Ganin ido complete Novel - Chapter 70
Ganin ido complete Novel Chapter 70: Ganin ido complete Novel Chapter 70. Kallon sa na yi, sai kuma na yi murmushi domin yanayin yanda ya yi tambayar ne ya…
3,351 words
Kallon sa na yi, sai kuma na yi murmushi domin yanayin yanda ya yi tambayar ne ya bani dariya ba kaɗan ba.
Matsowa na yi tare da shigewa jikin shi na ce.
"Laifin me ka min da zan yi fushi mijina? Welcome...and I miss you."
Tattausan lips ɗinsa na ji yay min light peck a goshina sannan ya saka hannayensa ya kewayena da su tare da ɗora fuskarsa a gefen wuyana na ɗan lokaci sannan ya janye yana kallon cikin idanuna ya ce.
" Congratulations Bibina...na yi matuƙar farin ciki da jin kyakkyawan labarin cewa mu ɗin en uwana. Na sha mamaki sosai da na ji yanda abubuwa suka kasance, duk da cewa babu mamaki a cikin al'amarin ubangiji. Duk abinda ya tsara zai faru, to tabbas zai faru babu makawa. Jininmu ɗaya ta gefen iyayenmu mata, Grandma ɗinki da Grandma ɗi na uwa ɗaya uba ɗaya suke wai su ɗin twins ne. And mahaifiyarki da mahaifiyarki Noura, suma ɗin twins ne Bibi..."
Hawayena na share ina jinjina masa kaina da murmushi na ce.
" And...kai ɗin Yayana ne, kuma mijina, ɗan uwana. Miye yafi wannan farin ciki? Ga dangina na samu...kana ji ko Dayaa? Ban san waye kakana ko kakata na gefen uba ba, amma a jiya...samun Abiyh da na yi da Ammah..na ji farin ciki sosai wanda sai da na zubar da hawaye...wai dama haka ake ji? Daman idan ka rasa wani a lokaci ɗaya ya bayyana a gareka farin ciki da daɗin rai ne ke hana zuciyar ka sukuni.? Alhamdulillah! Babu abin da za mu cewa ubangiji sai godiya."
"Ina son ki Bibi! Kamar yanda na saba faɗa...ke ɗin ta daban ce a cikin dubban mata. Har yanzu ta dalilinki ne ta kuma sanadin ki ne duk waɗannan alkairan suke ta faruwa...Ina alfahari dake. Not me alone...gabaɗaya dangi kowa yana alfahari da ke. Kin cike mini kowane gurbi, kin zamto mafaka ta, mafaka ta har abada."
Murmushin jindaɗin yanda yake ta koɗa ni na yi sannan na ce.
" Mu je kaci abinci..."
Gaba na shiga har muka isa muka zauna na shiga serving na shi.
"Bibi..."
"Uhmm"
Na amsa ba tare da na kallesa ba.
"Waye ya yi wannan girke-girke!"
Sai yanxu na ɗago na kalleshi ina murmushi nace.
"Masu aiki mana."
"Kina shan routine drugs ɗin ki kuwa?"
"Sosai. Ko ɗazu sai da na sha."
A tare muka ci abinci wanda a yanzu cin abincina ya ragu sosai ba kamar can baya ba. Bana ci da yawa, sai dai kuma ba'a jimawa sosai nake sake neman wani.
Bayan mun kambala ya shige ya yi wanka sannan ya fita masallaci. Nima ina kambala isha na fice na shige can inda su Aunty Labiba aka zauna ana ta abu ɗaya wato fira. Nan aka yanke cewa idan gari ya waye. Za'a gyara ɗakin Hairiyyah da gidanta ke nan cikin estate ɗin su, wato sabon gidan da akayi. Sannan itama Suwara, ana gama ɗaura aure gobe, talata za'a juya da ita zuwa gida Nigeria.
A Rooftop ɗin gidana muka haye ni da Aunty Labiba, sis Noura, Aunty Nadeeyah, Hairiyyah da kuma Suwara. Wani shafin fira muka buɗe sabo, fira ce mai matuƙar muhimmanci da ta ƙara mana ilmi akan zamantakewa na yau da kullum. Duk firar nan da muke sai wani tausayina suke suna faɗin wai naje na kwanta waye-waye. Ni kuma dariya kawai nake musu domin wallahy bana jin komai, kawai nauyin cikin ne da kuma sauyin da jikina ya samu nake jin wani iri, amma sam bana jin alamar wata rashin lafiya ko wani abu makamancin haka.
Muna muna fira muna shan daddaɗan shayin ya kasance musu al'ada da ɗan taɓa snacks, abin da dai ranka yake so. Sai kusan ƙarfe ɗaya da wani abu na dare sannan muka sauko kowa ya nufi mahutarsa kafin gobe a ɗora kuma.
Ina shiga na tarar ba kowa, daman na sa a raina cewa, tun da naga bai kirani ba nasan cewa shima ɗin yana can tare da su Jaddi.
Zaunawa na yi kamar da gaske da sunan na jira sa. Sai gashi ban ƙara sanin ina kaina yake ba sai da na farka da asuba na jini a cikin jikin sa. Na yi mamakin duk yawan fitsarin da nake tashi yi akai-akai yau sai gashi tunda na kwana ɗin ban farka ba, wata ƙila kuma tsabar gajiya ce shiyasa hakan.
Muna gama breakfast aka fara shirye-shiryen ɗaurin auren Emraan da Suwara yayinda muka ɗunguma gidan Hairiyyah wurin gyara mata ɗaki.
Hmm! Wai akace masu abu da abunsu. Wato an zuba mata kaya na ji da gani tamkar ba za'a mutu ba. Daman kuma yankewa suka yi da cewa, a ɓangaren su Jaddan su za su zuba mata kayan buƙata, su kuma gefen su Aunty Labiba can za su zuba na Suwara. Wannan tsarin da suka yarda da shi babu algus, domin wata duniya ce a ka ƙirƙira a wannan yankin na Suhaib da Hairiyyah.
Muna nan gidan aka kira akace an ɗaura auren, sannan bayan an kambala kuma an mayar da auren Abiyh da Ammah.
Ji na yi idanuna sun cika da hawaye, wanda a lokacin babu abinda nake son gani sai fuskokin su Ammie da kuma Amarya da ango, wato Abiyh da Ammah. Ko ya za su a ransu yau ɗin nan, bayan tsawon shekaru da rabuwa har tsufa ya kama su ga shi a yau za su ƙara kasancewa da juna. Datse tunanin na yi daga ƙarshe ina fatan koma miye, yasa su kasance da juna a wannan karon har mutuwa.
Da yamma misalin ƙarfe shida aka shiryo Hairiyyah aka kawota ɗakin ta tare da tarin addu'o'i da fatan zaman lafiya da farin ciki mai ɗorewa.
Bakin Suhaib ya kasa rufuwa a wannan daren, duk inda ya gifta bakin nan nasa har kunne.
Nan muka gama tsokanarsa bayan ta fito daga ɓangarensu Jadda mukai masa fatan alheri ya wuce. Wai don Suhaib ya raina ni, har da cewa na dafo masa ruwan zafi da breakfast da safe.
Washe gari ma, da wuri aka fito da Suwara, tare da su Aunty Labiba su Mummy Na'imatu da su Baba Ustaz domin komawa gida.
Wani irin Kuka Suwara ta fara wanda kowa da ke wurin sai da ta saka shi kuka. Da ƙyar aka samu da rarrashi da komai aka yi nasarar saka ta a mota.
Bayan an kammala komai cikin farin ciki da fatan alheri. Bayan kwana biyu kuma, su Ammie suka shirya tare da su Annie, Abiyh da Ammah suka wuce Qatar.
Hmm! Sai abun yake yiwa kowa kamar a mafarki, musamman Ammah, wacce Hawayenta suka kasa tsayawa. Cike da kewa muka rabu da juna tamkar kar mu rabu. Musamman Noura da ta bani muhimmanci sosai nima kuma nake jin ta har cikin zuciyata tare da sauran en uwa.
Bayan tafiyarsu Ammie da kwana ɗaya muma muka fito domin tafiya gida.
Har gaban Jadda na je na tsuguna da ƙyar domin zama a ƙasa yanzu yana bani wahala.
Da wasu irin hawaye ta kalleni a raunane ta ce.
"Ki yi haƙuri Beenafah. Na aikata kuskure. Sumaiha twin sister ɗina ce, ina jin ciwon da take ji a raina a duk lokacin da wani na ta ya shiga matsala. Da ita da iyalanta, wallahy ina yi musu ƙaunar da ni kaina ban yiwa kaina ita. Sai ga shi ashe sara na yi akan gaɓa dara taci gida. Ki yi haƙuri ya yafe mini."
Tafin hannuna na saka nima na share nawa hawayen, ina jinjina kaina na ce.
" Jadda kin san me? A duk lokacin da wani abu zai zo mana tsakaninmu da musulmi ɗan uwanmu, to abinda yafi cancanta shi ne mu fara duba matsalar da ido na gaskiya ido na basira. Idan muka ce son zuciya shi ne abinda zai fara zuwa farko...to tabbas zamu cutar da waɗanda ba su da wani laifi a garemu. Ni kin gano cewa jininki ce, da ace baki gano hakan ba, to tabbas da ba za ki taɓa ɗaga mini ƙafa ba."
Kaina na ɗora akan cinyar ƙafarta a hankali na ce.
" Kada ki ƙara ji a ranki cewa wai na riƙe ki a rai. Komai ya wuce a gare ni, kuma ko mijina ban faɗa masa ba. Na ɗauke shi a matsayin ƙaddara. Allah ya sadamu da alheri."
"Amin. Na gode Beenafah. Allah ubangiji ya sauke ki lafiya ya bada rayayye mai albarka. Allah ya ƙara miki albarka ya ƙara muku zaman lafiya da haƙuri a cikin rayuwar aurenku."
Tare muka fito da sauran mutanen gidan da suka rakomu har bakin mota. Hairi wacce hannun ta ke cikin na Suhaib ne ta kalleni tana ta murmushi ta ce.
" Mummy! Allah ya kai lafiya ya saukar mini dake lafiya. Please ki yi mini alƙawarin haifo mai kama dani..."
Dariya muka fashe da ita sannan na Suhaib ya buɗe mini mota yana faɗin.
"Allah ya tsare Hajiyata. Allah ya saukar mana dake lafiya."
A haka muka yi sallama da su sannan daga baya sai gashi ya shigo motar shi ma muka kama hanya.
********
Gefen Jafaru kuwa, bai samu nutsuwa ba sai da ya tattara kuɗin account ɗinsa ya cire su gabaɗaya sannan ya haɗa da babbar wayarsa ya siyar suka tafi wurin malamin.
Bayan ya gama masa bayani ya ɗauko wani ƙullin magani ya bashi sannan ya ce.
"Wannan....ka saka mata a lemu, kunu, fura ko duk wani abin sha dai. Sai ka bata tasha da hannunka da na ta...sai wannan kwallin kuma, a ranar da ka tabbatar za ta sha wannan magani, to a ranar za ka saka shi a idanun ka.....wannan kuma, ƙwan Kurciya ne,...eh..wannan shi ake kira so Tsuntsu ne. Shi kuma,ka gan shi guda uku ne. Ka soya ɗaya ka ci, ka dafa ɗaya ka kwarɗe ka ci sai kuma ka samu gindin bishiya ka binne ɗaya."
Ji ya yi wata irin matsananciyar zufa ta shiga tsatstsafo masa ta ko'ina tsabar yanda ya ji abubuwan wanda babu ɗaya mai sauƙi.
" Ka ji abin da na ce maka?"
Jiki a sanyaye ya ce.
" Malam abun ne na ji kamar babu ɗaya da zai yiyu...ko dai akwai wani aikin da za a ɗan canja wanda ba dole sai na haɗu da ita ba?"
"Babu wani aikin da za a canza da shi Jafar, idan wannan ɗin ya yi maka to ka karɓa ka tafi. Muddin dai ka aiwatar da komai yanda na ce maka, to Beenafah za ta tsaya a tare da kai har ƙarshen Rayuwarta."
Hannu Uka ya kai yana zungurarsa,yana yi masa alama da ido akan ya karɓa.
Hannu biyu yasa ya karɓa sannan ya ajiye masa kuɗin suka yi godiya suka tashi.
Tun a hanya yake mita tamkar zai fashe da kuka yana faɗin.
"Ni duk wannan abun ina zan ganta dan Allah? Ina zan ganta ballantana ma in iya aiwatar da aikin nan? Kai koda ace na samu ganinta, ban san yanda zan yi na ba ta abu da hannuna ba in ce ta sha..."
"Mts! Ka kwantar da hankalinka mana abokina. Farin ciki ya kamata ka yi da wannan mafitar da ka samu. Kasa a ranka cewa aiki wannan har an yi shi an gama..."
Ji ya yi ma ya ƙara ɓata masa rai, hannu ya saka a aljihu ya fito da ƙwan wanda yake mini-mini sosai ya ɗaga sama yana kallo yana faɗin.
" Miye wannan ɗin ma da zai ce wai in soya ɗaya in ci sannan in dafa ɗaya? Ni gaskiya ba zan iya ci ba. Saboda haka gabaɗaya zan binne su..."
Girgiza kai Uka ya yi sannan ya ce.
"A'a fa abokina! Kada ka yi yanda ba'a ce maka ba, wallhy idan aikinka ya lallace ni ba ruwana kada ku ma ka yi blaming ɗina. Mts! Wai sai kace ba namiji ba! Ina duk zarrar ka take?, ina iƙirarin son da ka ke yiwa Beenafar yake? Common ɗan abu wannan wai ka hau complain akai. Miye wahalar a nan? Kawai ka shige jikin en gidanku ka riƙa samun update a kanta domin ka ji yaushe za ta zo ƙasar. Da zaran ta zo ai magana ta ƙare, yanxu gidansu kamar gidan ku ne, in ta kama har mota ka hau kana iya hawa ka cim mata har Sokoton da sunan ba ta haƙuri kawai ka aiwatar da aikinka, idan ma Gusau ɗin ta zo Kaga shi ke nan ta kwana gidan sauƙi. Sai aikin wannan ƙwan. Shi ke nan fa da ka kambala ka same ta kenan har abada, iyaka ka koma gefe ka jira, da kanta za ta hauka ce tace babu kowa a ranta sai kai...sannan wannan malamin ka yarda da shi Jafaru, aikinsa yi da cikawa ne. Ina tabbatar maka sai ka dawo da kanka kana masa godiya."
Ajiyar zuciya ya sauke yana mai jin nutsuwa sosai a ransa sannan ya yi wani murmushi ya ce.
" Na gode sosai Ukasha. Ka fiye mini su Qatada sau dubu miliyan. Allah ya barmu tare. Duk ranar da burina ya cika na samu Beenafah. Na yi maka alƙawarin wani abu wanda har ka mutu ba za ka manta da ni ba."
Cikin jin daɗi Uka ya yi wata dariya sannan ya ce.
" Allah dai ya biya, na Beenafah ko dubu ta taru. Kabewar kan kabari baƙin cikin mai taushe. Ai wallahy wannan matsiyacin mutumin sai ya gane cewa ya ja da babban mutum irin ka."
Da haka ya yi ta wani kuranta shi yayin da shi kuma Jafarun ke jin duk duniya babu wani shege sai shi.
Daga dare zuwa wayewar gari,har ya gama aikata wannan aikin ƙwan wanda sai da ya gama ya dinga amai tamkar zai mutu tsabar yanda yake jin ƙyanƙyami. Abu wasa-wasa sai ga shi an sadashi da gadon asibiti. Gashi ba shi da takamammiyar dubu biyar ta kai nai. Dole sai da aka gida Baba ya turo masa da kuɗi dubu ashirin aka masa ƙarin ruwa da maganguna sannan aka sallame shi.
******
Gefen su Mummy Zaliha kuwa, sai da suka yi wata biyu cikin na uku sannan suka dawo gida, bayan an sha jinya ya samu ya farfaɗo.
Koda suka iso sun iske gidan na su an ƙara gyara shi sosai an saka musu furnitures ya dawo gida abunda ake kira gida.
A ranar da suka dawo a ranar su ma su Hussaina suka dawo daga gidan Alhaji Baba ita da Humaida.
Humaida duk tayi wani baƙi ta lalace tsabar ɗorawa kai damuwa da tunani.
Suna nan Daddy suka fashe da kuka, domin dai lafiyar nan kam sai dai ace Alhamdulillah! Murmushi ya yi musu yana mai girgiza kansa ya ce.
"Ku daina Kuka Hussaina, doguwar jinya itama wannan kaffara ce. Ni a haka ma na godewa Allah. Kun ga dai irin rayuwar da muka rayu a ciki, daula kamar ba za ta ƙare ba ko? To ina so ku ɗauki wannan a matsayin darasin rayuwa, wallahy komai na duniya yana da farko kuma yana da Ƙarshe. Musamman zalunci, gaskiya ce kaɗai ba ta ƙarewa,...har abada ba za ku taɓa jin an ce wai gaskiyar mutum ta ƙare ba sai dai ace ƙaryarsa ta ƙare."
Hussaina na kuka sosai ta ce.
" Daddy darasi na nawa kuma? Yanda muka wuce muka bar Ammie a ranar da muka koma Abuja, Beenafah tana ta kuka tamkar za ta mutu amma baka saurare ta ba, haka tarihi ya maimaita kansa da kansa. A ranar da za su wuce, Humaida na ta kuka kamar za ta ɗauke numfashi suka wuce suka barta....Daddy aure na sau biyu aka nema, kamar za'a yi, amma sai aka fasa. Wannan kaɗai ni ya ishe ni darasi. Na ji daɗi na kuma godewa Allah da har yasa kuka gane gaskiya. Allah yasa mu cika da kyau da imani, Allah ya yafe muku ya baku aljanna maɗaukakiya. Ku ɗin iyayenmu ne, komai zai faru har abada ba za mu taɓa canja ku ba, kamar yanda kuma ba za ku canja mu ba..."
Share hawaye Humaida ta yi tana kallon Mummy ta ce.
" Ni ina so na koma gidan Aunty Aysha."
Ido Mummy ta zuba mata na ɗan lokaci tana kallonta, sannan daga ƙarshe ta lumshe idanun ta hawaye masu ɗumi suka zubo mata ta girgixa kai ta ce.
" Humaida rayuwar da ƙunci ko? Kin ji komai ya sauya miki ko? Hmmm! To ke da ba ki ma wani ji ma a cikin daɗin ba kika kasa daurewa. Ina ga Beenafah wacce ta taso cikin gata gaba da baya amma muka nakasar mata da rayuwarta? Yah Allah ka yafe mana haƙƙin waɗan nan mutanen da muka ɗaukarwa kanmu."
Husaina ta ce.
" In Sha Allahu komai ya wuce Mummy. Yanzu haka ma sun haɗu da dangin mahaifiyarsu, Ammie ta gano iyayenta na gaskiya, har Sheikh ɗinma. Sannan da Mijin Beenafah da ita Ammie dangi ɗaya suke jinin su ɗaya. Abun duk da bamu gani ba. An ce ya ƙayatar sosai."
Jikin Daddy ne ya yi sanyi jin ta ambaci sunan Sheikh. Da magiya da komai aka kira daga Canada aka ce ga mahaifin Mulaifa yazo. Amma bai ji kunyar Allah ba ya yi masa bayani da cewa wai duk sun mutu a car accident. Gudu kada ya ci gaba da neman su watarana ya same su, sai ga shi yanxu ba Sheikh ba, hatta iyayenta na gaskiya sun bayyana. Ina ma ace Dr. Bello yana nan ya ga iyayen Mulaifa. A gaban kowa yasha tabbatar mata da cewa yana ji a jikin sa watarana za ta haɗu da iyayenta da dangin ta cikin farin ciki.
Yana mai jin wani iri a ransa ya ce.
"Na taya su murna. Allah yaci gaba da tabbatar musu da zumuncin su har Aljanna."
"Amin amin."
"Bari na tashi na ɗora girki. Daddy miye kake so kaci?"
"Abu mai sauƙi mai Husaina, mai ruwa haka..."
Jinjina kanta ta yi sannan ta waiga wurin Mummy ta ce.
"Ke fa Mummy?"
"Duk abin da ku ka dafa zan ci. Ina aka samu kayan abin ci haka?"
"Uhmm! Uncle Isma'ila ya bani dubu ɗari jiya, daman kuma tun shekaranjiya Aunty Aysha da Hassana sun turo kuɗi suka na siyo kayan abinci kafin ku dawo. To sai na haɗe, duk da cewa Humaida sai da ta matsa na siyo mata waya a ciki, amma Alhaji Baba ya bata dubu hamsin, sai muka je ta zaɓa ta ɗari da talatin....amma dai kayan abincin komai an siyo Alhamdulillah!"
" To ba komai ai, Allah ya ƙara bamu wasu masu albarka. Gwanda da kika siya mata, ai ba komai. Ki yi haƙuri kin ji ko Humaida? Ki yi ta haƙuri da rayuwa. Ran da akwai kuɗin siya miki abun da kike so a siya miki, randa kuma ba kuɗin sai ki yi haƙuri. Watarana haka za ki wayi gari ma babu mu a duniyar. Saboda haka ki yi haƙuri. Idan mijin Aysha ya yarda sai ki zauna a gidan sa, idan ya ce bai amince ba sai ki yi haƙuri kin ji ko Humaida."
Kuka take sosai tana jinjina kanta alamar zancensa ya shige ta sosai.
Haka suka ci gaba da gurguruwa wanda Salman, Ahlan da kuma Uncle Isma'ila ne wadanda ke tallafe da su. Hafiz Shagon Isma'ila ya ke tafiya har yanxu wanda duk wata yake yi masa albashi.
Islamiyyah suka koma ita da Humaida wanda daga makaranta sai gida. Zumuncin su suna nan suna yi da su Beenafah a waya.
*******
Gefensu Aunty Labiba kuwa. Suna isa aka shige da Suwara sashen Hajiya ita da su Aunt Fattoom da Mummy Razia da suka zo a tare da su.
Ainahin gidan Ya Mohaa da ke cikin gidan inda aka saka Beenafah a lokacin auren su nan, aka sake yi masa fenti aka gyara musu su biyu ita da Ziza.
Duk wasu makaman rashin arzikin ta tuni ta watsar da su bayan ta ɗauki shawarwari da kuma faɗan da iyayenta suka yo mata da ta je gida bayan ta yi cika arba'in ɗin Mima.
Hakan yasa suka shimfiɗa rayuwar zaman lafiya wanda Emraan ɗin ya raba musu kwana biyu-biyu kamar yanda uwargida Ziza ta zaɓa.
******
Su Ammie ma, sai ana saura kwana biyu a ɗauki azumi suka sauka a Sokoto ita da Bahrain da kuma Dr. Basheer wanda ya cim musu a can kwana biyar da suka wuce.