Kenza eBookz

Ganin ido complete Novel - Chapter 25

Ganin ido complete Novel - Chapter 25

Ganin ido complete Novel Chapter 25: Ganin ido complete Novel Chapter 25. " Baki isa ki rusa mini mafarki na ba Hassana, ko za ki mutu sai kin auri…

3,369 words

" Baki isa ki rusa mini mafarki na ba Hassana, ko za ki mutu sai kin auri Ameer....mi ma kika ce wai? Za ki kashe kanki ko? Kin daɗe baki kashe kan naki ba. Ana neman a gyara miki hanyar gobe mai kyau, amma tunda kina sakarya shi ne kike neman rusawa. Na baki dukkan wata dama, amma shi ne kike nema ki kai ni ƙasa ko? To wallahi tallahi Ƙarya kike yi!"

Ƙara juyowa tayi ga Daddy tana faɗin.

" Kai kuma! Ina mai tabbatar maka, idan ka biyewa tausayi da shiriritar yaro, to zai kai ka ƙasa ne ba tare da ka shirya ba, kada ka bari wannan dramar ta ta takai ka ga yin danasani..."

Jinjina kan shi ya yi da wani kalar murmushi a fuskar sa yana kallon cikin idonta ya ce.

" Idan fa baka iya kama ɓarowa ba Hajiya Zaliha to tabbas ɓarawon ne zai kama ka.."

Duƙawa ya yi ya ɗago Hassana suka zauna a tare gefen kujera ya kalleta a tausashe ya ce.

"Wane ne Salman?"

Cike da jin wani irin sanyi a ranta ta kalle shi ta ce.

"Salman Abubakar ne sunan sa, Shi ɗin daga jihar Jigawa ya fito, ya kasance ɗalibi mai ƙoƙari da tarin baiwa wanda har a Nile ake yin alfahari da shi. Yana da kirki haka zalika iyayensa. Ya kambala degreensa tun last year a ɓangaren nursing. Sai dai kuma;su ɗin ba masu hali ba ne, domin ko karatun da ya yi a Nile University under scholarship ne.... "

Wani irin dafe ƙirji Mummy ta yi cike da gigitaccen tashin hankali ta ce.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Hassana kin kashe ni...kin kashe ni Hassana! Yanzu ashe ma duk wannan akan matsiyaci ɗan matsiyata kike yin sa? Mi na sama ya ci ballantana ya bai wa na ƙasa?.."

Shi ma Daddyn cike da jin wani irin tashin hankali ya ce.

" Subhanallahi! Hassana! Miye haka dan girman Allah? A a gaskiya, ko ni nan ba zan amince da wannan ba... "

" But amma Dadd... "

Hannayenta ya jimƙe a nashi cikin sigar rarrashi ya ce.

" Hassana please! Kada ki bari soyayyar banza ta zo ta yaudareki, gidan kuɗi shi ne farin cikin duniya Hassana ba gidan wahala ba. Koda yana da hali mai kyau ya kuma iya soyayya to dame zai kula da ke?"

Cike da saka hope ta ce.

"He's so much hardworking guy Daddy, Salman can take care of me, yana buge-bugen sa bai zauna haka ba..."

Wayar da ke hannun Mummy ta rabko mata a gefen goshin ta da ƙarfin tsiya wanda ya yi sanadiyyar datsewar goshin na ta sai da jini ya fito.

A gigice Daddy ya kwasheta suka garzaya asibiti ba shiri.

*******

Yaya Ashiru kuwa, washe gari tun da wuri suka juya zuwa komawa Kano tare da Yaya Nura, wanda a hanyar ne ya kira Beenafah a waya domin ya sanar mata abin da yake faruwa kamar yanda ya yi mata alƙawari. Ga shi fa zaune a gaban mota tare da Yaya Nuran, amma kuma hakan bai hana mishi kiran Beenafahr ba domin gudanar da ƙudurinsa.

Ya kirata cike da jin wani sabon yanayi suka fara magana da nufin gabatar mata da ƙudurinsa, sai gashi kwatsam ya ji lokaci ɗaya wayar ta yanke,ƙoƙarin kira yake ta sake yi amma kuma ce masa ake wayar a kashe ta. Tsoro ne ya mamaye masa zuciya tuna kamar irin haka ne ya faru da su a baya wanda har yayi sanadiyyar rabuwarsu tsawon lokaci.

Cike da tashin hankali ya kalli Yaya Nura dake zaune a mazaunin driver yana tuƙa motar ya ce.

"Yaya dan Allah dan girman Allah ka yi mini uzuri ka sauke ni a nan. Wallahi tallahi akwai matsala! Akwai matsala wallahi Yaya! Dan Allah ka sauke ni na juya na koma Gusau,..."

Gefen Hanya Yaya Nuran ya samu ya parker tare da riƙo hannun sa da er damuwa ya ce.

" Kaga Ashiru! Please ka nutsu ka yi mini bayani, mi ke faruwa?"

" Yaya Beenafah ce muna waya da ita.... Koda yake ma ai kanajina ina magana, to... To shi ne wayar ta yanke, kuma ina ta kira yanzu a kashe... Ka bari na koma kada na sake rasa ta kuma dan Allah Yaya... "

" Calm down please! Babu abin da zai faru in sha Allahu, wata ƙila caji ne babu...."

Wata irin magiya ya fara masa yana faɗin.

"Dan Allah Yaya ka taimakeni mu juya yaya kuje gidan su ku nema min auren nan! kada wani abu yaje ya faru..."

"To shi kenan na ji,amma kuma tun da har saura kaɗan mu isa Kanon nan ka yi haƙuri, gobe idan Allah ya kaimu sai mu juyo mu dawo. Na yi maka alƙawarin wannan."

Ta haka Yaya Nura yayi nasarar shawo kansa har suka samu suka isa garin Kano.

******

Ni kuwa, ina shiga gida na tarar da wata mata wacce ake kira Hibbatu mai yiwa Ammie kitso ta zo suna zaune tana lallaɓe mata kanta suna fira . Hankalin Ammie a matuƙar tashe ganin har na zarce lokacin dawowata gida sosai amma kuma ban dawo ba. Ga Waya Bahrain ya nema ya rasa, gabaɗaya sun bincike gidan amma ba su ganta ba.

Riƙoni tayi muka zauna hankalinta a tashe ta ce.

"Beenafah lafiya? Miye ya same ki?...." Hannunta ta kai akan wuyana zuwa goshina ta ci gaba da faɗin.

"Na ji jikin ya yi zafi sosai, kuma kalli yanda fuskar ki ta yi ja, ga idanun ki ma sun kumbura da alama kin yi kuka. miye abun da ya same ki..."

Wani murmushi na ƙirƙiro ina kallon fuskarta na riƙo hannayenta na ce.

"Kai Ammie! Ji yanda kika wani ɗaga hankalinki? Ba wani abu bane ya same ni ba kawai dai zazzaɓi ne kuma ma nasha magani na ji sauƙi...."

"Tun yaushe ne baki da lafiya?"

"Daman koda na tashi ina jin alamar rashin jin daɗi, to shi ne fa ina cikin aiki sai zazzaɓi ya rufe ni, amma yanzu Alhamdulillah! Na samu sauƙi gaskiya."

Jinjina kanta ta yi alamar gamsuwa ta ce.

"Kin ɗauki wayar nan kin tafi da ita ne?"

Saurin girgiza kaina na yi ina ɗan wawwara ido na ce.

"Ni? Waya? A'a! A nan inda nake ajiyeta a nan na ajiye... Ba'a ganta ba ne?"

"Wallahi ba'a ganta ba, tun da Bahrain ya dawo yake ta nema har ya wuce Islamiyya bai ganta ba.... Kinga ta tabbata kenan wani ya shigo gidan nan ya sace ta, domin na san cewa ba za ki taɓa tafiya da ita ba."

Jinjina kaina na yi alamar bata tabbaci na ce.

" Gaskiya kam sai dai idan wani ya ɗauke ta, amma ni ban fita da ita ba."

Daga haka na miƙe na rarrafe na shige ɗaki ina mai jin wani irin tsoro yana sake mamaye dukkan wani ɓargo da sassan jikina.

Hibbatu kuwa da ke gefe tana faman rarraba ido akanmu ne ta kalli Ammie ta ce.

" Hmm! Hajiya Mulaifa kenan! Mu fa magana ta gaskiya duk irin halin da kuke ciki da 'ƴar ki babu abinda bamu sani ba a unguwar nan..."

Cike da tashin hankali Ammie ta dafe ƙirji da dukkan hannayenta guda biyu ta ce.

"Mine ne wannan Hibbatu?"

Sake taɓe baki ta yi ta ce.

"Uhmm! Ko makaho ya lalabi rayuwar da Beenafah take cikinta ai wallahi yasan barikin da take yi.. Ko yau ma da ganin wannan fuskar ta ta da yanayin ta yasan daga inda ta fito....."

Wani irin zaro ido waje Ammie ta yi a gigice ta ce.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Bariki Hibbatu???"

"Ƙwarrrrai kuwa! Bariki nake nufi, tana zuwa tana yowar iskanci tana yo miki same-same kina ci kina jin daɗi...nan da Allah ya tashi tona muku asiri ai har ƙofar gida aka dinga zuwa da mota ana ɗaukar ta ana kai ta ga 'ƴan bariki ana dawowa da ita. Kuma ni gaskiya naga wautar ki a nan Hajiya Mulaifa...domin Beenafah kalar ta kalar manya ce, bai kamata ki bar ta a nan wurin ƙananun yara ba,ma su baku' ƴan canji da kuma abincin kaiwa ga bakin salati...saboda haka, idan har kin amince;ni ki bani ita, na san manyan Hajiyoyi a Abuja, Lagos da Kaduna inda za a haɗata hulɗa da manyan jiga-jigan da suka da ce da ita....."

Wani irin gigitaccen mari ne Ammie ta sauke mata wanda shi ne ya zamto cikon maganarta ta ƙarshe. A gigice ta miƙe tsaye tare da dafe kunce ta na ja baya.

Itama Ammien Miƙewa ta yi tana wani irin hucin ɓacin rai tana wani nuna ta ta ce.

" Saboda kunya ta yi miki ƙaranci Hibbatu! Shi ne za ki tsaya kina faɗar maganganun banza ga 'ƴata wacce ta kasance komai ta rayuwata..."

Da gudu na fito na tsaya gaban Ammie ina faɗin.

"Lafiya Ammie?"

Cikin tsananin zafin rai ta shiga nuna Hibbatun tana faɗin.

"Ina fa lafiya tunda ta zo har cikin gidana tana neman yaga mini rigar mutunci na..."

Ƙofa na nuna mata ba tare da neman wani ba'asi ba na ce.

"Fita Malama!..."

Kallonmu ta shiga yi daga ni har Ammie tana faɗin.

"Zan fita kada ku damu...."

"Eh fita.. Fita malama na ce miki."

Na faɗa ina mai ɗaga mata murya ganin tana so ta gardama mini. Bayan ta fice ne na kalli Ammie na ce.

"Miye wai ta faɗa miki haka ne?"

Guntun tsaki ta ja tare da komawa kan tabarmar ta zauna tana faɗin.

"Manta da ita can, shirmen banza ne kawai."

A nan na samu wuri kusa gareta na kwanta tare da ɗora kaina akan cinyarta na lumshe idanuna ina jin komai na dawo mini kuma. Ji nake tamkar in tashi in zazzage mata matsalata ko Allah zai sa ta sama mini mafita. To amma ta ya ya? Zancen Yaya Ashiru in ce mata me? Bayan na ɗauki waya bata sani ba sannan kuma an tarwatse wayar a ƙasa. Sannan Emraan ɗinma ta ina zan fara? Ince mata ya buge wayar a ƙasar ya ce mini kuma wai ni zai aura? To ai wannan ma ba mai yiyu ba ne, wata ƙila kuma duk a gama ta mutumin nan yana shaye-shaye da alama.

Haka na yi ta nuƙu-nuƙu da matsalolin zuciyata yayin da na barwa kaina sani da rashin makar abin yi kuma. Ko Ya Jafaru da ya ce Farisa ta kawo mini waya a yau ƙin karɓarta na yi domin komai ya fice mini a kaina yau.

Haka na lallaɓa washe gari na tafi gidan Hajiya a matuƙar tsorace, domin ban san kuma mi zan je na tarar a gidan ba yau.

Ganin irin yanayin da nake ciki yasa Munira cewa kawai na kwanta a ɗaki in barta ta yi ayyukan kafin in samu in warware.

Misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe Emraan ya fito ya samu Munira a dining area tana goge-goge ya kalle ta ya ce.

"Munira ina Beenafah?"

Ɗan Jim tayi sannan ta ce.

"Ya Emraan! Yaushe ka dawo?"

"Just answer my question, ina Beenafah?"

"Tana ɗaki."

"Wanne ɗakin?"

"Ɗakinmu na can waje."

Fitowa ya yi a hankali ya kewayo zuwa inda su Inna Kuluwa suke ya kalli Haula ya ce.

"Haulatu ina ne ɗakin da Beenafah take?"

Ɗakin ta nuna masa cike da son neman ƙarin bayani akan mi yasa yake neman ɗakin da Beenafah take. Kallon shi suke har ya kai bakin ɗakin sannan ya tura ƙofar ya shiga.

Within seconds ya ƙarewa ɗakin kallo sannan sannu a hankali ya tako daidai inda nake kwance ya zauna a gefen katifar ya ce.

"Beenafah!"

Wani irin firgigit na yi na miƙe zaune domin muryarsa na jita sosai har cikin kwanyata ina zaro ido na kalle shi, shi ne kuwa zaune a gefena. Wayyo Allah na!!!

"Can we talk a little??"

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....

*PAGE 26*

"amm! Ina nufin za mu iya yin magana?"

Cike da tsoro na fara matsawa baya a hankali ina mai jin sabon tsoron sa na ƙara dukar mini zuciya.

Ganin irin yanayina sai hakan ya sanya shi miƙewa tsam ya koma jikin ƙofa ya jingina still muna facing juna da shi in a calm voice ya ce.

" Ki yi haƙuri da abinda ya faru...ni ba haka nake ba, kawai dai abin ya mini wani iri ne a jiyan kin gane....saboda haka kada ki ji tsorona, har abada ba zan iya cutar dake ba. Abun da na sani, shi ne ina sonki sosai, ina matuƙar ƙaunarki....And magana ta gaskiya, I can't wait long, matuƙar dai za ki amince da ni, to bana so a ɓata lokaci. Saboda haka zan baki dama ki yi nazari a kaina amma kada ki ce mini a'a, ina roƙonki. Ina son ki, ina so kuma na aure ki. Sai dai... I won't force you Idan har kika ji cewa you have no feelings on me. Ina fata za ki yafe min da abin da ya faru jiya... Dan Allah!"

Ya ƙarashe maganar yana mai haɗe hannayensa tare da ɗan rusunowa da kansa kaɗan alamar roƙo sannan daga baya ya juya ya fice.

Yana fita ya ci karo da Munira da Haulatu suna tsaye a bakin ƙofar sun yi cirko-cirko fuskar su cike da alamar tsoro.

Kallon su ya yi hankalinsa kwance ya jinjina kai ya ce.

"Ina son Beenafah, kuma zan aure ta in sha Allahu ba da jimawa ba. So please! Don't misunderstood me."

Daga haka ya sa kai ya tafi abinsa hankali kwance, tamkar ba shi ne ya yi maganar ba.

A tare suka shigo ɗakin kowaccen su kuma na rige-rige kawo wa gare ni, cike da tashin hankali Haula ta janyoni tana faɗin.

" Beenafah! Dad...da gaske ne wai Ya Emraan ya faɗa miki son ki yake auren ki zai yi??"

Su ne suke faɗin maganar, amma kuma jin ta a bakin su ya ƙara jefani cikin matsanancin tashin hankali da ruɗani. Wai da gaske abin da ya faɗa musu kenan?

"Beenafah ni fa ina cikin tsananin ruɗani da tashin hankali..."

Ajiyar zuciya Munira ta yi sannan ta kallemu ta ce.

"Naga duk kun wani gigice wai....Ni fa ban ma ga wani abun tashin hankali a nan ba..."

Kallon da na muka jefa mata mai alamar tambaya shi yasa ta jinjina kanta tana mai bamu tabbaci ta ce.

"Eh, saboda shi ne yace yana sonki ba kece kika ce kina son sa ba. Sannan tabbas! Tun da har ya furta to lallai zai cika in dai Ya Emraan ne.... Haula kin manta labarin da Hairi ta bamu yanda akayi wurin zancen auren sa? Ai da farko Aunty Lailah ya so ƙanwar mijin Aunty Labiba, amma tunda suka shiga raina masa hankali ya ba ta baya musamman da ta ce mishi tana ganin kawai su haƙura da juna, tun daga sannan bai sake waiwayarsu ba, bayan ya koma wurin aiki sai ga shi kwatsam watarana ya dawo da labarin Aunty Ziza Hajiya ta so ya auri 'ƴar nan Zamfara amma ya ce tunda har Zizar ta ƙauna ce shi to fa shi bai da wata matar idan ba ita ba. Ƙarshe haka ya tabbata. To in Allahu ko a nan ma hakan ce za ta tabbata muddin dai ba kece kika janye ba..... "

Miƙewa na yi da sauri ina mai girgiza kaina domin abin da ba ma zai yi yu ba kenan, hakan yasa na baro musu ɗakin na koma can ƙarshen flowers ɗinda ke jere a Layin veranda ɗin na zauna ina mai rushewa da kuka. Wannan ɗin ba abu ne mai yiyu wa ba? Na zo da sunan mai aiki sannan in ne mi ruguza farin cikin ma su gidan ai hakan ba zai faru ba, domin nasan har abadan abada ba za su taɓa bari ya aureni ba saboda munyi hannun riga ni da shi a komai na duniya.

Haula kuwa, kallon Munira ta yi jiki a sanyaye ta ce.

"Wai ko Muni kina tunanin cewa wannan maganar da Ya Emraan ya yi da gaske yake? Ni fa wallahi hankalina ya tashi sosai.. Munira kin fa san wa su masu kuɗin nan dangane da masu aiki sai a hankali!!!"

Cike da ɗan shakku Munira ta ce.

"To Haula! Duk da cewa bana shaidar Ya Emraan ɗin amma kuma bana tunanin ya aikata wani mummunan abu akan Beenafah. Ina kyautata masa za to, domin duk tsayin zamana a gidan nan ko alamun maganar banza ko kallon iskanci bai taɓa yi mini ba, kema kuma na san haka, sauran masu aikin su da suka gabata kafin mu ma haka. Saboda haka, tunda har hakan ta faru, ina ji a jikina da gaske yake kuma in sha Allahu alheri zai faru."

"Touhh! Allah ubangiji ya ƙaddara ya kuma zaɓa muna mafi alheri baki ɗaya."

"Amin, shi kaɗai zamu ce."

Haɓa Haulatu ta kama tana jinjina kai alamar al'ajabi ta ce.

"Uh uhm! Ko ya za ta kaya idan Aunty Ziza da Hajiya suka dawo?"

Dariya Munira ta sheƙe da ita tana gyaɗa kanta ta ce.

"Akwai kallo ko... Tabbas akwai ɗanɓarwa...to wai ke Haula ko dai daman Aunty Ziza ta gano cewa mijin nata ya kamu da son Beenafahr ne? Ki duba irin abubuwan da ta dinga yi mata ɗin nan komai cike da wulaƙanci..."

Cikin yarda da zancen na Munira ta gyaɗa kanta ta ce.

" Tabbas kuwa, biri ya yi kama da mutum. Haba! Ashe ba a banza Aunty Ziza ta dinga gallazawa rayuwar Beenafah ba. "

" Wallahi kuwa! Yanzu dai mu bata lokaci ta yi nazari tukun. Amma dai gaskiya ni ina bayan wannan maganar ɗari bisa ɗari muddin dai shi ɗin da gaske yake."

******

Misalin ƙarfe uku na rana, Ashiru ne da 'ƴan uwansa zaune a kan tabarma yayin da Ammie ke zaune a wurin ƙofar ɗakin ta, sai Babansu Jafaru shima zaune a gefe ɗaya.

Bayan sun gama gabatar da maganar da ta kawo su ne Babansu ya Jafaru ya yi gyaran murya a hankali ya fara yi musu bayani da cewa.

"To! Alhamdulillah! Mun ji dukkan abun da kuke tafe da shi, amma kuma kamar yanda muka yi muku bayani tun farko, cewa ni ɗin maƙoci ne kawai, zama na mutunci ne ya haɗa mu da su tsawon shekaru uku, kuma tun da muke dasu a unguwar nan babu wanda ya taɓa samun su da wani abun ashsha, sai dai kuma, har yau babu ko mutum guda da ya taɓa zuwa nan da sunan dangin su...."

Ɗan ƙara gyara zamansa ya yi sannan yaci gaba da cewa.

"Abin da har yasa na yi wannan maganar kuwa shi ne; shi aure, ana gina shi ne akan turba ta gaskiya da kuma amana, wanda duk wani abin da zai je ya dawo duk rintsi zumuncin iyaye na nan har abada ba zai rushe ba, sanadiyyar komai an kafa shi akan gaskiya. To magana ta gaskiya bamu san wasu dangi nasu ba kamar yan da kukaji, sannan ni ba zan iya shiga gaban wannan al'amari ba amma dai akwai Wan mahaifinta wanda suke Uwa ɗaya Uba ɗaya wanda a yanzu haka yana Abuja. To In Sha Allahu zamu tuntuɓa daga gareshi daga nan sai ku shirya ku tafi can wurin sa idan har hakan ya yi muku, kunga duk yanda kuka yi da shi, magana ta ƙare,ko ba haka ba?"

Jinjina kai suka yi dukkan su na gamsuwa da bayanin sa yayin da wa su daga cikinsu suka cika da shakku na wannan rayuwar da su Beenafahr suke kai. Bayan ya ɗan tsahirta na ɗan lokaci sannan baya ɗai daga cikin yayyun Ashirun ya ce.

" Ba matsala In Sha Allahu, zamuje kuma zamu jira daga gare ku, idan ma Abujar zamu je mu same shi, wannan duk ba matsala In Sha Allahu. Allah Ubangiji ya tabbatar mana da alherinsa amin. Mun gode sosai."

Shima Yaya Nura ya ce.

"Alhamdulillah! Kuma munji daɗin faɗa mana gaskiya da kuka yi, domin ita gaskiya ita ce mutuncin ɗan adam, hakan kuma shi ne daidai....mun gode Hajiya, sai munji daga gareku."

Daga haka suka kakkaɓe suka tashi suka fice tare da Babansu Jafaru wanda daga nan ya koma gida.

A mota Yaya Kamal ya kalli Ashiru ya ce.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull