Kenza eBookz

Garkuwa complete novel - Chapter 20

Garkuwa complete novel - Chapter 20

Garkuwa complete novel Chapter 20: Garkuwa complete novel Chapter 20. A hanyarsu ta komawa side ɗinsu ne, Gimbiya Saudatu ta kalli Laminu cikin takaici…

4,326 words

A hanyarsu ta komawa side ɗinsu ne, Gimbiya Saudatu ta kalli Laminu cikin takaici tace "Banza kawai me tsoron zuci me dan ya matso kusa dakaii ka wani firgita ka razana har ɓari jikinka keyi ka miƙa mishi jaridar, da zamu iya kaita a tallata". Wani irin wawan ajiyan zuciya Laminu yayi tare da cewa. "Uhummmm Umma kenan wato, fa duk wannan kumfar bakin da kikeyi abinda yasa kike yinta da jin daɗin yinta, dan wancan Jabeer ɗin bai taɓa kifa miki bari bane shiyasa. Wallahi Allah da ya taɓa marinki da waɗannan hannayenshi da kike ganin taushinsu kamar na jarirai shakka babu, wlh suma zakiyi sai an yayyafa miki ruwa". Cikin kufula Baba Basiru yace. "Kai tafi daga nan banza mai zuciyar mata, ji abinda kake cewa kan mari ɗaya tak daya taɓa yi maka". Wani irin kallo Laminu yayi musu kab lokacin da suka shiga falon Gimbiya Saudatu. Cikin rumtse idonshi sabida tuno marin da Jabeer ya kifa mishi randa yayi gangancin zai zageshi. Da sauri ya buɗe idanunshi cikin kara yace. "Yesss sabida baku ya shararawa mari ɗayanba shiyasa. Kuna sanefa mari ɗayan da yayi min. A take kunnena ya rinƙa zubda jinin da Ni dai har yau bansan ta inda ya ɓulɓuloba, wlh Allah lokacin daya mareni kusan suma nayi, har yau in na tuno marin sai inji kunnena yayi gummmmm". Cikin zafi Gimbiya Saudatu ta yunƙuro zata surfawa ɗan nata masifa, sai ta kuma komawa ta zauna jin Baba Nasiru na cewa. "Uhummm Dafa gskyar Laminu, in dai Jabeer ya ɗauki hannun mahaifinshi to tabbas, suna da zafin hannu mai ban tsoro, In dai ya gado hannun Ya Habibullah to fa duk abinda suka mara wlh in dai dabbace sai dai a matso mata da wuƙa, in kuwa mutum ne to, tabbas zai sha azaba mai raraɗi. In jifa ne ma sukayi ma basa saɓawa saiti sai sun samu abin harinsu, in kuma tsuntsune ko ƙananan halittu tofa in suka harba sai lahira." Sai kuma ya ɗan tsaya ya kallesu cikin dakiya yace. "Munada buƙatar sabon shiri, akanshi, zamuyi mgnin bakinshin nan da baya mutuwa". Cikin takaici Gimbiya Saudatu tace. "A duk cikin ababen da ake dangantawa dasu babu, abinda yafi cimin rai kamar meda, zoo ɗin masarautar sade ɗin Jabeer. Wlh duk sanda najiyo kukan Ɗawisun Masarautar da sauran tsuntsaye nakiji kamar in je in samisu shinkafar tsuntsaye suci su mace kab ɗinsu kowa ma ya huta." Barrister Kamal dne dake, Jinsu ta window ɗin falon. Ya jinjina kai tare da jan hannun Sulaiman suka tafi yana mai cewa. "Uhum naku burin dai baza taɓa cikaba in sha Allah". Su kuwa nan sukaci gaba da tattaunawa yadda shirunsu a kanshi zai kaya.

Jakadiyarsu kuwa saida taga fitansu ta sauƙe ajiyan zuciya. Jafar kuwa saida yaga Barrister Kamal ya fita kafin jikinsa ya dena rawa da karkarwa.

Shi kuwa Haroon da sauri yabi bayan Jabeer cikin sauƙe nannauyan numfashi yace. "Wato kai bakinka bazai mutu bako." Cikin kufula ya juyo ya kalli Haroon jin ya yace mishi irin Abinda kullum Abba yake cemishi. A hatsale yace. "Eh bakina bazai mutuba ba kuma zan bar ko wanne taƙadirinba, duk wanda yace dani tak zai samu amsa dai-dai da zancensa. Wannan zarerriyar matarfa ta kiyayeni, kadafa ta fusatani, tam!". Ya ƙarishe mgnar da taune lips ɗinshi. Cikin sanyi Haroon yace. "Nifa tsorona ɗaya Jabeer kada su cutar da kai, so dan Allah duk abinda zasuyi maka kosu Jalal da ya Jafar kada ka tanka musu. Yanzu wannan sharrin ya zamuyi dashi?". Wani irin kallo yayiwa Haroon cikin sauƙe numfashin yace. "Tuni na magance ta, na saye jaridun, tun kafin a fiddasu, shima dan ya ɗauka ne tun kafin inji inje wurin. Kuma gashi shima a hannun yanzu sai dai su nemo wani sharrin. Kuma batun basu amsa, da sun gane sun dena sako Mahaifiyata a duk abinda zasuyi min da Ni dai ko kallo basu isheni ba." Cikin sauƙe numfashin Haroon yace. "To Alhamdulillah Allah ya kare gaba". Amin yace tare da zama bisa kujerarshi ta musamman wacce take kyautace ga Sheikh Abdulkarim. Tab ɗin shi ya ɗauka ya fara wasu yan dube-duben.

Anan falonshi suka zauna, shida Haroon. Jin muryar Gimbiya Aminatu na ratso falon ne yasa Haroon yin murmushi cikin sabo da tsohuwar yace. "Yauwa Gimbiyar Lamiɗo kizo kiyiwa wannan jikan naki faɗa". Murmushi tayi mai ƙayatarwa, a hankali ta ƙara so cikin falon ita ɗaya hadimanta suka tsaya a can babban falo da abincin data kawo mishi. A hankali tayi taku zuwa gabanshi gefenshi ta zauna, cikin sanyi ya kalleta. Ita kuwa cikin kulawa tace. "Jabeer, ya jikin naka". Cikin harshen fillanci yace. "Da sauƙi". Yadda ya bata amsa a taƙaicene yasa ta kalli Haroon tace. "Yaci wani abu kuwa?". Da sauri yace mata ehh. Cikin kula tace. "Me yaci!?." Murmushi yayi cikin tsokana yace. "To da sanyin safiyar nan dai an sanshi magantuwa". Dariya ta ɗan yi tare da cewa. "Taso kuzo kaci abinci". Kanshi ya girgiza mata tare da cewa. "Bana buƙatar komai, kawai ki gayawa wannan dottijon mijin naki da sufanshi baya gaya mishi dai-dai ya gargaɗi Gimbiya Saudatu ta dena zuwa min side ɗina. In kuwa taƙi wata ran zan bar Jalal yayi mata ɗan karen duka". Murmushi tayi tare da cewa "To naji taso muje kaci wani abun". Dai-dai lokacin Lamiɗo da Galadima suka shigo. Ɗanzagi da dogari kuma suka tsaya a can bakin ƙofar shigowa falon.

Bayan sun zauna ne Lamiɗo yace. "Ya ƙarfin jikin?". Rai a ɓace yace. "Ai baka da case da raina da lfyata, ko in samu sauƙi ko kada in samu ba matsalarka bace, tun da gani kake iyayena sun haifa maka nine dan ka bawa wasu ƙattin daji su dakani". Murmushi Lamiɗo yayi cikin tsokana yace. "To wai in ban basu kaiba wa kake son in basu?". A hatsale yace. "Ka basu kanka mana, me zai hana kai ka tuɓe gwanjinka a zaneka, dan masifar rainin wayo sai ka nunani, duk da tarin jikokinka da suke wurin." Murmushi Galadima yayi tare da cewa. "Yanzu dai jikin da sauƙi gashi, har zanar ta maidaka mataɗaci, ka fara shiri nan bada dadewa ba za mu koma ka rama". Da sauri ya ɗago kanshi daga kallon Tab ɗinshi ya zuba musu tare da nuna kanshi. Ido suka zuba mishi. Shi kuwa cikin tsuke fuskarsa tamkar zaiyi ruwan jini yace. "Ni! Ni!! Ni!!! Muhammad Jabeer Kuma a wancan garin, me zanje inyi a can, wannan garin ko a mafarki bana fatan Allah ya gwada minshi, dan Wallahi Allah kenan duk duniya babu garin da na tsana sama da wannan garin. Na tsani garin bana ko son jin makamacin sunan garin. Da garin da mutanen garin gaba ɗaya basa cikin jadawalin jerin mutanen da zuciyata zata sosu har gaban abadan me na samu a wannan garin banda tozarci da ɓaƙar azaba." Murmushi Lamido yayi kana cikin son jikan nashi ya dafa kafaɗarshi tare da cewa. "A makon-nan ma kuwa zaka koma wannan garin da izinin Allah". Mgnar Lamiɗo ta ƙarshe da yace da izinin Allah ne yasashi yin shiru. Haka suka ƙaraci mgnarsu bai kuma ɗago kanshi ya kallesu bama bare ya kulasu.

Bayan sun tafine. Ummi da Gimbiya Aminatu suka samu suka sashi ya ɗanci abinci.

Zuwa azahar kuwa sai ga Sarkin Musulmi Jalaluddin da Sitti.

A sashin Gimbiya Aminatu Sitti ta sauƙa shi kuwa Jalaluddin a sashin amininshi Lamiɗo ya sauƙa. Saida akayi sallan la'asar kafin suka isa sashin, Jabeer. Sosai suka nuna mishi kulawa da gata, Inda yaketa son huce haushin da yakeji a kansu tunda sune dai suka sashi yin wannan abun a bisa dole. Hajia Mama kuwa daɗi kamar ta goya Sittin dan kulawa da so.

Sai washe gari. Suka koma Laddi julɓe sunan jihar da nanne asalin tushen masarautar sarkin Musulmai yake.

Mama kam hankalinta ya konta ganin jikin Jabeer yayi sauƙin sosai.

Batul kuwa babu nacin da batayiba ta samu ta ganshi ido da ido abin yaci tura.

A haka kwanaki sukayi ta tafiya, ana bawa Jabeer kula tamusamman.

Yayinda Sarkin Shaɗi kuwa yake ta tsuma bilalin Shaɗin masarautar Joɗa wanda a ƙalla tsawon kusan shekaru ɗari biyu da wani abu. Suna binne cikin ramin tsuminsu Wanda da dafin macijin gadin masarautar ake tsumashi.

Umaymah kuwa tana shirin zuwa duba jikin ɗan ƴar uwar tata ɗa mafi soyuwa a gareta sama da ƴaƴan data haifa a cikinta ma.

Yau kwana biyar da faruwan abun. Sosai jikinshi yayi ras.

Yaune kuma Umaymah ke tahowa jirgin yamma zata biyo.

Shi kuwa Jabeer zuwa yanzu ko mgnar kowarshi wannan garin ba'ayi sabida irin ɓacin rai da yake baiyana a fuskar shi, in an mishi mgnar zuwa garin.

Allah ya sani yana jin ya tsani wannan gari tsana mai tsanani. Yana masifar jin kunyar komawa na wannan garin da a tsakiyarshi akashi cire suturarshi ya zauna dagashi sai boxes.

Yakanji kamar ya faɗi ya mutu in ya tuna garin.

Ƙarfe biyar dai-dai motocin da suka ɗauko Umaymah suka iso cikin harabar masarautar.

Dai-dai lokacin kuma Hajia Mama da Batul suna gab da shiga sashin Jabeer, A tsakiyar falon sukayi kiciɓis dashi. Yana sanye cikin tufafin da sune suturarshi, al'kyabbar ruwan madarace, sai kayan dake cikin al'kyabbar su kuwa ruwan bonbitane, yayi wani irin masifar kyau, sai ƙamshi yake bazawa tako ina. Fuskarshi ta fito ras cikin hiraminshi ruwan madara, Wani irin ƙyalli da sheƙin kyau yakeyi. Duk da ba murmushi a kan fuskarsa amman ana iya gano tsantsar farin cikin da yake ciki. A hankali yake taku, Ya Jafar na biye dashi a baya, Cikin tarin kula da nuna soyayyarsa Hajia Mama tace. "Masha Allah, Ɗan Umaymah yayi kyau, ga farin ciki ya wadaci kekyawan fuskarnan taka". Kanshi ya ɗan kauda ya kalli Ya Jafar daketa jan hannunshi su fita, cikin nitsuwa yace. "Sun isoma". Cikin jin daɗi tace. "Eh haka dai Jamil ya gaya min". Ta ƙarishe mgnar tana juya baya tare da Batul da cikin sanyi tace. "Ya Jabeer ya jikin?". Cikin jan gajeren tsaki yace. "Lfyata lau". Murmushi tayi sabida jin zazzaƙar muryar shi.

A tare suka fito su Mama na gaba shida Jafar suna baya.

Suna fitowa harabar Side ɗin shi. Motarshi da Sheykh Abdulkareem yasa aka taho mishi da ita wacce bai taɓa hawantaba, asalima gani yake tamkar almozzaranci ne, sai yau ya bawa Haroon key ɗin ta yace a ɗauko mishi Umaymahnshi, shi bazai je ɗaukotaba sabida. Lamiɗo yace bazai fitaba. A hankali ya tsaya ganin hancin motarshi ƙirar Mercendes benz maybach Exelero wacce ta kai kimanin $8 million dollars.

Da sauri ya ƙarasa jikin motor. Hajia Mama na biye dashi. Yana isa inda suke yasa tattausan hannunshi ya buɗe marfin motar. Karo na forko da naga murmushi a fuskarshi, cikin tarin shaƙuwa da kulawa yace. "Marhababuki ya Umaymah, ta faddal". Wani irin murmushi Umaymah tayi cikin tsantsar so tasa hannu ta kamo hannunshi daya nuna mata alamun ta fito. Wani irin yalwataccen murmushi mai nuna tsantsar jin daɗi ya kumayi lokacin da yaji tasa hannunta tsakiyar kanshi. Da sauri ya rusuna a bakin motar cikin sanyi ya manna kanshi da guiwowinta dake zuro woje, kanshi ta shafa tare da cewa. "Allah yayi maka al'barka ya kare mana kai da kariyarsa mai tarin yawa ya iya maka abinda idonka baya gani". Amin Amin, su Haroon da Jalal, Jamil, Hibba, ƙanwar Haroon, da kuma Imran, Sulaiman, Aunty Juwairiyya dake kusa da Umaymah. suka amsa tare da murmushi a fuskokinsu. Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya tashi kana ya buta hanya ta fito. Tana fitowa Hajia Mama ta ƙara so gareta cikin tarin baiyana jin daɗi ta ruggume Umaymah tare da cewa. "Ta ɗanki kawai kikeyi, mu har mun kusa mu bushe a tsaye". Murmushi Umaymah tayi tare da cewa. "Afwan ya Aunty kin san in Jabeer na yana wuri bana ji da ganin kowa sai shi". Haroon ne ya taɓe baki tare da cewa. "Uhumm ai mun saba ganin wariyar launin fata". Hannunta tasa ta ɗan zunguri Haroon tare da cewa. "Kishi". Jamil ne ya ɗan kallesu lokacin da suka ɗunguma suka nufi Sade ɗin Jabeer cikin tura baki yace. "Allah ko Mama kada ki bari Umaymah ta sauƙa a sade ɗin Hamma in dai ba sade ɗinmu zata sauƙaba Muda muke ƙanana sai ta sharemu saishi. Tunda hakane ta sauƙa side ɗinkin". Cikin dariya Umaymah ta juyo da sauri ta kalleshi tare da cewa. "To Jamil harda kai, wato kaima ɗan team ɗin Haroon ne ko? To sha kuriminka Aunty bazata shiga tsakanin uwa da ɗaba, ko Hajia Mama?". Ta ƙarishe mgnar tana kallon Hajia Mama daketa murmushi cikin jin daɗin tace. "Haka kuma ɗa bazai shiga tsakanin ya da ƙanwaba, Gaba ɗaya Jabeer ya kwace mana ke". Murmushi mai kama da dariya sukayi gaba ɗayansu lokacin da suka shiga cikin falon.

Shi dai Jabeer sai murmushi yakeyi. Ya Jafar kuwa in yaga Jabeer na murmushi sai shima ya ɗanyi murmushi. Aunty Juwairiyya ce ta ɗan kalli Batul dake gaida Umaymah sakin fuska tace. "Matar ƙani yau tun safe ban jikiba". Wani irin murmushin jin daɗi tayi Allah yasani in Aunty Juwairiyya tace mata matar ƙani tana jin daɗi. Cikin happy tace. "Yau a kitchen na wuni inayiwa Umaymah girkinsu na larabawa". Murmushi Juwairiyya tayi tare da cewa. "Yo ai na rigaki, dama girkin bare bari kikayi mata". Kanta ta ɗan juya takalli Sheykh Jabeer dake zaune kusa da Umaymah, in zaiyi mata mgna sai ya juya harce zuwa larabci. A ranta take addu'o'in Allah ya nuna mata ranar da zata zauna kusa dashi haka a matsayin abar sonshi. Tattausan Lips ɗin shi masu kama da kunnen fure ta kalla. sunan jazir sai sheƙi sukeyi a cikin tattausan sajenshi da gemun tamkar an shafa musu mai. Allah ya sani randa ta samu lips ɗin nan a matsayin mallakinta, tabbas sai ta kusan haɗiyesu.

Hajia Mama da kanta da ita da Aunty Juwairiyya ne suka rinƙa kawowa Umaymah abubuwan motsa baki yaran yar uwarta na zagaye da ita, Hibba ce yar autarta ta ƴar kimanin shekaru 16 kalli Jabeer cikin cikin sanyi tace. "Hamma Jabeer Aunty Jazrah tace in gausheka, wai yaushe zamuje". Kanshi ya juyo ya ɗan kalli Hibba cikin son yarinyar yace. "Hibba auta yaushe kikeso muje". Da sauri tace, sai na tambayi Aunty Jazrah". Murmushi yayi kana ya kalli Aunty Juwairiyya yace. "A shigar mata da kayanta, a ƙara gyara mata masauƙinta, yafi fadar Jalaluddin kyau". Dariya sukayi baki ɗayansu. Shi kuwa Sheykh Jabeer kamar ba shi yayi mgmar ba. Ita kuwa Umaymah da Hajia Mama hararanshi suka ɗanyi tare da cewa. "Ai babu fadar da zatafi fadar shi kam, shinefa gatanka". Murmushi ya ɗanyi tare da cewa. "A a kam Allah ne gatana, shi kuma da yake son ayi ta ɗimata". Juwairiyya kanta tayi mamakin sakewar Jabeer sosai Duk wanda ya ganshi zaiga tarin farin ciki tare dashi.

Nan dai suka zauna akayi ta hira.

Saida aka kira magriba ne, duk suka miƙe sukaje sukayi al'wala.

Batul kuwa tafi kowa farin cikin, zuwan Umaymah ko ba komai ta samu ganin Jabeer yadda take so.

Bayan an idar da sallan isha'i ne suka dawo masalacin. A nan bisa dinnin area. Suka zauna nan sukaci abinci.

Koda suka gama ne, sunata hira a falon harda Jakadiyarsu. Jabeer ne da yanzu ya fito falonshi cikin nitsuwa yace. "Kai dan Allah ku barta ta huta mana". Sai ya kuma ɗan kalli Umaymah tare da cewa. "Umaymah muje ki gaisa da Lamiɗo, ya kirani yanzu yanata min ihu a kunne wai yaji kin iso tunda yamma kuma ban kai mishi keba". Da sauri ta miƙe tare da cewa. "To muje". Hibba ce ta tashi da nufin binsu sai kuma ta zauna, jin Jabeer nace mata. "Zauna Hibba saida safe kuje da Jalal." Sai ya kuma kalli Jakadiyarsu cikin taushin murya yace. "Ummi muje". Itama da sauri ta miƙa.

A tare suka fito yana gaba Umaymah na binshi, Jakadiyarsu na bayansu. Suna tafe cikin jin daɗi ko ina yayi lib sai sanyin korayen ciyawi da furannin da dogayen bishiyoyin gwanda da ayaba da sukayiwa ko ina ƙawanya.

Suna isa ƙofar Gimbiya Aminatu da sauri. Sallama ya basu hanya, wanda a ƙa'ida sai ya shiga ya nemawa mutun izinin shiga kafin ka shigo. So amman Jabeer baida hijabi da sashin kakanin nashi, shiyasa kai tsaye suka wuce. Shiru babban falon babu kowa. Haka yasa suka wuce sashin Lamiɗo, a hankali yayi sallama, Cikin murmushin Lamiɗo ya amsa sallamar tare da cewa. "Bismillah, ku shigo". Kusan a tare suka kutsa kai cikin tamfatsen falon nashi.

Wani irin kallo sukayiwa juna, Ganin...!

By *GARKUWAR FULANI*

Ganin wani irin hayaƙi fari tas yana fitowa, tako wacce ƙofa na jikin curin. Da sauri Galadima yasa hannunshi ya kamo hannun Jabeer yaja da ƙarfi. Alamun ya nitsu ya zauna, cikin mamaki ya zubawa tarin hayaƙin dake bulbulowa daga ƙofofin ramin shirgegen curin. Su kuwa ga ɗayansu hankali konce suke zaune. Ido ya zuba musu tare da cewa. "Me hakan?". Da sauri Lamiɗo ya girgiza mishi kai hakanne ya sashi jan gajeren tsaki tare da cewa. "Nifa ba son wannan soki burusun naku da surkunlenku nakeyi ba. Me gamina da ku da tsare-tsaren naku. Fisabilillahi me wannan?". Cikin faɗa Lamiɗo ya sa hannu zai bugi bakinshi da sauri ya kauce. Cikin hatsala Lamiɗo yace. "Wannan bakin naka da baya mutuwa, komai sai kayi inkarin a kai tabbas sai na kashe bakin nan". Wani kallo yayi mishi tare da cewa. "Uhumm ai babu mai kashe bakin Muhammad Jabeer sai Allah". Ganin zaija suma suyi surutune ya sasu kauda idonsu kanshi.

Bayan kusan mitinu goma, sai ga hayaƙin nan ya bar fitowa, Sai wani irin huci. Da sauri Jabeer yace. "Nifa zan tafi, inma kun mance in tuna muku yau jumma'a ace, inada abinda yafi wannan abun naku mahimmanci a rayuwata ta duniya da ƙiyama, yanzu gashi har kusan sha biyu." Murmushi sukayi baki ɗayansu ba tare da sunce mishi komaiba. Sabida dama sun san za'ayi haka kam. Sabida kowa ya sani shi Jabeer yana barranta da duk irin waɗannan ababen gado na sarauta shiyasa sarautar kanta shi bata ɗaɗashi da ƙasa ba.

Da sauri ya buɗe siraran idanunshi da kyau. Sabida ganin wani irin ƙaton maciji ya sako kanshi cikin babban ramin da yafi girma.

Da sauri yace. "Innalillahi wa innailaihi rajiun!." Sai kuma ya zubawa maciyar nan idanu. Tana fitowa cikin ramin ta, zuɗuɗuɗuɗuɗu. Haka yake zaro jikinshi. Haƙiƙa dole duk wanda bai taɓa ganin macijinba bai kuma san da zamanshi ba, dole ya razana. Dan ma shi zuciyarshi na cike da tsoron Allah so irin wadannan ababen ba kasafai suke firgitashiba. tashinsa fahimtar ko wani ɗan abin sihirin za'ayi mishi ne. Wani dagon numfashi yaja mai ƙarfi ya sauƙe ganin. Yadda macijiyarna taketa keta fitowa taƙi ƙarewa. Su dai su Lamiɗo shiru sukayi a zaune. Saida ta gama fitowane, ya rage iya bindinta sai gashi ta fito bindinta na kananmaɗe da wasu irin kitsastsun bulalin da ka gansu kasan tsoffine. A hankali ya turo bindinshi gaban Lamiɗo, Ya ajiyesu, sai kuma ya sumkuyo da kanshi ya zaro harshensa ya rinƙa lasar bulalin nan saida suka fito ras kamar an wonkesu. Kana ta juya ta nufi cikin curin zuɗuɗuɗuɗuɗu ta koma, Kamar forko sai ga hayaƙin.

Wani nannauyan numfashi Jabeer ya sauƙe tare da cewa. "Uhum inda ranka kasha kallo. Oh ni Muhammad Jabeer an ɗauramin jakar tsaba za'a jazamin kaji su bini su tsastsageni. Du wai wadannan abubuwan na menene wai dan Allah". Ya ƙarishe mgnar yana kallonsu baki ɗayansu, fuskarshi cike da alamun fargaban gudun saɓawa ubamgijinshi.

Su kuwa saida hayaƙin ya gama ɓacewa baki ɗaya sannan Lamiɗo ya fara miƙewa kana suma duk suka miƙa. Sarkin Shaɗi ruggume da bulalin.

Juyawa sukayi zasu nufi hanyar da zata ɓullo ta falon Lamiɗo, da sauri ya ɗan motsosu tare da cewa. "Dan Allah shi wannan abun me amfanin zamanshi a nan? Wurinda Kum san duk baƙin da suke zuwa tako wani sashi na duniya ganin abin tarihin masarautar Joɗa muna kawosu nan. Yanzu in wata ran yunwa ta koroshi ya fito ya cutar da mutane fa me zakuce?". Cikin ƙosawa da mgnar Galadima ya gyara riƙon da yayiwa sandarsa cikin sanyi yace. "Bata tare da yunwa, macijiyar da duk wata sai an ajiye mata motar ƙwai a cikashi da kiret-kiret na ƙwai shine abincinsa". Da sauri Galadima ya nufi hanyar fita. Lamiɗo kuwa tuni sun tafi.

Ganin sun tafi sun barshi a nan a tsayene. Yasashi sauƙe numfashin tare da juyawa ya nufi, ƙofar da zata sadashi da falonshi.

A hankali yake taku, cikin kasala da mutuwar jiki, da mgnar zuci. "Wai ya zanyine? Wanna wacce irinyar masifeffiyar rayuwace? Yaushe zamu samu Allah ya gama tsarkake mana wannan masarautar Joɗa ya rabata da wadannan tsarabe-tsaraben gargaji. Wannan wacce iriyar fitinace?". Dogon numfashi yaja lokacin da ya shigo falonshi, babu kowa, can babban falo ma babu kowa bisa dukkan alamu duk sunje shirin sallan jumma'a ne.

A hankali ya kutsa kai cikin bedroom ɗin shi. Kai tsaye bathroom ya wuce. Jallabiyar jikinshi da hirami da vest ɗin ya cire, Cillasu yayi cikin injin wonki. A hankali yake taku kanshi a sunkuye dagashi sai boxes Sky blue. A hankali ya shiga cikin wurin wonkan. Kamar yadda ya saba haka yayi wonkan jumma'a anshi.

Bayan ya fitone ya nufi drower'n glass ɗin dake cikin bathroom ɗin. Wani tattausan Baby towel ya ɗauka bisa saman kafaɗunshi ya ɗauri ya fara gogewa, yana tsane ruwan jikinshi. Kana a hankali ya ɗauki wanni babban towel ɗin ya ɗaura daga saman ƙirjinshi. Wanda ya sauƙo har guiwa shi, a hankali yasa hannun ta ciki ya fara murza boxes ɗin yayi ƙasa, dashi yana zuwa sharabanshi ya riƙe shi ya zare ƙafa ɗaya, kana ya zare ɗayar ma. Lallaɓeshi yayi ya matse kana ya shanyashi kan ƙarfin silver da yake na shanya. Farar jallabiya ya zura a jikinshi, kana ya kwance towel ɗin. Dashi ya goge suman kanshi.

Cikin hamzari ya fito bedroom, Kai tsaye gaban dreesing mirror ya nufa, mai ya shafa a dukkan sashin jikinshi. Kana ya taje tattausan suman kanshi tare da shafa mishi manshi, wani Duaol jannah mai masifar daɗi ya shafawa jikinsa, kana ya ɗauki wani ƙaramin kum ya tace tattausan sajenshi ya kontar dashi lib-lib hakama gemunshi.

Saida ya gama komai na gaban Mirror kana ya nufi babban drower'nshi da sauri-sauri yakeyin komai. Wani tattausan jallabiya mai masifar kyau da taushi fari ƙal ya zaro. Kana ya ɗan yi sama da kanshi ya kalli cikin tsep ɗin ƙarshe na drower'n inda al'kyabbanshi suke jere a kimtse tamkar shagon saidasu. Hannu yasa ya zaro wata sabuwa dal tana cikin ledanta tana haɗe da hiramin ta da komai. Rufe wannan wurin yayi kana, ya buɗe wani sashin inda ƙananan kayan shi ke jere, boxes and singlet ya zaro farara ƙal suma sabbi ne. Da sauri ya rufe drower'n kana yazo ya ajiyesu bakin gadonshi. Ba tare da ya cire jallabiyar jikinshi ba, ya saka boxes ɗinshi saida ya dai-dai-ta zamanta a jikinshi da kyau ya kimtsa komai nashi yadda zaiji daɗi tafiya, kana ya zare jallabiyar ya ajiyeta bakin gadon Singlet ɗin ya yasa, sannan ya ɗauki farar tattausar jallabiya mai dogon hannun ya saka, jallabiyar daya cire ya ɗauka ya gaban ƙaton drower'n nashi ya nufa, wani side ɗin ya buɗe nan ya saƙalata. Kana ya dawo bakin gadon. Ledan al'kyabbar ya farka da ƙarfi da kuma sauri sabida ganin tuni ƙarfe ɗaya da rabi tayi, yasan yanzu masallacin ya cika maƙil da mutane. Ɗan gajeren tsaki yaja, tare da ci gaba da warware al'kyabbar. Yana gamawa ya zurata a jikinshi, al'kyabbar baƙace, sai gefen bakinta da akayiwa kolliya da wani zare mai masifar kyau Golding color irin mai sheƙi da ɗaukar ido, hakama, kan kafaɗunsa har zuwa hannunta anja zirin irin wannan kolliyar. da sauri ya dai-dai-ta zamanta a jikinshi, kana Ya juya ya nufi, gaban dreesing mirror da hiraminshi a hannunshi, Yana isa ya ajiye baƙin abin, kana ya ware farin hiramin shima da kolliyar Golding color a jikinshi, ya ninkeshi kamar yadda muke ninke dankwali, bayan ya gama ne. Ya ɗaurashi a kanshi ya dai-dai-ta zamanshi kana, ya ɗauki baƙin abin wanda shima an zagayeshi da Golding color ya sakashi a akanshi, ya fito ras tamkar a Saudia. Allah ya sani yana masifar son wannan shigar da jin daɗinta a jikinshi babu takura babu matsi gashi ka suturtu da kyau mayu masu kallon tsiya irinsu Jazrahda Batool duk basa iya ganin komai a jikinshi ba.

Da sauri ya nufi wurin aje takalma shi wanda yake na glass ne marfin ya buɗe kana, ya ɗauki wasu takalma irin nasu na sarauta Golding color ne kuma half cover ne, zura jajayen sawunshi yayi a ciki, kana ya koma gaban mirror, wani kolba turaren OudKareem mai masifar ƙamshi mai sanyi, ya fesa a duk sashin jikinsa. Kana yasa hannunshi ya ɗauki carbinshi. Farin galashi ɗan siriri ya manna a idonshi. Kana ya juyo da sauri zai fita, sai kuma ya tsaya cike da mamakin ganin. Haroon tsaye ya zuba mishi ido. Ya buɗi baki zaiyi faɗa sai kuma yayi shiru jin Haroon na cewa. "Kada kace zakayi faɗa Lamiɗo ne yace inzo in kiraka, lokaci na tafiya fa." Bai kulashi ba kawai yayi gaba, da sauri Haroon ya bishi tare da cewa. "Wannan baza ƙamshi haka sai kace wurin amarya zakaje, gsky kayi kyau sosai masha Allah". Bai kula Haroon ba sabida addu'o'in da yakeyi. Amman duk da haka saida ya bawa Haroon amsa a zuciyarshi, yake cewa. "Akwai wani wuri da yafi cancanta da ɗan adam yayi shiga ta tsabta da kyan shiga da ƙamshi sama da masallacin ne? Innal masajida lillafa, duk duniya da babu wurin da Allah ya keɓanta yace dakinshine sai masallatai. Nan zamu gana dashi. Domin idan mu bama ganinshi ai shi yana ganin mu". Murmushi Haroon yayi, dan Jabeer bai san mgnar da yakeyi a zuci ta fito filiba.

A haka dai suka shiga Masallaci.

Dole yau a gaggauce yayi Kudbar jumma'a dududu 15 minutes yayi yana kudbar kan halaccin mace ta kalli mijin da yakeson aurenta, kamar dai yadda yayi al-ƙawari a wancan satin. Daga nan aka kabbarta sallah.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull