Garkuwa complete Novel - Chapter 26
Garkuwa complete Novel Chapter 26: Garkuwa complete Novel Chapter 26. Wasu irin tagwayen numfarfashi Umaymah ta sauƙe tare da cewa. "Alhamdulillah!…
4,285 words
Wasu irin tagwayen numfarfashi Umaymah ta sauƙe tare da cewa. "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!". Da sauri ta juyo ta ruggume Jakadiyarsu a hankali tace. "Alhamdulillah Ummin Jabeer itace. Wlh itace". Cikin wani irin tarin jin daɗi Jakadiyarsu ta ɗan kalli Shatu, tare da yin murmushi mai cike da ma'anoni.
Jakukkunan dake hannunta ta ajiye, kana ta iso kusa da ita ido ta zubawa fuskarta kana tace. "Ɗiyata menene sunanki?". Cikin yin ƙasa da ido Shatu tace. "Aysha". Kusan a tare sukace masha ALLAH. Nan Umaymah kam ta juya da sauri ta fita.
Ita kuwa Jakadiyarsu Jabeer shirya mata kayan data shigo dasu takeyi a drower'n. Tare da bata umurnin taje tayi al'wala.
Umaymah kuwa tana fita kai tsaye Side ɗin Jabeer ta nufa.
Shiru ba kowa, da kamar duk sun tafi masallaci ne.
Aunty Juwairiyya da Hibba kuwa suna sashin Juwairiyyan. Ummi kuwa na can wurin Shatu.
Kai tsaye ɗakin da nanne masaukin ta, ta nufa. Bathroom ta faɗa ruwa ta ɗan watsa tare da yin al'wala kana tafito tazo ta kabbarta sallah.
Ita kuwa Shatu zaune take bisa sallayan. Tunda ta idar da sallan bata tashiba. Sai kanta data jingina jikin gadon da take gefenshi. A hankali ta rumtse idanunta tare da motsa laɓɓanta tana karatun al'ƙur'ani cikin sanyin murya, Ummey da Junainah ne suka faɗo mata a rai shine ya sata zubda hawaye wasu na korar wasu. Kewarsu da begensu, ya tuno mata su Ya Gaini da marigayi ya Lado. Ummi kuwa itama bisa sallayan take tana lazumi.
A haka har lokacin sallan isha'i yayi.
Jin wata zazzaƙar murya mai matsifar daɗi na karatun. Hannun tasa ta share hawayenta dan jin karatun takeyi yana ratsa mata zuciya ya tsananta zubar hawayenta.
A hankali ta miƙe itama ta kabbarta sallan isha'i. Hakama Ummi.
Bayan an idarne. Ummi ta miƙe tsaye ta ninke abin sallan, kana a hankali take taku har kusa da ita. Cikin sanyi ta zauna bakin gadon tare dasa hannunta tsakiyar kanta a hankali tace. "AYSHA kuka kikeyi!?." Da sauri ta jujjuya kai alamar a a tana mai share hawayenta. Cikin kula Ummi tace. "Kuka mana kikeyi, gashi kinata zubda hawaye! Kiyi haƙuri kinji ko Aysha ki bar kuka, in kinji kewan mamanki ki kalleni a matsayinta, in kinji kewar yayarki ki kalli Juwairiyya a matsayinta, in kuma yayu maza kikaji kewarsu ki kalli Jalal da Jamil a matsayinsu. In wani abu na damunki ki gayawa Sheykh, shine mijinki kuma majiɓancin lamuranki in kinji kewar ƙanwa mace ki kalli Hibba a matsayinta,". Bata hafimtar kalaman wannan matar, bare tasan me take nufi saboda babu mutun ɗaya da ta sani cikin mutanen data kira mata. Abu ɗaya ta fahimta Sheykh shine wanda wai tace shine mijine ko majiɓancin lamurane, bata sanshiba bai kuma santaba ta ina zai jiɓanci lamuranta, Shin ta yaya zata zauna a wannan gidan da tun shigowarta take ganin ababe masu ban tsoro." Jin tayi shirune yasa. Ummi shafa bayanta tare da cewa. "Jikinki na rawa zazzaɓi kikeyi ne?." Cikin sanyin murya tace. "A a sanyi nakeji". Da sauri ta ɗan miƙe tare da cewa. "To bari in rage gudun A/C'n". Ragewa tayi kana tazo ta zauna kusa da ita.
Umaymah kuwa tana idar da sallan isha'i, ta miƙe ta dawo sashin Gimbiya Aminatu. Tayi matuƙar mamaki ganin batun auren Jabeer ya karaɗe masarautarsu gaba ɗaya, taki wani sashi kawo abincin amarya akeyi.
Ita da kanta da Gimbiya Aminatu sukayi ta shigar da Foodflaks ɗin abincin cikin ɗakin da take suna jerawa a gabanta.
Shi kuwa Sheykh Jabeer bayan an salla. Ya fito kamar koda yaushe su Jalal na biye dasu a baya. Haroon kuwa suna tafiya a jere, suna cikin tafiya duk suka tsaya fuska a haɗe Jabeer ya juyo ya kalli gefen hagunshi da yaji an dafa kafaɗarshi, Jadda ne ya ɗan kalleshi kana ya kauda fuskarshi ba tare da yace mushi komaiba. Murmushi Jadda yayi cikin sakin fuska yace. "Ƙarfe tara dai-dai jirginmu zai tashi. Zamu koma da kawunan naku duka". Cikin muryar dake nuna cewa yana cikin tsananin ɓacin rai yace. "Allah kiyaye hanya". Ya ƙarishe mgnar tare da juyawa yaci gaba da tafiyarshi.
Shi kuwa Jadda murmushi ya kumayi, fahimtar Sheykh yana tsananin fushi da baƙin cikin abinda sukayi mishi.
Lamiɗo ne ya kalli Aminin nashi tare dayi mishi alamun ya barshi. Su tafi.
Daga nan suka juya duk suka nufi, sashin Lamiɗo, inda aka gama shirya manya-manyan Foodflaks a tsakiyar falonshi bisa wani tattausan Turkey carpet mai masifar kyau da taushi.
Nan suka zauna sukayi Dinner sunayi suna hira, Tare da yaransu.
Bayan sun gamane, suka miƙe dan tafiya Airport sabinda lokacin tafiyarsu ya kusa. Kusan a tare suke fito zuwa babban falon dake tsakanin side ɗin Lamiɗo dana Gimbiya Aminatu.
Bayan sun zaunane, Sallama yaje ya sanarwa Gimbiya Aminatu cewa Sarki Jalaluddin yana neman Umaymah da Amaryar Sheykh.
Jin saƙon Sarki Jalaluddin daga bakin hadimanta da Sallama ya isarwa saƙon ne yasa ta miƙe ta nufi ɗakin da Umaymah take.
A cikin ɗakin kuwa, cikin kula Umaymah take gabatarwa Aysha da abin ci dana taɓa ka lashe dana motsa baki. Adda Rumana kuwa kamar tasa mata abinci har bakinta, Itako Aysha kanta a sunkuye, ta zubawa kulolin abincin ido tana ganin ikon Allah dake wanzuwa cikin kayayyakin cimar, da sai dai gidan wane da wanen. Fahimtar kunya ne ya hanata cin komai yasa suka fito falo suka barta, da Umaymah kawai wacce taketa janta a jiki ganin hakane yasa, ta ɗan yarda taci abincin kaɗan.
Suna zaune a nanne Gimbiya Aminatu ta shigo ta sanar musu saƙon sarki Jalaluddin nan, Umaymah ta sake saka mata wata al'kyabbar cikin jin daɗi tace. "Aysha ki saki jikinki dani, ki gaya min dukkan abinda kikeso, yanzu kinga wurin kakanunki zan kaiki. Sarki Jalaluddin mahaifina ne, wanda kuma shine mahaifin maman mijinki, ɗaurin auren sukazo shida yayunmu da ƙannenmu maza yanzu zasu koma jiharmu ne. Kinga wannan kuma Gimbiya Aminatu itace ta haifi mahaifin mijinki. Kana Sarki Nuruddeen ɗan Sarki Bubayero jikan sarki Joɗa, shine kakan mijinki. Mu ma mahaifiyarmu na Raye mijinki ne yasa mata suna Sitti, tana jiharmu ita bata samu zuwaba sai daga baya zata zo". Ajiyan zuciya tayi tare da kamo hannunta kana taci gaba da cewa. "Mijinki ɗan babban family ne gaba da bayanshi. A ƙalla zai ɗaukeki shekaru goma cikin masarautar Joɗa data musulmai baki gama sanin adadin dangi da yawan yan uwan mijinki ta gefen mahaifiyarshi da mahaifinshi ba. Yanzu muje su ganki ki gansu." Cikin sanyi tace. "To Aunty". Murmushi Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa. "Ba Aunty ku bace, Mijinki Malam Jabeer yafi yarda da ita fiye da kowa a dangin mahaifiyarshi, Umaymah yake kiranta". Kai ta gyaɗa tare da mgnar zuciya. "Ikon Allah". Ita kuwa Umaymah murmushi tayi kana tana hannunta suka fita. A falo suka samu Jakadiyarsu, da sauri Umaymah tace. "Yauwa kinga wannan itace Jakadiyarsu, itace ta rainesu tun suna yara, bayan mahaifiyarsu babu wanda yasan halin Jazlaan sama da ita a cikin wannan masarautar, ki kasance mai bin umarnin ta, domin itace idonki cikin wannan masarautar, Jazlaan a matsayin uwa mahaifiya yake kallonta ba baiwar gidansu ba". Cikin nitsuwa Aysha ta gyaɗa kai tare da cewa. "Nagode". Ita kuwa Ummi murmushi tayi tare da bin bayansu.
Suna isa bakin ƙofar tayi musu iso bayan ta shiga ta sanar musu da isowarsu.
A hankali suka shiga, cikin nitsuwa take bin takun Umaymah. Ita kuwa Umaymah har gaban Sarki Jalaluddin da Sarki Nuruddeen taje da ita, cikin shaƙuwarta dasu, ta ajiyeta a gabansu tare da cewa. "Jadda ga amaryar Sheykh Jabeer a sanya musu al'barka". Murmushi yayi tare da kallon Aysha. Wani nannauyan ajiyan zuciya ya sauƙe tare da cewa. "Allah ya sanya al'khairi ya basu zaman lafiya. Allah yasa tazo mana da hasken da zai kore duhun daya meye hasken idanunmu". Amin Amin suka amsa baki ɗayansu. Uncle Abdulkareem ne ya ɗan kalleta cikin sanyi yace. "Allah yayi miki al'barka dake da mijinki ya baku zaman lfy mai ɗorewa". Kanta ta ƙara sunkuyawa, Ita kuwa Umaymah matsota tayi tare da cewa. "Kinga ɗan ɗago kanki ki kallesu. Kinga ga Mahaifina. Ga Sarki Lamiɗo". Sai kuma ta nuna Abba dake zaune cikin murmushi tace. "Ga wannan shine mahaifin Jabeer mamanshi kuwa sai gobe a bisa ƙaidar masarautar keda shi Jakadiyarsu da Sallama zasuyi muki jagora ku zagaya cikin masarautarsu baki ɗayansu a nuna miki ahlinsu to da ɗakin mamanshi za'a fara kaiki". Kinga wannan shine babban Yayanmu sarki mai jiran gado. Ga kuma wa ƙaninmu Abdulmumin." Murmushi Lamiɗo yayi tare da cewa. "A a Khadijah a rana ɗaya kikeso ɗiyar taki tasan komaine? Ai abun da wuya, dole sai a hankali zata gane mu". Murmushi Jakadiyarsu tayi tare da cewa. "Hakane kam. Amman gwara an gabatar mata da manya". Sarki Jalaluddin ne ya gyara zamanshi tare da cewa. "To Khadijah mu yanzu zamu wuce, ke kuma sai yaushe?". Murmushi tayi tare da kallon gefen damanta inda Haroon ke zaune da wani kekkyawa mutun mai matsakaici shikara. Mi kama dashi wanda bisa dukkan alamu babanshi ne. Kauda kanshi yayi daga kallon da Umaymah keyi mishi, cikin ƙasaita alamun shima jinin sarauta ne, yace. "Ni kada ki wani kalleni, bance komaiba". Murmushi dattawan sukayi baki ɗayansu, Haroon ma murmushin yakeyi. Ita kuwa Umaymah kauda zance tayi da cewa. "Yauwa Aysha kinga wannan shine Haroon ɗan uwa kuma aboki amini abokin faɗan Jabeer. Akwai kuma ɗan yayanmu Ibrahim shine shaƙiƙin Jabeer shi yana Cairo, amman kwanan zai dawo ki ganshi." Jadda ne ya kuma tsareta da cewa. "Khadijah yaushe zaki koma?". Cikin sanyi tace. "Jadda in Abban Haroon ya amince zanyi wata ɗaya rak, sabida ganin yadda lamuran zasu tafi. tsakanin yaran, ita kanta Aysha tana buƙatar makusanci tare da ita, sabida baƙonci a irin gidajenmu abune mai wuya ga wanda ba irin gidajen ya taso ba". Murmushi Abban Haroon yayi tare da cewa. "Ba laifi na Amince, Amman bazaki ɗauki azumi a nan bada". Da sauri tace. "Na yarda". Haroon ne ya ɗan juya idonshi alum lissafi kana yace. "Ke nan sati uku zakiyi tunda azumin saura wata ɗaya". Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa, Jadda ne ya kalli Jakadiya tare da bata umarnin su tafi ita da Aysha. Gane abinda yake nufine yasa ta kamo hannun Aysha suka fita. Gimbiya Aminatu na biye dasu a baya.
Gyaran murya Jadda yayi bayan sun fita, cikin nitsuwa da girma ya kalli Umaymah tare da cewa. "Alhamdulillah Khadijah, aure dai an ɗaura, duk da tarin tsana da ƙin abin da ɗan naki keyi. Haƙiƙa baya son wannan abun da akayi mishi. Naga fushi da tashin hankali mai tarin yawa a ƙwayar idanunshi da fuskarshi. Ina da yaƙini bisa halin Jabeer in ya tsani abu tofa ya tsaneshi kenan har gaban abadan, wannan shine babban tashin hankali na, Sabida yanada lafiya da tsayuwa kan kaifi ɗaya. Ya gayawa kakarshi Sitti babu wani gari na duniya da yakejin ya tsana sama da wannan garin. Yace baya son garin da mutanen garin. Sabida anci mishi zarafi a garin a gaban kafurai an tozarta shiga ta addinin Musulunci". Shiru sukayi baki ɗayansu, tabbas sun san hakane mgnar Jadda. shi kuwa Jadda a hankali yaci gaba da cewa. "Yanzu kubar Yarinyar a ta kwana a nan. Kana a ɗan ɗaga kafa har sai an gyara mata inda zata zauna, kamar ko wacce amarya. Sannan kada kuyi mishi mgnar auren bare ita yarinyar, in anyi haka fushinsa bazai tsanantaba, zaici gaba da al'amuran rayuwarshi, tunda shi mutum ne mai ibada da kuma aiyuka". Murmushi Haroon yayi tare da cewa. "In dai baza'ayi mishi mgnarta ba, to wallahi mancewa zaiyi da ita da babinta ma gaba ɗaya". Lamiɗo ne ya gyara zama tare da cewa. "Ya isa". Murmushi Umaymah tayi sabida ta lura har yau su Lamiɗo basu gama sanin Jabeer da halaiyarsa ba.
Shi dai Jadda nan ya jadadda musu cewa, kada suyiwa Sheykh Jabeer mgnar sai an gama gyara komai na sashinta. Ko gaisuwar su bari sai bayan kwana uku a zagaya da ita cikin Masarautar.
Nan dai sukayi sallama suka, tafi baki ɗayansu.
Suna tafiya, Umaymah ta koma ɗakin da Aysha take, nan ta samu Ummi na zaune da ita. Nan ta zauna ta suka ɗan yi hira ganin alamun gajiya da bacci a tattare da itane yasa, sukayi mata saida safe suka fita suka tafi.
Ratsawa sukayi wurin Gimbiya Aminatu suka mata saida safe kana suka fita suka tafi.
Cikin tsananin jin daɗi suke tafiya, har suka iso bakin. Mashigar sashinsa, cikin nitsuwa sukaci gaba da tafiya. Shiru ba motsin komai suna gab da isa bakin ƙofar, suka tsaya cikin zaro ido, suka kalli Laminu da Gimbiya Saudatu, cikin haɗe fuska da zafi Umaymah tace. "Aoozubikalimatillahi taaa'ammati minshirin makalaƙa!." Cikin tsantsar tsanarta Gimbiya Saudatu tace. "A kanki hegu masu jajayen kunnuwa". Tana faɗin haka taja hannun Laminu suka fita. Su kuwa Umaymah da sauri sukayi ciki.
A falo suka tsaya. Ba kowa a falon haka yasa tayi sauri ta nufi arear'n Side ɗin Jabeer, a falo ta samu Haroon konce bisa kujera. Yana ganinta ya tashi zaune. Cikin gimtse dariyarshi murya a hankali yace. "Yau duk kayan ahlin masarautar Joɗa sai an yagesu baki ɗayansu." Ya ƙarishe mgnar yana nuna mata ƙofar ɗakinshi.
A hankali ta kutsa kai cikin ɗakin tare da yin sallama. Can ta hangoshi kan gadon yana konce rigingine, idonshi a lumshe, a hankali takeyin taku tana nufo inda yake. tare da mgnar zuci. "Wato harda sharrin Haroon zayiwa ɗan Umaymah". A hankali ta zauna bisa bedside drower'n. Idonta ta sauƙe bisa goshinsa, cikin mamaki ta juyo ta fuskanceshi da kyau ganin yadda Goshinsa ke....!
By *GARKUWAR FULANI* "Kamar tsoffin karnuka". Cikin fusata Gimbiya Saudatu ta miƙe tsaye tare da nufo inda yake. Shi kuwa kanshi ya jinjina tare da cewa. "Kinyiwa kanki Garkuwa da kika tashi daga kan kujerata". A hatsale tace. "Wai kai a zatonka tsoronka nake jine ko meye?". Da sauri ya jujjuya mata kai tare da tsuke fuskarsa alamun baison sautin amon muryanta da take ɗaga mishi, a daƙile yace. "A a, na isa inyi zaton tsorona kikeji. Ke da bakinji tsoron Allah'n daya halicce ki bama, ina zakiji tsoron wani bawa nashi, ai masu tattausan zuciya suke tsoro". Hannu Baba Nasiru ya ɗago da alamun zai kifeshi da mari. Ba zato yaji ya kama hannunshi, kana ya ɗan juyo fuskarshi gareshi, cikin sakekkiyar murya yace. "Wai ku meyasa bakwa gane, yare da harshenmu na bani adam ne? Meyasa kukafi son Yaren dabobbin marasa hankali, a zatonka ka kai matsayin da zaka ɗago hannunka ka mari fuskanta?". A hatsale ya fuzge hannunshi tare da cewa. "Da uwarka kakeyi, kasan wacece dabbar ai!. Ɗan hegiya mai jajayen kunnuw..!". Shiru yayi bai ƙarisa mgnarba ganin wani irin kallo da Jabeer ke mishi, ido cikin ido. Kana ya ɗaga hannunshi na dama, yana ɗan buga bayan tafin hannun damanshi cikin tafin hannunshi na hagu. Still idonshi na kan fuskar ƙanin Mahaifinshi, miƙar da tafin hannunshi yayi, tare da mishi alamun datsa a cikin tafin hannunshi, kana cikin danne fushinsa, dan baya son su gane abinda ke masifar ci mishi rai, sai dai duk danniyarsa ya rigada, sun gane babu abinda ya tsana a duniya sama da azagar mishi mahaifiyarshi bare a suffantata da ƙaddararta, da binta da kalaman bita da ƙulli. Baba Basiru ne, yayi wani irin dariyar mugunta kana ya ɗan matsa baya kaɗan cikin izza yace. "Datse mana wuya zakayi, dan a zagi waccar munafukar da Allah ya nuna mata ishara tun a duniya". Murmushi mai rauni yayi kana yace. "Mahaukaciyar tsohuwar ku ko! Eh na gane lallai kam, batunka haka yake". Cikin fiffiƙewa suka fara kumfar baki ina dalilin zaicewa uwarsu mahaukaciyar tsohuwa". Daga nesa za'a iya jiyosu. Shi kuwa ko Aunty Juwairiyya dake Dinning area bata jiyo abinda yake faɗa. Domin cikin nitsuwarsa yake zaro musu, duk amsar mgnar da sukayi mishi tunma kafin harshensu ya huta. Gimbiya Saudatu kuwa, a masifance tace. "Ai asirinku zai tonu nan bada dadewa ba, munafukar kakar takace, tayiwa mahaifiyarsu asiri ta haukatata dan baƙin kishi irin nata". Murmushi yayi ganin yadda ƙannnen mahaifinshi keta ihu uwa karnuka. Allah ya sani lamarinsu yana bashi mmki har yau ya rasa me yayi musu mai zafi a duniya da suke gaza danne tsanarshi a aransu. Me Mahaifiyarshi tayi musu da suke masifar tsanarta?. Kanshi ya juya ya kalli Umaymah daketa murmushi mai cike da jin daɗin yadda yake komai a nitse. Juyawa yayi zai nufi gefen hanyan falonshi. Sai kuma ya ɗan tsaya ganin Gimbiya Saudatu tasha gabanshi. Cikin danne shakkarsa tace. "A haka zaku ƙare. Komai na muna furci, anje anyi aure a muna furce a ɓoye, sannan an kawota yau kwana uku kenan an kasa fito da ita a nunawa mutane ita, dan masifar rashin gsky. Ko dai cikin shegene da ita yasa kuke ɓoyeta." Da sauri Umaymah ta ƙara so inda suke, cikin tsuke fuska tace. "A kanki shege zai samu, in sha Allah bazai samu a tsatson yar uwata ba, kin kuma yi gaggawa, da yake dama aikin shaiɗan ne dole zakiyi ta aikatashi. Ki koma ki wanke idonki zai kawo miki Amaryarshi matarshi kuma uwar ƴaƴan shi, har Side ɗin ki, cikin falonki, har gaban ki. Kinaji zai gabatar mata ke da munanan ɗabi'unki dan tasan irin zaman da zatayi dake". Laminu ne yace. "Ke kuma waya kasa dake, ki bari ƴan gida suyi mg...!". Wani irin tsalle yayi ya koma baya, jin marin da Jalal wanda yanzu ya shigo ya kifa mishi ta bayanshi. Da sauri Baba Nasiru da Baba Basiru suka juyo kan Jalal, alamun wai zasu dakeshi. Karkata kai yayi ya kallesu da gefen ido. Kana a hankali yasa hannunshin ya ɗaga rigarshi, wata ƴar madai-daiciyar bindiga AK 47 ya zaro a ƙugunshi . Wani irin wawan birki sukaja, tare da cewa. "Eh lallai babu shakka masarautar Joɗa ta raini tantirin ɗan ta'adda bindiga, wato abin har yakai ka matakin riƙe bindiga". Kanshi ya tankwashe tare dasa bakin bindigar yana sosai tattausan sajenshi irin na Hamma Jabeer ɗin shi. Kana da bakin bindigar ya nuna musu hanyar fita. Ai a jere suka juya suna fita. Gimbiya Saudatu na cewa. "Duk wanda yaci tuwo dani, tabbas miya zaisha. Amaryar munafurcin a fito da ita mu ganta in an taki gsky". Laminu ne ya amshi zancen da cewa. "Menene ma abin gani a Bororiyar daji". Da haka dai suka fita. Shi kuwa Sheykh Jabeer wani irin kallo na tuhuma, da tarin mamaki yakeyiwa Jalal. Bindiga a hannunshi, shi kuwa Jalal ganin yadda duk suka zubawa bindigar idone yasashi. Meda ita cikin rigarsa. Kana ya juya da sauri ya nufi hanyar fita. Jabeer bai ce mishi komaiba. Yana ganin ya fitane shi kuma ya juya, ya nufi falonshi. Bedroom ya wuce, a hankali ya zauna bakin gado, tare dasa hannunshi yana buɗa bakin al'kyabbar jikinshin sai kuma yasa hannu shi na dama ya dafe kanshi, kalmar amarya mata ya maimaita a fili. Wani irin rumtse idanunshi yayi da ƙarfi Allah ya sani shi yama mance, batun wannan jagulellen auren da akayi kamar na wasan yara. kanshi ya ɗago a hankali ya kalli Umaymah dake shigowa da sallama a bakinta. Gefenshi tazo ta zauna bisa bedside drower'n tana fuskantarshi. hannunshi yasa, ya fara cire hiramin kanshi. ita kuwa Umaymah cikin hikima tace. "Idan mutun yana yi maka fatan ci baya to kayi mishi nuni da nasarorin rayuwarka, ban cika son takura maka akan baka umarnin yin abubuwan da baka soba, to amman bani da zaɓi akan duk wata al'ada ta masarautar Joɗa, da cikin masarautarmu ne, tabbas inada damar hana wani abun da saka wani abun." Cikin rauni ya kalleta da idonshi da sukayi jazir a hankali yace. "Me Mahaifiyata tayi musu mai zafi da suka sata a gaba ita da ah'linta. Duk abinda sukeyi Mata bata kulasu, bare ta kai ga ramawa, tana haƙuri akan komai, haka yasa suke zaton tsoronsu takeji. Ita kullum yanayi musu uzuri. su kuma kullum fatansu su cutar da ita har dai suka samu nasarar cutar da rayuwarta sannan muma basu barmu ba. Ni na gaji da zama cikin masarautar Joɗa, zan bar musu garin gaba ɗaya". Sauƙe numfashin tayi tare da cewa. "Basu da nasara a rayuwarsu. Nasara ɗaya ce garesu kuma sun yi ta. Ta ƙare musu". Sai kuma ta ɗan kalleshi cikin sanyi tace. "Jazlaan!". A hankali ya amsa mata. Fuska ta ɗan raunata kana a hankali tace. "Yau kwanan matarka uku a gidan nan!". Da sauri ya kauda fuskarshi a kanta wani irin haɗe fuska yayi tare da taune lip ɗin shi na ƙasa ta ciki. Shi ya mance da wannan batun yana rayuwarshi hankali konce. Wannan kariyar matar Gimbiya Saudatu tazo ta tono zancen. Ita kuwa Umaymah a hankali taci gaba da cewa. "Baka gantaba! Baka nemeta ba! Baka san halin da take cikiba! Baka nunata wa ah'linku ta masarautar Joɗa, a matsayin ta, na matarka. Lamiɗo yayi mgna har ya turo Umminka taxo ta sanar maka, sai tace bata so ɓacin ranka. Abbanka yace shi bazai ce maka komaiba, sabida babu abinda baka saniba kan al'adar masarauta. Yace kada wanda yayi maka mgna akan matarka sabida. kai ba jahili bane, duk ka fimu sanin haƙƙin mace akan mijinta. Yace kunya tashi kake son yi a idon mutane!". Kanshi ya fara jujjuyawa a hankali yace. "Me kukeso inyi! Umaymah ya kuke son inyi? Bazan iya juya kaina in dawo yadda kukeso bafa, daga yadda Allah ya halicce ni". Cikin hikima da sanyi tace. "Ka shirya gobe, ka gabatar da matarka ga ƴan uwanka da iyayenka". Hannunshi biyu yasa ya dafe kanshi. Tare da rufe idonshi, sabida sarawar da yaji kanshi nayi. sai kuma ya ɗan kalli Umaymah jin tana shessheƙan kuka. Cikin sanyi yace. "To!". Murmushi tayi tare da shafa kanshi kana ta juya ta fita da sauri.
Kai tsaye sashin Gimbiya Aminatu ta wuce, ta sanar mata yadda sukayi da ɗan nata.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, a hankali ya miƙe al'kyabbar jikinshi ya zare, kana ya nufi bathroom da jallabiyar.
Yana shiga ya zare jallabiyar da snglet ɗin. Kana ya shiga wurin wonkan. Ruwan sanyi ya sakarwa kanshi. sabida sarawar da kanshi keyi, tun ihun dasu Baba Basiru sukayi mishi a kanshi. Ga kuma wani sabon zance na zagaye idanun mayu da kulullukan masu konciyar ɗaukan rai na masarautarsu. A ƙalla yayi mituna biyar ruwan sanyin na zubo mishi a tsakiyar kai, kafin ya fara sauƙe ajiyan zuciya alamun kan ya fara lafawa. Al'wala yayi kana ya fito. A nan drower'n glass dake bathroom ɗin nashi ya kimtsa kanshi cikin wasu datsastsen yadi mai masifar kyau Super Nour, Noble blue mai ɗan karen kyau, tattausan yadine mara nauyi, kana yanada ɗan shara-shara kaɗan, riga da wonɗo ne dai-dai jikinshi rigar half jomfa ne wanda aka watsa mishi aiki da da baƙin surfani. in ka tsura mishi ido sosai zaka iya hango shatin snglet and white boxes jikinshi. Wani Oud mai daɗin gaske ya fesa. Kana ya fito.
Baƙar fula ya kafa a kanshi wanda ya bawa tattausan gashin kanshi damar baiyana ta gefe da gefen kanshi da kuma ƙeyanshi.
Fararen kyawawan Ƙafafunshi, ya zura cikin. Wasu tattausan takalma baƙi. Sai kuma yasa hannu ya ɗauki carbinshi. Agogon dake liƙe saman mirror ya kalla, Lokacin sallan la'asar yayi, dan haka dole babu baccin tsakanin azahar da la'asar ɗin da ya dawo yi.
A masallaci ya samu su Haroon da Jamil.
Bayan anyi sallan ne kowa ya kama sabgogin gabanshi. Shi Jabeer komawa gida yayi. Ya saka garen kayan jikinshin kana. Ya fito, Ummi ya samu tsaye a tsakiyar falon, cikin kula tace. "Zaka fitane?". Kai ya gyaɗa mata alamar eh. ba tare da damuwar rashin bata amsarba tace. "Da yan rakiya ko kai ɗaya?". Yana gyara zaman hular kanshi yace. "Ni kaɗai. Zanje gidan Malama Abubakar ne!". Murmushi tayi tare da cewa. "Ka gaida minshi". "In sha Allah zaiji. Umaymah fa?". Gane abinda yake nufine yasata cewa. "Tana can sashin Gimbiya Aminatu, wurin ɗiyarta Amarya Aysha". Kanshi ya ɗan sunkuyar ba tare da yace mata komai ba, ya fita. Malam Abubakar shine, malamin da ya fara ɗiga mishi harafin Ba''un a allon shi, wato Be a fillance, Basinmi'arra a hausance ko?. A wurin shi yayi sauƙan forko, sai dai zuwa yanzu, shi Jabeer shike ƙara wa Malam Abubakar sani, akan Nahawu da Tajwid sabida shi da karatun zaure yayi.
Umaymah kuwa, ita da kanta ta sanarwa Lamiɗo cewa, gobe Sheykh zai gabatar da amaryarshi.
Haka yasa, ta fara shirya Aysha, shiri na musamman. Cikin Hadiman Juwairiyya ɗaya daga cikinsu. Mai suna saratu, itace Umaymah tasa ta yarfawa Aysha zanen lalle mai ɗan karen kyau. Kana Ummi da kanta ta wonke mata kai sabida ita keyiwa Juwairiyya ma. Sosai ta fito ras. Ita kuwa Shatu duk abinda sukeyi Mata. Tunanin Hibba al'hinin da tun randa tazo bata kuma ganinta ba. tana son ta tambayesu ta rasa ta ina zata fara, dole dai haka ta haƙura tai shiru.
Washe gari ranar talata. Da hantsi, ko ina na sashin Gimbiya Aminatu sai ƙashi yakeyi, sabida shiri da kimtsa amarya. Umaymah da kanta take kimtsata, wani irin dakekken wagambarine mai matukar kyau Royal blue, tasaka doguwar rigace. Tayi cib-cib da jikinta. wani irin ɗauri ɗan kwali Aunty Juwairiyya ta murza mata a kanta, irin mai stpes ɗin nan. Kana sai wata farar al'kyabbar masarauta fara ƙal mai kolliyar zaren aiki da ulunta Royal blue. da surkin Golding color mai sheƙi. Wasu fararen takalma masu ratsin Sky blue ne a kekyawan kafarta da yasha jan lalle, takalman basu cika tsini da tuduba, sai dai kuma ba dab da ƙasa bane. Tayi kyau iya kyau, sai ƙamshi da sheƙi take zubawa. Umaymah ce ta kama hannunta har zuwa falon Lamiɗo, wanda bai rigaya ya fita fadaba.
Gefen Gimbiya Aminatu ta ajiyeta, kana tace. "Bari inje inzo da Angon." Murmushi Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa. "To kuyi sauri dai". To tace kana ta fita.