Kenza eBookz

Gudu da waiwaye bilyn abdul - Chapter 13

Gudu da waiwaye bilyn abdul - Chapter 13

Gudu da waiwaye bilyn abdul Chapter 13: Gudu da waiwaye bilyn abdul Chapter 13. Abinda ya bani mamaki koda muka gama karyawa yau bai fitaba, zamansa yay a…

3,016 words

Abinda ya bani mamaki koda muka gama karyawa yau bai fitaba, zamansa yay a gidan, sai ma waya da ya ɗauka ya kira Yaya Mudan ya kawo masa wasu kaya zai yanka a gidan. Ni dai ƙala banceba, sai dai zuciyata nata zungurata akan nai masa maganar wanka. Na daɗe ina mulmula maganar kafin da ƙyar na iya fiddata, "Yaya ko zakai wanka tunda akwai sauran ruwan zafi a filas?". Shiru banji ya amsaba, hakane ya sakani satar kallonsa, sai naga ashe ni yake kallo shima, jinai duk na daburce, dan kallon dai irin na kinma samin idon nan ne, to amma ya zanyi tunda nai suɓutar baki. Banyi zatoba naji yace, "Haɗa ruwan". Ai zumbur na miƙe kamar dama a ɗofane nake, ina kallonsa ya kauda kai yana murmushi, da alama dai yanda nake a tsoracene ya bashi dariya shima. Duk da ya kauda idonsa kar naga murmushin naji sanyi a raina sosai, dan na jima banga hakan daga garesa ba. Ina dawowa daga kai masa ruwan na haɗa wanke-wanke na fice abina gaban rijiya. Ina ƙoƙarin farawa yazo ya gittani ya shiga bayi.

Kamar jirana maman Ama take sai gata itama ta fito dana wanke-wanken daga ɗaki tazo ta tsira kujera gefena ta fara. Da farko tsokanar Amatullah na fara muna dariya, sai ta rage murya ƙasa-ƙasa tana faɗin, "Amarya anya kuwa wannan amaryar jiyan zamu dai-daita da ita? Babu wanda zaice gidanan ga yanda daren farkonki ya kasance saboda kunsan kanku daga ke har mai gidanki, amma ita jiya ihu taitaima mutane na rashin mutunci, ita ba budyrwa ba balle ace". Sosai gabana ya faɗi jin ta ambaci daren farkona, gefe kuma ina mamakin wannan saka ido irin na maman Ama, wato ita idonta na kammu ashe akan taji yaya mukai daren farko? Tab anya kuwa zaman gidannan bazai canja saloba?. Ban samu bata amsa ba naji motsi a bayanmu, da sauri na waiga sai naga Yah Ahmad ne, da alama dai yama ji duk mi maman Ama ta faɗa, dan wata uwar harara ya zabgamin yana ƙaramin tsaki ya shige ɗaki. Innalillahi kawai na iya ambato a raina, na kai kallona ga maman Ama dake cigaba da zabga surutu ita koma lura da yah Ahmad ɗin bataiba...... "Amarya wai yanaga kinyi shiru....?" Murmushin yaƙe nayi ina girgiza mata kai, "Babu komai maman Ama, kawai dai banda abin faɗane, ni kitsoma nakeson naje, nasan kuma Yaya bazai barni naje gidaba, ko akwai maiyi anan kusa?". Nai maganar domin kauda surutanta marasa ma'ana. Tace, "Eh to sai dai nan gidan matar Ali, ta iya kitso kam sosai wlhy, dolene kikayi oga sai yayi biyan da bai shiryaba". Nanma Murmushi kawai nayi, hakan kuma yay dai-dai da sallamar Yah Mudanseer daga soro. Na gane muryarsa shiyyasa na amsa masa ina faɗin "Ya Mudan ka shigo mana". Ya shigo da sallama, ya gaida maman Ama ba tare da ya kalli inda muke ba ya shige ɗakinmu. Nima tashi nai na zubar da ruwa dan na gama sai tukunya, itama a tsaitsaye nai wankinta na kwashi kayan nabar maman Ama a wajen. A ɗaki na iske Yah Mudan suna hira da Yah Ahmad, sai tsokanarsa yake yana murmushi, nima ina shiga ya dawo da tsokanarsa kaina, dariya kawai nayi na ajiye kwandon wanke-wanken dana ɗora a tire ina gaidashi, a kuskure muka haɗa ido da Yah Ahmad dake duba littafi turamen zani kusan shida ajiye a gabansa. Babu shiri na ɗauke kaina, shima sai ya ajiye buk ɗin yana kallon Mudanseer. "Mudan zokaje can wajen kaɗanyo mana cefane kafin ka wuce, dan yankannan zai iya ɗaukata dogon lokaci ban iya tashi nayo ba". "To yayana ɗan gidan Ayyah, angon ƙanwata Umm-Ru ma na". Ya ƙarasa sunana da ɗai-ɗai saboda hararar da Yah Ahmad ya banka masa. Fita yay yana dariya, Yah Ahmad yace, "Shashasha kazo ka amshi kuɗin". Daga bakin ƙofa yace karka damu akwai kuɗi jikina, ƙanwata mi za'a sayo?". Kallon Yah Ahmad nayi dan nima dai bansan mi za'a sayo ɗinba tunda ba taɓa tambayata yay ba idan zaiyo cefane shi, niko kullum abincina baya wuce taliya da mai da yaji saboda shegen kwaɗaina, sai shinkafa da wake, ko dafa duka. Shima da ya kalleni sai ya janye idonsa ya maida ga Yah Mudan ɗin, shine ya lissafa masa abinda zai sayo, ya miƙa masa ɗari biyar yana cewa, "Ka ƙara da wannan tunda cefanen da yawa". "A'a kabarsa yaya, akwai kuɗin ɗinki da yaron malam ya bani yanzun nan zanzo nan, bara naje na dawo". Yah Ahmad ya maida kuɗinsa a aljihu, Yayinda Yah mudan ke ficewa shi kuma. Ni dai duk ina zaune gefe ne ina saurarensu, tsarinsu na ƙara birgeni, dama can kowa yasan akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu.

"Zo nan" na tsinkayo muryar Yah Ahmad. Kallonsa nayi, dan banyi zaton dani yake ba ganin dai muna zaune ba wani nesa sosai da juna ba, yanda ya tsatstsareni da idanu yasa na miƙe zuwa gabansa na tsugunna. Yace, "zauna da ƙyau". Zaman kuwa nayi cikina na sake ɗurar ruwan tsoro. Kallona yay sosai ko ƙyaftawa bayayi, ga fuskarsa babu alamun wasa yace, "Ina wasa da ke?". Da sauri na girgiza masa kai idanuna na cika da ƙwalla, dan bansan mi nayi ba, sai matse hannuwana nake cikin na juna. Ya cigaba da faɗin, "Kinsan daga yau ɗinnan da nake miki magana, idan har na sake ganinki zaune da matarcan kuna wata doguwar hira bayan gaisuwa sai na miki shegen duka a gidannan, wato ma har labarin daren farko kika bata....?" Da sauri na girgiza masa kaina ina faɗin, "Wlhy A'a Yaya, ALLAH ban taɓa ba tunda nake". "Ba gashi tana miki hirarba, ke har kinkai girman sanin akwai wani abu shi daren farko ga amarya daman?". Hawayen da suka zubomin a saman fuska na share ina cigaba da girgiza kai dan na kasama magana. Ahmad dake haɗiye dariyar yanda Umm-Rumana ta rikice da ƙyar ya kuma zazzaro mata idanunsa, danshi duk yana yine danya ƙwaɓeta da wuri karta saka kanta a wannan masifar ta shegen gulma, shiyyasa tunda suka tare a gidan ɗabi'un maman Ama basu masaba har mijinta, sam bayason mu'amularta da Umm-Rumana ɗin. "Kinga daga yau, bama itaba, ko wannan da aka kawo jiya karnaga wata aminta ta haɗaki da kowace shegiyar mata ama anguwarnan ba gidannan kawai ba, inko hakan ta kasance kema kinsan sauran, tashi ki ban waje". "Kayi haƙuri dan ALLAH Yah Ahmad, zan kiyaye insha ALLAHU, amma dan ALLAH ka yafemin". Duk da ta bashi tausayi sai cayay kawai, "Ya rage naki". Tashi Umm-Rumana tai ta koma gefe tana cigaba da sharar hawayenta. Ahmad dake buɗe zani ɗaya zai fara yanka yace, "Wlhy kika bari Mudan yazo yaga waɗannan hawayen ko, saina sassafaki a ɗakinnan". Babu shiri Rumana ta goge hawaye tsaf, sai ko ga Mudanseer ya dawo ɗauke da leda yellow mai layi-layi. Yana ajiyewa ko zama baiyiba yace zai koma yana da aiki a shago, gashi zaije makaranta da yamma. Godiya nai masa yay mana sallama ya fice.

Haka na tashi na fidda cefanen, Yah Ahmad nata yankan ɗinkinsa da duk ya maida hankalinsa wajen. Sai da zan fita waje girkine yace nayi anan ƙofar ɗaki basai na fitaba. Duk da nasan zafin wuta zai ƙarama ɗakin zafi haka nabi umarninsa tunda risho ɗin ba hayaƙi yakeba, kayan miya kawai na fita na wanko tare da ɗanyen kifi da Yah Mudan ya sayo mana a waje nazo ɗaki na niƙa a gireta, kifin kuma nai ƙoƙarin sashi a wuta danna ɗan tafasa da kayan ƙamshi na rage masa ƙarni. Maman Ama kawai kake iya jiyowa a tsakar gida da yaranta, amaryarmu kuwa suna ɗaki sai dai kajiyo sautin dariyarsu. Da yake girkin bawani mai yawa bane dan danan nagama girka mana shinkafa jalof, wadda a ido kawai dolene ta birgeka saboda aikin nutsuwa ne, na kwashe a kula gaba ɗayanta na gyara wajen kamar banyi komaiba. Har lokacin kuma Yah Ahmad nata yankan kayan, sai lokaci-lokacine yake amsa waya idan an kirashi, nama lura mafi yawa abokansane ke tambayar lafiya? Sunga bai fitaba, saiko Customers masu amsar ɗinki ko masu kawowa............✍🏻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 [7/27, 6:06 PM] Sis Hajiyyaye: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

*(16)*

.............Kiran sallar zuhur da akeyine ya saka koda na gama gyara wajen sai ban zauna ba, na ɗauki buta na fita. Ina fitowa Amaryar jiya da mijinta suka fito daga bayi da alama wanka sukayo tamkar ɗazun da safe, harga ALLAH ban kawo komai a raina ba, saima sannun da sukaimin na amsa na shige banɗakin. Na fitone idona ya sauka akan mama Ama dake leƙe ta Windown ɗakinta, sai dai ganin kamar na ganta ya sakata saurin sakin labulen, kaina kawai na girgiza, na zauna bakin rijiya ina alwala. Sai ko gata itama zumut ta fito da buta a hannu, tazo gab dani take faɗin, "Amarya an tashi kenan?" Kallonta nayi da ƴar fara'a nace, "Ai dama ba barci nakeba, aiki nake yima a ciki". Tai wata ƴar dariya idonta ƙyam akan jelar gashina, "Ai najiyo ƙamshi har nake zance da zuciyata akan yau kuma amarya a ɗaki ake girki? Ko kayan daɗi za'aci tunda naji ƙamshin kifi na tashi". Nace, "A'a, kawai dai dan Yah Ahmad na gidane na zauna saboda na tayashi hira". Buɗar bakinta sai cewa tai "Ku hirar kuke, wasuko da ranar ALLAH suna gado suna murzar juna, wannan matar inaga da bamu da maza a gidannan lallai da munsha kallo, aini yau naga bariki wai wanka da miji da tsakar rana". Shiru nayi danni sam maganar tata tazomin a baibai, na farko dai ban gama fahimtar gundarin maganar ba, na biyu kuma bansan minene matsalarta da wannan amarya ba, miye laifi idan tayi wanka da mijinta? Bayan malamin islamiyyarmu ya taɓa bamu wata ƙissa da MANZON ALLAH ke wanka da *Nana Ai'sha (R.A)*. Zaram na miƙe saboda fitowar Yah Ahmad daga ɗaki, a duƙe na ƙarasa alwalar maman Ama na tsaye a kaina, tana jiran Yah Ahmad ya gotamu ta ɗora maganarta daga inda ta tsaya. Da azama na bar wajen ganin ya nufi bayi, na faɗa ɗakina ba tare da na sake koda waiwayenta ba. Gaskiya matarcan lamarinta na bani mamaki da ɗaure kai, shikenan kai bazaka damu da rayuwarka ba sai ta wani, dole nazo na roƙi Yah Ahmad komawa makaranta kodan gujema halayyar maman Ama ta son kafa da'irar gulma a gidannan.

Ina idar da salla ne na fara kimtsa kayan danaga ya kammala yankawa, sai biyu suka rage bai taɓaba, na tattare ƙyallayen na saka a leda suma na share ɗakin dan ya samu wajen cin abinci. Ranar dake a tsaye tasaka garin ɗaukar wani mugun zafi, da ace ina da dama kayan zan cire nasha iska wlhy. Haka dai na gama shirya masa abinci a tabarma na ɗauki kofi ina zuba ruwa, bisa tsautsayi na ɗan zubar, wanda na gama zubawa na ɗauka nakai gaban abincin nasa, sannan na dawo ina duba tsumma danna goge wanda na zubar. Abinka da sabuwar leda, ashe na ɗan ɗisar da mangyaɗa a wajen sanda nake girki, koda na goge wajen kuma ban lura da nanba,, ga ruwa ya zuba, ina ɗora ƙafata da dube-duben inda ruwan ya zuba kawai naji na tafi gaba ɗayana, sai gani ƙasa. Fashewa nayi da kuka saboda wani azabar zafi daya ratsa ƙashin ƙafata da ƙuguna. Sosai nake kuka dan na kasa tashi, bansan yaya akai kunnen maman Ama ya jiyoniba, sai gata ta shigo jiki na ɓari tana tambayata lafiya?. Ganina ina kuka rike da ƙafa da hannu ɗaya, ɗayan kuma na riƙe ƙugu ya sakata faɗin, "Faɗuwa kikayine?". Kaina kawai na iya ɗaga mata ina cigaba da kukana, takai hannu zata taimaka min danna miƙe sai ga Yah Ahmad yay sallama ya shigo. Da mamaki ya kalli maman Ama ɗin sannan ya kalleni fuska babu walwala, "Miya faru?". Maman Ama ta buɗe baki zata bashi amsa nai saurin katseta.... Kuka na kuma saka masa wanda ni kaina nasan harda taɓara nace, "Faɗuwa nayi". Hannuna dake cikin na maman Ama ya kalla, ba tare da ya kalleta ba yace, "Barta kawai zan tada ita". Koda ta sakeni a zatona zata fita, sai naga matarka ta gyara tsaiwa tana kallonmu sai kace wasu tv ɗinta. Wannan abu da Maman Ama tayi ya zafi Ahmad a zuciya, dan haka da gayyar cusa mata baƙinciki ya rungumi Umm-Rumana ya ɗagata cak zuwa saman gado, tunda ya fahimci matarnan muguwar ƴar sa ido ce. Aiko tamkar ya sani, dan tsayawa tai taga yaya za'a kwashe, daga ita har mijinta sun fahimci Ahmad bai taɓa taɓa Rumana ba, har gulma suke akan hakan, wai baya son Rumana hankalinsa nakan Samina har yanzun. Wani irin zaro idanu tayi na tsagwaron mamaki, maimakon ganin hakan ya sakata fita saita sake maƙalewa. Rumana kuwa tunda Ahmad ya ɗauketa jitai hawayen sun gudu saboda tsabar al'ajabi, sam bata kawo hakan a ranta ba, jitai kawai jikinta na wata irin tsumar tsoro, dan a rayuwarta hakan shine na farko gareta. Ya kwantar da ita a gadon sai dai rabin jikinta na saman jikinsa, a hankali yace, "A inane kika buge?". Hawaye Rumana ta matso da suka cika mata idanu, ta nuna masa ƙafarta, ƙugun kuma kunya takeji shiyyasa ta kasa nuna masa dukda nan yamafi ƙafar buguwa. A mamakinta sai gani tai ya tura hannunsa cikin rigarta ya shafa ƙugun yana faɗin, "Shinan bakison a taɓane ragguwa?" ya ƙare maganar da matsa wajen. Jikin Rumana har rawa yake ta ƙankame Ahmad ba tare da ta shirya hakanba, ga wani siririn kuka data sakar masa na jin zafi, bai bartaba yanata matsa wajen yanda ƙashin zai saki. Ita ko ta ruƙunƙumesa tamkar zata koma masa ciki. Dauriya kawai Ahmad yakeyi, amma gaba ɗaya jinin jikinsa yamutsawa yakeyi ta kowacce kafa, tsigar jikinsa yanda ta tashi ya saka kowanne gashin jikinsa fitowa ta ɓularsa. Karo na farko a rayuwarsa da ƴamace ke a jikinsa kwance, abinda ya jima yana kissimawa da Samina kawai, a yau sai ga saɓanintace kwance a jikin nasa. Kasancewarsa gwanin kamewa yasa baka fahimtar yana a mawuyacin hali koda a fuskane, saima kalmar Sorry da yaketa ambatama Umm-Ruman a hankali yana cigaba da murza ƙugun". Saɗaf-saɗaf maman Ama ta fice a ɗakin wani abu na tokare mata maƙoshi, dan ita gani tai soyayya suke a gabanta kawai. Duk yanda Ahmad yaso daurewa ya kasa, hakan yasashi zamewa ya kwanta yana saka Rumana sosai a jikinsa, wai shinan duk azuwan gyarane, taƙi tsayawa ya matseta, wannan damar Rumana da azabar matsa gurin ciwo ya isheta ta kuma mannema Ahmad sosai tana kuka da roƙonsa dan ALLAH ya bari hakanan, akwai zafi sosai. Sam shi baima san tanaiba kam a yanzu, dan ɗiff kunnensa ya toshe, salon yanda yake matsa mata wajenma kawai zai baka tabbacin ya fara canja tasha ne.

Har maman Ama taje ɗakinta sai ta kasa daurewa, tsabar hassada nacin ranta ta kasa zaune ta kasa tsaye, maganin zafi ta ɗauka ta dawo ɗakinsu Umm-Rumana, tunda ta ɗaga labule taga yanda suke mai makon ta koma da baya sai catai "Yauwa ga maganin zafi kozata shafa a wajen insha ALLAHU zai saki". Yanda tayi maganar da ƙarfine ya dawo da Ahmad hayyacinsa, ya buɗe idanun da suka canja launi da ƙyar, kafin ya yunƙura ya tashi zaune da Umm-Ruman a jikinsa, ita tanata shashshekar kukane, shiko sai ajiyar zuciya yake saki a jere kamar jaririn dake neman abinci bai samuba. Fuskarsa mugun tamke yakai dubansa ga maman Ama, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa saboda yasan muryarsa zata iya fallasa tsantsar buƙatar dake a tare dashi a halin yanzu. Maman Ama ta ajiye musu maganin zafin gefen gadon ta fice kamar gaske, amma saita maƙale a bakin ƙofa. Umm-Ruman ta raba jikinta da nashi tana share guntun hawayenta, murya a matuƙar shaƙe yace, "Sannu, kawo ƙafar muga itama". Rumana ta marairaice idonta na sake cika da ƙwalla, "Yaya dan ALLAH ka bari na huta sannan, ALLAH akwai zafi". Kansa ya girgiza yana kamo ƙafar, "Waya ce miki idan aka barshi anjima bazakiji zafinba, saima kinfiji fiye da yanzu" ya ƙara maganar yana matsa ƙafar itama. Nanma ta ɗanyi kuka tana rirriƙe masa hannu saboda ƙafarma ta ɗan bugu, sai da ya tabbatar ta matsu sosai ne ya sauka a gadon, jakkarsa ta kaya ya buɗe ya fiddo maganin zafi, dan ko kallon wanda maman Ama ta ajiye baiyiba, a ƙafar ya fara shafawa kafin ya kalli Rumana cikin ɗan ɗaure fuska yace, "Juyo bayan ki ɗaga rigan". Cike da jin kunya Rumana tabi umarninsa, shiko yay mursisi yana shafa mata a wajen. Bayan ya kammala ya miƙe tsaya yana cewa, "Kwanta kiɗan huta na minti biyar maganin ya shiga wajen sosai". Babu musu ta kwanta tana gyara rigarta, shiko ya ajiye man zafin saman mirror ya koma saman tabarmar ya zauna. Yunƙurawa tai zata tashi tana faɗin, "Bara na saka maka abincin". "Barshi zan zuba kawai". Yay maganar yana buɗe kular abincin. Dole Rumana ta koma ta kwanta, Ahmad kuma ya zubama kansa a binci a filet ɗin da Umm-Ruman ta ajiye. Sai ya samu kansa da yawan kallonta, kaɗan-ƙadan idonsa sai ya kai gareta. Rumana kuwa barcin wahala ne yay gaba da ita ba tare da ta shiryama hakanba. Maman Ama dataji shiru sai ta kama gyaran murya, da faɗin, "Sannu amarya kinji" Ahmad duk yana jinta, amma sai yay kunnen uwar shegu da ita, jin anƙi bata amsa taja ƙafafunta ta koma ɗaki.

★★★★★★★

Koda na farka bayan la'asar kaina kawai na gani a ɗakin, babu kayan da ya yanka, sai kular da abinci kawai ke ciki da kofin ruwa, filet da ƙaramin kofi da yay amfani dasu ma can na hangosu ya saka a robar da nake tara wanke-wanke. Sakkowa nai daga gadon, dukda har yanzu ina ɗanjin zafin amma ba kamar ɗazunba, takarda dana gani saƙale a hannun kofin ruwan na zare ina warwarewa.

_Idan kin tashi kici abinci, ga maganinan kisha kuma._

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull