Ganin ido complete Novel - Chapter 7
Ganin ido complete Novel Chapter 7: Ganin ido complete Novel Chapter 7. " Ah to! Ni da ka yi shawara dani ma tun farko ai wallahi ba gidanda za'a basu sai…
3,346 words
" Ah to! Ni da ka yi shawara dani ma tun farko ai wallahi ba gidanda za'a basu sai dai su je can susan yanda za su yi,da shikenan mun huta da gaibu."
"Eh to, banƙi ta taki ba, amma dai kinsan ko ya ya ne su ɗin jinina ne tunda ƙanina ne ya haife su. Da ace kin amince kamar yanda na ce tun farko da sai mu zo nan da su, idan yaso ita ɗin sai a barta a can..."
Da sauri ta ɗaga hannunta ta ce.
"A'a wallahi. Rabani da gayyar tsiya gayyar na ayye. Su tsaya can inda yafi dacewa da su"
****
Zaune nake na buga uban tagumi a bakin wurin da na ajiye kwanonin wanke-wanke ina ta karanta wasiƙar jaki tsawon lokaci.
Muryar Ammie na ji a kaina tana faɗin.
"Beenafah...!Beenafah Lafiya kuwa?"
Kukan da nake riƙewa ne ya ƙwace mini ina kallonta na ce.
"Ammie Yaya Ashiru! Ina matuƙar jin kewar sa a rayuwata, shikenan Ammie, Shikenan mun rasa Yaya Ashiru da gaske? Mutumin kirki wanda ya ɗaukemu tamkar en uwansa."
Cike da tausayawa ta dafani ta ce.
"Ki yi haƙuri, In Sha Allahu watarana zamu sake haɗuwa tun da muna a gari ɗaya..."
"To Ammie shikenan? Shikenan da gaske rayuwarda zamu ci gaba da ita kenan? Da gaske Daddy ya rabu damu tamkar bai san su waye mu a wajen sa ba?"
Kujerar tsugunno ta janyo ta zauna a kusa dani a hankali ta ce.
"Beenafah! Ki daina cewa haka domin babu wanda yasan gobe. Ki ci gaba da kyautatawa Allah za to, ki yi haƙuri, lokaci ya yi da ya kamata mu manta da bayanmu mu fuskanci gaba. Kinga cikin wata ukun nan, mun ci kuɗi sun yi dubu dari biyu, kuma idan bamu yi wani shiri ba sauran kuɗin nan suma haka za su ƙare. Ko million kake da shi matuƙar baka riƙa juya su ba kace za ka riƙa zara watarana sai an wayi gari ba ko biyar...."
Jiki a sanyaye na ce.
" To ko yanzu Ammie miye ya rage? Dubu ɗari da saba'in mi za su ce mana? wacce sana'a zamu tsira da su har ta iya riƙemu har kuma muci abinci a ciki Ammie? Ga Bahrain dole ya kamata ya koma school Ammie...."
Miƙewa ta yi ta shiga ɗaki ta ɗauko wata jaka ta buɗe tare da fitowa da wani tsumma dake dunƙule. Kwance ƙullin tayi, sai dai kuma wayam! ba komai a ciki.
Cike da tashin hankali ta shiga faɗin.
" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! "
" Lafiya Ammie? Miye kike nema haka?"
Na faɗa nima hankalina a tashe ina mai tsatstsareta da ido.
Ɗakin ta sake komawa ba tare da ta tankani ba ta hau birkita kayan dake ɗakin wanda tana yi tana hawaye a hankali tana kiran sunan Allah. Sai da ta yiwa komai namu kaca-kaca amma kuma da alama ba ta yi nasarar samun abin da take nema ba.
Cike da damuwa na ce.
"Ammie wai miye kike nema haka?"
Lumshe idanunta ta yi a hankali sannan ta buɗe tana mai share hawaye ta ce.
"Ba komai Beenafah. Yanzu miye abin yi?"
Ɗan Jim! Na yi ina nazari tsawon lokaci sannan daga ƙarshe na ce.
"Muje a kai Bahrain makaranta kada kuɗin nan ya iyarda salwancewa, gashi shikenan tallafinmu ya ƙare na wurin Dr. Basheer."
***
Islamiyyar Ummul-Qura dake Muslim foundation muka kai shi inda muka masa registeration dubu goma sha ɗaya komai da komai. A nan suka yi mana tayin makarantar bokon su domin har boko ake a wurin, amma sai muka ƙi amincewa saboda yanayin rayuwa. Bayan naga jadawalin su sai na ji makarantar ta burgeni sosai, hakan yasa na ja Ammie gefe na ce.
"Ammie mu biya masa nan ɗin kawai, makaranta ce mai kyau.."
"Amma Beenafah.."
"Ammie karki damu. Ina da plan, in sha Allah zamu iya. Ki ƙarfafani Ammie in cika mafarkina akan Bahrain, Daga term sai term ne fa.."
Cikin shakku ta ce.
"Beenafah.."
"Mu je Ammie in sha Allah zamu iya."
Bayan mun kambala tun a hanya Ammie take mita har muka iso gida.
Bayan ta zauna na ɗauko mata abinci da ruwa da magani sannan na zauna a kusa da ita.
"Ni fa Beenafah duk ba wannan ba,yanzu ke dan Allah kina ganin ba mu ɗauko abin da yafi ƙarfinmu ba? Dubu tamanin da shida fa muka bayar zama ɗaya! Kin san fa har yanzu ina kan zuwa follow-up. Don ma Allah ya taƙaita mana yanzu an rage magungunan ba kamar can baya ba, amma kuma har yanzu bamu daina saye ba. Ga abinci, ga buƙatocin rayuwa..."
Hannunta na riƙo ina murmushi na ce.
"Ammie...Dole mu yi aiki tuƙuru domin goben Bahrain. Saboda haka mu samu wata sana'a da zamu riƙa yinta a cikin gida ko kuma ni na riƙa fita da tallar..."
Da sauri ta girgiza kanta ta ce.
"Har abada, komai zai faru Beenafah ba za ki yi tallah ba. Mu siyo kayan ƙulle-ƙulle mu riƙa saidawa a gida."
Da wannan shawarar na amince mata na karɓi kuɗi na tafi kasuwa na yo mana sarin kayayyaki muka zauna muka ƙulla sannan na shiga maƙotan da muke da su zagaye damu na tallata musu.
****
Haka rayuwa taci gabar mana da tafiya wanda yau da gobe bata bar komai ba, gashi mun wayi gari sana'ar da muke ta cikin gida kaɗai ta tabbatar mana ba zata iya riƙe mu ba.
Da ƙyar muka samu mu kayi masa registeration ɗin third term satin nan da ya gabata. Gashi komai ya yi mana tsaye sai godiyar Allah.
Yau ma Ammie na zaune waje akan sallaya misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe ta buga uban tagumi na fito cikin shirina na zauna dab da ita na ce.
"Ammie kina tunani ne akan abin da zamu ci gobe ko? Ai na duba na gani, shinkafar kwata-kwata iyakacinta yau, ga shi ba kuɗi kuma ba wani dogon ciniki.. Ni ina ga Ammie, ki ɗauki shawarar Maman Fakiha ki yarda na riƙa soya Awara da dankali a ƙofar gidannan, zama a haka bai zai yi ba..."
Da sauri ta girgiza kanta tana mai tsiyayar da ruwan hawaye ta ce.
" A'a Beenafah! Kowa da ra'ayinsa, Maman Fakiha tana iya ɗorawa 'ƴar ta talla, ni ba zan iya ba."
"Ammie ki yi mini izini na tafi gidan matar nan da na yi miki bayaninta wacce Biba ta kaini wurinta. Kinga aikin ba na kwana bane iyaka naje da safe daga zaran na gama mata aikinta sai na dawo gida abina. Zan ce mata bana buƙatar komai kawai idan wata ya yi ta biyani kuɗina, hakan zai taimaka sosai... "
" Beena... "
" Ammie dan Allah kada ki ce a'a. Wannan ita kaɗai ce hanya tunda bakya son na yi talla....."
Ganin still kamar tana kan doubting yasa na kama hannayenta tare da rausayar da kaina murya a ƙasa sosai na ce.
"Ammie! Idan ma kina wani tunani a kaina ne please ki daina. Kinfi kowa sanin wace ce ni,abinda zan iya da wanda ba zan iya ba...in sha Allah zan yi iya yina Ammie....."
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa*
*FREE-BOOK*
*PAGE 10*
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta jinjina kanta ta ce.
"Shikenan. Allah yasa a dace."
"Amin..."
"To amma kin san gidan ne?"
"Eh, bayan gidanmu ne fa wanda muka taso, wannan Layin baya ɗinnan. Amma dai zan hau Mashin ga ɗari huɗu nan a hannuna yanda zai mini sauƙin ganewa."
"OK to, Allah ya tsare."
"Amin."
Har na miƙe tsaye sai kuma ta kalleni ta ce.
"Yau ni zan yi girki kenan Beenafah?"
Da sauri na ɗaga yatsata na ce.
"A'a Ammie...."
"Zan iya fa, ba abinda zai faru..."
"A'a ni dai Ammie dan Allah. Kada ki yi, ga sauran ɗumame nan zai isa kuci da ranar nan har na dawo..."
Murmushi ta yi ta ce.
"To na ji, idan ni an yi mini dole to shi Ɗa na fa? Shima tuwon zai ci? Kin san fa hali..."
Dariya na yi sannan na ce.
"Kai Ammie wane irin an yi miki dole magana ba daɗin ji haka..."
"Eh mana,..."
"Ammie shima idan ya dawo ya ci tuwon kawai, kisha masa toka dole zai ci ya wuce. Ban yarda a kunna wuta idan bana nan ba, ƙarshen magana. Na wuce sai na dawo."
Dariya ta yi tace.
"To Uwa, Allah ya tsare."
Ni ma dariyar nake har na fice daga gidan zuciyata fal da farin cikin samuwar sauƙin Ammiena. Sai yanzu ma na gane cewa akwai hikima cikin tashin Daddy zuwa Abuja da kuma korarmu da ya yi. Na sani akwai ciwo har abada a rayuwarmu amma kuma nisantar su da mukayi ya sauya mana rayuwa daga baƙin ciki da ƙunci zuwa farin ciki na dai-dai rayuwar da Ubangiji ya zaɓa mana. Da ace har yanxu muna tare da su da yanzu ciwon Ammie yana nan yana ƙara hauhawa da yin barazana ga rayuwarta.
Daga gidanmu zuwa titi akwai tazara sosai, ga uwar rana yau ana ƙwalawa, hakan yasa na samu wata inuwa na zauna ina hutawa. Duk wata Keke-Napep ɗinda za ta wuce haka zan ƙura mata ido ina kallon mammallakinta har sai ta ɓacewa ganina. Tun bayan da muka rabu da Yaya Ashiru haka nake akoda yaushe na fito daga gida sai in riƙa jin kamar zan gansa a ciki,zuciyata ta kasa mantawa da shi ko na rana ɗaya.
Ni ɗin yarinya ce ƙarama mai ƙaramin tunani, a shekarun rayuwata da irin rayuwar da nake fuskanta bana tunanin na san ma miye soyayya take nufi. Kawai dai ina jin tsananin kewar shi wanda wasu lokutan har kuka nake yi da fatan Allah ya haɗani da shi watarana. Rashin Yaya Ashiru ya bar mini wani tabon da ba zai taɓa goguwa ba a zuciyata.
Bayan na gama hutun jakin na miƙe na ƙarasa titin na tare abun hawa na yi masa kwatancen inda zai kai ni. Unguwar dama can sananne wuri ne ba yanka za ka sami mutumin da zai ce bai san wurin ba.
Muna isowa kan corner na sauka daga nan don kada ma na hango tsohon gidanmu na sharce daga nan kawai na wuce gidan.
Ban san cewa na yi katoɓara ba sai da na iso bakin gate ɗin gidan mai gadin su ya tsareni yana min tambayoyin wai wace ce ni kuma daga ina nake?
Jiki a sanyaye na ce.
"Wurin matar da ke ɓangaren can na dama na zo..."
Wani irin kallon sama da ƙasa ya yi mini sannan ya ce.
"Gaskiya yanzu an daina barin ma su neman taimako suna shiga gidan nan saboda haka ki yi haƙuri kawai ki wuce..."
Gabana ne ya yanke ya faɗi jin yana neman lalata mini shirina wanda shine last hope ɗina a yanzu. Cike da magiya na fara roƙonsa na ce.
"Dan Allah ka taimaka mini mana...Allah fa na ce!"
"Ahf! Komai fa za ki ce ba zan barki ki shiga ba tunda mai gidan da kansa ya umurceni.."
"Haba malam dan Allah! Kayi haƙuri ka ce mata mai aikinda Biba ta kawo mata ce."
"To kinga sai yanzu kikayi magana...Bari na sanar mata a waya in ji."
Daga haka ya ciro 'ƴar ƙaramar wayarsa daga aljihu ya daddana ya kira. Bayan sun gama magana ya kalle ni ya ce.
"An ce ki shiga."
Da sauri na tura kaina gidan ina faɗin na gode. Ina shiga na ƙwanƙwasa sai ga wata matashiya ta zo ta buɗe rungume da blender a hannunta ta ce mini na shigo.
Wuri na samu cikin haɗaɗɗen parlurn da ya amsa sunan sa parlour na zauna tsawon lokaci ina ta kallo a TV can sai ga ta ta sauko.
Gyara zamana na yi da kyau bayan ta zo ta zauna, na ce.
"Ina wuni?"
"Lafiya ƙalau.....Sai yanzu ki ka zo?"
Da sauri na girgiza kaina na ce.
"Ki yi haƙuri, mahaifiyata ce ta yi rashin lafiya sai da muka yi jinya a Sokoto."
"OK.. Ya ma kika ce sunan ki?"
"Sunana Beenafah."
Jinjina kanta ta yi sannan ta ce.
"Beenafah! Kin ganni nan? Bana son ƙazanta,bana son kwaɗayi, bana son sata, sannan uwa uba bana son shisshigi da kuma ƙeta. Akan waɗannan sharaɗoɗan ne yasa na kasa zama da masu aiki da yawa, sai Hajjo kaɗai wacce kika ga tazo ta buɗe miki ƙofa. Mahaifiyar Biba ta yi aiki a gidanmu tsawon lokaci kuma munyi zama na mutunci da ita shiyasa da ta kawo ki ta roƙeni na ji ba zan ƙi yi mata alfarma ba hakan yasa na amince. Allah yasa za ki iya kiyayewa da duk abinda na faɗa miki."
Gyaɗa kaina nayi a hankali na ce.
" In sha Allahu zan kiyaye."
"Sunana Labiba Attahiru Araam, ni ɗin nan Lauya ce ta gwamnati a ƙarƙashinsu nake aiki. Nan shi ne gidana, na haifi yara Uku, Raudah ita ce ta farko amma ta rasu ba jimawa, sai Adeel, da kuma Hanan."
Ban san dalilin hawayen ta ba, ko kuma don ta tuna da 'ƴar ta tace da ta rasu Allah masani, hakan sai yasa na ji tausayin ta sosai a raina, a hankali na ce.
" Allah ya gafarta mata yasa tana aljanna."
Jinjina kai tayi sannan ta ce.
" Amin. Yanzu ya kike so ayi?"
Cikin rashin fahimtar tambayar ta na ce.
"Ki yi haƙuri, amma ban fahimci tambayar ba."
Shiru ta yi na ɗan lokaci sannan daga ƙarshe naga ta danna wani abu can sai ga Hajjo ta shigo ta zauna a gabanta cike da ladabi ta ce.
"Ga ni Aunty Labiba."
Kallona ta yi ta ce.
"Wannan sunanta Beenafah, kije da ita, duk wani aikin shara da goge-gogen da kika san kina yi daga yau itace za ta koma yinsa, ki nuna mata komai yanda yake. Ke kuma sai ki ci gaba da wanke-wanke da girki kamar yanda kika saba."
"Tau yayi Aunty Labiba, In Sha Allah."
A tare muka ratsa babban parlourn da ita muka miƙa wata doguwar ƙofa haka, sannan ta kai ni wani parlourn wanda ya fi wancan da muka baro haɗuwa da tsaruwa. Nan ta shiga nuna mini duk inda zan riƙa sharewa da gogewa har da ɗakunan dake sama guda biyu da wani parlourn. Tana gama nuna mini ta bani kayan aiki ni kuma ba ɓata lokaci na ɗaure hijabina na yi na gama. Ko da na kambala ƙarfe biyu na rana ta yi. A can baya na zagaya inda na ɗebo ruwan mopping a famfo nayo alwala na zo kan verandar ɗin ƙofar baya na yi sallah sannan na dawo wurin Hajjo na ce mata na kambala.
Nan na jira ta ta shiga ta fito ɗauke da kula a hannunta ta ce mini ga shi in ji Aunty Labiba ta ce sai gobe na dawo. Godiya na yi mata na kamo hanyar fitowa daga gidan. A harabar gidan na tarar da wata haɗaɗɗiyar mota an wangale ƙofofinta yara na fitowa kimanin su shida, manya da ƙanana. Da alama wannan kam driver ne don ya yi kama da driver ɗin musamman yanayin yanda ya yi shiga.
Tsaye na yi hangame da baki ina kallon su har suka nufi ƙofafin uwayensu wanda da alama waɗannan da suka nufi gidan Aunty Labibar su ne Adeel da Hanan ɗinda ta faɗa mini ɗazu.
Kallona drivern ya yi ya ce.
"Malama Lafiya?"
Girgiza masa kaina na yi na ce.
"Ba komai."
"To ki wuce zuwa inda za ki mana."
Taɓe baki nayi sannan na sa kai na wuce a raina ina mita wai driver da shi zai riƙa wani iskanci kamar shi ne da gidan,aikin banza kawai.
****
Maple Crescent, Notting Hill, London, United Kingdom.
Misalan ƙarfe shida na yamma Ahlan ya shigo gidan bayan ya dawo daga wurin aikinsa. Tun da ya shigo yake ƙwala kiran Aysha amma baiji ta amsa ba. Duk wani lungu da saƙo dake gidan sai da ya duba amma bai ganta ba sai da ya kewaya garden sannan ya tarar da ita tana zaune tana darza kuka gwanin tausayi kamar ko yaushe idan abin ya ciciyeta.
Cikin tashin hankali ya isa gareta yana mai janyo ta jikin sa cike da nuna tsantsar tausayi ya ce.
"Aysha! Mummy ce ba?"
Sai yanzu ta ɗago idanuwanta da suka rine sosai tsabar yanda tasha kuka cike da karyewar zuciya ta ce.
"Ahlan shekara uku! Shekara uku ban haɗa fuska da iyayena ba. Me naiwa Mummy da zafi haka? Me nai mata dan Allah? Ahlan Wai har Daddy ya ce mini ita ce ta haifeni..."
Ƙara sassauta muryar sa ya yi sosai cikin ƙwararawa ya ce.
"Haba Ayshan Ahlan! Kada zuciya ta saka ki aikata abin da za ki dawo daga baya kina dana sani. Mummy ita ce wacce ta haife ki kawai dai akasi ne aka samu, ba komai bane wannan illa sharrin shaiɗan. saboda haka ki ci gaba da haƙuri ki ci gaba addu'a..."
"Ahlan har yaushe?.."
"Kai...Haba Aysha! Kin taɓa jin an ce haƙuri ya ƙare a duniya? Duk wanda kika ji an ce wai ya yi haƙuri bai ci riba ba to kaɗan ya yi...."
"Ahlan wallahi ina cikin tsantsar baƙin ciki da ƙunci. Akan abin da bai taka kara ya karya ba wai Mummy ta ce mini na yi nesa da ita, idan na sake tako inda take bata yafe mini ba duniya da lahira. Abu kamar wasa...Ah.. Ahlan.."
Rungumeta ya ƙara yi sosai ya shiga lallashinta kamar yanda ya saba har sai da yaji sautin kukan ta ya ragu sosai. Shi kansa bai taɓa ji ba kuma ya daɗe ko yace har yanzu yana kan mamakin rayuwa irinta surukar sa Mummy Zaliha. Ɗanka! Ka ce wai yayi nesa da kai, idan ya sake takowa sai ka tsine masa albarka. Wannan wace irin uwa ce..
"Ahlan..muje ka ci abinci.."
Da sauri ya dakatar da ita da faɗin.
"No Aysha... Zauna abin ki, bari naje sai na fara yin wanka tukun. Ina Baffa?"
"Baffa yana gun Salma yana bacci."
Miƙewa ya yi ya nufi ciki, bayan ya yi wanka ya shirya, ya yi sallar magrib sannan ya ɗauko wayarsa ya kira Daddy, bayan sun gaisa cike da girmamawa ya ce.
"Ahm! Daddy daman dangane da zancen Aysha ne, a matsayina na Mijinta kai kuma a matsayin Uba a gareta. Ya kamata ace an kai ƙarshen wannan abun, koma minene Mummy take ji ta yi haƙuri ta yafe mata. Yanzu ga auren ƙanwata Firdausi ya tashi, dole muna da buƙatar zuwa gida amma ta ce matuƙar Mummy ba ta amince da ta zo gida ba ita ba za ta je Nigeria ba. Daddy tun Baffa yana zanin goyo rabonmu da gida gashi yanzu har ya yi shekara uku. Aysha bata cikin walwala, kullum cikin kuka da damuwa. Kai kanka Daddy idan na kiraka kullum magana ɗaya ce cewa ta ƙi ta haƙura..... "
" To yanzu mi kake so Ahlan?"
" Eh.. Daman cewa na yi dan Allah ka ƙara bai wa Mummy haƙuri ko Allah zai sa ta sauko ta janye furucinta."
Daga can ɓangaren Daddyn ya ce.
" In sha Allahu zan ƙara ƙoƙartawa in gani. Zalihar ce ta cika kafiya wallahi."
"To daddy na gode, Allah ya bamu alheri."
****
Hayin malam Ibrahim. Gusau, Zamfara State. Nigeria.
Ina shiga na zauna kusa da Ammie tare da dire kular da ke hannuna ina murmushi na ce.
"Ammie sannu da gida."
Kallona take kallo mai cike da alamar tambaya ta ce.
"Yauwa. Wannan fa?"
"Ammie har na gane gidan har na yi aikina na yau na kambala sai kuma gobe..."
"Wannan kular fa?"
"Bayan na kambala aikina na faɗawa Hajjo, shine taje ta sanar mata sai gashi Hajjon ta kawo mini wannan kular ta ce Hajiyar tace na tafi sai gobe."
Jinjina kai ta yi alamar gamsuwa sannan ta ce.
"Miye tsarin aikin?"
"Shara ce da goge-goge kawai. Idan Mijinta yana sashenta sai sha ɗaya na safe zan tafi, idan kuma ba sashenta yake ba ƙarfe tara na safe ta yi min a can."
"Ta faɗa miki nawa za ta baki a wata?"
"A'a Ammie. Ba muyi maganar kuɗi ba gaskiya. Amma dai da gani matar tana da kirki.."
"Duk da haka ki kula Beenafah."
"In sha Allah Ammie. Kin san me ma..."