Kenza eBookz

Ganin ido complete Novel - Chapter 61

Ganin ido complete Novel - Chapter 61

Ganin ido complete Novel Chapter 61: Ganin ido complete Novel Chapter 61. Dariya Baba Kalin ke yi har yana kwantawa tsabar yanda abokin na shi ke bashi…

3,371 words

Dariya Baba Kalin ke yi har yana kwantawa tsabar yanda abokin na shi ke bashi dariya wanda har sai da ya ga ya fara tsarguwa sannan ya daina. Sosai ya shiga bashi shawarwarin yan da zai yi har ya samu ta dawo gare shi. Wannan shawara ba ƙaramin farin ciki ta bashi ba domin ta sanyaya mishi zuciya ba kaɗan ba.

********

Da ƙyar na samu ya amince min, ko shi don Hairi ta dawo ne yasa ya amince,amma cewa ya yi kada na wuce hour ɗaya highest Idan na jima a gidan.

Sosai na yi masa godiya sannan washe gari muka shirya muka fito misalin ƙarfe huɗu na yamma. Oga Sule muka tarar ya kawo wata sabuwar Mota babba baƙa wulik har bakin harabar gate na biyu ya kara ta.

Muna shiga na yi masa bayanin gidan su Hafsa sai gashi nan da nan ya kaimu har ƙofar gidan, daman gidan su ba shi da wani nisa da Islamiyyarmu domin kan hanya suke.

Sosai ta ji daɗin ganina kamar yanda nima na ji daɗin ganin su har da en ajinmu. Nan muka zauna muka yi ta fira ana ta nishaɗi har aka shirya za'a wuce da ita wurin wanka, nan na bata 50k sannan Hairi ta bata jakar turaruka da Hajiya ta bayar da kuma package na spices da Aunty Ziza itama ta aika aka karɓo da Eatry ɗinta. Sosai taji daɗin wannan kyautar har da Maman su sai da tayi godiya domin kayane masu yawa masu kuma tsada.

A tare da Fakiha muka fito ta rakomu har mota, Babu wanda bai yi mamakin ganin Ya Jafaru tsaye a gefe ba yana aikin kallon mu. W

Take annurin fuskata ya ɓace domin idan akwai wani wanda na tsana a rayuwata yanzu to Ya Jafaru ne. Kallona Fakiha ta yi ta ce.

"Dan Allah Beenafah ki yi haƙuri, cewa yayi ki ɗan basa lokaci kaɗan yana so ya baki haƙuri ne akan abun da ya faru ranar.."

"To kuma babu inda zai bani haƙurin dole sai nan gidan mutane?"

Da sauri ta girgiza kanta tana faɗin.

"Ba haka ba ne, ya ce min dan Allah kada ma in bari su Mama su ji, shiyasa ya zaɓi nan ɗin."

Taɓe baki na yi tare da ƙara ɗaure fuskata na ce.

"OK! To ki ce yazo nan mana ya faɗi dukkan abin da zai faɗa..."

Girgiza kai Hairi ta yi tana faɗin.

"A'a Mummy! Tun da yace ki je dan Allah ki je, ba gamu ba...ga mutane ko'ina. Ki je ki saurare shi."

Jin maganar da Hairiyya ta yi ne yasa na taka tamkar zan haɗiye zuciyata na mutu saboda baƙin ciki. Ina zuwa na tsaya tare da kallon shi a sheƙeƙe na ce.

" Ga ni..."

Ƙasa ya yi da murya kamar da gaske ya ce.

" Zuwa na yi in faɗa miki wallahy tallahy har abada ba zan taɓa haƙura da ke ba. Na san cewa kina so na Beenafah, kawai dai ƙaddara ce ta yi mana rigaye a tsakaninmu. Saboda haka na ba ki lokaci ki je ki yi nazari. Dan Allah Beenafah ki dawo gareni...Ya Jafarun ki ne fa! Ban san komai ba idan ba son ki da ƙaunar ki ba. Ba zan iya rayuwa ba idan babu ke Beenafah..Na san cewa fushin zuciya ne ya sanyaki aikata abin da kika aikata kamar yanda nima fushin zuciyar ne. To amma ki sani ni babu wata mace a raina har abada sai ke. Ko shekara ɗari za ki yi zan iya zaunawa na jira k... "

" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Jikina na rawa na furta masa hakan ina mai Girgixa kaina,sannan daga ƙarshe na ce.

" Ubangiji Allah ya shirye ka."

Daga haka na juya na je na shige mota ina mai yiwa su Fakiha yaƙen ƙarfin hali domin kaɗan ya rage zuciyata ta tarwatse tsabar baƙin ciki. A yau tabbas yaci darajar su Hairi ne,domin hana so in yi wani move ɗinda za su gane cewa akwai matsala, amma da ba dan haka ba wallahy tallahy da sai na yi masa abin da yafi na ranar ma.

Wai anya Ya Jafaru bai haukace ba kuwa? An ya bai fara shaye-shaye ba? Idan ba shi ba wane irin ƙarfin hali ne haka ɓarawo da sallama? Shi yanzu ashe har yana da guts ɗin biyoni cikin taron jama'a yana faɗamin maganganun banza? Wallahy darajar Su Mama na ke dubawa amma Kada ya bari ya kai ni maƙura. Ji yanda Mama ta dinga magiyar bani haƙura dan Allah? Amma saboda Jakki ne shi shi ne yau ya sake dawowa. Ya Hamza ma ko ɗazu sai da ya kirani da safe muka gaisa lafiya lau ya yi mini ya jiki. Amma da yake ƙwaƙwalwar kifi ne da shi ya kasa gane kawaicin da nake masa. Shi ne fa dalilin da yasa na cire son zuwa gidan su Yaya Ashiru a raina da nake ta ɗoki,domin ban san shi ma ta ya ya zai karɓeni ba daga har iyayensa. Ina jin kewar sa a raina, kuma na so zuwa gidan su kamar me, to amma hakan ba zai samu ba, domin kada ya gaza fahimta ta kamar yanda wannan shashashan yake.

Koda muka isa gidan na tarar wai Aunty Ziza ta kawo min Ɗinkin da zan sanya gobe wanda sun yi kyau ba kaɗan ba. Amma kuma ni dai ban yanke saka su ba, domin Aunty Labiba ta kawo mini ɗinkunan da Ya Mohaa ya biya domin a ɗinkamin tun daga Kaduna wurin Aunty Nadeeyah. Kuma kayan Mijina sun zan saka gaskiya, sai daga baya watarana can na saka idan ina ra'ayi, amma ban nuna mata ba, domin sosai na yi ta zuba mata godiya tare da yaba yanda Ɗinkunan suka tsaru.

Washe gari da wuri aka gama tsara komai. SOS event aka gayyato na musamman suka ƙawata harabar gate na ɗaya da decoration wanda ya haɗu sosai. Wani abun burgewa da farin ciki shi ne, RANIA (Mima) shi ne sunan da Emraan ya raɗawa Babyn. Hakan ba ƙaramin farin ciki ya sanya Ya Mohaa ba, domin daga yanda yake ta nanata min maganar cike da jindaɗi shi ne ya tabbatar min da cewa ya yi farin ciki sosai da wannan karamcin da Emraan ya yi masa.

Nan aka sha Hidima wanda ni ina wuri ɗaya domin ban yi wani zirga-zirga ba kada na wahala da yawa. An ci an sha Alhamdulillah! an sha hotuna kamar ba gobe ga kayayyakin rabawa nan kamar banza komai an yi shi Masha Allah. Su Ammie na wuce nima na tattara ni da Hairi muka shige ciki.

Bayan na kambala sallar Isha na miƙe daga parlourn da muke zaune na ce musu zan shiga na yi wanka na kwanta domin na gaji sosai. Na gama cire kaya kenan na ɗora towel na ga wata sabuwar number tana kira na. Ba tare da kawo komai a raina ba na yi picking domin na san cewa na baiwa en ajinmu numbernta da yawa, to wata ƙila daga cikin su ne wata ta kira. Sai dai kuma, muryar da na ji ita ce ta kusa Sumar da ni tsabar mamaki da al'ajabi.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

*PAGE 51*

Cikin wata irin magiyar da ba za ta mishi amfani ba kamar yanda ni ma har abadan abada ba za ta taɓa yin tasiri a kaina ba ya ce.

"Dan Allah Beenafah ko sau ɗaya ne ki tsaya ki saurareni!..."

Shiru na yi ba tare da na yi magana ba kamar yanda shima daga can ɓangaren ya ɗan janye wayar daga kunnen sa ya kai idanunsa akan ta ya duba kyau domin tabbatarwa cewa na yanke kiran ko ban yanke ba. Wani irin sanyi ne ya ji ya ratsa shi har da lumshe idanunsa sannan ya mayar a kunnensa ya ce.

"Beenafah! So ɗaya ne, kuma shi nake miki. Kada ki manta su irin masu kuɗin nan babu abin da suka sani idan ba son kansu ba. Ina so ki auna da kaifin hankalinki ki gani, ke fa ƙaramar yarinya ce wacce ba ta yi wani zurfin ilmi ba. Ke ɗin ba kowa bace idan aka kwatanta da Engineer domin yafi ƙarfin ki ta ko'ina, Babban mutum ne wanda duniya ta san da zamansa, yana da kuɗi, yana da ilmin da ke ko kan akaifar ƙafarsa ba ki kamo ba,da za ki zauna ki nutsu ki yi nazari, sam! Ke da shi baku dace ba, kawai yana amfani dake ne na ɗan wani lokaci domin biyan wata buƙatar sa. Daman wata mummunar ƙaddara ce ta yi masa hijabi da samun matar da ta dace da shi, tunda kuma a yanzu dama ta samu, ba jimawa zai aure Macen ta waye, ta goge, ta yi ilmi mai zurfi da ta fiki komai ta kowace fuska, a wannan lokacin ne za ki dawo bola shara marar amfani, daga ƙarshe saki ne zai biyo baya na wulaƙanci ma...Beenafah! Ba wai ina faɗa miki shaci faɗi ba ne, abun da zai faru kenan nan da ɗan wani lokaci domin har abada mutum kamar Engineer Mohaa ba zai zauna da ke a matsayin matarsa wacce zai iya nuna ta a duniya ba..."

A gigice na fashe da wani kuka ina mai ɗaga murya ina girgiza kaina jin wasu sababbin abubuwan da suka shiga yawo a kai na ina neman ƙaryata shi na ce.

"Ƙarya ka ke!!! Ƙarya ka ke Ya Jafaru. Dayaa har abada ba zai taɓa yi mini haka ba, duk inda muka shiga bai taɓa ƙin nuna ni ba, da alfahari yake nuna ni a ko'ina..."

"Ƙarya ne! He's just pretending. Muhammad ba zai taɓa son ki ba, har abada Beenafah ba zai so ki ba. Komai yake miki yana yi ne kawai domin kara akan sadaukarwa da ya yi miki. Sadaukarwa ki ce a gare shi Beenafah yasa yake miki duk waɗannan abubuwan, amma sam ba zai iya ɗaukar ki a matsayin matarsa ba ta dindindin har abada..."

Ƙara kwantar da muryarsa ya yi jin kamar kalamansa sun fara kamani sun kuma soma yin tasiri a kaina ya ce.

"Beenafah! Ke da shi Sam baku dace ba. A GANIN IDON ki ne kike ganin kamar yana son ki amma sam ba haka ba ne. A lokacin da za ki kai ganiyarki ta cika Mace cikakkiya...shi a lokacin ya riga ya gama amfani domin ya tsofe sosai. Da ni kaɗai kika dace Beenafah, saurayine ni mai jini a jiki, tazarar da ke tsakaninmu ba ta yi nisan da za ta hana mana zama mata da miji ba har abada. Ni ka ɗai na san irin son da nake miki wanda har abada babu wani mahaluƙin da zai so ki kamar ni Beenafah. Idan har na rasa ki ban san a wanne hali zan faɗa ba. Ki tausayi min ki zo gareni dan Allah. Ba zan matsa miki ba, ki je ki yi tunani Beenafah, duk abin da na faɗa miki haka yake."

Sulalewa na yi na zube akan ƙafafuna tare da janye wayar daga kunnena. Sosai Kukana ya tsananta domin notukan kaina gabaɗaya sun kwance a halin yanzu.

Da gaske ne waɗannan kalaman da yake faɗa mini ko kuma yaudarata yake yi? Kamar yanda nake ƙoƙarin auna maganganunsa...haka wasu tunanuka barkatai suka shiga bijiro mini. Da gaske Ya Mohaa amfani kawai yake dani? Da gaske zai yi wani aure har ya auro wacce ta Fini komai? Tabbas ni da shi ajinmu ya yi nesa da juna, sam idan ana zancen sa ban isa na nuna kai na ba domin ya yi mini ratar da ta ko'ina ba zan iya kamo shi ba har abada. To amma wanne rashin adalci ne zai sa ya ji cewar ni ban cancanta ba? Na san tabbas ni ɗin ban yi karatu ba, ko secondary school ban kambala ba, shi ɗin kuma babban mutum ne sannan mai kakkaifan ilmin zamani da na addini wanda duniya ta san da zamansa. Idan ya ce ya ɗauko mai aji irin sa har abada na sani ba zan kai labari ba. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wayyo Allah na wayyo ni kai na...!! Mi yasa zai nuna a GABAN IDO na cewa yana so na amma kuma can cikin zuciyarsa ba haka ba ne? Yanzu ni da na sadaukar masa da kaina da rayuwata ba tare da sanin mi zai zo gabana ba har yana iya tunanin butulce mini? Idan kuwa hakane sam bai mini adalci ba.

Ƙarshe girgiza kaina nayi ina mai jin tunani na neman haukatani gabaɗaya. Idan har Ya Mohaa zai iya yin haka a gareni to mi zai rage min a duniyar nan? Shi ne wanda na fara jin soyayya a kansa kuma na yarda da ita. Rayuwata da fata na duk na ɗora su a kansa. Idan ya ce zai juya mini baya in yi ya da rayuwata kenan?

Haka dai na kwashe tsawon lokaci ina ta saƙawa ina warwarewa wanda ban samu komai ba sai ƙarin tarin damuwowi da ruɗanin da ban san ma yanda zan misalta shi. Lokaci ɗaya na dawo tamkar wata er maye domin na rasa ma wane kalar tunani zan yi.

Da ƙyar na samu na rarrafa na haura kan gado na kwanta ina mai jin yanda wani irin ciwon kai ya yi mini dirar mikiya, kafin ka ce mi...jikina ya ɗauki wani irin zafi tsabar yanda nake cikin tsananin ruɗani da damuwa.

Ina jin alamar buɗe ƙofa na yi saurin rufe idanuna tare da jan duvet na lulluɓe har saman kaina. ko ba'a faɗa ba nasan cewa aikowa ya yi a dubani domin tun ɗazu yake kiran wayata amma na kasa ɗauka wanda ban san dalilin hakan ba.

Muryar Hairi na ji tana faɗin.

"Mummy...mummy! Aunty Beenafah.."

Juyawa ta yi tare da faɗin.

"Halo Daddy kana jina? I told you cewa ta yi bacci,because tun around 9pm ta baro mu tace za ta yi wanka ta kwanta domin tana jin gajiya, har warning ɗina ta yi tace kada na zo ɗakinta domin ba za ta saurare ni ba ita bacci za ta yi."

"Favourite kin tabbata Bibi tana lafiya?"

Dariya ta yi tana mai gyaɗa kanta tamkar yana a gabanta ta ce.

"I'm 100% sure Daddy! Ka kwantar da hankalinka Bacci take yi...bari ma na rage mata gudun ACn nan because na ji kamar ya yi yawa...kada mura ta je ta kama mana babynmu a banza tun yana ciki in shiga uku in lalace..."

Remote ta ɗauka ina hangota da maƙalallen idona ta rage gudun sannan ta kashe mini fitila ta fice tare da ja mini ƙofa.

Ina ganin ta fice na miƙe zaune ina mai tattaɓa jikina domin in tabbatar cewa da gaske sanyi ya yi yawa? Sam ban ji wani abu makamancin hakan ba domin zufa nake ta ko'ina. Hannuna na kai ina shafa cikina tare da lumshe idanuna na zubo da wasu irin zafafan hawaye a rai na ina faɗin.

'Wanne Babyn Hairi? Babyn da nasan ko shi amfani ne kawai yake dani domin ya samu cikar burinsa na zamo wa uba a karon farko na rayuwar sa, tabbas na san da ba don wannan ba banga wani dalili da zai sa ya yi ɗokin haihuwa da ni ba, ni ɗin nan da ba kowan kowa ba...da sauri na sake ɗora ɗayan hannun nawa na dafe cikin baki ɗaya ina mai girgiza kai cike da jin wata irin matsananciyar ƙuna a raina na furta a fili na ce.

"Ka yi haƙuri Babyna..amma idan har ta tabbata cewa zargina akan mahaifinka ya tabbata....i won't regret for doing my second thought..."

Daga haka na komar da kaina kan Pillow ina mai jin yanda zuciyata ke wani irin zafi tamkar an kunna mini wuta a cikinta. Miyasa ma tun farko zan aikata? Idan har hakan da gaske ta kasance ya Ammiena za ta yi kenan? Sosai hankalin ta ya kwanta ganin yanda nake zaune lafiya ina farin ciki...to idan wani abu ya bijiro sabo daga sama mi zai faru da ita? Kada sanadiyyar hakan ta sake rasa tunaninta.

"...Ke ɗin ba kowa bace idan aka kwatanta da Engineer domin yafi ƙarfin ki ta ko'ina, Babban mutum ne wanda duniya ta san da zamansa, yana da kuɗi, yana da ilmin da ke ko kan akaifar ƙafarsa ba ki kamo ba,da za ki zauna ki nutsu ki yi nazari, sam! Ke da shi baku dace ba, kawai yana amfani dake ne na ɗan wani lokaci domin biyan wata buƙatar kansa..."

"....amma sam ba zai iya ɗaukar ki a matsayin matarsa ba ta dindindin har abada..."

".....Daman wata mummunar ƙaddara ce ta yi masa hijabi da samun matar da ta dace da shi, tunda kuma a yanzu dama ta samu, ba jimawa zai aure Macen ta waye, ta goge, ta yi ilmi mai zurfi da ta fiki komai ta kowace fuska, a wannan lokacin ne za ki dawo bola shara marar amfani, daga ƙarshe saki ne zai biyo baya na wulaƙanci ma..."

Waɗannan su ne maganganun da suka shiga dukan ƙwaƙwalwata ba tare da bata sarari kona Second ɗaya ba. Waɗannan kalaman sun yi mini illar da ko ruwan guba nasha bana tunanin za ta iya cutar dani ta lahantani kamar yanda suka yi ba. Na ɗimauta na gigita. Sam tunanina bai kai can ba. Sai yanxu na tabbatar da cewa ni mahaukaciya ce domin ban taɓa yin irin wannan tunanin ba. Kwata-kwata hangena bai yi nisan wannan ba sai yanxu.

Haka na kwana ba tare da runtsa ba, domin sam bacci bai yi gigin kawo mini farmaki ba, sanin irin mummunan yanayin da nake ciki a wannan daren.

Daƙyar na iya lallaɓawa na watso ruwa sannan na zo na yi sallah na sake komawa na ƙudundune.

Wani irin amai ne na ji ya taso mini lokaci ɗaya, ba shiri na diro ina mai faɗawa toilet na shiga kakari tamkar zan amaye hanjin cikina. A gigice Hairi ta shigo har toilet ɗin ta kamani tana ta faman yi mini sannu. Sai da ta tabbatar cewa na gama sannan ta bani ruwa na kuskure bakina muka fito.

Kallona ta yi cikin tausayawa tamkr za ta fashe da kuka ta ce.

"Sannu Aunty Beenafah! Daman baki da lafiya ne? Na harda jikin ki ya yi zafi..."

Murmushin ƙarfin hali na yi mata domin na kwantar mata da hankalinta na ce.

"Lafiya ƙalau nake, kawai dai yanayin ne bana jin daɗinsa..."

"Allah sarki! Kewar Daddy kike ko? Shima na san duk inda yake yana can hankalin sa a kanki..wallahy ko jiya ba ki ji yanda duk ya ruɗe ba jin ya yi ta kiran ki ba ki ɗaga ba. Ko bayan na kwanta sai da ya sake kirana domin ya ƙara tabbatarwa na ce masa kina nan lafiya ƙalau.."

" Lafiya lau nake, kema ki kwantar da hankalinki. Kira mini Biba in faɗa mata abinda za ta dafa mini.. "

Har ta kai ƙofa na kirata ta waigo na ce.

" Dan Allah kada ki faɗawa Yayanku, kinga kada a ɗaga masa hankali."

Jinjina kanta ta yi tana faɗin.

"In Sha Allah ba zan faɗa masa ba. Daman ai yau ne zai dawo.."

Daga haka ta jiya ta wuce.

Tea Kawai na iya sha ko shi don na ji kamar na fara jin juwa because kamar na faɗi haka nake ji. Daman a 'ƴan kwanakin nan duk na yi lattin cin abinci sai na ji yanayina na neman sauyawa.

Duk wanda yake gidan ya fahimci cewa sam bana cikin yanayin walwala ta, domin maganganun Ya Jafaru sun kasa barin ƙwaƙwalwata , ko kaɗan na kasa samun sukuni.

Ina gama shan Tea ɗin na shirya na cewa Hairi ta faɗawa Oga Sule cewa zan ta fi gida wurin Ammie na ya shirya ta kai ni.

A tare muka tafi mu biyu dani da Hairi. Muna shiga gidan muka tarar an yi Uwar siyayya komai da komai gashi nan da alama ma yanzu aka gama sauke kayan.

Bayan mun gama gaisawa ne na kalli Ammie na ce.

"Ammie wannan kayan fa?"

Kallon kayan ta yi sannan ta kalleni ta ce.

"Siyayya ce na yiwa Hassana, Mijinta ya zo, gobe za su koma gida."

"Ok. Allah ya tsare hanya."

"Amin. Yau fa suka ce za su wurin ki tunda kema tafiya za ki yi, amma tunda kin zo bari na kira su na faɗa musu sai su zo nan ɗin..."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull