daina bibiyata ba. Ammie ma har cire kunya ta yi tai masa magana amma bai ji ba.
Bayan mun kusa isa makarantar na kalle shi na ce.
"To sai ka koma haka ko Ya Jafaru? Ko kuma har cikin makarantar za ka rakani?"
Murmushi ya yi mini tare da tallafe hannayensa akan ƙirjinsa ya ce.
"Dole dai a nan zan tsaya ko bana so Beenafah. Allah ubangiji yasa kin shiga a sa'a, Allah ya baki ilmi mai amfani da kuma tarin albarka. Allah yasa yan da nake rakaki duk inda za ki je da ƙafa watarana ya nuna mini na ɗaukoki a abun hawanmu muna tafe muna farin ciki..."
Ba tare da kawo komai a raina ba na ce.
" Ameeeennnn! Ya Jafaru, sai na dawo."
Nan ya tsaya yana ta ɗaga mini hannu har na shige cikin gate ɗin.
Ina zuwa na wuce office ɗin shugaban makarantar wanda daman na saba da shi ta dalilin Bahrain. Bincike suka mini kamar yanda dokar makarantar ta tanada, na yi iya abinda zan iya wanda dole wani abin na manta sa tunda na share tsawon lokaci rabona da makarantar domin ni ko ƙur'ani ban gama saukewa ba ko da na bar zuwa amma dai bai fi hizib bakwai ba da ya rage mini, hakan yasa bayan gama mini bincike suka jefa ni a aji uku.
Haka na ci gaba da tafiya, idan gari ya waye zanje na yi aikina zuwa ƙarfe biyu in dawo in wuce islamiyya tare da Bahrain. Komai ya dawo mini sabo tamkar a mafarki. Gidan su Hajiya ma na samu natsuwa da kwanciyar hankali sosai domin har na manta da wata matsala a gidan.
****
Royal Crest University of Arts and Management (RCUAM) Sydney, New South Wales, Australia.
Tun kwana uku da suka wuce Daddy ya shirya zuwan sa makarantar su Hafiz, yana sauka ƙasar direct ya wuce makarantar, department ɗinda Hafiz yake wanda ko Mummy bai sanarwa cewa zai zo ba, kawai dai ya faɗa mata cewa zai yi tafiya zuwa ƙasar waje amma bata san cewa makarantar Hafiz zai zo ba.
Yana isa ya tarar da wata Mata a reception suka fara musayar kalmomi da turanci, ya ce.
"Good morning ma'am. Ni ne Alhaji Mudassir Wazeer, mahaifin Hafiz Mudassir Wazeer, ɗalibin da ke karatu a wannan makarantar, na zo ne daga Nigeria."
Murmushi matar ta yi tare da jinjina kai da ɗan nuna alamun mamaki akan fuskarta ta ce.
" Oh! Gaskiya wannan tafiya ce mai nisa sir, sannu da zuwa, da fatan komai lafiya?"
Daddy ya ce.
"Not really. Na zo ne na musamman in ga academic officer ko kuma kowane lecturer daga department ɗin su, I need to confirm something personally."
Jinjina kanta ta yi tana mai ɗaga wayarta ta kira wani lecturer mai suna Mr. Collins. Bayan ta gama mi shi bayani direct tasa aka kai shi office ɗinsa dake can hawa na huɗu.
Bayan ya shiga sun gaisa ba ɓata lokaci ya zayyana masa buƙatarsa kamar yanda yayiwa receptionist ɗin sai Mr. Collins ɗin ya ce.
"Of course sir, Hafiz yana daga cikin manyan ɗalibanmu ma su hazaƙa da muke tutiya da su, he's very brilliant in class, active in presentations. Ko a last semester he got a GPA of 4.12. Gaskiya ba shi da wata matsala."
Cikin wani irin farin ciki Daddy ya ɗaga hannu sama ya ce.
" Alhamdulillah!, that's my boy."
Wata takarda Mr. Collins ɗin ya ɗauko ya buɗe sannan ya kira waya yana connecting computer ɗinda ke gabansa ya saka numbern Hafiz sai gashi hotonshi da bayanan shi sun bayyana har da result ɗin shi na tsawon shekara biyu, da kuma bayanan shekaru biyu da suka rage masa da zai kambala nan gaba. Sannan kuma ya faɗa masa cewa, ai sai dai ya fara wani course wanda shekara ɗaya ne da watanni sannan yanzu daga baya ya ɗora da wannan.
Da sauri Daddy ya miƙa masa hannu yana murmushi ya ce.
"Thank you so much Mr. Collins, ina matuƙar alfahari da ɗana, yanzu na tabbatar cewa ba kuɗin banza nake kashe masa ba. Daman rashin tura mini result ɗin ne ya ɗaga mini hankali tun farko."
Daga haka ya yi sallama da shi ya fito, Yana fitowa wajen Campus ɗin ya ɗaga waya ya kira Hafiz domin ya zo su gaisa amma kuma a lokacin shi Hafiz ɗin suna da shiga wata test. Bayan ya zauna zaman jiran shi ƙarshe kuma cikin rashin sa'a suka wuce wurin wani Debate a wata ƙasar, kuma sai nan da wasu kwana uku za su dawo.
Haka ya juyo ya dawo gida cike da alfahari ya cewa mummy.
"Makarantar su Hafiz na je."
Cikin nuna mamaki ta ce.
"Makarantar su Hafiz kuma Alhaji?"
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"ƙwarai, hankalina ne bai kwanta ba, shiyasa na shirya naje na bincika da kaina, kuma ki ji yaron nan Hajiya Zaliha, ashe yana can yana performing ni ne ban fahimce shi ba."
"Haba! Ni ma wallahi na yi mamaki ace wai duk irin basira da ƙoƙarin Hafiz kace wai kana zarginsa..."
"Eh, abun da yasa kika ga na ƙara ɗaukar zafi; Alhaji Mansur ya yi mini alƙawarin ba shi babban matsayi a kamfanin sa dake Lagos. Kinga ba zan yi sanya da hakan ba."
Cike da farin cikin jin wannan kalamin Mummy ta ce.
"Kaga daga ya samu wurin shikenan, ga kuma en biyu da za su auri 'ƴa' ƴan sa..."
"To ai shi ne Hajiya, amma kuma kin ce mini Hassana tana neman to botsare wa wannan maganar..."
Lokaci ɗaya annurin fuskarta ya ɓace ta wani girgiza kai ta ce.
"Ai wallahi tallahi! Bijirewa wannan maganar tamkar ta ɗauki hannuwanta ne ta ɗora su saman tukubar tsire mai tsananin tururi da zafi."
"Noo! Kar ki damu, munyi magana da ita kuma ta amince..."
"To wallahi ni dama an gaggauta yin auren nan kawai, in ya so can su iyarda karatun na su tun da haka abin ya zamo.."
Miƙewa ya yi yana faɗin.
"Ai tunda har ta amince ba wata damuwa, gwanda a bar su su ƙarasa karatun na su zai fi.... Bari na je, yau ni zan ɗauko Princess ɗina da kaina,na yi missing ɗin ta sosai kwana biyu. (Humaida)."
****
Ashiru kuwa, abu wasa-wasa tun su Umma na ɗaukar al'amarin kamar na wasa, kullum cikin yi masa faɗa suke suna ganin laifin sa har suka dawo rarrashi ganin kamar abin na nema ya zamo masa da cikas a cikin rayuwar sa.
Daga baya ma sai ya kamu da ciwo wanda sai da aka dawo da shi gida, ana ta magani. Ayya kullum kwanan duniya ta kasa yarda da cewa wai su Beenafah mutane ne, duk wanda ya zo duban Ashiru ce masa take gamo ya yi da Aljanu suka shafe sa. Shiyasa kullum cikin yi masa hayaƙi da turaren Aljanun suke, duk inda Ayya ta ji ana bada taimakon iska sai ta je ta karɓo masa, shi kuma duk abin nan ji yake kamar zai yi kuka idan suna faɗin wai da Aljanu ya yi gamo,wanda shi yasan Sam ba haka bane kawai dai ƙaddarar sa ce tazo a haka.
Da haka suka samu Allah ya taimake su ya warware, da rarrashi da komai ya koma Kano, daman kuma gashi Yayan nasa ya buɗe masa nasa shagon wata bakwai da suka wuce domin yana da farin jinin kasuwa da kuma basirar iya mu'amala da mutane wanda tunda ya koma bai dawo ba sai yanzu da ya rage saura kwana biyar auren ƙanwar sa da take bin sa Zulfa'u.
Yana shigowa gidan ya tarar duk 'ƴan uwansu da danginsa sun taru ana ta hada-hada.
Kallon su wata abokiyar wasar sa ta yi tana dariya ta ce.
"Yayan Aljana an samu isowa?"
Wata uwar harara ya maka mata tare da buga uban tsaki ya ce.
"Bana son rainin wayau Sabila..."
Ayya dake zaune bisa ƙofa tana duba tabarmi da kayan tarkacenda su Fa'iza suka siyo daga kasuwa ta kalle shi ta ce.
"To ai ba ƙarya kika yi ba Sabila ƙyale shi, gaskiya ce baya so...Wallahi idan kika ga yarinyar nan Sabila za ki ce ita ce ta halicci kanta, saboda tsabar kyau, ko gashin kanta kaɗai abun tuhuma ne wanda hatta Nufaisa sai da ta kasa haƙuri duk yarintarta sai da abin ya bata mamaki har yasa ta tambayeta cewa duk gashin ta ne..."
Fa'iza dake tsaye gefen Ayya ta ce.
" Ki ji fa Ayya.. Wai bata taɓa ganin iyali mai yawa irin namu b... "
Da mugun ɓacin rai ya ɗaga hannu domin kifa mata mari sai dai kuma cikin rashin sa'a ya kuskure. Ai kuwa, da gudu ta runtuma ɗakin umma ba shiri tana haki.
Juyawa ya yi ransa a zafafe ba tare da ya gama gaisawa da mutane ba ya koma ɗakinsa ya yi kwanciyar sa.
Kallon Sabila Ayya tayi wacce tuni ta cika ta batse, cikin rarrashi ta ce.
"Sabila... Ashiru yana da wata irin tsinanniyar zuciya, ki daina yi masa zancen yarinyar nan indai kina so a samu a shawo kansa a kanki. Domin mu idan son samunmu ne ma zuwa wata kaka mai zuwa kawai ayi a huta ku wuce can tare da shi, ke kuma sai kinsan yanda za'a yi da rarrashi da komai kisa ya manta yarinyar. Wannan bala'i da mi ya yi kama... "
Jiki sanyaye Sabilar ta kalli Ayya ta ce.
" Ayya kin san sha'anin Aljanu fa akwai ruɗarwa, kada ma ace ta aure shi ne... "
" Kaii! Don Allah bari ma yi mini wanga batu na banza...ko ta aure shi ai bata fi ƙarfin Allah ba, wallahi tallahi da ayoyin Allah za'a halakata kuma dole ta fi ce ta ƙyaleshi."
Haka dai suka yi ta firar, Ayya na ƙara ƙwararawa Sabila gwiwa akan Ashiru.
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 21*
Yau tun da na shigo babban gate na tarar da yawan motocin da ke harabar wurin sun ƙaru fiye da yan da na sansu.
A kitchen na tarar da su Munira suna ta faman darzazar aiki. Bayan mun gaisa fuskata ɗauke da mamaki na ce.
"Muni buki ake a gidan ne?"
Girgiza kai ta yi ta ce.
"Za dai ayi, kwana biyar mai zuwa...."
Dariya ta koma yi ƙasasa tana kallona ta ci gaba da cewa.
"Mutuniyarki ce ta haihu, jiya bayan kin tafi suka iso daga ƙasar waje."
Tsaki na ja ina ɗan yi mata hararar wasa na ce.
"mts! To miye abun dariya a nan kuma? Allah ya raya. Mi aka samu?"
Sai kuma na dawo murmushi ina mai bin su da ido ina jiran amsar su.
Haula ce ta jinjina kai ta ce.
"Ɗa namiji aka samu, Wallahi baki ganshi ba, barakallah kamar Ya Emraan."
Jinjina kai na na yi na ce.
"Masha Allah! Allah ya raya....Bari kiga bawa yaje ya yi aikinsa da wuri ya huta. Tashi muje Hajiya Muni."
Tare muka shige muka bar su nan suna ta aikin haɗa breakfast. Duk da cewa baƙi sun cika gidan,nan take mukayi komai muka kambala kuma muka dawo kitchen ana ta kai kawo wurin kai musu abincin kari.
Muna tsaye na ce musu bari na shiga na gaishe da Hajiya domin ban ganta ba a ɗa zu.
Munira ce tace.
"Ko ɗa zu ba ki shiga inda zaki ganta ba ne... Duba.. Idan kika shiga ta wannan ƙofar."
Ta faɗa tana mai nuna mini wata ƙofar wacce ni dai ban taɓa ganin an buɗe ta ba, ta ce.
"Da kin shiga akwai ƙofofi guda biyu, sai ki shiga ta hannun daman ki."
Miƙewa na yi na shige ba tare da jin komai ba, nan take ko sai gani cikin wani parlourn wanda ban taɓa sani da shi ba, kuma gashi duk a cikin rufi ɗaya. Ikon Allah!
Ina shiga na duƙa ƙasa na gaishe su ita da wasu baƙin da na tarar,bayan sun amsa Hajiya ta kalle ni ɗauke da murmushin samun sabon Grand Son a fuskarta ta ce.
"Beenafah kinga masu haihuwa sun dawo ko? Aziza an haihu na samu Muhammad ɗina."
Ni ma murmushin na yi na ce.
"Allah sarki! Allah ya raya..."
"Amin. Su Haulatu sun kai ki kin yi mata barka kuwa?"
Girgiza kaina na yi na ce.
"A'a, yanzu dai nake batun tafiya."
"To gaskiya kam, ya kamata ki je ki ga Mummaduna."
Miƙewa na yi na fito ina wani rarraba ido na cewa Haula.
"Hajiya fa ta tambayeni wai na yiwa Aunty Ziza barka, na ce a'a, shi ne ta ce ya kamata na je....muje dan Allah ku rakani."
"Jiya koda muka je kin tafi saboda haka yanzu aiki muke, kin dai ji yanzu Hajiya ta kirani a waya.."
"Haba mana dan Allah! Muni.."
"Sai dai fa idan za ki jira in wani abu ya shigar damu kije ki yi mata,amma yanzu da ta gan mu bata tunanin aikinda muke za ta ƙara tula mana wani.... Mts! Sai da fa akace ta koma gidanta amma matar nan ta kafe wai ita sai an yi suna."