Gurbin ido huguma complete - Chapter 32
Gurbin ido huguma complete Chapter 32: Gurbin ido huguma complete Chapter 32. A toilet ma bata yima kanta qauron kallo ba,a nutse take bin toilet din da…
4,488 words
A toilet ma bata yima kanta qauron kallo ba,a nutse take bin toilet din da kallo,kamar ba muhallin wanka ba,tuna abinda ke gabanta da kuma wanda ke jiranta yasa ta qara gaba zuwa jacuzzi bathtub,ta hada ruwa dai dai da ra'ayinta sannan ta koma gaban wani oval shape glass sink dake da wata qaraman drower a qasa,gaba daya kayan amfaninsa ne a ciki kana hangosu tarwai kamar ruwa bai taba wajen,kama daga brush toothpaste sponge da tarin shower gel masu tsadan gaske,sai kayan shaving nasa,clippers da sauransu.
Wadda ke a bude ta dauka tare da sponge din dake wajen data tabbatar dashi yake amfani,lumshe idanuwanta tayi sanda qamshinta da dumin ruwan ya hadu waje daya,sai taji kamar kada ta gama wankan,sosai qamshin ya burgeta ya kuma zauna mata a kwanyarta.
Rarraba idanu ta shiga yi data tuna bata ko shigo da kayan da zata canza ba,hakanan bazata iya maida rigar data cire din ba,ta koyi wata irin tsafta da gayu na daban,bata da wani sauran zabi,dole ta matsa jerin fararen towels din dake maqale a wata silver hanger ta cira daya,tun kafin ta raba shi a jikinta qamshinsa yayi mata maraba,ba kasafai ta fiya son cudanya da duk abinda ke qamshinsa ba,sai ta maida ta dauko wani,saidai.shima din dai sammakal,ganin tana bata lokaci yasa dole ta daurash cike da fargaba,bata manta waccar ranar ba da towel din yaso zamewa daga jikinta,Allah ya taimaketa batayi me gaba daya a gabansa ba,sai ta sake dauko wani ta lullube kanta sannan ta fito.
Da amna ta fara cin karo,zaune kan sleeper sofan dake gaban gadon da game a hannunta,bisa dukkan sabuwa ce yau din ta fara amfani da ita,sam ta mance da yarinyar,dazun tana ina sanda suke magana?,Allah yasa bata a wajen.
Kai ta daga tana duban maimunatu dake riqe da towel din dake kanta wanda ke shirin zamewa
"Anty moon,ga kayanki" duban inda ta nuna matan tayi,sai ta gyada kai,ta qarasa gaban mirror dinsa.
Kaman madubin mace,cike da kayan shafa designers amma irin na maza,bata da sauran xabi,hakanan ta bude mayukansa ta shafa na shafawa,duk amna anyi shuru an nutsu an sami game,sannan ta dawo tana daga kayan da amnan tace nata ne.
Tana duba kayan pant da breezier dinta suka fado daga tsakiya,sai ta fidda idanu cikin mamaki,ta daga kai tana duban amna
"Amna....waye ya daukomin kaya?"
"Daddy ne,nina rakashi" wata irin kunya ce ta kamata kamar zata nutse a wajen,musamman da taji suna fidda qamshin musk,saita qanqamesu kamar ta fasa kuka, knocking da taji anyi ya sata kwashe kayan da sauri,ta kuma koma toilet ta sakasu,tana sake jajantawa kanta,shikam baiji kunyarta ba?, dakinta ma ya shiga kenan?,bayan wannan dame dame ya gani nata?,Allah yasa baiga wani abu na kunya ba a dakin.
Sanda ta tsaya a gaban madubi ita kanta tayi mamakin yadda kayan suka karbeta,suka dace da fatarta,a gurguje ta shirya,ta sanya takalmanta ta kuma yi rolling silk vail din dake mahadin kayan,take ta qara wani kwarjini sosai,saidai gaba daya ranta a jagule yake,hakanan akwai raguwar fara'a sosai daga kan fuskarta,sam sam bata shirya yin wata tafiya ba,musamman ma ace dashi,bugu da qari ma tana ji da tsoron kada tafiyar ta shiga qarewae hutunsu a koma makaranta banda ita,batason tayi missing koda kwana daya ne,amma a yadda taga ya dauki abun serious bata da wanin sauran zabi.
Yana tsaka da waya suka fito ita da amna,gaba daya ilahirin jikinta qamshin turaren yake,turare ne daya ajjiyeshi ya daina amfani dashi,saboda yadda yake kashe masa jiki da zuciya,ta wani glass dake jikin space din da aka maqala babban plasma din ya hangota,duk da bai juyo ba amma yana ganinta tarwai,sai ya lumshe idanunsa sannan ya sake budesu,yana ci gaba da qare mata kallo ta glass din ba tare data sani ba,har suka iso inda yake bai juyo ba bare yayi alamun ya gansu,saidai duk wani taku nata akan idanunsa ta saukeshi,kusantowarsa wajen d qamshin turaren sai ya fara raba masa hankali,da coolness din nan nasa dake bayyana kansa wasu lokutan yace
"I will call you later" ya zame wayar daga kunnensa ya jefata a aljihu,ya kuma bita da hannuwansa da yake yawan sanyasu a aljihun,sannan ya waiwayo.
Yawun bakinsa ne ya kusa daukewa,gaba daya kallon daya mata ta glass din gaibu ne,yanzun yake ganin ainihin zallar reality,inda ace ita ya bawa damar dauko kayan zaice tayi da biyu ne,saidai da kansa ya dauko saboda favourite color dinsa kenan,sai gashi sun mata wani mugun kyau fiye da tsammaninsa.
Idanunsa ya aza bisa fuskarta,baby face dinta a hade babu sauran fara'a,idan ma ya kula da kyau ta sake tsuke dan qaramin bakinta data zizarawa man lebe daya sanyashi yake qyalli,sai yadan rage kaifin kallon da yake mata,ya maida dubansa kan agogon hannunsa,ko bai magana ba tasan qorafi zaiyi kan ta bata musu lokaci,ta zaci zai amsa,sai taga ya kama hannun amna sunyi gaba,dole tabi bayansa.
Ta zaci zai bata dama ta koma sashenta ta kintsashi ko ta dauko abunda take da buqata,amma sai taga baice komai da ita ba,hakanan ta bishi kamar zatayi hawaye,wannan mulkin kama karya ne da kuma qarfa qarfa,ai ba ita daya bace a gidan,me yasa bazai dauka unaisa su wuce ba?, Da wannan mitar da take tayi can qasan ranta ta qarasa motar,ta kama daya side din ta bude murfin ta shige.
Har suka isa airport bata ce ko uffan ba,yana ankare da hakan,haka kawai ya samu kansa da monitoring mood dinta,wanda shi kansa baisan dalilin hakan ba.
Sosai take kallon tsarin airport din,karon farko a rayuwarta abinda ko kusa bata taba kawowa zuciyarta zai faru a rayuwarta ba,saidai tayi qoqarin kame kanta,bata wani zarme da yawa ba,tana bin komai da lura,sai kuma abinda taga sunyi sannan,hakan ya sanya batayi wani abu daga kwafsa ba,dama kuma a idanu batayi zubin wadda zaka tsammaci ba sananniya bace a fagen,duba da jibga jibgan motocin da suka yima ja'afar din rakiya bisa jagorancin shugaban ma'aikata na kamfanin nasa.
Bayan an gama checking luggage dinsu suka amsa boarding pass sannan suke wuce gates,wannan karon amna ta dawo hannunta,dukka passingers ne dake jiran tashin jirginsu daga gomben zuwa Lagos,cikin kujerun dake wajen ta hangi jabir da fa'eemansa,tana kwance sosai ajikinsa,da alama wani abu yake nuna mata cikin waya.
Yaga jabir din amma baiyi ya ganshi din ba ganinsu tare da fatiman,miskilancin ya motsa,muryar amna tana kiran sunansa yasa ya ankara da shigowarsu wajen,da sauri fatiman ta gyara zamanta abinda ya bawa jabir daman tashi yana sanya wayar a aljihu,yayin da fatima ta budewa amna hannunta,akwai sabo tsakaninsu saboda tana da son yara fatiman,don haka ta nufeta, maimunatu ta bi bayanta,sai taji ta fara sakewa,don da alama da fatiman zasu wuce gaba daya.
*_To masu karatu, honeymoon za'a je ne ko yawon bude ido?,meye zai faru?,😂,nidai bana ce ba,ku biyoni mu qarasa bin qwaqwafin labarin tare daku_* [11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 65
"I hate it,i already told you,duk sanda kika sakemin kuka irin hukuncin da zan miki kenan" sai ya matsa a hankali ya bude mata qofan yana dubanta
"Open your eyes" kasa budewar tayi,shi wai bazai fuskanci halin da take ciki ba
"I said open your eyes ko na sake punishing dinki" jin haka yasa ta bude idanuwan nata a hankali,tana ganin qofar a bude ta taka da hanzarinta kamar zai sake kamata ta fice.
Gaba sink ya tsaya ya dafe hannayensa yana jin yadda mararsa ta riqe sosai,wani abu da yayi fama dashi shekarun baya kafin aurensa da shaheeda,wanda kusan shine silar aurensa na farko,sai yayi qas da kansa yana tattare hankalinsa waje daya,yana jiran komai nasa ya dai daita,wanda a qalla ya kusa kashe minti goma sha biyar a haka kafin ya sakarwa kansa ruwa mai bala'in dumi sosai,yana jin yadda mararsa keta murdawa tana saki.
Sanda ya fito bata dakin,koda duba falo bata nan,sai ya sanyama qofar key ya shirya a hankali,sallah yaso fita yayi cikin jam'i amma sai ya kasa,cikin daki yayita,yana idarwa amna na shigowa nan ta zauna tana masa zubar tata.
Bayanan duka duba aikin yakeso ya shigar su tattara za'a miqawa gwamnatin lagos tare da wasu muhimman takardu da kuma roqan a qara musu wasu gurare dake daura da wajen,ya debo duka kayan aikin ya jona system a charge amma sai ya kasa komai,jikinsa ya mutu murus,mararsa kuma ciwo take da gaske,bai dauki ciwon a bakin komai ba,ya zaci surutun amna ne zai hanashi aikin,don haka ya zaunar da ita,ya jawo mata suratul mulk yace tayita biyawa,cikin qarfin hali ya jawo system din ya kunnata.
Tun aikin baiyi nisa ba yaji ciwon ya matsa masa,sai ya dauka wayarsa ya turawa jabir tex don ba kasafai ja'afar din ya fiya son kiran waya ba,yace ya fiddo key din mota zai rakashi wani waje,ya maida wayar ya ajjiye yana jingina jikinsa da bayan kujera,dai dai lokacin da maimunatu ta shigo dauke da coffee.
Duk lokacin daya dawo takan dafa masa,saidai amna take bawa ta kai masa,yau din da bata ga amnan ba batason sake shigowa su hada idanu,amma dole ta dauko ta shigo dashi.
Idanuwansa a kanta,har ta qaraso ta ajjiye masa,sannan ta danja baya tana fita a dakin ya bita da kallo,kunnuwansa nakan karatun amna da yake saurare yana mata gyara inda ta kuskure kadan kadan kuma marar tasa naci gaba da murda masa.
Maimunatun ce ta sake turo qofar
"Yaa jabir yana magana" ta fada masa idanunta a qasa,baice komai ba sai ya miqe kawai ya dauki wayoyinsa yana duban amna
"Ina zuwa,yanzu zamu dawo" ya fada yana fita daga dakin,ya wuce ta falo ya fice.
Cikin mota ya sameshi zaune yana jiransa
"Ina zamu?,na gama tsara bazan fita ba sai gobe,gaba daya hutun da naso samu aikin nan bai barni na sake ba" ya fahimta sarai me yake nufi,baice masa komai ba sai ya karba key din motar,sukayi exchanging seat ya tada motar suka fice bayan ya saita map ta wayarsa,ya dinga directing nasa zuwa nearest private hospital.
Da mamaki jabir ya kalleshi bayan ya sanya hancin motar cikin asibitin
"Waye ba lafiya?"
"Nine" ya amsa masa kai tsaye, cikin damuwa jabir din yace
"Subhanallah,me ya sameka?,daga dawowarmu?"
"I don't know" ya amsa masa a taqaice,sai ya qyaleshi kawai,da alama 'yan miskilancin ne suka motsa.
Sanda suka shiga akwai likita,amma kuma da layi,saidai akwai special service,amma kudinsa ya ninka normal consultancy fee din da ake biya.
Jabir ne ya biya komai kamar yadda suka saba,duk sanda wani zaiyi wani lalurar rayuwa indai daya yana wajen shike biyan komai,kai tsaye suka isa qofan consultancy room
"Ka shiga kawai,zan jiraka a nan" jabir ya fada,bai matsanta masa ba ya shiga ya barshin.
Musabaha ya bawa inyamurin likitan hannu sukayi,ya tarbeshi da fara'a da girmamawa da alama yasan aikinsa,duk wani bayani daya kamata yayi masa yayi masan,ya kuma dubashi harda scanning,ya daga takardar yana kalla,sannan ya dawo da dubansa kansa cikin harshen turanci
"Yallabai,ka taba samun matsala irin haka?" Idaonsa ya lumshe yana gyada masa kai
"Amma ba'a taba gaya maka kayi aure ba?"
"An taba" ya amsa masa kai tsaye
"Seriously dole kayi aure,kana buqatar hakan,binciken da nayi ya nuna ba zaka iya zama a haka ba,kayi qoqari kayi,zan rubuta maka magungunan da xaka samu relief,pain din ya ragu" shuru yayi kawai yana saurarensa,kamar yanzunne ake gaya masa wannan maganar a shekarun baya,akwai case kenan ya fada a ransa.
Har suka fito jabir baice masa komai ba,shi dinne ya cewa jabir zasu tsaya a pharmacy zai karba magani ya ajjiye takardar a tsakiyarsu,kallon takardar jabir yayi,har zai tada motar yace
"Am sorry,ina zuwa" ya bude murfin motar ya koma ciki,bai wuce mintuna goma ba ya dawo,still bai sake ce masa komai ba ya tashi motar suka wuce.
Jin shurun yayi yawa sai ja'afar din yayi gyaran murya
"Jibi ne zamu koma....ka siya mana ticket?"
"Zan siya" ya amsa shi a taqaice. Kusan zaman kurame sukayi har suka siya maganin suka koma masauki,fuskar jabir din kamar akwai abinda yake nazari.
°°°°°°°°A nutse ja'afar ya daga kai ya kalli jabir bayan ya miqa masa ticket din guda biyu ya kuma gama karanta abinda ke jiki,hankalinsa kwance yake cin abincinsa
"Ticket din lagos to gombe ya kamata ka siya mana,amma ina ganin na lagos to johannesburg"
"Eh,daga nan can zamu wuce,ya kamata mu dinga samun lokaci muna dan hutawa koda ba yawa,just one week kawai zamu dawo" shuru yayi na dan sakanni yana duban jabir din,jabir din wani mutum ne na musamman cikin rayuwarsa,yana da matuqar muhimmanci a rayuwarsa,hakanan ya isa ya yanke hukunci cikin rayuwarsa kamar yadda yasan shima hakan take a wajen jabir,bayason ya maida niyyar alkhairin da yayi masa,uwa uba kuma shi kansa yasan yana buqatar wani hutun, tunda ko da sukazo nan din wani irin ayyuka ne suka hadar musu,ba wani hutu ko qanqani,amma kuma bai shiryama wannan tafiyar ba kwata kwata
"But.....kasan amma tayi maganan amna,akwai biki a dangin mommynta,jibi kuma zasu wuce har da ita"
"Nayi waya da hisham,yacemin ya shigo lagos jiya,yaje wani aiki a teaching hospital,gobe zai koma,so na yankan musu ticket shi da amnan zasu wuce gombe gobe da yamma,mu kuma zamu bi south african airways flight sha biyu na rana" boyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana ajiiye ticket din a gefansa,duk wani hanzari nasa jabir ya kasheshi,bashi da wani sauran uzuri kuma da zai bayar.
Shuru kawai maimunatu tayi tana binsa da kallo sand ayake ficewa daga dakin,bayan ya gama gaya mata inda zasun,idanuwanta suka tara ruwan hawaye sosai,saura kwanaki hudu kacal a koma makaranta,tana murna gobe zasu koma sai kuma wata tafiyar bagatatan ta taso?,hakanan ta shiryama amna kayanta da sauran tsarabarta ta nan,ta hade jakankunan dana qananun kayan da fatima ta lodo mata,don babu inda zata je dasu.
Tun tara na safe hisham yazo ya dauki amna,bata damu sosai ba don ta saba da uncle hisham din,ta kuma san cewa gwani ne wajen iya kula da yara da biyewa shirmensu,haka kawai ja'afar ya hanata fita su ko gaisa da hisham din bare suyi sallama da amna,ya rufe qofan dakin ya fita da card key din suna sallama dasu a farfajiyar hotel din,sai ta window ta leqasu,tana nan a tsaye har suka fice,shi kuma yana tsaye suna magana da jabir din.
Maimakon ta saki labulen ta koma kamar yadda take so saita kasa,ta aza idanuwanta akansa tana kallonsa,sanye yake da long sleeve zip up hoodie wine color da wandonta,gashinsa a kwance kamar ko da yaushe baqi sidik,kana kallonsa kaga baqin bafullatani,qafafunsa slipper ne,ya dan kere jabir tsaho da kadan,amma kana duban fuskarsa zakasan ba ma'abocin fara'a bane,saboda yanayinsa ya nuna,sabanin jabir da ko yaushe fuskarsa ke a sake,kadaran kadaham.
Kamar wanda aka yiwa cunenta ya daga kansa zuwa saman yana saukesu a bakin window din,cikin jikinsa yaji kamar ana kallonsa,cikin hanzari ta saki labulen taja da baya ta fada saman gadon gabanta yana faduwa,idanu ta fitar
"Allah yasa bai ganni ba" ta fadi tana dafe goshinta,idan ya ganta aita tafka abun kunya.
Sauke idanunsa yayi daga kallon wajen,yaga labule ya motsa alamun an koma da baya,gaba daya lissafin tafiyar ne cikin ransa,baisan me jabir ya qulla ba,amma yafi kowa sanin halinsa,bai taba wata magana data dangancin iyalinsa dashi ba,amma ya tabbatar da biyu ya shirya wannan tafiyar,koma meye zaiyi qoqarin kame kansa da mutuncinsa,ba zaiyi abinda mutuncinsa zai zuba a idanun qaramar yarinya ba(niko nace sannu gembo sarkin son girma,muje dai zuwa 😒).
Tun kafin sukai ga shiga jirgi ta fahimci tafiyar gaba daya kamar ta musamman ce,kamar kusan koma fiye da rabin matafiyan couples ne(wato miji da mata),kowa ka ganshi tallafe da matarsa,harda jabir wannan karon murje idanunsa ya ja fatimansa jikinsa sunata hirarrakinsu qasa qasa.
Karon farko da taji abun ya burgeta,sai ta dauke idanunta zuwa sashen da ja'afar din ke tsaye tun dazu yana amsa waya,cikin sa'a ta samu ita yake kallo,kallo kuma na kai tsaye,abinda bata sani ba ya dan jima a tsaye yana karantar expression nata directly,ya karanci akwai wani abu da ya motsa zuciyarta.
Cikin kunya ta kauda idanunta daga kansa,sai ta zaro wayarta daga qaramar jakar da tayi amfani da ita ta kunna data ta shiga watsapp dinta,rasa me zatayi tayi,bata da interest nayin chart yanzu da kowa,sai ta koma viewing status na mutane,kafin ta gaji da wannan,ta shirin sauka notification na wani app ya shigo mata,sai ta danna ta shiga,tana duba sabbin pictures da quotes na soyayya da suka dora,wannan yadan dauke mata hankali.
Sanda suke wucewa zuwa jirgi fatima da jabir suna bayansu su kuma suna gaba,ya daidata kafadarsa da tata,abinda yasa ta sake gane tazarar tsahon dake tsakaninsu,batasan me ya faru ba,a hankali ta tsinci tattausan hannunsa cikin nata,ya hada dukka tafukan hannayensu ya matse guri daya,daga ido tayi ta kalleshi jikinta yana amsawa sai taga idanuwansa na kallon wani waje,a hankali ta maida dubanta wajen,sai a sannan ta fuskanci me yakewa,daya daga cikin ma'aikatan airport din ne,sanye da kayan aiki,ya zuba dukka idanuwansa a kansu,kafin daga bisani ya janye ganin ja'afar din ya kama hannunta,qaramin tsaki yaja bayan sun giftashi da kadan,ta zaci zaici zai sakar mata hannun amma sai taga yaci gaba da riqeta,har suka isa cikin jirgin.
Batasan seat number dinsu daya bane sai da tazo zama,kallonta yayi sanda yake sanya luggage dinsa daga saman kansu,hannunsa daya dauke da da wata sweater mara nauyi me kyau
"Anzo wajen,Allah yasa ba sanyi garesu ba" ta fada cikin ranta,don babu abinda yake takura ta a rayuwarta irin sanyi,batason zafi,amma kuma idan sanyi yayi yawa yana damunta. [11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 66
*_Johannesburg_* *_kemfton park,69 oleander avenue_*
( *Eagle rock executive guest house*)
Tun daga parking lot na guest house din maimunatu tasan wajen na dabanne,jabir da ja'afar suna gaba su kuma suna biye dasu,a hankali fatiman ke mata hira
"Zan samu na huta sosai gaskiya,wajen yamin kyua fiye da yadda sweetheart ya gayamin,anty moon,qilan fa ba zaki sake ganina ba sai ranar da zamu tafi" ta fada tana 'yar dariya,murmushi maimunatun ta sakar mata ba tare da tace mata komai ba,don ita nata lissafin daban yake,batasan ya zaman zai kaya na kwanakin da zasuyi ita da miskilallen mutum irin ja'afar ba,sai kuma ta sake sakin murmushi da kwanyarta ta tuna mata da fuskarsa,ya yake iya rayuwa haka kuma yake jin dadinta?,kullum fuska a dinke?,zata iya rantsuwa bata taba ganin dariyarsa ba sai miskilin murmushin nan nasa,shima sanadiyyar zuwan amna ne.
A main entrance su jabir din suka tsaya,da alama sallama suke don yana karbar muqullin private entrance da kowanne apartment ke dashi,waiwayowa jabir yayi ya dagawa fatimansa hannu,sai ta dubi maimunatu
"Anty moon,Allah ya qaddara saduwarmu" murmushin ta bita itama dashi tana amsa mata,sannan ta taka zuwa gaba a hankali inda ja'afar din ke tsaye,ya fara gaba shima a hankali tabi bayansa.
"Bismillah" ya sake cewa bayan ya bude dakin,yadan dakata kadan yana karanto addu'o'in shiga sabin muhallin da ba naka ba,sannan ya sake yin bismillah ya shiga tabi bayansa.
Dakin ya tsaya yana qarewa kallo,na meye jabir zai kama musu daki irin haka,maganan gaskiya ya fara gajiya da kwanciya saman sofa,sauqin abun ma large bed ne dai dai kwanciyan mutum biyu,sai bed sofa.
Knocking akayi,sai ya bude,ma'aikatan gidan ne janye da luggage dinsa,ya karba ya maida qofan ya rufe,ya jawota tsakiyan dakin ya aje a gefe guda.
Fidda abubuwansa masu amfani ya fitar daga cikin jakar,sannan ya rage kayan jikinsa ya shige toilet.
Tana zaune daga kan bed sofa din tana qarewa dakin kallo,kadan kadan sanyin garin yana dan busata,da alama ba'a jima da dauke ruwa a garin ba,don ya dauki sanyi sosai,qofar toilet din taji an taba,ya fito daure da tattausar hoodie bathrobe,sai tayi qas da kanta,batason tayi wani motsi bare yace tayi ba dai dai ba zaiyi punishing dinta da kalar abinda ba zata iya dauka ba,tana jinsa ya gama shirinsa tsaf,qamshin turarensa ya gauraye dakin,qafafunsa ya zurawa wasu boots da suka dace da shigarsa sannan ya miqe yana dan dubanta kafin ya kauda kai
"Kiyi waya reception idan akwai abinda kike da buqata,za'a kawo dinner"
"A dawo lafiya" ta fada a tausashe,sai ya lumshe idanu yana jin yadda muryar ta sauka masa a kunnuwansa,ya juya a hankali ya fice a dakin.
Yana fita din sai taji kamar an zare mata qaya,batajin zata iya wanka a yanzu,don a haka ma sanyin ya dameta,sunci abinci cikin jirgi don haka bata jin yunwa,sai kawai ta gyara kwanciyarta ta fidda wayarta,tana kunnawa taga free wi-fi na guest house din,babu passcode,don haka tayi connecting hankalinta kwance.
Duk yadda taso sakewa dole ta dauko electric duvet ta yafawa jikinta saboda yadda sanyin ke qaruwa,bata jima sosai ba bacci yayi awon gaba da ita saboda gajiyan zaman jirgi.
Bata farka ba sai bayan sallar magariba sosai a can,ta fahimci hakan ta agogon dake dakin da kuma agogon wayarta data maidashi na can saboda gudun kubcewar sallah,tana miqewa ta fahimci akwai room heater,sai ta kunnata,cikin lokaci qalilan sanyin ya ragu,gidan shuru duka ba dadi. Tana niyyar shiga toilet don ta watsa ruwa ko zataji qwarin jikinta akayi knocking aka kawo abinci.
Ajjiyeshi tayi tayi sallah,sannan ta ware wanda zata iya ci,tana ci tana duba lokaci,duk sai ta fara jin wani iri babu dadi,ina ya tafi?,ya kuma dade har haka bai dawo ba?.tun tana dubawa har ta haqura,ta kammala tayi sallar isha'i,ta cire kayan jikinta ta shiga toilet ta hada ruwa me zafi tayi wanka.
Duka jakan kayanta ta zauna ta hautsina,sai ta dafe kanta,da alama musayar jaka tayi,ta dauki wadda tace a tafi mata da ita ta bada wadda tayi niyyar tahowa nan din da ita,sai ta koma ta zauna kamar zatayi kuka tana bin kayan da idanu.
Duk ciki bata ga wata suturar arziqi da zata sanya ba,daga night gown din har sauran kayan sawa dake ciki,ta dan jima zaune tana tunanin mafita,babu.....itace amsar,don haka ta maida hannunta tana sake daga kayan ko za'a dace.
Da qyar ta tsamo wata a ciki,wadda a ganinta tafi kowacce tsarki,Two pieces ce in da top,wine color,ta cikin siririn hannu gareta kamar na vest silk and satin,iyakarta saman gwiwa,ta saman kuwa zallar net ne,long sleeve ce ita,ta kuma sauko har qauri,gaba daya zare daya ne ya riqe ta saman wanda dashi ta daure gaban rigar.
Gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta,iya kyau rigar tayi mata kyau fiye da kima,ita kanta taga hakan,saidai gaba daya babu sirri,kusan abinda ta rufe matan kadanne,sai tasa hannayenta tana jan top din zuwa qirjinta sosai,ko zata sake dan rufe mata wani abu,don gaba daya tudunsu ya fito sosai ta sama.
Dan qaramin tsaki taja ganin babu abinda zasu iya sake rufe mata,sai kawai ta yanke ta kammala duk abinda zatayi tayi hanzarin kwanciya kafin ya dawo,wannan yasa ta rage wutar dakin,tabar qwai daya,sai ta koma bandaki ta dauko hair drayer din data ganina ciki,saboda gashinta yadan jiqe sanda take wanka,batason kuma kwanciya da jiqaqqen kai.
Cikin gajiya jigata da kuma zazzabin da ya saukar masa ya turo qofar dakin a hankali,qarar hair drayer din ya hanata jin shigowarsa,uba uba kuma gaba daya ta sauke sumar tata zuwa gaban fuskarta,bata iya ganin komai sai gashin nata da yayi mata rumfa.
Cikin wata kasala fiye da wadda ya shigo da ita ya maida qofar ya rufe,idanuwansa a kanta,cikin wine color sleeping dress din da tayi masifar haskata,farin bayanta da fararen damtsenta ya fito ta cikin lace top din,hawan kalar jikin fatarta sai ya zama kamar wani ado na musamman,dumin dakin ya gauraye da qamshin hair mist dinta dake dai daita masa tunani a duk sanda ya shaqeshi,maimakon yaci gaba da shigowa sai ya kasa,gaba daya ya goye hannayensa a qirji,bayan ya taimakawa kansa wajen tsaiwa ta hanyar jingina da bangon dakin,yayin da idanuwansa suka ci gaba da sauka zuwa kowanne sashe na jikinta,daga bisani idanuwansa suka tuqe ga qugunta wanda yake daya daga cikin abubuwan dake daukan masa hankali.
Gaba daya ta kwashe gashin ta maidashi baya,tana hadeshi cikin dan mitsitsin robber band,tana cire drayer dinne taga kaman da mutum a dakin,a matuqar razane ya saki drayer din,ta kuma juya da sauri da niyyar neman mafaka ba tare daga gama tantance waye a tsaye ba.
Duk yadda yakejin kasala da mutuwar jiki taku uku ya kamota,da gaske ta tsorata sosai, saboda har yanzun dakin bashi da wadataccen haske,cikin wani irin coolness ya buda qirjinsa ya sanyata a ciki,ya kuma matseta gam,sannan ya dora habarsa a tsakiyar kan nata,tattausan qanshin turaren gashin yana shigar masa hanci,gami da aike da wani saqo mai nauyi a qwaqwalwa gangar jiki da zuciyarsa,ya kuma tadda mood din da yake ciki ya fara motsa abun.
"Relax......relax,it's me,ja'afar ne" ya fada da wata karyayyiyar murya,kaman ba muryar captain ja'afar ba,mai yawan zafi da karsashi.
Ajiyar zuciya ta saki tana jin wata nutsuwa na saukar mata,ta sauke ajiyar zuciya tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa,dumin dake jikinsa yana ratsa sassalkar rigar jikinta zuwa fatarta,duk da batasan temperature na jikinsa ba,amma zuciyarta ta bata zazzabi yake,dukkaninsu sukayi shuru kowanne bugun zuciyarsa na daduwa.
Kanta ta dauke daga qirjinsa saboda yadda qamshinsa ke kashe mata kowacce gaba ta jikinta yana kuma haifar mata da wani irin feelings,tare da tuna nata waccar ranar da ta kusa hallaka yadda dumi da qamshin jikinsa ya bata nutsuwa,ta zame a hankali,sai ya sauke hannayensa a hankali wadanda ya zagaye bayanta dasu,saidai still idanuwansa dake a wani jirkice suna kallon fuskarta data yi wani fresh
"Don't do this again,idan ka tsorata ambaton sunan Allah ake" kai ta gyada masa idanuwanta na qasa,gaba daya lissafinta a yanzu na yadda zata sutura jikinta ne,ko daya bata samu zaizo ya risketa a haka ba,tana tsoron duk wani acting a gabansa kada ya hukuntata kamar yadda yace,don ta karanci fada da cikawa ne shi din da gasken gaske.
Zamewa a hankali ta baya ya zauna kan bed sofa,yana jin wani abu na tsarga masa mai tsananin qarfi cikin kowacce jijiya da hanyar jini dake jikinsa,matsalarsa na shirin motsawa ta hade masa kuma da zazzabin da tun dazu yake faman son ganin ya kauda shi bai taba shi sosai ba.
Cikin dakiya da juriya data arama kanta ta juya ta koma bakin madubin,a matuqar tsarge take tattare kayan dake kai tana maidasu muhallinsu,duk da abubuwa da yawa batasan ma inda take ajjiyesu ba,batasan me yasa ba,amma gaba daya hankalinta ya dauku ga dumin da taji a jikinsa,wanda har ya fara jirkicewa izuwa zafi,ta gama ta juyo a hankali da nufin isuwa zuwa gado.
Ya fahimci abinda take nufin yi,amma shi idanuwansa basu shiryama hakan ba,bai taba jin wani abu da idanuwansa suka jarabtu da kallonsa ba irin maimunatu,tun yana tuhumar kansa da qaryata kansa kan cewa ba ita yake kallo ba har ya fara gasgata zaton zuciyarsa
"Hadamim coffee" ya fada yana sabule boot din qafarsa dama socks din gaba daya,lallausar qafarsa ta bayyana,ya sauketa saman rug din dake shimfide iya wajen,yana fidda wata zazzafar iska daga bakinsa
"La haula wala quwwata illa billah" ya furta a fili sanda ta bacema ganinsa zuwa qaramin falon dake manne da dakin,wanda acan aka kebance wani guri aka zuba komai na amfanin kitchen.
Wayoyinsa ya ciro da suketa kuwwa ya kashesu gaba daya ba tare da ya tsaya duba me kiran ba,ya cilla wayoyin gefan sofan da yake zaune yana jin yadda mararsa ke sake curewa waje daya tare da wani irin ciwo me suka,idanunsa ya runtse yana kuma cizar labbansa na qasa.