Kenza eBookz

Garkuwa complete Novel - Chapter 70

Garkuwa complete Novel - Chapter 70

Garkuwa complete Novel Chapter 70: Garkuwa complete Novel Chapter 70. Da sauri ta zame har ƙasa ta durƙusa. Sabida wani irin azabebben tokara da guiwa da…

4,363 words

Da sauri ta zame har ƙasa ta durƙusa. Sabida wani irin azabebben tokara da guiwa da Jalal yayi mishi bisa tsakiyar bayanshi. A take sai ga jini ta hancinsa da bakinsa.

Murya na rawa cike da rauni Shatu ta ɗago kanta. Ta kalli Jalal dasu Khalid kana ta kalli jinin bakinshi daya ɗan tsallo ya taɓa farin gyalen jikinta. Wani irin kukane mai cike da tsananin tausayi rauni ta fashe dashi tare da cewa. "Ayyah Jalal dan Allah ku barshi kada ku kasheshi ku barshi dan Allah".

A hankali Jalal ya ɗan tsaya yana maida wani irin azabebben numfashin haƙi.

Sheykh kuwa wani irin kallo mai cike da azabebben kishi ya watsawa Shatu. Tare da sa tafin hannunshi ya tallabe haɓarshi. Kana ya jingina kanshi da jikin bishiyar yana mai kallonsu.

Mamey kuwa itama zamewa tayi tanamai sakin kuka. Ummi, Inna Amarya, Aunty Juwairiyya, Sara, dama duk sauran matan dake wurin wasu irin hawaye ne masu zafi suka tsastsafo musu.

Junainah kuwa zuwa tayi ta durƙushe gaban Ba'ana gefen Shatu cikin wani irin azabebben kuka mai cike da rauni tace. "Wayyo Yah Ba'ana Dan Allah Adda Shatu ki hanasu dukanshi."

Da ƙarfi Junainah ta faɗa jikin Shatu lokacin da Jalal yayi wani irin juyi ya kifawa Ba'ana wani irin masifeffen mari da tafin ƙafarsa. Tare da cewa. "Wato kai gaka shege har zaka sa hannu ka daki jamin soja". Wani irin azabebben karkarwa jikin Ba'ana ya farayi tamkar mazari.

Wani irin kuka mai azabar ciwo da cin rai Bukar da Bugulu suka saki sabida ganin yadda hukuma ke azabtar da Ba'ana tamkar zasu ɗauke ransa.

Cikin rauni murya na rawa ido na zubda hawaye Mamey tace. "Jalaluddin ku bar dukanshi". A hankali Jalal ya koma baya ya zauna bisa dakalin ƙofar ɗakinsu Giɗi. Sabida yasan muddin Mamey ta kirashi da sunanshi kai tsaye to abu ya ta'azzara gareta. Domin Babana take kiranshi, sai gashi yau full name ɗinshi ta kira bama Jalal kawai ba.

Sai kuma ta kalli su Khalid kana ta juyo ta kalli Sheykh murya na rawa tace. "Muhammad ka hanasu dukanshi". Cikin wani irin yanayi Sheykh ya ɗagawa su Khalid hannu. Haka yasa suma suka koma gefen Jalal suka zauna suna haki da maida numfashi.

Shi kuwa Sheykh ido ya zubawa Shatu dake kuka tamkar ranta zai fita.

Gaba ɗaya wurin babu wanda rauni bai darsu bisa zuciyarsa ba.

Yah Jafar da Bappa kuwa tuni hawaye suke zubdawa.

Bukar da Bugulu kuwa da rarrafe suka iso gareshi.

Shi kuwa Ba'ana wani irin dogon numfashi mai cike da azaba rauni nadama ya fesar a wahalce kana a hankali ya fara yunƙurin tashi zaune. Amman Ina ya kasa ganin hakane yasa Bukar yin sauri yasa hannunshin ya tallaboshi ya ɗagoshi. Ya jingina bayan Ba'ana nan da kirjinsa. Ya zama suna fuskantar Shatu dake kuka tamkar ranta zai bar gangar jikinta gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi. Cikin wani irin rauni murya na rawa yace. "Mata!". Da sauri ta ɗago jajayen idanunta ta ɗaurasu kanshi. Wanda haka yasa ta saki wani sabon kuka, Junainah ma kukan ta saki da ƙarfi. Shi kuwa Ba'ana hawaye na kwarya yana ƙore jinin hancinsa da bakinsa murya can ƙasan maƙoshi yace. "Mata". Murya na rawa kuka na kumbe mata tace. "Na'am Yah Ba'ana". Wani irin murmushi mai rauni yayi kana a hankali yace. "Mata Ranar da nake tsoro tazo, ranar da na gaya miki zata iya ɓaci zata zo, gata yau tazo". Sai kuma ya ɗago ɗaya hannun nashi mai lafiyar ya sharce hawayensa, cikin sanyi ya jujjuya kanshi dake masifar mishi ciwo. Ido ya zuba mata ganin yadda take kuka har numfashin ta na fizga. A hankali yace. "Shatu kin san son da nake miki gsky ne?". Cikin kuka tace. "Na sani Yah Ba'ana na sani son da kake min gsky ne". Wani dogon ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe tare da cewa. "Alhamdulillah". Sai kuma ga hawaye shar-shar bisa fuskarshi.

Cikin rauni yace. "Ke kuma kin taɓa sona a ranki da gsky?". Kanta ta fara ɗan bugawa da ƙafar Sheykh dake gefenta. Tare da cewa. "Eh eh eh Yah Ba'ana na soka so na gsky na soka so irin wanda naso mu gudu tare mu tsira tare nasoka irin son da nake yiwa Yah Al'ameen sabida bana son irin wannan ranar tazo mana". Kanshi ya jujjuya kana cikin rauni yace. "Shatu haka ƙaddarar rayuwata take."

Sai kuma ya kalli Junainah a hankali yace. "Junnu me yasa kike kuka, bakya son a kashenine". Cikin kuka tace. "Bana son a kasheka Yah Ba'ana. Ina sonka kamar yadda nake son sun Yah Giɗi". A hankali ya sunkuyar da kanshi tare da sakin wani irin raunataccen kuka wanda saida Affan ya zubda hawaye.

Cikin sanyi yace. "Mata ina ƴarmu?". Cikin wani irin rawan jiki hawaye na kwarya. A hankali tasa hannunta ta amshi Afreen dake hannun Ummi. Kana ta juyo da rarrafe tamkar ƙaramar yarinya ta iso gabanshi cikin rawan murya tace. "Gata nan Yah Ba'ana".

Wani irin murmushi mai yelwa yayi wanda saida fararen haƙoranshi suka fito ras. Da idonshi ya nuna mata cinyarshi. Cikin kuka ta sunkuyo ta kwantar mishi da Afreen bisa cinyarshi.

Kana ta kife kanta cikin cinyoyinta ta saki kuka.

Shima kukan ya saki mai rauni. Kana yasa tafin hannunshi ya shafi kan tattausan suman gashin Afreen hawayenshi na kwarya suna ɗiga kan goshinta. A hankali yace. "Masha Allah, Allah ya raya mana ita bisa imani al'farma Annabi da al'ƙur'ani Allah yasa mahaddaciyar al'ƙur'ani ce, ya azur tata da miji na gari". Karo na forko da Sheykh ya motsa lips ɗin shi a hankali yace. "Amin ya Allah". Sabida daɗin Addu'ar da akayiwa ƴarshi.

Itama Shatu cikin kuka tace. "Amin thumma Amin". Sai kuma ta ɗago kanta a hankali jin yana cewa. "Naji lbrin Ummey ta tuno baya ta gane ahlinta ance min ma wai ɗan ta ne ya aureki ko?". Ina ta kasa mgn sai kuka, Ummeyn ce ta sharce hawayenta a hankali tace. "Eh Ba'ana na tuno baya, na gano ahlina Allah ya saka da al'khairi ya biyaka da mafi kyawun sakamako". Cikin rauni yace. "Amin Amin Ummey". Sai kuma ya kalli Bappa dake ta kuka a hankali yace. "Bappa kana kukan baka cika min al'ƙawarin da kayi bane?". Da sauri Bappa ya gyaɗa kai alamar eh. Kai ya jujjuya kana a hankali yace. "Ba laifinka bane, ƙudirin ubangijine ba gashi yanzu Ɗiyar Shatu ce a cinyata, wani bazai haifi ɗan wani ba ai. Ni na yafe muku yanzu na yarda na gane komai nufin Allah ne. Sai dai kuma ina neman yafiyarku al'ummar Rugar Bani baki ɗaya busa duk wata cutarwa da nayi muku." Sai ya kuma kalli ɗaya daga cikin yaransa da suka shigo tare a hankali yace. "Koda bana da halin muku bayani, ga Droo zai muku dukkan bayanin abinda ke tafe, gaba ɗaya na mishi bayanin komai kafin mu taho". Sai kuma yayi shiru jin duk anyi shiru ana jinshi sai shessheƙan kukan Shatu dake tashi. Kalato yawun bakinshi yayi ya haɗiye sabida wata irin azabebben ƙishin da yakeji tamkar zai kashesa.

A hankali ya kalli Ummey cikin rauni yace. "Ummey ƙishi nakeji ki sanmin ruwa". Yayi mgnar yana kallon Shatu data zuba mishi ido da sauri. Ya sani ta tuno bayanin daya taɓa yi matane na cewa in an bashi ruwa yasha zai ɓace zai tsiri.

Haƙƙun kuwa itama abinda ta tuno ɗin kenan sai dai bata saniba ya kakkarya duk waɗan nan abubuwan. Cikin rani yace. "Shatu Insha". Yace lokacin daya amshi kofin ruwan da Ummey ta miƙo mishi. Shiru batayi mgna ba sai kukanta daya ƙaru.

Sheykh kuwa zuwa yanzu Allah ne kaɗai yasan abin da yakeji a zuciyarsa sabida azabar zafin kishi.

A hankali murya na rawa ido na zubda hawaye yace. "Mata ina sha, ko kada insha zaki gaya musu, ki gaya musu mana". Da sauri Jalal yace. "Adda Shatu menene wani tsafin zaiyi ne?".

Da sauri ta kalli Jalal kana ta juyo ta kalli Ba'ana ta kuma juyowa ta kalli Sheykh. Cikin sanyi murya na rawa tace. "Ka." Dai-dai lokacin kuma Baroon yasa hannunshi ya bugi ruwan tare da cewa. "Idan yasha zai ɓace ne fa". Yayi mgnar sabida baisan Ba'ana ya ƙauracewa tsafi da asirce-asircen ba. A hankali ya juyo ya kalli Shatu tare da cewa. "Ƙarasa mgnarki domin itace kamar zaɓin rayuwata da mutuwa ta."

A hankali tasa hannunta ta ɗauki Afreen dake kallon fuskarshi tana wasa. Cikin rauni tace. "Kada ka sha Yah Ba'ana ka bari hukuma tayi maka hukuncin daya dace da kai".

Yana zubda hawaye yace. "Uhummm to shike nan Mata. Amman nasa baki san me nake aikatawa ba shiyasa kike tunanin hukuncin hukuma zai rageni da rai". Da sauri ta nufi cikin ɗaki tana kuka.

Kana su Jalal kuma suka kamashi sukasa a motarsu sukayi gaba dashi.

Su kuwa Bukar da Bugulu da kuka suka tafi. Yayinda duk mutane ke zubda hawaye.

Bayan anyi sallan la'asar ne. Sheykh yace su fito su tafi cikin disashewar murya Shatu tace. "Jamil aini zan kwana biyu". Kai Jamil ya ɗan juya yace. "A a Yah Sheykh yace ki fito mu tafi, wai ya fasa baza ki kwana ba". Jin haka yasa Inna Amarya dasu Giɗi da Gaini da Seyo da yanzu suka dawo sukace. Tabi umarnin mijinta. Dole haka ta fito suka tafi, harda Junainah.

Gaba ɗaya Rugar Bani tayi shiru tayi sanyi tamkar waɗanda akayiwa mutuwa.

A can masaraur Joɗa kuwa. Cikin wani irin ƙunan rai Sheykh ya kalli A....!

Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300 a yawan posting ne babbancinsu yake. Idan kinaso turo kuɗin ta Account 0005388578 Jaiz Bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai kiyi screenshort na Debit Alert ki turo ta WhatsApp 09097853276. Sai in saki a group, ku ƴan 300 in baki da damar biya ta Account to ki sayi katin Mtn na ɗari uku kacal ki copy numbers ɗin ki turo min ta whatsApp 09097853276. Banbancin special Group da Normal group a yawan posting ne kada kizo kice in miki ƙarin bayani ɗan Allah.

By *GARKUWAR FULANI* [4/4, 10:00 PM] +234 806 559 0880: Agogon hannunsa, ƙarfe 11:30 pm na dare har yanzu Shatu bata shigo inda yakeba. Idanunsa ya rumtse da ɗan ƙarfi, tare da gyara kwanciyarsa, ya mai jin wani irin zazzafan kishi na taso mai.

Allah Ya sani yana jin ciwo da zafi acikin zuciyarshi, har yanzu idan ya tuno yanayin tashin hankali da kuma tausayi da rauni’n da ya gani a fuskar Shatu, lokacin dasu Jalal ke dukan wannan taƙadirin tsohon saurayin nata.

Mchewww yaja wani dogon tsaki a fili yace. "Sabida shine zata barni ni ɗaya a ɗaki kamar wani marar galihu?"

Muskutawa yayi tare da fesar da zazzafar iska ta bakinsa, sosai yakejin kuna acikin zuciyarsa, wanda kuma duk akan Kishin Shatou’n da yakeji ne. A haka dai bacci b’arawo yayi awon gaba dashi bayan yayi ta juye-juye.

Ita kuwa Shatu tunda suka dawo ta gaza tsaida hawayenta. Allah Ya sani bata taɓa jin son Yah Ba'ana aranta ba, bata kuma jinsa a matsayin saurayin da take buri da fatan aure, sai dai tasan tabbas tana mishi so irin na ɗan uwan taka. Tana jinshi tamkar su Yah Al'ameen dasu Yah Giɗi. Tana mishi so irin na ƴan uwa musulmai da son ya gyara rayuwarsa ko ya samu rabauta ranar gobe kiyama.

Kuka sosai takeyi, rungume da Afreen damunta da yarinyar tayi ne kuma yasa ta fito da ita.

A falo ta samu Ummi zaune ita da Jalal. Cikin disashewar murya tace. "Ayyah Ummi ga Afreen kaina ciwo ina so inyi bacci ta hanani".

Da sauri Ummi ta miƙo hannu ta amsheta tare da cewa. "Tasha mamanta ai ko?". Kai ta gyaɗa mata alaman “Eh.”

Jalal ne ya ɗan kalleta sosai fuskarta, ta kumbura tayi jazir idanunta kuwa sunyi tib tib.

A hankali ya maida kanshi ga Ummi yana mai ci gaba da cewa.

“Ai daga can Rugar tasu cibiyar bincike na jiha muka kaishi. Alhamdulillah kuma shida bakinshi ya amsa dukkan laifukansa tare da yin bayanin komai, ya tabbata cikekken mai laifi da ake nema ido rufe, yanzu kai tsaye ba ɓata lokaci za'a kaishi kotu ta yanke mishi hukunci ranar Monday da izinin ubangiji.”

Cikin sanyi Ummi tace. "Allah sarki, Allah yasa ya samu da sauƙi".

Miƙewa Jalal yayi tare da cewa. "Wani da sauƙi kuma Ummi ai yadda yayi ta kashe mutane, da sace dabbobin su shima kasheshi za'ayi a rage mugun iri a duniya".

Jin hakanne kuma yasa cikin sauri Shatu ta koma ɗakinta. Bisa kan gadonta ta kwanta tare da kifa kanta kan pillow, wani irin sassanyan kuka ne ya kwace mata.

Lokaci daya Komai ya fara dawo mata sabo, tun randa ta fara ganin Yah Ba'ana da kuma yau da tayi mishi kallon da take tsoron kada ya zama na ƙarshe ne. Saboda ita dai bata taɓa sanin cewa yana sata da kashe mutane ba.

Haka ta dinga sak’e sak’e acikin zuciyarta, a ranar dai haka suka kwana kowa da abinda ke damunsa.

Washe gari kuwa, ranar Lahadi, Sheykh yana gida wuni zur amman Allah bai sa yaga idon Shatu ta fito ba. Wannan abun ya ƙara ingiza mishi zafin kishinsa, ji yakeyi tamkar yayi ta ihu dan takaici.

Bayan sallan azahar ne. Ya dawo a falon ya samu Ummi da Aunty Juwairiyya da Mamey. Wacce kuma ta shigo ne dan ta duba Shatu, da yawan kuka ya sakar mata zazzafan zazzaɓi da ciwon kai. To ta fito daga d’akin Shatou d’in kenan, suna zaune afalo ya dawo.

A hankali ya ɗan sunkuyo ya shafa kan Afreen dake cinyar Mamey. Tare da cewa. "Mamey ɗazu naje kina bacci". Tana kallon yadda yake shafa kan Afreen yana cewa. "Allah ya miki al'barka".

Murmushi tayi tare da cewa. "To masu ƴaƴa kaima Allah yayi maka al'barka". Cikin jin daɗi yace. "Amin Amin Mamey na".

Murmushi tayi kana tace. "Muna son mgn da kai". Da sauri cike da biyayya yace. "Toh Mamey gani".

Miƙewa tayi ta nufi waje, shikuwa gyara al'kyabbar dake jikinshi yayi tare da bin bayanta.

Kai tsaye Part ɗin Abbanshi ta nufa yana biye da ita a baya. Da sallama suka shiga.

Murmushi Abba yayi tare da miƙa hannunshi ya amshi Afreen daketa raba ido. Ita kuwa Mamey gefenshi ta zauna.

Da sauri ya zauna gabansu a ƙasa bisa Austrian carpet, ya tanƙoshe sawunshi ya fuskancesu da kyau.

Gyaran murya Abba yayi tare da zuba mishi ido, wanda haka yasa shi yin ƙasa da kansa.

Shiru-shiru basuyi mgna ba, hakane yasa ya sake ɗago kanshi da sauri yayi ƙasa da idonshi sabida ganin daga Abban har Mameyn ido suka zuba mishi. A hankali ya fara motsa lips ɗin shi yana cewa. "Astaghfirullah!!". Ya fara tubawar ubangijin mu. Kafin ya tubarwa iyayen nasa dan hakan da sukayi ya rauna tashi sabida bai san laifinsa ba.

Su kuwa sun mishi hakane dan su sa mishi rauni da kuma halarto da biyayyarsa.

Karo na uku ya kuma ɗagowa ya kallesu. Kawai sai ya tankwashe kansa bisa kafad’arsa murya cike da rauni yace.

“Dan Allah Abba Mamey kuyi haƙuri ku gafarceni idan wani laifi nayi muku, ku sanarmin dan in kiyaye gaba kada in maimaitashi". Sai kuma ga idanunshi sunyi rau-rau sun fara wani sheƙi alamun hawaye na tsastsafowa daga cikinsu.

Cikin tsare murya da fuska da kauda wargi Abba yace.

“Muhammad!”

Da sauri murya na rawa yace. "Na'am Abbana". Sai kuma ya kalli Mamey da itama ta kirashi. Amsawa yayi tare da zuba musu ido.

Kai titsiyewar iyaye akwai sa rawan jiki da fargaba a zuciyar ɗan adam. Cikin tsananin kausasa murya Abba yace.

“Ina bukatar in baka umarni kayi wani abu, ban saniba ko zaka iya min biyayya ko bazaka iyaba".

Cikin sauri ya kalli Mamey da tace. "Ni umarni nake so in baka".

Da rarrafe ya ƙara matsosu cikin rawan murya yace. "Abba matuƙar dai abin da zaka sani bai saɓawa umarnin Ubangiji da tsarin Addinin Musulunci ba, in sha Allah zaka sameni mai biyayya a gareka da izinin Ubangiji."

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe cikin yanayin gamsuwa. Shi kuwa a hankali ya kamo hannun Mamey, cikin sanyi ya had’a su ya tallafe haɓarshi sai ga hawaye shar-shar suna kwaranya murya na rawa yace.

“Tsawon shekaru goma sha uku ina kuka dare da rana kuka na cikin zuciya, ina so in ganki da idona ma Allah bai bani Dama ba. Nakanji wani irin daɗi na musamman in Umaymah ta bani umarnin inyi abu kai tsaye, sai inji kamar ban rasa uwar da zata tirsasani yin abinda ya dace ba. Mameyna bani umarni da izinin ubangiji zanbi zan miki biyayya".

A hankali tasa hannunta tsakiyar kanshi tare da cewa. "Allah yayi maka al'barka". Da sauri yace "Amin". kana ya kallesu yace. "Menene umarninku?." Kusan a tare suka haɗa baki wurin cewa. "Umarninmu shine ka amshi mulkin Masarautar Joɗa, da Lamiɗo yake son yin murabus, ka yarda ka mulki masarautar Joɗa domin kawo gyara da tsari irin na addinin musulunci, Ni Umarnine kai tsaye nake baka". Mamey ta kare zancen. Abba kuwa cewa yayi. "Ni kuwa al'farma nake nema".

Abun ya zo mishi amatuk’ar bazata amman kuma saidai umarnin iyaye ya wuce wasa.

Wani irin kukane mai rauni ya kwace mishi, take hawaye ya soma kwarara akan fuskarsa, cikin raunanniyar murya yace.

“Mamey zanyi na amince zan mulki masarautar Joɗa, Abba kaima kace umarnine kawai na amince zanyi muddin hakan zai saku farin ciki".

Cikin tsananin jin daɗi suka ɗaura hannunsu a kanshi tare da sa mishi al'barka. Sai kawai ya kife kansa bisa cinyar Mamey murya na rawa yace.

“Kuyi min addu'a da bakunanku masu al'barka, ku roƙa min Allah ya bani ikon zama adalin shugaba mai tausayin al'ummar sa, ku roƙa min Allah ya bani ƙarfin zuciyar yin mulkin, sannan ku roƙa min Allah yasa kada giyar mulki ta bugar dani, ta sani danasanin muku biyayya ranar gobe kiyama, ku roƙa min Allah yasa talakawa suyi farin ciki da alfahari dani a matsayin shugaban su".

Ya ilahi ya mujibadda'awati. Su kansu su Abba tausayin shi ya rufesu, domin yanzu suka gano abinda yasa yake tsoron mulki da gudunsa. Cikin sanyi sukayi ta jero mishi addu'o'i. Yana amsawa da. "Amin Amin. Ameeeeeeen ya rabbil izzati". Daga nan Abba yayi ta bashi baki da bashi ƙarfin guiwa.

Dole sai kiran sallan la'asar ne yasa suka fito suka nufi masallaci.

Bayan kuma sun idar da Sallah’n sun fitone. Abba ya sanarwa Lamiɗo da Galadima yadda sukayi. Sujjadar godiyar Allah Lamiɗo yayi sabida baiyi zaton abun zaizo da sauƙi haka ba.

Shi kuwa Sheykh Part ɗinsa ya koma. Junainah da Mimi yaran Aunty Juwairiyya ya wuce a falo, har yaje bakin ƙofar shiga falonshi ya juyo yace. "Junainah zo". Da sauri tace “To” ta biyo bayanshi. A falon ya tsaya a hankali yace. "Ina Adda Shatu ?". Cikin sanyi tace. "Tana ɗakinta". Da sauri yace. "Kuka takeyi ne?". Kai ta ɗan gyaɗa mishi alaman “Eh”

Uhummm kawai yace kana yace. "Jeki".

Ƙarfe tara dai-dai na dare ya fito daga Bathroom ɗinsa cikin shirin bacci.

Shiru yayi jiyo muryar Afreen nata kuka a falo. Da sauri ya jawo al'kyabba ya ɗaura akan men sleeping dress d’in dake jikinsa. Direct parlor’n ya fito.

"Ummi lfy kuwa meke damunta?". Yace yana zama kusa da Ummin. Cikin damuwa Ummi tace.

“Wlh tun ɗazu kuka takeyi, to uwar kuma Maman ba ruwa, saboda tun shekaran jiya bata wani ci abincin kirki ba".

Cikin ɓacin rai yasa hannunshi ya amshi Afreen, daketa wawure-wawuren hannunta tana kaiwa baki alamun yunwa.

A kafaɗarsa ya saɓa ta tare da miƙewa ya nufi Bedroom ɗin Shatu.

Ita kuwa Shatu tsananin ciwon kai da alamun zazzaɓin da take jine yasa. Take turawa Ummi Afreen ita, kuwa sai tsotsan take so. Sabida ba'a barta tasha yadda take buƙata ba. Cikin takaici ya tura ƙofar ɗakin tare da yin sallama, sounding a bit harsh yace. "Assalamu alaikum, ke ina kike?”

Shiru yayi saboda hangota da yayi akan sallaya, ta fuskanci al'ƙibila da alamun salla takeyi ko tayi ta idar.

Rai a haɗe ya zauna abakin gadon yana mai jijjiga Afreen daketa ƙananan kuka, tare da tsotsar yatsarta babba da ciccila ƙafa. Bisa kafaɗarshi ya sakata yana ɗan jijjigata da hura mata iska a kunnenta. A take ta fara sauƙe ajiyar zuciya don dama kukan harda rikicin yin bacci.

Da sauri ya juyo kanshi yana kallon Shatu jin kamar shessheƙan kuka take sauƙewa. Ai kuwa kukan takeyi ta ɗaga hannunta sama kaɗan tana addu'o'in.

A hankali ya juyo ya ƙara matsowa gareta, cikin tarin takaici ya dawo bakin gadon ya zauna, wani irin dogon numfashi mai nauyi ya sauƙe kana cikin takaici murya a daburce yace. "Kuka! Kuka!! Kuka!!! kikeyi har yau har yanzu, duk kukan da kikayi a can bai isheki ba? Duk kukan nuna mishi soyayyan da kikayi bai isheki ba, sai kin dawo min cikin gidana kina min kuka? kina tauye min haƙƙina dana ƴata akan wani can banzan ɓarawo!".

Da sauri ta juyo ta kalleshi, hawaye na zubo mata ta zuba mishi ido. Wani irin maƙoƙon kishine da baƙin ciki ya tokare masa wuya, a fizge da ɗan ƙarfi yace.

“In ma ni bakya sona! baki da lokaci na! Bakya buƙatar ganina! Bare ki sauƙe haƙƙina dake kanki, ai ita dai Afreen ƴar kice kuma tana da haƙƙin ta a kanki ko? In kuma kinajin duk kin tsanemu ne baza ki iya rayuwa damu da bamu haƙƙinmu ba, dan Allah ki gaya min ba sai kin zauna kina ta min kuka a cikin gida, kina cutar min da yarinya da yunwa ba, sannan kina tayar min da hankali ba, Ki faɗa min in bakya sona, In sama miki salama kije can ki auri shi wanda kike so ɗin!!!”

Ya ƙare maganar da ƙarfi. Cike da fushi da zafin kishi. Wanda har Ummi dake falon ta jiyoshi. Karo na forko kenan a rayuwar aure su da Shatu da taji yana mata faɗa haka. Jin hakanne kuma yasa da sauri ta kamo hannun Junainah suka tafi ɗakinsu.

Ita kuwa Shatu cikin rauni ta zuba mishi ido tana mamakin fusatarsa da kalaman da yakeyi.

Shi kuwa Sheykh cikin takaici yace. "Na sani ai dama ni na sani bawai sona kikeyi ba, dole akayi miki ko? dama shi kikeso! Wannan abun shi nake gudu da tsoron auren matar da ba sonka takeyi ba. Amman ba matsala kiyi ta sonshi. Nima ina da masu sona, kuma zan aurosu, su kuma kular min da ƴata".

Idanunta da ta zuba masa tad’an lumshe, cikin rawar murya tace. "Yah Sheyk...".

Da sauri cikin fushi da zafin kishin ganin son Ba'ana ne yasata wannan kukan. A faɗa ce ya daga mata hannu cikin tsawa yace. "Da Allah rufe min baki". Yana faɗin hakan ya juya ya fita daga d’akin, still rungume da Afreen akan shoulder dinshi.

Kai tsaye bedroom ɗinsa ya wuce. Cikin tafasan zuciya ya kwantar da ita can ƙarshen gadon nasa. Kana a hankali ya miƙe ya zauna sabida azaban tafasar da zuciyarsa keyi.

Ita kuwa Shatu wasu hawayene, masu sanyi suka zubo mata. Musamman da ta fahimci cewar, zafin kishine ya birkita mata salihin mijinta.

A hankali ta miƙe tsaye, tare da soma takawa ta shige Bathroom. Ruwan ɗumi kawai ta watsa tare da yin Brush kana ta fito daga cikin toilet ɗin. Turaren Oud mai daɗin ƙamshi ta shafa ajikinta. Tare da zura wata royal blue sleeping gown ajikinta mai adon net. Yayinda kuma har yanzu ta kasa tsaida hawayen dake kwance acikin idanunta.

Wasu lallausan sleeping shoe ta zura a ƙafarta, tare kuma da tubke long hair ɗin kanta, da bluesy ribbon. Tana gama kimtsa kanta kuwa, ahankali ta fito daga ɗakin, tare da jawo ƙofar ta rufe. kaitsaye ta nufi Side ɗinsa.

Cikin sanyi ta tura ƙofar Bedroom ɗin nasa tare da yin sallama can ƙasan maƙoshinta.

Ganinsa atsaye da tayi ne kuma yasa, ahankali ta jingina da jikin ƙofar tana kallon yadda yake zirya a tsakiyar ɗakin, shi kadai sai ya kai mari ya kau gouro. Ga wani irin numfashi mai ɗumi da yake fitarwa. Idanunshi kuwa sun kaɗa sunyi jazir.

A hankali ta nufo tsakiyar ɗakin. Cikin sanyi da kuma rauni ta nufi inda yake. Dai-dai lokacin shi kuma ya juyo. Yana juyowa kuwa ta faɗa jikinshi ta rungumeshi tsam a jikinta. Ashagwaɓe ta saki wani irin raunataccen kuka mai kashe jiki da zuciya. Murya na rawa cike da rauni tace.

“Kayi haƙuri Yah Sheykh ka gafarceni, na tuba please, kukana bawai inayi dan na ɓata ranka bane, banason fushinka, Dan Allah kada ka kwana kana fushi dani, I’m very scared dan bazan iya jurewa ba...”

Kasa ƙarasa maganan nata tayi, lokaci ɗaya kuma ta ci gaba da sakin Shessheƙan kuka, tare dasa hannayenta akan chest ɗinsa.

Shi kuwa Sheykh har yanzu fushi yakeji, saboda haka ma gaba ɗaya jikinshi rawa yakeyi dan tsananin takaici kukan da takeyi. Hannunshi yasa ya soma ƙoƙarin ɓanbareta daga jikinsa, murya adaƙile yace. "Ni Sakeni! ki barni!! kuma ki fita harkana!!! Kije can ki gama kukan naki a can ɗakinki, badai kinfi sonshi ba? maza fice min a ɗaki ni ɗakina ba wurin zubda hawayen soyayyar wani ƙato bane."

Jin hakanne yasa, cikin sauri tasa hannayenta ta saƙalo wuyanshi, tare da cusa kanta a ƙirji shi, murya a raunace tace. "Ni banason shi, da gaske Yah Sheykh ka yarda dani bana sonshi, aduniya waye zanso sama da kai? kaine fa Mijina, mahaifin ƴata, sannan kuma Garkuwa ta, tayaya zan so wani bayan kai?”

Da sauri yace. "Eh mahaifin ƴarki ko? Bama mahaifin ƴaƴan kiba, wato irin daga ita shike nan ko?".

Baby face d’inta ta shag’wabe, cikin kasala da kuma son sauk’ar masa da fushinsa tace. "I’m very sorry Zawj mahaifin yaƴana."

Idanunsa yaɗan lumshe, cikin kuma yanayin fara jin sanyi arashin ya tureta ya koma bakin gado ya zauna tare da cewa. "In dai bazaki bar kukan nanba fice min a ɗaki sanida kukanki yana ƙona min rai".

Da sauri tasa tafin hannunta ta share hawayenta. Kana ta matsoshi Ahankali ta kwanta a jikinshi tayi lib, laɓɓan bakinta taɗan tattauna kana a raunace tace.

“Please Yah Sheykh nabar kukan, amma ka yafe min, bazan sakeba dan Allah kayi haƙuri".

Ajiyar zuciya mai sanyi, ya sauƙe dan ta haɗashi da Allah ta gama zance.

Juyowa yayi asanyaye ya fuskanceta, tare dasa hannunsa ya ɗan tallafo kanta, shiru yayi batare daya ce komae ba, sai tsurawa fuskarta ido da yayi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull