Ganin ido complete Novel - Chapter 31
Ganin ido complete Novel Chapter 31: Ganin ido complete Novel Chapter 31. "Hmm! Kin girgiza ko? To wannan ɗinma somin taɓi ne akace wai hatsin gara a…
3,340 words
"Hmm! Kin girgiza ko? To wannan ɗinma somin taɓi ne akace wai hatsin gara a Langa. Dr. Bello shi ɗin ya kasance yana aiki a matsayin pharmacist wanda yake da specialisation in pharmaceutical manufacturing and Drug Formulation. Koda mukayi Aure yana matsayin Senior pharmaceutical Consultant a RoyalMed pharmaceutical Centre dake Toronto, Canada. Wadda ma'aikata ce wacce ta kasance Cibiyar da ke da alhakin bincike da kuma buga magunguna na musamman especially antibiotics da pain relievers. Shi ɗin ya kasance yana da kamfaninsa na ƙashin kansa na buga magunguna a Lagos Nigeria wato WazeerMed Pharmaceutical Ltd. Babban kamfani ne dake buga magunguna wanda yake da lasisi daga NAFDAC da kuma Pharmacists Council of Nigeria. Sannan kuma yana da Shareholder and partnership a kamfanoni biyu wanda suka yi haɗaka da abokansa. Na farko akwai FruitWave Beverages Ltd a Abuja Wanda kamfani ne da yake buga lemukan fruit da kayan shaye-shaye masu ƙara lafiya. Na biyu kuma akwai NordicBag Industries dake Toronto Canada wanda shi kuma kamfani ne da ake ƙera Jakunkuna da takalmi na alfarma waɗanda ake fitarwa ƙasashen duniya ciki har da Nigeria. Dr. Bello, ranshi ne kawai bazai iya cirewa ya bai wa Alhaji Mudassir ba. Amma duk wata ɗawainiya da kika sani tun daga sama har ƙasa shi yake yi masa komai. Alhaji Mudassir bai yi ƙarfin Dr. Bello ba , domin shi ɗin malamin makaranta ne wanda yake koyar wa a secondary school. Amma kuma sam bai dogara ga albashin da ake ba shi ba, domin Dr. Bello ya kasance shi ne bankinsa, wanda a duk lokacin da yake son kuɗi ko miliyan nawa ne iyaka ya kira waya shi kuma ya tura masa. Abincin sa, gida, motar hawa, suturarshi shi da iyalinshi, kudin makaranta kuɗin magani, duk shi ne. Bai san wata wahalar nema ba, bai san yanda ake nema ba iyaka da ya tashi buƙatar kuɗi ya yi masa waya shi kuma ya tura masa. A gidana Aysha, Husaina da Hassana suka zauna a Canada inda su kuma a can suka yi secondary school amma ba su kai ga kambalawa ba muka taho auren Ayshar a lokacin suna ss2 ne. Hafiz ma, shi ne wanda ya ɗauke sa bayan ya kambala secondary a nan ya kai shi Australia da kanshi ya nema masa Admission wanda akan pharmacy ne ya nema masa wai don ya zama kamar sa watarana, amma kuma daga baya ya juya zuwa Art akan wai ba zai iya ba. Wannan kenan! "
" Hmm! A lokacin da ya yi mini wannan furucin na cewa sai dai na tafi na bar masa su Beenafah! A lokacin na fashe da wani irin gigitaccen kuka wanda ya kusa zautani na faɗi akan ƙafarsa ina magiya ina roƙonsa. Daga ƙarshe ƙafa yasa da ƙarfin tsiya ya hamɓareni, gani da ɗanyen jariri a hannuna wanda abun ya zo mini a ba za ta shiyasa ban ankare ba muka wulla da ƙarfi sai gashi ƙoƙuwar kan shi ta bugi tiles nan take ya fashe sai jini... A gigice na fito ina wata irin kururuwa ina neman agaji, a loakcin bai gama tsara ƙudurinsa ba nasan shi yasa ya fito ya kaimu asibiti wanda kai tsaye aka ce sai an mishi aiki na miliyoyan kuɗi. Uhm! Duniya kenan aka ce rawar 'ƴan mata. Alhaji Mudassir dake tsananin girmamani da shi da matarshi, wacce ko inda nake zaune na ce ta zauna komai magiyar da zan yi mata ba zata zauna ba, wai su ne suke da guts ɗin wulaƙantani. Shi fa ya jiwa Sajjad ciwo a wannan lokacin amma kuma faɗa yake mini tamkar wanda ya ke yiwa 'ƴar cikinsa faɗa. Bayan ya biya kuɗin ba jimawa aka yi masa aikin. Haka suka wofintar damu da ni da yarana muka dawo tamkar bola a wurin su. Hakan yasa na samu mummunan ciwo na puerperial psychosis, wanda ciwon hauka ne yake kama mace idan ta haihu tana cikin matsanancin baƙin ciki da damuwa. Maimakon ya ɗaukeni ya kaini asibiti? Ba su yi hakan ba, sai suka mayar dani gida suka ce wai damuwa ce da gajiya, daga zaran na kwana biyu zan warware. Beenafah ce ke ta wahala dani, ta yi dani ta yi da yarana wanda a lokacin Hauka tuburan ta sameni, ina nan cikin wannan halin Sajjad ya mutu...."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!...Hasbunallahu wa ni'imal wakil..."
Aunty Labiba ta faɗa a firgice jin yan da maganar doke ta a ƙirji ba kaɗan ba.
"Uhm! Labiba kenan!...ke karan kanki yanzu kuka kike tamkar an yi miki mutuwa, to ki kwatanta da ni, shin ya zan ji a wannan lokacin?? Na gigita, na ɗimauta, na fita daga hayyacina, wanda ba shiri ya ɗauke ni zuwa Asibitin FMC, bayan mun shafe tsawon wata biyu daga nan aka tura mu zuwa Sokoto inda a can na yi jinya tsawon watanni bakwai. Bayan mun dawo. Ban haƙura ba na sake zuwa na ce masa ina so in koma ƙasarmu ya bani yarana ina so in tafi, ƙarshe ya dinga zagina yana faɗin cewa daman shi bai taɓa so na ba domin na raba shi da ɗan uwan shi, saboda haka babu inda zan je da yaranshi idan har zan tafi ga hanya.....Ba zan iya tafiya in bar su ba, hakan yasa na tafi kotu na shigar da ƙara, ƙarshe shi ne wanda yayi nasara a kaina domin ya gabatar da shaidu da dama cewa bani da lafiya ina da motsin ƙwaƙwalwa, kuma ko ba don haka ba, shi ne wanda yake da alhakin riƙe su saboda haka ina ji ina gani kotu ta bashi yaran, da na yi zancen Gadona kuma, ya kafe kai da fata yace shi bai yarda a raba gado yanxu ba tunda har bana cikin hankalina a bari dai sai na ƙara jin sauƙi domin kada watarana haukar ta sake ni in zo in ce masa ba a bani haƙƙina ba.....Labiba haka muka rayu cikin baƙin ciki da taskon rayuwa. Ta kai ta kawo sai Beenafah ta yi wanke-wanke cikin gidan Alhaji Mudassir sannan da zagi da komai Hajiya Zaliha za ta barbaɗo mana abinci ta kawo mana. Hakan yasa ciwo na sai ya yi kamar ya tafi sai kuma ya dawo. Haka ya ɗauki Beenafah da Bahrain kamar da gaske ya kaisu makarantar su Humaida, ƙarshe ko tafiyar shekara ba su yi ba ya cire su ya mayar da su wata ta gwamnati. Da farko ya kan ajiye mana buhuhuwan abinci da komai da kuɗi masu yawa. Duk yanda za su ji ina kokuwa da Beenafah basa fitowa, duk wani wanda suka san muna hulɗa ko ta gaisa wa ce sai da suka datse ta. Bahrain idan ya shiga gidan sai su yi ta zaginsa suna hantarar sa har da duka daga baya. ƙarshe a hankali ya janye duk wata hidima da yake mana ya tattara ma ya koma Abuja..."
"To amma kuma ko sau ɗaya ba ki yi attempting guduwa da su ba?"
Girgiza kanta ta yi ta ce.
"Ban yi ba. Ina ma naga lafiyar yin hakan? Ba ni da komai ba ni da ko sisi! Duk wata takarda da ta shafeni ko ta shafi Dr. Bello, ya ƙwace, ban san kowa ba banda wata mafita ba, haka muka rayu cikin ƙasƙanci tsawon lokaci, ya kankane komai ya riƙe, har inda yau ke motsi ban san mi ake ciki ba, sai lahira idan munje Allah ya bi mana haƙƙinmu.."
Jinjina kai Aunty Labiba ta yi da ruwan hawaye shaɓa-shaɓa a fuskarta ta ce.
" Amin. Amma kina nufin tun da kika baro Aden baki koma ba kenan?"
"Na koma...na yi ta zuwa lokacin da nake Canada. Sai dai kuma, zuwana na ƙarshe shi ne wanda naje a lokacin Bahrain yana da shekara biyu, amma kuma wannan zuwan bai yi mini daɗi ba a wannan loakcin, domin na samu basa nan wai sun je Qatar wurin dangin Sheikh, kuma daga nan zai ga likita domin baya jin daɗi. Ganina na ƙarshe da su shi ne wanda suka zo dubani ina da farkon shigar cikin Sajjad, kuma wani abin mamaki a wannan karon gabaɗayansu suka zo suka dubani har da su Ziyadah, to daga nan ban sake zuwa inda suke ba suma kuma ba su sake zuwa inda nake ba sai dai a Waya. Bayan wannan ƙaddarar ta gifta mana, duk wata hanya da zan bi in sadu dasu su suka san yanda suka yi suka daƙile ta har inda yau ke motsi."
Cike da jin wani irin tausayinmu Aunty Labiba ta share hawayenta tare da jinjina kanta ta ce.
" Ban taɓa jin labari irin wannan ba tun da uwata ta haifeni! Abun ya yi muni sosai... "
Jinjina kai Ammie ta yi ta ce.
" Wasu labarurrukan idan kina jin su sai ki riƙa ji tamkar a hikiya matuƙar dai ba akan ki suka faru ba ko kuma akan wani wanda kika taɓa ji ko kika taɓa gani ba. Duniya ta dawo yanzu kuɗi kawai ake bautawa. Alhaji Mudassir ya nuna mana so, so abin da ake kira so dagani har yarana, idan ya zo inda muke ko kuma muka zo rasa yake inda zai aza damu akan ɗoki da nuna mana soyayya daga shi har matarshi, Ashe wannan son Duk na GANIN IDO ne ba don Allah ba. A yanda Dr. Bello ya ɗauki Alhaji Mudassir tamkar uba da yanda shi Alhaji Mudassir ɗin ya ɗauki Dr. Bello ko a mafarki aka ce miki Zai iya cutar da iyalin Dr. Bello tabbas za ki Ƙaryata. Amma yana ganin ƙasa ta rufe masa IDO shikenan ya ɗauki rigar zalunci ya sanya ya shiga cutar damu tamkar bai san inda muka fito ba. Hatta wasu daga cikin abokansa, tun suna zuwa dubamu a hankali a hankali har suka janye jikinsu gabaɗaya tamkar ba su taɓa yin hulɗa da mijina ba. Abota da zumunci na amana a zamanin nan sun dawo na kuɗi, idan kana da ake yi da kai, idan ba kada kuɗi shikenan ka zama banza. Akan kuɗi babu abin da mutane ba za su iya ba..."
Cike da wuta a kalamanta ta kalli Ammie tana girgiza kai ta ce.
"Haƙiƙa Alhaji Mudassir bai ci bulus ba, kuskurensa ɗaya da ya barku a raye kuma ya koreku daga ƙarƙashin inuwarsa, hakan shi ne zai tabbatar masa da cewa ya yi sake da har ya bari ɗan Zaki ya girma....tabbas sai Alhaji Mudassir ya ɗanɗana kuɗarsa..."
Hannu Ammie ta ɗaga tare da girgiza kanta ta ce.
"Dan Allah na roƙeki da ki bar wannan maganar a nan da muka yi ta, shi ɗin azzaluman mutum ne wanda zuciyarsa ta bushe ba ta da wani ƙiren tausayi a tare da shi. Ni a yanzu; ko don lafiyata kaɗai dana tsira da ita da kuma freedom ɗinda yarana suka samu na gode wa Allah, kibar shi da girman haƙƙinmu da ya ɗaukar wa kansa, wallahi shi kaɗai ya ishe shi kaya ranar gobe Alƙiyama..."
"Allah sarki! Allah ya ji ƙan Dr. Bello ya gafarta masa yasa mutuwa ta zamto hutu a gare shi..."
Wani irin kyakkyawan murmushi ne ya suɓucewa Ammie tana mai jinjina kanta ta ce.
"Mutumin kirki! wanda ya ɗauki en uwansa da 'ƴa' ƴansu matsayi ɗaya da na shi 'ƴa' ƴan. Ya so ni ya kuma ƙaunaceni ƙauna ta haƙiƙa. A lokacin da na Haifi Beenafah shi ne wanda ya sanya mata wannan sunan sannan ya ce mini ita ɗin tauraruwarsa ce duniyarsa, ita ɗin 'ƴar sa ce shi ka ɗai, idan kuma ina son 'ƴa to nima na haifi tawa. A kowace shekara idan birthdaynta ya zagayo, to akwai ƙasa ta musamman da yake zaɓa mana mu tafi celebration na tayata murna, wanda har anniversary ɗinmu na ranar aure idan ya zagayo haka yake mana. Bayan na haifi Bahrain kuma, still ya ce Beenafah ce tauraruwarsa ni kuma a lokacin na cika da farin cikin samun ɗa namiji wanda shi bai ma yi wani ɗaukinsa ba kamar yanda yayi a lokacin da aka haifi Beenafah. A ranar da za'a zana masa suna na yi kuka kamar ba gobe, domin da ace na san sunan mahaifina a wannan rana da shi zan sakawa Bahrain, akan wannan dalilin ne na saka masa Suna BAHRAIN wanda ma'ana ta, shi ne ruwa biyu wato jinin Bahaushe da na Larabawa. SAJJAD kuma; Beenafah ce wacce ta saka masa domin ita ce wacce ta zamto uwa a gareshi har ya bar duniyar. Mun yi rayuwa mai cike da soyayya da kaunar junanmu, yarana sun rayu cikin gata da jin daɗin Uwa da Uba, hatta aikin Hajji da Umrah duk muka tashi tare muke tafiya wani lokacin harda Alhaji Mudassir da iyalansa baki ɗaya wanda babu abinda ya yanke mana sai a lokacin da mu ka zo ne komai ya yanke..."
Miƙewa Aunty Labiba ta yi tazo inda nake zaune ina ta rusa kuka jin yanda zuciyata ta lulluɓa da wani irin raɗadi da zafi akan irin rayuwar da muka tsinci kanmu a ciki. Ɗagoni tayi na miƙe tsaye ta rungumeni sosai a jikinta tana hawaye a hankali tana bubbuga bayana a hankali alamar rarrashi sannan ta ce.
"Da ciwo... Da ciwo sosai a rayuwarki Beenafah! Haƙiƙa kin cancanci rayuwar farin ciki Beenafah, dan Allah ki janye ƙudurinki na son taimakawa Yayana..."
A hankali na yi breaking Hug ɗin na kalleta ina jinjina kaina na ce.
"Shin ba ki ji tarihina ba a yanzu? Ni da na iya ɗauke nauyin kulawa da mahaifiyata a irin yanayin da take ciki na kuma kula da ƙannena tun ban san mine ne rayuwa ba ta ya ya kike tunanin cewa akwai wata kalar rayuwar da za ta bani tsoro a yanzu bayan na fara mallakar hankalin kaina? Mine ne sabon abu da rayuwa za ta zo mini da shi wanda ba zan iya ɗauka ba? Ba bu shi! Na rayu a gidan Mummy Zaliha tamkar wata baiwar da aka siyo domin bauta. Tunda na tsinci kaina a gidan ban san wani abu ba sai mummunar azaba da wahala. A lokacin da muke neman taimako kece kika tsaya mana kika sake bamu sabon hope ɗin rayuwa...ban dage da son auren ɗan uwanki ba wai don ƙashin kaina ba, sai dai ina da dalilina mai matuƙar ƙarfi amma kuma ba zan iya sanar miki ba a halin yanzu. Ammie ta riga ta amince da aurenmu gobe idan Allah ya kai mu, saboda haka ki tabbatar cewa kin cika mini sharaɗina auren ya zama cikin sirri har sai an kambala..."
Jinjina kanta ta yi ta ce.
" Ban isa na yi jayayya da hukuncin Allah ba Beenafah! Idan har wannan auren ya yiyu...Tabbas zan yi farin cikin da ban taɓa yin irin sa ba a duniya....Hajiya Mulaifa zan tafi.. Sai gobe idan Allah ya kaimu zamu zo da ƙarfe biyu na rana."
Jinjina kai Ammie ta yi tana mai miƙewa a tsaye ta kalle ta ta ce.
" Allah ya kaimu rai da lafiya. Wannan auren, idan har alheri ne Allah ya tabbatar mana da shi."
"Amin ya Allah."
Koda ta fice daga gidanmu har an fara kiraye-kirayen sallar Magrib. Hakan yasa muka miƙe muka tafi wurin gabatar sallahr Magrib.
Ina zaune ina Azhkar Bahrain ya kalle ni ya ce.
"Aunty Beena...wace ce wannan matar da tazo ɗazu hala? Naga sai wani koke-koke kuke da ku da ita.."
Murmushi na yi sannan na zaunar da shi muna fuskantar juna na ce.
"Ita ɗin ƙanwar mijina ce..."
Wani irin dum! Na ji a raina akan girman kalmar da na furta,sai na ji duk abin ya yi mini wani banbaraƙwai...
"Mijin ki kuma? Yaushe kika yi auren?"
"Ba'a yi,gobe dai za'a yi..."
"Yanzu kina nufin kenan ki tafi ki barmu??"
"To ai ba ni ba, hatta Ammie gobe aure za ta yi itama, shikenan za mu koma gidan Dr. Basheer na Sokoto har abada..."
"Da gaske kike Aunty Beenafah ta??"
Na share tsawon lokaci muna tattaunawa da Bahrain wanda Ammie tana zaune riƙe da counter a hannunta tana Azhkar ba ta ce mana komai ba. Sai da Yaya Hamza ya shigo riƙe da wayar Baba a hanunsa ya cewa Ammie wani ya kira yana son Magana da ita sannan muka taƙaita firar tamu.
Har yanxu da aka kawo mata wayar na lura da ita, ruwan hawayenta ba su tsaya ba. Ban damu da na binciketa waye ba domin nasan dai Dr. Basheer ne.
Bayan ta shige can Bedroom tsawon lokaci suna magana ƙarshe ta fito ta kalleni murya a ƙasa sosai ta ce.
"Dr. Basheer ya ce sun ƙara so suna Hotel a halin yanzu, gobe idan Allah ya kaimu za'a ɗaura auren da ƙarfe tara na safe..."
Shiru na yi ina nazarinta domin yanayin ta sam bai nuna wani ɗoki ko farin ciki ba, ban san mine ne a xuciyarta ba amma dai tabbas bata cikin yanayi mai daɗi.
Hijabinta ta ɗauka suka koma gidan ita da Yaya Hamza wanda bata dawo ba sai kusan sha ɗaya da wani abu na dare.
********
Washegari, ƙarfe bakwai na safe a gidanmu ta yiwa Dr. Basheer tare da mutum biyu da suka zo tare a matsayin wakilansa.
Ban san miye Ammie ta faɗawa Babansu Fakiha ba, sai gashi ya amince da shi akayi komai aka gama a masallacin Layin gidanmu.
Muna cikin gidansu Mama Baba ya shigo kamar almara ya ce an ɗaurawa Ammie aure ita da Dr. Basheer.
Kamar yanda take kuka nima haka nake yi duk da cewa ban san miye a cikin ranta ba. Waje muka dawo muka bar su a ɗakin ita da Mama da wata ƙanwar Mama suka zauna suka yi ta tattauna maganguna har misalin ƙarfe goma sha ɗaya.
Bayan an kambala komai cikin amincin ubangiji misalin ƙarfe biyu na rana sai ga Aunty Labiba ta iso kamar yanda ta yi alƙawari ita da mazaje guda huɗu waɗanda ban san su ba.
Gidanmu suka ɗunguma suka koma gabaɗaya aka sake hawa teburin sabon tsarin yan da ɗaurin auren nawa zai kasance yayin da nake kwance a kan gadon Mama ni da Fakiha muna tattauna wasu batutuwa.
Muna nan a ɗakin wanda in ban da salla babu abin da yake tadamu har da Yaya Hamza ya yi joining namu daga baya muna ta labari muna dariya tamkar babu wani abin da ya dame ni. Bayan mun yi sallar la'asar ne Yaya Hamzan ya shirya yana kallona cike da murna ya ce.
"Zanje ɗaura auren ki yarinya, saboda haka daga zaran kinga na dawo ki rugo da gudu ki lashe ƙafafuna..."
Murmushi kawai na yi tare da kawar da kaina gefe na shiga tunanin cewa wata ƙila wannan auren yayi nasara wata ƙila kuma ya faɗi. Bai fi minti talatin da fita ba sai gashi ya dawo da wani irin ihu yana faɗin.
" An zarge wata yarinya da igiyoyi guda uku masu matuƙar ƙarfi da tsawon gaske wanda ita da ta iya fitar da kanta a ciki to sai dai idan ita ce ta mutu ko kuma Engineer Muhammad Attahiru Araam ne ya mutu..."
Can gidanmu kuwa, Baba Ustaz na kiran Aunty Labiba ya tabbatar mata da cewa lallai an ɗaura ta fashe da wani irin kuka tare da faɗuwa ƙasa ta yi Sujada tana yi ta yiwa Allah kirari tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ta shiga jera addu'ar farin ciki da samun zaman lafiya da zuriya ɗayyaba.
Mamaki ne da al'ajabi ya cika su Mama ganin irin yanda take kuka tamkar wata zautacciya tana addu'a.
*******
Golden Pathways, Construction Ltd. Horizon Tower, Business Bay, Marasi Drive, Downtown. United Arab Emirates, Dubai.
A gaggauce ya shiga haɗa kayansa ta dalilin jiransa da ake yi domin tafiya ta gaggawa da ta taso masa zuwa ƙasar Mexico. Meeting ɗinda ya tsaya yi ne da wasu mutanen a office ɗin shi ne ya makarar da shi sosai.
Ya juya da nufin ɗaukar kayayyakin hannunsa sai ya ji wayarsa ta ɗauki ɓurari alamar wani yana son Magana da shi.
Yana ganin sunan Labiba ya yi wani irin ƙayataccen murmushi mai alamar Iska na wahalar da mai kayan kara sannan ya yi picking a gaggauce ya ce.
"Peace Ambassador (jakadiyar wanzar da zaman lafiya)...!"
Wani irin gigitaccen ihu ne ta doka wanda ya ke neman fasa masa dodon kunne ta ce.