Ganin ido complete Novel - Chapter 56
Ganin ido complete Novel Chapter 56: Ganin ido complete Novel Chapter 56. "Af! Kin ji ki da wani shirmen kuma. To miye a ciki da za ki tsaya yin 'ƴar…
3,367 words
"Af! Kin ji ki da wani shirmen kuma. To miye a ciki da za ki tsaya yin 'ƴar murya! Matuƙar dai mijin ki zai amince babu abin da zai hana, Allah ya kawo ku lafiya."
"Amin. Bari na barki ku ci gaba da hidimarku. Ina gaishe da Hajiya."
"Za ta ji In Sha Allahu. Sai da safe, Allah ya tashemu lafiya."
Ciki na koma tare da samun bakin kujera na zauna na dafe kaina ina ci gaba da tunani. Har yanzu lissafina ya ƙi tafiya daidai. Da ace fa Ammie tana da wasu dangin to da tabbas Sheikh zai faɗa mata. To amma bai san daga ina mahaifinta ya fito ba, sannan shin muna mada tabbacin cewa shi ɗin mahaifinta ne da gaske? Mahaukaci ne fa! Sannan ma idan har tana da dangi miyasa shi da take kallo a matsayin Baban ta zai zo ya hannun ta ta a wurin Sheik? Idan har yana da dangi mi zai sa a matsayinsa na mahaukaci su bar shi da ita? Idan har tana da dangi miyasa bai kai ta gare su ba tsawon lokaci? Mts! Kai! Gaskiya Wannan kama ce kawai. Ba ma zan gwada wannan katoɓarar ba, domin kada na je wurin gyaran gira a rasa ido, maganin kar a yi to kar ma a fara. A yanda ta samu farin ciki yanzu...ko kaɗan bana son na zama silar komawarta turkenta mai caɓo. To ko dai na bari idan ta dawo gida ta nutsu ɗin sai in kira ta?, ko kuma dai na bari sai na tafi munyi fuska da fuska sannan na faɗa mata?
Wannan tunanin shi ne abinda ya shiga zaga ƙwaƙwalwata ya hana min sukuni har na kwanta bacci da shi a cikin raina.
********
Tower 14, Porto Arabia, The Pearl, Doha, Qatar.
Sai da ya sauka a gidan sannan ya kira Suhaib ya ce ya kira Jadda ya faɗa mata cewa ya na gidansu Noura.
Bayan gama wayar sa ba'a rufa minti biyar ba sai ga shi ta kira shi da kanta saɓanin shi da ya shafe tsawon lokaci tunda ya dawo idan ya kira ta bata amsawa, sai dai idan da wayar Jaddi ko kuma wani a gidan, ko shi daga yanayin ta yanda take amsa kiran kasan ba don ranta ya so ba. Shiyasa har yau ya kasa daina al'ajabinta, at least ai dai ko na marmari ne ya ci ace ta yi masa ta ɗaga masa ƙafa ko don tsawon shekarun da ya yi ba tare da su ba. Yarinyar nan idan da tunani ya ci ace sun ɗaga mata ƙafa sun nuna mata kara. Sai dai ya fahimci ita ɗin mace ce mai tsattsauran ra'ayi da kuma tsayawa akan maganar ta.
Zaune yake kurum yana kallon mutanen gidan da ɗabi'unsu tun da ya shigo. Abu ɗaya ne zai ce ya ɗan ƙara mishi armashi dangane da zuwansa gidan shi ne zuwan Raihab wanda shi ɗin ƙanin Noura ne kamar yanda ya faɗa masa.
Sun jima a zaune babu wanda ya fito daga cikin su wanda har ya fara tunanin ta shi ya tafi sai ga mahaifiyarsu ta fito.
Farkon fara ɗora idonsa a kanta bai wani kawo komai ba, sai dai yanayin fuskar ta ya yi mishi kama da wata fuskar da ya haɗu da ita nan kusa. Bayan ta zauna sun gaisa ne ya ƙara jin abin a ransa, domin har muryar ta yi mishi sak ta fuskar da ya tuna cewa ya haɗu da ita sau biyu a rayuwar sa.
Hakan yasa bayan ta fita ya fito balcony ɗinsu ya kira Beenafah wata ƙila su ɗin suna da alaƙa da su. Bayan ya ji cewa ba su da dangi a Qatar ɗin ne ya yarda cewa tabbas wannan kama ce kawai. Idan ma ba shi ba, mutumin da yake ɗan Sudan miye haɗin sa da Yemen? Tabbas wannan kama ce kawai kamar yanda ta ce. Hakan yasa bayan sun gama wayar ya koma inda Raihab yake zaune yana mai shashatarda zancen ya kalle shi ya ce.
"Yayar taka ba ta nan ne na tafi har wani lokacin? Ina da ayyuka sosai a gabana and...Matata ma tana jirana a gida. Bana son na ɓata lokaci sosai a nan ba tare da na gabatar da abinda ya kawoni ba."
Cike da kwantar da kai Raihab ɗin ya ce.
"Ka yi haƙuri Yallaɓai, koda ka iso ta riga ta fita amma tana kan hanyar dawowa.."
Wayar shi da ta shiga ɓurarin neman agaji ne ya kai hannu ya ɗauka daga inda ya ajiye ya kara a kunnensa ya na mai yi mata sallama.
Murmushi ta yi daga can ɓangaren wanda har yana iya jiyo sautinta ta ce.
" Ka yi haƙuri Hammodina kada ka ji kamar na dameka...kai ɗin ne baka sanar wa kowa cewa zaka je gidan a yau ba, shiyasa ta fita, amma dai an yi mata waya yanzu ta ce tana kan hanya..Kana ji ko Hammodi? Noura nitsatstsiyar yarinya ce, sam ba ta da karauniya, kamar matarka haka take..."
Kai tsaye ya girgiza kansa ya katse ta da faɗin.
" Jadda Matata daban wannan daban..."
"Duk da haka, tana da halin nutsuwa da hankali kamar ita. Dan Allah ka sassauta mata ka ji hammodi? Ka bada haɗin kai yanda ya kamata."
"Hmhm"
Abin da ya furta mata kenan tare da jinjina kansa tamkar yana a gabanta. Jin bai ƙara jin sautinta ba yasa ya ajiye wayar kawai tare da lumshe idanunsa yana jin wani irin takaici da haushin maganganunta. Akan me za ta riƙa haɗa ta da Bibinsa? Ta san kuwa wacece ita a cikin rayuwar sa?.
Bayan ya ƙara jira na kusan hour ɗaya wanda har ya gama yanke tashi ya tafiyar sa, sai ga Raihab ya miƙe bayan ya gama amsa kira ya ce masa ya zo su shiga ciki. Yana shigar da shi ya juya ya tafi abinsa.
A zaune ya tarar da ita cikin shigar Abaya baƙa tayi rolling da gyalen ta so masha Allah.
Kafin yakai ga dire mazaunansa har ya ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa daga inda take zaune. Wanda shi in dai ganawa ne da yarinya irin haka to shi kam sai ya ce ba baƙon abu bane a wurinsa, domin an yi haka yafi a ƙirga wanda har sai da takai idan an ce mishi ga yarinya sai dai ya ce kawai ba sai ya ganta ba, kawai idan ta amince a ci gaba kawai da hidimar buki, daga ƙarshe haka za'a ƙare cikin rashin nasara wanda shi ne ciwon sa da baƙin cikinsa har aka ka zo kan Beenafah, lokacin da Labiba ta zo masa da zancen kwata-kwata bai saka shi a kansa ba har sai da ya ji cewa an ɗaura musu auren da gaske.
Cikin nutsuwarta ta furxo kalaman maraba a gare sa ba tare da ta ɗago ta kallesa ba. Ba ta jira amsar sa ba ta ɗora da cewa.
"Zan amsa auren ka ne kawai ba don raina yana so ba...domin bayan mijina da ya rasu bana jin akwai wani namiji a duniya da ya yi saura wanda zai iya bani farin cikin da na rasa. Zan yi ne don biyayyar iyaye..."
Take ya ji wani irin ɓacin ran da bai san ma daga ina yake ba ya yi masa dirar mikiya ya cake masa zuciyarsa, wani irin shegen kallo ne ya mata a hargitse ya ce.
" Ohh! Wai ke a ta wannan fuskar kika ɗauki abun? Waye ya ce miki na zo nan ne saboda ina son ki?"
A razane ta ɗago ido ta kalle shi domin kalamansa sun yi matuƙar zo mata a ba zata.
"Kallon me kike min? Kamar yanda kike tunanin babu namijin da zai iya baki farin ciki bayan mijin ki da ya mutu, haka nima bana tunanin akwai wata mace a duniyar nan da za ta bani farin cikin da matata take bani...wai miyasa ku wasu mata kuke abu tamkar babu ƙwaƙwalwa a cikin kan ku ne? Da aka ce na zo nan ɗin kin ɗauka shashasha ne ni marar aikinyi ko me? Da kin san yanda akayi har na zo nan ɗin da ba ki buɗe baki kin fara tarba ta da wannan banzar maganar ba... "
Kuka ta fashe masa da shi tana mai girgiza kanta ta ce.
"Matsalarka kawai kasani, shiyasa kake furta waɗannan kalaman a gareni..."
"Matsala? Ai ni Allah ya rabani da matsala tsawon lokaci, Alhamdulillah! Amma dai sai ke yanzu sabuwar matsalar da na samu ta haye kaina ta yi bake-bake. Da kike ma wani zancen matsala ke har matsala kike da ita? Saboda mijin ki ya mutu shi ne matsala? Zaman Auren shekara bakwai kaɗai har yasa kin iya kinibibin ƙin maza ko? To su waɗanda suke rayuwa tsawon shekaru talatin, arba'in, hamsin...ɗaya ya mutu ya tafi ya bar ɗaya su ce ya ya? Kowa fa a rayuwar nan ba shi da ikon zaɓarwa kansa Ƙaddara. Sannan kamar yadda farin ciki bai zama har abada haka ma baƙin ciki ba ya zama har abada. Kin rayu tsawon shekaru kina farin ciki, don yanzu wannan ƙaddarar ta same ki sai ki yiwa Allah butulci? ki ce duk ni'imominsa a gareki baki gode da ko ɗaya ba? akan mutuwar mijinki za ki yanke ƙauna daga gare sa? Tsawon shekaru uku bakya farin ciki to su 'ƴa' ƴan ki taya za ki iya ƙarfafasu?"
Hankali tashe ta haɗiye sauran kukan ta domin wannan mutumin ba ƙaramin mamaki ya bata ba. Ta ɗauka cewa zai zauna ne ya rarrasheta ya bata haƙuri akan irin yanda ta ke ji kamar yanda Maza da yawa suke mata idan sun zo gareta, amma sai ta ji yau kawai ta haɗu da wani mutum na daban wanda ra'ayi da rayuwarsa sun bambanta da na sauran mazajen.
Miƙewa ya yi sannan ya kalle ta ya ce.
"Ba nuna ƙiyayyarki a gare ni bane abin da yamin zafi...magana ta gaskiya ko! ni hakan taimakona ma kika yi,domin matata Allah ya sani bana da burin haɗata da kowace mace, saboda haka ki faɗa musu da bakin ki cewa har ki mutu ba za ki iya son wani mutum ba domin mijinki kawai kike so, idan kuma suna so suga farin cikin ki to lallai su dawo miki da shi. amma yanda kika tarbeni da munana nan kalamai ne abin ya mini zafi. Ni ba yaro ba ne, at least ya kamata ki tauna kafin ki furzo.."
"Ka yi haƙuri!"
"Kema haka! And....Idan har na sa ki jin ba daɗi ki yi haƙuri, amma dai kin san cewa ni ɗin ɗan uwanki ne ,yayanki. Ina da dama da ikon da zan yi miki faɗa idan har kika yi ba daidai ba."
Daga haka ya fito ya cewa Raihab ya yi masa sallama da Hajiya domin a wannan daren ya ke son komawa gida, ba zai iya kwana a wannan garin ba.
A tare ta fito da wasu kyawawan yara guda uku wanda tana tafe suna biye da ita har ta zo ta samu wuri ta zauna.
Da murmushi a fuskarta ta kalle shi ta ce.
"Ban san wace irin tattaunawa ku ka yi da Noura ba. Amma dai ina baka haƙuri da irin ɗabi'unta. Mutuwar Mijinta ne har yanzu ta kasa barin jikinta. In Sha Allahu komai zai yi daidai."
Cike da girmamawa ya jinjina kansa ya ce.
"Ba komai. Amma dai ina neman wata alfarma guda ɗaya;kada ku ce za ku tilasta mata, ta faɗamin Cewa ba ta da ra'ayi, Sam bana son ta sanadina ace rayuwar mace ta ƙuntata. Ita ɗin bazawara ce, tana da haƙƙin zaɓarwa kanta mijin da ya dace da ita. Ku ƙara mata lokaci ta ƙara fahimtar matsalarta domin neman mafita..."
Hannu ya miƙawa yaran yana murmushi, sai gashi sun zo gare sa gabaɗayansu suna masa murmushi. Babbar ce wacce za ta yi 7years ta gaishe da shi sannan mai bi mata da za ta yi 5yrs jin yayar ta ta gaishe itama sai ta gaishe da shi. Hannu yasa ya ɗauko ɗan ƙaramin ƙanin su wanda zai iya yin 3yrs ya ɗora shi akan ƙafarsa yana ta yi masa wasa yaran na gefensa suna masa surutu tsawon lokaci wanda har sai da ya ji cewa ya gaji sannan ya ajiye shi ya ce.
"Ni zan koma Hajiya..."
Lokaci ɗaya Hajiyar ta ji cewa ya kwanta a ranta tana son ya kasance mijin 'ƴar ta. Kalli yanda yake yi da yaranta wanda da alama yana matuƙar son yara sosai. Ko ba komai zai barta ta zauna tare da su a hannun ta ko don saboda zumuncin da ke tsakaninsu. Kallon shi ta yi ta ce.
"Dan Allah ka zauna zuwa gobe mana, kafin nan mahaifin su ya dawo sai ku tattauna da shi. Ko ba da auren ba ai nan ɗin gidanku ne kai ma..."
Jinjina kansa ya yi ta ce.
"Haka ne gaskiya. Na gode sosai da karamci. Amma ba zan iya jira zuwa gobe ba, ku ɗin m en uwa ne, ko ba don Ita ba zan iya dawowa watarana."
"To ba damuwa. Allah ya tsare, a gaida mutanen gidan."
Tun da ya baro gidan har suka isa Airport bai ji ya daina jin haushinta ba a ransa duk da cewa ta ce bata son sa, hakan ba ƙaramin faranta masa rai ya yi ba. Wayarsa ya ɗauko ya lalubo numbern Labiba ya kira ta. Tana ɗagawa bayan ta gaishe shi ya ce.
" Ni ɗin mutum ne mai takurawa Labiba? Ina nufin na cika zafi ko?"
Da sauri ta girgiza kanta tamkar tana a gaban sa ta ce.
"A a Daddy, waye ya faɗa maka haka? Kai ɗin nan fa kafi ruwa sanyi da son zaman lafiya"
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"Uhm! Yanayina ne ya canza, sai na yi mata faɗa sosai bayan ta faɗi wasu kalamanda ba su kamata ba..."
Hankali a tashe ta ce.
"Wace ce wannan?"
"Noura da Jadda ta ce sai na aure ta. But...Alhamdulillah! Ta ce bata yi, yanzu hankalina ya kwanta. Ina fata za ta yafe min ko ba komai mu ɗin 'ƴa uwa ne. sannan ina fata ta canja tunanin da take watarana, ko zai sa ta samu wani mijin ta yi aure. Ya yi wuri da yawa a cikin rayuwarta ta ce ba za ta sake wani auren ba."
Cikin farin ciki Labibar ta ce.
" Kai! Amma gaskiya na ji daɗi sosai, domin magana ta gaskiya ni dai ba son auren nake ba Allah ya gani. Don kawai bani da iko ne yasa na yi shiru. Allah ya ji ƙan mijinta ya bata haƙuri ya sanyaya mata zuciya."
"Amin. Zamu shigo cikin satin nan idan Allah ya nufa."
"Allah ya nuna, ai Mummyn Adeel ta faɗa mana."
"Amin."
*********
Emraan kuwa, shiryawa ya yi ya wuce wurin aikinsa wanda bai dawo ba sai da ya yi sati biyu cif. Yana shiga gidan bai ko bi ta kan Ziza ba ya ajiye kayansa ya shiga ya yi wanka sannan ya fito ya tafi gidan Labiba.
Koda ya je gidan bata nan bata dawo daga wurin aiki ba. Hakan yasa ya shiga gidan Hajiya Marwa wacce tunda ya shiga suka gaisa ta shige ciki bata ƙara Fitowa ba sai da Labiba ta kira shi ta ce ta dawo.
Yana shiga suna haɗa ido da ita ta yi murmushi ta ce.
"Sarakan en Zuciya Allah ya yi ka sauko?"
Ɗan sosa bayan kansa ya yi yana murmushi ya ce.
"Hajiya Labiba, Ziza ce idan ba haukace mata na yi ba ba za ta barni na zauna lafiya ba. Ki duba fa tun da na tafi nake ta kiranta amma taƙi ta yi magana da ni, sai dai ta ba wa Abeer Waya idan na gaji na kashe. Yau ma tana gani nan na dawo ko dai ta ɗago idonta koda da munafurci ne ta ce min na dawo lafiya. To tunda har ba bakin Uwa ne da ni ba ai dole na yi mata kishiya koda ko za ta mutu..."
"Innalillahi! Emraan wai kana cikin hayyacinka kuwa? Ƙarin aure hauka ne aka faɗa maka....kaga..! Kabi a hankali! Kabi a hankali wallahy kada ka je kallon ruwa kwaɗo ya maka ƙafa. Ka natsar da zuciyarka ka tsaya ka rarrashi matarka ku shirya tukun. Ƙwarya ƙwarya ce amma kuma kowacce da gurbinta. A iya zamanka da Ziza ba ta da wata matsala idan ba wannan makahon kishin ba, kuma son ka take,shiyasa take duk wannan...."
"Saboda tana So na sai ta hanani son wata, nima ai ina son ta..."
"Kishi fa gaskiya ne Lieutenant Emraan! Sai dai na wata yafi na wata, wata na hankali take wata kuma na hauka ta ke yi. Kuma mafi yawa suna nan zaune tare da mazajensu ana ta gurgurawa. Misali....Idan ka dubi Hajiya Marwa ,gata nan ai kishiyata ce. Tunda nake tare da ita tunda Barrister ya auro ni ko sau ɗaya bata taɓa jin tana sona ba, da ni da duk wani wanda zai fito daga waje na bata son sa, ta faɗamin haka ya fi cikon carbi. Sannan babu tashin hankalin da ba ta yiwa Barrister, amma bai taɓa sakinta ba wai don saboda ni, dalili...a tare na iskosu. Ina alfahari da mijina, domin yana kamantawa Emraan, yana iya ƙoƙarinsa wurin kamanta adalci a tsakaninmu da kuma haƙuri damu. To ina so kai ma ka koyi amfani da tracks ɗinsa, In Sha Allahu za ka yi nasara. Ka lallaɓa ta, ka kwantar mata da hankali, na san da ace bamu tattauna wasu maganganun da ita ba da yanzu abin da za ta yi maka sai yafi haka muni. Ba don ba'a son uwayen gida ko sun gaza ba ne ake ƙara musu abokan zama, aure zuwa yake. Ka lallasheta ku kai ƙarshen wannan. Idan har wani abu ya ƙara tasowa makamancin wannan kuma na bincika kai ne baka da gaskiya, to magana ta Allah zan haɗaka da Daddy, Baba Ustaz da su Kawu Ɗan Ladi...idan ya so sai su hana ka auren in ga yanda za ka yi."
Wani murmushi ne ya suɓuce masa tare da girgiza kansa ya ce.
" Ki yi haƙuri. In Sha Allahu za'a gyara ranki ya daɗe."
"Ai kai ne ranka ya daɗe, Allah sabbinane, mai laifi kuma ya yi fushi."
Nan dai suka ƙara taɓa fira sannan ya tashi ya tafi gida.
*******
Alarm ɗinda ya buga shi ne abin da ya tasheni yasa na motsa a hankali domin miƙa hannu na daƙilesa kasancewar bana jin zan iya tashi a yanxu. Jina kamar a cikin jikin mutum yasani saurin buɗe idanuwana a razane ina mai neman ƙwallara ihu.
"Shihh! Bibi! ni ne mana. Cikin dare na iso, kuma kina bacci, shiyasa na yi wanka na kwanta..."
A zabure na miƙe zaune ina ƙara murza idanuna domin ji nake kamar kunnuwa gizau suke min ba gaskiya ba ne kawai dai kewar sa yasa zuciyata da ƙwaƙwalwata jin cewa kamar shi ne a kusa dani...
"Ke ni ne fa. Taɓani ki ji.."
Ya faɗa yana mai kamo duka hannayena ya ɗora su akan fuskarsa yana mini murmushi.
"Wallahy kuwa kai ɗin ne da gaske...to amma miyasa ka dawowa kamar ana korar ka?"
"Saboda na riga na gama ganin duk wanda ya kamata ace na gani..."
Jinjina kai na na yi ina ta wani irin murmushin farin cikin ganin sa, lokaci ɗaya na ji na nemi baccinda na ke jin yana ƙoƙarin danneni na rasa.
"Are you Happy?"
Cikin jikinsa na koma na kwanta ina dariya na ce.
"Sosai ma kuwa. Welcome!"
Shiryawa ya yi ya fita masallaci nima na yi wanka sannan na yo alwala na zo nayi sallah bayan ya dawo ne muka koma muka kwanta na ce.
"Good morning!"
"Did you miss me?"
Dariya na yi kawai ina jinjina masa kaina alamar eh.
"Kamar ya kenan?"
"Kamar dai haka....Kamar haka...Kamar kuma haka."
Na faɗa ina mai kissing gefen wuyansa har zuwa fuskarsa kamar yanda yake min...
"Iyyehh! Ki ce an ƙara sabon course bana kusa..."
Dariya na yi ina faɗin.
"Yau za ka fita wurin aiki ne?"
"eh, zan fita yau. Gobe sai na tsaya mu yi shirin tafiya, jibi sai mu wuce."
"Uhm."
"Allah ya nuna mana."
"Amin."
Ƙarfe takwas na rakashi ya tafi na dawo gidan wanda ni tun a yau ma na fara shirina, ji nake kamar na buɗe idanuwana na ganni a gaban Ammie haka nake ji.