Kenza eBookz

Garkuwa complete novel - Chapter 53

Garkuwa complete novel - Chapter 53

Garkuwa complete novel Chapter 53: Garkuwa complete novel Chapter 53. Haƙƙoƙin mata a kan mijinta suna da tarin yawa. Kuma ya zamo wajibi a kan mai gida ya…

3,800 words

Haƙƙoƙin mata a kan mijinta suna da tarin yawa. Kuma ya zamo wajibi a kan mai gida ya tsareshi dai-dai gwargwadon hali, kuma wannan haƙƙoƙin Allah da Manzonsa sun tabbatar dashi, ga faɗin Allah madaukakin sarki akan haka inda yayi mgna cikin Suratul Baƙara aya ta 228:- (WALAHUNNA MISLULAZII ALAIHINNA BIL MA'ARUF WA LIRRIJALI ALAIHINNA DARAJAT) Mata sunada haƙki a kan mazansu kamar yadda aka sani. Sannan maza suna da wata daraja akan mata. Haƙƙokin mace a kan mijin ta, suna da yawa amman ga wasu daga cikinsu.

(1) Wurin zama ga matar aure wajibi ne a kan mijinta. Miji zai tanadi wurin zaman matarsa gwargwadon ikonsa da samunsa kamar yadda Allah maɗaukakin sarki ya faɗa a cikin Suratul Ɗalak aya ta 6:- (ASKINU HUNNA MIN HAISU SAKANTUM MIN WUJIDIKIM WALA. TUDAARUHUNNA LITUDHAYYIKUM ALAIHIN) Ku zaunar da matanku inda kuke zaune wato gidajenku. Ba mummunan wurin zamaba kada ku cutar dasu don ƙuntata musu.

(2) CIYARWA. Ciyarwa yana daga cikin abubuwan dake wajabta kan miji wato wajibi ne miji ya ciyar da matarsa, kuma ciyarwar zai yishi ne gwargwadon ikonsa kamar yadda Allah maɗaukakin sarki yace a cikin Suratul ɗalak aya ta (7). (LIYUN FIƘ ZUU SA'ATIH MIN SA'ATIH, WA MAN ƘUDIRA ALAIKU RIZKUHU FALYUNFIƘ MIMMA AATAHULLAH LAA YU KALLIFULLAHU NAFSAN ILLA MAA AATAHAA SAYAJA ALULLUHU BA'ADA USRIY YUSRAA). Ma'ana. Mawadaci sai ya ciyar da abinda Allah ya bashi na wadata, shi kuma wanda Allah ya ƙaranta masa arziƙinsa to sai ya ciyar daga abinda Allah ya bashi. Domin Allah baya ɗorawa bawa abinda bazai iyaba kuma ka sani Allah zai baka wadata bayan ƙuncin da ka shiga. Dangane da hadisin Annabi (A.S.W) yace a hadisin da a ka ruwaito daga mu'awiyya Bin Haidatu Allah ya ƙara masa yarda yace: Sai muka tambayi Manzon Allah (S.A.W) shin menene haƙƙin mata akan ɗaya daga cikinmu?. Annabi (S.A.W) ya ce. "Idan kaci abinci to ka ciyar da ita, idan ka ɗinka sutura to itama ka ɗin ka mata, sannan kuma in tayi maka laifi zaka bugeta, to kada ka bugeta a fuskarta kada ka munanata, idan zaka ƙaurace mata to kada ka ƙaurace mata a woje sai dai a ɗaki." (3) Kyakkyawan mu'amala. Shi mu'amala mai kyau babban abune ga ma'aurata. Especially shi miji, yana daga cikin haƙƙin mace akan mijinta, yayi mu'amala mai kyau da sakin fuska a tsakaninsu, raha da barkwanci ta yadda zasu shaƙu da junansu. Lallai waɗannan muhimman abubuwane da miji zai kiyaye su, kuma wajibi ne miji ya yawaita nasihi da wa'azi ga matarsa a kan harkar addini da sauran al'amuran yau da kullum sai dai a kula wurin nasihar da wa'azin kada ka tsananta kuma kada ka sake kwarai sabida sani yadda mata suke murɗaɗɗune sai anyi da lura. Duba da wani hadisin da Annabi (S.A.W) yana cewa a cikin hadisin da aka samo daga Abu Huraira inda yake cewa. Manzon Allah (S.A.W) yace: "Mafi cikar mumini a wajen imani shine wanda ya fiku kekkyawan ɗabi'a kuma zaɓaɓɓe a cikinsu shine wanda yafi Kyakkyawar mu'amala da iyalinsa. A wani hadisin kuma yace. Lallai ku sani cewa an halicci ƴa mace da ƙashin haƙarƙari ne bazata taɓa miƙewa gareka ba, wato ka sameta sak ba matsala, wannan kam bazai taɓa samuwaba in ka samu jin daɗinta to zaka samu jin daɗin ta ne a ƙarƙashin yadda take, (kuma ka sani in ka nemi miƙar da ita to tabbas zata karye. Karyewarta kuwa shine SAKINTA saboda haka sai kuyi taka tsan-tsan acikin lamuran."

Gyara zamanshi yayi da kyau, kana yasa hannunshi ya gyara gilashin fuskarshi da kyau, Sannan ya sa hannunshi zai ɗauki goran ruwan dake gabanshi. Da sauri ɗan agajin dake bayanshi ya ɗauki gorar kana ya buɗe ya tsiyaya mishi sassayan ruwan cikin kofi, kana ya miƙa mishi sannan ya koma inda yake ya tsaya.

Amsa yayi yasha ruwan sosai kana ya ajiye cup ɗin. Sunkuyar da kanshi yayi sosai sannan yasa hannunshi ya gyara hiraminshi ya rufe gefe da gefen fuskarshi.

Al'ummar jama'ar dake wurin kuwa kan sun nitsu sunyi shiru maza da mata manya da yara. Kab an zuba mishi idanu alamun ana dakonshi yaci gaba. Domin sosai walimar tayi armishi sabida dace da tayi da fasihin malami. Shiru kakeji sai sauti A\C dana numfarfashi. Aysha kuwa haka nan take jin wani irin mashahurin daɗi. Gaba ɗaya tsikar jikinta tashi takeyi, tana jin Allah yayi mata babban rahama da ni'imar duniya da bata Sheykh Jabeer a matsayin Garkuwan ta mijinta.

Da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi lokacin da yaji yace.

(4) SADUWA DA ITA.

Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300. 0005388578 Jaiz Bank Aisha Aliyu Garkuwa. Ta nan zaki turo kuɗin, sai screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta whatsapp 09097853276.

By *GARKUWAR FULANI*

Littafin nan na kuɗine, akwai Normal group 300 a wata biyu za'a kare Part 1 and 2, kiyi transfer'n dari uku ta asusuna na Jaiz bank. 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta whatsapp 09097853276. In Kuma special Group kikeso wanda a wata ɗaya za'a gama Part one, two. 1k zaki turo ta ac no ɗin nan 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number da nake whatsapp dashi 09097853276.

Akwai kayan gyaɗa na amareni uwar gidaye sitin hawa-hawa ne, akwai na dedai talaka akwai na masu hannu da shuni, in kina buƙatar saya kimin mgn ta whatsapp 09097853276.

Idonshi ya ɗan lumshe kana ya ɗanyi ƙasa da kanshi cikin nitsuwa yaci gaba da cewa. "Anan ana son miji ya dinga yin jima'i (Saduwa) da matarsa ko da sau ɗaya ne a cikin ko wanne tsarki ta, na Al'ada amman ƙaranci kada ya wuce wata huɗu ba tare da ya sadu da itaba kamar yadda wasu malamai suka faɗa, in bazai iya biya mata buƙatarta ba, kuma wannan za'a kauwacewa al'amarin jima'i kamar yadda al'ƙur'ani mai girma yace. (Allah yayi mgna game da mazajen da suke barin matansu basu kula su har tsawon wata huɗu kai harma suna ƙarawa da rantsuwa bazasu tara (Sadu) da suba, to idan daga baya sun dawo ga iyalan nan to shike nan Allah mai gafara ne mai jinƙai. Saboda haka idan muka dubi wannan ayar zamu fahimci cewa, idan miji ya bar matarsa tsawon wata huɗu bai sadu da itaba haka nan kawai ba tare da wani kyakkyawan dalili ba, to ya cuceta, kuma ana iya raba auren, Allah ya kiyaye.

Sai na (5) kiyaye mutuncinta kishi a kanta yana daga cikin mu'amala mai kyau tsakanin miji da mata ya zama miji ya kiyaye mutuncin matarsa da yin kishi a kanta, saboda haka wajibi ne ga miji yayi kishin matarsa ya kareta daga dukkan abinda zai taɓa mutuncinta da martabarta da dukkan abinda yayi kama da hakan domin mumini mai kishin gidansa ne, kamar yadda. Dabarani ya ruwaito daga Ammar Ɗan Yasir Allah ya ƙara musu yarda, cewa Manzon Allah (S.A.W) yace. Mutane uku bazasu shiga aljanna ba, 1 wanda baya kishin iyalansa 2 macen da take shigar maza, 3 wanda bai damuwa akan kowa da kowa ya shiga wajen iyalinsa. Sai Sahabbai suka tambayi Annabi (S.A.W) suka ce,. Ya manzon Allah shin dai bugegge sun san shi, to amman (Addayyus) wato mara kishi iyalinsa shine bamu sanshi ba. Sai Manzon Allah (S.A.W) yace musu. Shine wanda bai damuwa kowa da kowa kare da doki su shiga gidansa wato mutumin banza da wofi idan sun shiga gidansa baya damuwa. Shi wannan hadisin ya nuna mana cewa dole mu tsare mutuncin matanmu. Wannan kenan sune kaɗan daga haƙin mata akan mijinta.

Sai kuma haƙƙoƙin miji akan matarsa. (1) yin ɗa'a ga mijinta domin Allah ya faɗi a Suratul Baƙara aya ta 228. ( WA LIRRIJALI ALAIHINNA DARAJAH) Su maza sunada wata daraja a kan matansu. (2) Kula da dukiyarsa wajibi ne a kanki haƙƙine wanda ya zama dole mata su kiyayeshi Dole mace ta kula da dukiyar mijinta fiye da yadda shi zai kula dashi. Kamar yadda Allah Mai girma da ɗaukaka ya faɗa a Suratul Nisa'i aya ta 34. (FASSALIHATU ƘAANITAATUN HAAFIZAATUN LILGAIBI BIMA HAFIZALLAH) Allah ya ambaci salihai mata masu ɗa'a ga mazajensu masu tsoron Allah masu kiyaye abinda ke ɓoye na al'amuran mazan aurensu sobada Allah yace su kiyayeshi, kiyayewar kuma ta haɗa da tsare mutuncin kansu dana mijinsu ko yana nan ko baya nan. (3) Yiwa miji hidimar cikin gida kamarsu girki shara kula da yara da dai sauransu duk aikin macene. Kamar yadda Allah maɗaukakin sarki yace. (WALAHUNNA MISLULLAZZI ALAYHINNA BIL MA'ARUF) Mata suna da haƙƙi a kan mazansu kamar yadda suma maza sukeda haƙƙin a kan matansu. (4) ikon canza mata wurin zama daga wannan garin zuwa wancan gari. Kamar yana aiki a jihar Ɓadamaya sai aka canza masa wurin aiki zuwa Tsinako to yana ikon ɗaukarta daga can zuwa nan. Domin musulunci ya bashi dama kamar yadda Allah maɗaukakin sarki yace. (ASKINU HUNNA MIN HAISU SAKANTUM MIN WUJDIKUM WALA TU DARRUWHUNNA LITUDAYYIƘUN ALAIYHIN) ku zauna dasu inda kuke kada ku cucesu ku ƙuntata musu wajen zama. Idan muka dubi wannan ayar tana gargaɗin mazaje ne akan cewa kada ka sauya mata garin zuwa wani garin ya zama cutarwa a gareta. In taga cutarwa ne nan zata iya ƙin zuwa in ya matsa ta gayawa waliyansu. (5) kada mace ta shigo da wani mutun gidansu sai da izinin mijinta, domin wannan haƙƙine kuma damarsa ce. Numfashi ya sauƙe tare da kallon taron mazan kana yaci gaba da cewa. "A gurguje. (6) Neman izinin miji dan yin azumi. Baya halasta ga mace tayi azumi in dai na nafila ne sai tare da izinin mijinta matukar mijinnan yana gida tare da ita. Duba haɗisin daya gabata na haƙƙin maigida saboda haka ya zama dole mace ta nemi izinin mijinta kafin tayi azumi nafila amman banda na farillah". Haroon ne yayi wani irin murmushin jin daɗi kana ya kalli Jannart cikin raɗa yace. "Kinaji kina ɗauka kina fahimta ko?". Longoɓar da kai tayi.

Umaymah kuwa sai murmushi takeyi tana ƙara godewa Allah da samun Sheykh a ahlinsu. Mamma ma sai murmushi takeyi.

Jamil Jalal Azeez da Sadiq da Imran ne suka ɗan haɗe kansu suna ƴar hira ƙasa-ƙasa.

Da sauri suka ɗago kansu jin muryar Sheykh yana cewa. "Jamil ku fita waje kuna toshewa jama'a kunne". Cike da mamaki suka miƙe suna kallonshi suna al'ajabin ya akayi ya gane su kuma har yaji muryarsu. "Ku fita". Suka sake jin muryarsa, cikin tuttura baki suka fita. Aysha kuwa tafin hannunta tasa ta tallabe haɓarta, tare da zuba mishi ido cikin wani abinda bata san sahihancinsa ba, take kallon tattausan lips ɗinshi suna motsawa yana mai ci gaba da cewa.

Kanshi ya sunkuyar sosai, babu mai iya ganin kwayar idanunshi cikin tarin al'kunya yace.

"Haƙƙin jima'i haƙƙine wanda yake tsakanin miji da mata. Amman ƙarfin haƙƙin yafine gashi mijin, shi yake da haƙƙi mafi girma. Kuma shi wannan jima'in yana daga cikin manufofin aure, domin shi aure shi yake tabbatar da mutane su wanzu, su tabbata akan ma'aunin mutane su ba nau'in dabbobi ba. Domin shi dabba duk lokacin daya buƙaci biyan buƙata yin jima'i zai tare dabba mace ƴar uwarsa ne a hanya nan take ya biya buƙatarsa ya rabu da ita, kamar yadda muke gani a tsakaninsu yana faruwa. Shiyasa duk mazinaci bashi da banbanci da Dabba!. Jima'i babban al'amari ne cikin auratayya, domin biyawa kowa buƙatar sa, kana jima'i wata iriyar sutura ce wadda ma'aurata suke suturce junansu, kamar dai yadda Allah maɗaukakin sarki yace a cikin suratul baƙara aya ta 187:- (UHILLA LAKUM LAILATASSIYAMIRRAFASA ILAA NISA'A IKUM HUNNA LIBAASULLAKUM WA'ANTUM LIBAASULLAKUM) A halasta muku matanyenku kuyi jima'i dasu a dararen Azumi, domin su mata sutura ne a gareku, kuma suturce a garesu." Ɗan ɗago kwayar idanunshi yayi ya fuskanceta Aysha, kollon kwayar idanunta data zuba mishi yayi na ƴan wasu daƙiƙu kana yaci gaba da cewa. "A wata ayar Allah maɗaukakin sarki ya siffanta mata da cewa gonakine a garemu maza, ku zowa gonakinku a duk lokacin da kuke so. Ayar itace. (NISA'UKUM HARSULLAKUM FA'ATUN HARSUKUM ANNAA SHI'ITUM) Matanku gonakinku ne ku zowa gonakinku a duk sanda kuke so". Haroon ne ya ɗan matse hannun Jannart dake cikin nashi kana ya ɗan juyo ya kalleta. yana wani ja'irim murmushi.

Shi kuwa Sheykh gyara zamanshi yayi tare da ƙanƙance kwayar idanunshi ya watsasu cikin manyan idanun Aysha ya tsareta dasu. harshenshi ya ɗan turo woje ya ɗan lasi lips ɗin shi kana yaci gaba da cewa. "Kamar yadda aka faɗa shi jima'i Saduwa haƙkine ga kowa wanne ɗaya daga cikin mauratan, hakan ya sanya ya zamo wajibi ga mace lallai ne dole ta bada haɗin kai a duk lokacin da mijinta ya nemeta da jima'i matuƙar dai bata cikin haila ko jinin biƙi ko kuma da rana cikin watan Ramadan. Ko tana cikin wani uzurin wanda zai iya hanata biya mishi buƙatar sa. Uzurin kuma ya zama na Shari'a yardajjen kamar rashin lafiya mai tsanani. To in ba waɗannan uzurorinba babu wani dalilin da zai sa mace taƙi bada haɗin kai ta biyawa mijinta buƙatar sa. In kuwa taƙi bashi haɗin kai da son ranta, to zata haɗu da tsinuwar mala'ikun Allah kamar yadda yazo a hadisin Bukhari da Muslim wanda ke cikin. Minhaju Muslim shafi na 380 sun ruwaito daga Annabi (S.A.W) yace. ( Idan miji ya kira matarsa zuwa shimfiɗarsa don yin buƙatar sa, Saduwa da ita, sai taƙi yarda ta bashi haɗin kai, sakamakon hakan sai mijin ya kwana cikin fushi da baƙin cikin hakan da tayi mishi. To Mala'ikun Allah zasuyi ta sinemata har sai gari ya waye.

Lallai ne mace ta sani mijinta yana da ikon biya buƙatarsa da ita a duk lokacin da yaso hakan."

Juyowa yayi ya fuskanci mazan da kyau kana kwayar idanunshi a sunkuye yace. "Haƙƙin mace kuwa a kan jima'i malamai sun karkasu kan wannan hukuncin kamar haka. 1 Mafiya yawan malamai suna ganin wajibi ne ga miji ya biyawa matarsa buƙatar ta jima'i a duk sanda ta nema. Domin yin hakan yana cikin kekkyawan zamantakewa kamar yadda Allah maɗaukakin sarki ya yi umarni dashi inda yace. (WA'ASHIRU HUNNA BIL MA'ARUF) Kuyi musu kekkyawan zamantakewa babu cuta ba cutarwa. 2 Su kuma shafi'iyyah suna ganin cewa shi jima'i haƙƙin mijine sabado haka baza'a tilasta shi yayi dole ba. 3 Hanabila kuwa suna ganin cewa. Baya halasta miji yaƙi yin jima'i da matarsa fiye da wata huɗu. Saboda haka wajibi ne miji ya sadu da matarsa cikin ko wanne wata huɗu. 4 Ibn Hamza yana cewa wajibi ne miji ya sadu da matarsa cikin ko wanne tsarkin hailan da tayi. Matuƙar yanada halin yin hakan, domin yin hakan shine mafi ƙarancin tarawa da zaiyi da ita. Amman a karan kaina a fahimtata ni dai Muhammad nafi nitsuwa dana forkon nan wanda mafiya yawan malamai suka yarda dashi matuƙar yana da ikon yin haka, ya biya mata buƙatarta duk sanda ta nemeshi, domin yin hakan shine zai kiyaye mutuncinta da addininta kamar yadda Musulunci ya umarceshi da ya yi". Numfashi ya ɗan fesar kana cikin nitsuwa yace. "A gaggauce ga laduban jima'i. Wasu abubune wanda ake buƙatar aikatasu lokacin da mata da miji sukayi nufin saduwa. Jima'i da junansu, idan ka aikata waɗannan abubuwan zaka ƙara samun lada a wannan ibadar saduwar da zakiyi, amman kuma in baka aikata ba, bakayi zunubi ba,sai dai kayi asarar wannan ladan wanda aka tanada domin waɗanda suka aikata waɗannan abubuwan wojen koyi da sunnar Annabi Sallallahu alaihi Wasallama. Domin su waɗannan laduban Sunnah ce da. Masu yawa amman ga kaɗan daga ciki: (1) Addu'a ana son miji idan zai sadu da matarsa yace. "BISMILLAH ya kuma yi addu'a to idan yayi hakan yayi abinda ake so aiki da ladabi kamar yadda yazo a Hadisin Bukhari da Muslim, Tirmiziy Ibn Majah, Abu Dauda suka ruwaito Hadisin Abdullahi ɗan Abbas cewa. Manzon Allah (S.A.W) yace. Da ace ko wanne ɗayanku lokacin da zai zowa matarsa yin jima'i zai ce. (BISMILLAH ALLAHUMMA JANNIBAL SHAIƊAN WA JANNIBAL SHAIƊANA MARAZAƘTUNA) to idan Allah ya ƙaddara samun ɗa a wannan saduwar to shaiɗan bazai cutar da wannan abinda za'a haifaba har abada. Saboda haka ya kamata duk mijin da zai sadu da matarsa ya kiyaye wannan, in kuma kinga mijinki shagalellene ke mace kike tunasar dashi. Dan samuwa ya'yan da zaku haifa kariyar Allah. 2 Wasanni kafin jima'i. Yin wasanni gabanin jima'i domin samun cikekken jin daɗi, kamar yadda aka ruwaito. Daga Annabi (S.A.W). "Kada ku aukawa iyalanku da gaggawa, har sai wani abu na sha'awa ya fito musu, irin wanda ya fito maka, domin kada ka rigata yin inzali fidda manniyi. Sai wani daga cikin Sahabbai sukayi tammabaya. "Shin wannan jin daɗin mata daga gareni ne? Ma'ana Ni zan sa taji daɗin. Sai yace, Na'am zaka sata taji daɗi ne ta hanyar sumbatarta haɗa baki da baki ruggumarta da abinda yayi kama da haka. Idan kaga wani abu ya zo mata, na ruwan maniyyi irin wanda yazo maka, daga nan sai ka sadu da ita. 3 Tanadar kyalle domin goge maniyyi. 4 Kada ayi jima'i tsirara. 5 Yin al'wala idan zaka sake mai-maita na biyu ko na uku, ko fiye da haka."

Ɗan tsagaitawa yayi ya kalli hadimai mata dake ta jere ababen ci da sha akan ko wanne table yawan adadin mutanen dake zagaye da table ɗin yawan abubuwan da ake ajiyewa. Idonshi ya ɗan juyo ya kalli gefen maza. Nanma hadimai mazane keta jera abubuwan cin da na sha, kana. Ta gaba gaba kuma wurin VIP sukuma Jamil, Jalal, Azeez Sadiq sune suke ta jerawa.

Kanshi ya gyaɗa alamun gamsuwa da tsarin domin anyi komai cikin tsari da wadata da karamci da girma cikin nitsuwa mutane suka fara ci da sha.

Gyaran murya ya ɗan yi kana yace. "Abubuwan da aka haramta game da jima'i. 1 Jinin haila, da biƙi 2 jima'i ta dubura 3 Bayyana sirrin jima'i." Murmushi ya ɗan yi ganin mafi akasarin mutane sun fara hidimar ɗa'amu. Ajiyar zuciya ya sauƙe ganin tuni har goma na dare ta gota, babu wanda ya Ankara, alamun tabsirin walimar yayi zaƙi kenan. Numfashi ya sauƙe kana ya ɗaga hannun alamar addu'an rufe taron yace. "Subahanakallamumma wabi hamdika asshahadu alla'illaha illa anta astagafirukka wa'atubu illaik Allahumma salli ala muhammad wa ala ali Muhammad kama sallaita ala ibrahima wa barik ala muhammad wa ala ali Muhammad kama barakkata ala Ibrahim wa ala ali Ibrahim inna ka hamidul majid. Ya Allah ka meda kowa gidansa lfy yan nesa dana kusa. Allah ka bawa ma'aurata zaman lfy ka sanya al'khairi a rayuwarmu, ka azurta dukkan ɗan uwa Musulmi da ƴaƴa na gari." "Ameeeeeeen". Haka hall ɗin ya ɗauka.

Hadimai kuwa tuni sunci gaba da raba jakukkunan kyautar walima. Gefen maza, Sallaya da al'ƙur'ani da carbi da jallabiya da turare akasa a cikin ko wacce jaka da take ɗauke da hoton Haroon, Sheykh, Jannart Aysha. Turaren irin mai tsadar gaskenan ne. Hakama jallabiyar, ko dan sanin taron na manya ne.

A gefen mata kuwa, Shima sallaya ce da ƙur'ani da carbi da turare da manya-manya hijabai bibbiyu cikin ko wacce jaka. Haka akayi ta rabawa.

Cike da Mamaki Umaymah ta kalli Hibba da Azeema da Safiyyah da Jazrah da suke ta rabawa, kamo hannun Safiyyah tayi tare da cewa. "Ke Safiyyah wannan fa, yanzu na kira hadimai akan suzo su fara raba kyautukan da muka shirya." Murmushi Safiyyah tayi kana tace. "Eh gasu can suma sun fara wannan kuma kyautar Sheykh ne. Dama tun jiya yace mu raba da kanmu mu kuma tabbatar kowa ya samu. Gefen maza ma gacan su Jalal na rabawa". Wani irin murmushi mai cike da jin daɗi tayi kana ta jinjina kai. Ita kuwa Safiyyah sukaci gaba da rabiya. Suma hadimai suka zo suka fara nasu rabiyar.

Gyaran muryar da Sheykh yayine ya jawo hankalinsu gareshi. Cikin rauni murya a sanyaye yace. "Ƴan uwana ina neman addu'o'in ku, inada wata buƙata mai girma da nake nema wurin ubangijina kuma mai sauƙine in ya lamunce min. Na roƙeku al'farmar Annabi da Alqur'ani ku sani addu'o'in ku Allah ya biya min buƙatata". Kusan a tare duk hall ya ɗauki. "In sha Allah, Allah ya biya maka buƙatar ka". Amin Amin yace. (Kana nima Aysha Aliyu Garkuwa, inada buƙata wurin ubangijina fans ku tayani roƙo dan Allah, Allah ya cika min buƙata.)

Daga nan manyan mutane duk suka mimmiƙe suka fita. Nan kowa da kowa ma ya fara fita.

Haka motoci sukayi ta ɗibar mutane suna wucewa dasu gida.

Safiyyah, Ibrahim, Haroon Jannart, duk tare suka miƙe suka fita. Bayan suna fita Haroon yaja hannun Jannart suka shiga Mota. Ibrahim ma da Safiyyah motarsu suka nufa, cikin kula Safiyyah ta kalli Aysha dake gefenta tace. "Yah Sheykh bai fito ba ko". Ibrahim ne ya amshi zancen da cewa. "Eh ya tsaya yana gaisawa da Abokan Abbanshi ne. Bari in amso key ɗin motarshi sai ta jirashi a ciki kafin ya fito ko". Eh Safiyyah tace, kana ya juya ya koma ciki. Ita kuwa Aysha ɗan numfashin gajiya ta sauƙe tare da bin motarsu Umaymah da aminanta da ido kana tace. "To wai dole sai dashi zan tafine? Mu tafi kawai mana in dai ba rowar motar taku zakuyi min ba gashi kowa ya tafi sai mu kaɗai". Murmushi Safiyyah tayi tare da kamo hannunta ta ja suka jingina da motar Sheykh cikin raha tace. "Eh gsky rowar motar mu zamuyi miki, haka kawai zaki hanamu sakewa bayan kema ga motar naki mijin. Gsky ki jirashi ya fito ku tafi, dan wlh ya Ibrahim yace haƙurinshi ya ƙare daga nan hotel muka nufa". Ta buɗi baki zatayi mgna kenan Ibrahim ya iso da car key a hannunshi. Sa key ɗin yayi ya murza ƙofar ya buɗe kana yace. "Yauwa shiga nan ki jirashi yana nan fitowa". To tace a sanyaye kana ta juyo ta kalli Safiyyah daketa kerkerar barbara tace. "Allah kuwa tsoro nakeji sai inji zuciyata na tsinkewa". Murmushi Safiyyah tayi kana tace. "Wlh ba komai keda gaki ga GARKUWAR ki to me zai firgitaki". Kai ta jinjina kana tasa kai ta shiga, gefen mai zaman banza. shi kuwa Ibrahim key ɗin ya saka a mazauninshi a cikin motar kana yaja hannun Safiyyah yace. "Kinga mu tafi". To Safiyyah tace kana ta juya tabi bayanshi, tana cewa Aysha saida safe.

Murmushi Aysha tayi kana ta bisu da ido, har motarsu ta fita ta bar harabar wurin.

A hankali ta sauƙe ajiyan zuciya, kana ta juya ta kalli gefe da gefenta, Sam babu kowa a wurin sai hasken wuta tako ina sai inuwar fulawi da dogayen bishiyoyin namijjn gwanda. Da kuma inuwar motocin da suka ɗan rage wanda basu wuce biyar ba. Dan sam babu motsin kowa da komai. A hankali ta ɗan juya kanta gefe tana jiyo ɗan sautin kukan tsuntsaye su Sheykh da suke ciki kuwa sam ko muryarsu bata iya jiyowa gashi tsaka ninta da masu gadima tafiyace mai zaman kanta, fadawan kuwa suna ciki wurin ubanin gidajen nasu.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull