Kenza eBookz

Gudu da waiwaye bilyn abdul - Chapter 21

Gudu da waiwaye bilyn abdul - Chapter 21

Gudu da waiwaye bilyn abdul Chapter 21: Gudu da waiwaye bilyn abdul Chapter 21. Ga Samina kuwa duk ɓacin ran data shirya nunama Ma'aruff tana ganinsa sai…

2,885 words

Ga Samina kuwa duk ɓacin ran data shirya nunama Ma'aruff tana ganinsa sai taji ta daburce ta kasa ko tari, sai ma damuwa data shiga dangane da shashsharetan da yakeyi. Har aka tashi wannan dinner bataga fara'arsa ba, sai dai idan abokansa ko danginsa sunzo kusa dasu yin hoto ko magana dashine zataga yana murmushi, amma ita magana ma idan tayi saiya ja lokaci yake bata amsarta, wata kuma ya share abunsa kamar bai jiba. Ƙarfe ɗaya aka tashi, kowa ya kama gabansa bayan sunma Amarya da ango rakkiya gidansu, dan tsaruwa kam gida ya tsaru, dolene Samina ta kira kanta gwarzuwar shekara a wannan lokaci. Sai dai suna shiga yaga abokansa sun wuce da ƴan uwansa ya saki hannun Saminar, ɗakinsa ya nufa ya barta a falo tsaye, tun tana tsammanin fitowarsa harta ƙosa ta bishi, tsabar rainin hankali iskesa tai harya shiga wanka, ɗakin ba baƙonta bane, tunda ansha kawota cikinsa a aikata abinda akeso da ita a ciki, sai dai an canja kayan cikinsa, waje ta samu ta zauna tana tsumayen fitowarsa. Koda ya fito ya ganta kallo guda yay mata ya ɗauke idanunsa, cigaba yay da shirinsa kamarma baisan tana ɗakinba, ita dai Samina mamaki sai kuma ɗaure kanta yake, gani take tamkar ba Ma'aruff ɗinta bane mai sonta da ƙaunarta tare da tattalinta ga komai. Bayan ya gama shirinsa tsaf yazo ya zauna a bakin gadon yana kunna lap-top, ga kofi daya ciko da fresh milk ya ajiye gefensa. Kasa jurewa Samina tayi ta miƙe ta koma kusa dashi ta zauna tanata zabga ƙamshi mai daɗi kuwa. Murya a raunane tace, "Wai lafiya kuwa Sweet?". "Mi kika gani?" yay tambayar ba tare daya kalleta ba. Da ƙyar ta haɗiye busashshen yawun bakinta tana zuba masa mayun idanunta irin nasu Ahmad, "Sweet ka canja min, sai kace ba kaiba, kamar baka ɗokin ganina a gidanka matsayin amarya matarka ta sunna? Yanzu wane angone za'a kawoma amarya amma hankalinsa nakan aiki". Wata ƴar dariyar rainin hankali yayi ya juye gaba ɗayansa yana kallonta, yayinda yake kai kofin madararsa a baki yana sha. "To ke kuwa banda abunki wane zumuɗi kike son ganina a ciki? Babu wani abu baƙon a gareni daga wajenki ai, kokuwa wannan faudar da zanen ƙunshin zan zauna kallo?" yay maganar yana lakato kwalliyar fuskarta a ɗan yatsa. Wani mugun tsorone ya kuma dirar mikiya a fuskar Samina, tai galala da baki tana kallonsa ba tare da ta iya furta komai ba. Bakinsa ya taɓe yana kauda kansa daga kallonta, "Miye abun mamaki a zancena, kema dai kinsan kowane ango yana rawar jikine ga amaryarsa saboda abunda zai amsa mai muhimmanci a gareta, to ni kuma an bani tun a waje ai, mizanma ɗoki kuma yau?". Hawaye masu azabar zafi suka fara gudu bisa fuskar Samina saboda kalaman da Ma'aruff yake gasa mata akan abinda shine yafi ƙarfinta ya amsa ba itace ta bashiba, hasalima tabi duk hanyar da zatabi danta tsare abunta sai irin wannan ranar amma saida ya ruguza mata shirinta. Tashi tai ta fita da gudu tana kuka, ya bita da kallo yana taɓe baki, sai kuma yaja tsaki yana faɗin "Kajimin wawuyar yarinya, ballaga kawai mtsowww".

Samina kuwa ɗakinta ta shiga tunda dama ta sansa, ta faɗa kan gado tana fashewa da wani kuka mai ciwo, farawa da iyawa kenan, daga tarewarta Ma'aruff ya rasa dami zai tarbeta sai wannan rashin mutuncin?. Kuka tasha bana wasaba, ga maganin matan da aka ɗirka mata sai cizonta yake, har mararta ta fara mata ciwo. Ganinfa zata halaka kanta kusan biyu na dare ta sake miƙewa ta koma ɗakin Ma'aruff. Kwance ta iskesa hankalinsa kwance yana barci, cikin sanɗa ta haye gadon tare da ɗaga bargon ta shige cikin jikinsa ta ƙanƙamesa. Cikin jan tsaki Ma'aruff daya farka yace, "K wane salon iskancine wai haka ina barci zakizo ki tadani?". Banza tai masa ta fara masa salon data san yana saurin ruftawa, da zafin nama ya tureta daga jikinsa. "K banason rashin mutunci fa, mike damun tunaninkine?". Kuka mai tsuma zuciya Samina ta fashe masa dashi tana roƙonsa ya taimaketa karta mutu, sai faman riƙe mara take tana matse baki, ga hawaye wasu na bin wasu. Shiko kallonta yakeyi da maɗaukakin mamaki, shi sai yau yake fahimtarma abinda mahaifiyarsa ke faɗa masa akan rashin dacewarsa da wannan yarinyar...... Katse tunaninsa Samina data manne masa a jiki tayi, ya janye jikinsa yana hararta, "Wlhy ki kama kanki, ni na aikeki kisha abinda zai hanaki zaman lafiyar? Can kije kiji da matsalarki ni dai barci nakeji, dan haka tashi kibarmin ɗaki kokuma na fitar dake wlhy". Sabon kuka Samina ta fashe dashi tana durƙusawa a gabansa tana roƙonsa, amma sam yaƙi saurarenta saima faɗi yake ta fitar masa a ɗaki, inba hakaba wlhy zai lakaɗa mata duka, abinda take son shi baida ra'ayinsa yanzun.

DAREN FARKO ya zama DAREN WAHALA, Inji amarya Samina dake neman shiɗewa saboda azabar ziwon da mararta take mata, ruwan sanyi kam harta gaji da sheƙa ma jikinta ta sadaƙar mutuwa zatayi kawai kafin wayewar gari, tayi nadamar biyema su mama gaje da suka dinga ɗirka mata magunguna duk dan ta burge Ma'aruff, kuka kam tayi harma ta rasa hawayen zubarwa, Ahmad ya faɗo mata a rai, yanda yay wani irin murjewa ga wani sheƙi da choco fatarsa keyi, kawai saita shiga kawosa cikin ranta a wani irin yanayin daya sakata kuma fashewa da kuka, dan kuwa tana ƙiyastashi a rantane zuciyarta na hasko mata Ahmad tare da Umm-Ruman. Jitai tamkar numfashinta zai bar gangar jikinta lokacin da hakan yazo mata a cikin rai.

___________________________________

Ahmad ma kam baisan tanaiba, dan tun sanda ake dambarwar abokan ango sunce bazasu ɗauki tsoffi a motaba ya shigo gidan ya kaɗa kan matarsa suka ɗauki hanyar gida. Tana sashensu sunashan hira da Amminta da ƙannen Ammi da sukazo bikin Zainab taje ta sanar mata saƙon kira daga Ahmad akan tazo su wuce gida. Sam bataso wannan tafiya ba, dama ga tsoro a ranta na abinda ya faru a daren shekaran jiya, Ammi tai mata tsawa ganin taƙi ko motsi balle shirin tafiyar. Tashi tai tana matsar hawaye ta kimtsa ta fito, a sashensu ta iskesa suna faɗan da suka saba shi da Sakina, tun suna ƙanana idan tace masa ƙaninta sai ya ɓata rai saboda bayaso, to har yanzu da take a gidan aure ga ƴaƴa ba dainawa sukaiba, dan ko gidanta yaje sai sunyi. Ta girmesan amma tsiran bawani baneba, shiyyasa hakan ke bashi haushi. Su Yaya Maryam nata musu dariya Rumana ta shigo, ya zubama kan Sakina ranƙwashi yay saurin nufar hanyar ƙofar gida yana faɗin Rumana ta samesa a waje. Sosai yanzu kowa ke musu dariya har Ayyah da Gwaggo, dan kuwa Sakina taji zafin ranƙwashin nan sosai. Ya tsaya mana inba tsoroba, kuma zata kamashi saita rama. Ita kanta Rumana abun nasu ya matuƙar bata dariya, dan haka tabisa da kallo tana murmushi. Sallama taima su Ayyah dasu Yaya Maryam ɗin ta fita, lokacin anata hayaniya a ƙofar gida da abokan ango, dube-duben inda zataga Ahmad takeyi, duk da kuwa ƙofar gidan akwai hasken wutar nefa da aka kawo. Jin an kama hannunta tai saurin juyowa, ganin Yah Ahmad ne ya sakata sauke ajiyar zuciya a hankali, baice mata komaiba yaja hannunta suka bar wajen.

★★★★

Duk da Ahmad ya lura da fushin da takeyi sai ya shareta kamar bai fahimci abinda take jima haushin ba, lokacin da suka shigo gidan shiru dan kowa ya shige ɗaki ya kwanta, Ahmad ya buɗe musu ƙofa suka shiga. Kayan jikinsa ya rage itako Rumana ta samu waje ta zauna tanata kumbura fuska. Baibi takanta ba ya haɗa ruwan wanka ya tafi yowa, har ya dawo ɗakin tana a inda ya barta, murmushi yayi kaɗan yana girgiza kai, yasa tawul ya goge ruwan jikinsa ya shiga shirin barci. Sai lokacin itama ta miƙe ta ɗeba ruwan ta fita, da kallo kawai ya bita amma uffan bai ce ba. Itama dai wankan tayo, lokacin data shigo harya kwanta, sai dai ba barci yakeba waya yakeyi, Rumana ta kalli agogon ɗakin sannan ta kallesa, duk da bataji da wa yake wayarba hakan ya bata haushi, tako sake tsuƙe fuska waje guda. Duk abinda take Ahmad na lure da ita, ta kammala mutsu-mustun shirinta tazo gefen gadon nesa dashi ta kwanta a takure. Dai-dai nan ya ajiye wayar shima, matsowa yay tsakkiyar gadon ya jawota ta dawo jikinsa. Hancinsa saman dokin wuyanta yana hura mata iska yace, "Kodai mu koma ne kima amaryar zaman ɗaki?". Tasan baƙa ya faɗa mata, dan haka tai shiru, murya a shaƙe ya sake faɗin, "Dake fa nake magana". "A'a" ta faɗa tana ƙanƙame jikinta saboda abinda yake mata da hannunsa a cikin jiki. Bai sake magana ba sai sabon salo daya canjama kwanciyar tasu.

"Yau ɗinma dai babu sauƙi" cewar Umm-Rumana a zuciya tana share hawaye bayan ta gama gurzuwa a hannun jaruman mazaje. Da taimakon Ahmad yau ɗinma ta kimtsa jikinta tanata masa kuka, da yake kukan da biyune harda haushin ƙin barinta ta kwana gida sai na yau ya nema finma na shekaran jiyan, shi dai Ahmad idanuma ya zuba mata, sai dai a ƙasan ransa yanajin tausayinta dan shi kansa yasan shiɗin bana wasan yara bane, tunda yana a ganiyar ƙuruciyarsa ne, kuma yanzunma aka fara wasan🤭. Yanata lallashinta ta sigar shafa mata baya har barci ya kwashesu a haka su dukansu.

★★★

Washe gari Ahmad na gida har azahar bai fita ko inaba, hakanne ya saka Rumana fahimtar itama dai bazataje ko inanba kenan. Bataga fuskar tambayaba kuma dan haka tai shiru da bakinta sai haushi dake cinta a zuciya. Bayan anyi sallar azhar ɗinne Zainab da Ni'ima ƙanwarta sukazo, taɗanji daɗi, dan kayayyakin bikine wanda Ayyah ta haɗo tace a kawo mata, a wajensu takejin ai suma su Yaya Maryam duk sun tafi gidajensu ma, gidanma sai iya dangin mama gaje ne kawai da suke shirin zuwa buɗar kai gidan Samina.

_________________________________

Ko wacce amarya tana saka daren farkonta a jerin tarihin daren tunawarta koda takai tsufa saboda muhimmancinsa a gareta, sa ɓanin Samina daya zame mata daren baƙin ciki da wahaltuwar ciwo, da safe tashi tai tamkar wadda aka tsamo daga bakin kura, tayi wujiga-wujiga cikin azabar ciwo, ga kukan wahala datasha idanu sunyi luhu-luhu. Har lemon tsami sai da ta samo daƙyar a kicin ɗinsu tasha amma bataji yanda takeso ba, sai da taɗan samu kanta kaɗan harta sami damar gyara jikinta tai wanka, bataga ko ƙeyar ma'aruff ba a gidan kuma bataji motsinsa ba sam, gashi koɗan abincin da akan kawo daga gidan surukai washe garin kai amarya ita babu wanda ya kawo matashi. Ƴar kazar amarcin da ango yake kawowa nanma bata sameta ba a daren jiya. Komai ya dagule mata ta kowanne fanni, har zuhur bataga kowa ya leƙotaba ga yunwa ga damuwa ga ciwon mara, falo ta dawo ta kwanta cikin kujera tana hawaye, a lokacinne taji ana ƙwanƙwasa ƙofa. Tashi tai bayan ta ciri tissue dake saman center table ɗin falon ta goge hawayenta taje ta buɗe, ƴan uwan mahaifiyartane da sukazo buɗar kai. Matsa musu tai suka shigo tana musu sannu da zuwa, su dai sai binta suke da kallo. Duk da sunsha mamakin ganinta ita kaɗai a gidan sai basuce komaiba, yanda akasan amarya da farin jini sun zata kodai dangin mijinta sa iske wasu a ciki, duk da dai sun kula ƴan gayune kowa rayuwarsa yake babu ruwansa data wani, kuma yanda mijin nata yake firi-firi babu alamar kunya a idonsa ma ya hana kowa raɓarsu. Yanayin da suka ganta wujiga-wujiga basu kawoma kansu tana cikin damuwa baneba, ca suke kawai dai angone ya mori amarcinsa musamman lura da yanda take tafiya da sukayi, ita kuma ciwon marane ya sakata tafiya a dudduƙe😣🤭. Bata iya faɗama kowa halin da take cikiba har suka gama hidimarsu bayan la'asar sukai shirin tafiya, a lokacin kuma motar ma'aruff ta shigo cikin gidan. Ya fito daga mota sai wani tsume fuska yake tamkar baiga waɗanda suke a gidanba, kamarma zai wuce bazai gaidasu ba sai kuma dai miya gani oho masa, ya tsaya ya gaishesu cikin rashin girmamawa ya wuce abinsa. Wannan abu kuwa ya saka kowa a cikinsu yaye baki suna binsa da kallo harya shige, ita kanta Samina abin ya sosa mata rai. Su dai duk sun tafi zuciya a saɓule, yayinda wasu suka gumtsi abin faɗa da yaɗawa kuwa.

Samina na shiga falon taci karo da Ma'aruff tsaye yana cika yana batsewa, harara ta zuba masa tana jan tsaki zata wucesa. Baice mata komaiba ya fisgi hannunta ya jata ɗakinsa saikace wata abun banza, saman gado ya wurgata kawai ya afka mata. Sosai Samina taji warin giya a jikin Ma'aruff, hankalinta yay matuƙar tashi, duk da a buƙace take dashi sam batajin daɗin yanda yake mu'amulantarta yanzu, ga warin giya ya addaba ma, tsabar baisan abinda yakeba kuma danna mata bakinsa kan nata, yunƙurin amai samina ta fara tana kuka wiwi, Ma'aruff ya cire bakinsa jin zatai masa amai yako kaftama fuskarta mari. Kuka mai tsuma rai Samina ta saki, dama gashi da mugunta yake kusantarta saboda baisan ina hankalinsa yakeba, kuka take tana roƙonsa yayi haƙuri, ta tuba. Cikin maye yace, "Ba ke kike buƙatata tun jiyaba, dan uwarki kin samu ma shine zakimin yanga" ya ƙare maganar yana sake kafta mata marin daya sake gigitata. Yana samun nutsuwa kuma ya kwarayo mata amai a jiki mai azabar wari ya koma gefe yana sauke numfashi...............✍🏻

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_

_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇 *07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 [7/28, 1:22 PM] Haleemat M Musa: https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

*_GDW_*

*(25)*

..............Samina ma aman ta shiga kwararawa. Ma'aruff ya tashi zaune da ƙyar yana faɗin, "Kai wai k dan uwarki amai kikemin ma a ɗaki? To aiko saikin shanyeshi shegiya sauran titi, ƙilama bani kaɗai kike baiwa ba" ya ƙare maganar yana kai mata wani bahagon bugu. Dan wuyama Samina yanzu kasa kukan tayi, babu ko ɗigon tausayinta a ranshi ya tashi yashiga lakaɗa mata duka, ta ƙwaci kanta da ƙyar zata gudu, yace wlhy idan ta fita sai ya mata mafiyinsa tazo ta gyara masa gado da ɗaki, uwartace zatazo ta goge wannan aman?. Dole Samina ta tsaya dan duk a birkice take, ga tsoronsa ya kuma tasiri mata arai, tana kuka ta nannaɗe zanin gadon, shiko yana tsaye ƙyam a kanta da belt ɗin wandonsa. Haka ta haɗa ruwan morping tazo ta tsaftace gadon zuwa tsakar ɗakin, Ma'aruff kuwa na tsaye a kanta, sai da yaga komai yay masa need sannan yace ta haɗa masa ruwan wanka, kuma saita wanke bayin, danshi ya kula wai batada tarbiya, toshi zai koya mata tasa a gidannan😂🤭. Duk uban aikinnan da Samina keyi a bubbuɗe take tafiya saboda ɓarnar da Ma'aruff yay mata na afka mata, duk yanda yakeso haka tayi, tana hawaye harta kammala komai ta saka masa wankakken zanin gado ta feshe ɗakin da air parishioner. Zata fice ya kuma dawo da ita, "K dan uwarki juyo bayanki, ubanwa zai wanke miki wannan zanin gadon? Zoki ɗauka karkuma kibari na tashi barci na ganshi da dattin nan". Dawowa tai ta ɗauka ta fita dashi tana sharar ƙwalla. Shiko yaja tsaki yana nufar ban ɗaki, koda yayo wanka zuwa yay ya kwanta abinsa, barci mai nauyi kuwa ya sacesa hankali kwance.

A ɗakin tama data koma kuka taitayi rurus, ga warin zanin gadon dana giyar daya goga mata ya addabeta, dole ta ajiye batun zaman kuka gefe ta miƙe ta hau wankin zanin gadon hanci a toshe, sai da ya fita fes ta ajiyeshi gefe itama ta fara tsaftace nata jikin, ta shiga ruwan zafi kozataji nutsuwa akan baƙar muguntar dayay mata. A daren jiya ta wahaltu da buƙatarsa, sai gashi bata samu nutsuwar fitar abinda ya dametanba saima baƙar wahala data shawo, wahalar kuma ta mantar da ita buƙatar da take ciki gaba ɗaya.😣⛹‍♀

Tsakar gida taje ta shanya zanin gadon da ƙyar, ga yunwa nacin hanjin cikinta, ga damuwa, kayan cincin da aka kawo mata na gara wanda mama gaje tai bajintar yi saboda za'a kawo ƴa gidan masu kuɗi Saminar ta ɗiba, sai dai kuma tuno warin aman Ma'aruff da haɗa bakinsu da yayi ya faɗo mata a rai, saurin ture filet ɗin tai gefe saboda sabon amai da taji yana zuwa mata. Kanta ta dafe tana hawaye da faɗin, "Nashiga uku ni Samina, wace rayuwace na jefo kaina a ciki?".. Bata da mai bata amsa dan haka ta cigaba da raira kukanta a falon.

"Masu karatu ban saniba ko kuna da amsar bata"💁🏼‍♀️.

Ni dai Bilynku bani da🤩🤪⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀

★★★★

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull