Kenza eBookz

Gurbin ido complete hugumah - Chapter 27

Gurbin ido complete hugumah - Chapter 27

Gurbin ido complete hugumah Chapter 27: Gurbin ido complete hugumah Chapter 27. "Na dawo,nace bari na shigo na sanar miki" wata dariya ce ta zowa unaisa,ya…

1,458 words

"Na dawo,nace bari na shigo na sanar miki" wata dariya ce ta zowa unaisa,ya tabbata ja'afar din mugun dan rainin hankali ne,hakazalika da biyu ya dauki yarinyar ya kaita makarantar kwana saboda ya raina ajinta da kwanyarta,to amma hakan yayi mata ita din,tunda ko banza kawo yanzun tana dan samun wasu sauye sauyen,duk da cewa ko sau daya bau taba hada dakin kwana da ita ba

"To yayi" tace mata kawai taci gaba da shan lemonta tana kada qafa gami da ci gaba da kallonta,ganin babu wani magana data sake hadasu sai maimunatun ta miqe zata fita

"Agwai" ta kirayeta da sunan da maimunatun tafita sanin me sunan yake nufi,sunan yadan sosa ranta,amma bata nuna ba ta waiwayo tana dubanta

"Am please idan kin tashi girkinki,ki dinga yi iya cikinki,wanda naci a baya ma shahada nayi,don ba abinci kowanne irin mutum nake ci ba,so ina da masu aiki,zasu dinga yin komai" kai ta gyada sannan tayo gaba tana bar mata dakinta.

Ga mamakinta sai taji maganganun unaisa sun dan sosa ranta kadan,abinda tun tasowarta da irin cin zarafin data gamu dashi a rayuwa bata taba jinsa akan kowa ba,ko hakan yana da nasaba da zama dasu afra?,hakan na nufin ta fara sanin kanta da kuma sanin mene ne rayuwa?. Muje zuwa dai.

Tunda ta dawo gidan bataga koda gilmawar J ba,abinda ko sau daya bai ɗaɗata da ƙasa ba,sau tari mancewa take dashi kwata kwata cikin rayuwarta,tasa litattafanta a gaba tana ta haddar hadisan data daukarwa malamin islamiyyarsu alqawarin zata kawo masa su kafin a koma hutu,da kuma izifin data diba shima zata daw da haddarsa,don hatta haddar qur'aninta bata bari ta tsaya ba,tana ganin wannan damar ta roqa alfarma,yake mata qari kuma tana kawo masa.

Ta fannin boko ma litattafan da zasu sake inganta mata koyo da gane turancinta ta karba aro masu yawa daga library din makaranta ta taho dasu,wadan nan abubuwa sune abokan hirarta,kewar da tayi fama da ita zamanta na baya a gidan yanzu duka babu,mantawa ma take da inda take,wani lokaci ma idan tayi breakfast bata sake neman abinci saina dare,batajin yunwa sam idan ta duqufa karatunta,bare kuma ba wani motsi zatayi me yawa ba bare ya zazzage mata cikinta ya jawo mata yunwar ba,tana daki kwance,saman gado idan ta gaji ta dawo falo saman kujera,ba kasafai take shiga kitchen din ba,dalilin da yasa har zuwa sannan batasan ma kalar 'yan aikin da unaisa ke maganar ta kawo ba,don sanda zata shiga da safe basu soma nasu aikin ba,lokacin da zata sake komawa kuma dare yayi sun gama nasu aikin sun bar kitchen din.

To da wannan damar data samu yasa tayi karatu me yawan gaske,wanda ita kanta batasan ta yishi ba,hutun da akazo gida don yinsa nata hutun kadanne.

Randa tayi sati a gidan,tana daga bakin window dinta ne taji cewa ja'afar din tafiya yayi ashe,ta bakin unaisan sanda tayi baqi take rakasu zuwa parking lot na gidan xasu shiga motarsu,saita janye zuwa ciki,ta bude shafin gaba na littafinta taci gaba da karatunta.

Sai da tayi kwana takwas da dawowa sannan su fa'iza suka zo mata,harda amnanta,ranar kamar sallah haka ta jita,sun sameta anata sana'ar wato karatu,amna na jikinta ta dauketa zuwa kitchen don ta sama musu abun sha,kafin tayi tunanin me zata girka musu.

Sanda suka shiga amnan nata mata tambayoyi da zuba mata surutu,tabbacin yarinyar tayi kewarta matuqa,bata lura da unaisa dake tsaye riqe da cup da yoghurt a hannunta ba har sai data kirayi sunan yarinyar,tare suka waiwaya zuwa gareta ita da maimunatun,maimunatun ta dubi yarinyar data zubawa unaisa idanu tana kallonta,duba na rashin sani da kuma rashin sabo

"come-on baby,new mom dinki ce" unaisa ta fada tana murmushi gami da miqawa yarinyar hannu,karon farko da yaro ya burgeta,kasancewarta ba ma'abociyar son yara ba,tsantsar kamanninta da silly mahaifinta din nan ya bayyana,tana fatan batayo miskilanci irin nasa ba.

Kamar kuwa yarinyar tasan me take rayawa a zuciyarta,sai ta noqe kafada tana ci gaba da kallonta

"Zo mu gaisa mana,haba amna,nace miki new mon dinki ce" ta sake maimaitawa dai,sai ta sake maqale mata kafada,wannan karon kallon fuskar maimunatu dake duba lemon da zata dauko musu tayi

"Wannan ce new mom dina,ke ban sanki ba" ba unaisa da yarinyar ta fadawa maganar ba,ita kanta maimunatu taji mamakin maganar,ta dago kanta tana duban fuskarta,waye ya gaya mata itace new mom dinta?,ya akayi ta fahimci haka?,duk da dai yarinyar nada wata muguwar kwanya da kaifin basira,wanda maimunatu tafi tsammanin daga wajen mahaifinta ta gajeta.

Sauke amnan tayi qasa tana dubanta

"Itama new momma ce,kije ki gaisheta kinji" saita gyada kai,duk da bata sake jikinta ba amma haka ta nufi unaisan,abun ya yuma unaisan ciwo sosai,yarinyar ma ba zata zo wajenta ba sai wannan agwai din ta yarje mata,ta kuma yi mata umarni?,ta zabgawa maimunatu harara sanda ta riqe hannun amna,hararar da maimunatun bata ma san tana yinta ba,da hilata ta samu ta janye amnan zuwa part dinta,saidai suna tsaka da hira sai ga daya daga cikin masu aikin unaisan sun dawo da amnan,idanu fici fici da alama rigima ko ma kuka tayi musu.

To hutun kwata kwata na sati hudu ne,suna gama satittikansu suka sake diba suka koma makaranta,maimunatu ta sake dasa yaqin neman karatu,babu ji babu gani,bakin rai bakin fama,su kansu su afrah sunyi mamakin yadda qwaqwalwar maimunatun ta sake budewa daga zuwanta hutu zuwa dawowarta,ta dings musu dariya ganin yadda dukka suke mata duban mamaki,a wani yammaci suna hanyar zuwa islamiyya,bayan ta bada amsar wata tambaya cikin subject din math,shi kansa malamin sai data burgeshi yadda ta amsa question din a gaban allo.

To bata qarasa basu mamaki ba sai da sukaje islamiyyan,duka ta zubewa malaminsu haddar hadisan data yo,a washegari kuma zai karba na qur'ani,wannan yana daya daga cikin abinda ya sake zaburar dasu suma,sannan kuma farat daya sunan maimunatun ya fara tambari cikin makarantar,tun daga juniors dinsu zuwa seniors,cikin watanni shida kacal ta fara zama sananniya,duk wanda kacewa maimunatu abubakar muhammad zaiyi wuya yace maka bai santa ba,dalibai maza da kuma mata,saboda zuwan da tayi da tarin baiwarwarki a lokaci qalilan,kyakkyawar bafulatar usul,wadda ke dauke da wani irin kyau mejan hankali,musamman da a yanzun take zaman makarata,daga dakunan kwanansu sai ajujuwansu na boko sai kuma masallacin makarantar inda a nan suke gudanar da islamiyyarsu,fatarta ta sake wani irin haske,kamar zata tabata jini ya fito,jajayen labbanta da bata sanya musu komai sun sake ja,hakanan idanunta masu wani irin kyau da suke dauke da golden din qwayar idanu,ita kanta takan jima gaban mudubi tana kallon kanta,tare da tambayar kanta ita dince kuwa?,itace maimunatun rugar ummaru?,itace maimunatun inna furera?tabbas ta canza,canji me nisan tazara kuwa.

Duk da cewa gayu da wasu dabi'u nasu afrah sun ratsata,har sun zame mata jiki itama ba tare data sani ba,amma hakan bai hanata yin takatsantsan da kanta ba,qwarai ta sani cewa ba daya suke dasu ba,ita din akwai auren wani a kanta,zuwa yanxu ta sake samun ilimi sani da kuma wayewa kan muhimmancin aure da girman matsayinsa saman kan kowacce diya mace,duk da cewa takan manta sosai da cewa ita din matar wani ce,don shi kansa wanda aka daura mata igiyar ta sanadinsa ba ganinsa take ba,wani lokaci sai taje hutunta har ta dawo baifi su hadu sau daya cikinn gidan ba,idan an samu akasi ne suke haduwa biyu,gaisuwa kusan itace maganar da take gilmawa tsakaninsu,har yau har gobe basu taba wata magana data gota babin gaisuwa da amsa ba.

Tana qoqarin tunawa kanta cewa ita din me aure ce,bawai don damuwa ko soyayya ba,haka kawai cikin ranta takeji bai kwanta mata ba ko kadan,me yasa bai dauko halin hisham ba?,hisham din mutum ne da take matuqar ganin kima mutunci da kuma martabarsa,bata ga alama koda ta kuskure da zata nuna maka yana mu'amala da wani abun maye ko shaye shaye ba,sabanin shi da tun ranar data fara ganinsa tasan cewa mazuqin taba sigari ne,sauran abinda kuma yake sha wannann Allah ne kadai ya barwa kansa sani,tunda ita a nata hasashen,duk wanda yake shan sigari to yana shan komai ma na kayan maye.

Abu na biyu hisham din mutum ne me kimanta dan adam da darajtashi,koda yaushe yana faran faran da ita dama sauran qannansa,a gu daya take ganin kamewarshi da nashi salon miskilancin shima,idan ya fita cikin mutanen da suke ba ahali a garesa ba,ko kuma baqin fuska,a duk sanda zai dawo da ita makaranta ko kuma zai maidata,hira ce me tsafta take wanzuwa a tsakaninsu,yakan bata shawarwari da qarin haske akan karatunta,labarai da suke da nasaba da karatu,kamar labarin lokacin da yake dalibin secondary kamar ta,takan iya sakin jiki dashi kadan yanxu,wannan baquntar da take masa a da yanzu ta ragu sosai,yayin da shi kuma yake girmamata kamar yadda zai girmama dan uwansa,har wani lokaci yakan bata kunya ainun,ganin cewa ya girme mata nesa ba kusa ba,ita yafi cancanta ta bashi wannan girman.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull