Garkuwa complete novel - Chapter 68
Garkuwa complete novel Chapter 68: Garkuwa complete novel Chapter 68. Alhamdullah cikin ikon Allah da buyawansa yanzu cikin Shatu wata shida kenan kuma har…
4,486 words
Alhamdullah cikin ikon Allah da buyawansa yanzu cikin Shatu wata shida kenan kuma har yau magauta basu san da shiba dan bata fiye fita kuma cikin baida wani girma. Tana zuwa makaranta tana karatunta hankali konce. Tana waya da Ummeynta. Alhamdullah yanzu zazzaɓin daren da Sheykh yakeyin nan yazamo tarihi yawarke tsaf abinshi,suna rainon cikinsu cikin kula da tarai raya da ɗonkin ganin ranar zuwan Baby.
Zaune suke a parlour Ummi na saman kujera Shatu kuma na zaune a kasan carpet ta mimmike sawunta ta tasa ɗan madaidacin cikinta a gaba, tana ɗan kurɓar kunun tsamiya da Ummi ta dama mata, Ummi ta ɗan kalleta tare da cewa. "Ikon Allah kinga na sha a fa ɗazu Juwairiyya ke cemin Gimbiya Aminatu ba lafiya tana zazzaɓin mura". A jeyi cup ɗin kunun tayi tana cewa. "Allah sarki shiyasa tun jiya bata turomin haɗin furan nan ba Ummi muje mudubata tunda ba abinda mukeyi". Ta ƙare mgnar tana miƙe cafal kamar ba mai cikiba. Cikin fari kenan. A hankali ta shiga ɗaki taɗauki ɗan ma dai-dai-cin hijabi tasaka a kanta tafito,nan tasami Ummi rike da mayafin ta. Tare suka nufi sashin Gimbiya Aminatu.
Da sallama suka shiga parlour'n Gimbiya Aminatu. Ummi na gaba Shatu na biye da ita. Hajiya Mama da Gimbiya Saudatu duk suna zaune cikin parlour'n.
wani irin mikewa Gimbiya Saudatu da Hajiya Mama sukayi cikin tsananin kaɗuwa da zallar mamaki suke kallon cikin da basusan farkon saba sai daya baiyana kansa yau rana tsaka suka ganshi, Cikin wani irin tashin hankali da baƙin cikin Hajiya Mama ta juya cikin wani irin kiɗima tafice a parlour'n gaba ɗaya idanunta sun wani fiffito sun zazzaro waje saboda sabar firgici da baƙin cikin wannan cikin data gani.
Tana fita hanyar part ɗin ta tanufa hankali tashe, ɗago wayarta tayi tana tafiya tana daddanna shi tana sharar ƙwanar part ɗin ta takai wayar kunne, Tana wani irin huci na tashin hankali,daga cikin wayar kuwa ringing biyu zuwa uku a ka ɗaga me biye da kiran
yace. "Hajiya bar". Da sauri cikin ɗaga murya tace. "Dakata Boka gilmau bana bukatar gaisuwarka! haka mukayi da kai wani irin makudan kuɗine ban zubda makaba k". Cikin dakiya boka GILMAU ya katse ta. "Da kata Hajiya ki daina min ihu akunne dan ba fahimtarki zanyiba." Bokan yadakatar da ita kafin takarass faɗar kalmar k. data furta. Itako cikin musifar tashin hankalin da take ciki tace "Gani nan zuwa gurin ka yanzu dan wlh bazai yuwuba dole a sake sabon shiri". Tana kaiwa nan takashe wayar tashiga ciki taɗau mayafin ta da makullin mota da da wasu kuɗaɗe masu yawa a ɗaure bandir-bandir tafita tanufi in da mota yake tashiga taja da mugun gudu tafi tanufi gidan Boka.
Cikin rawan jiki take tuƙi hannunta ɗaya riƙe da waya ta kara a kunne wanda ta kira Jahan. Shi kuwa Sheykh (Jahan) kenan yana zaune a Office nashi yaga kira da layinsa na sirri a yar ƙaramar wayar da ko inganta a garƙame yake. Murmushi yayi ganin 3 bala'i da haka ya seba number. Wani murmushi iya salon taku yayi kana ya amsa kiran tare da ƙara wayar a kunne ya sauya muryarsa tare da cewa. "Hajia Mama Uwar Sheykh meke faru". Cikin faɗa tace. "Oouxubillahi subahanallahi Jahan kada ka sake cemin uwar Sheykh kai kasan duk duniya babu wanda yasa irin zallar tsanar da nakeyiwa wannan shegen yaron da sihiri baya cinsa data daɗi wlh yau ji nakeyi zan iya zubawa Part ɗinshi Dana ƙannenshi wuta su ƙone su mutu kowama ya huta". Wata iriyar ja'irar dariya yayi tare da cewa. "A a to yau kuma me kika gani a kansu ɗaya tada miki hankali ne haka". Cikin tafasan zuciya tace. "Dariya ma na haka kenan, to bari kaji wannan shegiyar matar tasace, naga cikine da ita cikima mai girma kuwa". Da sauri yace. "To dan ganin cikin ne hankalinki ya tashi". Cikin tsantsar tsana tace. "Wlh tallahi sai na zubda cikin nan wlh babu wanda zai ƙara haihuwa cikin ahlin A'isha nida nake son on ɓaddasu a masarautar Joɗa ya zanyi in barsu suyi ta haihuwa wlh zan zubda cikin in Kuma ya fito duniya tabbas zan kashe ɗan". Wani irin miƙewa tsaye yayi lokacin ɗaya zufa mai zafi ta karyo mishi gaba ɗaya jikinsa rawa yake, cikin saisaita nitsuwarsa yace. "Eh lallai wannan batun babbane bari anjima zanzo muyi shawarar yadda zamuyi". Yana faɗin haka ya katse kiran. Yatsarsa manuniya yasa ya sharce zufan daya feso masa a goshi. Kana sai kuma yayi murmushi tare da cewa. "Innalillahi wa innailaihi rajiun. Hasbunallahiwani'imanwakil." Yayi ta maimaitawa kana ya koma ya zauna ya dafe kanshi tare da cewa. "Uhmmmm Hajia Halima kenan rashin sani ya saki kina shuka a idon makorwa. Wai ni Muhammad Jabeer mena tsare miki nada yan uwan da mahaifiyarmu da kike so ganin baya mu, me cikin matata ya miki, meyasa zaki so cutarmi da Aish da ɗan...!
By *GARKUWAR FULANI* [4/12, 8:34 PM] Maman Aslam: Ƙarfe huɗu dai-dai, na yamma, wasu irin motoci ne masu masifar kyau da tsaruwa. Suke kutsa kai cikin airport ɗin, wanda a ƙalla sun kai bakwai. bisa alamu duk akwai cikekken nasaba da dama, dan har can asalin wurin da jirgi yake biyu daga cikin motocin suka wuce. Kana biyar kuma suka tsaya a ainihin harabar. A hankali aka buɗe motocin. Alhaji Abboi ne ya fara fitowa. Sai Bappa kana Al'ameen da wasu matasa uku masu kama da Al'ameen sai wata kekkyawar budurwa mai kama da Shatu sak wacce take riƙe da hannun Junainah. Sai Ummey da Inna Amarya da suka fito. Bisa alamu duka, sauran rakiya sukayiwa su Bappa. Gyara tsayuwarsu sukayi dan ganin matafiya nata shiga cikin jirgi, wanda yake ɗauke da tambarin Abboi. Cikin murmushi Appa ya miƙawa Bappa hannu sukayi musabaha kana a hankali yace. "Toh Malam Babayo Allah ya maidaku lfy ya kiyaye hanya". Cikin jin daɗi Bappa yace. "Amin Amin Abboi Ubangiji ya saka maka da mafi kyawun sakamako". Cikin jin daɗin Addu'a Al'ameen da saura zaratan samarin nan sukace. "Amin ya Allah". Sai kuma sukayi shiru jin Appa na cewa. "In kun isa ka gaida min Parvina da kyau, kana aci gaba da ɓoye mata abinda mu muka fahimta, har sai lokacin da ido zaiga ido muna da kekkyawan yaƙinin duk sanda taga wasu cikin masarautar Joɗa mu samman in ya shafi ahlinta in sha Allah zata iya tuno komai na baya". Ya ƙarashe mgnar a hankali yadda ko su Al'ameen basu jiba bare su Ummey. Cikin gyaɗa kai Bappa yace. "Inama ji a jikina komai ya kusa zuwa ƙarshe da izinin ubangiji. Dan yanzu dai nasan muna komawa Shatu zata zo, to inma batazo da waniba ina zaton zata zo da mijin nata, kuma inma bata zo ɗinba idan ta haihu shine shirinmu ta sanadin haka Ummeynta zata shiga masarautar Joɗa ba tare da an zargi komaiba". Kai Appa ya gyaɗa tare da cewa. "Tabbas komai ya kusa zuwa ƙarshe".
Yar Kekkyawar budurwar nan kuma mai kama da Shatu hannun Junainah ta sake ganin Bappa na miƙo mata hannu alamun tazo su tafi. Cikin sanyi Khadijah tace. "Ayyah Junainah zamuyi kewarki." Da sauri Junainah tace. "Adda Khadijah ina in Adda Shatu na ta haihu zakizo keda Dedde ko?". Kai Khadija ta jinjina tare da cewa. "In sha Allah kuwa, zanzo ki gaida min ita da kyau kinji ko my Junnu kice mata duk Ahlin Abboi muna kewarta." Da sauri tace. "To zan gaya mata, bey-bey Adda Khadijah sai kunzo". Tana faɗin haka ita da Bappa suka nufi cikin jirgi. Ita kuwa Khadijah ruggume Ummey tayi tana zubda hawaye tace. "Ummey zamuyi kewarki, dake da Junnu". Hannu Ummey tasa ta share mata hawayenta kana tace. "Nanda wata biyu dai Shatuna zata haihu zakuzo mu gana".
Da sauri Ummey da Inna Amarya suka nufi cikin jirgin bayan sunyi sallama da Abboi.
Basu tafiba saida sukaga tashin jirginsu.
Ƙarshe biyar da rabi jirginsu ya sauƙa cikin Ɓadamaya International airport. riƙe da jakukkunan kayansu suka fito, Junainah na gaba. Tanata murmushin jin daɗi. A haka suka iso asalin inda masu taryar matafiyan suke.
Yah Salmanu ku wanda shida Junaidu ne sukazo taryarsu cikin motar Yah Salmanu wanda tuni shima ya samu aikinsa, cikin Ɓadamaya an bashi gida da mota.
Wani irin tsalle Junainah tayi tare da rabkawa Junaidun kira wanda ta hangoshi yanata ɗan dube-dube alamun neman ta inda suke.
Jiyo muryar ta, A tare suka juyo shida Yah Salmanu. Wani irin murmushi mai cike da tarin jin daɗin Junaidu yayi tare da nufo inda suke gadan-gadan. Ita kuwa Junainah da gudu ta iso gabanshi, sai kuma ta tsaya tare da sakin murmushi bata abka jikinshi ba kamar yadda takeyi da can baya. Wani irin murmushi Yah Salmanu yayi tare da cewa. "Oyoyo My Junnu Allah sarki nesa mai raba masoya, watoma Junaidu kawai kika sani banda ni ko?". Cikin jin kunya alamun shekara ɗaya nan data ƙara cikin shekarunta yanzu ta zama yar shekaru goma sha uku hankali da nitsuwa da kunya sun fara zuwar mata, cikin jin kunya tace. "A a Yah Salmanu na ganka mana". Sai kuma ta kalli Junaidu daya karkata kai yana kallonta cikin sanyi yace. "I miss you very very sorry so much my Junainah". Cikin rufe ido tace. "I miss You to Yah Junaidu, ya jikinka ka worke ko?". Da sauri yace. "Alhamdulillah garauma kuwa". Shi kuwa Salmanu da sauri ya isa gabansu Bappa jakukkunansu ya amsa, haka yasa shima Junaidu yayi maza ya amshi na hannun Ummey tare da cewa. "Oyoyo Ummey na Bappanmu Inna Amarya sannunku da hanya". Kusan a tare sukace yauwa. "Sannu Junaidu". Sai kuma Bappa ya kallesu tare da cewa. "Masha Allah Junaidu na ya girma." Ummey kuwa Salmanu ta kalla tare da cewa. "Kai sannu Salmanu ya bayan rabuwa?". Cikin girmamawa yace. "Alhamdulillah Ummey na munata kewarku Rugar Bani gaba ɗaya". Bappa ne ya jinjina kai tare da cewa. "Muma muna cannedai Amman munata kewarku". Ɗaga nan suka nufi inda motar Salmanu take. Suna shiga suka nufi Rugar Bani.
Kafin a kira mangriba dai sun isa.
Anayin sallan magriba da isha'i matan Rugar Bani suka rinƙa shigowa sunayiwa su Ummey sannu da dawowa da ganin amaryarsu.
Junaidu kuwa ana idar da salla ya dawo nanfa yaja Junainah gefa kaɗan cikin gidan sunata hira, tana bashi lbrin ahlin Abboi yayinda sosai yanzu faransaci ya kama bakinta.
A nan masarautar Joɗa kuwa. Ana idar da sallan isha'i suna fitowa a kan hanyar komawarsu cikin gidane. Lamiɗo keyiwa Sheykh batun zuwansu Rugar Bani da Umaymah ta gaya mishi. Ɗan juyowa yayi ya kalli Lamiɗo jin yana cewa. "In Allah ya kaimu goben da safe fadawa da bayi zasuyi muku rakiya, ka kuma ɗauki Jalal da Jamil da Umminku". Cikin kwaɓe fuska yace. "Bana wani buƙatar rakiyar bayi da fadawa da hadimai. Kuma Jamil da Jalal duk yanzu bana son yawonsu na aamu suɗan fara meda hankalinsu sosai kan aiyukansu sun rage zaman gida da yawace-yawace kuma ma ni tafiyata ta sirrice, bana ma son asan Aisha bata gida bare asan inda take, sabida gsky wanna Hankakar Hajia Mama mai farin gaba bakin baya sata iyasa aje can Rugar ayi mata komai, badon dole bama bazata jeba, sabida rugar ba tsaro." Jinjina kai Lamiɗo yayi cikin gamsuwa da zancenshi yace. "Eh to wannan ma hakane ba matsala kuyi tafiyar sirrin ammanfa zakuje da Ummi". Kai ya gyaɗa alamun to daga nan sukayi sallama.
Yana shiga falon ya samu ba kowa. Falonshi ya wuce a nan ya samu Shatu kwance bisa kujera. Matsawa kusa da ita yayi tare da cewa. "Ya dai Aish lfy kuwa yau ba hira ina Ummi ina Juwairiyya?". Ido ta lumshe tare da cewa. "Wlh Ummi zazzaɓin mura ke damunta". Cikin kula yace. "Assha subahanallahi tasha mgni kuwa?". Kai ta gyaɗa tare da cewa. "Eh tasha har tayi baccima". "Toh Allah ya sauƙa". Yace yana zare al'kyabbar jikinshi. Amin Amin. Tace tana tashi zaune. Gefenta ya zauna ganin haka ta ɗan gyara zamanta tasa mishi abinci ya fara ci.
A hankali ta kalli wayarta dake gefenshi ganin ta kawo haske alamun ana kiranta. Miƙo mata wayar yayi. Junaidu tace tare da amsa kiran. Cikin dariya yace. "Adda Shatu na rigaki ganinsu yau kam gani ga Junainah na, ga Ummey ga Bappa munata hirarmu sanyin hunturu na kaɗamu ga farin wata, Adda Shatu farin cikin Rugar Bani ya dawo kamar yadda kika sani a da can baya". Cikin tsananin jin daɗi tace. "Alhamdulillah Junaidu nima in sha Allah gobe iwar haka muna tare da yardar Allah, ina my Junnu". Da sauri Junainah dake c jinsu tace. "Gani nan Addana". Murmushi tayi kana tace. "Ina Ummey na?". "Gata can cikin baƙi" Junaidun ya bata amsa. Daga nan ta katse kiran. Ta juyo da sauri ta kalli Sheykh dake cin abinci. "Alhamdulillah Hamma Jabeer su Ummey sun iso". Cikin sakin fuska yace. "Masha Allah, Alhamdulillah". Da sauri tace. "Gobe sammako zamuyi ko". Ajiye spoon ɗin hannunshi yayi sabida ya ƙoshi gyatsa yayi tare da hamdala kana a hankali yace. "Aishhhhhhhh ya za'ayi muyi sammako, kin matanta gobe jumma'a ne? Sai munyi sallan Jumma'a sai mu tafi ko? Please kada kice komai kin ji kiyi haƙuri sai munyi sallan". Cikin rashin iya masa jayaya tace. "To Allah ya kaimu Lokacin". "Amin Amin". Yace
Daren ranar sosai Shatu ta sama mishi gamsuwa iya gamsuwa. Sai da komai ya lafa kuma ta narke mishi, tare da kamo hannusa ta ɗaura kan ɗan cikin nata daya tattare ya koma gefe ya bawa iyayen nashi dama. Da sauri ya tashi zaune yana sauƙe numfashin. Tafin hannunshi ya kife kan cikin. tare da fara murza wurin a hankali yana dai-dai-ta kwanciyar yaron yana mgn a hankali. "Afwan Ƴar al'barka gyara kwanciyarki ko, kada ki wahal da Amminki, yauwa yarinyar kirki, Allah ya miki al'barka ya fito dake duniya lfy ya tsareki da kariyarsa ya al'barkaci rayuwar ki ya raya mana ke bisa imani yauwa Kekkyawar jikar Mamey da Ummey". Murmushi sosai takeyi ganin yadda yake kalamai masu daɗi akan cikin a hankali tace. "Yah Sheykh bafa jinka yakeba". Murmushi yayi tare da kissing cikin kana a hankali yace. "Ita Kekkyawar mgn tana tasiri akan shuke-shuken fulawima hakama akan yaron ciki, musamman da mahaifinshi ko mahaifiyarshi, bakyajin duk sanda nake masa mgn yakanyi ta jujjuyawa". Ya ƙarashe mgnar yana lakace hancinta. Daga nan dai yaje yayi wonka haka itama.
Ummi kam sosai mura yayi mata rubdugu.
Washe gari ranar jumma'a kuwa, gaba ɗaya Shatu gani take lokacin baya gudu ta gama shirinta.
Bayan an idar da sallan Jumma'a. Sheykh ya nufo Side ɗinsa, su Jamil na biye dashi a baya. Yana shiga ya samu Shatu a falo tana zaune gaban Ummi dake kwance bisa kujera ɓare mgni takeyi tana bata. Sara kuma nacan kitchen tanayi musu girki.
Cikin sauri ya wuce falonsa jim kaɗan kuma ya fito. Da sauri ya kalli Ummi tare da cewa. "La! Ummi bar mgnin nan yanzu zamu tafi Valli dake in duba miki wani mgnin". Da sauri Shatu ta kalleshi jin yadda yake mgn kamar hankalinsa a tashe, Shi kuwa Jamil ya kalla tare da cewa. "Yi maza kaje ka kira min Baba Ado direba". Da sauri Jamil yace to kana ya juya ya fita. Jalal kuwa Dinning area ya nufa riƙe da waya a kunne yana mgn da Hibba.
Ummi kuwa, to kawai tace. Shi kuwa Sheykh cikin kula da alamun sauri da gaggawa yace. "Aish zo". Da sauri ta miƙe tabi bayanshi.
Suna shiga falonshi ya juyo ya ruggumeta gam-gam a jikinshi cikin sanyi yace. "I'm so sorry afwan Mar'atussaliha. Wani aikin gaggawa ya sameni a Valli Hospital, wasune sukayi hatsari. To biyu daga cikinsu sunada ciki, sun jikkata sosai dole sai anyi musu CS. Dole yanzu zan tafi can. Nasan ke kuma kin matsu mu tafi Rugar Bani, shiyasa na kira Baba Ado zai kaiki. In Kuma zakiyi hakuri sai gobe muje tare to?". Cikin sanyi da tausayawa matan tace. "A a Hamma Jabeer babu komai Baba Ado ya kaini, kaje ka taimakesu. Sabida sun fini buƙatar ka a yanzu, tunda su ransu da lfyarsu zaka taimaka da abinda ke cikinsu." Ta ƙarashe mgnar da bashi ƙarfin guiwar yin aikinshi cikin nitsuwa". Lip ɗin ta na ƙasa ya sumbata tare da cewa. "Masha Allah Mar'atussaliha, ngd Matuƙa da kekyawar fahimta. Allah ya miki al'barka in sha Allah nima zanzo". Ya ƙarashe mgnar yana zaro wasu sabbin kudin rafa-rafa ɗaurin dubu hamtsin-hamtsin guda biyu ya bata. Kana a hankali ya sunkuyo ya durƙusa ya kife guiwowinsa a ƙasa. Hannu yasa ya ture rigar jikinta sama. Dai-dai kan hudar cibijiyarta ya mannawa kiss kana ya fara kissing ɗin cikin tako ina. Ita kuwa Shatu ido kawai ta lumshe tare dasa tafin hannunta bisa kanshi. Ya daɗe yana kissing cikin da sauri-sauri, kana ya manna kunnenshi bisa cikin tare dasa hannun ya zagaye ƙugunta. A hankali ya fara karanto Ayatulkursi'u yana tofawa yana idarwa ya sake saida yakaranceta ƙafa bakwai kana yayi falaƙi 3 nasi 3 ƙulhuwa 3 ya ƙara da azubikalmatillahi har ƙarshe. Ya tofe a cikin sannan ya taso. Ya ruggumeta tare da cewa. "Allah ya kaiku lfy yasa ku samesu lfy ki gaida min Ummey da Bappa da kyau. Akwai tsarabar Junainah tana cikin motar kice ina gaisheta". Cikin sanyi tace. "Zasuji Ngd matuƙa Allah ya ƙara buɗi ya rufe asiri". Fuskarta ya shafa tare da cewa. "Amin My dear bey'. Yana faɗin haka ya juya ya fita. Itama ta binshi a baya.
Da sauri Ummi ta miƙa jin yana ce mata. "Toh Ummi mu tafi". Da sauri Ummi tace. "Toh Shatu sai mun dawo". A hankali tace. "Ummi nina yanzu zan tafi Baba Ado zai kaini". Dai-dai lokacin Baba Ado da Jamil suka shigo da sallama. Ita kuwa Ummi cikin ƙarfin hali dason zuwa gidansu Shatu ta ƙiddigi zarginsu tace. "A a Sheykh ba tare zamu jeba". Kanshi ya ɗan juyo kana a hankali yace. "No Ummi kada ki damu zamuje ɗaukota yanzu dai Baba Ado zai kaita". Sai kuma ya juyo ya kalli Baba Ado a hankali yace. "Baba Ado na yarda da tuƙinka amman a ƙara kulawa kuje a hankali, tafiyar kuma ta zama ta siiri kada kowa yasan da ita kuka fita kaji ko". Cikin mutunta juna Baba Ado yace. "In sha Allah ba matsala". Daga nan yace. "Jamil fito mata da kayanta, mu mun tafi". Nan suka fita shida Ummi. Ita kuwa Jamil ya kai mata kayanta cikin motar da Baba Ado ya kawo har bakin Part ɗin su.
Tana fita Jalal na binta a baya, ya rage Sarace kadai ke musu aikin abincin dare.
Tana shiga motar Baba Ado yaja a bakin Part ɗin Lamiɗo suka tsaya nan ta shiga tai musu sallama kana suka fito suka tafi.
Ƙarfe uku dai-dai suka isa Rugar Bani. Motar nayin parking tayi sauri ta fito. Junaidu dake fitowa gidan ne, yayi maza ya nufi inda take fuska cike da murmushi yace. "Oyoyo Adda Shatu masha". Cikin tsananin jin daɗi tace. "Oyoyo Junaidu. Yauwa isa ka shigo min da kayana". Da sauri yace to, kana ya nufi. Wurin motar inda Baba Ado ya fito mata da jakarta da kuma ɗaya jakar wacce Sheykh yayiwa Junainah tsaraba. Amsar jakukkunan yayi ya ajiye a bakin zauren kana ya dawo kusa da Baba Ado ya bashi hannun suka gaisa tare da cewa. "Ka iso mana Baba". Cikin nitsuwa Baba Ado yace. "A a ba komai yaro sauri nake zan juya so nake kafin a kira la'asar na isa gida." "Bazaka tsaya ku gaisa da Bappanmu Baba". Junaidu ya Kuma faɗa. A a ba matsala sai in munzo ɗaukarta. Dole Junaidu ya barshi yaja mota ya tafi.
Shatu kuwa cikin wani irin masifeffen jin daɗi da begensu ta kutsa kanta cikin gidan tare da cewa. "Assalamu alaikum Ummey ina kike Junanaih Ina Inna Amarya". Wani irin zabura Ummey dake cikin ɗaukita tayi tare da miƙewa ta nufi waje da sauri. Junainah kuwa da fitowarta daga ban ɗaki kenan. Wani irin ihu mai cike da tsalle da jin daɗi tayi ta cilla butar hannunta can gefe. Tare da nufo Shatu a guje tana cewa. "Wayyoooooooo Allah na Adda Shatu na Ummey ga Adda Shatu na Oyoyo". Ta ƙare zancen cikin tsananin jin daɗi tare da nufo Shatu haiƙan ƙadaran. Zaro ido Ummey tayi tare da cewa. "A a fa a a Junainah kada ki faɗa jikinta zakiji mata ciwo". Sai kuma tayi shiru tare da zuba musu ido ganin itama Shatu gudun takeyi cikin ƴar sassarfa kamar ba mai cikiba. ta nufo Junainah. Wani irin ruggume juna sukayi da ƙarfi tare da cewa. "Alhamdulillah". Sai kuma ta ɗago Junainah data makaleta tafara jujjuyawa da ita. Da sauri Ummey ta nufosu tana cewa. "Na shiga uku Shatu ki sauƙeta zakiji ciwofa. Inna Amarya ma da sauri ta nufosu tana. "La hailahalillah Shatu zaku faɗifa". Junaidun da shima yanzu ya shigo da jakukkunan sai kallonsu yake yana murmushi.
Ita kuwa Shatu Ummey na isosu ta sauƙe Junainah kana ta faɗa jikin Ummey ta ruggume ta gam-gam tana maida numfashi da haki take cewa. "Oyoyo Ummey na yau kam daɗi zai kasheni". Itama Ummey wani irin ruggume ta tayi cikin tsantsar jin daɗi da tsananin so. Tace. "Oyoyo Shatuna Boɗɗona mangana yar al'barka." Sai kuma tayi saurin janye jikinta jin yadda ɗan cikin yake wutsul-wutsul da sauri ta kamo hannun ta. Ita kuwa Shatu hawayen farin ciki take zubdawa. Inna Amarya kuwa taburma ta shimfiɗa musu a tsakiyar gidan. A ƙarƙashin inuwar bishiyar mango da bishiyoyin ayaba suka zagayeshi hakan ya bada daddaɗan inuwa mai sanyi. Da sauri Ummey ta ajiyeta. Ruwan sanyin da Inna Amarya ke miƙa mata ta amsa ta bata. Ba musu ta amsa ta kafa kai dan hakin da takeyi yasata jin ƙishi. Gefenta Junainah ta zauna. Ummey kuwa gabanta ta zauna Inna Amarya kuma gefenta. Junaidu kuma shigar da kayanta ɗakin Ummey yayi kana ya fito ya gaisheta sannan ya tafi.
Ita kuwa Shatu a hankali ta zame ta kwanta ta ɗaura kanta bisa cinyar Ummeynta cikin sanyi tace. "Alhamdulillah yau gani ga Ummey na". Murmushi Ummey tayi kana ta shafa cikinta tare da cewa. "Shatu ki dena wasa da jikinkifa, kada kije ki tadawa kanki naƙuda lokacin ta baiba". Cikin jin ɗan kunya tace. "Toh Ummey itama ai yau tana farin cikin ganinki". Sai kuma tayi maza ta miƙa zaune. Jin muryar Bappa na cewa. "A a a masha ALLAH yau gani ga Shatu na". Cikin sauri ya iso inda suke gefenta ya zauna ita kuwa hijabinta ta gyara tana ɗan rufe cikinta alamun kunya tace. "Oyoyo Bappa na". Cike da jin daɗi yace. "Sannu Shatu na.
Nanfa suka fara gaggaisawa da hirar yaushe gamo, ɗaya Bayan ɗaya haka take tambayar ahlinta wato ahlin Abboi. Su iro ma suna dawowa aka zauna ana hira. Inna Amarya kuwa da Ummey gidin murhu suka koma sunata haɗa miyar jumma'a. Junainah kuwa na liƙe da ita.
Sai salla ne kawai yake ɗagasu a wurin.
Sai bayan sallan isha'i kuma duk suka zauna bisa taburma suna hira suna cin abinci.
Cikin nitsuwa Shatu ta juyo ta kalli Bappa dake gefe dashi dasu Iro yayinda farin wata ya haskasu ras, numfashin ta ɗan fesar tare da cewa. "Bappa na ya lbrin su Yah Giɗi na". Tayi mgnar hawaye na ciko mata ido". Cikin sanyi yace. "Wlh Shatu jikina na gaya min su Giɗi suna gab da baiyana. Dan wayewar asuban yau nayi mafarkinsu wai Mijinki ya dawo min dasu da hannunshi. In sha Allah kuwa suna kan hanya da izinin ubangiji tabbas suna hanya, muci gaba da Addu'o'in da muka sabayi".
Cikin gamsuwa da jin sanyi tace. "In sha Allah kuwa."
Nan sukayi ta hira maƙota nata zuwa Binto budurwar Ya Gaini tazo haka Hari.
Sune basu shiga sai kusan ƙarfe sha biyu na dare. Yau ko Junainah batayi bacci ba.
Suna shiga suka kwanta, Ummey na kan ɗaya gadon ita kuwa Shatu ita da Junainah suna kan ɗaya gadon.
Cikin sanyi Ummey tace. "Uhumm Shatu ya mai gidan naki da mutanen gidan naku?". Dogon numfashi ta sauƙe tare da cewa. "Uhumm Alhamdulillah Ummey yana lfy yace in gaidaki shima zaizo da tarema zamuzo to sai aka kai wasu asibitinsa sunyi hatsiri". Cikin sanyi tace. "Ayyah Allah ya basu lfy". Amin tace kana a hankali ta gyara kwanciyarta tare da jawo hand bang ɗin ta hannun tasa ta fito da cakuleti masu daɗi ta miƙa Junainah da sauri ta amsa ta ɓare tasa a baki. Ita kuwa Ummey ta kalla tare da cewa. "Uhmmm mutanen gidansu kuwa masu cike da sarƙaƙiya da mugunta suna can sunata fama da muguntarsu. Kai Ummey gidajen sarauta akwai wuyan zama". Kai ta jinjina tare da cewa. "Ke dai ki dage da addu'a in sha Allah babu abinda zai sameki". Cikin gamsuwa tace. "In sha Allah kuwa, shima Yah Sheykh yana yawan mana addu'o'in". Kai Ummey ta jinjina cikin gamsuwa.
Dai-dai lokacin kuma. Sheykh ne tsaye tsakiyar falonshi gaba ɗaya ya rasa me ke mishi daɗi. Tsaki ya ɗan ja, tare da cewa. "Gidan ba daɗi". Sai kuma ya zauna bisa kujera, a karo na biyar ya kuma kiranta stiil bata ɗagaba. Sabida wayar na sailent kuma tana cikin hand bang ɗin ta. Allah ya sani ta mance da batun wani suyi waya dashi.
Dogon tsaki ya ɗan ja tare da cewa. "Yayi kyau Aish wato kin samu su Ummeynki ni kin mance da nima". Haka dai ya kwanta yanata jan tsaki a haka yayi bacci.
Ita kuwa da Ummey kusan kwanan zaune sukayi ranar.
Koda asuba sukayi salla wani hirar suka kuma buɗe wa. Harda Bappa daya shigo. Nan ta jawo jakar da Sheykh yace tsarabar Junainah ne. Tana buɗe wa daga sama ta samu wata leda cike da kayayyakin kwalam na makwaɗaita irin Junainah. Sai kuma wasu irin tsala-tsalan turame atamfa da Shadda da lashi da hijabai guda biyar-biyar iri ɗaya alamun na Ummey da Inna Amarya. Sai kuma wasu dogayen riguna masu kyau guda biyar irin na larabawa da alamun na Junainah ne sai dai zasu ɗan mata tsawo kaɗan. kana sai takalma na manya da kamar na Junainah. Sai kuma wasu irin yadin Getzner masu kyau kala biyar sai manyan al'kyabba guda biyu da alamun na Bappa ne. Sai kuma kuɗi a cikin ko wanne kaso alamun kuɗin ɗinkin ne, sai can ƙasar jakar kuma turaruka ne masu tsadar gaske da sabulai da mayukan shafawa. Ido kawai suke zuba mata. Ita kuwa cikin jin daɗi tace. "Gashi inji Yah Sheykh". Cikin jin daɗi Junainah ta fara tsalle da ribibi kan kayan zaƙin sam batama kula kayan suturun ba. Bappa da Ummey da Inna Amarya data shigo musu da karin kumallo kuwa cikin fulaku da kawaicin fulanin kwarai sukace. "Kai Shatu ya zakiyi ki barshi yayi mana irin wannan hidimar haka". Cikin sanyi tace. "Ayyah Ummey kawai kusa mana al'baka". Cikin sanyi suka haɗa bakin cewa. "Allah ya muku al'baka ya sauƙeki lfy". Amin Amin tace tana jawon akoshin ɗumamen gashesshen naman.
Nan Bappa ya fita su kuma suka zauna suka fara cin abinci. Ranar ma dai haka suka wuni hira, sam ko ta kan wayarta bata biba.