Gudu da waiwaye bilyn abdul - Chapter 9
Gudu da waiwaye bilyn abdul Chapter 9: Gudu da waiwaye bilyn abdul Chapter 9. Ana idar da salla Ahmad ya shigo, kasancewar massalacin a ƙofar gidan yake,…
2,896 words
Ana idar da salla Ahmad ya shigo, kasancewar massalacin a ƙofar gidan yake, Rumana na zaune saman abin salla tana azkar. Yanda yay sallama ciki-ciki haka ita ta amsa masa a hankaki, baice mata komaiba yazo ya sake hayewa gadon ya kwanta. Rumana ta ƙarasa azkar ɗinta sannan tace, "Ina kwana". Kamar bazai amsa mataba sai kuma taji ya amsa da "Lafiya". Daurewa tai ta sake cewa "Ya jikin?". Nanma dai shirun yayi, harma sai da ta fidda tsammanin zai amsa sai kuma yace, "Alhmdullh". Daga haka kowa yay shiru, shi dai barcine ya sake kwasheshi, saboda maganin bai gama sakinshi ba. Itako duniyar tunani ta faɗa, a ranta sai ƙara girmama hukuncin ALLAH takeyi, yanzu nan Yah Ahmad matsayin miji yake a gareta? Wata zuciya tace, "To gashi ma kun kwana a ɗaki ɗaya". Nannauyan numfashi ta sauke, wanda har Ahmad ya jiyota sama-sama a ɗan barcin da ya figesa.
Umm-Rumana na zaune a wajen har gari ya fara haske, ɗakin kawai take bi da kallo daki-daki, Ahmad dai nata barcinsa, wanda daga inda take tana iya jiyo saukar numfashinsa a hankali. Sama-sama ta fara jiyo motsin matar gidan da yarinyarta dake kuka, sai kuma zuwa can tajiyo maganar mijin shima suna fira. Idanu ta lumshe tana tuno gidansu, yanzu tasan gidan nacan da hayaniyar yara daga kowanne sashe, musamman ma sashensu da ke da ƙananun yara da sashen baba ilyasu. Barcine ya sake saceta a kan abin sallar itama.
Sallamar Zainab ce ta farkar da Ahmad, ya buɗe idanunsa kafin ya tashi zaune yana amsawa, yakai idonsa kan Rumana da ko motsi bataiba, janyewa yay ya bama Zainab ɗin izinin shigowa. Sai da ta sake yin sallama sannan ta shigo, ta sauke tiren kanta da aka ɗora kofin silba babba da kwanon silba guda biyu akai. "Yaya ina kwana" ta faɗa lokacin da take kaiwa ƙasa durƙushe. Amsa mata yay yana ƙoƙarin sakko da ƙafafunsa ƙasa. Tace, "Gashi inji Ayyah, tace yaya jikinka? Idan kaci abinci dan ALLAH kasha magani, idan kasha zataji a zuciyarta kasha, idan kuma bakashaba ma zataji bakashaba". Guntun murmushi yayi badan ya shiryaba, a ransa yana kuma jin ƙaunar Ayyah sosai. A hankali ya furta, "Kice mata zansha insha ALLAHU". "To yaya zan faɗa" Zainab ta amsa tana taɓa ƙafar Umm-Rumana yanda Ahmad bazai luraba. Shi baima san tanaiba, ƙoƙarin sakkowa yake daga gadon. Dai-dai nan Rumana ta buɗe idanunta. Zainab ta matsa kusa da ita tana ƴar dariya, Ahmad kam buta ya ɗauka ya fita ya barsu suna gaisawa.
Bayan tafiyar Zainab da Rumana taita roƙon ta zauna taƙi, acewarta ance karta daɗe. Rumana tahau gyaran ɗakin dan Ahmad bai dawo ba, sai da ta gama shara ne ta fito danta share waje sai taga butar a jiye, kenan nan ya ajiye ya juya ya fita. Share tsakar gidan tayi gaba ɗaya, tana ƙoƙarin wanke banɗaki matar gidan ta fito ɗauke da kwanikan da suka karya. "A'a amaryace dayin shara da safen nan? Harda su wankin bayi?". Murmushi Rumana tayi, cikin girmamawa tace, "Ina kwana". "Lafiya lau amarsu, ya amarci da angon naki?". Kasa amsawa Rumana tayi, saboda jin kunya, matarma tayi dariya kawai tana ajiye kwankan bakin rijiyar dake gidan. Rumana ma ta fito daga bayin riƙe da botiki, gaban rijiyar ta ajiye tana faɗin, "Rijiyar akwai ruwa kenan". "Eh akwai ruwa Amarya, sai dai babu guga wlhy, jiya da safe Ahmad ya jefashi cikin rijiyar saboda tsabar rashin jinsa". Kallon rashin fahimta Rumana tai mata, jin ta ambaci sunan Ahmad. Matar data farga da kallon sai tayi dariya, "Au yi haƙuri, na manta sunan mai gidanki kenan Ahmad, bashi nake nufiba, yaron wajena shima sunansa kenan, sai ƙaramar Faɗima muna kiranta Amatullahi". Rumana tai murmushin jin kunya tana cewa, "ALLAH ya raya mana su akan sunna". "Amin ya rabbi Amarya, amma ke yaya sunanki? Ni sunana Husna, amma yanzu dai anan anguwar anfi sanin maman Ahmad". "ALLAH sarki, ni Umm-Rumana, sai dai ni zanke ce miki Maman Amatullah to". "To babu damuwa Umm-Rumana amaryarmu, ai dole a ɓoye sunan mai gida, kije ga ruwa can a banbuna ki ɗiba kafin Abban Ahmad yazo ya ɗakko gugan". "Nagode sosai" Umm-Rumana ta faɗa tana nufar Banbun ruwan kalar ganye dake ƙofar ɗakin Maman Ahmad.
Wanka tayo da ruwan data ɗiba, tayi alwalar walha kamar yanda ta saba ma kanta tun tana gida. Kayanta da aka jera cikin Wadrobe ta buɗe ta ɗauki zani da riga na leshi ta saka, sama-sama ta shafa mai saboda zafi da aka fara, batai wani kwalliya ba sai fauda data shafa da kwalli a idonta. Ta fara jin yunwa, dan haka ta matsa gaban tire ɗin da zainab ta kawo ta buɗe, Fankasu ne da yay luhu-luhu a kwanon silban farko, sai miya a ɗayan kwanon tana ta ƙamshin manshanu, kofin kuwa kunune na tsamiya shima sai ƙamshin kayan yaji yake, tana rufewa Ahmad na shigowa da sallama, kanta a ƙasa tai masa sannu. Ya ajiye ledar hannunsa da kofin roba mai murfi madai daici yana amsawa. Zama yay a bakin gadon idonsa akan kwanikan data gama buɗewa yace, "Miye wannan a ciki?". "Fankansu ne da kunu". Baikai ga amsawa ba wayarsa tai ring, fiddota yay daga aljihun jallabiyarsa ya duba. "Manyan ƙasane haka suka tuna damu?" yay maganar wayarsa a kunne. Daga can Zaheedah tai dariya tana maida masa amsa da "Ai kune manyan ƙasa Shema, yanzu gudun namu da akeyi har takai ai bikinka babu gayyata?". Murmushi yayi mai sauti, wanda har ya saka Umm-Rumana satar kallonsa da mamaki, ta daɗe bataga Murmushi a fuskarsa ba, duk da dama can itadai bayi mata yakeba sai da taga yanayi a majalissar abokansa ko idan yana tare da Samina, maganarsa ta sata sake maida hankalinta garesa batare da tasan dalilin hakanba. "Bani da bakin kare kaina kam, amma dai ina roƙon amin uziri, nasan dai Sufyan ne ya sanar miki, kuma inada tabbacin bazai gaza miki bayani ba". "hhh hakane kam ango, ai banyi fushiba, yanzu ma dai taya murna na kira nayi, ALLAH ya sanya alkairi, yasa nanda wata tara muzo suna tunda ba ai biki da muba". Sai da ya saci kallon Rumana dake wasa da yatsun hannunta kanta duƙe ya lumshe ido, sannan yace, "Humm, kina lafiya? Ya mutan gida?". "Lafiya lau kowa da komai yake" Zaheedah ta amsa duk da taso ya bata amsar maganarta ta farko. Sun ɗan taɓa hira kaɗan, a cikin hirar take faɗa masa sai tazo ganin amarya.
Bayan ya ajiye wayar ya kalli Rumana da har yanzu kanta ke a ƙasa, "Zubamin kaɗan, sai ki haɗamin shayin nan, anjima nasha kunun". Da to ta amsa tana miƙewa, ƙaton banbun ruwanta da aka zuba kwanikan amfani ciki ta buɗe ta ɗauki filet da cokali da kofi, dukda a wanke suke fes sai da ta sake ɗaurayewa sannan ta dawo inda take, sai faman gyara gyalenta dake zamewa take harta kammala haɗa masa shayin, ta zuba fankasu uku yace, "ya isa haka, zuba miyar a kai kawai". Da "to" ta amsa. Bayan ta gama taɗan kallesa, a ɗarare tace, "Ko a saka Sallaya a ƙasa". Kai ya ɗaga mata yana cigaba da danne-dannensa a waya.
Ganin zai fara cin abincin sai ta miƙe zata fita. "Kefa?" Yay maganar ba tare da ya kalleta ba. "In....in..ba banajin yunwa" tai maganar cikin in ina tana sosa gefen kunne. Manyan idanunsa ya ɗago ya kalle, hakan yasata saurin maida nata ta risinar. "Dawo ki zauna ki karya ko ranki ya ɓaci". Dawowa tai tabi Umarninsa, zata zuba wani fankasun yay mata nuni da wanda ta zuba masa. Duk jikinta tsuma yake, itace yau zataci abinci kwano ɗaya da Yah Ahmad?. Yanda ta takure kanta duk yana kula, amma sai yay kamar baisan tanayiba, yaci gaba dacin abincinsa duk da baya masa daɗi sosai a harshe saboda zazzaɓin da yayi, ga damuwar Samina tana nan daram a ransa babu abinda ya ragu a ciki. Bai sake tanka mata ba har suka cinye ukun data zuba masa, wanda shine ya cinye kaso mafi yawa a ciki, buɗe kwanikan yay ya ƙara wasu ukun ya saka miya, Rumana dai na kallonsa batako motsaba, gabanta ya tura filet ɗin ba tare da yace uffanba. Ta kallesa da sauri suka haɗa ido, yanda ya sake tsuke fuska ya sata maida kanta ƙasa da sauri ƙirjinta na lugude, tadai fahinci itace zata cinye wannan kenan?. Yanda bai sake bi takansa ba itama ta kasa kallonsa, ya ajiye kofin tea ɗin da ɗan saura a ciki alamar dai ya ƙoshi, miya tuna kuma oho masa, sai taga ya jawo ledar da madara ke ciki ya fasa ɗayan sacet ɗin ya zuba a kofin da sukari sai nescafe, ya zuba sauran ruwan zafin kofin ya motsa, gabanta ya ajiye ya miƙe nanma bai tanka ɗinba dai. Da kallo ta bisa har ya ɗakko ledojin jiya ya ajiye inda ya tashi, ya buɗe banbun da kwanika ke ciki ya ɗauki kofi, sannan ya buɗe ƙaramin banbun danya ɗeba ruwa amma wayam babu komai. Miƙewa Rumana tayi tana faɗin, "Babu ruwa ai, naje zan ɗiba a rijiya wai gugan ta faɗa jiya, bara nasamo maka wajen maman Amatullah". Baice komai ba ya miƙa mata kofin. Bata jimaba ta dawo ɗauke da ruwan leda a filet. Koda ta ajiye a gabantsa sai ya tsirama ruwan ido kawai ba tare da ya ɗaukaba. Hakan ya saka Rumana tsayawa tana kallonsa itama. "Babu ruwane a gidan sai wannan?". Ya faɗa yana nuna filet ɗin. "Na tambayeta ne shine ta bani wannan wai na rijiyar baida daɗi sosai suma wannan suke sha. Filet ɗin ya tura gabanta, da alamun ɓacin rai a fuskarsa kaɗan yace, "Bani wancan haka nan". Tamkar Umm-Rumana zata fasa kuka haka taji, yanzu mata tai musu abin alkairi kuma sai yace ta maida? To mi zata ce mata ita kuwa?. "Zaki ɗauka ne? ko sai kin gama tunanin?". Kafin ya rufe baki ta sungumi filet ɗin ta fice cikin sassarfa..............✍🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
*(12)*
............Jiki a sanyaye ta koma ƙofar ɗakin maman Amatullah. Maman Amatullah dake zaune tana ɗura zoɓo a gorori na saidawa ta amsawa Rumana sallama tana faɗin "shigo mana Amarya". Kunya duk ta lulluɓe Umm-Rumana, ta ajiye filet ɗin ruwan tana magana cikin in ina "Dan ALLAH kiyi haƙuri, wai ya fi son na rijiyan". Murmushi maman Ama tayi, tace, "Amarya karki damu, haka maza suke, abinda suke buƙata kawai suke so, bara na ɗiba miki wannan yafi ɗan sanyi to". Rumana dai batace komaiba, ta amsa ruwan tana mata godiya ta fice. Inda ta barsa nan ta iske sa yana danna waya, ta ajiye kofin ruwan a gabansa "Ga shi". Bai ce komaiba ya ajiye wayar.
Tana cin abincin da aka sakata dole tana satar kallonsa yanda yake shan magani kamar zaiyi kuka, sai yayi kamar zai sha sai ya fasa yana matse ido, idan kuma ya jefa a baki da ƙyar yake haɗiyewa kamar zaiyi amai. Ba sabon abu bane a wajenta tunda tasan baya son magani, ya ɓata lokaci sosai kafin ya gama shan maganin da bai wuce kwayoyi shida ba. Ficewa yay, mintuna kaɗan sai gashi ya shigo, botiki ya ɗauka ya fita tare da ƙaramin banbunsu. Hakan yasa Rumana miƙewa itama ta shiga tattare kwankan da suka gama, ta ɗakko wani filet ɗin ta juye kazar jiya ta ɗora a tiren da zainab ta kawo abinci ta ajiyesu gefe. Mamaki ya bata ganin yana ɗibar ruwa, da alama dai gugar ya fiddo dan ga ƙugiya nan a gefe ya ajiye. Kwanikan ta ajiye gefe ta koma ɗakin, tana ƙoƙarin shiga ta tsinkayo muryarsa yana faɗin, "Ki kwashe kwanikan nan shima ki fiddosa". "To" kawai ta iya cemasa. Yanzu ita ina zata saka waɗannan kwankan haka? Duk da basu da yawa ɗakin babu wani fili mai yawa daya rage, kuma dai bata ce zata jerasu a ƙasa ba ai. Haka dai ta gama fiddasu ta ɗauki banbun takai masa, sai da ta ɗauraye shi sannan ta ajiye. Ya ɗauki wanda ya cika da ruwan ya kai ɗakin, itako sai kallonsa take, dan banbun yanacin kusan boket huɗu. Ruwan ta ɗiba a ƙaramar roba ta koma gefe tana wanke kwanikan, shi kuma ya ɗauki banbun data ajiye ya maidashi ƙofar ɗakinsu ya ajiye, idan ya cika botiki sai yaje ya juye. Hakan da Rumana ta ganine ya sata miƙewa tabar wanke-wanken, idan ya cika botikin sai taje ta juye, a haka har suka cika banbun da botikan uku, biyu na roba ɗaya na ƙarfe. Ƙarasa wanke-wanke tazo tanai, shikuma ya ɗauki ruwan botikin ƙarfen ya nufi bayi. A lokacin kuma Maman Ama... Ta fito riƙe da Amatullah tana kuka. Rumana tai murmushi tana kallonsu da faɗin, "A'a Amatullah yaya dai?". "Rigima kawai mara dalili, ɗan zoɓon dana rage na ƙasan botiki ta zubarmin a ɗaki, shine kuma bazan gogeba sai na bar mata tai wanka a ciki". Rumana tace, "Lallai hajiyar ɓarna kenan, ina Yayana shi? Ban ganshiba tunda na tashi?". "Wannan ai tun jiya bama ya gidan, da ƙanwata tazo jiya da yamma ya maƙale mata sai da ta tafi dashi". "ALLAH sarki, to ALLAH ya dawo dashi lafiya". Rumana ta faɗa tana kama Amatullah data rarrafo wajenta. Ɗaukarta tayi, ta zauna a bakin rijiyar tana mata wasa, ahaka Ahmad yazo ya wucesu. Ƙin shiga ɗakin Amatullah tayi, har sai da ya leƙo, kamar ance ta ɗago sai suka haɗa ido, "Zonan" ya faɗa kawai yana sakin labulen. Miƙewa tai ɗauke da Amatullah ta nufi ɗakin. Tsaye ta iskeshi yana taje sumarsa a gaban mirror, tace, "Gani Yaya". Bai tankaba sai da ya gama, ya ajiye kum ɗin yana faɗin, "Bara naje can gida baba na kirana, naga babu abin girki ko?". Tai jimm saboda bata gane kan tambayarba. Katse mata tunani yay da cewar, "Risho nake nufi ko abin gawayi". "Eh babu, amma inaga zasu kawo yau sukace". "Okey" kawai ya faɗa yana ƙoƙarin ɗaura agogo a hannunsa, mikuma ya tuna sai taji ya ja siririn tsaki tare da kuncesa ya buɗe jakar daya ɗauki kaya ya jefashi ciki, ya zaro wani ya saka, kumatun Amatullah dake miƙa masa hannu tanason ya ɗauketa yaɗan shafa ya wucesu batare da yace komaiba. Rumana tai ajiyar zuya bayan ya fice tana ɗan girgiza kai, aranta tana tunanin ko yaya wannan zama nasu zai kasance kenan oho?. Fitowa tai tsakar gida tanama Amatullah wasa, inda maman Ahmad ke ɗan mata hira daga kicin ɗinsu tana girkin rana. Ita dai Rumana murmushin ta yafi hirar yawa, dan dama can ita bamai yawan magana bace, ta kuma kula Mama Amatullah akwai surutu. A haka su Fa'iza sukazo suka iskesu, sosai Rumana taji daɗin ganinsu. Suka shiga ɗaki sai shaƙiyanci suke mata, harda tambayarta wai yaya jiyan? Dan sunga Yah Ahmad a gida yanata ƙyallin angwanci. Duka takai musu, suka kauce suna dariya, haka sukaita tsokanarta, kazar kuwa da suka gani sai da ta ɗiba musu, suka kuwa ci suna faɗin, "Tunda ke tsoro ya hanaki kici muko ci mukayi, Rumana wai dan ALLAH da wuya kamar yanda ake faɗa?". Rumana ta kalli Salima mai maganar tana faɗin, "Minene?". Gado Salima ta nuna mata da yin magana ƙasa-ƙasa kamar mai munafunci. Tashi Rumana tayi tsaye, "Oh ni ALLAH ya shiryeku, ni dai babu ruwana wlhy, kuje ku tambayo Yah Ahmad ɗin mana". "Kutumelecy amma baki da man kai Rumana yasin" cewar Fa'iza. Salima tace, "A'a so take ya maidamu niƙaƙƙiyar gyada ta ƙuli-ƙuli alkur'an, kinga kuwa yanzu da muka haɗu dashi a gida sai wani cin magani yakeyi, niko a raina har gulmarsa nayi, nace waishi Yah Ahmad yamayi auren bazai canjaba ne?". Dariya Fa'iza da Rumana suka sanya, Salima ma mai maganar ta tayasu tana sake cewa "Wlhy na zata yau zan ganshi fuska a washe, Rumana ko dai baki bada kai bane?". "Wai Salima yaushe kika koma hakane? To ALLAH ya gyara lamarinki da wuri, kema dai na kula auren kikeso". Fa'iza tai saurin faɗin, "Mi takeci na baka na zuba, Wlhy Malam yace muma mu kawo mazan aure, wai muna gama jarabawa aure za'ai mana, abinda Yaya Samina tayi ya tada hankalin kowa, bazasu sake yarda ƴaƴansu suyi zurfi a karatuba sai dai idan mijinka naso ya kaika da kanshi". Cikin marairaice murya Rumana tace, "Kuma godema ALLAH kuda gashi zaku ƙarasa, ni kam nasan ai nayi kenan". "Karkice haka wlhy, tunda Yah Ahmad nason karatu zai barki ki ƙarasa, ALLAH dai yasa kar bebin mu yay shigar sauri kawai". Hararta Umm-Rumana tayi. Suka sanya mata dariya. Daga nan suka koma hirar Samina, tare da iskance-iskancen data tsuro dasu a gidan a safiyar yau. Rumana tace, "ALLAH ya ƙyauta to, ALLAH ya shiryeta". Amin dai, su Fa'iza suka faɗa a tare.
Su Fa'iza na gidan har Sadiya da Na'ima ƙanwar Rumana suka kawo abincin rana da ƴan tarkacen kwanika da aka ƙara saima Umm-Rumana, harda ƙaramin risho da abin gawayi, sai Abu dake biye dasu da ƙatuwar jakkar Ahmad ta kaya da tarkacensa. Sannu Rumana tai musu, suma suka zauna aka ɓalle hira, Abu nata zuba musu shirme suna kwasar dariya, yaran anguwa kuma nata shigowa jefi-jefi ganin ɗakin amarya, harma da mata maƙwafta ƴan gutsiri tsoma, dan yanda auren ya kasance duk ya shiga kunnensu.
_________________________