Ganin ido complete Novel - Chapter 54
Ganin ido complete Novel Chapter 54: Ganin ido complete Novel Chapter 54. " Thank you Bibi...Allah ya yi miki albarka. Allah ya ƙara mana zaman lafiya da…
3,346 words
" Thank you Bibi...Allah ya yi miki albarka. Allah ya ƙara mana zaman lafiya da kwanciyar ya bani ikon faranta miki a koda yaushe...In Sha Allahu na yi miki alƙawarin ba zan ƙara damuwa da komai ba."
Murmushi na masa ina mai jinjina kai na nace.
"Amin Yah Allah. Allah ya tsare ka, ya kai min lafiya ya dawo da kai lafiya..."
"Amin. Suhaib ya sanar mini jiya cewa zai zo. To na ce ya bari sai na sanar miki tukunna..."
A mamakance na ce.
"What? Sai ka sanar mini fa ka ce?"
"Yeah! Ai kece mai gida. Yanda kika ce haka za'a yi."
Ina wani irin murmushi na jinjina masa kaina na ce.
"To na amince ya zo dan Allah...kada fa kasa Hairi ta yi fushi dani..."
Dariya ya yi ya ce.
"Ba za ta yi ba ai. Domin ta san cewa you won't hurt her.."
"Allah ya tsare, bare na je kada na saka ka kayi latti."
Daga haka na sauka da kaina na rufe masa motar sannan drivernsa ya shiga suka wuce.
Har na shige ciki ban daina murmushi ba, hakan yasa ni ban ma lura da fitowar Hairiyyar ba sai da naji tana dariya a bayana. Waigowa na yi ina ƙara faɗaɗa murmushina na ce.
"Miye kike a nan ɗin??"
Tana dariya ta ce.
"Soyayya daɗi ko Aunty Beenafah? Kuna son juna sosai...Daddy yana matuƙar ƙaunar ki."
Bansan lokacin da wani irin kyakkyawan murmushi ya suɓuce min ba sannan na jinjina mata kaina na ce.
"Ni ma haka Hairi...ina matuƙar ƙaunarsa a raina..."
Tana wani irin blushing ta jinjina Kanta ta ce.
"Ina jin wani abu makamancin haka a kan Suhaib Aunty Beenafah...sati biyu kacal! Amma soyayya nema take ta zautar da ni..."
Dariya na fashe da ita cikin sigar zolaya na ce.
"Ga Soyayya ga exams jibi. Wanne za'a fasa daga ciki? Idan kika zaɓi exams Suhaib zai ji wani iri, idan kuma kika zaɓi Suhaib kika bari soyyaya ta saka kika faɗi exams Daddy zai ci ƙaniyar mutum..."
Dariya ta fashe da ita tana wani girgiza kai ta ce.
"Amma dai gaskiya Aunty Beenafah kin min ɗaya...shi ne za ki bini da bad thought..maimakon ki ƙarfafa ni? Soyayyar nan fa yanzu na fara ta..."
"Da gaske?"
Na tambaye ta ina mai bin ta da wani irin kallon mamaki domin sai nake jin kamar ma ban yarda da ba ace wai bata taɓa yin soyayya ba.
"Wallahy Saurayina guda ɗaya ne Khaleel, kuma kullum muyi faɗa mu shirya muyi faɗa mu shirya haka muke. Duk da cewa muna da buri watarana muga munyi aure...to Amma shigowar Suhaib a cikin rayuwata, yanayin daban ne Aunty Beenafah, ina jin wasu abubuwa a raina wanda ban taɓa ji akan Khaleel ba..."
Jinjina kaina na yi ina murmusawa na ce.
" Hakan shi ne mafi alheri a gare ki In Sha Allah. Allah dai ya nuna mana lokaci lafiya. Shin nan da shekara biyu aka ce ko?"
Bata san lokacin da ta maka min wata uwar harara ba tace.
" Wai ma! Kafin azumin nan fa, shekaranjiya na ji Daddy yana magana da Baba Ustaz yana shaida masa..."
Waro ido na yi ina dariya na ce.
"Kambu! Yau Hairi ni za ki harara akan Suhaib? Ya yi kyau! Bari na kira Daddy na faɗa masa.."
Da gudu ta faɗo jikina tana mai rirriƙeni cike da magiya tana dariya ta ce.
" Na shiga uku! Wai daman hararen ki na yi Mummy? Please forgive me...ba zan sake ba. Ba laifina ba ne laifin soyayyar IG SUHAIB ce....ki yi hak'uri dan Allah...Yo idan kika faɗa wa Daddy ai na san daga yau sai dai na nemi wani gidan uban ba wannan ba..."
Dariya muka sake fashewa da Ita sannan na ce.
" To na ji. Sake ni naje na yi wanka. Kin ci abinci? "
Girgixa kanta ta yi tana mai janye jikinta daga nawa ta ce.
" Nima tashina kenan, wanka kawai na yi."
"Ok...bari na yi wanka na fito."
"To miye abin da za'a yi wa Suhaib ɗin?"
Waigowa na yi na ce.
"Na me kenan?"
"abinci haka...yanda za'a tarbeshi"
Girgiza kaina na yi ina dariya na ce.
"Bari na yi wanka na fito, sai mu shiga kitchen ɗin mu gani."
"OK!"
*******
Gefen su Aunty Labiba kuwa, koda suka koma gida har Ziza tana gidan, ta dawo kamar yanda Emraan ya sanar mata cewa ta shirya ta dawo gida kafin ya iso.
Sun yi matuƙar kaɗuwa da suka ji Ziza na jajanta musu abin da ya faru. Wato Hajiya bata ji duk abin da ake faɗa mata ba? Idan ba shi ba miye na zuwa ta faɗawa Ziza wannan abun dan Allah?
Duk yanda suka nuna mata rashin jin daɗinsu ita ko kaɗan hakan bai dame ta ba, domin a yanzu ta yarda cewa faɗin gaskiya da kuma tsayawa akan gaskiya yafi komai daɗi da sa mutum ya kasance cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Ziza ma ai yanzu ita ɗin cikin dangi take, ya kamata duk abin da ake ciki a riƙa sanar mata domin ɓoye-ɓoye ba shi da wani amfani.
Bayan Nadeeyah ta koma Kaduna da kwana Biyu Labiba ta zo gidan sanadiyyar kiranta da Emraan ya yi.
Tana shigowa ta tarar da su zaune, Hajiya, Ziza da kuma Emraan ɗin.
Zaunawa ta yi ta gaishe da Hajiya sannan suka gaisa da Ziza ta kalli Emraan ta ce.
"Ina fata lafiya?"
Jinjina kansa ya yi yana mai yin ɗan guntun murmushi ya ce.
"Lafiya ƙalau. Kawai ina so muyi wata Magana ce mai muhimmanci....and..i call the presence of you ne don ku zama shaida akan maganganuna....Tun jiya da na shaidawa Ziza zancen aurena ta hana min sukuni take ta tashin hankali. To abin da nake so ku ji ku kuma shaida...wallahy tallahy ba ta isa ta hanani yin abin da raina yake so ba. Zan ƙara maimaitawa a gaban ku. Zan yi aure ba don na gaji da ita ba, zan yi aure ba don tana min wani laifin ba, ina son ta. Amma kuma ba shi zai hanani ƙara aure ba. Ku ja mata kunne ta kiyaye, bani da niyyar cutarwa a gareta, Idan ta bani haɗin kai lafiya ƙalau za mu zauna kamar yanda Suwara ta bani kalaman ta..."
Wani irin kuka ne mai ƙarfi ya ƙwace mata jin sunan Suwara da ya ambata wanda tun a daren jiya wannan sunan ya tsaya mata a ƙahon zuciya. Bata san lokacin da ta shiga Girgixa kanta ba tana faɗin.
" Wallahy Hajiya Emraan baya sona. Ina murna cewa tun da ya rasa Beenafah shi kenan ya haƙura, yanzu kawai rana tsaka kuma ya dawo min da wani zance na auren wata banza er Sudan..."
"Ziza ki daina kiran er uwata da banza! Tun Jiya na yi warning na ki akan ki kiyaye kalaman ki a Kanta domin Ita ɗin er uwa ta ce...Ziza idan fa kin so zaman lafiya zamu zauna mu ma fi ruwa zaman lafiya. Idan kuma tashin hankali kike nema to sai dai ki tafi can gidanku ki Ƙarata. Sannan kada ki manta...wan can lokacin da kika tafi gida, kin dawo gidan nan ne bayan Yaya Mohaa ya dawo dake...to kuma a yanzu ki fahimta...ita wannan ɗin ƙanwarsa ce. Ba lallai ya tafi don dawowa da ke ba. Idan kika sake tafiya da sunan ya ji, ki ɗauka cewa mun rabu kenan na har abada, domin ni ba zan ɗauki wannan ba..."
Kallon shi Aunty Labiba ta yi cikin tsantsar mamaki ta ce.
" Haba Emraan! Miyasa za ka nemi tsaurara kalaman ka haka? Ita ɗin fa macece, kuma kishi gaskiya ne...ko ma miye ai dai kana ɗaga mata ƙafa ko don yanayin ta tunda kasan ciki ne da ita...wai miyasa ku maza baku da adalci ne wani lokacin..."
Cikin jin wani irin ɓacin rai ya shiga jinjina kansa yana faɗin.
" Shin yanzu Labiba kina goyon bayanta ne ni kuma kina ɗora min laifi ko ya ya?"
" Eh! Idan ma hakan ka ɗauka Hakane! Idan har ka kira mu ne a matsayin na gaba da ku domin neman maslaha ai ba cancanta ka riƙa magama irin haka ba. Kishiya fa za ka mata, to sai ka dake ta ka hana ta kuka...ka bari abi komai a sannu mana.."
Miƙewa ya yi yana wani irin huci tamkar wani kumurcin maciji akan ɓacin rai ya fice ya bar musu parlourn.
Itama Ziza yunƙurawa ta yi a hankali ta tashi ta wuce ɗakinta ta bar su nan su biyu tana ta kuka. Abu ne ya game mata goma da ashirin, gidan Iyayenta sun haɗe mata kai nan ma sun haɗe mata kai babu mai ganin laifin shi sai na ta ake gani saboda tsabar son zuciya.
Kallonta ta mayar gun Hajiya tana faɗin.
" Hajiya wai kin yi shiru ba ki ce komai ba?"
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali sannan ta ce.
" To Labiba mi zance? Emraan ya ƙi ya saurareni, sannan itama Ziza taƙi ta kwantar da hankalinta. Shin duk abin da zaman lafiya bai bayar ba dan Allah tashin hankali na bayar da shi? Tun a wancan lokacin da ya ke neman Beenafah nake ta tausar mata zuciya bata saurare ni ba. Idan tace ba za ta iya haɗa miji da Beenafah fa to ita wannan ɗin miye aibinta? Sam bana son wani abin da zai kawo musu ɓaraka a tsakanin auren su, to amma dukkan su babu wanda za ki faɗa masa ya ji."
" A a kam! Bari na je na yi mata magana.."
Tana gama faɗar haka ta tashi ta bita har sashenda take inda ta cimma ta zaune a ƙasa ta miƙe ƙafafunta sannan ta ɗora kanta akan gefen kujera tana kuka.
Zaunawa ta yi gefen ta a hankali ta kira sunanta.
Ɗagowa ta yi ta kalle ta kawai ba tare da ta amsa ba.
"Ki na ji ko Ziza...ita fa rayuwar nan cike take da ƙalubale akoda yaushe...ƙarfin imaninmu da haƙurin mu shi ne zai ɗoramu akan ta har mukai ga yin galaba a kanta Watarana. Kin auri Emraan akan kina sonsa kamar yanda shima ya aure ki akan yana son ki...kuma har yau har gobe,har abada nasan a wannan tafarkin kuke so ku kasance har zuwa numfashinku na ƙarshe. Tun da kuke da shi ba ku taɓa samun wata matsala ba, domin kuna son juna kuma kuna bin hanyoyi domin kiyayewa. To ina so kisan cewa aure a wurin namiji zuwa yake, lokaci ne kuma idan har hakan ya kasance to ki yarda cewa yana daga cikin zanen ƙaddarar sa......Wani, da mata ɗaya yake rayuwa har ya mutu, wani da mata biyu, wani uku wani kuma huɗu. Duk cikin su babu wanda Allah yace ya saɓa ko ya kauce hanya. Tun da har kika ga cewa mijin ki ya zaɓi cewa ya auri Wata bayan ke, to ki zama mai haƙuri ki amshi wannan ƙaddarar. Koda ace ran ki baya so ki yi haƙuri ki bai wa zuciyar ki magana. Ki daina ɗaga masa hankali kina ɗagawa kan ki. Idan fa suna cikin giyar neman auren nan wallahy ko mutuwa za ki yi ko kaɗan ba zai ji cewa zai iya fasawa ba. Ke a lokacin da kike hauka shi a lokacin ji yake tamkar kina ƙara tura sa ne cewa yaje ya yi. Bari na faɗa miki wani sirrin da baki san da shi ba Ziza. Idan Kika nuna kin yi farin ciki kuma kin amsa hannu biyu, wallahy tallahy kunyar ki zai riƙa ji kuma za ki ƙara miki girma da daraja a idonsa, duk abin da zai yi sai ki ga sai ya nemi shawarar ki, duk abinda kika ce shi za'a yi. Amma idan kika nuna hauka da rashin haƙuri, to shi kuma a lokacin zai dinga fito miki da hanyoyin na rashin mutunci domin kawai ya ga kin Ƙuntata...dan Allah Ziza ba don ni ba, don Allah Ziza ba don Emraan yana ƙanina ba. Ki yi hak'uri ki kwantar da hankalinki ki bari ku zauna lafiya. Kin ce bakya son kisantaka da Beenafah, yanzu ma kince bakya so da wannan, tun yana neman abin ƙwarai har sai kin sa ya kai watarana ga nemo miki abin da zai fi ƙarfin ki."
Jinjina kanta ta yi tare da share Hawayenta ta ce.
" Na gode sosai Aunty Labiba. In Sha Allahu zan gwada amfani da wannan shawarar in gani ko zan iya.."
Cike da murmushin nasara ta jinjina Kanta ta ce.
" Na gode sosai da kika fahimce ni. Allah ya baku haƙuri ya baku zaman lafiya...Ziza! Ba wai ina faɗa miki haka ne don GANIN IDON ki ba, har cikin zuciyata nake faɗa miki waɗan nan kalaman, domin kamar yanda kike kallona a matsayin dangin mijinki, nima ɗin dangin mijin wasu ce, idan har har na cutar da ke, to nima zan iya haɗuwa da kalar nawa ƙalubalen wurin nawa dangin mijin."
Daga haka ta miƙe ta fice daga ɗakin ta koma tana ta kiran Emraan a waya amma bata samun sa. Hakan yasa dole ta hak'ura ta fita kitchen wurin su Munira.
Suna ganin ta suka ta so suka gaishe da ita sannan ta ce.
" Kun kaiwa Ziza abinci yau kuwa?"
Girgiza kai Haulatu ta yi tace.
"A'a. Bamu kai mata ɗaki ba, mun dai jera a table..."
"To ku haɗa mata please ku kai mata a ɗaki. Kuma ku riƙa lallaɓawa da ita musamman kunga yanayinta a yanzu dole sai haƙuri."
"In Sha Allahu Aunty."
Murmushi ta yi tana kallon Munira ta ce.
"Munira har yau baki taɓa tambayata ƙawar ki ba."
Ai kuwa, tamkar ta sosa mata wurin da yake mata ƙaiƙayi, bakinta har yana rawa wurin furta.
"Wallahy Aunty Labiba Beenafah tana ranmu, mun kasa mantawa da ita, kuma bamu san a ina take ba. Ranar ma da muka matsawa Oga Sule shine ya ɗaukemu ya kaimu gidan su amma sai aka ce mana sun tashi daga nan."
Jinjina kai ta yi ta ce.
"Tabbas sun tashi. Amma ta yi aure ta auri Daddy, tana zaune a Dubai yanzu haka a tare da shi...."
Tamkar idanuwansu za su zazzago su faɗo ƙasa, haka suka riƙa kallonta da wani irin maɗaukakin mamakin da ya hana musu ma yin magana.
"In Sha Allahu watarana za su zo, za ku ganta."
Cikin nuna farin ciki Munira tace.
"Allah ya ƙaddara ya nuna mana wannan lokacin...hmm! Allah mai iko da Buwaya! Yanzu Beenafah ita ce ashe ta auri Daddy? Allah ya sanya alheri da albarka ya bada zaman lafiya."
"Amin."
Juyawa ta yi ta koma ciki yayin da suka shiga yin aikin da ta basu suna yi suna firar Beenafah cike da farin cikin irin mijin da ta samu. Tambayar kan su suka shiga yi cewa ko ya akayi hakan ta kasance?
*******
Gefen su Daddy kuwa. A hankali ya shiga warwarewa lafiya na samuwa har ya murmure baki ɗaya.
Sai dai kuma, abubuwa sun juye musu fiye da tunaninsu, komai ya lalace musu wanda hatta abincin da za su ci, Salman ne da Ahlan ke ɗauke da nauyin abincin su da ma wasu sauran buƙatocin rayuwa.
Humaida ma sun samu wata private school wacce ba mai tsada sosai ba suka mayar da ita wanda babu watarana da za ta zo ba tare da ta yi kuka ba.
Aunty Aysha tana nan a tare dasu bata koma ba, amma Ita Hassana daman ba su jima da dawowa Gusau ɗin ba ta koma garin Mijinta, amma kullum tana biye da su da labarin duk wani motsin su.
Husaina kuma tana nan tare da Fahil wanda jira suke Daddy ya ƙara warwarewa ya turo magabatansa. Rayuwar su yanzu gabaɗaya ta yi sanyi sosai kamar ba su ba. Musamman Daddy da ya koma wani abin tausayi kullum yana riƙe da carbi a hannun sa yana tasbihi, daga zaran ka kalleshi sau ɗaya sai ya baka tausayi. Aysha da Husaina sune ke ta hidima da su. Yau ma Aysha na zaune a bakin rijiya tana wanke musu kayan su suna firar Fahil da Husaina sai ga Mummy ta fito daga ɗaki ta kalli Aysha ta ce.
"Aysha!"
Ɗagowa ta yi ta Kalleta ta ce.
"Na'am Mummy."
Ɗan matsowa ta yi dab da Ita suna kallon juna ta ce.
"Aysha ya kamata ki zo ki shirya ki koma gidan mijinki haka nan. Kada mu zo muyi abu har na wuce hankali. Alhamdulillah! Alhaji dai ya samu sauƙi kuma abubuwa sun natsa mana. Kinga kin baro shi da Baffa tsawon lokacin nan, ya kamata ki koma gida hakanan..."
Jinjina kanta ta yi ta ce.
" Daman munyi maganar da Ahlan shekaranjiya, ya ce min yaushe zan dawo tunda Daddy ya samu sauƙi. Shi ne nace ya saka lokaci, ya ce min to in shirya ƙarshen satin nan sai na koma."
"To ba laifi. Allah ya nuna mana lokacin lafiya."
Daddy wanda tun da ya fita sallar asuba bai dawo ba sai yanxu sha ɗaya na safe. Karo ya ci da Babansu Ya Jafaru wanda har wayau ya kasa sakewa da shi. Shi ne farkon wanda ya fara miƙa masa hannu domin su gaisa.
Bayan sun gaisa ne Baba Habibun ya kalle shi ya ce.
"Ya jikin?"
"Jiki Alhamdulillah malam Habibu mun godewa Allah.."
"To, Allah ya ƙara afuwa.."
"Amin, Na gode."
Har ya juya da nufin tafiya ya ji muryar Daddyn a hankali yana faɗin.
"Malam Habibu..."
Waigowa Baba ya yi ya ce.
"Na'am"
"Amm...Dan Allah na ce har yanzu ba ka ji labarin inda Hajiya Mulaifa take ba? Dan Allah idan ka sani ka taimakeni ka faɗa mini, akwai abubuwa masu muhimmanci da nake so in sanar da ita dan Allah.."
A kaikaice Baba Habibu yake kallonsa har ya dasa aya. Girgiza kansa ya yi kai tsaye ya ce.
" Gaskiya dai bani da labarin ta kamar yanda na saba faɗa maka...Allah ya bayyanar maka da ita, shi ne addu'a ta a gareka.."
Cike da karyewar zuciya ya ce.
" To amin Ya Allah Malam Habibu, na gode sosai."
Hanya Baba Habibun ya kama wanda yana tafiya yana gunguni a ransa, Sam dawowar wannan mutumin wannan unguwar bai yi masa daɗi ba, domin wallahy baya ma son ganin sa. Shiyasa ya hana Maman Fakiha hulɗa da su, kuma ya gargaɗeta akan riƙe sirrin inda Ammie take domin ita da kanta ta neme su alfarma da cewa ko a mafarki kada su taɓa faɗawa su Daddy cewa ga inda take kamar yanda suka yi alƙawari da Aysha.
Yana batun buɗe ƙofar gidansa ya ji ana yi masa magana ta bayan sa. Koda ya waigo sai ya ga ashe wasu mutane ne guda biyu. Bayan ya basu hannu sun gaisa ne ɗaya daga cikin su ya miƙa masa takarda.
Da sauri Daddy ya ɗaga masa hannu ya ce.
"Dan Allah na roƙeku da ku faɗamin miye abin da wannan takarda ta ƙunsa kai tsaye kada ku tsaya wahalar da ni."
Ajiyar zuciya mai shirin miƙa masa takardar ya sauke sannan ya ce.
"To a gaskiya...wannan ɗin takardar sammaci ce daga kotu da aka shigar da kai ƙara domin tuhumarka akan dukiyar Hajiya Mulaifa da ta 'ƴa'ƴanta da kuma tauye musu haƙƙi na tsawon shekaru..."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Abin da ya iya furta wa kenan yana mai girgiza kansa cike da damuwa. Hannu ya miƙa ya karɓa yana mai yi musu godiya sannan ya juya ya shiga gidan.
Ganin irin yanayin da yake ciki lokaci ɗaya ya ɗaga musu hankali musamman Mummy. Sai faɗin take.
" Alhaji Lafiya kuwa?"
Girgiza kansa ya shiga yi hankali tashe ya ce.
"Ba lafiya kam! Wallahy ba lafiya Zaliha. Takardar sammaci ce daga kotu, Mulaifa ta shigar dani ƙara, za ta yi shari'a da ni...kuma a wannan karon Zaliha...daga ni har ke, tabbas kashinmu ya bushe"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Mummyn ta faɗa tana mai ɗora hannun ta a kai ta fashe da wani irin kuka.
Da sauri Aysha ta karɓi takardar ta shiga karantawa tamkar idanuwanta za su zazzago. Sai da ta karantar takardar yakai sau goma sannan ta miƙe da gudu ta faɗa ɗaki ta ɗauko wayarta jiki na rawa ta kira numbern Ammie. Tana ɗagawa ba ta jira komai ba ta fara mata wata irin magiya tana kuka tana faɗin.