Kenza eBookz

Ganin ido complete Novel - Chapter 23

Ganin ido complete Novel - Chapter 23

Ganin ido complete Novel Chapter 23: Ganin ido complete Novel Chapter 23. Sai da ta cika wata uku da haihuwa a gidan cif sannan ta shirya ta koma gidanta.…

3,247 words

Sai da ta cika wata uku da haihuwa a gidan cif sannan ta shirya ta koma gidanta. Hakan ya ƙara bani wata damar samun kwanciyar hankali wanda bani da wata matsala a yanzu. Shi ma Mijinta ni dai tun bayan sunan da na ganshi sau ɗaya ban sake ganin shi ba har yau.

A duk lokacin da ta zo gidan ta ganni a zaune bana aikin komai, hakan ba ƙaramin baƙin ciki yake bata ba. Da wannan ta yi nasarar shawo kan Hajiya akan dole ya kamata ace na koyi girki ko don yau da gobe. Ta hakan tayi amfani da ƙarfin ikonta tasa Oga Sule ya ɗaukeni ya kai ni Ziza Eatry and more inda na duƙufa koyon girke-girke ba kama hannun yaro.

Babban wurin abinci ne dake titin bypass mai sassa daban-daban da ake gabatar da abubuwa a ciki, wanda aka ƙawata shi da kayan girke-girke na zamani wanda babu abun da babu.

Manyan hotunan ta ne kakkafe a babban reception ɗin, sai hoton wani daban wanda ban san wanene shi ba sannan hoton mijinta yana sanye da kaki.

Ma'aikatan dake wurin kuwa, ganin Oga Sule ke kawoni akodayaushe yasa suka saki jiki dani sosai muna harakar mutunci da su yayinda na ƙara kwantar da kai ina ƙara samun ilmi.

A wurin wata Aunty Subai'a ce na tambaya cewa wace ce Ziza wai? Domin ganin irin yanda take hulɗa da mutane daban-daban a wurin yana matuƙar bani mamaki.

Cike da alfahari ta fara mini bayanin ta da cewa; ita ɗin ta yi karatu a ƙasar France inda ta karanci Culinary Arts a Le Cordon Bleu University. A nan ta yi degree ɗinta a fannin girke-girke, ta koyi abincin ƙasashe daban-daban tare da samun gogewa daga manyan chefs na duniya.

Ziza ta kasance Mace mai baiwa ta musamman wadda Allah ya horewa hikima da fasaha a harakar girki.

Bayan ta dawo ƙasarta Nigeria da taimakon Daddy Ashraf shaharren ɗan kasuwa wanda ya kasance zaman mahafinta domin tun tana 'ƴar ƙarama ya ɗauko ta ya dawo da ita hannun shi a nan Potarcourt inda a nan ne bayan ta dawo ta samu damar cike mafarkinta na buɗe babban gidan girke-girke na Ziza Eatry. A hankali ta fara suna har ta zama cikin manyan gwanayen da ake ji da su a duniyar girke-girke a Nigeria. Sannan daga baya a hankali tana ƙara girma har ta fara samun gayyata daga ƙasashen waje, Dubai, Turkey, France da Kuma Saudi Arabia inda take yawan halarta domin gabatar da gasanni da kuma shirye-shirye a fannin girki. Ta samu awards na African Female Chef Wanda aka gudanar a ƙasar Ghana, sannan ta samu award na Best traditional Cuisine Innovator a Dubai food Expo Sannan kuma da award na Taste of Excellence a Paris International food festival.

A Kaduna suka haɗu da Emraan, bayan sun yi aure aka kawo ta Gusau, inda Emraan ya cika mata alƙawarinta na buɗe mata reshen ta na Ziza Eatry a nan bayan wancan dake gudana a portacourt ɗin.

Har laƙani gareta akan ƙwazonta wanda ake kiranta da shi wato Queen Ziza the Flavour Master, wannan Sunan ya samo asali ne ta dalilin yadda ta iya haɗa aroma, texture da Kuma presentation na abinci gwanin burgewa akodayaushe.

Suna yawan yabon halayenta na kirki da kuma son mutanen da take da shi amma kuma ni Sam ban gani ba, domin ko sau ɗaya bata nuna mini kirkinta ba sai baƙin hali da mummunar fuska wacce a duk sanda na kalle ta, to bana hango komai sai tsantsar tsanata wanda har yau na rasa dalili.

Haka na ci gaba, kullum idan gari ya waye Oga Sule ko Lawan har ƙofar gidanmu suke zuwa su ɗaukeni su kaini, idan ƙarfe uku ta buga na rana su dawo dani har na tsawon wata uku. Wanda ban sani ba ko ita gani take kamar mugunta ce ta mini,bayan bata san cewa wannan abun da ta yi mini ba tayi matuƙar taimaka min kuma har abada ba zan daina gode mata ba domin ta ƙara inganta mini rayuwata.

A haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar damu yau daɗi gobe akasinta,inda yanzu na doshi tsawon shekara ta biyu ina aiki a gidan Hajiyar. A gefe ɗaya kuma ina nan ina zuwa Islamiyya, Alhamdulillah na samu na kambala sauke Al-Kur'ani kuma ina ci gaba da litattafaina. Ina nan ina ta ƙara samun gogewa a rayuwa ta gefen ƙawayena su Hafsa da kuma su Munira. Gefen Ya Jafaru kuma;yana nan sannu a hankali ya kambala aji ɗaya ya shiga aji na biyu. A kullum kwanan duniya sai ya kirani a wayar Mama sau ɗaya ya ce a kirani yana so mu gaisa,baya dawowa sai ƙarshen Semester idan ya kambala exam ko kuma idan wani wani uzuri ya ta so. Wani abun da yake ɗauremin kai kuma ya tsaya a raina shi ne, yanzu kwata-kwata ya daina matse mini kamar yanda yake yi ada. Kuma tun ranar na kira shi da wayar nan bai taɓa kirana da ita ba, idan ma na kira shi baya ɗagawa sai dai ya kirani ta wayar Mama muyi magana wanda a yanzu na daina kiran sa ma da ita, kuma ko ya zo bai taɓa cewa yana so ya ga wayar ba. Sai dai maganarsa guda ce kullum, na kula da kaina kamar yanda yake kulawa da kansa.

Gefen Yaya Ashiru shima yana Kano abinsa, amma dai shi baya shafe cikakken wata ɗaya bai zo ba, sai dai kuma, baya wuce kwana ɗaya ko biyu yake juyawa ya koma, shiyasa na ƙara samun kusanci da kuma shaƙuwa da shi sosai. Dokar Ammie tana nan wacce ta sanya mini akan waya, bana fita ko'ina da wayar nan, amfaninta a gareni kawai sai idan ina gida, wanda shima daga zaran Yaya Ashiru ya kirani sau ɗaya da magariba, baya ƙara kirana sai kuma wata goben amma kuma muna ɗaukar lokaci akan wayar muna magana wacce duk yawanci hirarrakin duniya ne.

Gefen Daddy kuwa, babu wani labari tsakaninmu da su, bamu da nasu haka zalika suma ba su da namu labarin. Komai tamkar a mafarki haka yake tafiya tsakaninmu da su Daddy tamkar bamu rayu da su ba. Alhamdulillah! Ubangiji duk inda yake so yaga bawansa a nan zai barshi, duk abinda ya rubuta maka ya nufeka za ka samu to tabbas babu wanda ya isa ya hana hakan faruwa. Ga shi dai muna raye kuma cikin rayuwa mai daɗi ba tare da su ba. Idan ka dogara ga Allah haƙiƙa ya isar maka da komai.

Uncle Isma'ila sau biyu ya taɓa zuwa gidanmu, ganin gidan yana nan tsab hakan yasa ya ɗauke ƙafarsa, kuma ni duk zuwa biyun da yayi ban taɓa haɗuwa da shi ba, sai dai daga baya Ammie ta bani labari. Rayuwa tayi mana komai Alhamdulillah, muci mai kyau musha kyau sannan mu gabatar da sauran buƙatocin rayuwa duk a cikin inuwar Aunty Labiba da kuma Ahlinta wanda babu komai tsakaninmu da su sai fatan alheri.

****

Misalin ƙarfe biyar na yammar ranar Talata. Ashiru yana zaune a bakin ƙofar ɗakin Ayya suna magana kwatsam sai ga Yaya Nura ya shigo.

Wata irin zabura Ashirun ya yi ya miƙe tsaye yana wani rarraba ido alamun rashin gaskiya.

Kallon shi Yaya Nuran ya yi calmly yana girgiza kai ya ce.

"A'a! Zauna abin ka, ni indon ganina ma bari wata razana."

Wuri ya samu ya zauna yayinda har yanzu Ashirun yake a tsaye. kallon Ayya ya yi suka gaisa sannan ya tambayeta Umma ta ce ta fita anguwa. Ɗaya daga cikin ƙannen na su ne wata ta zo ta ɗauki jakar Yaya Nuran ta shigar masa da ita ɗakin Umma daga nan shi kuma ya miƙe ya ce idan sun yi sallar Isha yana so su zo a zauna yana da maganar da yake so su tattauna akai.

Tun da Ashiru yaga shigowar Yaya Nura bai sake samun nutsuwa ba, musamman idan Umma ta dawo ya faɗa mata cewa sai da yace masa kar yazo amma ya ƙetare maganar sa ya yi tahowar sa.

Sannan yanzu bai san wane kalar hukuncin Yaya Nuran zai yanke masa ba, domin abin da har ya ɗauko shi a wannan lokacin daga Kano ya kawo shi Gusau to tabbas abin nan ba ƙara mi ne ba.

Da wannan tunane-tunanen ne ya samu jiki sanyaye ya gabatar da sallar Magriba da Isha sannan ya tattaro ya dawo gidan.

Bai ƙara shiga tashin hankali ba sai da yaga Yaya Kamal da kuma Aunties ɗinsa guda biyu, Nasma da kuma Nusaiba. A bakin ƙofar ɗakin Ummar ya tsaya ya togace domin ya kasa ƙarasowa ciki.

Wani kallon Umma ta jefa mishi sannan ta ce.

"Ai sai ka ƙara so ciki kai ake jira mutumin banza kawai!"

A hankali ya saɗaɗo ya zauna a gefen Nusaiba tare da faɗin ina wuninku.

Babu wanda ya amsa daga cikinsu tsawon lokaci sannan daga ƙarshe Yaya Nura ya sauke wata ajiyar zuciya ya ce.

"To! Alhamdulillah! Ni dai maƙasudin tara ku a nan shi ne; Ashiru dai ƙanina ne kamar yanda yake a gare ku kuma, bani da wani buri a raina face inga na gina shi kamar yanda nima na ginu. Shiyasa na tsaya na ɓata lokacina da kuma kuɗina wurin ganin ya samu ilmi ya kuma samu hanyar dogaro da kansa. Mutumin kirki ne, domin gaskiya idan na ce ga kuskurensa da ya taɓa yi wurin saɓa mini to na shiga haƙƙinsa. Yana nan yana karatunsa lafiya lau ba wata matsala kasuwancinsa ma haka, komai na tafiya yanda ya kamata kuma ana kan samun alheri babu laifi,to amma yanzu matsala ɗaya ce wacce ku kanku nasan kun san da ita kawai dai kun yi shiru kun zuba masa ido ne bama kamar ke Umma da Ayya. Tun da yarinyar nan ta dawo rayuwar sa shikenan ya rasa sukunin rayuwa, bai da wani aiki sai nata bai da wata magana sai tata, yanzu a wata sai ya zo Gusau sau biyu ko sau uku kullum cikin zarya yake akan ƙarfe, Maman Nabil har da magana ta yi masa kwanaki akan ya sararawa hanya amma bai saurareta ba, sannan ni kaina a wannan karon sai da na faɗa masa cewa kada ya zo, amma haka ya shure maganata ya ɗauko ƙafa ya dawo... "

Cike da jin haushi Yaya Kamal ya maka masa wata uwar harara ya ce.

" To tun da har ya nuna ba'a isa da shi ba ai shikenan, sai yaje ya yi ta abunda ya ga ya fiye mish... "

Girgiza kai Yaya Nura ya yi ya ce.

" A'a, duk batun hakan bai taso ba. Ku kanku kun sani, an yi faɗan an yi mi amma kuma bata sauya zani ba..."

Kallon sa Umma ta yi ta ce.

" Nura ka daina cewa wai ba zai canza ba! shi ne ya haifi kansa ko kuma haifar sa akayi da zai ce yafi ƙarfin mutane... "

" To ai ni Umma ina da wata shawara wacce nake tunani da kuma ganin ita ce maslaha a wannan al'amarin. Kawai aje a nema masa aurenta. Idan akayi auren sai ya tattara ta su dawo Kano gabaɗaya kinga shikenan an huta an yi maganin abun... "

Wata irin zabura Ayya ta yi ta ce.

" Kai Ina! Gaskiya Nura wannan magana ba za ta yiyu ba, mutanen nan fa ni har yanzu ban yarda da su ba, hatta kuɗin da Uwar ta ta kawo wai a siyawa Zulfa Tsintsiya suna nan na maƙale su a kusurwar ɗakina... "

Girgiza Kai Nasmatu ta yi tana faɗin.

"Haba Ayya! Dan Allah ki daina wannan maganar. Hasashen fa da kike akan mutanen nan sam ba gaskiya ba ne, tashi suka yi daga gidan da suke suka canza wuri ba tare da kowa yasan inda ɗan uwansa yake ba. Sannan tun da ya samo inda suke har yau kin ƙara jin cewa sun ɓata?.....Ni dai Yaya Nura Ina goyon bayan wannan maganar kawai a nema masa aurenta kowa ma ya huta, domin zaryar hanyar nan da yake ta yi yawa..."

Jinjina kai Yaya Kamal Ya yi, ya ce.

" Tabbas nima na goyi da baya, tsawon lokacin nan da aka share yana bibiyarta, komai za'a yi ba zai daina ba, saboda haka a saka lokaci kawai mu shirya muje a nema masa aurenta."

Nusaiba itama ta ce.

" Ni ma na amince da wannan shawarar, kuma wallahi Beenafah yarinya ce mai nutsuwa da hankali, daga ita har mahaifiyarta suna da kirki sosai, ko haihuwar nan da na yi kwanakin baya sai da suka zo mini barka."

Ido ya juya ya kalli Umma ya ce.

"Umma ke baki ce komai ba??"

Girgiza kai ta yi ta ce.

"Bani da matsala domin ba ni ce zan zauna masa zaman auren sa ba, Allah yasa alheri yasa albarka."

"Ke fa Ayya?"

"Hmm! To! Ni dai gaskiya na so ya Auri Sabila tun da dai ita ce wacce muka sani, amma kuma ɗan yau nasan baka isa ka shiga gaba da al'amarin shi ba,saboda haka nima na amince amma dai ba don raina ya so ba."

Babu wanda bai dara ba a wannan amsar ta ƙarshe da Ayya ta bada, sannan daga ƙarshe Yaya Nura ya ce.

" To abu yayi kyau, kuma In Sha Allahu zan tattauna da su Alhaji Nasiru suma (cewa da sauran yuyyunsu da kuma en uwan su) nan da sati biyu zamu kai ƙarshe, gabaɗaya zuwa wata ɗaya, sai mu zo muje gidan wurin nema masa ita. Saboda haka gobe a tare zamu koma da kai ƙafata ƙafarka, ina so zan tafi ɗauko kaya, dole za ka tsaya a Shago.... "

Wata Hararar Umma ta sake jefa mishi sannan ta ce.

" To yanzu sai na gani kuma idan haƙurin wata ɗaya ne ba za ka iya ba, tunda har an yi wannan maganar ina so ka tsaya ka fuskanci kasuwancinka."

Tamkar wanda aka zarewa lakka haka ya gyaɗa mata kai a hankali ya tashi ya bar ɗakin.

Can wajen ƙofar gidan ya fice gabaɗaya yana nazari. Shifa wallahi notukan kanshi ma sun kwance a halin yanzu, ya kasa rarrabe cewa shin a yanzu farin ciki yake ciki ko kuwa. Auren Beenafah fa akace za'a nema masa amma kuma bai taɓa furta mata cewa yana sonta ba. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Abin da ya shiga nanatawa kenan yana mai samun wani ɓaragurbin tunane daga wani ɓangare na zuciyarsa cewa to idan ta ce ita bata son shi da aure fa?? Tambayar kan shi ya fara na cewa to shi ɗin yana sonta kuwa? Duk da tsoro ne fal a cikin zuciyar sa amma hakan bai hana mishi murmusawa ba a lokacinda ya tsinci kanshi da yiwa kansa tambayar. Tabbas yana sonta yana yi mata wani son da baki ma ba zai fasalta shi ba.

Wayarshi ya zaro daga Aljihu ya duba agogo. Ƙarfe goma sha ɗaya saura na dare, saboda haka lokacin kiranta ya wuce a gareshi amma kuma magana ta gaskiya ba zai iya kai wa Magribar gobe ba tare da ya bayyana mata halin da ake ciki ba. Hakan yasa ya tura mata text da cewa dan Allah gobe ta yi haƙuri ta tafi da wayar wurin aikinta yana so ya yi wata magana da ita mai matuƙar muhimmanci.

*****

Tun a daren jiya, da mamakin rashin kiran Yaya Ashiru na kwana a raina har gari ya waye.

Ina yin sallah na janyo wayar da sunan yin azkhar ɗinda nake yi wanda yake Application ne mai zaman ƙanshi a wayar kwatsam sai ga text ɗin Yaya Ashiru na gani.

Na daɗe tsawon lokaci ina jujjuya maganar a ƙwaƙwalwata sannan daga ƙarshe kawai na yi murmushi na tashi na yi duk abin da zan yi sannan da zan tafi na maƙale wayar a hijabina abin da ban taɓa yi ba. Wato yi wa Ammie rashin gaskiya da kuma saɓa maganarta, wanda ni har ga Allah ban yi hakan da wata manufa ba, kawai dai na ƙosa ne in ji shin wacce magana ce yake so ya furta a gare ni,domin ba zan iya jira har Magrib ɗinba.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️

*GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....

*PAGE 25*

Ina isowa ko zaunawa ban yi ba na wuce na yi duk aikinda ya kamata na yi, daman kuma gashi Hajiya bata nan ta tafi Dubai kamar yanda ta saba tafiya wasu lokutan sannan Aunty Ziza ma bata ƙasar kamar yanda Su Munira suka faɗa mini, shiyasa muke zaune muna cin karenmu babu babbaka,musamman saboda babu wasu ayyuka akanmu masu yawa.

Muna zaune a ɗaki bayan mun kambala karin kumallo suna firar su ni kuma ina zaune a gefe riƙe da wayata ina game Ina murmushi, musamman da na ji irin firar da suke wacce a yanzu ita suka sakawa gaba tunda Haula ta yi saurayi, wani ne ya zo har gidan yace yana sonta shi ne fa Hajiya ta bashi dama akan ya riƙa zuwa tun da daman iyayenta sun yi magana.

Na yi nisa sosai a tunani wanda har yasa na daina fahimtar abin da suke faɗi na ji Munira ta daki cinyar ƙafata tana dariya ta ce.

"Ga masu yi nan ba'a magana...."

Tayi maganar tana mai fashewa da dariya sannan ta sake kallon Haula sai kuma ta kalleni ta ce.

"Beenafah ta raina mana wayau Haula, duk ana zancen soyayya sai da tayi shiru alhali tafi kowa ƙwarewa..."

Ɗan zaro ido na yi ina mai nuna kaina da yatsa na ce.

"Ni wai? Gaskiya a'a.."

Jinjina kanta ta yi idonta still a cikin nawa ta ce.

"ƙwarai kuwa.... Shin kina lura da kanki kuwa musamman a 'ƴan kwanakin nan Beenafah ?"

Cikin rashin fahimta na girgiza kaina na ce.

"A'a! Miye ya sameni Munira? Ko na rame ne dan Allah?"

Wata dariyar suka kwashe da ita har sai da suka sakani murmusawa nima sannan Munirar ta ce.

"Ki ci gaba da rainawa kanki hankali wai ke kina rai na mana..."

"Wallahi da gaske nake miki Munira..."

"To naji, ba zancen rama nake miki ba, zance ne na kin zurma sosai a cikin soyyaya wacce a yanzu har baki iya ɓoyewa ko a gabanmu ne musamman a 'ƴan kwanakin nan."

Saurin girgiza kaina na yi na ce.

"A'a wallahi ni kam...to mima yasa kika ce haka? Soyayya fa! Ni bana soyayya da kowa..."

Dariya Haula ta yi ta ce.

"A taki haukar kenan? Amma ko makaho ya shafa rayuwar da kike ciki a yanzu yasan cewa kina cikin shauƙi da begen soyayya."

Itama Munira murmushi ta saki tare da ɗan ƙara matsowa kusa dani tana faɗin.

"A gabanki fa saurayinki Ashiru ya so ya mareni amma kuma ba ki nuna kin damu ba, haka kuka riƙa rawar jiki tamkar za ku haɗiye juna a wannan ranar wanda babu komai a cikin idanun ku sai zallar soyayya..."

Still cikin rashin yarda na sake girgiza mata kaina ina mai jin wani iri na ce.

" Yaya Ashiru ba saurayina ba ne Munira, shi ɗin tamkar yaya yake a wurina... "

Saurin katseni ta yi tana wani jinjina kai ta ce.

" Oh! Haka ne.. To bari in gaya miki Beenafah, ita Soyayya ba lallai sai an faɗa miki da baki ba. Akwai abubuwan da zuciya ke yi da kanta wanda idan kika fara jin su, to ki sani kin faɗa a cikin soyyaya."

Sake gyara zamanta ta yi da kyau ganin da gaske na bata dukkan nutsuwata ta ci gaba da cewa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull