Ganin ido complete Novel - Chapter 5
Ganin ido complete Novel Chapter 5: Ganin ido complete Novel Chapter 5. "Sannu Hajiya! Ya jiki? Ashe kuma wasu ƙaddarori ke ta faruwa?"
3,364 words
"Sannu Hajiya! Ya jiki? Ashe kuma wasu ƙaddarori ke ta faruwa?"
"Wallahi kuwa. Jiki mun gode Allah."
"Ubangiji Allah ya baki lafiya yasa kaffara ne."
"Amin. Na gode Allah ya saka da alheri."
Ɗayar ce ta karɓa da cewa.
"Ai Ashiru yayi mana bayanin duk abin da ya faru, abin takaici abin baƙin ciki mutumin da ya kaɗeta ko dai ya fito a mota yace Allah ya sawaƙa bai yi ba. A lokacin da ya kaɗeta dama tafiyarsa ya yi da abin ba zai dame mutane ba da ace wai sai da ya tsaya ya ga an sakata a Napep tsabar iskanci sannan ya juya ya wuce,wannan wane irin rashin imani ne?"
Take na ji takaicin mutumin nan ya dawomin sabo a raina, wanda bayan su Daddy da wasu tsirarrun mutane; shine mutum na gaba da tsana a rayuwata.
"To ya za'a yi! Tunani da hankalin mutane ya banbanta, kowa da irin yanda Allah ya halicce sa. Abu mafi muhimmanci shine tana raye bata mutu ba, Fatanmu shine Allah ya bata lafiya."
Cewar Yaya Ashiru yana mai ƙureni da kallo ganin yanda lokaci ɗaya yanayina ya canza.
Ni kuma jin wannan furucin yasa na ɗan saki raina na kalli yaran da ke wurin wanda ciki har da sa'annina da ma waɗanda suka girme mini na ce.
" Yanzu Yaya Ashiru waɗannan duk gidanku ɗaya da su?"
Dariya suka yi dukkan su sannan daga baya ya gyaɗa kan shi ya ce.
"Ƙannina ne! kin gansu su tara cif,akwai biyu da sukayi aure, bayan su kuma akwai Maza uku mata biyu waɗanda su ne yayyuna. Wa su kinga Mamansu nan, wa su kuma kinga ta su Maman nan. Kuma ita wannan...Umma muke ce mata." Cewa da maman su, sai kuma ya nuna ɗayar ya ce. " Ita kuma wannan, Ayya muke kiranta."
Murmushi na yi ina jinjina kaina na ce.
"Masha Allah. Ban taɓa ganin irin wannan familyn ba."
Cike da mamaki ɗaya daga cikin ƙannen nasa ta ce.
"Ba ki taɓa gani ba?"
Bakin gaskiyata na gyaɗa mata kaina na ce.
"Da gaske nake miki. Duk familyn da nake gani,Mama da Baba, mostly yara uku, yara biyu, highest yara biyar haka..."
"To amma..."
Da sauri Yaya Ashiru ya katseta da faɗin.
"Fa'iza ya isa haka, ku tashi mu tafi na mayar daku na koma wurin aikina."
"Ni kuma tambayata ɗaya ce, dan Allah duk wannan gashin da nake gani naki ne?"
Cewar wata ƙaramar yarinya wacce iyakarta may be sa'ar Bahrain.
Dariya muka sake fashewa da ita dukkanmu sannan na saka hannu ina ƙara janyo zaren gashin kan nawa na gyaɗa mata kaina na ce.
"Eh, gashina ne mana. Kema ai kina da shi..."
Lokaci ɗaya Yaya Ashiru ya miƙe yana faɗin.
"Ji wata tambayar shirme dan Allah? Ku tashi mu tafi please."
Jinjina kai Ayya tayi ta ce.
"Haka ne kam, ku tashi mu tafi. Allah ya ƙara bi da lafiya."
"Amin Yah Allah mun gode sosai, Allah ya saka da alheri ya bar zumunci. Allah ya mayar daku gida lafiya."
"Amin yah Allah Hajiya."
Daga haka suka miƙe suna ta yiwa Ammie addu'a na rako su har bakin gate.
Kallona Yaya Ashiru ya yi bayan sun wuce bakin Napep ɗin ya ce.
"Yaushe za ku tafi asibitin? Kin san fa an ce ku gaggauta tafiya."
Jinjina kaina na yi na ce.
"Haka ne, in sha Allah zuwa jibi zamu tafi kamar yanda suka ce."
"To Allah ya kai mu, In Sha Allahu zan zo zuwa ƙarfe shida na asuba na kai ku tashar."
"Na gode sosai Yaya Ashiru Allah ya saka da alheri ya bar zumunci."
"Ba komai Beenafah, Allah ya bata lafiya."
Bayan na dawo daga rakiyar su na zauna inda nake na ci gaba da Wankina ina ƙara girmama kirkin Yaya Ashiru da familynshi. Daman ashe akwai family irin haka mai yawa da suke rayuwa so simple. Ga shi dai haɗuwa ɗaya tasa tamkar mun yi shekara da sanin juna.
***
Daren da ana gobe zamu tafi Sokoto Sai misalin ƙarfe tara na fita na je wurin Baba mai shago na ce ya kira mini Daddy sanin cewa wannan lokacin shi ne lokacin da na saba samunsa a gida,sai dai kiran duniya an yi amma yaƙi ya ɗauka kuma bai kira ba har kusan tara da arba'in na dare.
Tsintar muryar Baba mai Shago na yi yana faɗin.
"Beenafah ya ƙi ya ɗaga wayar nan fa. Ya kamata ki koma gida hakanan,ki faɗamin koda ya kira daga baya mi zan faɗa masa?"
Jiki sanyaye na ce.
"Kawai ka ce mishi Beenafah ce ta so ta yi magana da shi kuma ta koma gida."
Daga haka na juya jiki a mace na fara tafiya, ina kan hanya ina tafe ina lissafi, abubuwa duk sun isheni, lissafin kuɗi na shiga kamar wata zararra, gaba ɗaya kuɗinda ke account ɗinmu sun tafi, har so na yi na ce ayi mini checking balance amma tsoro hanani. Ga term ya yi na biyan kuɗi both islamiyya da boko dole zan yiwa Bahrain registration kamar yanda nayi last term, ko yanzu idan har Daddy bai tallafa mana ba, kuɗin nan sai mun wayi gari ba ko sisi, dole mu tattala su mu shiga yin sana'a da su kamar yan da Aunty Husaina ta shawarceni....
Ina cikin tunane-tunane ban ankara ba kawai na ji habshin Kare da gudu ya biyo ni, ba shiri na shiga falfalawa ina mai fashewa da kuka domin na tsani kare a rayuwata, ina tsoronsa sosai ko ganin sa idan nayi hankalina ta shi yake. Ina hango wa su mutane bakin wani gate da alama masu gadi ne, suna zaune a benci na nufe su ba shiri, wurin na tsallaka lambatu zuruf na faɗa ciki gwiwata ta bugu haka ɗan yatsan ƙafata.
Take ɗaya daga cikin su ya ɗaga sandarsa ya kori Karen sannan suka yo kaina a tare mai sandar ya miƙa mini hannu na fito ina ta kuka suna ta faman yi mini sannu.
"Ke ko yarinya ina za ki je da daren nan?"
Cikin sheshsheka na ce.
"Gi...gig..gida zan tafi."
"To ina ne gidan na ku?"
"Wan can titin na baya."
"To muje."
Ba musu na shiga gaba shi kuma ya bi ni a baya bai tsaya ba sai da muka kai ƙofar gida ya ga na shiga sannan ya koma. Tsayawa na yi na yaga gefen ɗankwalina na ɗaure babban yatsan ƙafata da ya kwaile yana zubar jini, sannan na duba gwiwata ta dama wadda naga itama ta goge sosai.
Bakin famfo na je na wanke fuskata na goge da hijabina sannan na shiga gidan, ina gudun kada Ammie ko Bahrain wani ya ga yanayina kuma ban so hankalin su ya tashi.
Gaba ɗaya daren ranar ban yi wani baccin kirki ba kasancewar raunukana da suka kwana suna mini azabar zogi da raɗaɗi, sai da na lalaɓo Rub na shafa nasha maganin ciwon jiki sannan na ɗan samu sauƙi.
***
Katamfe Extension, FCT Abuja, Nigeria.
Daddy yana zaune a cikin sabon gidansa da ya saya ya sake renovating kira ya shigo wayarsa, kamar ya san cewa Beenafah za ta sake kiransa da wannan numbern sai ya yi saving ɗinta. Yana ganin sunan da ya yi saving da ita ya buga tsaki ya mayar ya ajiye.
"Alhaji, Hafiz ya ce mini ya yi ta kiran ka amma ba ka ɗaga ba, lafiya kuwa?"
Cewar Mummy dake shigowa ɗakin yanzu ɗauke da trayn slize fruit a hannunta. A hankali ta ajiye saman glass center table ɗinda yake gabansa sannan ta samu wuri cike da ƙasaita ta zauna a kusa da shi.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce.
"Wallahi ban lura ba, da yake Beenafah ce ta tasani a gaba da kira shine na ajiye wayar, to ina ga lokaci ɗaya kiran ya shigo da na ta."
Wani irin ɓata rai ta yi ta ce.
"Ita kuma da kullum kwanan duniya ba ta gajiya da ɗorawa mutum lalura, kamar gare su babu ta yanke cibi. Shegiyar yarinya kawai. Mts!"
"To yanzu dai ai an kai ƙarshe, bata ganni ba, waya kuma sai idan na ga damar yin picking zanyi. Miye Hafiz ɗin ya ce?"
"A'a, cewa ya yi yanata jiranka baka aika masa da kuɗin ba tun jiya."
"Kash! Wallahi kinga kuwa na manta ne, amma gobe In Sha Allah zan tura masa."
"Allah ya kaimu."
Suna nan a zaune suna fira sai ga su Husaina sunyi sallama sun shigo,bayan sun gaishe da su suka samu wuri suka zauna.
Kallon su Daddy ya yi ya ce.
"Ya na ganku duk kunyi wani iri? Any problem?... Uhm! Hassana, miye matsalar?"
Ɗan yatsina fuska Hassana ta yi cike da mulki ta ce.
"Ni Daddy problem ɗina ɗaya ne, ni dai bana son driver yana kai mu school, na fi so a bamu mota mu riƙa zuwa da kanmu, wallahi most of our friends duk da Mota suke zuwa da kansu..."
"Drivern yana da matsala ne?"
"Eh Daddy, baya zuwa da wuri, ko yau har kusan magrib muna hanya, ga shi wani irin baƙauye da shi Daddy, ni wallahi yana kofsa mana..."
Mummy itama dai taɓe bakin ta yi ta ce.
"To Allah na tuba daman wanda ya girma a ƙauye bai taɓa zuwa gari irin Abuja ba ai dole ya yi ƙauyanci wallahi. Ni fa, ko Biba don dai ta iya aiki ne kuma Humaida na sonta kawai yasa na ke zaune da ita, amma da ba don haka ba wallahi banga dalilin da zai hana na koreta ba. Saboda haka, Alhaji kawai ka yi musu yanda suke so su ma su shiga cikin tsara su kece rai ni kamar ko yaushe."
" To shikenan, gobe idan Allah ya kaimu zan ce ya damƙa mu ku key a hannun ku... "
Cikin shagwaɓewa Hassanar ta ce.
" Haba Daddy dan Allah! Nile University fa! ... Ni gaskiya wannan motar ta yi mana local da yawa sai dai a saya mana sabuwa er yayi.."
"To kar ki damu in sha Allahu gobe-goben nan za'a kawo muku sabuwa...."
Daga haka ya mayarda kallon shi gun Husaina wacce tayi tuƙun-tuƙun da rai tun ɗa zu ya ce.
"Husainata ya dai? Ko ke wannan tsarin bai miki ba?"
Girgiza kanta ta yi cikin yanayin ta na ko in kula ta ce.
"Ba komai Daddy, ni duk wannan baya gabana, fatana shine Allah ya bamu sa'a. Duk yan da akayi dai-dai ne."
Tsaki Mummy ta ja tare da girgiza kai ta ce.
"Shashasha kawai, marar wayau."
Daga haka suka koma firar su hankali kwance suna nishaɗi.
***
Ƙarfe shida na safe a ƙofar gidanmu ta yi wa Yaya Ashiru kamar yanda ya yi alƙawari.
Hankali a tashe ya kalleni ganin yanda nake ɗingishi ya ce.
"Beenafah lafiya? Miye ya sameki a ƙafar?"
Murmushi na yi na ce.
"Wallahi tsautsayi ne, jiya da dare ina tafiya ban lura ba na faɗa lambatu."
"Dan Allah ki riƙa kulawa kinji ko? Allah ya ƙara tsarewa."
"Amin, na gode."
Bayan mun isa Tashar, da kan shi ya shiga layi ya amso mana ticket ɗin motar da zamu hau.
Bayan ya bani a hannuna ya kalle ni ya ce.
"To amma Beenafah miyasa za ku tafi da Bahrain? Karatun sa fa yana samun cikas sanadin wannan uzururrukan? Sannan yanzu ba'a san odar dawowar ku ba"
"Hmm! To Yaya Ashiru ya zan yi? Dole na tafi da shi domin bani da inda zan bar shi..."
Kai tsaye ya ce.
"Wannan karon ki bar shi a hannuna mana, sai na kai shi gida wurin su Umma.."
Da sauri na girgiza kaina na ce.
"A'a. Gaskiya ba zan iya ba..."
Cikin nuna zallar mamaki ya ce.
"Beenafah ba ki yarda dani ba ne?"
Ɗan guntun murmushi na saki sannan na girgiza kaina na ce.
"Ba haka bane Yaya Ashiru.."
"To idan ba haka bane miye ne? Ki bani shi, na yi miki alƙawarin kai shi islamiyya kullum tare da boko. Na kai shi na dawo da shi har ku dawo. Dan Allah ki yarda dani."
"Ka yi haƙuri Yaya Ashiru, amma ba zan iya barin Bahrain ako'ina ba."
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace.
"Shikenan. Allah ya tsare ya kai ku lafiya yasa kuma a dace."
"Amin. Na gode sosai."
"Ina wayar hannunki?"
Cirowa na yi na miƙa mishi. Nan naga ya buɗe wayarsa ya ciro simcard ya saka ya kunna sannan ya miƙo mini ya ce.
"Ɗayan MTN ɗina ne na saka muku, zan kira ki In Sha Allahu."
"Na gode sosai Yaya Ashiru, na gode."
Kallon Bahrain ya yi ya ce.
"Bahrain! Allah ya tsare ka ji ko? Allah ya bai wa Ammie Lafiya."
"Amin Yaya Ashiru, sai na dawo."
Har ya juya zai tafi, a hankali na kira sunan sa ya juyo idanuwana cike da ruwan hawaye na ce.
"Na gode Yaya Ashiru.."
Da murmushi a fuskar sa ya kalle ni ya ce.
"Ke! Miye kuma abun kuka a nan? Ki tabbata kin ajiye wayar a kusa dake zan kiraki."
"To Yayana na gode, ina gaida Umma da Ayya, da Fa'iza..."
Dariya ya fara mini yana gyaɗa kai, jin nayi shiru ya sanya shi cewa.
"En hen! Da Fa'iza... Da wa kuma?"
Dariyar nima nayi na ce.
"Da wacce ta tambayeni cewa gashina ne.. Da ma sauran da ban sani ba."
"To duk za su ji In Sha Allahu. Bye-bye, Allah ya tsare."
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa*
*FREE-BOOK*
*PAGE 8*
Muna isa suka tarbemu kamar yan da aka saba suka kai ta Female Psychiatric In-patient Ward. Nan take suka fara assessing nata wanda Dr. Kenna ne da sauran nurses suka duƙufa akanta tare da likitocin orthopaedic na Psychiatric hospital ɗin.
Bayan sun gama bata duk wani taimakonda ya kamata, Dr. Kenna ya kirani zuwa Office ɗinsa wanda ya kasance cikin manyan likitocin da suke kulawa da ciwon Ammie. Tare da Bahrain muka shiga Office ɗin muka zauna.
Bayan ya gama duk rubuce-rubucen da zai yi ya rufe ya kalleni ya kira sunana a hankali da cewa.
"Beenafah!"
Ɗagowa na yi na kallesa na ce.
"Na'am Likita."
"A yanzu mun duba mahaifiyarki, kuma Thank God her condition was stable now and it's improving. Magana ta gaskiya mahaifiyarki tana buƙatar cikakkiyar kulawa ta ƙwaƙwalwa tare da ci gaba da kula da karayar da take hannunta dama kuma sauran abubuwan da duk suka danganceta da ku gaba ɗaya. Because of this reasons, dole za ta zauna a nan aƙalla tsawon wata biyu zuwa uku. Idan ta ci gaba da yin responding da kyau ta hanyar magunguna da Psychological support, za mu iya ba ku sallama da shawarwarin yan da za'a ci gaba da kulawa da ita kamar yan da aka saba idan kuka koma gida..."
Nan dai ya ɗauki tsawon lokaci yana mini bayani da ƙarin shawarwari da kuma hanyoyin da zamu bi wurin ganin ciwon nata ya warke baki ɗaya.
Cikin ladabi bayan ya sauke maganarsa na gyaɗa kaina, zuciyata cike da fargaba na ce.
"Mun gode sosai Dr. Kenna, In Sha Allah zamu yi iya ƙoƙarinmu."
"Yauwa... Yanzu ga wannan." Ya ƙarashe maganar yana miƙo mini takarda, bayan na karɓa ya ce.
"Yanzu za ki je ki biya wannan kuɗin, mun riga mun yi amfani da duk abinda muke buƙata a yanzu."
"Ok to. Na gode."
Tare da Bahrain muka fito ina riƙe da hannun sa wanda muna tafe ina duba takarda wacce ke ɗauke da abubuwan da ya ce sun yi amfani da suka kama dubu tamanin da bakwai da ɗari huɗu.
Haka muka ci gaba da zirga-zirga har dare sannan muka je inda aka tanadarwa patient relatives, domin idan suna ɗakin jinya akan magani to ba'a barin kowa tare da su sai malaman jinya kawai. Shimfiɗa muka yi muka kwanta misalin sha biyu saura na dare bayan munyi addu'a.
Jim kaɗan da kwanciyata na ji abu na zuuu! A ƙarƙashin jakar kayanmu da na dunƙule na ɗora kaina na yi matashi da ita. Tashi na yi na buɗe jakar na tarar ashe waya ce ke ringing wacce shaf! Na manta da ita.
Koda na ɗauko kiran ya riga ya yanke. Ina dubawa naga 32 miss calls wanda na tabbatar ba kowa bane illa Yaya Ashiru kuma wallahi bakin gaskiyata na manta da ya saka wani simcard a wayar. Ina kan mayar da wayar a jaka na sake jin wani ringing ɗin yana tashi.
Ɗauka na yi na kara a kunnena tare da yin sallama na ce.
"Yaya Ashiru...."
"Haba Beenafah dan Allah! Duk kin ɗaga mini hankalina, tun kuna hanya nake kira ba'a ɗaga ba sai yanzu."
"Allah sarki Yaya Ashiru! Ka yi haƙuri dan Allah, ni wallahi na manta ma da wani zancen waya."
"Ok. Da fatan kun isa lafiya?"
"Lafiya ƙalau muka iso Yaya Ashiru, har an bata gado an duba ta. Kuma Alhamdulillah Likita ya tabbatar mini ana samun sauƙi sosai."
"To masha Allahu, na ji daɗin wannan labarin, Allah ya bata lafiya."
"Amin yah Allah."
"Ina Bahrain?"
Ɗan leƙa fuskar sa na yi kaɗan sannan na jinjina kaina na ce.
"Gashi nan a gefena ya yi bacci."
"To Ki kula kin ji ko?"
"In sha Allahu Yaya Ashiru na gode sosai da kulawa."
***
Satinmu biyu a asibitin aka cire mata POP ɗin hannunta da aka yo mata aikinsa tun daga Gusau, bayan sun tabbatar ƙashin ya soma haɗuwa aka sake yi mata physiotherapy domin kada hannun ya samu matsala,kuma Alhamdulillah komai yana kan tafiya dai-dai, sauƙi sai ƙara samuwa yake.
Bayan munje mun biya kuɗi muka samu wani wuri a farfajiyar asibitin muka zauna munata kallon yadda mutane ke ta zirga-zirga. Idan an wuce da wannan kalar marar lafiyar Jim kaɗan za ka ga an wuce da wani wanda matsalar shi ta fi na ɗa zu.
Tun da muka zauna nake hankalce da yanayin Bahrain, sosai ya shige gashi, cike da nutsuwa yake kallon kowane patient da aka wuce da shi. Jinjina kaina na yi na ce.
"Bahrain ka gani ko? Hakan ya ƙara tabbatar mana da cewa ba mu kaɗai ke fama da irin wannan jarabawar ba. Sai mu godewa Allah domin ko a cikinsu yanayin Ammie yana da sassauci sosai. Kuma In Sha Allahu duk ranar da Allah ya ce ta warke gaba ɗaya za ta warke da ita da ma sauran ma su jinyar baki ɗaya. Addu'armu Allah ya ƙara ba su lafiya baki ɗaya ya yaye musu wahala...."
"Aunty Beenafah da gaske Ammie kenan za ta warke kaman yan da Dr. Basheer ya ce mana jiya ko?"
Murmushi na yi mai sauti ina jinjina kaina na ce.
"Sosai kuwa Bahrain, In Sha Allahu.."
"To Aunty Beena daga zaran ta warke da gaske muma za mu koma Abuja inda su Humaida?"
Tamkar ya kwaɗa mini guduma a tsakiyar kaina haka na ji saukar kalamansa lokaci ɗaya. Kwata-kwata ban yi tsammanin wannan tambayar ta sa ba a wannan lokacin.
"Aunty Beena..."
"In Sha Allah Bahrain, kada ka damu watarana muma zamu je har ma gaba da Abuja..."
Cikin zumuɗi ya ce.
"Da gaske Aunty Beena? Ina kenan?"
Hannunshi na jimƙe a na wa ina mai ɓoye hawayena tare da ƙirƙiro wani murmushi na ce.
"Ni ma ban sani ba Bahrain, amma In Sha Allah idan har ka yi ƙwazo sosai a makaranta to watarana tabbas wannan mafarkin naka zai cika...."
Shekarar Bahrain goma a duniya amma wallahi idan ya yi mini wata tambayar rasa nake yanda ma zan yi na amsa masa tambayar. Haka muka zauna yana ta mini tambayoyi wanda ban yi nasarar tserewa daga gare su ba sai da kiran Yaya Ashiru ya shigo wayar hannuna wanda shima mun jima muna magana da shi sannan daga ƙarshe na yanke wayar bayan mun gama.
Yaya Ashiru mutumin kirki ne wanda ban taɓa haɗuwa da irin sa ba a duniya kuma har na mutu ba zan sake haɗuwa da mai kirkin sa ba. A yanzu yana daga cikin manyan ginshiƙan da suke taka muhimmiyar rawa wurin ci gaban farin cikinmu. Duk da cewar baya tare damu, muryar sa kawai da hikimar iya zancen sa a waya tana wadatarmu. Wata irin shaƙuwa ce ta shiga tsakaninmu wanda a kullum sai mufi hour muna magana a waya, bama kamar idan dare yayi, sai mukai kusan sha biyu muna fira har sai idan ya ji alamun bacci ya fara kamani sannan zai yi mini sallama ya kashe wayar.
***