Gurbin ido huguma complete - Chapter 22
Gurbin ido huguma complete Chapter 22: Gurbin ido huguma complete Chapter 22. Yana shirin bude motar yaji sallamar khadim a bayansa,sai ya waiwaya yana…
3,349 words
Yana shirin bude motar yaji sallamar khadim a bayansa,sai ya waiwaya yana amsawa,cikin girmamawa ya miqa masa wasu ledoji dake hannunsa
"Gashi inji ammi" jim yayi na sakanni yana bin ledar da kallo,sai kuma ya bude masa back seat bau tare da yace komai ba,khadim din ya fahimta abinda yake nufi,don haka ya qarasa ya saka musu su a baya,har ya juya zai tafi yace masa
"Kace mata na gode" yayi maganar ne sanda yake shigewa cikin motar,ya maida.murfin ya rufe ba tare daya jira cewar khadim ba.
A hankali yake tuqin kamar wanda baison isa gidan,tafiyar data daukeshi mintuna masu tsaho fiye da mintunan da zasu isheshi a al'adance,horn daya mai gadin gidan ga dage masa gate din,sai a sannan yadan ja motar da gudu ya shige da ita farfajiyar gidan,sannan ya faka ta a parking lot idanunsa na sauka kan wata qaramar sabuwar mota ruwan zuma,ya dauke kansa yana kashe tasa motar.
Har ya fito ya tuna da ledojin da ya bari cikin motar,sai ya koma ya debosu,tun kafin ya bude ma ya fuskanci meye a ciki,sai ya riqesu a hanauyensa,dai dai sanda me gadin gidan ya iso cikin rusunawa ya fara gaidashi,amsa masa yayi cikin kulawa,saboda yana daga cikin dabi'arsa girmama duk wanda yake aiki a qasansa,barshi dai da zafinsa miskilanci rashin daukan raini da rashin son wasa da aiki,hannunsa ya sanya cikin aljihunsa ya fiddo 'yan dari biyar biyar sababbi guda shida ya miqa masa,hannu biyu ya sanya ya karba yana ta zabga godiya,yayin da shi kuma yayi gaba abinsa ba tare da yace tak ba.
Sai da yayi addu'ar shiga gida sannan ya kutsa kai cikin babban falo,shuru yake babu alamun motsin me rai cikin gidan,cikin nutsuwa ya fara takawa zuwa stairs,sai kuma ya tsaya cak saboda maganar da abbi da kuma amma suka gaya masa a daren jiya da yau,ledojin hannunsa ya kalla,a hankali sai yayo baya,ya kuma nufi qofar dake hannun dama na falon.
A hankali ya tura qofar,falo ya bayyana,wanda aka qawata da kalolin kujeru da curtains masu azabar kyau,royal blue da golden,komai na falon,a tsaftace yake cikin qamshi da sanyi daya gauraye da sabunta,ci gaba yayi da tafiya har ya isa qofar bedroom din,itama ya turata ya shige.
Dai dai lokacin da take zaune saman abun sallah,saboda ganin yadda lokaci yaketa tafiya,an doshi sha biyu na dare,kuma ana binta sallar isha'i da kuma shafa'i da wuturin da batayi ba.
Can qasan maqoshinsa yayi sallama idanuwansa suna sauka a kanta,gabanta ya buga fat,don bata tsammaci shogowarsa din ba,saboda dukkan wata magana daya gaya mata a jalingo ta haddacesu tsaf a kanta, janye kansa daga wajen da take yayi,ya isa gaban madubi ya ajjiye ledar a kai,sai ya tsaya yana goye da hannayensa a qirjinsa.
Raka'ar qarshe take amma kawai sai ta miqe taci gaba da kawo wasu raka'o'in,abinda ya sanyashi sakin hannayensa kenan,ya kuma juya a hankali ya fice a dakin bayan yaja qofar kamar yadda ya ganta.
Sallamewar sallarta ta fito ne hade da ajiyar zuciya,ta danyi shuru tana karanta la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,tana kuma jin yadda zuciyarta take bugawa,lumshe idanunta ta sakeyi,ba shakka tana tsananin tsoronsa,tana tsoronsa bilhaqqi da gaske,hoton sanda ya zuba mata lafiyayyen marin nan ya gilma a idanunta,sai kuma sanda yake zuqar hayaqin taba yana bulbular da ita daga bakinsa zuwa hancinsa,sai ta girgiza kai,tana jin wani bala'in haushinsa yana ratsata.
Yaya akayi ya kasance mashayin taba?,bayan shi din ya fito ne daga gidan tarbiyya kamar haka?,mutane masu karamci dattako da sanin darajar dan adam?,bata tunanin akwai wanda yasan yana sha din cikin gidan,don ko da wasa bata tabs jin anyi magana makamanciyar wannan ba.
Tunanin ta ture gefe,ta fara karanto azkar dinta da bata samu tayi ba a yau din,gefe na zuciyarta kuma cike taf da kewar amna,tana jin cewa zaiyi wuya bata nemi su anni su bata yarinyar ba,don ko a yau ma sai da akayi wayon janyeta sannan suka tahi,wanda ita bata kawo hakan ba,ta tsammaci zasu taho ne da ita,amma sai taga akasin hakan,to me zata zauna ne tayi a gidan?,gwara gwara ma ace da amnan,zata taimaka mata wajen debe kewa.
Kamar yadda ya shiga sasssan maimunatu haka ya shiga na unaisa,saidai ita ya sameta tsaye ne a gaban mudubi tana kallon kanta bayan ta gama sake feshe jikinta da turare tana gyara zaman rigar jikinta.
Sallamarsa hade da turo qofar ya sanyata saurin maida mayafinta saman kanta, ta rufe ruf,saidai tana iya hangensa ta cikin mudubin,wani sassanyan abu ya ratsa zuciyarta ya kuma haifar mata da yalwataccen murmushi akan fuskarta,a fakaice taci gaba da binsa da kallo,tana jin wani farinciki yana ratsata,burinta ne na tsahon wasu shekaru Allah ya cika mata shi,duk da cewa ranta ya baci a dazun da ganin irin gidan daya zaba a jjiyeta kuma tare da wata,saidai anty talatu ta kwantar mata da hankali
"Kinsan baso yake ba,ta yiwu yayi hakanne don ya baki haushin dama harkiyi wani abu da zai janyo a fasa gaba daya,dole fa saikin anjiye rashin haqurin nan,kin janyo hankalinsa a hankali a hankali,sanda zai canza miki gida ko ya rabaki da qasar ma gaba daya bai sani ba" qwarai ta gamsu da maganganunta,don haka ta ajjiye komai gefe a ranta.
Cikin salo ta amsa sallamar tasa cikakkiyar amsawa,bai sake cewa komai ba itama ya ajjiye mata ledar,ga zatonta zai qaraso koda gefanta ne yace wani abu da ita,saidai gani tayi yana shirin ficewa,muryarsa can qasa ya furta
"Gudnyt" ya tursasa zuciyarsa ta fada,duk don son ganin yayi abinda ya dace bakin gwargwado.
Gabanta ne ya fadi sanda yake gab da fita,ta daga kai tana dubansa ta madubin,zuciyarta tana bata shawarar tsaidashi,yayin da wata zuciyar ke hanata,tana gaya mata girman wannan rana a wajenta,ita yafi kamata ace an tsaida,an kuma nema kasancewarta cikin dakin,tana wannan shawarar da tattaunawar da zuciyarta har ya fice.
Kasa zaune tayi,ranta ya baci sosai,ta dinga kai kawo tana tunani a ranta,shin sassansa ya tafi ko kuwa na maimunatu?,sai taji zuciyarta taqi aminta da hasashen daketa mata yawo,don bai kamata ace sassan maimunatun ya fara sauka ba,tunda a qa'ida itace babba,ta girmewa maimunatu,ita ya kamata ta fara karbar baquncinsa,tafi maimunatu sanin rayuwa dama komai da komai da za'a tarairayi mutumin da ya jima babu mata a gefansa kamarsa,don haka ta gyara rufin mayafinta,ta kuma bude qofar ta fito.
Bata ma isa sassan maimunatun ba taji motsinsa daga sama,don haka taja birki,ta kuma koma nata sassan,girman kai yana sauko mata,tana jin ba zata iya nemansa a yau ba itama.
Yana shiga dakin ya sauke ajiyr zuciya mai qarfi kamar zai tofar harda qirjinsa,ya soma bin dakin da kallo,an qawata masa shi yadda yakeso ya kasance,idanunsa daya bayan daya suna sauka kan hotunan shaheeda da amna da amra wanda aka musu tare yasa aka gyarasu aka shiryasu a falon gwanin burgewa,kai kace idan ka kirayesu zasu amsa,zakayi tsammanin har yanzu sune ke rayuwa cikin gidan,addu'ar da baya gajiya dayi musu yayi wani abu na motsa ransa,ya wuce zuwa bedroom dinsa.
Sai daya gama duba komai daya ce a sanya masa a dakin,wanda yake buqatar ya canza masa waje ya canza masan ya ajjiyeshi inda yakeso,sannan ya fidda kayan jikinsa ya zubasu a laundry basket,sai ya wuce toilet kai tsaye,ya daura alwala sannan ya fito ya kuma bude walking wardrobe dake manne da bedroom dinsa ya shiga ya duba wasu navy silk pyjamas Natalya's company,ya shirya kansa wadata jikinsa da turaren da yake amfani dashi duk dare,sannan ya feshe kansa da BB hair spray.
Abun sallarsa ya shimfida sannan ya tattara dukkan hankalinsa da nutsuwarsa ga alqibla.
Unaisa kuwa kusan raba dare sukayi suna waya da anty talatu qanwa ga mahaifiyarta haj Aayah,tana gaya mata abinda yafaru,ita kuma tana shirya mata yadda zata aiwatar da komai,sun jima sosai suna tattaunawa kafin suyi sallama
"Amma dai lafiya ko?" Haj Aayah da suke kwance daki daya da qanwarta wadda bata kai ga komawa gida ba ta tambayeta
"Eh to,lafiya amma ba lau ba" abinda ya farun ta gaya mata,sai ta sauke ajiyar zuciya
"Yaron nan fa ba lafiyar kwanya ya cika ba,idan anyi magana sai kuce depression ne ya kamashi bawai ciwon hauka ba,ni tsorona ma kada ya kama min diya ya jibga,don banjin zanyi kawaici,babu yadda banyi da unaisa ta haqura dashi ba amma ta kasa haqura" murmushi talatu tayi
"Banda abinki yaaya,ta yaya yana da ciwon hauka zan goya ma unaisa baya ta aureshi,an gaya miki ciwon damuwa ne,kuma a yanzunma komai yana wucewa tunda gashi ya amshi mata har biyu,mudai burinmu kawai diyarmu tayi zarra ta zama star dinsa,don kishi da bafulatana sai an kula,shegen surkulle garesu" haka suka yita tattauna maganar a tsakaninsu a daren.
Itako maimunatu wani nutsuwa ta sauko mata bayan ta gama dukka addu'o'inta ta isa ga gadonta ta kwanta,gadon data dinga ji kamar ba nata ba,dakinma kansa jinsa take kamar an bata aronsa ne,kewa da kadaici suka dinga damunta,sosai ta dinga ji cikin ranta inama ace an bata amna,sannu a hankali idanuwanta suka dinga nauyi,bacci kuma me qarfi ya fusgeta.
*Follow my arewabooks account for more latest pages*
*Arewabooks:HUGUMA* ______________________________
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107
*_THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 29
Tafiyar mintuna ita ta sadasu da unguwar cikin gidan minister,sun samu tarba me kyau bayan haj Aaya ta samu sanarwar zuwansu,waje na musamman cikin gidan tasa aka kaisu,sannan tasa aka taso mata unaisa dake barci a sannan,ta fara shiryata da kanta bayan ta sanyata ta sake wanka,cikin wani material na alfarma mai dan banzan kyau da tsada.
Karo na biyu ja'afar ya sake duban agogon hannunsa,yayin da yake biye da maganar da jabir din ke masa kan dakunan da aka kamawa baqinsu sunyi kadan,za'a qara wasu da kuma yadda suka tsara event din da za'a gudanar
"Komai yayi,amma banda ni a taronku,saboda babu abinda zanje a ciki,walima ce kawai ta zama sunnah,ita dince ma nake tunanin zanje,anma fa babu tabbas itama,kada ka zura jiki da yawa" yayi dukka wannan maganar yana kallon lafiyayyen agogon dake kwance a fatar hannunsa
"Time up" yafada yana miqewa tsaye cak,sai jabiru ya bishi da kallo
"What do you mean?" Sai daya zuba hannayensa duka cikin aljihun rigarsa yana duban jabir
"Mintuna takwas nayi niyyar ware mata a yau din,kuma ta cinyesu wajen jira, you know.....i don't wait for anyone,amma dai na cika maganar abbi tunda nazo" dubansa jabir yake cike da mamakinsa,ja'afar.....ja'afar?.
"Amma dai abbi ba cewa yayi ka shigo gidan ka fita ba ko?,cewa yayi kuga juna,ka ganta ne J?"
"Na meye sai na ganta?,no need" ya amsa masa yana dage kafadarsa,sai ya juya da zummar takawa yabar wajen,dai dai sanda ta iso,cikin matuqar ado,mutum uku cikin masu aikin gidan na biye da ita da.manyan trays da aka jerawa kayan ciye ciye da shaye shaye.
Idanunta a kansa,kamar yadda fuskarta ke baibaye da murmushi
"Hello" ta fada tana waving hannayenta,murmushin fuskarta na sake fadada
"Welcome our bride" amsar jabir kena data qara ninka farincikin dake zuciyarta
"Thank you " ta amsa masa kafin ta sake maida dubanta ga ja'afar wanda har yanxun yake tsaye
"am sorry,i keep you waiting ko?" Ta fada tana murmushi,sai ya motsa kafadarsa
"Don't mind,ina cika umarni ne" gatsal jabir yaji maganar tayi masa,bai murmure daga wannan ba yaji unaisan na cewa
"Have a set please?,kaman maganan zaune tafi ta tsaye"
"It's too late......lokacin zamana ya cika,i have a lot to do,see you later" ya fada yana qetareta zai wuce abinsa.
Wani abu ne ya tsayawa unaisa a wuya,duka wannan lokacin data bata amma ko na minti uku cikakke bai kasance da ita ba zaice tafiya zaiyi?,uwa uba ma sau daya tak taga ya kalleta ya dauke kai?,tana da tarin.abubuwa masu yawa da takeson su tattauna dashi,don haka batayi qasa a gwiwa ba tabi bayansa tana tsaidashi
Cak ya tsayan,sai taji abun ya mata nauyi kasancewarta maje mai bala'in jin kai,sai itama fa tsaya tana duban ingarman bayansa take tsaye sosai tsakanin mayalwatan kafadu dake cike da siffar qarfi da cikakkiyar tsaiwa ta cikakken namiji,a hankali taga ya waiwayo,ya kuma tako zuwa gabanta ya tsaya,tsaiwar da taji ta har tsakiyar kanta,saboda tazarar dake tsakaninsu bata da yawa,uwa kuma wani shegen kwarjini yayi mata,wanda ya mamayeta kota ina,qamshin lallausan turarensa ya ziyarci hancinta,sa'annan kuma hucin fitar numfashinsa data rasa me yasa yake fita da nauyi haka?,bata gane amsar tambayar tata ba sai daya fara magana,ta fuskanci cikin fushi yake,ransa ne ya baci,abinda ya bata tsoro kenan,duk da cewa fuskarsa a murtuke take cike da rashin fara'ar da dama can kowa da ita ya sanshi,to amma wannan bacin ran dake kwance saman fuskarsa bai jima da samoshi ba
"Ki kula,ki kuma yi a hankali,banason matsi ko takura,zaifi kyau ki kasance me nisantata akan yunqurin kusantata da kikeyi,stay away from me.....na gaya miki wata gaskiya guda daya wadda babu lallai a samu wanda ya gaya miki ita?" Yayi maganar yana dage girarsa dukka biyun,bata amsa masa ba saboda wani yanayi daya shigeta,shima bai damu ta amsa din ba ya dora mata
"Bana buqatar rayuwar kowacce mace da sunan matata a cikin tawa rayuwar,already na rufe wannan babin,idan kin shirya ma kuma kutsa kanki ciki...... it's okay for me" ya qarasa fada yana dage kafadunsa,sai ya juya cikin takun nan nasa mai cike da ginshira yana barin wajen.
Ko sau daya batayi yunqurin tsaidashi ba kamar dazun,sai kallo data bishi dashi qirjinta yana dukan uku uku har ya bacewa ganinta,kafin muryar jabir ta katse mata dukka hanzarinta
"Are you okay?" Ya tambayeta yanason karantar yanayinta,don baisan me ja'afar yace da itaba,kasancewar akwai tazara tsakaninsu,amma yafi kowa sanin halinsa,tabbas something bad happened,akwai abinda ya gaya mata,saboda yadda fuskarta ta sauya gaba daya ta kuma birkice.
Abirkicen ta girgiza kai
"Akwai damuwa tabbas" batayi qasa a gwiwa ba ta gaya masa maganganun da sukayi,sosai jabir yaji babu dadi,amma a zahiri sai ya kawar da hakan daga saman fuskarsa
"Karki damu,nasan J,a yanzun rashin sabo ne ya kawo yake gaya miki haka, with time zaku saba,zakiga kuma kaman bashi ba" sosai yayi qoqarin gaya mata maganganu masu kwantar da hankali,har sai daya fuskanci ta nutsu sannan ya taka mata gaban main entrance na gidan,sannan ya wuce zuwa inda suka ajjiye motarsu.
Hannu yasa ya bude murfin motar idanunsa na sauka kan fuskar ja'afar,wanda ya kwantar da seat din motar ya kuma miqar da bayansa sosai a kai,jin bude motar baisa ya motsa ba,har sai da jabir ya shigo,sannan ya bude kyawawan idanunsa da suka sauya kala a hankali ya watsasu kan fuskar jabir
"Kaci sa'a kaine,da saidai kazo ka samu empty din wajen"
"Yanzun ma me ya hanaka tafiya?,tunda kazo kayi abinda ranka yakeso?" Ya amsa masa yana dan nuna masa bacin ransa,duk da yasan ja'afar din dole abishi a sannu,saboda wata irin zuciya da yake da ita da bata iya qaramin so ko qi ba,hakanan ba qaramin riqo shaheeda ta yiwa rayuwarsa ba adan tsukin lokacin na zaman da sukayi.
Bai sake cewa jabir komai ba,sai dan qaramin tsaki da yaja yana tada seat din ya zauna sosai,tun basuyi nisa ba suna isa wani guri yace jabir din ya saukeshi qofar wani gini,kamar ya tambayeshi me zaiyi sai yaja baki ya qyaleshin,ya saukeshin ya kuma wuce da motar.
***********Dukkan tafukan hannayenta ta buda tans kallon tsakiyarsu,batasan me zata tuna ba,saidai ta samu kwanyarta fayau babu komai tun daga sanda taji ana hargowa sa hayaniyar zuwan al'ummar gombawa,ta dai tsinci kanta da matuqar sanyi da kuma faduwar gaba,wanda tunda aka fara bikin kwana hudu kenan yau cikon na biyat bataji irinsa ba sai yau,tasa ran ganin anni da amnanta cikin matan da suka iso,saidai babu daya cikinsu,kusan dukka baqin fuska ne idan ka cire anty maama wadda ita ta jagoranci tafiyar.
Ko ba'a gaya mata ba tasan cewa ayau qaramar hukumar ta gembu ta karbi baquncin manyan mutane irin wanda bata taba karba ba,jiniya da qarar ababen hawa kala kala ke tashi,hayaniyar da hatta cikin dakin da take zaune bai tsira ba,dakin dake cike da 'yammatan fulanin da suke danginta ne,duk kuma cikinsu bataga gaje ko gilmawar inna furera ba,tun ranar da za'ayi mata kamu inna fureran ta iso,da tarin sharrikanta wanda ya zame mata tonuwar asiri saboda zuwan yuuma garin,wadda da ita ake gudanar da komai,batasan inda inna fureran tayi ba tun ranar da aka silleta,umarni dai na qarshe da aka bata maimunatu tayi yaqinin shine abu mafi tsauri a wajenta da zai iya sanyata batan dabo
"Ki tattaro duk wata dukiyar dabbobi ta shatu da maimunatu dake hannunki ki kawo mana ita" bammmm!!!!.
"Alhamdlh,aure ya dauru" muryar maroqin mai babban maqogaro ta kwararo cikin gidan,ta kuma isar da saqon nasa inda yakeson ya isa,lungu da saqo na gidan,sai kuwa mata suka dauki guda,gudar data zagwanyar da duk wani qwarin gwiwa na maimunatu,ta nannade kanta da kyau cikin mudukajenta(kayan saqi na zallar lallausar auduga na musamman da matan bappa sama'ila suka tanadar mata harda na yafawa saboda wannan ranar),take taji kamar zazzabi keson kamata saboda sanyi daya fara ratsa qashinta wanda batasan dalilinsa ba,tana jin 'yammatan na waqe waqensu na fulani suna kuma tsokanarta amma ko motsawa batai ba.
Tana ji daga tsakar gida wata qanwa ga kakarsu ta wajen mahaifi tana fadin tare za'a wuce da ita da 'yan daurin aure zuwa can gombe,sunce nan da awa daya a shiryata" gabanta yayi mummunar faduwa,tana jin fargaba sosai,tana jin kamar su annin baqinta ne,duk da zuciyarta na gaya mata,bawai dasu anni zata zauna ba,zataje ne tayi rayuwa da wasu mutane na daban da batasansu ba,batasan halaye da dabi'unsu ba,bakuma tasan yadda zata fusakanci zama dasu ba.
Tana jin sanda aka gama tiri tirin hada kayayyakinta tsaf,yuuma na tsaye akai,tamkar ba daga dangin ango ta fito ba,domin tace ita din a yanzun uwace ga maimunatu bawai suruka ba,ita ta riqeta ta rakata zuwa gaban baffaninta da wadanda ke a mazaunin uwayenta a yanzu,sunyi mata dukkan nasihar da akewa kowacce diya mace a al'ada sanda ta tashi tafiya gidan miji,dukkan wannan abubuwan maimunatu ganinsu take kamar a majigin film bawai a gaske ba,kamar raqumi da akala haka take biye dasu sanda suke riqe da ita zuwa jerin gwanon motocin dake jiran fitowarta,su kuma tashi dasu zuwa gombe.
Shi daya ne cikin motar sai driver kamar yadda jabir ya tsara hakan ba tare dashi ya sani ba,zaman da yayi cikin motar ya yishi ne yana jiran fitowar jabir da yace yayi mantuwa a inda suka zauna,duba daya zakayi masa kasan cewa ango ne shidin zammm,yayi wani irin kyau na musamman cikin wata arniyar shadda ruwan sararin samaniya,wadda ta lashe maqudan kudade tun daga wajen siyota har ya zuwa dinkin da aka yi mata,aikin hannu me matuqar kyau tsari da kuma tsada,takalmin sauciki kalar dark blue sosai daketa daukar idanu saboda sabunta kyau da kuma tsafta yana aje gefe,qafafunsa babu komai sai sock,gefensa ya fidda babbar rigar ya ajjye,a samanta ya cire hularsa kalar dark dark blue da ratsin light mai wani irin walqiya da daukar idanu ya ajjiyr hade da babbar rigar,hatta da links din hannun rigar gold color ya cireshi,ya nade hannun rigar zuwa gwiwar hannunsa,gargasarsa dame kwance luf ta bayyana sosai.
Wata magazine data wallafa sunayen fitattu kuma manyan kamfanunuwan gine gine a satin yake dubawa,kamfaninsu shine yazo a jeri na biyu,duba bayanan yake,amma can tsakiyar qirjinsa wani irin nauyi ne dake cunkushe a cikinsa,ranar ta yau gaba daya tazo masa ne kamar cikin mafarkai,tunda ya auri shaheeda kuma mutuwa ta rabasu bai taba tsammanin akwai rana irin wannan da zata zo ba,dukka wannan abun yanata qoqarin yaqi da abinda yakeji cikin zuciyarsa ne,amma a yau din,babu wadda ke ziyartar zuciya da kuma tunaninsa sai shadeedan,yana tuna rana irin ta yau cikin rayuwarsu data kafa masa tarihin da bazai gogu ba har abada.
Haske ne kadan ya bayyana a motar bayan an bude murfin motar,yana shirin daga kansa ga zatonsa jabir ne,sai yaji muryar mata suna fadin