Kenza eBookz

Gurbin ido huguma complete - Chapter 50

Gurbin ido huguma complete - Chapter 50

Gurbin ido huguma complete Chapter 50: Gurbin ido huguma complete Chapter 50. Da kansa ya bude mata motar ta shiga,ya tattara mata hijab dinta daya fito…

3,367 words

Da kansa ya bude mata motar ta shiga,ya tattara mata hijab dinta daya fito zuwa ciki ya rufe mata,sannan ya zagaya seat dinsa yana jin zuciyarsa wasai,duk wani nauyi da tayi ya nemeshi ya rasa cikin qanqanin lokaci,yayin da itama ta langabar da kanta a kafada tana kallonsa sanda yake zagayowa ta gaban motar zuwa seat dinsa

"Ya Allah,yashe ta fara sonsa har haka ne?" Saita lumshe idanunta itama sirritaccen murmushi yana kubce mata. [11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 78

Wata shirt ta zaqulo,tana da dan fadi daban,dama irinta take nema,sai ta zura,tayi amfani da turarensa ta feshi jikinta,sannan ta dauki hair drayer dinsa ta fara busar da gashinta da ya dan jiqe,ta gama fa shafeshi da mansa mai qamshi,sannan ta dauki band ya fara kiciniyar daurawa.

Duk tsaiwarsa a dakin sai lokacin ya qaraso,sai daya iso dab da bayanta sannan yayi sallama,ta fito da idanunta tana kallon fuskarsa data sauya,daga fuskar da babu rahamar fa'a zuwa fuskar data saba da murmushi ciki yan mintuna qalilan,ya soma takowa zuwa inda take tsayen.

"wa yace ki sakamin riga?" Ya fada cikin sigar tsokana,amma kuma yana dan bata rai,narai narai tayi da idanu tana langabe kai

"Banga kayan da zan saka ba" kai ya jinjina yana isowa dab da ita,ya sanya hannuwansa duka biyu ya nade rigar sama ya riqe qugunta yana kallon fuskarta,tafin hannuwansa saman lallausar fatar jikinta yana kallon tsakiyar idanuwanta

"Gaskiya bazan iya baki aro ba,nima ita zan saka" yayi maganar yana tafiya da hannayensa zuwa sama,inda yake ta tsole masa ido tare da jan hankalinsa,narai narai ta sakeyi da ido,a narke tace

"Please mana,aro kawai?" Kai ya girgiza

"Bazan iya ba"

"Don Allah"

"Ok,but let me feel your....." Sai maganar bakinsa ta.katse, numfashin sa ya fusga kadan,saboda tuni yakai.hannuwansa inda ya nufa,kafin tace komai ya tsugunna ta qasan rigar ya cusa kansa.

Fara qoqarin zamewa tayi amma inaa,ya saka dukka hannuwansa biyu ya riqeta sosai ta bayanta,cikin qanqanin lokaci ya fara birkita mata kwanya,saqonnin da yake aikema qwaqwalwartata sun girmama,ta fara tangal tangal zata fadi,sai ya zare kansa daga ciki yana dubanta da idanuwansa da suka sauya launi

"Please nima,ki sanmin dan kadan,i promise you wannan karon no more any pain.....i promise.....i promise angel" ya fada a dan rude saboda yadda hankalinsa yayi gaba.

Bata jin dadi idan taganshi a gabanta cikin kwantar da kai yana roqarta akan hakkinsa,a hankali ta gyada masa kai tana lumshe idanu,caraf taji ya sureta yana cewa

"Thank you angel moon, thank you" ya azata a tausashe saman gadon ya maye gurbin duvet yana sanyata tsakiyar qirjinsa gami da sake lullubeta da wata tattausar soyayya mai dimautarwa da kuma gigita hankali.

Kaman yadda yayi mata alqawarin kuwa babu wani sauran radadi data fuskanta,saima tarin kunya da ya barta da ita, saboda yayi ta koya mata abubuwa yana sanyata tana responding masa saqonninsa,abinda ya basu wani irin dare mai matuqar qayatarwa,daren daya sake.narkar da kowannensu,ya kuma sukurkutar masa da tunani,ya sake dasa musu so da qaunar juna mai tsanani.

Ko bayan komai ya kammala cikin jikinsa ya matseta tsam,idanunsa a rufe yake cewa

"Let's make this lovely journey last for a lifetime,do not ever let me go,am yours as long as you want me to" wani irin abu taji yana sulalewa yana kwaranya a kwanyarta,ta gyada masa kai a hankali ta lumshe idanu tana jinta a wata duniya ta daban,dama haka soyayya take?,sai ta tuna da wani korean drama data gani,kamar haka a lokacin ta dinga imagining kanta,amma sai zuciyarta ke gaya mata it can't,ashe zai yiwu,harma fiye da yadda take hasashe.

°°°°°°°°°°shi da ita dukkaninsu a shirye suke tsaf,ita cikin shirin komawa makaranta,shi kuma cikin shirin office,tsaye take shima haka,tana rungume tsakiyar qirjinsa suna musayar numfashin juna da kuma scents na turarukansu,kowannensu ji yake kamar bazai iya tafiya yabar dayan ba,cikin wata karyayyiyar murya yace

"Can we go?" Ta gyada masa kanta a hankali zuciyarta na karyewa kamar kuka zai subuce mata

"Okay angel.....but,inason naji kalma daya a bakinki,me yasa kikemin rowarta,baki taba gayamin ba" sai data daga kai ta kalleshi sannan ta tambayeshi

"I want you to say i love you ja'afar" murmushi tayi tana cusa kanta sosai cikin qirjinsa,kunya....kunya takeji wallahi,tun jiya ya gama sakwarkwatar da ita gaba daya

"Uhnnnn.... please,say it" ajiyar zuciya ta sauke,tana jin yadda zuciyarta keta azalzalarta kan ta fada din,cikin wata irin murya dake dauke da amo na daban ta fadi

"Ina sonka,ina qaunarka.....i love you"

"Da gaske daga zuciyarki ne?" Saita jinjina masa kai cike da qwarin gwiwa

"Ina nufin dukka abinda na fadi din,da gaske nake,daga zuciyata ne" zallar farinciki ya kamashi,sai kawai ya hadeta cikin jikinsa,ta sauke ajiyar zuciya tana jin dadin kasancewarta a qirjinsa,akwai wata nutsuwa mai tarin yawa tattare da gurin,har batasan tayi subutar bakin furtawa ba

"Hugging someone taller than you is the best feeling ever,bcoz you fell protected" wani murmushi mai dadi ne ya subuce masa,ya dagota yana duban fuskarta dake a kulle

"Really?" Kai tsaye ta gyada masa kai

"Zanci gaba da rungumarki har gaban abada,kuma.koda baki a jikina cikin qirjina kina zuciyata,and i will give you protection everywhere you go bakin rai bakin fama". Da qyar suka yakice juna ya dauketa sai makaranta.

Ko cikin mota sai data kusa missing first period sannan ya barta,ta wuce dakunansu ta saka uniform ta koma aji,shi kuma yaje yayi confirming maidota da yayi yayi singing.

Tun a aji suka dameta da iskanci su afra,saita sharesu saidai tana ta smiling,saboda ita kanta tasan jiyan tabar mata abubuwa masu yawa da bazata.mance dasu ba,su afra kuwa haka ta haqura da tsiyar da suketa mata har sukayi haquri sukayi shuru.

Tofa captain ja'afar da maimunatu sun fasa dadin abun,kwana daya rak yaji ya kasa sukuni,da qyar ya raka zuwa qarshen sati ran Friday ya sake zuwa ya nema alfarma ya daukota,tazo tayi masa weekend,idan yaso Sunday da yamma ko Monday da sassafe ya maidota.

Wani irin weekend mai bada kala sukayi, weekend din da tunda yazo duniya baijin akwai wanda ya fishi dadi a wajensa,ran litinin kuwa basu samu fita daga gidan ba sai azahar,da qyar ya taushi kansa,yana da tabbacin ya kusa gazawa,haqurinsa ya kusa qarewa,don haka ya sama kansa more effort ya gama aikin da xai sanya ya fake dashi ya raba maimunatu da makarantar gaba daya ta silarsa.

K'arfe shida da mintuna ya shiga gidansu kamar yadda yawancin lokuta yake zuwa a yanzun,amma sai ya wuce sassan ammansa,ya sameta a falonta a zaune,ita daya saboda yaran basu dawo a islamiyya ba,duk girmanki a gidan dr marwan baki wuce zuwa islamiyya ba,har su salma 'yan university da ake shirin aurarwa,kasancewarsa sanannen mai ilimin addini,yakance neman ilimi baya qarewa dan adam sai idan mutuwa yayi,akwai makaranta nan saman unguwarsu me special classes irin nasu.

Duqawa yayi nan gabanta ya gaidata,sannan ya zame ya zauna sosai yana jan fruit din dake gabanta hade da qaramar wuqa tana gyarawa,da alama zatayi fruit salad ne, murmushi ta bishi dashi,har yau baya ganin ya girma ko ya taka wani matsayin da zai hanashi kama mata aiki idan yazo ya taras tana yi.

"Manya,me yake faruwa tsakaninka da unaisa ne?" Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke,duk duniya baya iya boyema mahaifiyarsa komai,don haka ya labarta mata komai a nutse.

Sosai hankalinta ya tashi,amma kuma bata nuna masa ba

"Haquri ake da sha'aninmu,tunda ai bata taba aikata hakan ba,sai ka bata uzuri" kai kawai ya gyadawa ammansa,amma bayajin zai taba iya riqe unaisa,bayason suci gaba da zama yana zaluntarta Allah ya kamashi kan hakan.

Bai tashi a kai ba sai da suka gama aikin duka tare sannan ya daura alwala ya fice sallar magariba.

Daya dawo wajen anni ya wuce,itama tana falo baba tabawa na gefanta suna kallon musabaqar duniya da ake haskowa a wata channel,wata 'yar nigeria ce ke karatun a yanzun,suna ta tattaunawa akai,saidai kowanne hannunsa riqe da carbi da alama basu jima da gama sallah ba. Baba tabawa ce ta miqe tana marabtarsa

"Barka da zuwa" ya amsa mata cikin girmamawa yana zama,sannan suka gaisa

"Ina uwar dakina?,tayi mana nisa"

"Suna makaranta"

"Uhmmm.... makaranta ko gantali daga wannan kwararo zuwa wancan?" Anni ta fada tana tabe baki,daga kai yayi ya kalleta,sai kawai murmushi ya subuce masa,shi qarfin halin anni dariya yake basa,batasan a yau idan yaso.maimunatu ta gama zuwa makaranta ba?,ya fita iya kwaso rigima sosai,amma tana da wani babban matsayi a rayuwarsa,sannan she deserved respect daga wajen kowannensu,don ta taka rawar gani a rayuwar duk wani ahali nata

"A daiyi haquri a sassauta"

"Yoni ai bazan dauki wannan iskantun ba,kowa ta kansa zaiyi ya shiga hankalinsa,bazan bari a haifamin jika tsakanin qarya da gaskiya ba"

"Kin samawa kanki sauqi" ya fada hankalinsa kwance yana relaxing cikin kujerun hadi da lumshe idanu,dariya taso qwacewa baba tabawa saita fice,yayin da annin ta watsa masa daquwa

"Kayi ta kanka ja'afaru ka kiyayeni fa?"

"Na kiyeyeki" ya fada ba tare daya bude idanunsa ba,don shi yanzunma weekend dinsu na baya yake tunowa yana sa masa nishadi,tare da shirya musu next weekend yadda zai wakana.

Kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai abbi ya shigo,cikin girmamawa ya miqe yana masa sannu da zuwa,bai zauna ba sai da abbin ya samu waje ya zauna nan kusa da tsohuwarshi

"Dama ina nemanka,naji dadi dana ganka" sai yayi bismillah yana zama

"Zauna" ya bashi umarni,ya aikata hakan yana tattara hankalinsa akan abbi din.

Maganganu ne duka kan unaisa,da yadda tace batasan wani abu daya faru ba,qarshe ma dai saita buge da fadin irin zaman da sukayi,shuru ne ya biyo baya,anni tana ta jeranta abubuwan cikin ranta,ita gaba daya yarinyar bata yi mata ba,sannan data sake kawo mata qara ta kuma kalli tsantsar idanunta tace mata ayi masa fada bata taba kwanan turaka ba saita qarasa sare mata a rai,babu kunya ko qanqani cikin lamarinta,sannan ita kanta ta sanya cikin jikokinta sun mata bincike,sakamakon ba mai dadi bane, saidai dan yau baka bashi qofa haka kai tsaye.

Shima abbi din kusan hakan take,amma bayaso lokaci guda ya bashi go ahead na aikata wani abu,saboda gudun halin dan yau,don haka yace dashi

"Ka samu lokaci kaje ku fahimci juna ka dawo da ita dakinta"

"Zan samu lokaci" yace da abbin kawai,yanayin fuskarsu kawai ya nuna suma akwai abinda suke dannewa. [11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 77

Tunda suka shiga motar ko sau daya bai sani hannunsa daga cikin nata ba,yana riqe dashi gam yana murzawa a hankali,ya dameta kan ta fada masa me yasa tadan rame ba kamar yadda ya dawo da ita ba?,ko akwai mai matsa mata?,ko makarantar babu dadi?" Tsaf ta boye idanunta cikin hijab,taqi kuma cewa komai dashi,sai ya sakar mata lallausan murmushi

"Ni bari na gaya miki....tunda ke kina boyemin,kada nace kina sona ko?" Curewa ta sakeyi waje daya dariya mai dan siririn sauti tana qwace mata,abinda ya sake jan hankalinsa a kanta kenan,ya saki murmushi shima me sautin

"Bana iya baccin,bana iya cin abinci,Allah kinji nace miki Allah,tunda kika tafi kika tafi da dukka farinciki da walwalata,har na dinga jina kamar marayan da babu uwa babu uba" kanta ta daga a hankali,bakinta ya subuce tace

"Kamar ni kenan?" Idamunta na nuna alamun rauninta,tausayinta ya tsarga masa sosai, cikin ransa yace

"Kin kusa yin dariya in sha Allah" amma a fili saiya riqe hannunta dakyau,ya jashi zuwa qirjinsa saitin zuciyarsa

"Ki daukeni kamar uwa da uba a wajenki,nayi alqawari zan cike miki dukka wani gurbi da gibi da kike dashi a rayuwarki" idanunta ta maida ta lumshe,tana jin kewarsu,maganarsa ta ta katse mata tunani

"Wannan zafin jikin tun yaushe kika fara shi?"

"Last week ne"

"Ya kamata kiga likita kenan,don kada yaci gaba" ya fada tana sanya signal a motarsa,kanta ta girgiza tana bin titin da zai kaisu gidana abbi da kallo

"Yana sauka.....amna nakeson ka daukomin,tunda na dawo ban ganta ba" fuska yadan kwabe kamar yaro qarami

"Noooo......so nake mu shiga duniyar da zata bamu nutsuwa,wadda babu kowa a cikinta daga ni sai ke" yadda yayi maganar yana rage gudun motar ya kuma sanya idanunsa cikin nata sai wani nauyin ya kamata,ta maida kanta baya ta jinginar tana rufe idanuwanta.

A parking lot na gidansa dake government road ya tsaya,sannan ya kirayi me gadin,ya gaya masa ya rufe masa gidan,idan anzo nemansa yace he's not available😂,kasaqe mai gadin yayi yana maimaita kalmar

"Yallabai kamar wani layin waya?" Ya fada a ransa

"Jeka" ja'afar din ya fada yana sallamarsa,sai ya amsa da to yana komawa bakin aikinsa.

Yanxun ma daukar abarsa cak yayi har zuwa sassansa,tare sukayi alwala sukayi sallar la'asar data kubce musu su duka,ya waiwayo yana dubanta a hankali bayan sun isar,sai ya zame ya kashingida yana tokare jikinsa da jikinta,idanunsa a qasa

"Me zakaci?" Ta tambayeshi saboda tunawan da tayi yace bai iyacin abinci

"Anything angel,indai daga gareki ne zanci,amma for now dai barci nakeji" ya fada yana zamewa a hankali,ya aza kansa saman cinyarta kwanciyar rigingine yadda yake ganin fuskarta fes,yana kafeta da wani irin kallo,idanuwansa suna lullumshewa.

Hannunsa ya sanya ya zare tafin hannunta data rufe fuskarta dasu,muryarsa da matuqar rauni yace

"Noooo.....don Allah please ki barni na more,don Allah,badon ni ba" sai ya maida hannuwansa ya harde a qijinsa yana ci gaba da kallonta,idanuwansa na masa nauyi,wani irin barci na rinjayar idanuwan nasa,a hankali yana kallonta suna rufewa,har suka rufe gaba daya,wani daddadan baccin da ya manta rabonsa dashi yayi awon gaba dashi.

Saukar numfashin sa cikin nutsuwa ya tabbatar mata baccin yakeyi da gaske,a hankali ta sauke idanuwanta kan fuskarsa

"Ma sha Allah,fatabarakallahu ahsanul khaliqin" ya fita a bakinta,asalin kyau ta gani dab da ita cakude cikin fata chocolate color.

A hankali take qare masa kallo,kwantacciyar sumar fuskarsa mai santsi baqa sidik data sake qwawata fuskarsa,wani irin gyaran fuska yakeyi,kamar na jaruman fina finan qasar hindu,koma waye yake masa aski tabbas expert ne,ya kuma san aikinsa,bata taba damuwa da aski ko sanin me askin maza ke ciki ba,amma a yanzun askin ya burgeta sosai.

Yatsanta guda daya ta sanya tsakanin gashin girarsa masu laushi tana zagaya girar,caraf taji ya kama hannunta,ya riqe da kyau cikin tattausan tafin hannunsa,cikin murya dake cike da mayen bacci yace

"Am sorry angel,hannunkin nan mai laushi da yawa zaya hanani yin bacci,har gwara kici gaba da kallona,na baki dama,ina jinsa kamar garkuwa ne a tattare dani" yana gama fadin hakan ya sanya hannuwan nasa qasan kuncinsa yayi filo da tafin hannun nata,yana kuma sake gyara kwanciyarsa sosai cikin jikinta,kamar qaramin yaron dake jin rigima ya samu mamarsa ta dorashi kan cinyarta.

Kunya da mamakin yadda baccinsa ya katse,ya kuma fahimci kallonsa takeyi ya kamata,sai tayi shuru kawai tana murmusawa kadan kadan,har zuwa sanda itama nata baccin ya iso,ya rinjayeta,sai gashi a hankali ta kifa fuskarta a tasa,sannu a hankali suka fara musayar numfashin juna.

Shi ya fara farkawa,amma sai ya gaza motsawa saboda yadda tayi masa rumfa,cikin jikinsa ya dinga jin wani abu yana shigarsa yana ratsashi,ya dinga sauke murmushi shi kadai,zaiso su tabbata a haka,saidai kuma yana dan motsawa kadan itama ta farka,ta kuma tashi da sauri cikin kunya da mamakin yadda gaba daya tayi male male a jikinsa,daga kanta zuwa qirjinta.

Juyowa yayi sosai yana fuskantarta kamar dazun da idanuwansa da suka dan kada kadan sabida baccin daya tashi a shi

"Yunwa nakeji,please ayimin taimakon gaggawa" kai ta gyada masa tana murmushi dake nuna zallar kunya

"Uhmm madam,a taimakeni,tsohuwar yunwa ta tashi" da ido tayi masa nuni kan ya dagata,bai dagata ba ya tsareta da ido amma girki yakeso,mirginawa gefe yayi da sauri yana cewa

"Ya salam.....afwan" abinda ya bata damar tashi kenan,ta dauki ribbon dinta daya zame yayi nasa waje ta tattare sumarta mau santsi waje daya sannan ta tashi,yana kwancen har yanzu cikin mutuwar jiki yana qare mata kallo,idanuwansa suna lullumshewa,shi daya yana sake tsumuwa da ganin surarta,kasancewar yanzu babu hijabi a jikinta.

Har takai qofa taji yace cikin wata irin murya daya cika taushi da yawa

"Angel moon" sai ta tsaya cak ta waiwayo,murmushinsa shine abu na farko data fara gani sannan ya motsa bakinsa,cikin wani slow ya furta

"I love you"....." Wani kunya ya bata yadda ya furta mata maganar,da kuma yadda ya kafeta da idanu,sai ta juya da dan sassarfa ta fita a dakin,bata tsaya ba sai datakai kitchen,sai ra jingina da freezer din cikin kitchen din tana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya gami da murmushi mai taushi,ko wanne second da zaizo ya wuce mamaki J yake bata,completely ya canza,wai dama haka yake?,sai ta tuna wani hira da suka taba yi da afra,a sannan ta dauka sharrinta ne,bata gasgatata ba sai yanzu

"Hmmm,rabu da miskilallun na masu jin izza da isa,da yawansu idan kikaga yadda suku sukurkucewa akan soyayya sai sun baki tausayi,Allah saiki rainasu inda xaki gansu gaban macen da suka matowa,amma suna fitowa waje sai suyita wani izza suna muzurai" saita sauke wani sabon murmushin,ta taka zuwa tsakiyar kitchen din,kwanyarta na mata searching,cikin abubuwan data karanta a dairy din shaheeda a favourite food nashi,wanne ne mai sauqi da zata dafa masa.

Rub da ciki yayi bayan ta fita,ya jima a haka yana hasashen yadda yakeji a jikinsa akan maimunatu,da yadda soyayyarta tayi masa wani irin kamu,yana jin buqatuwa sosai zuwa gareta,saidai yanason ya bata space,kada ta dauka jikinta kawai.shine abinda yake buqata.

Toilet ya shiga yayi aswaki da miswak na Aarak,wanda indai yayi bacci irin hakan yakeyinsa,ya fesa mouth fresh a bakin nasa bayan ya daura alwala sannan ya fito,yanason ya qarar da dukka lokacinsa tare da ita.

Sam sam bataji shigowarsa ba,sai tsintar kanta tayi jingine a qirjinsa,ya zagaye ta ta qugunta,ya sanya hannuwansa saman plate tummy dinta,ya kuma dora kansa saman kafadarta yana leqen abinda take dafawa,da muryar dake wanzar da soyayya a zukata ya fara magana

"Shine kika gudu?,bayan ko kwatar abinda yake raina ban gaya miki ba?,lemme tell you one to two reasons that make me love you" sai ya sake mannata cikin jikinsa sosai kamar xai maidasu abu daya,ya sake qas da muryarsa

"I love you because you make me feel again that am worth something.....i love you because you make me smile when I almost forgotten how to.....i love you angel for so many reasons" gaba daya kalamansa sun kashe mata jiki,kawai saita kasa ci gaba da yanka dankalin da takeyi akan chopping board,tana riqe dai da wuqar kawai a hannunta.

Sakinta yayi daya lura da haka,sai ya zame ya dawo gabanta,ya karba wuqar ya fara yayyanka mata da sauri da sauri,har yadda ya iya ya bata mamaki,yana yankan yana daga kai yana kallonta kamar zata bace masa,hakan ya sanya saura kadan ya datse hannunsa,don haka ta karba aikinta tace ta gode

"Ko kin koreni ba inda zani" narai narai tayi da fuska,zuciyarta cike fal da saqonni amma kuma nauyi da kunya hadi da rashin sabon da har yanzu basuyi ba ya hanata furtawa,ya gama karantar qwayar idanunta da kyau,don haka murmushi kawai ya saki

"A juri zuwa rafi da tulu diban ruwa" ya fada a ransa.

Kusan shi ya tayata dukka aikin sukayi suka gama tare,tun cikin kitchen din ya zuba ya fara kaiwa cikinsa,itace mutum ta uku a duniya da yakejin dadin abincinsu fiye ma da yadda ransa yakeso,da qyar ya iya kaiwa falo ya zauna tayi serving nashi.

Dadin sai ya masa yawa,ya dinga jinsa yana yawo a wani gajimaren farinciki,yana ci yana kallon fuskarta har ya kammala.

Daure da babban towel ta fito a wanka bayan ta baroshi a falo yana waya,awa kusan daya kenan,a nutse ta qarasa walking closet dinsa tana dudduba kayan da zata saka,saidai babu wanda zai mata,hasalima gaba daya an kwashe sauran kayan da sukayi ragowa na mata,taja tsaki yafi a qirga,dole daga baya ta fara lalube cikin trouser dinsa ta samo daya ta saka,ya mata mugun yawa,saita tsugunna ta lanqwashe qasansa,sannan ta shiga dubawa cikin rigunansa ko zata samu wanda zata saka a jikinta. [11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 79

Weekend na musamman suka sakeyi kamar yadda ya shirya musu,don wannan karon daga makaranta kai tsaye airport suka zarce,already ya siya musu ticket zuwa kano,akwai aikin duba ginin company dinsa da yakeyi,cikin 'yan awanni ya gama dubawar suka sauka a Bristol palace,a nan suka more amarcinsu sosai,kwanaki biyun da sukayi ta sakar masa zuciyarta harma da gangar jikinta,wani sabo da shaquwa ne sosai suka shiga tsakaninsu.

Ta dauka Sunday ko Monday da sassafe zasu wuce,amma sai taji baice komai ba,itama kunya da nauyinsu take ji shi yasa bata tanka masa ba,ta fuskanci makarantar takai masa ko ina,kawai lallabawa yake yana ma anni kawaici.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull