Kenza eBookz

Garkuwa complete novel - Chapter 42

Garkuwa complete novel - Chapter 42

Garkuwa complete novel Chapter 42: Garkuwa complete novel Chapter 42. Jikin gini ta jingina kanta tare da sakin shessheƙan kuka mai cike da azaba murya na…

4,491 words

Jikin gini ta jingina kanta tare da sakin shessheƙan kuka mai cike da azaba murya na rawa take cewa. "Innalillahi wa innailaihi rajiun. Hasbunallahuwani'imal wakil, la haulawala ƙauta illabillah. Wayyo Ummey na, Wayyo Bappa na, zan mutu baku sani ba." Wasu zafafan hawaye masu ɗumine suka zubowa Ummi saboda tsananin abin tausayi da ta gani a tare da yarinyar.

Hibba kuwa cikin kuka ta kira Umaymah tana kuka tace. "Umaymah Aunty Aysha tanata kuka tana cewa, zata mutu Ummeyn ta bata samiba, tunda aka shafa mata mgnin da sarkim baka ya bayar bata sake zamaba sai zirga-zirga takeyi". Cikin kiɗima Umaymah tace. "Innalillahi. Ina Ummin ku? bata waya". Cikin kuka tace. "Ummi ma kuka takeyi". A hargitse Umaymah tace. Ki bata waya nace dan ubanki". Da sauri ta miƙawa Ummi wayar. Cikin raunin murya Ummi tace. "Khadijah Aysha ba lfy, azaba yayi mata yawa fa. Ta ƙasa zaune ta kasa tsaye". Cikin sauri Umaymah tace. "Ina Jazlaan!?." Cikin sanyi tace ban san inda yajeba, amman tunda magriba bai dawoba." Da sauri Umaymah ta katse kiran Number Sheykh tayi ta kira. Sai dai duk layukanshi suna shiga baya ɗagawa.

Cikin tashin hankali ta kuma kiran. Lamiɗo tayi mishi bayani. Anan take Lamiɗo ya kira sarkin baka yace mishi, ga halin da ake ciki.

Sai ya bawa Lamiɗo tabbacin. Eh dama zaiyi iya zafin da anjima zai lafa.

To nan Lamiɗo ya kira Umaymah ya gaya mata. Ita kuma ta kira Ummi ta gaya mata yadda Lamiɗo ya gaya mata, ta ɗora da cewa. "In sha Allah gobe zan biyo jirgi inzo. Kuma ko ban samu jirgiba Haroon zai kawoni a mota, zanzo Ummin Jabeer hankalina yayi matuƙar tashi kan matsalar nan". Cikin kukan tausayi Aysha daketa ɗan bubbuga sawunta tana cewa. "Wahyyy wahhyy". Tace. "Eh gsky kam kizo, Umaymah ɗazu ko Hajia Mama da tazo saida tayi ta kukan tausayin Aysha". Katse kiran Umaymah tayi. Tare da wucewa turakan Abban Haroon nan ta gaya mishi abinda ke faruwa. Nan take ya bata izinin zuwa.

Sheykh Jabeer, kuwa sai ƙarfe sha ɗaya saura ya shigo gidan. Lokacin kuma Ummi ta rufe ƙofar ɗakin Aysha sabida hanyar fita take kamawa. To hakane yasa sam baiji motsin komaiba ya wuce Side ɗinsa. Wonka yayi kana yayi nafilfilinshi sannan ya kwanta baccin.

Ummi kuwa da Aysha kwanan tsaye sukayi. Aysha tana kuka tana zirgani. Sai can gabanin asuba irin iskar sanyin asuba ɗin nan ta fara kaɗawane wani sassanyan baccin azaba da wahala ya saceta. Hibba ma sai lokacin tayi bacci. Nanne Ummi ta samu ta koma ɗakinta tayi al'wala. Jin ana salla a masallacin ne yasa tace sai tayi salla taje ta tashesu kafin nan ta ɗanyi bacci kaɗan.

Bayan an idar da sallane. Ta miƙe a hankali cikin magagin baccin da batayi ba, ta nufi ɗakin Aysha. A hankali ta wuce bathroom. Abun buƙatar yin wonka duka ta motso matashi kusa, Hatta makilin saida ta matsa matashi bisa Brosh. Sannan ta fito, a ta sunkuyo kan Hibba tare da cewa. "Hibba! Hibba!! Muhibbat!!!". A hankali ta buɗe idonta. Cikin sanyi tace. "Je kiyi al'wala kizo kiyi salla sai ki maida baccin". Miƙa tayi a hankali tare da cewa. "Ummi nayi salla". Jin hakane Ummi ta gane kenan tana fashin salla.

Kai ta gyaɗa kana ta isa inda Aysha take. A hankali ta sunkuyo kanta tafin hannunta ta kife kan goshinta. pit-pit haka jijiyoyin kanta ke harbawa. A hankali tace. "Aysha! Aysha!! Cikin sanyi tayi ajiyan zuciya mai tsawo tare da buɗe kumburarrun idanunta a hankali. Cikin sanyi Ummi tace. "Ya jikin". A hankali tace. "Alhamdulillah". Cike da jin daɗi Ummi tace. "Masha Allah. Allah ya ƙara mana lfy, yanzu tashi kiyi wonka al'wala kiyi salla sai kizo kiyi baccin ko". A hankali tace. "To". Kana ta yunƙura zata tashi da sauri ta zaro idonta waje cikin tsoro take kallon hannun nata. Ummi ma cike da tsoro take kallon hannun. Ya kumbura yayi jazir. Cikin tsoro da jin raɗaɗi cikin fata da naman hannun tace. "Ummi kalli". Cikin danne fargabanta, dan kada ta razanata tace. "Yauwa ba komai kinga abin cikin ya fito ko. Tashi kije kiyi wanka kizo kiyi salla. Kisha tea kafin nan ki konta zuwa sha ɗaya dai sarkin baka zaizo shida Lamiɗo.

Cikin sanyi ta miƙe tana mai kallon hannun ta nufi Bathroom ɗin. Da ido Ummi ta rakata. Ganin ta maida ƙofar ta rufe ne yasa. Ummi juyawa durowarta ta buɗe wata doguwar riga ta ɗauko mata mai taushi hannunta guntu kuma tanada ɗan fadi da ɗan kwalinta. Wondon irin mai tsayuwa iya guiwa nar ta fito mata dashi sai bra turare ta fesa musu kana ta ajiye mata su kan gadon. Sannan ta fita ta nufi kitchen.

Ita kuwa Aysha, a hankali ta tsaɓule kayan jikinta, kana ta goge bakinta, fes sannan tayi wonka. Saidai duk abinda takeyi hannun na gefe sabida tana jin yana ɗan zuƙa da tauna. Wurin yin al'wala ne tayi ta zubda hawaye tana tausayawa masu hannu ɗaya.

Koda ta fito a bakin gado ta zauna. Wondon ta saka, sannan ta zura doguwar rigar dake mai faɗice. A hankali ta sa hannunta ta ɗaura ɗan kwalin a kanta a kaikaice. Bra ɗin kuma, medashi tayi cikin wodurob.

Da kyar tayi salla, tana idarwa. Ummi na shigowa da kofin tea a hannunta. Amsa tayi tasha. Ajiye kofin tayi tare da yin gyatsa a hankali tace. "Alhamdulillah". Sannu Ummi tace tare da kallon agogon dake jikin ginin ƙarfe Shida da minti arba'in. "To yanzu konta ni, bari in shiga kitchen inyi mana breakfast". Kai ta gyaɗa kana ta miƙe ta dawo, kan gadon ta kwanta.

Ita kuwa Ummi juyawa tayi ta nufi kitchen. Nan ta samu Saratu tazo fara aikin sukayi.

Ita kuwa Aysha, a hankali ta buɗe idonta data lumshe, sabida jiyo zafin da ta kwana dashi daren jiya, yana tasowa a hankali take jinshi. Ɗis-ɗas sai kuma ya ɗanyi shiru.

A hankali hasken rana ya bayyana a sararin samani. Wanda haka yayi dai-dai da bayyanan ciwon da taji jiya, ya mamaye hannunta da jikinta da zuciyarta. Wani irin yunƙuri tayi tare da tashi zaune. Cikin zafi tace. "Sheehhhhhhh Wayyo! wayyo!! wayyo!!! Ummi hannuna yana dawowa." Wani irin tsalle ta daka tare da miƙewa tsaye. Cikin tsananin zafin da taji ya mamaye illahirin jikinta ne yasata, sakin wani irin kuka mai baiyana azabar da takeji.

Kife kanta tayi a jikin wodurob, tana bubbugashi tare da cewa. "Innalillahi wa innailaihi rajiun."

Da sauri Ummi ta fito daga kitchen ta nufi falon Aysha, jin Hibba na rabka mata kira. Da sauri ta iso tare da cewa. "Suhanallali!. Aysha hannun ne kuma". Da sauri ta ɗago hannun ta nunama Ummi shi, gaba ɗaya hannun rawa yakeyi kar-kar tamkar mazari.

Wani irin juyi tayi da ƙarfi tare da kife kanta jikin gini. Tare da sakin shessheƙan kuka mai sauti, tana cewa. "Wayyo Allah na, Wayyo Ummey na. Wayyo Bappa na, zan mutu". Sai kuma ta kuma muƙewa cikin azabar rawan jiki da alamun a gigice take, cikin rawan murya tace. "Wayyo Allah na, Ummi ku kaini wurin Bappa na ku maidani gidanmu ku kaini wurin Ummey na". Ta ƙarishe mgnar tana wani irin tsastsafo zufa mai zafi. Safa da marwa ta farayi tare da cewa. Wayyoooooooo hannuna zai tsinƙe". Sai kuma ta juya a gigice cikin kiɗima da fitar hayyaci. Ta nufi falo, sabida yadda rana ke ƙara zafi, haka ciwon ke ƙara tunzura da ruruwa. Da gudu Ummi tabi bayanta tana cewa. "Shatu! Shatu!! Tsaya mana". Amman ina kafin ta fito falon tama ita kuma ta isa babban falon. Ganin hakane yasa Ummi da Hibba biyota a guje. Da sauri Ummi tasa hannu ta kamo hannun ta, mai lafiyar tana cewa. "Shatu ki nitsu ki tsaya ina zakije". Wani irin kuka ta saka mai cike da rauni hannunta ta fizge a hannun Ummi kana ta ɗaurashi tsakiyar kanta.

Dai-dai lokacin Sheykh ya turo ƙofar falon ya shigo. Jamil da Jalal na binshi a baya, Cikin al'ajabi ya zuba musu ido. Jalal da Jamil kuwa da sauri suka nufi inda suke. Shi kuwa shigowa cikin falon yayi ya ɗan tsaya gefen hanyar fita.

Ita kuwa Aysha aza hannunta tayi tsakiyar kanta, tare da kife kanta jikin gini tana bubbugawa tare da buga sawunta tana cewa. "Wayyoooooooo Allah na wayyoooooooo hannuna. Ummey zan mutu". Ta ƙarashe mgnar cikin rauni, abin gwanin ban tausayi. Hibba kam da Ummi tuni kuka sukeyi. Hakama sara. Ummi kuka takeyi tana cewa. "Sheykh zata fasa kantafa zata yiwa kanta illa". Wani irin zabura tayi ta juyo a firgice sabida wani irin masifeffen ciwo da suka da raɗaɗin da taji yana ratsa jiki da jinin da zuciyarta. Hannu tasa ta ture ɗan kwalin kanta, tare da yamutsa gashin kanta, fit ta fice cikin haiyacinta, wani irin juyawa da sassarfa tayi ta nufi hanyar fita tare da buɗe bakinta da ƙarfi zata kurma wani irin gigitaccen ihu.

Cikin wani irin zafin nama. Da tamkar gilmawar walƙiya Sheykh yasa hannunshi ya kamo hannunta na hagu. Tare da fizgo ta ya tsaida ita gabanshi. Da sauri yasa tafin hannunshi ya rufe bakinta data buɗe da niyar kurma ihun. Wani irin fizge-fizgen azaba ta farayi tana ƙoƙarin ƙwace kanta. Tuni su Ummi sun cika falon da kuka ganin tamkar ta zauce. Jalal da Jamil ma tuni idonsu ya cika da hawaye tab.

Ganin yadda take fizge-fizge ne. Yasashi janta ya nufi Side ɗinshi da ita, amman ina abin ya wuce zaton mai zato. Ganin yadda takeyine, yasa suna shiga cikin corridor'n. Ya ɗan juyo ya kalleta jin yadda taketa fizge hannunta. Idonshi ya tsura cikin nata, da sauri tayi ƙasa da kanta, tare da ƙara sakin kuka. Ganin haka ne ya cicciɓeta ya nufi bedroom ɗin shi kai tsaye. Yana shiga ya sauƙeta tare da maida ƙofar ya rufe ya jingina da ƙofar yana kallonta. Ita kuwa cikin kuka da fita haiyacinta. Ta nufi bakin ƙofar gefen ƙofar ta fara buga kanta. A hankali yasa hannunshin ya jawota gabanshi. Ido ya zuba mata yana kallon fuskarta data kumbura tayi ja dan yawan kuka, ga zufa daketa tsastsafo mata ga jikinta daketa karkarwa. Taune lip ɗin shi na ƙasa yayi tare dasa hannunshi kan ƙugunta ya zagayo ƙugunta da hannun nashi kana ya jata ya mannata da jikinshi tare da ruggumet....!

🤣🤣🤣🤣 Hahaha ko ya wannan salon jinyar zata kaya?

Ko meye Ba'ana zaiyi kan jinyar Shatu?.

To ina hayaƙin daya fita ya shiga a part's ɗin masarautar Joɗa?

Anya kuwa Sarkin bakan masarautar Joɗa ba Magauta yakewa aikiba?

Shin Ɗalha mai gyaran tayis ma zuwa yakewa aiki?

Wacce nasara ce kan shiga tsakanin Sheykh da Shatu a zaman jinyar?

To wai ina lbrin Boleru ne?

Shin waye ne ya jinyaci su Junaidu wanne asibiti aka medasu?

Jalal da Jamil kam menene sana'ar su ko aikinsu?

Meyasa Shatu ke zargin Hajia Mama da Aunty Juwairiyya?

Shin menene gsky abinda Lamiɗo da Galadima ke son ƙullawa?

Menene manufar Arɗo Bani nayin kalaman da suka tunzura Lamiɗo har akayi gasar Shaɗi kuma har akayi aure? Me suke son cimwa a masarautar Joɗa?

Su waye baiyannun da boyayyun magautan Sheykh da ahlinsa?

Me yasa Yah Jafar ke ji da Shatu?

Shin Jazrah da Batool zasu haƙura da burin ransu na son Sheykh?

Wai waye Sheykh ya gani a harami lokacin yin ɗawafin ban kwana? Waye ya kuma gani a Airport?

To wai ina lbrin su Yah Giɗi, Seyo, Gaini? Yayun Shatu? Ina suke suna raye ko sun mutu!

Waye Boleru?

By *GARKUWAR FULANI*

Hannunshi bisa suman kanta dake zube a kafaɗunta. Yana karatu cikin daddaɗan sautin shi mai ratsa jiki da zuciya. Yana mata tofi a hannun. Ita kuma tasa hannun hagun ta. Ta saƙalo wuyanshi ta cusa yatsunta cikin tattausan sumar dake kwance a ƙeyarshi tana maida numfashi a hankali.

Wasu irin abubuwa yakeji sunayi mishin yawo a jiki yana zaga jinin jikinshi gaba ɗaya. Yar-yar haka yakejin tsikar jikinshi na zubawa.

Hancinsa ya ɗan cutsa kan suman kanta, ƙamshin ya ɗan shaƙa tare da lumshe idonsa yana nazari maijin wani irin sassanyan abu a zuciyarshi.

A haka bacci ya ɗauke su gaba ɗayansu.

Ummi da Saratu ne suka shiga kitchen sukayi girki Umaymah kuma ta share mata ɗakinta fes. Kana ta kira Jadda ta sanar mishi duk abinda ke faruwa.

Yace zai turo mai magani.

Tana gama waya da Jadda ta kira ƙanwarta Aunty Hafsat itama ta gaya mata.

Nan dai ta ɗan kwanta itama tayi bacci.

Bappa kuwa ya kamo hanyar zuwa masarautar Joɗa. Hakama Barun ɗan aiken Ba'ana.

Sai sha biyu saura suka farka, a tare. A hankali ya buɗe kyawawan idanunshi, miƙa ya ɗanyi a hankali tare da yin addu'a. "Alhamdullazi ahyana, ba'adama a mautana wa ilaikal nushur". ajiyan zuciya mai sanyi ya sauƙe tare tsurawa kwanciyar da sukayi ido, cikin sanyi yace. "Wash tashi na gaji". Cikin jin kunya ta ƙara lumshe idonta tare da shaƙar ƙamshin jikinshi. dan batasan ya akayi ba kuma ta yayane tazo ɗakinshi har suka kwanta hakaba har sukayi bacci.

A hankali ta mirgina gefe ta kwanta. Shi kuwa ido ya zubawa hannun tare da ɗan tashi zaune hannunshi ya ɗan sa ya taɓa hannun nata idonshi ya zuba mata cikin nata a hankali yace. "Ban amince ba, Sarkin baka ya sake baki wani mgnin kisha ko ki shafaba. Bana so, tunda ya fara baki mgnin ciwon gaba yakeyi ko baya?". A hankali tace. "Gaba". Kanshi ya ɗan jingina da jikin kan gadon acikin lumshe ido yace. "Saida ya shafa miki hannun ya fara kumɓura, da ya kara ya sake ƙara kumɓura, dan haka bana so kada ki sake bashi jikinki ya shafa miki komai kinji ko?." Ya ƙarashe mgnar cikin sigar kula

Cikin sanyi tace to. Tana kallonshi ya sauƙa kan gadon. Shi kuwa Sheykh Bathroom ɗinsa ya shiga. Ya rage manyan kayan Kana ya rage dagashi sai boxes. cikin mamaki ya sunkuyo ya kalli boxes ɗin, jin damshi da wa kuma harbawa da Sheykh ɗinsa keyi. Baki ya kuma tsokewa tare da cewa. "Uhumm tooh abin har ya kai hakane?". A haka yayi wonka kana ya fito.

Bata ɗakin shiyasa yayi shirinsa yadda ya kamata.

Kana ya fito yayi break Sannan ya fito.

A falo ya samu Lamiɗo da Galadima da Sarkin bakan. Cikin tsuke fuskarsa ya nunawa sarkin baka hanyar fita tare da cewa. "Tashi kaje. Maganin ya isa haka". Da sauri Umaymah tace. "Gsky kam a barshi haka tunda anayi ba sauyi sai ci gama yakeyi". Murmushi Lamiɗo yayi kana yace. "To shike nan Khadijah." Sai kuma ya kalli Sarkin bakan yace. "Kada ka damu jeka kawai". To yace kana ya fita. Bayan ya fitane Lamiɗo yace. "To anyi maka yadda kakeso hankalinka ya kwanta. Amman munyi mgnar da mahaifinta yace min. Yana zuwa da wani mai mgnin".

Shi dai gyara al'kyabbar jikinshi yayi, kana ya sallamesu ya tafi. Daga bisani su Lamiɗo suka tafi, bayan sun tattauna da Umaymah.

Ranar ma dai haka Aysha ta wuni yanzu da sauƙin anjima sai a hankali.

Ƙarfe goma na dare Ummi ta taimaka mata tayi wonka. Kana tazo tasa wata doguwar ribar baccin.

Hijabi ta zura a kai kamar koda yaushe. Miƙewa Umaymah tayi tare da cewa. "Zo mu tafi". To kawai tace kana ta miƙe tabi bayanta.

Da mamaki take kallonta. Ganin sun nufi Side ɗinsa. A falo suka sameshi da jallabiya a jikinshi. Cikin mamaki yace. "Lfy kuwa Umaymah?".

Ajiye Aysha tayi bisa kujera kana ta juyo ta kalleshi tare da cewa. "Lfyar kenan! gata ku kwana ana kaga zahirin yadda take kwana".

Kafin yayi mgna ma ta juya ta fita, taja ƙofar ta baya gim ta rufesu.

A hankali ta jingina da kujera tana mgnar zuci. "Uhumm ni in Bappana yazoma gwara na bishi mun tafi tare. Ummey ma zatayi min komai da gatana ba sai anyi ta min hakaba".

Ta gefen ido ya kalleta dan bata san mgnar ta fito fili ba.

A hankali ta miƙe kan kujerar tare da lumshe idonta.

A hankali bacci ya saceta. Shi kuwa kallon da yakeyi tashar ƙasashen Larabawa, shi yaci gaba dayi.

Sai sha ɗaya da rabi ya miƙe yana kallonta murmushi ya ɗan yi kana ya juya ya shiga Bedroom.

Wonka yaje yayi kana ya dawo. Ya zura jallabiya kan boxes ɗin shi bnnarshi ya cikashi bam.

A hankali ya fito falon ganin tana baccine, yasa ya koma ɗaki ya kwanta.

Sha biyu nayi ciwo ya tasheta, Cikin bacci ta miƙe da ƙarfi tare da cewa. "Innalillahi, wahhhhhhyoohhhhhh Shyyyyyyt". Sai cikin kunnenshi yaji sautin. Shiru yayi yana kasa kunne can kuma sai yaji tana. Kuka tare da alamun tana zirga-zirga. A hankali ya miƙe kana ya fito. Ganin yadda ta ɗaura hannun a kaine yasashi. Jan ɗan gajeren tsaki jawota yayi suka nufi bedroom. Bisa gado suka zauna. Hannun shi yasa ya tallaɓe nata. Kana ya fara mata tofi.

Yanayi tana jin abin na lafawa, har saida yaga ta daina shishitan. Sannan yace. "Kwanta to". Cikin jin daɗi abin ya lafa ta kwanta. Shima konciyar yayi ya bata baya. Mitti biyar tsakani. Ta miƙa zaune da sauri tare da cewa. Wayyo Allah na yana dawowa." Fuskarshi ya kwaɓe kana shima ya tashi zaune. Hannun ya kuma jawowa. Ya fara yi mata tofi cikin 15 minutes sai gata tana lumshe idonta alamun bacci zatayi.

A hankali yace. "Kwanta to". Ba musu ta kwanta. Kamar da fari bayan 15 minutes ta kuma zabura ta tashi. Harda kuka wannan karon dan dare ya fara nisa ciwon zai fara tsananta. Da sauri ya miƙa zaune tare da jawota ta faɗa jikinshi sabida ganin alamun guduwa zatayi. Cikin sanyi yace. "Yau naga ta kaina yanzu bazaki barni inyi bacci ba, kiyi addu'a mana". Jin yadda take shirin ɓare baki zatayi kukane ya sashi. Fara yi mata tofin still kuwa abu kam ya lafa.

Umaymah kuwa da Ummi sun kasa bacci sai kasa kunne sukayi.

Ita jin shiru-shirun ba motsinsu ba kuka bata kuma dawobane yasa suka ɗan samu nitsuwa suka kwanta bacci.

Sheykh Jabeer kuwa ranar haka suka kwana ba bacci. Yayi mata tofi har yawun bakinshi ya kafe.

Sai asuba bacci ya saceta. Shi kuma kawai wonka yayi yazo ya fara nafilfilinshi. Ana kiran assalatu ya nufi masallaci. A falo ya samu Umaymah cikin kula ta kalleshi tare da cewa. "Jazlaan ya jikin nata ka samu kunyi bacci kuwa". Cikin sanyi yace. "Ni ai yau kamar jemage na kwana idona biyu bakina bai huta da tofiba. Yanzu dai tana bacci nayi ta tashin ta ma taƙi. ki leka ki tasheta." Yana faɗin haka ya fice.

Sanin bazai dawo da wuri bane yasa da aka idar da sallan. Umaymah taje ta tasheta. Suka dawo nan Side ɗinta. Sosai sukayi mamakin ganin hannin ya ɗan sace kaɗan kumburin ya ragu.

Da kyar aka taima mata tayi wonka tasha tea.

Shi kuwa Sheykh sai bakwai da rabi ya dawo. Yana dawowa ya konta bacci. Ita kuwa Aysha tuni rana na tashi ciwon na tashi. Gashi wani irin masifeffen yunwa takeji tamkar taci babu. cikin sauri ta miƙe, daga zaune da take da sauri Umaymah ma ta miƙe tare da cewa. "Bismillah, ya tashi ko?". Ganin ta nufi hanyar falonne tayi maza ta bita a baya tare da cewa. "Tsaya Aysha kada ki fita kinji ko?". Cikin muryar wahala tace. "Umaymah zanje wurin Yah Sheykh ne yayi min tofi, in yamin tofi yana rage ciwon sosai". Cikin sauƙe numfashin tace. "To jeki".

Da sauri taci gaba da tafiya. Tana yarfa hannunta na hagu. Kai tsaye bedroom ta wuce. Cikin borgo ta hangoshi konce. Da sauri ta iso. Hannu tasa ta saman borgon da niyar ta tasheshi. Dai-dai kan bnnarshi dake neman hudo borgon ta sauƙe hannunta tare da kamawa. Da nufin jan borgon.

Wani irin azabebben abune yajin ya zirta mishi daga tsakiyar ƙoƙon kanshi har zuwa kan babbar yatsar ƙafarshi, lokacin ɗaya yaji wani fitinenne abu ya diro mishi. Jin yadda ta cabki Sheykh ɗinshi Ido ya bude cikin magagin baccin da baƙon yanayin da yaji ne ya kwaɓe fuska kamar zaiyi kuka yace. "Wash Allah na ni Muhammad me kuma zan miki? Me kikeso in miki? Dan Allah ki barni inyi bacci". Yaye borgon tayi, tare da zama kusa dashi ta miƙo mishi hannun kusa da bakinshi tare da cewa. "Uhum yimin tofi". Cikin bacci ya zuba mata ido a hankali yace. "Ke ba baki iya addu'a bane da bazaki rinƙa yiwa kankiba". Cikin rawan murya tace. "Naka yafi, samar da sauƙin da wuri . Dan Allah Yah Sheykh kayi min ai addu'an miji yafi karɓuwa da wuri". Kanshi ya meda ya konta kana yace. "To kawo hannun fitinenneya kawai". Miƙo mishi hannun tayi shi kuma ya fara yi mata. Tofin Cikin ikon Allah kuma zogin ya fara lafawa. Da ya bari sai zogin ya dawo haka dai dole ya rasa baccin.

Kasan cewar yau jumma'a ne, sha biyu dai-dai. Yace. "To tafi wurin Umaymah tayi miki Ni zanyi shirin jumma'a."

To tace kana ta fita ta tafi.

Shi kuwa wonka ya shiga yayi kana ya fito ya kimtsa tsab cikin jallabiya Royal blue. Al'kyabbar kuwa ruwan madara.

Yayi kyau sosai yana fitowa su Jalal na isowa nan suka tafi masallacin.

Cikin ikon Allah kuma yau hannun da sauki kukan ba sosaiba kumburin ya ɗan ragu.

Yauma da dare can Umaymah ta kaita wurin shi suka kwana kamar jiya. Da gari ya waye kuma kasan cewar asabarce. Babu inda zaije nanma ta tsareshi ta hanashi bacci.

Yunwa da ciwo sunsa bata iya baccin.

Cikin sanyi tace. "Yunwa nakeji". A hatsale yace. "To cinyeni mana kawai ki huta". Cikin share hayenta tace. "Yimin tofin inje inci abinci". Haɗe fuskarshi yayi kana ya fara mata tofin. Hannu tasa ta damƙi cikinta Yau kwana biyar kenan rabonta da wani abu mai nauyi sai tea taketa sha kamar yar yaye. Tana ganin ya koma ya kwonta. Ta miƙe ta fito a falonshi ta samu Umaymah na jera mishi abinci a Dinning area. Tana ganin ta fito tace. "Aysha ya hannun?". A hankali ta juyo tare da cewa. "Umaymah yunwa nakeji, bazan iya shan tea ba na gaji dashi."

Da sauri tace. "To zo nan." Ta ƙarishe mgnar buɗe Foodflaks ɗin. jolof ɗin taliyace ce da kifi da jan nama, yaji kabeji da karas ga kuma dafeffen kwai an ɓare an jera a sama. Shi ta zuma mata a plate. Kana ta buɗe ɗaya kular gasasshen jan namane mai ɗan romo mai kauri. sai kuma biredi, da flaks ɗin shayi. Zuba mata gasashen naman tayi da romon mai ɗan yawa kana tace. Shigo kizo ki zauna kici.

Da sauri ta haɗiye yawun bakinta. Tare da shaƙan ƙamshin girkin. hannunta mai lfyar ta saka. Tsakankanin ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu nan da sukayiwa wurin labule. Ta buɗe hanya tasa kai ta shiga tana kare hannunta mai ciwon. Cikin rashin sa'a igiyoyine suka dauwo suka biyota suka bugi hannu mai ciwon. Cikin wani irin masifeffen zafi. Ta fara kada lafiyeyyen hannun tana cewa. "Innalillaheeeeeeeee, wayyo Allah na." Sai kuma ta fara zagayawa cikin Dinning area. _Duk wanda ya taɓa ciwon hannu ko yatsa shi kaɗai zai iya sanin halin da mutun ke shiga in ya fame._ Da sauri Umaymah ta ƙamato, ta riƙe tana jero mata sannu kana tana rabkawa Sheykh Jabeer kira. "Jazlaan! Jazlaan!! Jazlaan!!!". Da sauri ya buɗe idonshi tare da dirowa kan gado ya nufi hanyar fita jiyo yadda Umaymah ke auna mushi kira.

A falon ya tsaya tare da juyowa ya kalli Dinning area. Ganin yadda Umaymah take kiɗime mene yasashi nufarsu da sauri.

A can babban falon kuwa. Ummi da Hajia Mama da Aunty Juwairiyya dake falone suma suka shigo da sauri jin yadda Umaymah ke abkawa Sheykh kira da alamun a razane a kiɗime.

Suna shigowa falon suka nufi Dinning area ɗin inda suka hangisu.

Shi kuwa Sheykh yana isa yasa. Hannunshi ya jawo Dinning chair tare, da tallafawa Umaymah su ajiyeta bisa kujerar. Dan idonta duk ya tafi sama yana ƙafewa kamar zata suma. Ganin haka, Ummi ta iso da sauri hakama Hajia Mama da Aunty Juwairiyya wanda taketa maimaita innalillahi cikin ruɗanin, ganin halin da Shatu ke ciki.

Shiko Sheykh Ganin Umaymah da Ummu bazasu iya bane, yayi maza ya kamoto, cak ya ajiyeta kan kujerar. Umaymah kuwa Fridge ɗin shi ta buɗe goran ruwan zam-zam mai sanyi ta miƙo mishi. Ummi ce tasa hannunta ta amshi gororar sabida shi yasa hannunshi duka biyu ya tallabe kagaɗunta.

Ita kuwa Shatu cikin tsananin azabar da takeji idanunta ke tafiya can sama takejin muryoyinsu. Ido ta buɗe jiki na rawa, ta kalli Hajia Mama data matsota tare da cewa. "Sheykh matsa bani ita nan ta sumane". Ta ƙare mgnar tana ƙoƙarin kai hannunta bisa hannun Shatu mai ciwon. Hakane yasa cikin karkarwan jiki ta ɗora hannun nata saman kanta tare da cewa. "Bana so kada ki taɓani, ku fice min daga nan, cutar da kumkayi mijina na bayama bai ishekuba ne?". Cikin sauri ya ƙara sunkuyowa tare da cewa. "Keh ki nitsu ki tsaya ciwo yasa kinawa kowa kallon mugu, Hajia Mama ne zata cutar dani?". Sabida ya lura kamar bata haiyacinta. Ita kuwa Shatu ganin Hajia Mama na ƙara matsotsune yasa tayi maza tasa hannunta mai lafiyar ta ruggume ƙugunshi cikin rauni da rawan muryar azaba tace. "Shi mugu idan ya cika mugu ai baya bayyanawa duk mugun da ya baiyana kanshi bai cika muguba. Sai kuma ta fara jujjuya kanta. Da sauri ya mshi goran zam-zam ɗin da Ummi ke miƙa mishi, tare da tareta ta gaba ganin alamun zata faɗi. Taretan da yayine yasa ta afka kan cinyoyinshi kasan cewar a tsaye yake ita a zaune. Buɗe gorar yayi ya sa a hannunshi ya watsa matashi a fuska. Da ƙarfi taja numfashin, tare da meda idonta ta lumshe. diba yayi ya kuma watsa mata. A karo na uku ne daya watsa matsamata ne tasa hannunta na hagu ta zagayo ƙugunshi da ƙarfi. Sabida ruwan zam-zam ɗin. Daya taɓa hannu mai ciwon sai taji. Wani irin sanyi ya ratsa hannun.

Shiru yayi yana tsaye a gabanta. Tana ruggume dashi. Tana sauƙe numfashi murya can ƙasa tace. "Umaymah zanci abinci". Sunkuyowa yayi cike da kunyar ganin yadda ta ruggumeshi. Ummi da Hajia Mama da Aunty Juwairiyya kusa kasake sukayi suna kallonsu. Shi kuwa janye jikinshi yayi. kana ya koma gefen Fridge ɗinsa. ita kuma Umaymah hamdala tayi tare da cewa. "To". Matso da plate duka biyu tayi gabanta. Kana ta jawo ɗaya kujerar tace. "Jazlaan bata abinci taci. Bari inje in kawo mata kunu. Tunda tace bata son tea". Jin haka su Ummi sukayi gaba, ita kuma ta bisu a baya. Da sauri yace. "In bata kuma Umaymah". Cikin faɗa tace. "Yes! Sabida bata iya kai abinci bakinta da hannun hagu. Kuma baka yarda da a baka bayi a Side ɗinkaba bare su bata taci. Dan haka sai ka batan". Tana faɗin haka ta fita.

Ita kuwa Aysha cikin jin yunwar na neman illatamata rayuwa. tasa hannun hagun ta ɗauki Fork ɗin. tsakiyar plate ɗin ta sokashi kana ta murɗa. Sannan ta ɗago hannun a kaikace kafin ta isar dashi bakinta baifi tsalli shida ya rageba. Gashi har jikin rigarta duk ya zube mata.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull