Garkuwa complete Novel - Chapter 4
Garkuwa complete Novel Chapter 4: Garkuwa complete Novel Chapter 4. Suna shiga cikin ɗakin, da sauri Sheykh ya karisa gaban wani kekyawan mutun fari ƙal…
4,475 words
Suna shiga cikin ɗakin, da sauri Sheykh ya karisa gaban wani kekyawan mutun fari ƙal mai tarin tsabta wanda yake tsananin kama da Jamil duk da duk suna kama da juna amman Jalaluddin yafi kama da Jabeer, Jamil kuma yafi kama da Jafar. Zaune yake bisa sallaya, ya jingina kanshi da jikin gado, karatun al'ƙur'ani yakeyi cikin nitsuwa da da cikar tajwid, babu ɓata ko na ɗigo, yana karatun ne hawaye na kwaranya daga kwayar idanunshi, A hankali Sheykh Jabir yasa Hannu ya kamo hannun ɗan uwan nashi, A hankali Ya Jafar ya buɗe idanunshi ganin mutumin da shi kaɗai ke sashi yin abu yayi ko ya hanashi ya hanune ya sashi gyara zama still yana karatu. A tausashe Sheykh Jabir ya ɗan ranƙwafar da kanshi cikin salon tausayawa da muryar larabawa yace. "Sadakallahul Azeeeeeem". Jin hakane yasa wannan bawan Allah'n ya ɗago tafin hannunshi addu'o'in ya, fara karantawa kusan tsawon 3 minute sannan suka shafa a tare, Cikin wani zafi da ƙuna Sheykh Jabeer ya taune lips ɗin shi na ƙasa hannunshin yasa ya kamo na Ya Jafar ɗin, ba musu ya miƙar dashi, kan gadonshi ya zaunar dashi, A hankali ya juyo ya kalli Juwairiyya cikin sanyi yace. "Yaci abinci kuwa?". A hankali tace, "Tunda asuba daya dawo masallaci na bashi yaci abinci, kuma yanzuma na bashi ya ɗan ci". Kanshi ya rausayar kana yace. "Maganin shi fa kin bashi". Kai ta jinjina tare da cewa. "Eh na bashi maganin yasha". Jin hakane yasa Sheykh ya kamo hannun kekyawan Yayan nashi ya kontar dashi bisa gadon blanket yaja ya rufe mishi rabin jikinshi a hankali yace. "Ya Jafar kayi bacci, kaji jikinka zafi". Shiru bai kulashiba sai dai, ya lumshe idonshi.
A hankali ya juyo ya kalli Matar ɗan uwan nashi kuma ƴar kawunsu yayan Mamansu yace. "Juwairiyya Nagode". Hawayen dake zubo mata ta sharce tare da kamo yaranta ta ruggumesu, Jamil kuwa tuni yaketa zubda hawaye. Cikin rawan murya Juwairiyya tace. "Sheykh ka dena gode min nimafa Ya Jafar ɗan uwanane kuma mijinane, uban ƴaƴana, to in ban kula dashiba da waye zan kula a duniya?." Kanshi ya kauda kana ya juya ya nufi hanyar fita a ranshi yanajin ko sai yaushe manyan burukan rayuwar da fatanshi da addu'o'in shi zasu ƙarɓu yana ganin daraja da girman Juwairiyya domin tayi musu tsantsar halacci ta zauna da ɗan uwanshi a matsayin majanuni, a haka suke tafiya yana zancen zuciya. Jamil na biye dashi a baya.
A haka suka fito, suna tafe hadimansu na biye dasu a baya. A hankali ya ɗan juyo ya kalli Jamil da yasan yanada rauni dan Jamil yanada tausayin ɗan uwanshi duk da yanada shekiyanci amman yanada rauni a kansu abu kaɗan ke sashi kuka, Sashin dake tsakanin sashin su Jamil dana Ya Jafar suka wuce wanda nanne sashin Sheykh, sashin su Jamil ɗin suka shiga. Kai tsaye suka wuce har cikin bedroom. Tsaye suka sameshi yana taje suman kanshi mai yawa ga wondo iya ƙugu duk rabin boxes ɗinshi a woje ga wondon da rabin jiki duk woje waishi kirezi ko? da alamun fita zaiyi. "Meya hanaka zuwa masallacin jumma'a da wuri jiya? Waɗannan kolaben barasar na waye ne?". Sheykh ne ya jero mishi tambaya biyu a lokaci guda, A hankali Jalal ya juyo cikin shakku da shayi da kwarjin Hamma nasu ke sasu ji yace. "Mamace ta aikeni, jiya shiyasa na dawo a ƙurerren lokaci. Kolaben barasar kuma nasu Ashid ne, na kwace ne lokacin da suka saya, dan karsu sha". Kanshi ya gyaɗa dan ya gamsu ya kuma yarda dan yasan duk rintsi ƙanennshi basa mishi ƙarya. Cikin faɗa yace. "Ka kula da salla, ka tsaida ita kan lokacinta, kasan irin abokan da zakayi yawo dasu, ka tabbatar kaikeyi nasara akan juya halaiyarsu daga mummuna i zuwa kekkyawa. Shiyasa ban hanaka mu'amala da suba, domin manzon Allah yace. "Mutun ɗaya ya shiryu ta dalilinka, tarin ladan yafi a baka tarin jajayen raƙumi. Kada ka bari suyi nasarar juya rayuwarka daga kekkyawan i zuwa mummunan.
Kanshi ya gyaɗa cikin ladabi yace. "In sha Allah". Daga nan suka juya baki ɗayansu, Kai tsaye sashin Hajia Mama suka wuce. Inda hadimanta sukayi musu iso, Har cikin bedroom ɗinta suka shiga, A bakin gado suka sameta, zaune, yayinda baiyawarta Mansura keyi mata tausa. Murmushi tayi tare da kallonsu yadda suke a jere, koda maƙiyinsu ne sai sun burgeshi sun bashi sha'awa yayi fatan inama da ƴaƴansa ne. Kan dantsatsetsen shimfiɗar kilisa mai kyau da zanen tsuntsuwar ɗawisu, suka zauna, Cikin kula tace. "GARKUWAN FULANI, Jamil, Jalal, Allah yayi muku al'barka". Amin Amin, Sheykh da Jamil suka amsa, Jalal kuwa shiru yayi, Ita kuwa Hajia Mama murmushi tayi tare da cewa. "Babanmu mai Al'farma Sarkin Musulmai Jalaluddin meya farune naga fuskarka a haɗe?". Kanshi ya girgiza alamar. "Babu". Shi kuwa Sheykh ido kawai ya zuba kan wayarshi, Jamil ne ya ɗan gyara zama, tare da cewa. "Mama Abba fa". Kai ta ɗan jinjina tare da cewa. "Abinda yasani nemanku kenan, Abbanku ya tafi Abuja jiya da dare, yanzu kuma Gimbiya Samira zatabi bayanshi". Shiru Sheykh yayi a ranshi yake jinjina al'amarin mahaifinsu. Babusu a cikin dukkan sabgogin rayuwarsa komai nashi saidai suji a bakin Hajia Mama ko kuma a jaridu ko gidajen Radio ceɗi meɗinshi da amaryarshi Gimbiya Samira ƴar sarkin Nokan ce ita kuwa mijinta shine rayuwarta babu ruwanta da sabgar kowa. Sam Abba bai shaƙu dasuba da wuya ka ganshi zaune dasu yana hira dasu kamar uba da ƴaƴan shi. Saɓanin Maimartaba ko meye zaiyi Sheykh zai sani shine mutumin da yake shawara dashi akan duk abinda ya shafi addini. Kanshi ya ɗan kauda tare da cewa. "Allah ya dawo dashi lfy". Amin Amin sukace baki ɗayansu, Cikin kula yace. "Hajia Mama Affan fa sai yaushe zai dawo?."
"Next month?". Ta bashi amsa a gajarce.
A gogon hannunshi ya ɗan kalla kana a hankali ya miƙe tare da cewa. "Zan wuce Hospital shugaban ɗaliban makarantar ya kirani cewa sunada mara lafiyar da take buƙatar kulawar gaggawa".
Kai ta ɗan rausayar tare da cewa. "A dawo lfy". Amin Amin sukace kana suka fita suka tafi.
Daga nan kai tsaye FADA suka nufa. Inda sarkin fada yayi musu iso zuwa ga Maimartaba kakansu.
Suna shiga suka samu fada na cike da dattawa karsu Waziri, Matawalle, Galadima, Wambai, Ɗan isa, ɗanm' buram, sairkin Dogarai sarkin Gida, da kuma Duba gari, kana, sai kuma hadiman dake tsaye bayan sarki sunayi mishi fifitar sarauta da maficin fiffigen Ɗawisu.
Farin dattijo bafulatani, mai cikar haiba. Yana cikin manyan kaya na sarakai, wanda al'kyabbarsa kaɗai ta kai kuɗin mallakar wani gidan, A gabanshi suka zauna gaba ɗayansu uku, A hankali Sheykh yasa tafin hannunshi kan rumfar sawun kakan nashi da suke kan wani tim-tim mai girma da masifar taushi. taɓa sawun kakan nashi yayi tare da cewa. "Barka da hantsi Maimartaba, ya sawun naka?". Duk maganar nan da yayita a hankali yake yinta ko Jamil da Jalal dake gefenshi basujiba. Shi kuwa Maimartaba hannunshi ya ɗaura kan tsakiyar kan Sheykh wanda tun kafin ya zauna ya tura hulanshi ya koma baya, dafa tsakiyar kanshi yayi tare da cewa. "Alhamdulillah". Sai kuma ya kalli Jamil da Jalal da suke gaidashi, dan su sai yanzu suka haɗu dashi tunda gari ya waye, Tsaɓanin Sheykh da kullum tare suke dawowa masallaci sallan asuba daga nan kuma ɗakin hutunshi suke shiga kakarsu mace ta kawo musu abin taɓawa.
Bayan sun gaggaisa ne da mutanen fada, suka fita suka tafi.
Sashin kakarsu Gimbiya Aminatu suka nufa. Basu da hijabi da sashin kakar tasu shiyasa kai tsaye suka shiga a falo, suka sameta, Da alamun yanzu ta fitito Dan ga al'kyebba a jikinta ga kuma hadimanta a zagaye da ita.
Cikin tarin so da ƙaunar Jazlaan ɗin nata take kallon su, Murmushi tayi tare da cewa. "Miskili kafi mahaukaci ban haushi, kai dai kaji abinda malam zaice kada kace zaka binciki aikin malam".
Shiru Jamil da Jalal sukayi, shi kuwa Sheykh ido ya zuba mata. Ita kuwa rausayar da kai tayi tare da cewa. "Eh mana kaji abin da malam yace kada ka duba aikinshi, dazu na gama jin wani wa'azin ka da kayi kan falala da ni'imomin dake cikin aure, kana bayani duk maluntar mutun darajarsa bata cikaba in bashi da aure. Sai najima wa'azin kamar da kanka kakeyi. Meyasa ne Jabeer kayi niyar yin aure mana ka cikata nasabarka da kamalarka da martaba da darajar ka data masarautar Joɗa". Jalal ne ya miƙe tare da cewa. "Ke in anzo gaisheki sai ƙaƙale-ƙaƙalen zance tsiya kika iya ni na tafi dan inada aikin yi". Haratanshi tayi tare da cewa. "Tafi daga nan mai ƙugu kamar buzuzu hegiyar masifa". Hararanta yayi kana ya juya ya fita. Ita kuwa Gimbiya Aminatu. Jamil ta kalla wanda shima ya miƙe yabi bayan Jalal.
Shi kuwa Sheykh numfashin ya fesar tare da cewa. "Maganinki ya kare koda saura?." Da sauri tace. "Yauwa magani ya ƙare a kawo min wani". To yace kana ya mike ya fita.
Daga bakin harabar sashin kakar tasu, Fadawanshi ke biye dashi a baya har parking lot ɗinsu mai ɗan karen girma da kyau, duk zagaye suke da fulawowi masu kyau. Wasu tsala-tsalan motocine da a ƙalla sun kai su takwas sai sheƙi sukeyi.
Da sauri Ado drevernshi ya buɗe mushi ƙofar wata mota mai ɗan karen kyau wacce bada ita ya fita jiyaba, dan ita sai ranakun jumma'a-jumma'a yake hawanta, wannan ta yau mai kalar ruwan tokace sai sheƙi takeyi, yana shiga sauran fadawanshi suka yi yunƙurin shiga motocin dake jere a wurin a gefen wurin wanda dasu akeyi mishi rakiya.
Da sauri ya ɗaga musu hannu, cikin in in narsa da in yana saurin mgna yake fitowa yace. "Kkku ba bari ba'a bukatar rakiya". Da sauri suka ɗan rusuna tare da haɗa baki wurin cewa. "Aje lafiya a dawo lfy Allah ya kiyaye gabanka da bayanka Sheykh". Amin Amin yace a taƙaice kana ya shiga motar, sarkin ƙofa ya rufe mishi marfin sannan Ado yaja suka tafi.
Suna fita kai tsaye Babbar jami'ar dake cikin babban birnin Ɓadamaya suka nufa.
A can cikin makarantar kuwa, Kasan cewar duk ɗaliban jami'ar sun san babban Doctor zai shigo yasa gaba ɗaya harabar asibitin dake cikin jama'ar cika da taron tsala-tsalan ƴan mata ƴaƴan manya, duk mai matsalar lfy tana fatan ya dubata sabida ƙwarewarsa.
A hankali wasu ƴan mata biyu suke taku a farfajiyar shiga asibitin, bisa alamu duka ɗayar bata da lfy dan ɗayar na rike da hannunta, kuma a hankali suke tafiya.
Cikin tausayawa ɗayar ta kalli wacce ta riƙewa hannun a hankali tace. "Garkuwa ki daure kiyi sauri mu isa, wallahi zamu samu layi da yawa, kuma wannan Sheykh ɗin kasaitarsa nada tarin yawa, yanada doka da ƙa'idoji da tsari, yanada tsauri kan tsare kima da darajar addininshi, daga shigar jikinki in kinyi kuskure kaɗan na shigar kima wallahi bazai dubaki ba. Shiyasa ahlul kitabi dake cikin makarantar nan suke masifar shakkarsa, kinga gashi azahar ta kusa, kuma wallahi ko sarkin garin nanne yazo ya dubashi in dai lokacin salla yayi to tashi zaiyi ya fita ya barshi, gashi shiru-shiru da ido yake hukunta mutun".
A hankali wacce aka kira da GARKUWA tasa hannu ta gyara niƙab ɗin dake fuskantar, wacce ta dace da wata kekyawar arabian gawn dake jikinta wanda dama shigartace haka kullum sabida gudun kada wani ya ganta ya tsaida ita dan tasan duk namiji daya nuna yana sonta har lahira ake kasheshi wanda kuma duk Rugarsu akeda yaƙinin Ba'ana ne dan mutunne mai masifar baƙin kishi, yasha sanar mata a kanta zai kashe kowa ba damuwarsa bane da fari duk wanda ya nuna yana sonta da bulalin shaɗi yake korarshi, to yanzu duk wanda yace yana sonta sai dai a wayi gari ya rasu. Cikin sanyin muryar dake nuna azabar da takeji, murya na rawa tace. "Rafi'a, bazan iyaba marata ciwo kamar zata ɓalle, ki sakeni kije ki amsar mana foldana kafin in ƙaraso". Jin haka yasa Rafi'a cewa. "Zaki iya tahowa ke ɗaya?". Kanta ta gyaɗa mata a hankali. Hakan yasa cikin sanyi ta saketa kana ta wuce cikin Hospital ɗin da sauri.
Dai-dai lokacin kuma motar Dr Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero ta kutso kanta cikin farfajiyar. Bayan Ado ya dai-dai ta parking ne a cikin rumfar adana motor da aka rubuta Dr Jabeer a samanta. Ado ne ya fito da sauri ya buɗewa, Sheykh marfin motar, a hankali ya zuro ƙafafunshi ya fito. Cikin nitsuwa ya fara taku yana ratsowa cikin farfajiyar Hospital ɗin. Kasan cewar ta gabas ya fito Aysha kuwa ta yamma ta fito sai ya zama suna fuskantar juna. Yayinda sai sun haɗu wuri ɗaya zasuyi kwana sun fuskanci kudu inda nanne mashigar cikin asibitin.
A hankali suke takowa suna fuskantar juna. Sosai ya zuba mata ido sabida ya lura gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi alamun tsananin ciwo takeji gashi a hankali take taku. Ita kuwa Aysha, tafiya takeyi da kyer sabida azaban ciwo da mararta keyi. Kanta a sunkuye take tafiya, hakan yasa bata san da mutunba a gabanta.
Da sauri Sheykh ya tsaya sabida wani irin bugawa da ƙirjinsa ya fara. Ganin ta tunkaroshi gadan-gadan, kuma daga yanayin tafiyarta tamkar zata faɗi ƙasa. Ganin tayi wani irin sunkuyawa tasa hannunta duka biyu ta damƙe mararta da takeji tamkar caccakarsa akeyi da allura.
Gefe ya ɗan tsaya yana kallon ikon Allah, ita kuwa GARKUWA rumtse idanunta tayi da karfi, wata fitinenniyar zuface ke tsastsafowa tako ina, a hankali ta fara buɗe idanunta jin kartan da mararta keyi ɗin yana ɗan lafawa, a hankali ta zubawa kyawawan sawunshi idanu, cikin sauri ta ɗago kanta, ganinta tsaye gab kusa da namijin da bata saniba ne yasata ja da baya da sauri tare da miƙe tsawonta cikin firgici murya na ɗan rawa tace. "I'm very sorry". Bai kulata ba, sai kauda kanshi da yayi gefe. Ita kuwa Garkuwa cikin sanyi tace. "Dan Allah kayi haƙuri". Kai ya ɗan gyaɗa mata alamar Uhumm. Ita kuwa cikin sanyi tace. "Uhumm kaima Doctor Sheykh ɗin kazo ganin ne?". Da mamaki ya ɗan kalleta da gefen idonshi, sai kuma ya ɗan juyo kanshi kaɗan jin muryarta a sanyaye taci gaba da cewa. "Muyi sauri mu shiga ance yanada shegiyar ƙasaita da isa, wai ko sarkine yake dubawa in dai lokacin salla yayi tashi yakeyi ya fita". Cikin tarin mmki ya ɗan waro kyawan idanunshi tare da cewa. "Umh". Ita kuwa Garkuwa, hannu tasa ta matse mararta tare da cewa. "Muyi sauri mu shiga, kaga kuwa kayi sa'a kayi shigar mutunci dan ance shi baya son ganin musulmi da lalatacciyar shiga, ancema in mace tayi shigar banza baya dubata, kaji shishshigin mutunfa ko meye ruwansa da rayuwar wasu ai kowa yayi mai kyau dan kansa ko?". Rolling Ball eyes nashi yayi tare da gyaɗa mata kanshi. Kana ya tsuke fuska yaci gaba da tafiya. Ita kuwa Garkuwa cikin yin ƙasa da murya tace. "Uhum shidama akace shine shugaban tuzuran ƙasar nan, yana zaune baiyi aureba, ai zama ba aurema ba kyau tunda dai yanada damar yi ko?". Ɗan tsagaita takunshi yayi tare da cewa. "Hummh". A hankali ta bishi a baya cikin yanayin muryar mara lfy tace. "Dan Allah ka tsaya in rigaka shiga kar yace sai ya dubaka kafin ya dubani". Dai-dai lokacin kuma suka kutsa kansu cikin asibitin. Da sauri Garkuwa ta zazzaro idanunta baki ɗaya, tare da dafe ƙirjinta ganin gaba ɗaya Nurses ɗin dake ƙoƙarin fitowa sunyi maza suka koma baya, tare da rusunawa suka haɗa baki wurin cewa. "Barka da hantsi Sheykh". Kai kawai ya gyaɗa musu yaci gaba da tafiya, har ya shiga cikin wani ɗan corridor ya shiga wanda zai sadashi da tamfatsetsen Office dinshi ba tare daya ratsa ta cikin Reception ɗin su ba.
Ita kuwa Garkuwa gaba ɗaya tsorone ya rufeta, Gefen Rafi'a taje ta zauna wanda a take kuma mararta taci gaba da murɗawa da kartawa.
Da ƙarfi ta damƙi hannun Rafi'a. Cikin tausayawa Rafi'a tace. "Sannu, in sha Allah bazamu jimaba za'a kiraki, dan na nemi al'farman sauran sun yarda Khadija Nasir Shugaba ce aka shigar, ƴar gwamnan, ba lfy". Kai kawai ta iya gyaɗa mata, sai taune lips ɗinta da takeyi.
Shi kuwa Sheykh yana shiga Office dinshi, ya fara aikin daya kawoshi cikin ikon Allah kuwa Khadija ta samu sauƙi tunda ya dubata aka bata magunguna.
Mutun biyar ya duba, na shida kuwa, Aysha ce.
Koda aka kira sunanta jiki a mace ta miƙe ta nufi inda take ganin ana shiga. Nurse namiji na gabanta. A haka suka shiga, Ajiyan zuciya taja a hankali sabida tsaruwa da kyau da tsabta da ɗan karen ƙamshin da ya ziyarci hancinta, su sukasa ta son bin Office ɗin da kallo amman ina ciwo bazai bartaba.
A hankali ta iso gaban table ɗin baƙin Glass dake gabanshi. Ɗaya daga cikin kujerun biyu dake gaban table ɗin ta zauna. Ƙasa tayi da kanta cikin tarin ciwo da fargaba. Shiru tayi zaune bisa kujerar tayi ƙasa da kanta. Shikuwa Sheykh ko kanshi bai ɗago ya kalli inda takeba wanda wannan al'adarsace da wuya ya kalli mutun, mafiya yawan lokuta yafi kallon mutun ta cikin gilashi table ɗinshi, shiru Office ɗin sai sautin A/C da yake busawa, shima kanshi Nos ɗin sai ya gaza abin cewa, Ita kuwa Aysha pat-pat haka zuciyarta ke duka, gashi tana jiyo mararta na fara kartawa. Kusan tsawon 1 minute suna a haka, cikin dakiya da rauni ta ɗan nago kanta ta kalleshi, Ga mamakinta sai taga asalima hankalinshi baya kanta, yana dai murza yatsunshi da alamun tasbihi yakeyi. Shi kuwa Sheykh duk abinda takeyi yana ganinta ta kan glass ɗin, Cikin sanyin murya tace. "(Jam ɓanɗuna). Ina kwana". Shiru bai kulataba har sawon wasu daƙiƙun har ta fara zaton ko bai jita bane. Da sauri ta ɗago kanta jin yayi mata magana, cikin wata sahihiyar murya a takaice yace. "Suna?". Cikin fargaba ta tace. "AYSHA ALIYU GARKUWA....!
*Uhummm wani kayan sai amale, wani littafin yafi ƙarfin a baka lbri ka iya haƙura baka karantaba. GARKUWA YA WUCE ZATON MAI ZATO*
By *GARKUWAR FULANI* 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘
*GARKUWA*
PAGE 5
NA *AYSHA ALIYU GARKUWA*
📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘
*LITTAFIN GARKUWA na kuɗine ga masu buƙatar biyan kuɗin samun damar karantawa al'ummar Niger da kewaye ga number da zakuyiwa mgn +22799460151 biya ɗari uku, ko dubunki ɗaya kacal un saki a group. Gareku mutanena mutanen ƙasata in kina buƙatar GARKUWA ga hankaɗo min ɗari uku kacal! ko dubu ɗaya rak! Ta asusuna na Jaiz bank, 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyan ki ta number ta 09097853276. Mutanen Ayyah SP Group bana son KATI. Kuma al'ummar 300 in ba dole ba yaseen bana son KATI, to amman in babu yadda zakiyi, nasan akwai irina ƴan ƙauye, ba POS. Kuma kuna son karantawa, to hankaɗo katin mtn ɗinki na darinki uku kisha karatu. Allah ya nuna mana ƙarshensa lfy kamar yadda ya nuna mana forkonsa lfy. ALLAH ya bamu haƙurin zama da juna*
```Fans 1&2 sarakan surutu, Ina gaidaku ina ji daku har cikin ƙoƙon raina. SP Group, inai muku jinjina dubu-dubu.Fans 3 Allah ya rayamu ku cika maƙil. Group ɗin kurame kuma ina sane duku ina kuma jin daɗin nitsuwarku ba surutu. i love all my fan's irin lodi-lodin nan mafa```
```Gyaran amare uwar gidaye masu jego da masu tada komaɗa da sabunta dararen satin forko na amarci. Ku garzayo gani gareku da tsaraba kamarsu, tsumin Tsartai, sa buzu kuwa, garin babambaɗe, garin maɗi mai maɗemaɗin ni'imomi, bunbar ke ɗaya, gumbar Mali mai taken kolli mai sheƙi sai dai gsky ita tanada tsada, gumbar Uku csrmazaƙoi, gumbar haɗin inabi dabino kwakwa riɗi. Akwai haɗin ilan waddi, duk ba fula tani in yaji ilan waddi uhumm, akwai garin Belɗam yel, akwai tsumin ta baje, akwai kwanon ƙasaitacciyar mace, akwai kirɓeɓɓen tsumin domin mutanen nesa, akwai mgnin sanyi Infection, akwai butar sirri mai. abubuwan dai da yawa, gani ya kori ji, in kina buƙata kiyi min mgn ta wannan number 09097853276 kada ki kira dan ban fiye daga kiraba, gwara kimin mgn ta whatsapp in kinga bana kusa Turo min text message ta in-box```
A hankali ya ɗan ɗago ƙwayan idanunshi ya kalleta. Kanta a sunkuye hannunta biyu duka na kan mararta cikin wani, irin yanayi take wanda yake nuni da tana cikin wahala. A hankali ya maimaita sunan cikin zuciyarshi. "AYSHA ALIYU GARKUWA! To GARKUWAN ina? GARKUWAN meye?." A fili kuma kauda idonshi yayi daga kanta ya maida idanunshi kan tarin foldan dake gabanshi, wanda sunanta ke rubuce akan na samanshi yaja da yatsu biyu.
Shafin forko ya buɗe a folder kana, yasa hannu cikin wani ɗan abu mai kama da kofi wanda yake cike da biro masu kyau da tsadar gaske.
Tsiraran idanunshi ya lumshe sabida wani irin bugu da yakeji zuciyarshi nayi tun sanda ya hango yarinyar har zuwa yanzun nan da take gabanshi a zaune. Rubuce-rubuce yayi a ciki irin nasu na Doctors masu kama da tafiyar wahainiya. Kanshi ya kuma ɗagowa ya kalleta a fizge da gefen idonshi, sunkuyar da kanshi yayi tare da cewa. "Meke damunki?". Cikin shessheƙan wahala da son danne kukan da ke son kabce mata tace. "Marata, da bayana". Kai ya ɗan jujjuya tare da kallon shekarunta dake rubuce a cikin folder din, Yar shekara ashirin kuma da ƙorafin ciwon baya, cikin dakekken sauti yace. "Yaushe ya fara miki ciwo?". Hannu tasa ta cikin niƙabin da yayiwa fuskarta ƙawanya ta share hwayenta a hankali tace. "Shekara uku da suka wuce".
"Meyasa bakije asibitiba tun lokacin?". Ya tambayeta a daƙile.
"Ina zuwa asibiti duk sanda ya tashi".
"Kamar yaushe da yaushe yake tashi?". Ya jefo mata tambayar kamar yadda zuciyarshi ke harbawa da ƙarfin tsiya da kuma sauri-sauri, Kai ta sunkuyar tare da cewa. "Duk ƙarshen wata daga 21 zuwa 25". Shiru yayi kamar bai jitaba sai wasu rubuce-rubucen ya kumayi. Saida ya gama sannan ya tura mata folder ɗin gabanta. Jikinta na rawa tasa hannu ta ɗauki folder ɗin, ta yunƙura zata tashine, ya basu damar samun kusanci da juna, da sauri ya rumtse idanunshi sabida wani irin azabebben bugu da zuciyarshi keyi tamkar zaiyi tsalle ya faɗo woje, cikin zuciyarshi yake maimaita. "Innalillahi wa innailaihi rajiun." A hankali ya buɗe kyawar kyawan idanunshi jin bugun zuciyarshin ya fara yin ƙasa-ƙasa, ido ya zubawa mata ganin ta juya tana tafiya, wani abin al'ajabin a gareshi shine duk taku ɗaya da zatayi tana nesanta dashi sai yaji zuciyarshi na tsinkewa yana bada wani mugun bugun ras-ras, yayinda bugun tsinkewanta kuwa yaketa dai-dai-ta, Cikin mamaki ya sunkiyar da kanshi yana kallon yadda takeyin taku, tana riƙe da mararta, taje gab bakin fofar fitane, Taji wani irin murɗa da kartan da mararta ya farane yasa ta sakin wani sauti mai cike da wuya. "Wayyoooooooo Allah na, Wayyo Ummeyna cikina". Da sauri nurse ɗin nan yayi kanta tare da cewa. "Isah Allah rena joɗu". Ya ƙarishe mgnar da nuna mata kujerun farin ƙarfe dake gab da bakin ƙofar. Bata da zaɓin daya wuce ta zauna ɗin, domin gaba ɗaya ƙafafuwan ta rawa sukeyi alamun bazasu iya ɗaukar nauyinta ba ga duhun daya rufe mata ido. Sunkuyowa Nos ɗin yayi ya amshi folder kana yace. "Zauna bari inje Pharmacy in amso miki magungunan da alluran sai ayi miki". Kai kawai ta iya gyaɗa mishi tare da bashi.
Har ya fita sai kuma ya dawo yace. "Ok sir". Jin Sheykh Jabeer yace mishi ya turo ta gaba Da sauri ya fita.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, tasbihinshi yaketayi da yankan yatsunshi yake ƙidayar, sabida, suma yatsun su kasance cikin bautar Allah shiyasa yake ƙidayar amman ba don wai yasan adadin salati da hailala da istigifarin da yakeyiba, wannan ubangijine kawai masanin adadinsu.
Bayan fitar Nos ɗin da kamar 1 minute wata, Kekyawar budurwa ta shigo, cikin yauƙi da ƙasaita, sai wani irin masifeffen ƙamshin da take zubawa.
Ƙarasowa tayi gaban table ɗin nashi ta zauna, cikin yauƙi da korkosa tace. "Barka da rana Al' Sheykh". Ko inda take bai ɗaga ido ya kallaba, ya lura ya gane akwai wani abu tattere da yarinyar, dan mafi akasarin ranaku sai tazo, wai bata da lfy, kuma takan zo da ciwuka mabanbanta ne. Sanin ba musulma bace yasashi ƙara tsuke fuskarsa tamkar zatayi aman wuta, a zafafe yace. "Name". Cikin yauƙi da son isar da aikin da aka bata tasa hannu ta jawo foldan ta dake sama tura mishi gabanshi tayi, Cikin harshen hausa da tasan bai fiye son English language ba a rayuwarshi a hankali tace. "Breast ɗina kemin ciwo, har bana iya sa bra." Sai kuma tayi ƙasa da mayafinta dake jikinta, hannu tasa kan zip ɗin gaban rigarta tana ƙoƙarin zugeshi ƙasa tare da cewa. "Kalli Nipples ɗin sun.... Cikin tsananin firgita da tsoro, ta miƙe da azaban ƙarfi, jin yadda yasa hannunshi ya bugi table ɗin da azaban ƙarfi wani irin gigitaccen tsawa mai firgitarwa ya daka mata tare da cewa. "Tashi, daga gabana". Karkar jikinta ke tsuma sabida kwarjinshi da tsoronshi sun daki zuciyarta da take cike da fajirci dama dan bata kallon fuskarshi ne ta iya faɗin waɗannan kalaman ma. Dai-dai lokacin kuma, Nos ɗin nan ya shigo, ganin yadda AYSHA ta gigice taketa karkarwa, alamun tana son ta miƙe kuma ta kasa tashi.
Shi kuwa Sheykh foldan ɗin Rabeca ya jawo wani rubutu yayi saman foldan ɗin kana ya tura matashi gabanta cikin zafi da tsauri ya nunata mata hanyar fita tare da cewa. "Fice min daga Office daga yau in kina buƙatar ganin Dr kije gun Dr Ute, shi zakiyiwa duk sakarcinku na al'jihun baya. Ba niba, sannan daga nan ki wuce Zaria kije asibitin Shika domin ina zaton breast cancer kike dashi". Da sauri tasa hannu ta ɗauki foldan ɗin, gaba ɗaya jikinta na rawa, juyawa tayi ta fice tare da yin magana can ƙasa yadda bazai jitaba tace. "Allah ya sauwaƙa Ni bani da breast cancer, mugun bakin kawai."
Shi kuwa Sheykh Jabeer komawa yayi ya jingina da jikin kujerar lumshe idonshi yayi a ranshi yake haɗa kalaman da yaci karo dasu a safiyar yau. Kakarshi tace mishi, aji mgnar Malam kada a duba aikinshi, ta jaddada mishi, wai yayi aure, kana wannan mayyar yarinyar da in tana kusa dashi zuciyarshi ke barazar fashewa, kuma tace mishi wai shine shugaban tuzuran ƙasar nan baki ɗaya. Tabbas wannan shaidace na abinda ake faɗa a cikin gari a kansa kenan, yaji ya sani Sitti ma da take son suje saudia wai so take ya zaɓi matar aure a can, ga wannan kafurar da ya san turota akeyi ta tallata mishi kanta, don a samu cinikin jarida ya hauhawa ta hanyar buga kanun labarai cewa, Sheykh mazinacine ko kuma mata yakebi shine ya hanasa aure. Jingina kanshi yayi da kujerar tare da mgn a zuciyarsa. "Ya ilahi ya mujibadda'awati". Ta yayane ta inane wa zai gayawa cewa, shifa yanada banbanci da sauran maza, ba kamar kowa yake ba, taya zai gaya musu ko zai samu a daina binshi da kalmar yayi aure, me zaiyi da mace ta yaya zai fahimtar dasu su barshi ya huta.
Wannan shine nazarin da yakeyi cikin zuciyarshi,