Garkuwa complete novel - Chapter 74
Garkuwa complete novel Chapter 74: Garkuwa complete novel Chapter 74. A hankali ta jawo wayarta. Abboi ta kira, bayan sun gama gaisa ya alhinta abinda ya…
4,439 words
A hankali ta jawo wayarta. Abboi ta kira, bayan sun gama gaisa ya alhinta abinda ya faru ya ɗaura da cewa. "Dama can gobe zamu zo ko ba komai zanzo inga amryata, inga mummunace ko kekyawa". Ya ƙare mgnar da ƴar raha da son kontar mata sa hankali. Murmushi tayi tare da cewa. "Allah ya kawomku lfy Appa na, da Ummey na da Junainah take kamafa". Tayi mgnar cikin jin kunya duk da yawan shaƙuwa dake tsakaninsu. Murmushi yayi tare da kallon Dedde dake jin duk tattaunawar da sukeyi yace. "Ato kekkyawace sadaki ta garken shanun Bappa zai bata". Dariya sukayi baki ɗayansu kana sukayi sallama da juna. Daga nan kuma Bappa ta kira, wanda tun ɗazu Abboi ya shaida masa abinda ya faru yana ɗagawa yace. "Shatu na ya jikin Aisha ƙaramar dai?". A hankali ta ɗan shafa kan Afreen tare da cewa. "Alhamdulillah Bappa na ba komai ta samu lfy gatama tana bacci". Cikin jin daɗi yace. "Alhamdulillah ga Ummeynki tun ɗazu hankalinta a tashe yake". Amsa Ummey tayi cikin kula tace. "Boɗɗo na me sukayi miki?". Cikin yin ƙasa da murya tace. "Ummey na so sukayi su kashe miki jikarki tun baki ganta ba, dan Allah da Manzonsa Ummey na kizo gobe". Cikin kaɗuwa da begen son ganin Shatu da ƴar tata tace. "In Sha Allah Gobe za muzo tare da Abboi da izin Ubangiji". Cikin jin daɗi tace. "Alhamdulillah naji daɗi na, Gobe ina cikin gatana". Su kuma ta kalli Umaymah da ta shigo yanzu tare da cewa. "Alhamdulillah Umaymah na Gobe Ummey na zatazo da Bappa na da Deddena da Abboi". Cikin wani irin masha'hurin farin cikin alamun son tabbatuwar wani abu Umaymah tace. "Alhamdulillah Allah ya kawo mana su lfy". Amin Amin sukace baki ɗayansu.
Haka dai akayi wunin sunan jiki a mace da abinda ya faru.
Sai can da yamma ne da Afreen ɗin ta farka daga baccin suka ganta lfy lau kafin hankalin kowa ya kwanta. Nan Umaymah suka fito da kayan suna na gani na burgewa, da aka haɗawa mai jego da Ɗiyarta.
Kayan da Sheykh yayi musu kuwa abin sai dai ace son barka.
Gaba ɗaya wunin yau shima ya kasa fita ko nan da can tunda akayi sallan Jumma'a ya shigo ya wuce Side ɗinsa. Bini-bini ya kira Shatu ko Umaymah ya tambayi jikin yarinya.
Bayan sun dawo sallan la'asar ne. Jalal ya biyoshi har cikin falonshi, gefen Haroon ya zauna kana a hankali yace. "Shima sarkin al'adun sunan harda shi a sahun Magauta sai dai biya shi Hajia Mama tayi da dubu ɗari bakwai daga baya yace min tace in ƴar ta rasu zata cikata mishi dubu ɗari uku ya zama one million". Cikin mamaki Haroon yace. "Ikon Allah ikon gaske, wai ita wannan shegiyar matar meyasa bazamu fito mata a fili bane mu nuna mata mun san komai mu kuma juyo kanta". Cikin taune lips Sheykh yace. "Uhumm bazaku gane bane,". Da sauri Umaymah dake shigowa tace. "Ni na gaji bazamu gane me ɗin ba kuma". Cikin wani irin yanayi mai rauni cikin sanyi murya na rawa yace. "Affan ina ɗagawa Hajia Mama kafane sabida Affan ina jin takaici in na tuno a cikinta Affan ya fito, ku kun san waye Affan kun kuma san asalin zahirin gskyar so da ƙaunar da yake mana, kunsan yadda yake faman faɗa da yaƙin sauya mahaifiyarshi daga mummunan ɗabi'a eh zuwa kekkyawan ɗabi'a. Ta yaya zanci zarafin ta al'halin Affan ya ɗaukeni matsayin Uba ya ɗaukeni ciki ɗaya muka fito,kada ku manta son da Affan kewa Mameynmu Jalal ka duba tarin son da Affan yakeyi muku kaida Jamil. Ko a lahira wani kanci al'barkacin wani. Ina barine sabida ko Affan zai samu nasarar juya halinta". Ya ƙarashe mgnar hawaye na zubo mishi. Gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi tabbas sun san waye Affan ko su Jalal basa so da shaƙuwa dashi kamar Affan. A hankali yace. "Duk abinda nasa Affan zaiyi minshi babu musu koda baya son abin duk inda na aikeshi zaije min duk abinda na bashi zaɓi zaɓina yake bi, Affan da kanshi ya fara nuna min baya son inci abincin Hajia Mama wacce take uwace a garesa, yayi hakane sabida zargin tana samin abu a cikin abinci. Yasha yin kuka yana mgiya in ya tareta tana wani abun me zanyiwa Affan in nuna mishi halaccin ɗan uwantaka banda in rufawa mahaifiyarshi asiri". Shiru yayi ganin kiran Affan daya shigo wayarshi. Jiki a mace itama Umaymah ta zauna.
A hankali ya kara wayar a kunne bayan a amsa kiran. "Assalamu alaikum Hamma Jabeer". Affan ya faɗa cikin tsananin so da ladabi ga ɗan uwan nasa. "Wa alaikassalam Affan kana lfy". Sheykh yayi mgn yana mai jin wasu zafafan hawaye na tsastsafo mishi. Murmushi Affan yayi cikin yanayin shi na Happy mood yace. "Alhamdulillah Hamma Dr Akarmakallu Yah Sheykh, mun sauƙo lfy". Jingina bayan sa yayi da kujera tare da cewa. "Alhamdulillah Affan Allah yayi ma al'baka". Da sauri yace. "Amin Hammana".
Sai kuma yace. "Jamil ne yazo ya daukomu a airport to yanzu mun biya mun sauƙe Yah Sulaiman da Malam Abubakar. To gani tare dasu Giɗi ɗin yanzu su ina zamu kaisu, umarni nake jira Hamma?". Cikin sanyi yace. "Alhamdulillah Affan ku dawo dasu masarautar Joɗa ku wuce dasu Part ɗinsu Jalal a sauƙesu a can. Bawa Jamil wayar". Da sauri yace. "An gama sir yadda kace haka za'ayi ga Jamil ɗin". Ya kare mgnar yana miƙawa Jamil wayar. Saƙale wayar yayi da kafaɗarsa tare da cewa. "Assalamu alaikum Yah Sheykh". Gyaɗa al'kyabbar jikinshi yayi tare da cewa. "Wa alaikassalam Jamil ka kaisu part ɗinku ɗakinka ka nuna musu Bathroom suyi wonka. Aunty Rahma zata kawo musu abinci ka tabbatar sunci sun ƙoshi. Sannan Jalal zai ɗauki Dr Kabir zaizo ya dubasu in sunada matsalar lfy zai kula da komai". Cikin gamsuwa Jamil yace to yana kallon kekyawar fuskar Giɗi ta madubin motar.
Shi kuwa Sheykh a hankali yace. "Toh Umaymah a hakan ta yaya zan tozarta mahaifiyar Affan wanda duk munin halinta uwa dai uwace." Cikin rauni Umaymah tace. "Wannan hakane Jazlaan amman Hajia Mama tanayi mana illa a rayuwa". Sosai jikin Haroon yayi sanyi. Shi kuwa Sheykh Jalal ya kalla tare da cewa. "Kaje Valli ka taho da Dr Kabir". Jiki a mace Jalal yace to kana ya miƙe ya fita.
Umaymah na biye dashi a baya, har taje bakin ƙofar fita a hankali yace. "Ayyah Umaymah Ɗiyar taki ta kawo min ɗiyar tawa mana in ganta". Murmushi tayi tare da cewa. "Toh". Shi kuwa Haroon da sauri yace. "To bari in baka wuri dan nasan dai uwar ɗiya za'a gani ba ɗiyaba".
A hankali yace. "Mutun da abinsa". Dariya Haroon yayi kana ya nufi ƙofar da zata sadashi da Garden.
A hankali ta turo ƙofar Bedroom ɗinsa. Tare da cewa. "Assalamu alaikum". Cikin wani irin happy yace. "Wa alaikissalam". sai kuma ya juyo ya fuskanceta tare da buɗe mata hannunshi. Cikin sauri ta faɗa jikinshi ruggume da Afreen haɗe su yayi ya ruggume tare da cewa. "Alhamdulillah ya Allah ka tsare min ahlinna ka cika mana farin cikinmu".
"Amin ya Allah". Ta faɗa a hankali sai kuma ya jawo hannunta suka zauna a bakin gadon. Cikin narke fuska yace. "Nayi fushi Aish tun ɗazufa na aika kizo baki zoba sai yanzu". Cikin sanyi tace. "Ayyah Malam sallan la'asar nakeyi". Cikin sauri ya kalleta tare da cewa. "Kai haba dai Aish da gaske shine baki gaya minba yaushe kika fara salla". Murmushi tayi tare da cewa. "Yoh ai dama ina salla". Lakace hancinta yayi tare da cewa. "Batun gsky dai my dear yaushe kika samu tsarki?". Cikin nitsuwa tace. "Yau da safe, nai wonka naci gaba da salla tunda naga jinin biƙin ya ɗauke na samu tsarki". Kanshi ya gyaɗa tare da cewa. "Masha Allah, jego yayi kyau kenan Boɗɗo na, dama wasu matan kafin satin sunama sun samu tsarki sun fara salla, kinga kema kina ɗaya daga cikinsu wasu kuma sai anyi arba'in ma, wasu har hamsin suna likin. Koda yake ke dama al'adarma kwana uku kikeyi ko". Kai ta gyaɗa mishi. Hannunshi ya cusa ƙasan pillow'nshi tare da zaro key ɗin sabuwar mota dal a leda. Kamo hannun ta yayi ya danƙa mata key ɗin tare da cewa. "Al'ada kwana uku baƙi kwana bakwai kai naji daɗi na, na more". Da sauri ta buɗe tafin hannunta tare da kallon key ɗin sai kuma ta lumshe idonta jin ya manna mata tattausan lips ɗinsa a goshi ya sake mata sassayan kiss. Tare da cewa. "Taki ce motar sai dai bani son kiyi tuƙi nafi son a jamin ke, sai daifa bana miji zai jamin keba. Sara taki zata zama yar rakiyarki mai jan mota da tayaki kula da Babynmu, duk inda kuke in bana kusa daku. Gimbiya Aminatu zata bamu wata mai girki". Cikin wani irin farin cikin ta ruggumeshi gam-gam a jikinta. Da sauri yace. "Wayyo Aish zaki danne Mimi na". Da sauri ta kwantar da Afreen gefe, kana ta faɗa jikinshi ta rungume shi. Murmushi yayi mai cike da farin ciki cikin wasa yace. "Zaki bani abin daɗi?". Da sauri tace. "Ban workeba". Dariya mai ɗan sauti yayi tare da haɗe bakinsu wuri guda.
A part ɗinsu Jalal kuwa. Yah Giɗi Seyo Gaini ne zaune bayan duk sunyi wonka, sun saka sabbin kayan da Jamil ya zaro musu cikin durowarsa.
Cikin wani irin yanayin jin daɗin duniya da kuma bege da kewar iyaye da ƴan uwa wanda da sun cire tsammani. A hankali Yah Giɗi ya kalli Jamil dake miƙo mishi turare yana cewa. "Kai masha Allah sai kunga yadda kukayi kyau, farinku ya ƙara fitowa". Cikin rauni Giɗi yace. "Dan Allah bawan Allah, nan ina muke ne? Kuma ina wanda muka dawo dashi? Sannan ina za'a kaimu? Wayasa aka fito damu?". Da sauri Jamil ya zauna gabanshi kamo hannun shi yayi a hankali yace. "Nan kuna cikin Ɓadamaya ne, cikin masarautar Joɗa, wanda kuka dawo dashi kuma Yayana ne Affan ya tafi ƙofar matarshi. Wanda ya taimake ku yasa aka fitar daku kuma babban Yayanane Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa. Yana nan matarsa ta haihu yau akeyin suna. Sai in ya nitsu zaizo wurinku shi zai gaya muku ina za'a kaiku". Wasu irin hawaye ne suka tsunkowa Gaini murya na rawa yace. "Alhamdulillah kowa yace yaya zaiyi ya manta da Allahu wahidun ƙahharar sarki buwayi gagara misali mai badawa mai hanawa mai raya mai kashewa mai kawo sauƙi cikin tsanani mai yaye tsananin duhu ya wanzar da haske". Ido Jamil ya zuba musu cike da so da ƙaunar su, sai kuma ya kalli Seyo da yake zubda hawaye cikin sanyi yace. "Ko wanne hali ahlinmu ke ciki". Da sauri Jamil yace. "Yanzu muje falo kuci abinci kunji dan Allah ku bar kukan". Kasan cewar ya haɗa su da Allah yasa ba musu suka tashi. Amman badon hakaba farin cikin da suke ciki ya kori yunwa bare ƙishi.
A tsakiyar falon suka zauna. Jamil da kanshi ya zuba musu abincin da Aunty Rahma ta kawo musu. Sukaci suka sha.
Dai-dai lokacin kuma aka kira sallan magriba. Nan sukayi al'wala kana Jamil ya jasu sukayi jam'i.
Shatu kuwa bata bar ɗakin Sheykh ba saida ya tafi masallaci. Ta fito cike da farin ciki. Aunty Amina da Khadijah da Umaymah da Hibba ta samu a falonta Umaymah ta miƙa wa key ɗin tare da cewa. "Umaymah Yah Sheykh ya saya min mota". Cikin jin daɗi Umaymah tace. "Masha Allah. Allah ya sanya al'khairi". Amin Amin sukace baki ɗayansu. Kana duk sukayi al'wala haramar salla.
Ƙarfe goma da rabi. Duk baƙi sun watse. Sai su Umaymah da su Aunty Amina. A falon Shatu suke suna hirarsu cikin salama Ummi na ruggumi da Afreen. Umaymah kuwa na haɗawa Shatu tea da fifitashi da kyau. Aunty Rahma kuwa kitso Khadija keyi mata. Junainah da Ishma kuwa suna can babban falon da Hibba da Jalal.
Sara da Larai da indo hadimar Aunty Juwairiyya kuwa tattare kitchin sukeyi da kimtsa ko ina na gidan.
Sheykh kuwa a hankali ya jawo wayarshi daya tattare wacce yake waya da Hajia Mama da ita. Kiranta yayi. Tana amsawa yace. "Ƴar ta mutu ko?". Wani irin gigitaccen tsaki taja tare da cewa. "Inafa ta mutu na dai ji ta suma amman wannan Shegen yaron duk abinda nayi a kanshi ko matarsa yanzu dama yar tashi abun baya tasiri. Sannan babban tashin hankali na, shima Sarkin al'adun suna bai dawoba. Kuma wayarshi na shiga baya ɗagawa, tsorona kada dai sun ganeshi". Cikin sauya muryarsa ih zuwa muryar Jahan yace. "A a ba dai kamashi ba kam, sai dai ko in yana jin tsoron amsa kiran nakine sabida kada kiyi mishi faɗa tunda ƴar bata rasuba kada kice bai iya aikinsa bane a ganina fa shine yasa baya amsa kiran naki". Cikin tashin hankali tace. "Ni babbar matsala ma yau tunda gari ya waye hankalina yake a tashi zuciyata na tsinkewa gaba ɗaya tsoro ya rufeni ji nakeyi wani mugun abu yana tunkaro rayuwata, naje gidan boka kuma ya koroni shima sai tsalle yakeyi yana kaɗe jikinsa Wai komai na gab da dawo mana". Murmushi mai cike da jin daɗi yayi a ransa yake zaton ko shiryace zata zo mata, haka yasa yace. "Sai gobe zanzo muyi mgn in kaiki gidan wani sabon boka". Da sauri tace. "To".
Daga nan ya katse kiran. Kana ya miƙe ya fito falo, a hankali ya kalli Jalal da Hibba tare da cewa. "Jamil fa". "Yana Part ɗin mu". Jalal ya bashi amsa". To yace kana ya juyo ya kalli Yah Jafar da yanzu ya shigo kenan. A hankali ya tsaya gaban Sheykh. A hankali suka lumshe idonsu a tare, da sauri Sheykh da Jalal da Hibba suka matso kusa dashi sosai jin yana cewa. "Jabeer zuciyata na tsinkewa tun jiya sai inji kamar wani abu zai faru". Cike da mamaki Jalal yace. "Wlh nima tun jiya zuciyata ke tsinke kirjina yaita bugawa". Wani irin rumtse ido Sheykh yayi tare da cewa. "Nima abinda naketa fama dashi kenan tun jiya, to da Aisha ta suma sai nai zaton ko abinne ke samin tsinkewar zuciya. To kuwa still abin bai bariba saima ƙaruwar da yakeyi yana tsananta". Cikin sanyi Hibba tace. "To kuyi ta addu'a hakama Umaymah da Mamma da Aunty Rahma sukace suna ji". Kai suka gyaɗa gaba ɗaya. Hannun Yah Jafar ɗin Sheykh yaja suka nufi Part ɗin su Jamil.
Su kuwa su Jalal zama sukayi suna kallon Ishma da Junainah daketa sabgoginsu.
A hankali Sheykh ya zauna tare da kallon Jamil dake zaune tsakiyarsu Giɗi a hankali yace. "Ka barsu su huta mana". Cikin sanyi Jamil yace. "Allah ko Hamma Jabeer ina so in tafi wurin Khadijah ma sai inji zuciyata na tsinkewa kamar dai zan samu wani abu". Cikin kula Sheykh yace. "Uhmm duk haka mukeyi kaita mai-maita innalillahi wa innailaihi rajiun". To yace. Shi kuwa Sheykh nitse ya kalli Gaini da zai kai sa'an Affan. Cikin kula yace. "Sannunku da hanya". A tare sukace sannu.
Jamil ne ya ɗan kallesu tare da cewa. "Shine babban yayanmu Sheykh da yasa aka fito daku". Da sauri suka ɗan gyara zama suka matsoshi tare da cewa. "Allah sarki bawan Allah mun gode Matuƙa Allah ya saka da al'khairi ya kula da ahlinka fiye da yadda ka kula damu". Cikin jin daɗi yace. "Amin ya rabbil izzati, amman kuma duk haka ya farune sanadin Sulaiman da aka rufeshi tare daku". Cikin gamsuwa sakace. "Ayyah". Sai kuma Giɗi ya ɗan share hawayen da suka zubo mishi tare da cewa. "Ayyah bawan Allah yaushe zamu koma Rugar Bani muga Bappa da Inna da Ummey da Shatu da Junnu". Cikin gamsuwa da tausayinsu Sheykh yace. "In sha Allah nan kusa amman nafi son sai naga kunyi aski kun ƙara hutawa, gobe zuwa jibi da kaina zan medaku". Cikin wani irin masifeffen jin daɗi sukace. "Allah ya kaimu". "Amin Amin". Yace kana ya musu sai da safe.
Daga nan wurin Abbanshi da Lamiɗo da Galadima yaje suka ɗan yi wata mgnar kana ya dawo.
Ranar dai haka suka kwana gaba dayansu babu wanda yayi isasshen bacci sabida masifar bugawa da ƙirazansu keyi.
A can Rugar Bani kuwa. Ko abincin dare Ummey bata iya ciba. Haka nan sai taji zuciyarta na tsinkewa yana bugawa. Tun abun bai damunta har ta gayawa Bappa, so ya bata ƙarfin guiwa da yin addu'a.
*Ba'ana* Zaune yake gaban yaransa cikin rauni da yanayin damuwa yace. "Nanda wata uku masu zuwa zan koma ƙasar Nigeria zanyi yaƙin neman Shatu koda zan rasa rainane, zan koma gareta. Zan gaya mata ko mutuwa nayi sonta ne ajali na". Cikin bashi ƙarfin guiwa ɗaya daga cikinsu yace. "Zama kayi nasara". A hankali yace. "Babu tabbas, domin tunda na rasa Shatu nakega nayi rashin babbar nasara". Sai kuma ya miƙe ya shiga cikin ƴar ƙaramar bukkarsa.
Murmushi Baron yayi tare da katse kiran da yayi Sheykh yana jin duk bayanan Ba'ana. Dan shi Baroon yanzu ya zama ɗan aikin Sheykh dan tun zuwansa lokacin ciwon hannun Shatu. Da fari har yasa a kirasa daga baya yasa aka dawo dashi. Ya biyashi kuɗi masu tarin yawa, yayi mishi duk bayanin ɗaya nema, kana yasashi ya koma wurin Ba'ana kuma ya naɗo mishi rahoto da duk wani motsin Ba'ana yana turo mishi. Alhamdulillah kuma yanzu duk shirin kama Ba'ana yakeyi.
Washe gari ranar asabar yau babu aiki. Da misalin ƙarfe goma na safe jirginsu Abboi ya sauƙa cikin birnin Ɓadamaya.
Kai tsaye Salmanu yayi musu jagora zuwa Rugar Bani dan a take suna sauƙa wasu tsala-tsalan motoci guda biyar suka iso wanda dama su tun jiya suka iso. A ƙasan plate number motocin akwai tambarin hatimin kan shanu a ƙasa ansa Abboi, irin tambarin dake jikin jiragen Abboi kenan.
Suna zuwa kuwa babu ɓata lokacin suka isa har cikin gida. Inda nan Arɗo Bani da kanshi da sauran dattawan sukazo. Bayan sun gaggaisane Abboi ya ɗan yi gyaran murya tare da cewa. "Toh Alhamdulillah lallai komai yayi forko to tabbas yana da ƙarshe, to bayan bincike da bin diddigi dai mun gama fahimtar inane asalin wannan baiwar Allah'n kuma munada yaƙinin daga masararutar Joɗa ta fito. To yau dai kam ranar data kamata mu shiga da ita ciki da yardar ubangiji tazo. Kamar yadda muka tsara, yanzu zamu tafi". Cikin tsananin jin daɗi da kuma fargabar ko ya al'amarin zai kasance Bappa yace. "Alhamdulillah mu duk a shirye muke, fatanmu Allah yasa ina munje ta tuna baya, ta tuno ita wacece". Da sauri Arɗo Bani yace. "In Sha Allah ma zata tuna Malam Babayo". "Allah yasa haka". Al'ameen ya faɗa. Amin Amin sukace kana duk suka miƙe suka fito.
Kana Bappa yazo yacewa Ummey da Dedde su fito. Nan suka mara musu baya.
Mota ɗaya Bappa da Abboi da Arɗo Bani suka shiga. Ummey da Dadde da Al'ameen kuwa suma mota ɗaya suka shiga. Sauran kuma ƴan tsaronsu ne a ciki sai motar Yah Salmanu da Hafsi ƙanwar Shatu a haka suka fito daga Rugar Bani suka nufi Masarautar Joɗa.
A hankali Ummey ta jingine kanta da jikin kujera tare da dafe ƙahon zuciyarta a hankali ta furta innalillahi wa innailaihi rajiun". Sabida tsananin tsinkewar da zuciyarta keyi Dedde kuwa hankalinta naga makiyayan dake zirya.
A nan cikin birnin Ɓadamaya a tsakiyar Masarautar Joɗa kuwa.
Gaba ɗaya su Umaymah suna falon Shatu. Aunty Rahma ce da su Sara a kitchin, Aunty Juwairiyya tana part ɗinta da Hibba.
Junainah da Ishma kuwa suna kitchen tare da Aunty Rahma. Kowa sabgar gabansa keyi. A hankali Shatu ta miƙe ta nufi ƙofar falon Sheykh da sallama a bakinta.
Shiru ba kowa a falon tray'n breakfast ɗinshi shida Haroon ta ajiye bisa Dinning table. Ganin ba kowane yasa ta turo kanta cikin bedroom ɗin.
Shiru ba kowa a hankali ta ƙara so ciki tana cewa. "Salam Yah Sheykh". Ƙofar bathroom ta matso a hankali ta tura ba kowa a ciki komai yana kimtse tsab-tsab. "Toh ina yaje kuma yau Lahadi kuma ai babu inda zaije". Shiru tayi tare da juyowa ta matso tsakiyar ɗakin jujjuya kanta tayi ba mutun ba alaman mutun a ɗaki. Har ta juya zata fita, sai kuma tayi sauri ta juyo tazo bakin gadonshi, abun data hanƙo ƙasan pillow'nshi ne yasa ta sunkuyowa da sauri hannunta tasa ta zaronshi. "Innalillahi wa innailaihi rajiun". Ta faɗa jiki na rawa tare da sakin fuskar robar da Sheykh ake amfani da ita a matsayin Jahan. Da sauri ta juyo da nufin zata fita, sabida tsoron daya rufeta. Sai kuma tayi sauri taja da baya tare da zare idanunta dai-dai lokacin da ta iso jikin marfin wodurob ɗin sa Wanda yayi dai-dai da lokacin da Sheykh ya turo marfi ya fito. A gigice take jujjuya kai tare da zaro ido. Sai kuma ta juya da sauri ta kalli fuskarnar da ƙarfi ta buɗe baki tare da cewa. "Innalillahi wa innailaihi rajiun Yah Sheykh". Da sauri yasa hannunshi ya kamo nata ya fizgota jikinshi cikin haɗe fuskarsu wuri ɗaya yace. "Na'am Aysha please kada kiyi ihu tsaya nitsu nine Muhammad Jabeer Yah Sheykh mijinki Abu Afreen". Cikin yanayi kaɗuwa tace. "Yah Sheykh kai mutum ne ko al'jan". Da sauri ya kamo hannunta suka iso gaba durowar. Buɗe ƙofar yayi, kana a hankali yasa hannunshin ya ture, al'kyabbas ɗin shi dake jere a hanga a saƙale, sai ga wani ƙofa mai kamar glass. A hankali yace. "Aysha nitsu ki jini kinji ko". Cikin sauƙe numfashi tace. "Toh". Kanshi ya gyaɗa kana a hankali yace. "Kinga wannan wurin ko?". Da sauri tace. "Eh naga kamar ƙofa ne". Jawota yayi suka ɗan matso hannunshi yasa ya tura ƙofar da sauri tace. "Lahh". Sabida ganin wata ƴar siririyar hanya mai tsawo. A hankali yace. "Ni mutum ne Aish yanayin tsarin masararutar Joɗa ne yasa dole nake amfani da wasu ababen. Kinga wanan hanyar har cikin bedroom ɗin Lamiɗo da Abba na duk akwai su. Muna haɗuwa dasu a ɗakin Lamiɗo lokuta da dama. In kina so anjima zan nuna miki, dan yanzu Lamiɗo ya rufe ƙofarsa ne da yanzu zamuje". Da sauri tace. "Me kukeyi a ɓoyen". Jawo ƙofar yayi ya rufe kana a hankali yace. "Ina wani aikine Aish Kuma aikin sirrine, tsawon shekaru inayi babu wanda ya sani sai Lamiɗo da Abba na da Umaymah sai yau kuma da kika zama ta uku". Ya ƙarashe mgnar yana jawota suka zauna bakin gado. A hankali ta sauƙe numfashi ido ta zuba mishi a hankali tace. "Kai SS ne ko Yah Sheykh?". Murmushi yayi tare da cewa. "Ba'a faɗa kiyi shiru kada wani yaji kinji ko sirri ne Boɗɗo na". Murmushi mai cike da jijjina tayi mishi. Shi kuwa ruggume ta yayi ya koma baya ya kwanta.
Dai-dai lokacin kuwa motar Salmanu dake gaban motocin su Abboi ta kusa kai cikin matsarautar Joɗa bayan an wangale musu gate.
Wani irin rumtse ido da ƙarfi Ummey tayi tare dasa kanta bisa guiwowinta sabida wani irin masifeffen tsarawa da kanta yayi da azaban ƙarfi.
Kai tsaye bakin part ɗin su Sheykh Salmanu ya nufa dasu sai dai Motar Abboi da sauran duk a can baya bakin fada suka tsaya inda Bappa ya nuna musu.
Yadda suke ƙara kusanto Part ɗin su haka sarawa da bugun zuciyar da Ummey keyi yake ƙaruwa.
A can cikin falon Shatu ma, da sauri Umaymah da Mamma Suka kalli juna sabida masifar bugawa da ƙirazansu sukayi.
Sheykh kuwa da ƙarfi ya ruggume Shatu sabida ji yayi tamkar zuciyarsa zata faso ƙirjinsa ta fito woje. Jalal da ke Part ɗin Yah Jafar da sauri ya rumtse idanunshi shida Yah Jafar ɗin.
Hakama Jamil dake tare dasu Gaini.
A hankali motocin sukayi parking. Ummey kuwa wani irin ƙara rumtse idanunta tayi da masifan karfi. Dedde kuwa a hankali ta buɗe ƙofar. Ta sako ƙafarsa cikin shigarta ta al'farma.
Shi kuwa Al'ameen da sauri ya zagayo ya buɗe wa Ummey kofar tare da cewa. "Ummey mun iso bismillah". Cikin tsananin danne sarawar da kanta keyi ta ɗago jajayen idanunta a hankali ta zuro ƙafafuwan woje.
Ras ras Din dab din dab haka zuciyarta ta bada wasu tagwayen bugu. Da sauri tasa hannunta ta dafe ƙirjinta. Dedde kuwa a hankali ta zagayo inda take. Shi kuwa Al'ameen a hankali yace. "Bismillah ku shiga ga ƙofar". A hankali Dedde tace to kana ta nufi ƙofar. Ita kuwa Ummey cikin rawan jiki ta ɗaga ƙafarta ta dama ta ɗaura kan barandar tare da ƙara dafe ƙirjinta da rumtse idanunta sabida jujjuyawan da kanta ya fara. Shi kuwa Al'ameeen bayansu yabi.
Shi kuwa Salmanu a hankali ya kalli Hafsi ƙanwar Shatu dake bin Khadijah. Cikin yin ƙasa da murya yace. "Ko in ɗagaki ne in kaiki". Cikin jin kunya tace. "A a Yah Salmanu zan shiga da ƙafata".
Su Bappa kuwa Sarkin ƙofa ne yayi musu iso zuwa cikin fada.
A hankali Dedde ta kai hannunta ta kama handil ɗin ƙofar falon ta murɗa tare da turawa kana tasa ƙafarta ta dama ciki bakinta ɗauke da sallama.
Aunty Rahma dake fitowa daga kitchen Junainah na biye da ita da sauri ta ɗan juyo ta kalli Dedde tare da cewa. "Wa alaikassalam". Ta ƙarashe amsa sallamar tana matsowa dan ganin wani irin fitinenne kama da Dedde keyi da Shatu.
Da sauri ta juyo bayanta jin Junainah na cewa. "Lah Oyoyo Dedde".
Dai-dai lokacin kuma Ummey ta ƙarasa shigowa ciki wanda hakan yayi dai-dai da bugawar da kanta yayi wanda saida tayi sauri sa hannunta duka y ta damƙe kanta da masifan karfi tare da cewa. "Innalillahi wa innailaihi rajiun". Da ƙarfi wanda haka yasa Dedde juyowa ta fuskanceta sanadin juyawar da Dedde tayi kuma ya bawa Aunty Rahma da Junainah damar ganin fuskar Ummey da kyau. Wani irin sauri Junainah tayi ta nufi inda suke ganin yadda gaba ɗaya jikin Ummeynta yake karkarwa da tsuma.
Aunty Rahma kuwa cikin wani irin tsananin firgita da kaɗuwa ta zazzaro idanunta waje har kamar zasu faɗo. Wani irin taku mai cike da firgici tayi tana matsowa gaban Ummey dake jujjuyawa tana mai-mai-ta. "Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani'imanwakil". Wani irin matsowa kusa da ita Aunty Rahma tayi tare da buɗe baki da ƙarfi tace. "La ha ila ha illahu Muhammadu Rasulullahi Sallallahu alaihi Wasallama. Aunty Mamey!." Ta ƙarashe kiran da azaban ƙarfi da rakaɗi. Ummey kuwa. Kiranta da Aunty Rahma tayi yasata ƙara gigicewa. Karkar haka jikinta ke rawa. Cikin wani irin gigitaccen murya Aunty Rahma ta fara rabkawa ahlinta kira. "Umaymah! Mamma Jazlaan ga Aunty Mamey ta dawo da izinin ubangiji Jazlaan, Jafar, Jalal, Jamil, Umaymah. Kuzo ga Aunty Mamey...". Wani irin azabebben zabura...!
Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k ne kacal zaki turo ta asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Normal group Kuma 300 zaki turo ta asusuna ɗin sai kuyi screenshort na Debit Alert din ku turo min ta whatsApp 09097853276.
By GARKUWAN FULANI