Kenza eBookz

Gurbin ido huguma complete - Chapter 33

Gurbin ido huguma complete - Chapter 33

Gurbin ido huguma complete Chapter 33: Gurbin ido huguma complete Chapter 33. "Silly girl" ya fada qasa qasa,sake mele baki tayi zata sake sakin…

3,342 words

"Silly girl" ya fada qasa qasa,sake mele baki tayi zata sake sakin kukan,kamar yasan da haka ya kuma daga shanyayyun idanunta acikin nata,sai tayi hanzarin kulle nata idanun,ita kadai tasan me yake haifar mata idan ya mata irin wannan kallon,yana qara mata razani a kansa da kuma wani irin kwarjini da takeji kamar zai sata narkewa a wajen.

Sannu baba tabawa ta matso tana mata sanda ta duqufa yana mata tofi a hannun nata,ya kwashi kusan minti talatin yana mata tofin babu tsayawa,sannan ya zare hannunsa daga cikin nata

"Sannu maimunatu" baba tabawa ta fada fuskarta na nuna alhini,idanunta akan hannun nata da yayi jaa abinka da farar fata,kanta ta gyada

"Ko za'a kaita asibiti?" "no need,bazai komai ba....in sha Allah,zanma hisham magana,zai prescribing mata pain killer,sai a kawo,she will be okay"

"To Allah yasa"baba tabawa ta amsashi,duk da bata gane komai da komai da yake fada ba

"Ki cire hijabin kisha iska" baba tabawa tace da ita,sai ta noqe taqi motsawa,ta yaya zata fidda hijabin data saka saboda yiwa jikinta shamaki,ya fuskanci sarai saboda shi din taqi motsawa,sai ya miqe kawai yana kwashe wayoyinsa ya xuba a aljihunsa

"Manya....ai ba abinda kaci" kai ya gyada

"Am okay,thanks" daga haka ya juya yana barin falon,yana kuma sanya hannunsa a aljihunsa yana laluben key din motarsa,don yau a masallacin wuro bokki yakeson yin ssallar juma'a,yanason kuma samun gaba gaba,ya tabbatar abbi ma yana ciki yanzu haka. [11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 46

Tunda ya dawo gidan baba tabawa tasan ya shigo,ta kuma gayawa maimunatu a fakaice indirectly cewan ya dawo din,ta yita zuba ido taga ta fita yi masa sannu da zuwa ko wani abu makamancin hakan amma bata gani ba,tunda tasan unaisa bata nan,dazun da ta zaga baya tana tsinkar musu lemon tsami taga fitarta,babu kuma alamun ta dawo.

Abun nata cin ran baba tabawa,har zuwa lokacin da suka zauna cin abincin dare,ta dubi maimunatu

"Waiku kam.....haka akewa miji?,ya fita ya wuni fafutukar nema muku abinci,ya dawo amma ko arziqin sannu da zuwa a gaya masa bai samu ba?,sa'annan ace abincin da zaici ma a gidansa ya gagaresa a kasa sammasa?,anya kuwa maimunatu?,ta yaya zaki bata dukka yardar da anni ta baki?,ta dora duk wani fatanta da burinta akanki amma kina neman bata kunya?" Qasa tayi da kanta,tana jin kunya da nauyin suna kamata tun gabanin xancan ma yaje kunnen annin,tabbas tayi kuskure da gaske,to amma kuma shi dinne.....ba irin sauran mutane bane,batasan ta yadda zata fuskanci bahagon mutum irinsa ba,yau inda ace shi din kamar hisham yake to da da sauqi sauqi,amma.....he's totally different from what they are seeing about him,ba abu bane mai sauqi tunkararsa

"Kiyi haquri baba,baice yana buqata ba"

"Kin taba nuna damuwa ko gwada kaiwar bare ki Fatima hakan?,bari na fito miki a mutum maimunatu" baba tabawa ta fada tana gyara zamanta,abinda ya sanya maimunatu tattara hankalinta waje daya

"Gaba daya na fuskanci inda zaman aurenki ua dosa,bansan na abokiyar zamanki ya yake ba,a gajarce zan gaya miki,ba'a yankewa mutum hukunci ba tare da ka ma'amalanceshi ba,ki sauya,ki zama kamar kowacce mace a gidanta,ki sauke naki hakkin da nauyin,ko meye zai taso a gaba....ko meye zai biyo baya zaki fita a ciki,kiyimin alqawari daga yau zaki canza,inason ganinki kamar kowacce macen auren maimunatu,ina miki sha'awar hakan,na san ja'afar,yana da zuciya me kyau wani abune daban ya canzashi,kuma ina kyautata zaton duk wanda ya aro wani hali da ba nashi ba,rabashi dashi abune me sauqin gaske,zaki canza maimunatu?" Kai ta gyadawa baba tabawa a hankali,tana sake jin nauyi,saboda tana ji a ranta da gasken butulci take son tayi,tana qasan inuwar alfarmarsu,ta samu rayuwa me kyau me cike da gata,sannan ta kasa ciyar da dansu abincin da shine ya siyo shi?,bayan duka duka bata zaman wata biyu ma cikin gidan?.

Da kanta baba tabawa ta shirya abincin cikin wasu sababbin warmers masu kyau

"Dauka maza kikai masa,daga yau babu ruwanki da abokiyar zamanki,duk sanda kika fuskanci yana da buqatar abinci kuma bata nan,bata kuma bashi ba,koda ba ranar girkinki bane dauka ki bashi,ke Allah zai bawa ladan".

Daki ta koma,ta zabo hijab cikin hijabs dinta ta sanya,ba abinda hijab din keyi sai qamsin turaren wuta na kaya,ya kuma amshi fatarta qwarai,kalar blue black,da kallo baba tabawa ta bita sanda ta fito,kamar tace mata ta canza mayafi a maimakon hijab din,amma sai kuma ta canza shawara ta qyaleta.

A hankali ya sauke ajiyar zuciya,sannan ya tura hannunsa cikin sumarsa yana yamutsata,hakanan yaji kawai komai baya maaa dadi,sai yakai hannunsa guda daya ya rufe system din dake gabansa ba tare daya damu da yayi shutting down dinta ba,duk da muhimmancin hakan,sai ya koma a hankali ya jingina bayansa da kujerar da yake zaune,ya kuma hade yatsunsa waje daya yana lumshe idanuwansa.

Wani irin bugu zuciyarta take sanda takai step din qarshe na benan,tana ji kamar ta koma,amma kuma idan tayi hakan bata kyauta ba,kamar ta wofantar da maganar baba tabawa ne,ci gaba tayi da takawa cikin tsoro da fargaba,tana tafiya kamar ba zata kai qofar da zata sadata da ainihin falon ba.

Sanda ta isa qofar sai taja ta tsaya cak,ta runtse idanunta da qarfi,a karo na farko zata fara taka sassansa,batasan da wacce fuska zata kalleshi ba,tsoronsa yana nan fal cikin zuciyarta,tanason baiwa kanta qwarin gwiwa,ta dora hannunta saman handle din,ta runtse idanunta gami da dauke numfashinta sannan ta tura ta sanya kanta.

Daga inda yake zaune miqe da qafafunsa saman table din gabansa idanunsa a rufe yaji an motsa qofar,saidai duk da haka hakan bai sanyashi motsawa ko bude idanunsa ba,a zatonsa unaisa ce,wadda ta gaza haqurin zuwa wajensa da ziyartarsa lokaci lokaci,bayan ya riga daya tabbatar mata gaskiyar abinda ke ranshi gami da bata zabi.

A hankali sassanyan qamshin da ya hanashi sukuni wunin yau,ya kuma wuni dashi cikin jikinsa ya fara cika masa hanci,ya kuma gauraye da sallamarta cikin siririyar muryarta din nan mai dauke da wani amo na musamman,ba tare daya shiryama faruwar hakan ba ya soma bude idanunsa da suka sauya launi saboda mintunan da suka dauka a kulle.

Fes ya sauke idanunsa a kanta,cikin shigar da yawanci shaheedansa ke yinta,shigar da yakan tsokaneta da ita zamanin da suna raye

"I want to see my wife gani na haqiqa..... please madam, remove it" murmushi take jifansa dashi,sannan ta zare din tana fadin

"Am all yours,and belongs to you".

Haka kawai ya samu kansa da gaza dauke idanunsa daga kanta,wani abu na masa yawo tsakiyan kai kamar ana yamutsa kwanyarsa,duk da cikin hijab take amma hoton dazu ke masa yawo cikin idanunsa,ya qureta da kallon dashi kansa yasan idan da ace ita din ba halaliyarsa bace ya kauceea koyarwar addini,baisan me ya sanya masa qulafucin kallonta haka ba.

cikin matuqar juriya da kuma dauriya take bawa kanta confidence,abun dazunke tabata,tana jin kakar qasa ta tsage mata ta shige,ko kuma tayi fiffike ta fice a dakin,ta iso gab dashi kana ta sulale a gabansa ta tsugunna,abinda ya bawa turarenta damar isa gareshi da kyau

"Barka da dare" tayi maganar da wani irin tune,sai ya tashi ya zauna sosai yana sauke sambala sambalan qafafunsa daga saman table din zuwa qasa

"Barka" ya amsata a taqaice,bata tsaya jiran cewarsa ko wani abu ba ta fara fidda warmers din,ya bude baki kaman zaiyi magana kiran jabir ya shigo wayarsa,sai ya maida hankalinsa ga amda wayar,inda ita kuma hakan ya rage mata wani mugun nauyi da takeji an aza mata tun farkon shigowarta falon,rawar da hannayenta keyi suka ragu,ta fidda koma ta kuma yi serving dinsa ta jera komai cikin nutsuwa,sai ta miqe ta fara takawa zata bar falon,cikin ranta cike da fata da addu'ar kada wani abu ya tsaidata.

Dan binta yayi da kallo kadan yana karantar tafiyartata duk da amsa wayar da yakeyi,tamkar wata me tafiya saman rairayi ko yashi mai laushi,duk da bai iys ganin qafafunta saboda hijabin da ya saukar mata,amma kuma yanayin tafiyarta kawai zai gaya maka qafafunta akan tsari suke,janye idanunsa yayi yana jan dan qaramin tsaki,tsakin da ya bayyanarwa jabir ta cikin wayar

"Lafiya?" Ya tambayeshi a taqaice

"No... it's not a matter,ina jinka" yayi maganar yana sauke dubansa ga abincin,wanda tuni yaja ra'ayinsa,bai kuma iya gama wayar ba ya zamo a hankali daga saman kujerar,ya sanya spoon din data ajjiye masa ya diba ya fara ci.

Har cikin ransa yaji nutsuwa da abincin dari bisa dari,dama baba tabawa zabinsa ce akan abinci,don haka duk wani tsohon cinsa ya tashi,yaci abincin sosai fiye da kima,ya kuma kwantar da tsohuwar yunwarsa,haka nan ya dinga jin wata nutsuwa na saukar masa,ba shakka samun abinci gamsashe ma rahama ne,duk wata gajiya da kasala da yake ji fiye da rabinta ta kama gabanta,sai ya samu kuzarin yin aikinsa fiye da dazun,ya sake kunna system dinsa,yaci gaba da nazarin meeting dinsu na dazu wanda tuni PA dinsa yayi documenting komai ya aiko masa,ya dinga cire kusakuran da yayi a dazun,lokaci lokaci yana dan jan tsaki,baisan ya akayi gaba daya dan qanqanin abu irin wannan ya dagula masa lissafi ba,saidai duk da hakan a yanxun ma idan ya tuna sai yaji tsigar jikinsa tadan zuba,yakan dan lumshe idanunsa kadan kana ya bude ya ture komai yaci gaba da aikinsa.

Binta da kallo baba tabawa tayi lokacin da tayi sallama take shigowa falon,sai taci gaba da kallonta baki bude,har ta iso tana zubewa saman kujera

"Wash" ta furta ba tare da tunanin komai ba,ta fadi kalmar ne saboda yadda taji kamar an bubbuge mata gabbanta,uwa uba kuma gudun zuciyarta daya qaru wanda sai a yanzu take qoqarin sai saita kanta.

Hijabinta ta zare ba tare data lura da kallon da baba tabawa ke binta dashi ba,ta isa ga fridge ta bude,ta fidda ruwa me sanyi saboda yadda takejin maqoshinta ya bushe sosai,bata buqaci cup ba ta balle murfin ta fara sha a hankali,idanunta na hango mata shi cikin falon nasa da bai fiya haske ba,cikin wata abaya ta maza

"A haka he's very calm and quiet,amma macijin sari ka noqe ne" ta fadawa kanta da kanta tana cire robar daga bakinta,ta dora ragowar saman fridge din sannan ta juyo.

Sai a sannan ta lura da kallon da babab take mata,ta kuma tsargu,amma kafin ta tambaya ita ta rigata

"Har me?,wai har kin dawo?" Kai ta gyada mata tana neman wajen zama,hannu tasa ta kama baki,sai kuma ta kada kai

"Nidai nasan ba'a ajewa miji abinci a taho a barshi dashi"

"Aiki yake baba,kuma waya ma yake amsawa,so yana buqatar space,may be wayar ta sirrice" ta fada har zuciyarta,saidai ita baba tabawan ta kalli hakanne da sunan bawa kai kariya kawai

"To Allah ya kyauta" yadda baban tayi sai duk maimunatu taji bata ji dadi ba,saboda itama baban kamar bataji dadin yadda tayin ba,to amma kuma ta yaya zata iya zama dashi a muhalli guda?,ko abincin data kai din kawai tasan karambani tayi da kuma bin umarni,tana da yaqinin zaiyi wuya yacu,ta fahimci kamar yana da jin kansa,izza da kuma qasaita,bai taba neman wani abu daga garesu ba cikin gidan dai dai da ruwan sha kuwa,sai taja wayarta kawai ta kunna data tahau sabon Whatsapp dinta,ta kuma fara da yiwa qawayen nata guda uku sallama.

Taci sa'a kuwa ta samu afrah a online,cikin mamaki take tambayar da gaske itace,sai suka zarme da hira,wadda ta daukesu lokaci mai tsaho,daga bisani sukayi sallama bayan ta bata labarin latest Korean dramas masu zafi da suka fito.

Kai tsaye ta wuce Vidmate ta saukesu masu yawan gaske,saidai tana tunanin yadda zata kallesu a nutse ba tare da sun hanata bitar karatuttukanta na makaranta ba. [11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 49

A kasalance yabar sashen nata zuwa nasa,gaba daya ta sakarwa jikinsa wata irin kasala,ya rasa dalilin da ya sanya duk sanda incident irin haka zai faru tsakaninsu sai haka ta kasance.

Sam bai kula da wanzuwar mutum a wajen ba,har ya kama stairs zai hau yaji an kirayi sunansa a tausashe,sai ya tsaya cak,ya kuma waiwaya a hankali.

Unaisa ce tsaye,sanye da wata fatar gown,kanta babu dankwali sai qaramin vail data yafa a kanta me shara shara,idanunta a kansa,tana dubansa cikin wani irin kallo wanda ya nuna yadda tayi laushi har cikin idanunta,qasan ranta tana jin wani irin qaunarsa tana fusgarta,zuwa yanzu takai maqura,hakanam tana jin haqurinta yana neman gazawa,tayi iya matuqar qoqari a irin yadda ta saba rayuwarta,sai ta sake sassauta fuskarta tana fatan ya duneta da idanun tausayi,bata taba kawowa cewa izzarsa miskilancinsa da kuma jin kansa sunkai har haka ba,tayi tunanin a kurkusa zata tagi da imaninsa kamar yadda yake tafiya da imanin duk wani da namiji,fara takowa tayi a hankali,yana biye da ita da idanu,har zuwa sanda yaga tana shirin wuce iyakar da yakega ya kamata ta tsaya

"Stop there" ya fada da muryarnan tasa dake dauke d wani irin amo,ba zato babu kuma tsammani sai jinta yayi ta fada jikinsa gaba daya,ta kuma sanaya hannunta ta qanqameshi da kyau idanunta yana tara qwalla.

"Meye haka?, what's this?" Ya fada yana yunqurin tureta daga jikinsa,saidai hakan bai samu ba saboda yadda ta sake cukuikuyeshi tana fadin

"Na gaji.....na gaji,am going to kill my self indai ba zaka saurareni ba" furucin nata yayi masa banbarakwai sosai atsakiyan kansa,diyar musulmi ke zance aikata ta'addanci a karan kanta?,bawai don ya damu ko kima ya tsorata da furucinta ba yace

"Okay,okay......sakeni tukunna" kamar ba zata sakeshin ba sai kuma ta sakeshi,ta kuma ja da baya tana dauke qananun qwallar fuskarta,hannyensa ya shiga yarfewa kamar wanda wani abun qi ya tabawa fata,fuskarsa ya sake hadewa ya tsare gida sosai yana dubanta

"Am all ears" ya fada yana goye hannuwansa a qirji,idanunta tadan watsa bangaren sasan maimunatu,ta yaya zatayi irin wannan maganar dashi a waje.irin wannan,by mistake yarinyar tazo guftawa ta jisu?,ta tabbatar idan haka ta faru ajinta ya gaba zubewa a idanunta har abada

"Am not comfortable here......i need privacy" kamar bazai amsata ba,sai kuma ya juya ya soma takawa zuwa saman a nutse cikin takunsan nan na daban,ta bishi da kallo tana jin wani abu yana tsarga mata,kafin daga bisani ta soma bin bayansa,tana qiyasta irin kalmomin da zatayi amfani dasu wajen ganin tasha kansa.

Suna isa tsakar falon idanuwanta na sake sauka ga hotunan shaheeda,yadda ta tsani mutuwarta haka ta tsani bude idanu taga wadan nan hotunan,asalima tana kishinsu fiye da yadda take jin kishin maimunatu,tunda a yanzun maimunatu bata tsare mata komai ba,bata ma.kallonta a matsayin matsala gareta,saidai tana jin haushin amsa sunan matar mijinta da tayi,harara ta jefi hoton dashi,wanda ja'afar dake qoqarin ganin ya saurareta idanunsa suka shaida masa hakan,wani abu me kama da mamaki ya saukar masa

"Harara?,for what?" Maida idanunsa yayi ga sassan da hoton shaheeda ke maqale,dai dai sanda ya dauke dubansa zuwa ga unaisa,itama dai dai sannan ya dauke idanunta zuwa kansa,sai suka hada idanu,kamar an zare wani abu daga zuciyarta taji,bataso ya ganta ba,amma ita ba wannan ne damuwarta ba,damuwarta ta fidda wadda ke cikin hoton daga zuciyarsa gaba daya,kamar yadda ta five a filin duniya,ita kuma ta maye gurbinta

"Uhmm.....go on" takowa ta soma yi tana sake nufoshi,ta dora dukkan wani yanayi da zai baka tausayi a kan fuskarta,saidai tana zuwa gab dashi ya sake dakatar da ita

"Don't do it" ya fada calmly gami da yi mata nuni da hannu kan yana saurarenta,bata da wani zabi illa fashewa da kuka harda sheshsheqa,abinda ya bashi mamaki ganin cewa shi din bai aikata mata komai ba,fuska ya hade sosai yana dubanta,sai kuma ya kau da kai yana jan tsaki can qasan ransa

"Bansan meye laifi na,ban kuma san me na aikata maka ba,don kawai nace ina sonka ja'afar?,ta yaya da hakkina a kanka tsahon shekara kusan guda ka takemin kamar bakasan da wannan ba"

"Anzo wajen" ya fada a ransa yana jin tana sake ficewa daga ransa,ta yaya yarinya mai cikakkiyar kunya da nutsuwa zata iya duban idanun da namiji.....duk da kasancewarsa mijinta,amma a matsayin budurwa ta gaya masa hakan?,well.....batayi laifi ba,tunda hakkinta ne kamar yadda ta fada din,amma bayajin koda danneshi akayi zai iya aikatawa,hes not in the mood gaba daya,bayajin wani feelings a yanzu a kanta ko dis.

Kujerar dake daura dashi ya qarasa ya zauna a hannun kujerar,yaci gaba da dubanta hankali kwance sanda taketa kukanta tana sake qara ma kukan salo a fatan da take na samun nasara a kansa,can qasan zuciyarsa yake qissima ta yadda zai raba kansa da wannan matsalar.....eh.....matsala mana,zuwa yanzun yana jin unaisan ta zame masa matsala,babu abinda take haifar masa banda kwasarwa kansa zunubi,bayan yana da tabbacin abune mai wahala ya iya karbarta cikin rayuwarsa,zuciyarsa wata irin zuciya ce mai wahalar sha'ani

"I already told you,zamanmu abu ne mai wahala da ban hango yiwuwarsa,ni am ready to dismissed you,the choice is yours.....karki sake tara ta da irin wannan shirmen" daga haka ya miqe ya nufi bedroom dinsa,ta yunqura zata bishi,saidai ko kafin ta isa ya maida qofansa ya rufe,ta daga hannu kamar zatayi knocking sai ta sauke,ta fahimci wasu daga cikin halaye da kuma dabi'unsa,idan ta sake tayi knocking masa qofa,batasan me zai biyo baya ba,sai ta juya da gudu gudu tana sauka daga stairs din kuka yana kufce mata,ta gaji gaskiya,ta kuma kai maqura,tana jin ta iso geji,batason kuma ta bata dukkan wani tanadi da tayi masa,zata dauki mataki na gaba itama da takeji har cikin ranta da zuciyarta shine dai dai.

°°°°°°°Ta tabbatar idan har ta zauna a wajen baba tabawa babu abinda zai hanata cewa taje takai masa abincin dare,wannan shine worst abu da zata sanyata,bata jin zata iya hada idanu ko muhalli dashi,gaba daya ya ajema ranta da zuciyarta wani abu,wani irin nauyi da kwarjininsa daya qaru cikin idanunta,gefe guda wani abu me kama da haushinsa da take ji,gaba daya halayyarsa batayi mata ba,hisham ya fishi sauqin kai kirki fara'a da iya mu'amala da mutane,komai nasa cikin tsumewa da tsare gida?.

Leqawa kawai tayi ta duba baba tabawan don tasan ta tashi kuma lafiya take,don ko ita tayi mamakin jimawar da tayi tana bacci

"Zan koma na kwanta baba,jikins yau banajin qwarinsa"

"Ashsha.....amma dai ba ciwon bane ko?,yana shirin dawowa ina shirin tattara komatsaina na koma inda nafi wayo?" Dubanta da kyau maimunatu tayi,gabanta ya fadi,sai taji an cire dukka sauran walwala daga zuciyarta,komawa tayi ta zauna a maimakon tashi da tayi dazun

"Tafiya kuma baba?" Kai ta gyada

"Eh,ai gwara na koma gida hakanan,tunda naga jikin naki ai yayi kyau,banda tsautsayin da ya faru yau ma ai da yau din a gida zan kwana" gaba daya jikinta ya gama mutuwa,batason tafiyar baban,saboda tasan ba komai bane zai faru sai zaman kadaici kara dadi,wanda a yanzun ta fara sabawa da rayuwa da mutane,daya daga cikin dalilan da ya sanya ko hutun makaranta bata fiya son ayi ba,banda tanason tazo taga anni wasu lokutan.

"Don Allah baba ki bari sai zuwa wani lokaci,ko kuma idan zan koma hutu,saura kwana ashirin gaba daya mu koma" kai ta girgiza

"Banda abinki maimunatu ta yaya zan zo cikin yara gotai gotai dani na zauna banda ma lalura ta rashin lafiyar?,ai gwara na tafi,kema kyafi sakewa kiyi bautar aurenki yadda ya kamata" daga qarshe ta shagwuba mata magana,wadda ta sanya bata sake cewa komai ba,sai tayi qas da kanta.

Bata sani ba ko kewar baban ta fara, yadda ta tsara guduwa daki batayi hakan ba,sai ta zauna suna fira sama sama,yayin da baban tayi amfani da wannan damar tana sake jan hankalin maimuntu a fakaice akan rayuwar auren nata.

Washegari gaba daya bata fito a daki da wuri ba,tana qiyasta lokacin da zai shigo gaida baba tabawa,ta kuwa qiyasta dai dai,don kuwa ya shigo gaida ita din,saidai a gurguje,don yana sauri zashi gida karbar kudin auren salma hafsa da kuma nadiya,harma da laila,sosai baba tabawa taji dadin labarin,bayan kuma maimunatu ta fito ta shaida mata.

Tun a waya ta kira laila tayi mata murna,saboda tasan yadda take son auren,don babu wanda ya zaci ma za'a karba harda nata,ta kuma dan tsokaneta,baba tabawa na zaune tana jinsu tana dariya,ko bayan ta gama wayar ma hirar familyn dr marwan din suka shiga,wanda duka baba tabawan ce ke bata labarin yawan zuri'ar khalidu akko,da kuma karamcin mutan gidan dr marwan din,wanda ita kanta maimunatu shaida ce,bata taba zaton a duniya akwai mutane irinsu ba,sun samu dukkan wata dama ta rayuwa,amma hakan baisanya sun wulaqanta kowa ba,ko kuma sun dauki kansu a wani abu ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull