Ganin ido complete Novel - Chapter 67
Ganin ido complete Novel Chapter 67: Ganin ido complete Novel Chapter 67. ******* Ni kuwa, da Dayaa ya zo mini da zancen wai na shirya idan lokaci ya yi na…
3,362 words
******* Ni kuwa, da Dayaa ya zo mini da zancen wai na shirya idan lokaci ya yi na bi Suhaib mu wuce Sudan maganar ba ƙaramin girgizani tayi ba, duk da cewa ya yi mini albishir da cewa na soke zancen auren sa da Noura. Sam ni dai ban ji nutsuwa ba, dama ace da shi ne. Ina nan ina ta lissafin tafiyarmu Nigeria wurin auren Hairi sai ga shi kuma daga baya zance ya sha bambam. Tun da na nuna rashin amincewata na ga kamar ransa bai yi daɗi ba yasa dole na amshi maganar hannu biyu tare da faɗawa da kuma Su Aunty Labiba halin da ake ciki. Inda hankalina ya ƙara kwanciya shi ne, dukkan su kowa ya goya baya tare da kwantar mini da hankalina suka ce ai ba komai can ɗin ma kamar gida ne ai. Kuma ma Aunty Nadeeyah za su zo tare da Mummy Na'imatu da Baba Ustaz da kuma matar Kawu Ɗan-Ladi, idan ana saura gobe ɗaura aure za su zo. Da wannan sai naji hankalina ya kwanta sosai.
Duk da cewa naga an cire ni cikin family group ɗin su na Familyn SAMI, Sam hakan bai dame ni ba, daman tun can ba ce musu na yi ina buƙata ba, su ne suka sakani don raɗin kansu, yanzu kuma don sun cire ni mi zai sa na ji zafi? Babu.
Nan aka hau shirye-shiryen auren su Hairi ba kama hannun yaro, haraka ake ta girma da masu ƙumbar susa da suka amsa sunan su.
Buki aka shirya na gani na faɗa ta kowane ɓangaren. Hairi tayi kuka har ta gaji da ta ji cewa wai ba zan tsaya wurin aurenta ba wanda yanda take kukan har ni sai da ta saka ni domin ta bani matuƙar tausayi, wanda yake son ka ai kaima sai ka so shi ka kuma damu da al'amarinsa.
Duk abin da ake sai da muyi ta gani muna chart ta Waya. Ban sha kuka ba sai ranar da muka shirya ni da Ango Suhaib zamu tafi Sudan, shi kuma Ya Mohaa shi da Ango Emraan za su wuce Nigeria. Tamkar zai yi kuka haka ya yi kamar wanda aka cewa shikenan mun rabu na har abada. Ko kaɗan yanzu ba ya son abun da zai rabamu da juna idan ba dolen dole ba. Da kuka da komai haka yayi nasarar lallaɓani na tafi ana saura sati ɗaya bikin su kuma suka wuce.
Ban san dalilin sa na haƙiƙancewa akan dole sai nayo wannan tafiyar ba, amma tunda har ina son farin cikinsa dole na yi haƙuri na amsa hannu biyu ko raina baya so. Ga Cikina yanzu ya fito sosai kamar wacce ta kai lokacin haihuwa amma kuma da saura sosai. Shi lallashina yake yana faɗin ai kada na damu domin cikin ya bani lafiya sosai fiye da yanda bamu tsammata ba, kuma In Sha Allahu lafiya lau zan je na dawo.
Koda muka sauka motocinsu suna ƙasa suna jiranmu, hakan yasa ba ɓata lokaci muka nufi gidan, gabana sai faɗuwar yake wanda na rasa dalili.
Bakin gidanmu Suhaib ya bada umarnin a ajiye mini kayana kamar yanda Ya Mohaa yace. Domin cewa ya yi na zauna a gidana, idan ina so in gansu sai in shirya in tafi domin kada ya zama can gidan an takura ni.
Sosai na yi na'am da wannan shawarar domin magana ta gaskiya zan fi jin daɗi a yanzu musamman da bansan ya za su karɓeni ba a wannan karon tunda wata ƙila gani suke kamar ni ce na hana ya aura er su.
Da shigarmu gidan, abun da zuciyata take rayamin shi na tarar ko Ince ya ma zarce yanda na hasasa, domin idan ba Suwara da Taimiyya ba...babu wanda ya yi mini tarbon arxiki har su Aunt Fattoom. Babu abunda yafi bani al'ajabi da mamaki kamar yanda Jadda ta yi mini. Tamkar wata baƙuwar suka fara gani haka suka tarbeni a wulaƙance a yatsine. Musamman Jadda, domin a yanda nake gaisheta ma ko alamar arzikin ta tsaya ta kalleni ban samu ba. Da farko na ɗauka yanayin baƙi ne da ya cika gidan yasa wata ƙila bata ganeni ba, sai daga baya da naga tana ta zuwa tana dawowa ne yasa na sake cewa.
"Jadda na fa iso tun ɗazu.."
A ɗan tsawace ta yi mini wani kallon sannan ta ce.
"To Beenafah zan raba kaina gida goma ne? Ko ba ki ga ina ji da baƙi ba ne? Ki jira ina zuwa tunda dai ke baƙuwa ba ce a gidan nan."
Wallahy a yanda na ɗimauta na gigita da mamaki sai da naji ɗan cikina ya hautsina tamkar zan sako fitsari haka na ji. Mutanen da suka cika parkourn sai kallona suke tamkar na nutsa cikin ƙasa haka naji, ga yunwa daman ga fitsari ina ji ga gajiya. Sannan tun ɗazu su Suwara sun wuce ban ƙara ganin giftawar su ba.
Wani irin matsanancin kuka ne yaso ƙwace mini amma dole na dake domin ina jin tsoron kada na yi kukan kuma ya zamto matsala. Bayan ƙara zaman kusan mintuna talatin babu wanda ya kula ni yasa na miƙe har ina dafe kaina tsabar yanda na ke ji na lallaɓa na fita zuwa gidana. Ina shiga na rufe da Key na je da sauri na yi fitsarin da ya addabeni sannan na fito jiki na rawa na kira Suhaib na ce dan Allah yasa a kawo mini abinci domin tun da na shigo gajiya ta rufeni na kasa fita wurin Jadda, amma idan na ci abinci na yi wanka na huta, zan fito In Sha Allah.
Ina nan ba jimawa sai ga Taimiyya ta ƙwanƙwaso mini. Tambaya ta take hankalinta a tashe akan cewa miye yake damuna ganin kamar nasha kuka na ce mata ba komai, kawai gajiya ce. Daga haka ta juyo domin ta ce mini aiki take ana jiranta.
Haka na koma na je naci abincin sannan naji na fara dawowa hayyacina. Salloli nayi sannan na rarrafa na watsa ruwa wanda a lokacin ƙarfe tara na dare ake magana na samu wuri kawai na kwanta.
Wani irin kuka ne ya ƙwace mini mai tsananin na rashin taƙamaimen ma abunda yake damuna. Tambayar kaina na fara da cewa ni nai musu? Minai musu da har na cancanci wannan wulaƙancin? Ko ba su kulani domin komai ba suna kula ni ko don cikin jikansu da yake jikina. Har yanxu babu wanda ya biyo sawuna...Jadda taƙi ta zo taƙi ta aiko a bincika lafiyata, ya na zo, na ci abinci ko banci ba?
Ina nan na ji wayata na ringin, ina dubawa naga kiran Suhaib ne yake ce mini wai ga Jaddi a bakin ƙofata yana son Magana da ni.
Ta shi na yi da ƙyar na rarrafa na je na buɗe sai gashi a tsaye yana mini murmushi. Kayayyaki ne a hannun sa, ganin hakan yasa na janye ya shigo daga ciki muka zauna a parlour.
"Beenafah an zo lafiya?"
Sosai na shiga ƙoƙarin ɓoye hawayena ina murmushin Ƙarya na jinjina kai na na ce.
"Lafiya ƙalau Grandpa..."
"To miyasa kike na ke kaɗai? Ba za ki shiga can ba ne? Kamar zai fi ko? Domin kada ki zauna ke ɗaya."
Jinjina kaina na yi na ce.
"In Sha Allahu daga zaran na kambala abin da nake zan je Grandpa.."
"To masha Allahu. Kinga kayan fruit nan na kawo miki su, har gona naje da kaina na ɗebo su daga bishiyarsu domin ki ke kaɗai. Sannan wannan...."
Ya ɗago wata kwalba yana nuna mini ya ce.
"Za ki riƙa shan murfi ɗaya a kullum kin ji ko?"
Sosai na ji duk wani baƙin cikin da suka ƙunsa mini ya washe yanda Jaddi ya nuna tsantsar kulawarsa a gare ni. Ya jima yana mini addu'a sannan daga ƙarshe ya miƙe da nufin tafiya. Har ya kai ƙofa sai kuma ya juyo yana murmushi ya ce.
" Af! Kin ga kuwa na manta, Na sa an gyara miki Rooftop ɗin ki, naga kina son wurin, hakan yasa na saka aka shirya miki shi, idan kina so za ki iya tafiya ki zauna."
Yanzu kam har da guntun hawayena wurin yi masa godiya. Yana fita sai ga kiran Dayaa ya shigo. Ɗauka na yi muka gaisa ya shiga yi mini tambayoyi akan yanda tafiyata ta kasance da kuma yanda na ji zaman gidan na wuni ɗaya. Murmushi kawai nake ina ce masa komai lafiya lau amma ba don komai ɗin yana lafiya ba. Sosai ya damu yana ta tambayata abin da yake damuna na ce masa gajiya ce. Yanzu haka ina so ma na kwanta. Da haka na samu ya ƙyaleni tare da yi mini fatan tashi lafiya.
Wato abinda na ɗauka a wannan tafiyar tawa;Mutane a kullum kwanan duniya ƙara baka darasi suke. Domin su Jadda sun bani darasin da har na koma ga Allah ba zan manta ba. Wato dole sai sun ƙuntata mini tunanin cewa ni ce na hana auren Mijina da er su Noura.
Haƙiƙa na yi nadama, na yi nadamar wannan zuwan da nayi, kuma har abada ba zan daina nadama da baƙin ciki ba. Wato duk abin da na yi gudu ban tsere masa ba. Dani da babu ni duk ɗaya,babu wanda yake damuwa da shin na fito ko kuma ban fito ba. Gidan ya cika sosai da sosai mutane ta ko'ina. Ni kaɗai ke kwana a gidana domin su Suwara suna can suna gararinsu na 'ƴammata. Jadda ta koma mini wata mace ta daban, domin Jaddar da na zo na tarar a wancan zuwan ba ita ba ce a yanzu. Na kasa gayawa mijina halinda nake ciki. Kullum sai dai in yi masa Ƙaryar cewa ina lafiya kuma komai yana tafiya daidai, amma ba don komai ɗin yana lafiya ba. Tamkar wacce take cikin ƙungurmin daji tana neman agaji yanayin da na tsinci kaina kenan a ciki. Na ƙagu na ƙosa ranar bukin ta zo inga su Aunty Nadee ko zan samu na ji sanyi a raina. Hatta abinci wannan sai idan na kira na ce a kawo mini. Wallahy na san idan na faɗa masa halin da nake ciki nasan cewa shi da su har abada. Amma ba zan yi hakan ba, dole na yi haƙuri, Allah yana sane dani, kuma ma ai ba nan zan tabbata ba, ana gama bukin Dayaa zai zo nan mu wuce gida idan ya kawo Hairi ɗakinta. Da wannan idan na tuna sai in ji er nutsuwa ta shigeni. Shiyasa akoda yaushe nake kan yin waya da su Ammie su Aunty Labiba duk da cewa babu wanda na faɗawa halin da nake ciki.
Bukukuwansu kawai suke ta yi masu cike da ƙayatar wa.
Yau koda na wayi gari, a farin ciki nake, domin an tabbatar mini cewa Su Aunty Nadeeyah suna hanya. Hakan yasa na shirya da wuri amma dai ina cikin gidana ban fita har sai da na ji cewa sun iso.
A wani babban parlour ne na musamman aka saukar da su wanda yake can cikin wani mansion ɗin da ake buɗe saboda su.
Kusan sanƙamewa na yi a tsaye ganin cewa wai harda Ammie suka zo. Daman ita amma suka ɓoye mini babu wanda ya faɗa mini?
Shigowar Jadda shi ne abinda ya yanke mini hanzarina na tsaya a nan inda nake tsaye ba tare da motsa ba.
Tana kallon inda nake sai kuma ta mayarda kallonta wurin su Ammie wanda ita ce mutum ta farko da idonta ya fara sauka a kanta.
"NANA MARYAM? ba cewa kika yi ba za ki samu zuwa ba? Saboda wannan shashashar mai son kanta ta hana Hammodi ya auri Noura shi ne kika yi fushi Nana maryam??"
Waigowa ta yi sai kuma ta dawo da kallonta gare ni cike da tsana ta ce.
"Ke ɗin kin cika mai son kanki Beenafah! Ke fa macece.. Kisa kanki a takalmin Noura. Idan kice mijin ki ya mutu aka ce ga ɗan uwanki zai aure ki domin ya tallafeki keda marayun 'ƴa'ƴan ki amma matar shi ta ce bata amince da ya aureki ba ya za ki ji dan Allah? Kin cika muguwa azzaluma marar tausayi Beenafah...sam ba ki kyauta mana ba..."
Aunt Fattoom dake tsaye a bayanta cike da shock ta ce.
"Jadda Wannan fa ba Nana Maryam ba ce ki duba ki gani? Nana Maryam ta fi wannan jiki...sannan su ne fa dangin Emraan da akace za su zo...ga Nadeeyah ai kin gane ta.."
Da gudu ni kam naje na faɗa Jikin Ammie ina mai fashewa da wani irin mugun kuka jin irin munanan kalaman da ta yarfa mini.
Lokaci ɗaya dukkan ilahirin jikinta ya ɗauki rawa, ta hau nuna Ammie da yatsa tana rawar baki alamar magana ta ke son furtawa amma kuma hakan bai samu ba, domin ganin kawai muka yi ta zube ƙasa somammiya.
✍️ *OUM-AMEER* ✍️
*GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 55*
Bayan Jaddan ta farfaɗo ne da gudu Aunt Fattoom ta fita, ba jimawa sai ga ta tare da wata tsohuwa wacce kamanninta sak Jadda tamkar an tsaga Kara.
Kallon Jadda tayi wacce ta soke kanta a ƙasa ta ke ta rusa uban kuka, hankalinta a ɗimauce ta ce.
"Samaahat! Da gaske ne abinda Fattoom ta faɗo mini?? Da gaske ne?"
Yatsanta kawai ta iya ɗagawa a raunane ta nuno saitin inda muke tsatstsaye tun ɗazu mun zubawa sarautar Allah ido, daga mu har su Mummy Na'Imatu su Aunty Nadeeyah, al'ajabi ya ishemu ya sha mana kai. Musamman ganin irin uban kukan da take rusawa.
Direction ɗin yatsan Jaddan ta biyo jikinta yana wani irin ciccira sosai ta zo ta tsaya gaban Ammie.
"NANA HAUWA?? Nana Hauwa da gaske ke ce? Daman ina da rabon sake ganinki a duniyar nan? Dan Allah ki mini magana....ki mini magana dan Allah.."
Wani irin matsanancin kuka ne ta sake fashewa da shi, kukan da duk mai zuciya a ƙirji matuƙar yana da tausayi sai ya ji wani abu idan ya ji yanda take kukan tsabar yanda ta gigice.
Kallon kallo muka fara wanda kowa sai bin ta yake da ido domin mun ji wani abu na daban wanda ya ruɗa mana zuciya, musamman Ammie wacce aka kira wai da NANA HAUWA bayan ta ji ɗazu an kira wata da NANA MARYAM.
Tasowa Jadda ta yi ta zo ta ɗago Tsohuwar tana kallonta cike da tausayi ta kira sunanta ta ce.
"Sumaiha! In Sha Allahu ta'ala! Ko kokonto babu, wannan ita ce Nana Hauwarmu. Itace, ABUBAKAR SIDDEEQEE ya ɗauka cewa wai shi yana da wayo, ya ɗauka cewa wai shi yana da dabara, ya manta cewa Ubangiji shi ne wanda yake da iko akan komai. Sai dai kuma...Allah ba azzaluman sarki ba ne! Yana tunanin ke ce wacce ya cutar, sai ga shi ya shiga jarabawar da ya kasa jurewa."
Ƙara matsowa tayi dab da Ammie ta saka hannu ta shafo fuskarta wanda dukkan su sai da suka ji wani abu mai kamar shock ya shige su a lokaci ɗaya.
" Tabbas gaskiya kika faɗa Samaahat, bana buƙatar kowace shaida domin wannan 'ƴa ta ce Nana Hauwa!!!"
Wani irin zazzare ido muka fara jin wata iriyar magana kuma mai ban mamaki. Ammie ba ta tsaya komai ba kawai ta rungumeta tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka. Duk da cewa bata da tabbacin cewa da gaske ne ko a'a. Kukan da tsohuwar ke yi ya daki zuciyarta ba kaɗan ba.
Tsaye muke kamar wasu shashashu inda su kuma suka hau kiraye-kirayen wayo yi.
*********
Auren da za'a ɗaura gobe juma'a, dole aka ɗage shi zuwa ranar Monday daga nan ɓangaren Emraan, wanda shi kam na Suhaib ba'a fasa shi ba.
Tsawon kwana biyu kenan na kasa matsawa daga jikin Ammiena kamar yanda itama ta kasa matsawa daga jikin mahaifiyarta kamar yanda tsohuwar tayi iƙirari duk da cewa har yanxu ba mu ji wata gamshashshiyar hujja ba. Hmmm! Allah sarki! Uwa kenan!.
Daman tun a jiya, Noura da mahaifiyarta suka iso wanda tabbas kallo ɗaya za ka yi mata da Ammie Kaga kamanninsu tsantsa, dole duk wanda ya gansu ya ruɗe ya kasa bambance su da juna Indai ba kasan su sosai ba. Duk da cewa Ammie ta ga wannan ƙwaƙwƙwarar shaidar...har yanxu a zuciyarta ta kasa yarda muddin ba sheikh ta gani a gaban ta ya tabbatar mata ba.
Nikam na yi kuka sosai tare da neman su gafara domin sai da suka haɗu ne na gane kuskurena, da ace na ɗauki maganar Dayaa tun a ranar da ya kirani da yanxu sun jima da ganawa da juna. Amma sai nake gani da kuma tunanin cewa kada na ɗaga musu hankali a banza alhali babu abinda suka haɗa.
Zaman jiran isowar Sheik muke da kuma ainahin mahaifinta wanda aka ce sun iso kaɗan ya rage su ƙara so.
Fitsarin da ya matsamin ne yasa na miƙe ina kallon Ammie na ce mata zan je na yi fitsari.
Jadda na ganin na miƙe ta taso itama ta biyoni tana faɗin na yi a hankali kada na zame, amma dai bari ma ta rakani.
Wani uban tsaki na ja a raina, ina faɗin ai duk neman gindin zama ne, idan ba shi ba, ni yarinya ce da za ta ce kada na zame? Tun can bata san cewa kada na zame ba sai yanzu? Zamewa ta nawa kuma? Ai gwanda ma ace na zame na faɗin wallahy ya fiye mini alheri da irin azabar da suka ɗanɗana mini kwana biyu.
Ina shiga gidana na datse ta ciki, sannan na wuce na yo fitsarina na fito. Wayata na ɗauko na kira Dayaa muka sha fira wacce bana gajiya da saurarensa sannan daga ƙarshe muka yi sallama yana faɗamin cewa ana kan shirya Hairiyya ɗin gobe Lahadi za su taso zuwa nan ɗin In Sha Allah.
Ina hango tsayuwarta, na juya naje ta ƙofar kitchen na buɗe na fice, ta baya na zagaya na shige na barta a nan.
Shiga ta ba'a fi minti uku ba sai ga su sun shigo. Wani irin ɓari jikin Ammie ya ɗauka ganin da gaske kuwa Sheikh ne da wannan mahaukacin wanda yake zuwa a matsayin babanta. Duk da cewa baya cikin wannan shigar da ya saba ta mahaukata,yana shirye cikin shigar Larabawa waɗanda suka jiƙe da kuɗi da kuma jindaɗi, ga shi kuma da medicated glass, duk hakan bai hana mata gane shi ba, tabbas a yau ta shaida shi. Shi ne wannan.
Kukanta ne ya tsananta wanda tama rasa ina za ta dafa. Da kanshi ya iso har inda take, sai dai kafin ya ƙarasa Isa, wannan tsohuwar wacce muka ji Jadda ta kira da Sumaiha ce ta tare gaban shi cike da zafi a kalamanta ta ce.
"Kada ka taɓa mini 'ƴata SIDDEEQEE!!!"
Ta shi Ammie ta yi taje ta faɗa jikin Sheikh tana kuka ta ce.
"Sheikh...Wai miye yake faruwa? Su waye waɗan nan ɗin? Na rantse da Allah ba don na ganka a tare da su ba, tabbas ba zan taɓa aminta da duk abinda za su faɗa mini ba."
Jinjina kai Sheikh ya yi sannan ya dafa kafaɗunta yana mai zubar da ƙwalla ya ce.
"Mulaifa! Tabbas wannan shi ne mahaifinki. Shi ne wanda ya kawo ki gare ni. Ya dawo bayan kin ɓata daga gareni Mulaifa. Ya ce mini ya kwanta matsananciyar jinya ne lokaci mai tsawo, shiyasa bai dawo ba, bayan ma ya warke akwai wasu dalilai da suka hana shi dawowa sai a wannan lokacin. Kin gan shi ko? Abubakar Siddeeqee ne ashe wanda aka fi sani da Siddeeqee a ƙasar Qatar. Sam shigar da yake a wannan lokacin ta hana mini na shaida shi...Na yi kuka, na yi addu'a da neman Allah ya bayyana mini ke domin in damƙa ki hannun mahaifinki. Kullum sai na roƙi Allah akan ya ƙara mini tsawon rai domin na ga na mayar da amanar da aka bani. Sai dai, a neman ki da na yi ta yi ƙarshe Yayan Mijin ki shi ne wanda ya tabbatar mini da cewa kun mutu a haɗarin mota daga ke har 'ƴa' ƴan ki...Mulaifa! Ki gafarceni. Ban san abinda ya faru da rayuwarki ba, amma tabbas laifina ne dana haɗa ki aure da mutumin da ban sani ba..."
Waigawa yayi Wurin Wanda aka kira da Siddeeqee ya kamo hannun sa ya jona dana Ammie ya ce.