Garkuwa complete novel - Chapter 82
Garkuwa complete novel Chapter 82: Garkuwa complete novel Chapter 82. Sai ya kuma sake baiyana ya kuma bace, saida yayi haka sau uku kana ya ɓace sai…
4,385 words
Sai ya kuma sake baiyana ya kuma bace, saida yayi haka sau uku kana ya ɓace sai muryarsa ke tashin cikin rauni yace. "Baroon kaci amanata ina sane na Barka. Nayi hakane dan ka jawo shi wannan mai jajayen kunnuwa ya kawo min ita har nan. Ku a zatonku tarkonku na faɗa baku san cewa nawa tarkon kuka faɗa ba sa'ansu ɗaya nayi tuba na gaske bazan sake kashe raiba." Sai ya kuma bayyana still hannunshi riƙe da hannun Shatu cikin rauni murya na rawa tace. "Ayyah Yah Ba'ana dan Allah ka sakeni kada ka rabani da ƴan uwana da ƴata".
Wani irin jujjuya kai yayi tare da cewa. "Bappa kun kasa cika min al'ƙawarin da kukayi min ko. Kai kuma Baroon kaci amanata ka muna furceni. Shatu ke kuwa kin yiwa soyayya ta ta gsky riƙon sakainar kashi. Wani abu kuke tunanin zaifi min ciwo da zafi sama da rabuwa da Shatu". Sai kuma ya kalli Sheykh daya zuba mishi ido yana takaronto addu'o'i babu ƙaƙƙautawa ido cikin ido ya tsare Ba'ana da ido. Shi kuwa Ba'ana murya a mace yace. "Ko na bar barun a raye kaima watan wata rana zai ci amanarka tabbas zaici amanarka maci amana kuwa gubane". Cikin sauri suka juyo kan Baroon daya saki wata iriyar gigitaciyar ƙara tare da komawa bayan Sheykh. Shi kuwa Sheykh ido ya zubawa inda Shatu take tana nufoshi alamun Ba'ana na matsowa inda yake. Da sauri sojojin dake wojen suka shigo da gudu
Lokaci ɗaya mutane suka fara tururuwan shigowa gidan sabida ihun da Baroon yakeyi yana kiran sunan Ba'ana yana bashi haƙuri.
Jalal kuwa da sauri ya kuma nufo inda Shatu take wanda da ita suke gane inda Ba'ana yake. Cikin tsoron kada ya cutar da Sheykh ya nufosu. Gib ya kuma ture Jalal tare da cewa. "Ummey ki gayawa wannan yaron zan illatashi fa ya dena matsowa inda nake". Gaba ɗaya tsoro ya rufesu jin furucinsa.
Jalal kuwa hatsala iya hatsala ya hatsalo allurar ta motso to amman kuma faɗa da Ba'ana tamkar faɗa da iska mai kaɗawa ne ko kuma duhu. Da sauri Ba'ana ya juyo kawai sai ya fara dukan sojojin nan baki ɗayansu. Ya bugi wannan ta nan ya bugu wan can ta can. Kana ya haɗa da shaƙo wuyan Baroon. Kurma ihu da kakarin mutuwa Baroon yakeyi da ƙarfi. Wanda yasa gaba ɗaya gidan ya cika da mutane. Harda su Arɗo Bani. Bukar da Bugulu kuwa gefen Bappa suka tsaya suna kekrketa dariyar mugunta.
Junaidu kuwa gefen Junainah dake ta kuma ta tsaya yana bata baki.
Gaba ɗaya hankalin mutane ya tashi. Su Bappa da Arɗo bani da sauran dattawan Rugar Bani duk sai haƙuri suke bawa Ba'ana sabida ganin yadda yaketa dukansu Jalal ba sauƙi.
Ita kuwa Shatu da gudu ta faɗa jikin Sheykh sabida saketa da Ba'ana yayi.
Ganin ta nufi wurin Sheykh ne ya sashi sakin wuyan Baroon tare da barin dukan su Jalal. Ya nufo kansu Sheykh da Shatu. Cikin tsananin ruɗani Shatun ke cewa. "Yah Sheykh mu gudu zai maka illa". Jamil kuwa tuni ya fara aikinshi. Affan kuwa da Yah Jafar Kara matsowa kusa da Sheykh suke gudun kada a cutar dashi. Aunty Juwairiyya da Ummi da Sara da inna Amarya kuwa gaba ɗaya jikinsu rawa yakeyi.
Shi kuwa Sheykh murmushi yayi jin Shatu tace. "Wayyoooooooo Allah Yah Ba'ana ka sakeni". Hakane yasa ya fahimci Ba'ana na kusa dashi. Ido ya lumshe tare da ɗago hannunshi kana a hankali yace. "Bismillahi". Yana faɗin haka yaji hannunshi ya sauƙa kan hannun Ba'ana kuma ya baiyyana kowa na ganinshi. Cikin nitsuwa Sheykh ya fara karanto Ayatulkursi'u yana mai kallon Ba'ana ido cikin ido wanda a take ya karya duk wani sihirin da Ba'ana ke tutiya da tinkaho dashi da ayar Allah. (Haske ya kori duhu)
Da sauri Shatu ta koma bayan Sheykh ɗin. Shi kuwa Sheykh juyowa yayi ya kalli su Jalal daketa haki cikin haki da tsananin tafasar zuciya suka nufosu.
Shi kuwa Sheykh ido ya zubawa Ba'ana ganin yadda yaketa fiffizgewa da buga ƙafarshi ta dama da ƙasa amman ina ya kasa ɓacewa.
Cikin sanyi yace. "Jalal ku kamashi da sunan Allah bazai sake ɓacewa ba har abadan da izinin ubangiji".
Ai kuwa da sauri Jalal yasa hannunshi ya damƙo wuyan Ba'ana tare da cewa. "Bismillahi". Ai kuwa bai ɓace ɗinba.
Cikin wani irin tafasan zuciya da zafin yadda Ba'ana yayi ta libgarsu kamar shine sojan sune masu laifi cikin takaicin. Yayi mishi wani irin azabebben shaƙa tare da kima mishi naushi a cikinsa tare da kalmar "Bismillahi". Wani irin azabebben ihu mai rakaɗi da baiyyana azabar da yaji yace. "Wayyoooooooo Allah na rana,". Cikin haki Jalal ya kuma haɗa mishi wani naushin tare da cewa. "Kasan Allah ne kafurin banza matsafi". Dai-dai lokacin kuma sauran abokanshi sojojin suka rufe Ba'ana da azabebben duka da ammaton sunan Allah wanda hakan ke ƙara kwance duk wani ɗaurin sihirin dake jikin Ba'ana.
"Ya ilahi ya mujibadda'awati." Mamey da Ummi ke faɗi sabida wani irin dukan zaban da su Jalal keyiwa Ba'ana.
Ita kuwa Shatu cikin tsananin tsoro da kerma ta ɗan leƙo. Dai-dai lokacin Khalid ya murɗe hannun Ba'ana ɓas ya bada sautin karyewa. Da sauri ta rumtse idanunta tare da sakin wani irin kuka mai ciwo a rai. Da sauri Sheykh ya juyo yana kallonta.
Bappa kuwa dasu Arɗo Bani dasu Yah Jafar kab Bukar da Bugulu suke kallo wa ɗan da suke wani irin kuka mai cike da tashin hankali. Jamil da Affan kuwa sarawa su Jalal sukayi.
Mutanen Rugar Bani kuwa kab suna tsaye wasu tuni hawaye na zubo musu.
Da ƙarfi Ba'ana yayi wani irin azabebben ihu da kururuwa sabida taka hannunshi da Khalid ya karya. Wanda Umar yayi ɗaya sojan ya murza tare da buga mishi naushin da saida yayi birgiman kule ya iso har gaban Sheykh.
Cikin rauni da azabar raɗaɗi murya na rawa yace. "Mata! Mata zasu kasheni!". Cikin wani irin rauni da tsananin tausayi wani irin masifeffen kuka mai ƙarfi yan kwacewa Shatu.
Da sauri ta zame har ƙasa ta durƙusa. Sabida wani irin azabebben tokara da guiwa da Jalal yayi mishi bisa tsakiyar bayanshi. A take sai ga jini ta hancinsa da bakinsa.
Murya na rawa cike da rauni Shatu ta ɗago kanta. Ta kalli Jalal dasu Khalid kana ta kalli jinin bakinshi daya ɗan tsallo ya taɓa farin gyalen jikinta. Wani irin kukane mai cike da tsananin tausayi rauni ta fashe dashi tare da cewa. "Ayyah Jalal dan Allah ku barshi kada ku kasheshi ku barshi dan Allah".
A hankali Jalal ya ɗan tsaya yana maida wani irin azabebben numfashin haƙi.
Sheykh kuwa wani irin kallo mai cike da azabebben kishi ya watsawa Shatu. Tare da sa tafin hannunshi ya tallabe haɓarshi. Kana ya jingina kanshi da jikin bishiyar yana mai kallonsu.
Mamey kuwa itama zamewa tayi tanamai sakin kuka. Ummi, Inna Amarya, Aunty Juwairiyya, Sara, dama duk sauran matan dake wurin wasu irin hawaye ne masu zafi suka tsastsafo musu.
Junainah kuwa zuwa tayi ta durƙushe gaban Ba'ana gefen Shatu cikin wani irin azabebben kuka mai cike da rauni tace. "Wayyo Yah Ba'ana Dan Allah Adda Shatu ki hanasu dukanshi."
Da ƙarfi Junainah ta faɗa jikin Shatu lokacin da Jalal yayi wani irin juyi ya kifawa Ba'ana wani irin masifeffen mari da tafin ƙafarsa. Tare da cewa. "Wato kai gaka shege har zaka sa hannu ka daki jamin soja". Wani irin azabebben karkarwa jikin Ba'ana ya farayi tamkar mazari.
Wani irin kuka mai azabar ciwo da cin rai Bukar da Bugulu suka saki sabida ganin yadda hukuma ke azabtar da Ba'ana tamkar zasu ɗauke ransa.
Cikin rauni murya na rawa ido na zubda hawaye Mamey tace. "Jalaluddin ku bar dukanshi". A hankali Jalal ya koma baya ya zauna bisa dakalin ƙofar ɗakinsu Giɗi. Sabida yasan muddin Mamey ta kirashi da sunanshi kai tsaye to abu ya ta'azzara gareta. Domin Babana take kiranshi, sai gashi yau full name ɗinshi ta kira bama Jalal kawai ba.
Sai kuma ta kalli su Khalid kana ta juyo ta kalli Sheykh murya na rawa tace. "Muhammad ka hanasu dukanshi". Cikin wani irin yanayi Sheykh ya ɗagawa su Khalid hannu. Haka yasa suma suka koma gefen Jalal suka zauna suna haki da maida numfashi.
Shi kuwa Sheykh ido ya zubawa Shatu dake kuka tamkar ranta zai fita.
Gaba ɗaya wurin babu wanda rauni bai darsu bisa zuciyarsa ba.
Yah Jafar da Bappa kuwa tuni hawaye suke zubdawa.
Bukar da Bugulu kuwa da rarrafe suka iso gareshi.
Shi kuwa Ba'ana wani irin dogon numfashi mai cike da azaba rauni nadama ya fesar a wahalce kana a hankali ya fara yunƙurin tashi zaune. Amman Ina ya kasa ganin hakane yasa Bukar yin sauri yasa hannunshin ya tallaboshi ya ɗagoshi. Ya jingina bayan Ba'ana nan da kirjinsa. Ya zama suna fuskantar Shatu dake kuka tamkar ranta zai bar gangar jikinta gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi. Cikin wani irin rauni murya na rawa yace. "Mata!". Da sauri ta ɗago jajayen idanunta ta ɗaurasu kanshi. Wanda haka yasa ta saki wani sabon kuka, Junainah ma kukan ta saki da ƙarfi. Shi kuwa Ba'ana hawaye na kwarya yana ƙore jinin hancinsa da bakinsa murya can ƙasan maƙoshi yace. "Mata". Murya na rawa kuka na kumbe mata tace. "Na'am Yah Ba'ana". Wani irin murmushi mai rauni yayi kana a hankali yace. "Mata Ranar da nake tsoro tazo, ranar da na gaya miki zata iya ɓaci zata zo, gata yau tazo". Sai kuma ya ɗago ɗaya hannun nashi mai lafiyar ya sharce hawayensa, cikin sanyi ya jujjuya kanshi dake masifar mishi ciwo. Ido ya zuba mata ganin yadda take kuka har numfashin ta na fizga. A hankali yace. "Shatu kin san son da nake miki gsky ne?". Cikin kuka tace. "Na sani Yah Ba'ana na sani son da kake min gsky ne". Wani dogon ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe tare da cewa. "Alhamdulillah". Sai kuma ga hawaye shar-shar bisa fuskarshi.
Cikin rauni yace. "Ke kuma kin taɓa sona a ranki da gsky?". Kanta ta fara ɗan bugawa da ƙafar Sheykh dake gefenta. Tare da cewa. "Eh eh eh Yah Ba'ana na soka so na gsky na soka so irin wanda naso mu gudu tare mu tsira tare nasoka irin son da nake yiwa Yah Al'ameen sabida bana son irin wannan ranar tazo mana". Kanshi ya jujjuya kana cikin rauni yace. "Shatu haka ƙaddarar rayuwata take."
Sai kuma ya kalli Junainah a hankali yace. "Junnu me yasa kike kuka, bakya son a kashenine". Cikin kuka tace. "Bana son a kasheka Yah Ba'ana. Ina sonka kamar yadda nake son sun Yah Giɗi". A hankali ya sunkuyar da kanshi tare da sakin wani irin raunataccen kuka wanda saida Affan ya zubda hawaye.
Cikin sanyi yace. "Mata ina ƴarmu?". Cikin wani irin rawan jiki hawaye na kwarya. A hankali tasa hannunta ta amshi Afreen dake hannun Ummi. Kana ta juyo da rarrafe tamkar ƙaramar yarinya ta iso gabanshi cikin rawan murya tace. "Gata nan Yah Ba'ana".
Wani irin murmushi mai yelwa yayi wanda saida fararen haƙoranshi suka fito ras. Da idonshi ya nuna mata cinyarshi. Cikin kuka ta sunkuyo ta kwantar mishi da Afreen bisa cinyarshi.
Kana ta kife kanta cikin cinyoyinta ta saki kuka.
Shima kukan ya saki mai rauni. Kana yasa tafin hannunshi ya shafi kan tattausan suman gashin Afreen hawayenshi na kwarya suna ɗiga kan goshinta. A hankali yace. "Masha Allah, Allah ya raya mana ita bisa imani al'farma Annabi da al'ƙur'ani Allah yasa mahaddaciyar al'ƙur'ani ce, ya azur tata da miji na gari". Karo na forko da Sheykh ya motsa lips ɗin shi a hankali yace. "Amin ya Allah". Sabida daɗin Addu'ar da akayiwa ƴarshi.
Itama Shatu cikin kuka tace. "Amin thumma Amin". Sai kuma ta ɗago kanta a hankali jin yana cewa. "Naji lbrin Ummey ta tuno baya ta gane ahlinta ance min ma wai ɗan ta ne ya aureki ko?". Ina ta kasa mgn sai kuka, Ummeyn ce ta sharce hawayenta a hankali tace. "Eh Ba'ana na tuno baya, na gano ahlina Allah ya saka da al'khairi ya biyaka da mafi kyawun sakamako". Cikin rauni yace. "Amin Amin Ummey". Sai kuma ya kalli Bappa dake ta kuka a hankali yace. "Bappa kana kukan baka cika min al'ƙawarin da kayi bane?". Da sauri Bappa ya gyaɗa kai alamar eh. Kai ya jujjuya kana a hankali yace. "Ba laifinka bane, ƙudirin ubangijine ba gashi yanzu Ɗiyar Shatu ce a cinyata, wani bazai haifi ɗan wani ba ai. Ni na yafe muku yanzu na yarda na gane komai nufin Allah ne. Sai dai kuma ina neman yafiyarku al'ummar Rugar Bani baki ɗaya busa duk wata cutarwa da nayi muku." Sai ya kuma kalli ɗaya daga cikin yaransa da suka shigo tare a hankali yace. "Koda bana da halin muku bayani, ga Droo zai muku dukkan bayanin abinda ke tafe, gaba ɗaya na mishi bayanin komai kafin mu taho". Sai kuma yayi shiru jin duk anyi shiru ana jinshi sai shessheƙan kukan Shatu dake tashi. Kalato yawun bakinshi yayi ya haɗiye sabida wata irin azabebben ƙishin da yakeji tamkar zai kashesa.
A hankali ya kalli Ummey cikin rauni yace. "Ummey ƙishi nakeji ki sanmin ruwa". Yayi mgnar yana kallon Shatu data zuba mishi ido da sauri. Ya sani ta tuno bayanin daya taɓa yi matane na cewa in an bashi ruwa yasha zai ɓace zai tsiri.
Haƙƙun kuwa itama abinda ta tuno ɗin kenan sai dai bata saniba ya kakkarya duk waɗan nan abubuwan. Cikin rani yace. "Shatu Insha". Yace lokacin daya amshi kofin ruwan da Ummey ta miƙo mishi. Shiru batayi mgna ba sai kukanta daya ƙaru.
Sheykh kuwa zuwa yanzu Allah ne kaɗai yasan abin da yakeji a zuciyarsa sabida azabar zafin kishi.
A hankali murya na rawa ido na zubda hawaye yace. "Mata ina sha, ko kada insha zaki gaya musu, ki gaya musu mana". Da sauri Jalal yace. "Adda Shatu menene wani tsafin zaiyi ne?".
Da sauri ta kalli Jalal kana ta juyo ta kalli Ba'ana ta kuma juyowa ta kalli Sheykh. Cikin sanyi murya na rawa tace. "Ka." Dai-dai lokacin kuma Baroon yasa hannunshi ya bugi ruwan tare da cewa. "Idan yasha zai ɓace ne fa". Yayi mgnar sabida baisan Ba'ana ya ƙauracewa tsafi da asirce-asircen ba. A hankali ya juyo ya kalli Shatu tare da cewa. "Ƙarasa mgnarki domin itace kamar zaɓin rayuwata da mutuwa ta."
A hankali tasa hannunta ta ɗauki Afreen dake kallon fuskarshi tana wasa. Cikin rauni tace. "Kada ka sha Yah Ba'ana ka bari hukuma tayi maka hukuncin daya dace da kai".
Yana zubda hawaye yace. "Uhummm to shike nan Mata. Amman nasa baki san me nake aikatawa ba shiyasa kike tunanin hukuncin hukuma zai rageni da rai". Da sauri ta nufi cikin ɗaki tana kuka.
Kana su Jalal kuma suka kamashi sukasa a motarsu sukayi gaba dashi.
Su kuwa Bukar da Bugulu da kuka suka tafi. Yayinda duk mutane ke zubda hawaye.
Bayan anyi sallan la'asar ne. Sheykh yace su fito su tafi cikin disashewar murya Shatu tace. "Jamil aini zan kwana biyu". Kai Jamil ya ɗan juya yace. "A a Yah Sheykh yace ki fito mu tafi, wai ya fasa baza ki kwana ba". Jin haka yasa Inna Amarya dasu Giɗi da Gaini da Seyo da yanzu suka dawo sukace. Tabi umarnin mijinta. Dole haka ta fito suka tafi, harda Junainah.
Gaba ɗaya Rugar Bani tayi shiru tayi sanyi tamkar waɗanda akayiwa mutuwa.
A can masaraur Joɗa kuwa. Cikin wani irin ƙunan rai Sheykh ya kalli A....!
Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300 a yawan posting ne babbancinsu yake. Idan kinaso turo kuɗin ta Account 0005388578 Jaiz Bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai kiyi screenshort na Debit Alert ki turo ta WhatsApp 09097853276. Sai in saki a group, ku ƴan 300 in baki da damar biya ta Account to ki sayi katin Mtn na ɗari uku kacal ki copy numbers ɗin ki turo min ta whatsApp 09097853276. Banbancin special Group da Normal group a yawan posting ne kada kizo kice in miki ƙarin bayani ɗan Allah By
Ƙarfe huɗu dai-dai, na yamma, wasu irin motoci ne masu masifar kyau da tsaruwa. Suke kutsa kai cikin airport ɗin, wanda a ƙalla sun kai bakwai. bisa alamu duk akwai cikekken nasaba da dama, dan har can asalin wurin da jirgi yake biyu daga cikin motocin suka wuce. Kana biyar kuma suka tsaya a ainihin harabar. A hankali aka buɗe motocin. Alhaji Abboi ne ya fara fitowa. Sai Bappa kana Al'ameen da wasu matasa uku masu kama da Al'ameen sai wata kekkyawar budurwa mai kama da Shatu sak wacce take riƙe da hannun Junainah. Sai Ummey da Inna Amarya da suka fito. Bisa alamu duka, sauran rakiya sukayiwa su Bappa. Gyara tsayuwarsu sukayi dan ganin matafiya nata shiga cikin jirgi, wanda yake ɗauke da tambarin Abboi. Cikin murmushi Appa ya miƙawa Bappa hannu sukayi musabaha kana a hankali yace. "Toh Malam Babayo Allah ya maidaku lfy ya kiyaye hanya". Cikin jin daɗi Bappa yace. "Amin Amin Abboi Ubangiji ya saka maka da mafi kyawun sakamako". Cikin jin daɗin Addu'a Al'ameen da saura zaratan samarin nan sukace. "Amin ya Allah". Sai kuma sukayi shiru jin Appa na cewa. "In kun isa ka gaida min Parvina da kyau, kana aci gaba da ɓoye mata abinda mu muka fahimta, har sai lokacin da ido zaiga ido muna da kekkyawan yaƙinin duk sanda taga wasu cikin masarautar Joɗa mu samman in ya shafi ahlinta in sha Allah zata iya tuno komai na baya". Ya ƙarashe mgnar a hankali yadda ko su Al'ameen basu jiba bare su Ummey. Cikin gyaɗa kai Bappa yace. "Inama ji a jikina komai ya kusa zuwa ƙarshe da izinin ubangiji. Dan yanzu dai nasan muna komawa Shatu zata zo, to inma batazo da waniba ina zaton zata zo da mijin nata, kuma inma bata zo ɗinba idan ta haihu shine shirinmu ta sanadin haka Ummeynta zata shiga masarautar Joɗa ba tare da an zargi komaiba". Kai Appa ya gyaɗa tare da cewa. "Tabbas komai ya kusa zuwa ƙarshe".
Yar Kekkyawar budurwar nan kuma mai kama da Shatu hannun Junainah ta sake ganin Bappa na miƙo mata hannu alamun tazo su tafi. Cikin sanyi Khadijah tace. "Ayyah Junainah zamuyi kewarki." Da sauri Junainah tace. "Adda Khadijah ina in Adda Shatu na ta haihu zakizo keda Dedde ko?". Kai Khadija ta jinjina tare da cewa. "In sha Allah kuwa, zanzo ki gaida min ita da kyau kinji ko my Junnu kice mata duk Ahlin Abboi muna kewarta." Da sauri tace. "To zan gaya mata, bey-bey Adda Khadijah sai kunzo". Tana faɗin haka ita da Bappa suka nufi cikin jirgi. Ita kuwa Khadijah ruggume Ummey tayi tana zubda hawaye tace. "Ummey zamuyi kewarki, dake da Junnu". Hannu Ummey tasa ta share mata hawayenta kana tace. "Nanda wata biyu dai Shatuna zata haihu zakuzo mu gana".
Da sauri Ummey da Inna Amarya suka nufi cikin jirgin bayan sunyi sallama da Abboi.
Basu tafiba saida sukaga tashin jirginsu.
Ƙarshe biyar da rabi jirginsu ya sauƙa cikin Ɓadamaya International airport. riƙe da jakukkunan kayansu suka fito, Junainah na gaba. Tanata murmushin jin daɗi. A haka suka iso asalin inda masu taryar matafiyan suke.
Yah Salmanu ku wanda shida Junaidu ne sukazo taryarsu cikin motar Yah Salmanu wanda tuni shima ya samu aikinsa, cikin Ɓadamaya an bashi gida da mota.
Wani irin tsalle Junainah tayi tare da rabkawa Junaidun kira wanda ta hangoshi yanata ɗan dube-dube alamun neman ta inda suke.
Jiyo muryar ta, A tare suka juyo shida Yah Salmanu. Wani irin murmushi mai cike da tarin jin daɗin Junaidu yayi tare da nufo inda suke gadan-gadan. Ita kuwa Junainah da gudu ta iso gabanshi, sai kuma ta tsaya tare da sakin murmushi bata abka jikinshi ba kamar yadda takeyi da can baya. Wani irin murmushi Yah Salmanu yayi tare da cewa. "Oyoyo My Junnu Allah sarki nesa mai raba masoya, watoma Junaidu kawai kika sani banda ni ko?". Cikin jin kunya alamun shekara ɗaya nan data ƙara cikin shekarunta yanzu ta zama yar shekaru goma sha uku hankali da nitsuwa da kunya sun fara zuwar mata, cikin jin kunya tace. "A a Yah Salmanu na ganka mana". Sai kuma ta kalli Junaidu daya karkata kai yana kallonta cikin sanyi yace. "I miss you very very sorry so much my Junainah". Cikin rufe ido tace. "I miss You to Yah Junaidu, ya jikinka ka worke ko?". Da sauri yace. "Alhamdulillah garauma kuwa". Shi kuwa Salmanu da sauri ya isa gabansu Bappa jakukkunansu ya amsa, haka yasa shima Junaidu yayi maza ya amshi na hannun Ummey tare da cewa. "Oyoyo Ummey na Bappanmu Inna Amarya sannunku da hanya". Kusan a tare sukace yauwa. "Sannu Junaidu". Sai kuma Bappa ya kallesu tare da cewa. "Masha Allah Junaidu na ya girma." Ummey kuwa Salmanu ta kalla tare da cewa. "Kai sannu Salmanu ya bayan rabuwa?". Cikin girmamawa yace. "Alhamdulillah Ummey na munata kewarku Rugar Bani gaba ɗaya". Bappa ne ya jinjina kai tare da cewa. "Muma muna cannedai Amman munata kewarku". Ɗaga nan suka nufi inda motar Salmanu take. Suna shiga suka nufi Rugar Bani.
Kafin a kira mangriba dai sun isa.
Anayin sallan magriba da isha'i matan Rugar Bani suka rinƙa shigowa sunayiwa su Ummey sannu da dawowa da ganin amaryarsu.
Junaidu kuwa ana idar da salla ya dawo nanfa yaja Junainah gefa kaɗan cikin gidan sunata hira, tana bashi lbrin ahlin Abboi yayinda sosai yanzu faransaci ya kama bakinta.
A nan masarautar Joɗa kuwa. Ana idar da sallan isha'i suna fitowa a kan hanyar komawarsu cikin gidane. Lamiɗo keyiwa Sheykh batun zuwansu Rugar Bani da Umaymah ta gaya mishi. Ɗan juyowa yayi ya kalli Lamiɗo jin yana cewa. "In Allah ya kaimu goben da safe fadawa da bayi zasuyi muku rakiya, ka kuma ɗauki Jalal da Jamil da Umminku". Cikin kwaɓe fuska yace. "Bana wani buƙatar rakiyar bayi da fadawa da hadimai. Kuma Jamil da Jalal duk yanzu bana son yawonsu na aamu suɗan fara meda hankalinsu sosai kan aiyukansu sun rage zaman gida da yawace-yawace kuma ma ni tafiyata ta sirrice, bana ma son asan Aisha bata gida bare asan inda take, sabida gsky wanna Hankakar Hajia Mama mai farin gaba bakin baya sata iyasa aje can Rugar ayi mata komai, badon dole bama bazata jeba, sabida rugar ba tsaro." Jinjina kai Lamiɗo yayi cikin gamsuwa da zancenshi yace. "Eh to wannan ma hakane ba matsala kuyi tafiyar sirrin ammanfa zakuje da Ummi". Kai ya gyaɗa alamun to daga nan sukayi sallama.
Yana shiga falon ya samu ba kowa. Falonshi ya wuce a nan ya samu Shatu kwance bisa kujera. Matsawa kusa da ita yayi tare da cewa. "Ya dai Aish lfy kuwa yau ba hira ina Ummi ina Juwairiyya?". Ido ta lumshe tare da cewa. "Wlh Ummi zazzaɓin mura ke damunta". Cikin kula yace. "Assha subahanallahi tasha mgni kuwa?". Kai ta gyaɗa tare da cewa. "Eh tasha har tayi baccima". "Toh Allah ya sauƙa". Yace yana zare al'kyabbar jikinshi. Amin Amin. Tace tana tashi zaune. Gefenta ya zauna ganin haka ta ɗan gyara zamanta tasa mishi abinci ya fara ci.
A hankali ta kalli wayarta dake gefenshi ganin ta kawo haske alamun ana kiranta. Miƙo mata wayar yayi. Junaidu tace tare da amsa kiran. Cikin dariya yace. "Adda Shatu na rigaki ganinsu yau kam gani ga Junainah na, ga Ummey ga Bappa munata hirarmu sanyin hunturu na kaɗamu ga farin wata, Adda Shatu farin cikin Rugar Bani ya dawo kamar yadda kika sani a da can baya". Cikin tsananin jin daɗi tace. "Alhamdulillah Junaidu nima in sha Allah gobe iwar haka muna tare da yardar Allah, ina my Junnu". Da sauri Junainah dake c jinsu tace. "Gani nan Addana". Murmushi tayi kana tace. "Ina Ummey na?". "Gata can cikin baƙi" Junaidun ya bata amsa. Daga nan ta katse kiran. Ta juyo da sauri ta kalli Sheykh dake cin abinci. "Alhamdulillah Hamma Jabeer su Ummey sun iso". Cikin sakin fuska yace. "Masha Allah, Alhamdulillah". Da sauri tace. "Gobe sammako zamuyi ko". Ajiye spoon ɗin hannunshi yayi sabida ya ƙoshi gyatsa yayi tare da hamdala kana a hankali yace. "Aishhhhhhhh ya za'ayi muyi sammako, kin matanta gobe jumma'a ne? Sai munyi sallan Jumma'a sai mu tafi ko? Please kada kice komai kin ji kiyi haƙuri sai munyi sallan". Cikin rashin iya masa jayaya tace. "To Allah ya kaimu Lokacin". "Amin Amin". Yace
Daren ranar sosai Shatu ta sama mishi gamsuwa iya gamsuwa. Sai da komai ya lafa kuma ta narke mishi, tare da kamo hannusa ta ɗaura kan ɗan cikin nata daya tattare ya koma gefe ya bawa iyayen nashi dama. Da sauri ya tashi zaune yana sauƙe numfashin. Tafin hannunshi ya kife kan cikin. tare da fara murza wurin a hankali yana dai-dai-ta kwanciyar yaron yana mgn a hankali. "Afwan Ƴar al'barka gyara kwanciyarki ko, kada ki wahal da Amminki, yauwa yarinyar kirki, Allah ya miki al'barka ya fito dake duniya lfy ya tsareki da kariyarsa ya al'barkaci rayuwar ki ya raya mana ke bisa imani yauwa Kekkyawar jikar Mamey da Ummey". Murmushi sosai takeyi ganin yadda yake kalamai masu daɗi akan cikin a hankali tace. "Yah Sheykh bafa jinka yakeba". Murmushi yayi tare da kissing cikin kana a hankali yace. "Ita Kekkyawar mgn tana tasiri akan shuke-shuken fulawima hakama akan yaron ciki, musamman da mahaifinshi ko mahaifiyarshi, bakyajin duk sanda nake masa mgn yakanyi ta jujjuyawa". Ya ƙarashe mgnar yana lakace hancinta. Daga nan dai yaje yayi wonka haka itama.
Ummi kam sosai mura yayi mata rubdugu.
Washe gari ranar jumma'a kuwa, gaba ɗaya Shatu gani take lokacin baya gudu ta gama shirinta.
Bayan an idar da sallan Jumma'a. Sheykh ya nufo Side ɗinsa, su Jamil na biye dashi a baya. Yana shiga ya samu Shatu a falo tana zaune gaban Ummi dake kwance bisa kujera ɓare mgni takeyi tana bata. Sara kuma nacan kitchen tanayi musu girki.
Cikin sauri ya wuce falonsa jim kaɗan kuma ya fito. Da sauri ya kalli Ummi tare da cewa. "La! Ummi bar mgnin nan yanzu zamu tafi Valli dake in duba miki wani mgnin". Da sauri Shatu ta kalleshi jin yadda yake mgn kamar hankalinsa a tashe, Shi kuwa Jamil ya kalla tare da cewa. "Yi maza kaje ka kira min Baba Ado direba". Da sauri Jamil yace to kana ya juya ya fita. Jalal kuwa Dinning area ya nufa riƙe da waya a kunne yana mgn da Hibba.
Ummi kuwa, to kawai tace. Shi kuwa Sheykh cikin kula da alamun sauri da gaggawa yace. "Aish zo". Da sauri ta miƙe tabi bayanshi.