Garkuwa complete novel - Chapter 33
Garkuwa complete novel Chapter 33: Garkuwa complete novel Chapter 33. Cikin turo baki ta harari gefen fuskarshi, kana ta ɗan rusuno a hankali ta zauna.…
4,423 words
Cikin turo baki ta harari gefen fuskarshi, kana ta ɗan rusuno a hankali ta zauna. Bakin kujerar dake bayanta. Cikin muryar ƙunƙuni tace. "Bacci nakeji". Bai kulata ba, sai ma gyara zamanshi da yayi ya nuna mata plate ɗin gabanshi. "Cikin cinna bikin sama tace. "Bana gane kurmanci". Juyowa yayi ya watsa mata narkakkun idanunshi da bata iya gano meke cikinsu cikin nata. Karon forko kenan data ga zahirin yadda kalar ƙwayan idonshi suke, sosai kwarjinshi da haibarshi ya danne tsiwarta, a hankali ta matso kusa da inda yake. Rusunawa tayi har ƙasa a hankali ta buɗe plate ɗin data shirya mishi Chechen balls da ganyen Fork ta ajiyeyi mishi gefen plate ɗin kana tasa hannun zata ɗauki flaks alamun zata samunshi tea a cup ɗin. Yatsarshi manuniya ya ɗan ɗaga tare da kaɗa mata ƴatsar alamun bai sataba. Yamutsa fuska tayi tare da turo baki cikin yin ƙasa da murya can cikin maƙoshinta tace. "Karkaci ma in kaga dama". Ta gefen idonshi ya kalleta ba tare da ya juyoba yana kallon yadda takeyin mamul-mamul da lips ɗinta, Gyara zamanshi yayi tare dasa hannun ya ɗan ɗauki Fork ɗin Chechen ball ya ɗan soka kana ya ɗago alamun zai kai bakinshi sai kuma ya maida cokalin ya ajiye. Ɗago kanshi yayi ya zuba mata ido na 3 second kana ya nuna mata idonshi tare da lumshesu alamun ta rufe idonta tako gane abinda yake nufi. Cikin gunaguni tace. "Nifa zan tafi bacci nakeji, ba sai na rufe idona a nanba zan tafi kaci abinci k". Shiru tayi ganin kallo da yake mata da mayun idanunshi. tura bakin tayi tare da sunkuyar da kai kana ta murguɗa bakin. Shi kuwa Sheykh Jabeer, numfashin ya ɗan fesar kana a hankali ya muskuta ya gyara zamanshi, kaikaicewa ya ɗan yi yasa hannunshi cikin al'jihun jallabiyarsa. rafan dubu-dubu sabbi dal-dal ya fito dasu guda shida. Miƙo mata su yayi. Hannunta ta miƙo a hankali ta amshi kuɗin. Gyara zamanshi ya kumayi kana yasa yatsunshi biyu ya jawo ɗaya plate ɗin ya rufe ɗayan. Tsuke fuskarsa yayi da kyau tare da kafeta da ido cikin kakkausar murya yace. "Yau zanyi tafiya daga yanzu, zuwa ƙarfe biyu. Duk inda naje inada lbrin gidan nan duk abinda zakiyi zan sani, duk motsin masarautar Joɗa. Saboda haka ki kiyayi kanki da yiwa mutane tijara, Bana son fitsara da rashin sanin darajar manya, ki tsaya matsayinki, bana son shishshigi cikin al',amuram rayuwata. Ki kuma kiyayi murguɗa wannan bakin fitsarar in ba hakaba wata rana in kin murguɗa minshi bazai dawo dai-dai ba haka zai zauna a murguɗe a karkace, Allah ya nuna miki matsayi da darajar miji." Ƙasa tayi da kanta tare da cewa. "Kuɗin na meye ne". A daƙile yace. "Na yagawa ne, kije ki yaga ki zubdasu". Kallonshi ta ɗan yi ganin hankalinshi baya kantane, ta miƙe tsaya ta juya ta fita. Shi kuwa bayanta yabi da wani irin kallo.
Sosai yaci Chechen balls ɗin dan yayi daɗi sosai, kuma gashi rabanshi da abinci tun jiya iwar hakan, dan haka yaci iya abinda zai iya ci, kana ya miƙe yaje yayi wonka ya fara shiryawa.
Ita kuwa Shatu tana fitowa a falo ta samesu gaba ɗayansu harda Ya Jafar da Aunty Juwairiyya da kuma. Su Jalal da Hajia Mama. ganin hakane yasa ta ɗan juya ta nufi falonta bedroom ta wuce taje ta ajiye kuɗin sannan ta fito. Gefen Ummi ta zauna kusa da Hibba suka ɗan fara hira da Hibba ko inda Mama take bata kallaba.
Can ya fito cikin shigarsa ta yau da kullum.
Da sauri Jalal ya miƙe ya amshi ƴar Kekkyawar jaka ta maza dake hannunshi.
Dai-dai lokacin kuma Ya Hashim ya shigo tare da cewa. "Sheykh mu tafi lokacin yana ƙurewa". To yace kana ya kalli Ummi, Mama, Aunty Juwairiyya, Hibba, yace. "To zamu tafi". Kusan haɗa baki sukayi wurin cewa. "Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lfy ya dawo daku lfy". Amin Amin sukace. Ƙwayar idanunshi ya ɗan juya ya kalli inda take ba tare da kowa ya gane ya kalletanba, kana suka juya suka tafi nan su Jalal Jamil duk suka fito dan sune zasu kaisu Airport.
Daga nan suka tafi sha biyu dai-dai jirginsu ya tashi a international airport Ɓadamaya.
Sai kusa ƙarfe ɗaya su Jalal suka dawo, Sosai suka mamakin wannan karon Ya Jafar bai ce zaibi Sheykh ba.
Haka dai rayuwa tai-ta juyawa sa'a da wuni yau azumi ashirin ne aka kai wanda bahaushe ke cewa an gama goma na wuya za'a shiga na ɗokin salla. Tunda Sheykh ya tafi baiyi mgnar da kowaba a cikinsu har yau kwanansa biyar.
Yana can ƙasa mai tsarki ibada tayi daɗi baya tuna kowa baya tuna komai sai kusanci yake nema da yardar mahalinsa. Ko bacci Allah ya yaye mishi sai yayi baccin awa ɗaya zuwa biyu a wuni daga wannan kuma ya gamsu.
Kullum a a masallaci yake kwana. In gari ya waye sai yayi walahanshi yayi karatun awa biyu, sai ya tafi gidan ƙanan Sitti dake nan Madina wanda shidasu Baba Kamal duk nan suka sauƙa. to a nanne zai ɗan yi bacci.
To yau kuma shine daren da za'a fara tuhajjudi kuma sannan yaune suka baro Madina suka iso makka. Kai tsaye gidansu Sitti suka wuce. Nan suka samu itama Sitti da ahlinta sun iso, Umaymah ma da Haroon yau suka iso. Kana Ibrahim ma da ahlinshin sun iso daga ƙasar Cairo sosai Sheykh Jabeer yaji daɗin hakan. Yau ɗin kuma Yana ɗaya daga cikin dararen da ake tsammanin laylatul Ƙadir.
Kasan cewar babbar zuriya yake. Sheykh Jabeer Ali, ɗane ga Sheykh Ali jikan Sheykh Abdulkareem kenan, Wanda sunanshi aka sawa Jabeer. Yana matuƙar son Jabeer sosai. Hakan yasa tare suke shiga harami tare suke fitowa.
A nan gida Kautal kuwa hada-hadan jama'ar musulmai na tafiya bisa tsarin addinin musilunci kowa na shirin salla da kuma tarban wannan kwanaki goma na ƙarshe.
Yau miyar shuwaka sukayi da tuwo. Suna gama kimtsa komai ne suka dawo falo. Tv suka kunna suna kallo, suna ɗan hira. Gyara zama Ummi tayi tare da cewa. "Lallai yau in munyi garaje zamu makara". Da sauri Shatu tace. "In sha Allah bazamu makara ba, wannan uban bindigar da kukace in lokacin sallan Tuhajjudi yayi zava bugata ai zata tashemu". Hibba ce ta ɗan gyara kwanciyar ta, tare da cewa. "Kalli lokacin shabiyu saura yanzuma za'a fara, Ummi kai mana Tashar Saudi". Ta ƙarshe mgnar tana kallon Ummi da Rimote ke hannunta. To Ummi tace kana ta. Juya musu tashar. Inda suka samu tuni sun fara sallan Tuhajjudi. Inda ake nuna harami kai tsaye. Shiru sukayi suna kallon yadda haramin ya cika yayi maƙil da al'ummar Annabi. Kab an nitsu bakajin komai sai sautin muryar limamin dake karatun al'ƙur'ani cikin zazzaƙar murya mai daɗin sauraro. Koda aka tafi ruku'u gaba ɗaya a tare aka sunkuya hakan yasa abin yayi wani irin kyau mai ɗaukar hankali. Sun jeru tamkar zanen fefeyi. Hakama da suka tafi sujjada. Musamman da yake cameran ɗaukar sama akayi. Suna ɗagowa kuma aka juya cameran ya fuskanci limamin da sauran mamu na sahun forko wanda duk manyan malamai ne.
Cikin wani irin kallo Hibba ta miƙa da ƙarfi tare da...!
Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276 ko kiyi min TRANSFER din 1k Dan samun Special Group ta asusuna na 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276.
By *GARKUWAR FULANI*
Ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu darajar sheƙin Daimond da yayiwa wurin labule. Yayin da kuma hankalinta da idonta duk suke kan ƙafar tashi tana kallon zanen da take gani har kamar motsawa yakeyi a jikinshin, da kuma suffar macijiya. A hankali ta ɗago ƙafarta tare da take step ɗin forko, hankalinta kuwa duk yana baya, har ta juya kanta gaba ɗaya sam ganinta baya gaba. Cikin rashin sa'a kafar ta tsallake step ɗin forko bata isa kan dandamalin ta biyu ba, ta sauketa, cikin akasi ƙafar ta sule tare da yin shuuuuu tayi gaba. Wani ƙara mai ɗan karfi irin na maiyin azumi ta sake tare da rumtse idanunta da ƙarfi tana jiran taji ta ina ɗin ta zai karye. Wani irin ihu ta kuma sakewa, lokacin da taji ta faɗi gib a kan stpes ɗin kanta ya bugi dandamalin sama.
A hankali ya juyo kanshi ya kalleta a fakaice, Ba tare da yace mata ko ƙalaba ya juyar da kanshi ya fuskanci tray'n data ajiye mishi, plate ɗin fruits ya ɗan buɗe kana, ya ɗauki Fork ɗaya, janye ƙafafuwan shi, yayi ya sauƙo dasu ƙasa kana ya gyara zamanshi ya fuskanci Dinning table ɗin da kyau. Fork ɗin yasa ya fasa cikin dabino da yake irin na kwali nanne mai laushi ne, ture ɗan yayi gefe kana ya soki dabinon a hankali ya kai bakinshi, bayan yayi addu'o'in buɗa baki. Ido ya lumshe jin lokacin da sanyi da zaƙi da ɗanɗanon dabinon ya game mishi baki.
Ita kuwa Shatu kuka tasa tare da riƙe ƙugunta, da kanta cikin muryar kuka take cewa. "Wayyo Allah na. Wayyo Ummey na, bayana ya karye ƙuguna ya ɓalgace, kaina ya fashe ƙeyana ya tarwatse". Ta ƙasa Glass ɗin table ɗin ya ɗan kalleta, kana ya maida kanshi yaci gaba da cin dabino, yana maijin wani irin masifeffen dariya na taso mishi jin raki da Shatu ke zubawa. Saida yaci ƙwaya bakwai, kana a hankali ya fara tsira Fork ɗin kan ƴaƴan inabi masu masifar sanyi da daɗi, ci yakeyi yana jin ƙishin daya addabi moƙoshinsa na wucewa. saida ya tsinke nonon inabin kab ya cinye, kana ya fara soka kankana da akayiwa ƙaƙanan yanka kana aka barbaɗa garin madara a samansu, shima shanye rabinshi yayi. Wani sassanyan gyatsa yayi tare da ture tray'n gefe.
Ita kuwa Shatu sosai taji zafin faɗuwan ga azumi ga gajiyan aiki ga faɗuwa ga haushin yadda duk ihun da tayi babu wanda ya kulata, bare a kawo mata agaji, abun ya haɗe mata sai hawaye share-shere ta tabbatar da a gidansu ne tayi wannan ihun da gaba ɗaya iyayenta da yayunta da ƙanwarta duk suna kanta, da tuni an ɗagata a wurin ma. Bege da kewa da kukan rashin yan uwanta da watseman ahlinsu ne ya tunzura hawayenta. Ta kasa tashi sabida jikinta duk rawan yunwa da gajiya yakeyi ba ƙarfi sam.
A hankali ya miƙe tsaye bayan ya sha ruwan zam-zam mai ɗan sanyi kan ƴaƴan itatuwan da yaci. System ɗinshi ya ajiye kan Dinning table ɗin, tare da wayarshi. Gefenta ya ɗan ratsa ya fara taka steps ɗin tare da kallonta a fakaice. Yana gab da sauƙane ya ɗan motsa lips ɗinshi tare da cewa. "Kaɗan kenan in dai baki dena samin ido a jikina ba, Faɗuwa harda kareireyewa zakiyi in baki kiyayi yimin kallon ƙurillaba, na lura ku mutanen wancan dajin bakuda abinda kukafi so sama da kallon killataccen wuri na jikin mutun. Muddin baki dena satan kallon jikina ba, sai waɗannan mayatattun idanun naki sun tsiyaye kin huta ki zama makauniya babu ɗan jagora. Kiyi dai a hankali ko kya samu ki mutu da idonki,". Ya ƙarishe mgnar yana tafi kamar bashi yayi mgnar ba. Ita kuwa Shatu hannun tasa ta sharce hawayenta tare da rakashi da hararan kai mugune.
A falon ya samu su Ummi sunata dariya. Cikin sauri ya kalli su Jamil yace. "Kai wannan dariyar na menene, ku taso mu tafi masallaci". Cikin dariya Jamil yace. "Allah ko Hamma Jabeer ina zaton Hibba bata taɓa azumi ba sai bana. Ga yadda ta dawo wuni ɗaya, wai a haka kuma har ta fara lissafin wai yauwa yau mun kai ɗaya mun rage". Ɗan gajeren murmushi yayi tare da cewa. "Muhibbata tashi kije kiyi salla sai ki ɗan konta ki huta kafin a kira isha'i ko". Cikin sanyi tace. "To Hamma MJ". Jalal kuwa cikin yin ƙasa da murya yace. "Gobe ma zakiyi ne ko zaki huta". Cikin kwaɓe fuska tace. "Zanyi Umaymah tace, bana ko ɗaya in nasha sai na biya". Murmushi ya ɗan yi tare da cewa. "Ashe dai kin girma". Da sauri ta sunkuyar da kanta, shi kuwa yabi bayansu Jamil.
Duk sukayi gaba, Sheykh kuwa na bayansu. har yaje tsakiyar falon sai kuma ya ɗan tsaya jin Ummi na ce mishi. "Shetu fa". Cikin saurin tafiya masallacin yace. "Tana can ta faɗi wai ko ta karye ne naji tana cewa ban dai san mataba". Yana kaiwa nan ya fita, ita kuwa Ummi da sauri ta miƙe cikin zaro ido tace. "Karaya kuma? Innalillahi yaushe". Tayi maganar tana nufar falonshi, A bakin ƙofar shigowa sukayi kiciɓis da ita, da sauri ta tareta tare da tallabota, jin yadda jikinta ke rawane ta jawota suka fito falon cikin tausayawa tace. "Sannu Shatu". Cikin tausaya Hibba taketa jera mata sannu. Ajiyeta bisa kujera Ummi tayi tare da cewa. "Baki sha ruwan ba ma ko?". Kanta ta gyaɗa mata alamar eh. Hakane yasa Ummi tacewa Hibba ta ɗebo mata, abin shan ruwan a take kuwa ta kawo mata.
Bayan tasha ruwanne duk suka nufi cikin ɗaki dan yin salla.
Daga yin sallan magriba su Jamil suka dawo sukaci abinci kafin aka kira sallan isha'i, kana suka koma akayi sallan isha'i da asham sannan suka nufi harkokin su.
Shi kuwa Sheykh Jabeer daga Masallacin gidan Radio Ɓadamaya ya wuce, wurin yin shirin Fatawa.
Sai tara dai-dai ya dawo, gida. A kitchen ya jiyosu. Bisa alamu duk girkin abincin sahur sukeyi.
Shi kuwa bayan ya shiga, wonka yayi-yayi shirin bacci kana ya fito falonshi.
Soyayyan Arish da kwan ya ɗanci tare da tarfa ferfesun ya ɗan ci. masa biyu.
Jin cikinsa yayi tib ne, ya miƙe ya dawo falon. zama yayi bisa kujera yana kiran Umaymah, tana ɗagawa tace. "Jazlaan ina autata, ya azumin yau dai?". Gajeren murmushi yayi tare da cewa. "Umaymah autarki akwai raki, yau ita har ta fara lissafin an kai ɗaya saura 29/28". Dariya ta ɗanyi tare da cewa. "Kaɗan ma daga aikin Hibba". Sai kuma tace. "Ina ɗiyata kuma, ya azumin?." Kanshi ya ɗan jingina da kujera kana yace. "Alhamdulillah". Jin muryar Haroon na cewa. "Wai ɗazu ina ka shigane inata kiran wayar ka baka ɗagawa". Gyara zamanshi yayi tare da kurban coffee ɗinshi kana yace. "Na bar wayar a gida, da ɗaya na tafi na Fatawa".
"To ya Amarya?".
"Ban sani ba".
Cikin dariya Haroon yace. "Allah baka haƙuri".
Amsar wayar Umaymah tayi sukaci gaba da mgnar kan tafiyarsu Umrah. Daga bisani sukayi sallama, ya miƙa ya nufi ɗakin baccinsa.
A kitchen kuwa, bayan sun gama komai na sahur ne. Ummi ta cewa Shatu taje ta ɗauko Foodflaks ɗin dake falonshi.
To tace kana ta juya ta tafi. Koda ta shiga ɗan kalle-kalle tayi ganin baya nan, yasa ta harari falon ma gaba ɗayatare da cewa. "Mugu". Sannan ta ɗauki kwanukan ta fito.
Duk sauran abincin Saratu suka haɗawa ta kai musu ita da sauran hadiman. Wanke-wanke tayi kana ta tattare komai sannan ta wuce part ɗin su.
Su kuma ganin har goma tayi ne, yasa sukayiwa juna saida safe duk suka shiga.
Yauma kamar daren jiya haka sukayi.
Washe garima haka suke tafiyar da rayuwarsu. Cikin tsari da kuma samun damar hutu da ibada dan ribatar watan Ramadan ɗin.
A hankali aka fara nisawa cikin watan Ramadan, kwanaki suna ɗan mirginawa da kaɗan-kaɗan.
Yau wunin azumi na biyar kenan.
Da hantsi bayan sunyi walaha sunyi karatun al'ƙur'ani. Sanin yanzu Ummi na jin tabsir ɗin da yakeyi a masallacin Masarautar Joɗa ne yasa, Shatu tana gaisheta ta fito.
Hibba kuwa Side ɗin Aunty Juwairiyya ta nufa.
Ita kuwa Shatu falonta ta fito. Bisa kujera ta zauna, tare da kiran number Junaidu wanda Rafi'a ce, ta batashi data tare da bata haƙurin bazata samu zuwaba, sabida yayanta yazo sun koma jiharsu tare.
Ringing ɗaya ana biyu Junaidun ya amsa kiran ganin sabuwar number ne ya sashi cewa. "Ban gane wake mgna ba". Cikin jin daɗin yadda taji muryarshi ras alamun ya samu lfy tace. "Junaidu Adda Shatu ce fa". Da sauri ya tashi zaune bisa kekyawan gadon asibitin da yake kai tare da cewa. "Laah Adda Shatu kece? Wlh ban gane muryarki ba, Adda Shatu ya gida ya kwana biyu, ya kewan gida, ya lbrinsu Junainah". Cikin sauri tace. "Kai Junaidu duka wannan tambayoyin, ka bari mana in tambayeka ya jikinka, yasu Iri da Laure da Innaji da jikin". Murmushi yayi tare da cewa. "Alhamdulillah Adda Shatu duk jikinmu da sauƙin wasuma duk an sallamesu, yanzu nida Hamidu da Adamune kaɗai muka rage, kuma jikin da sauƙi sosai. Sai dan Baba Madune yana shan wuya, Satin daya wucema an sake yi mishi aiki". Cikin sanyi tace. "To yanzu su waye ke kula daku". Kanshi ya rausayar tare da cewa. "Uhumm mufa yanzu bamu da matsalar komai Adda Shatu kwantar da hankalinki, mun samu gata da kulawar wani babban likita mai mutunci. An canza mana asibiti ma an kawomu wani asibiti kamar na ƙasar woje". Cike da jin daɗi tace. "Alhamdulillah, dama dukkan tsanani yana tare da sauƙi".
Dogon numfashi Junaidu yaja tare da cewa. "Adda Shatu, ashe mun samu nasara, an kora mana mugun babarbarenen nan,". Uhum tace a taƙaice. Shi kuwa Junaidu cigaba da mgna yayi. "Adda Shatu Ya Salmanu ba lfy, yazo dubamu da jiki shima an kamashi gado. Shi yake cemin wai su Bappa sun tafi Lardi. Ayyah Adda Shatu yanzu sai yaushe zasu dawo? Kina mgna dasu ne?". Cikin dariya tace. "Faɗi gsky dai Junainah kake son tambaya dai. Junaidu. Suna lfy ina mgna dasu. Sai bayan salla zasu dawo." Da sauri yace. "Dan Allah Adda Shatu turo min number su". To tace tare da gyara konciyarta. Nan dai suka ɗan yi hira, kana sukayi sallama. Sannan ta tura mushi number su ɗin.
Suna gamawa ta kira Number Bappa. Bugu ɗaya ana biyu ya ɗaga. Cikin jin daɗin jin muryarshi tace. "Ina kwana Bappa na".
"Lfy lau Alhamdulillah Shatu ya Azumi, da baƙon wuri". Cikin sanyi tace. "Alhamdulillah, Bappa yaushe zaku dawo". Dariya yayi mai ɗan sauti kana yace. "Bayan salla". Cikin lumshe ido hawaye na zuba tace. "Bappa ina jin kewarku, bani da kowa nawa kusa dani. In na tuno su ya Giɗi hankalina na tashi Bappa inyi ta kuka babu mai sanin irin ciwon da nakeji a raina". Cikin sanyi yace. "Kwantar da hankalinki Shatu, su Ya Giɗi suna raye, sai dai suna cikin mawuyacin hali, suna buƙatar addu'o'in ki musamman a cikin wannan mata mai alfarma, na sanki bakya wasa da riƙo da ibada, amman ki ƙara kan yadda kike, in sha Allah wata rana zasu dawo garemu, cikin sauƙaƙƙiyar hanya, addu'a itace abinda suke so, shiyasa na gaya miki abinda Allah ya nuna min a mafarki a kansu". Cikin sassanyan kuka murya can ƙasa tace. "Zanyi Bappa zan ƙara zan dage, kuma zan roƙi a tayamu addu'o'in a masallatai da wurin tabsir." Cikin jin daɗi yace. "Yauwa Shatu na, ki kwantar da hankalinki, ki zauna lfy da mutanen da kike tare dasu, kiyiwa mijinki biyayya, kiyiwa mayanshi biyayya bana son musu in babba ya gaya miki abu matukar bai saɓawa shariyar musulunci ba." Cikin sanyi tace. "To". Da sauri yace mata ga Junainah". Cikin jin daɗi tace. "To a bata waya". Tsalle Junainah tayi tare da cewa. "Adda Shatu, kizo Lardi garin da daɗi kullum sai an gasa mana zabbi ko Tattabaru, insha nono da zuma inci naman insha zuma, inci su inabi sai na ƙoshi". Cikin so da ƙauna da shaƙuwar ta da yarinyar tace. "Allah sarki Junnu ke ko kewata bakiyi bako?". Dariya tayi tare da cewa. "Nayi kewarku mana harda Ya Junaidu ma nayi kewarshki". Murmushi tayi tare da cewa. "Na bashi number ku, zai kira ku gaisa". Tsalle tayi tare da nufar ɗakin Ummey. Ita kuwa Shatu cikin dariya tace. "Azuminki nawa". Da sauri tace. "Azumi na ɗaya ranan nayi rabi daga safe zuwa azahar jiya kuma na ƙarisa rabin daga azahar zuwa mangriba". Wani irin dariya ne ya rufe Shatu dariya takeyi sosai. Kewa da bege da son ƙanwar tata ya rufeta. Da Sauri ta tsagaita da dariyar jin Junainah na cewa. "Adda Shatu Bappa yayi aure an samo mana wata Inna mai kirki". Cikin mamaki tace. "Ke Junnu ƙarya ba kyau fa". Da sauri tace. "To ga Ummey ki tambayeta kiji". Ajiyan zuciya ta sauƙe jin muryar Ummey cikin sanyi da jin daɗi tace. "Ina kwana Ummey na ya gida, ya Junnuna nayi kewarku, Ummey wai da gaske Bappa yayi aure". Murmushi mai faɗi Ummey tayi tare da cewa. "To duk Alhamdulillah muna lfy eh Bappa yayi aure an bashi ƙanwar innarku, Indo kin santa ai ita take bin innarku, Bata taɓa haihuwa ba, to ashe mijinta ya rasu. Shine yanzu aka aura mishi ita. Kuma tanada hankali kamar innarku". Cikin sanyin jiki tace. "Eh na san Umma Indo tanada kirki, to Allah ya baku zaman lfy yasa kuyi irin zaman da kukayi da Inna". Amin Amin tace kana tai mata nasiha Sannan sukayi sallama.
Daga nan ta miƙa ta nufi ɗaki dan yin salla.
Ana idar da salla suka fito, kitchen suka nufa ita da Ummi da Saratu da tun ɗazu tana nan. Suka fara aikin buɗa baki sunayi suna kimtsa komai.
Kafin shida ta cikama sun gama komai.
Yanzu in sun zo buɗa baki ita da Ummi da Hibba tsakiyar falon suke dawowa. Jalal, Jamil, Imran, Sulaiman, kuma su zauna a dinning table.
Ya Jafar kuwa wani lokacin har can falon Sheykh zai wuce suyi buɗa baki a tare. Kana su tafi masallacin.
Haka dai komai yaketa wakana cikin aminci da tsari. A wurin al'ummar Annabi kowa ya nitsu ya maida hankali kan ibada domin neman rabauta.
Ƙarfe takwas dai-dai suka shiga kitchen dan yin aikin sahur. Cikin kula Ummi ta kalleta tare da cewa. "Ɗauko kwanu kan nashi". Kanta ta ɗan juyo ta kalli Ummi tare da cewa. "Ai bai dawo yaci ba ko?". Kai ta gyaɗa mata tare da cewa. "Baya cin ƙosai, kuma kinga doyan ma jiya baiciba, ya gaji dasu ne, ki ɗauko a juyewa su Saratu shi ki ɗan haɗa mishi wani abu kafin ya dawo". Cikin ɗan kauda kai tace. "Ummi ai ƙoshi yake shiyasa bazai ciba, a barshi kawai in yaji yunwar yacima wani bai saniba, ai yunwa ba Umaymah bace ko ke bare zaku lallaɓashi". Dariya Ummi tayi kana kuma ta haɗe fuska tare da cewa. "Je kiyi abinda nace ko". To tace ganin kamar ran Ummi ya ɓaci.
Bayan ta dawo da kwanukan ne, Suka bawa Saratu ta juye, kana ta harhaɗa wonke-wonken ta fara.
Ita kuwa Shatu cikin yin miƙa tace. "Ummi me zan dafa mishin?". Juyawa tayi tana haura wurin da Fridge yake tare da ce mata. "Duk abinda kika iya kika san ba mai nauyi bane".
Kanta ta gyaɗa tare da cewa. "To". Cikin ranta tace. "Bari inyi Special Arish, in yaga dama yaci in yaso ya bari, mutun sai zaɓe-zaɓe kamar mai ciki. Dankali ta ɗan ɗebo da Nama, kwai, tumatur, kabeji, Bama, maggi, tafarnuwa man gyaɗa, komai dai dai-dai misalin yadda zata buƙata duk ta ajiyesu kusa da ita.
Fere dankalin tayi ba tare da ta daddatsashi ba. Ta wonƙeshi fes kana tasa a ƴar tukunya tare da tarfa gishiri da ruwa dai-dai misali, sannan ta tafasashi. Kwan ta ɗauka ta fasa ta kaɗashi da kyau tare dasa yankekken al'basa da Curry da maggi da tafarnuwa ɗan kaɗan.
Ganin dankalin yayine ta juyeshi a ɗan kondo ta tsaneshi. Tare da ɗan barinshi yasha iska, kaɗan. Kana ta ɗaura Naman da maggi da gishiri da Curry da tafarnuwa da al'basa. bisa wata a ɗan tukunta. Sannan ɗaura man ta ɗauki dankalin ta tsomawa cikin kwan tana soyashi, saida ta gama ta ajiyeshi gefe. kafin nan naman kuma yayi lugub yayi laushin. saida ruwan ya kusa ƙarewa sai ta ƙara wata al'basar da tumatur suka nuna tare sannan ta kwashesu. Kabejin ta yayyanka ƙanana sannan ta ɗauki dafaffan kwai ta yayyanka shi da ɗan girma. Kana tasa Maggi da al'basa da Bama ta gauraya kana Ummi ta miƙo mata ɗan ƙaramin Foodflaks alamun ta amsa ta saka. Kanta ta jujjuya tare da cewa. "Bari in sa mishi a plate kawai tunda ya dawo". Da mamaki Ummi ta kalleta tare da cewa "Yaushe ya dawo?" Plate ta ɗauko tare da cewa. "Tun ɗazu". Da sauri ta sunkuyar da kanta ganin kamar Ummi na mata kallon Mamaki da tuhuma. Ita kuwa Ummi cikin Binta da ido tace, Ya akayi kika san ya dawo". Kai ta rausayar tare daci gaba da aikin kamar bataji Ummi ba. Plate ɗin ta ajiyeta, ta zuba Arish ɗin gefe kana tasa haɗin naman gefe, ta kuma zuba na Kabejin shima gefe. Ta shiryashi yayi kyau sosai. Ɗaya plate ɗin ta kife kanshi. Kana tasa spoon da Fork a cikin tray'n data ajiye plate ɗin. Ɗan madaidaicin flaks ɗin coffee ta ajiye gefe, kana tasa cup da tea spoon a ciki. Sannan turashi gefe. Zuwa lokacin kuma tuni Ummi da Saratu su gama aikin sahur ɗin har Saratu ta tafi. Sauran ta sako a wani plate ɗin tare da cewa Ummu gashi. Amsa Ummi tayi tare da cewa. "Ɗauki ki kai mishi to". To tace tare da ɗaukan tray'n ta fita.
A tsaye ta sameshi cikin wani tattausan jallabiya da alamun wonka ya fito, Sai wani irin masifeffen ƙamshi yakeyi.
Cikin nitsuwa ta wuce ta bayanshi, inda yake tsaye yana kunna Tv.
Bisa santa table ɗin glass mai garai-garai dake tsakiyar falon ta ajiye mishi. Kana ta juya a hankali ta fita.
Kai tsaye ɗakinta ta wuce, nan ta samu Hibba tuni tayi bacci. Wonka tayi da ruwan ɗumi tare da shafa mai kana tasa wata tattausar rigar bacci gajera iya karta guiwa. Hibaji ta zura a jikinta kana ta haura gado ta konta tare da jawo blanket ta duƙunƙune a ciki. Sabida ita bata son sanyi, shiyasa takesa ƙaton hijabi kana ta shiga borgo. Badon Hibba Bama dake masifar son sanyi da kashe AC'n zatayi.
Ƙarfe ɗaya dai-dai ta tashi bacci al'wala tayi kana tai ta nafila hakama Ummi. Sheykh Jabeer kuwa tuni ya tashi shima. Ya kira su Jalal ma a waya ya tashesu.
Ƙarfe huɗu da rabi dai-dai ta isa falonshi da tray'n abincin sahur ɗin shi. Ta ajiye ta juyo kenan shi kuma yana fitowa falonshi. Tazo tsakiyar falon kenan tana tafiyarta a hankali ba zato ba tsammani taji daram-dam ƙaran bindigar da kullum da asuba sai an saketa sau biyu, ta kuma kasa sabawa dashi bare ta daina tsoronshi. Wani irin tsalle da zabura tayi tare da ficewa a guje tana cewa. "Innalillahi wa innailaihi rajiun". Bayanta yabi da kallo tare da taɓe baki kana ya nufi Dinnin area.
Washe gari da safe yau Jumma'a kuma, yaune azumi na shida.