Kenza eBookz

Gurbin ido huguma complete - Chapter 34

Gurbin ido huguma complete - Chapter 34

Gurbin ido huguma complete Chapter 34: Gurbin ido huguma complete Chapter 34. Sai da ya gama gasata sosai sannan ya bude wancan ruwan ya tsiyaye tas,ya…

4,496 words

Sai da ya gama gasata sosai sannan ya bude wancan ruwan ya tsiyaye tas,ya hada musu wa na wankan tsarki,ta dan samu qwarin jiki kadan tayi da kanta,bayan sun gama ya sake hada wani dai still da zasuyi wankan sabulu,sai kawai ya shige bathtub din ya jata cikin jikinsa,dumin ruwan yana ratsasu shida ita,lafewa tayi sosai cikin qirjinsa,lallausan gashinsa ya zame mata kamar matashi,sosai bugun zuciyarsa ke mata tasiri a jikinta,tana jin yadda yaketa sauke qananun ajiyar zuciya kamar yaron da yaci kuka ya qoshi,sai ta lumshe ido kawai tana jin wani sauyi da yake samun duniyarta.

Yaye bedsheet din yayi sanda suka fito,sai ya maida abun rufar a madadinsa,wata lallausar mini gown ya sanya mata,ya fidda sock's doguwar socks cikin kayansa ya zura mata,sannan ya sake saka mata wata zip up hoodie jacket mai dogon hannu,don ya fuskanci itadinma zazzabi ne sosai a jikinta,shikam Three quater kawai ya zurawa jikinsa,ya sake rufesu da duvet ya sanyata cikin jikinsa sosai yayi mata rumfa, numfashinsu da dumin zazzabin dake jikkunansu suka fara gauraya da juna.

Dukkaninsu haka suka kwana da zazzabi me zafi,har gwara ja'afar gab da asuba nashi ya sauka sosai,nata dinne dai babu sauqi,don rawar sanyi takeyi sosai,ya sake kunne room heater ya kuma lullubeta da kyau amma a banza,dole ya dagata,ya zare mata dukka kayan dake jikinta,ya mannata da fatarshi suka samu good skin contact,nannauyar ajiyar zuciya ya sauke,don sake haduwar jikkunansu sake kunnashi ya soma yi,musamman tudun qirjinta da ya tokareshi da kyau,kai kace da gayya tayi hakan,numfashinsa ya fara canzawa tare da bugun zuciyarsa,ya lumshe idanunsa yana jin yadda take sauke numfashi a hankali cikin galabaita da gajiya,yana tausayinta,bazai iya sake tabata,taci wahalar daya kamata ace ya barta ta sake hutawa da kyau,da yaji abun yana neman fin qarfinsa,sai ya zare jikinsa daga nata bayan yaji zazzabin yadan sauka,ya sanya mata pillow,cikin bacci ta kama pillow din da hannunta da kyau,qaramin murmushi ya subuce masa,yadda tayin fuskarta a hade kamar idanuwanta biyu ya bashi dariya,ya gama saara mata wajen shagwaba da raaki,auta ce ko 'yar fari?,baisan a good awanne ajin zai ajjiyeta ba,yadda ta qanqame pillow din ya tabbatar da idanuwanta biyu ba zata yarda tayi hakan ba.

Alwala ya shiga ya daura da ruwa me dumi,abun sallah ya shinfida,ya tsaya sosai akai yana fuskantar ubangijinsa,ya masa baiwa a rayuwa har karo biyu,a cikin wannan rintsin rayuwar da mata na gari ke tsada da wahala,duk kuwa da cewa duniya cike take da tarin mata birjik,amma ta aure wahala take,saidia shi din ya kebanceshi da baiwa ta musamman.

°°°°°°°°°sai data yi kusan minti biyar da farkawa amma bata motsa ba,a hankali take shaqar tattausan qamshin dake fita daga jikinta jacket din nashi da har yanzu itace a jikinta,qamshin da babu abinda yake tuna mata sai daren jiya,abubuwan da suka faru suka runga dawo mata,sai ta dinga jin komai kamar a mafarki,kwanyarta ta dinga tuno kalaman da bakinsa suka dinga furta mata,sai ta sauke ajiyar zuciya me nauyi,ta kasa kunnenta taji ko zataji motsinsa ta koma ta sake lafewa?,jin shuru ya tabbatar mata da baya dakin kwata kwata,don haka ta miqe ta zauna sosai tana kallon lokaci,qarfe kusan sha daya da rabi na rana,tun asuba data yi wuf a daddafe tayi sallarta ta koma bata sake farkawa ba sai yanzu.

Zaune tayi tana qiyasta da yadda zata miqe,ko ina ciwo yake mata a jikinta,cinyoyinta kamar anyi ajiyar dutse,duk da ya ragu ba kamar daren jiya ba,sai ta yanke shawarar ta sake shiga bandakin ta hada ruwan zafi ta yiwa kanta yadda yayi mata jiya,tana zuro qafarta qafa taqi bata hadin kai,sai ta narke gaba daya zuciyarta ta karye,kada dai ace ya illatata gaba daya ba zata sake moruwa ba?,idan haka ya tabbata da wanne ido zata yima mutane bayani?,take qwalla ta cika mata idanuwa,ba dadewa kuma suka fara bin kuncinta,dai dai lokacin da ya turo qofar ya shigo.

Fes fararen idanuwansa da suka sake wani haske suka sauka a kanta,yana sanye da wata hoodie jacket wine color da baqin wando,ya sauke hular a bayansa,sai tattausan baqin gashinsa sake sheqi cike a kansa,ya sake wani fresh dashi,jikinsa na fidda rikitaccen qamshin nan nasa.

K'as tayi da kanta tana jin inama bata farka ba,yayin da murmushi ya subucewa fuskarsa,cikin zuciyarsa ya furta

"Yanzun ne ya kamata kiyi tsoro me dalili yarinya ba tsoron baya ba na sakalci da shagwaba" takowa yaci gaba dayi zuwa gabanta,yana ayyana yadda zai dasa zazzafar soyayyarsa a ranta,tunda ya fahimci ya ribatu da samun empty heart da bata taba daukan soyayya me zafi irin wadda yake buri ba,so yake tayi masa soyayyar da ba'a taba masa kwatankwacinta ba,yana buqatar ya samu qauna data ninka wadda shaheeda tayi masa,soyayyar da zata zama abar kwatance,ya riga da ya gama sallama mata rayuwarsa,saboda haka bayajin akwai wani abu da zai musu shamaki a tsakaninsu shi da ita.

"Gudmorning moon" ya fada da wata murya dake cike da shauqi,shauqin da tunda ya tashi har ya fita ya dawo shine taf a zuciyarsa,wani irin memorable night da bazai taba shafewa a rayuwarsa ba muddin yana da rai

"Ina kwana?" Ta fada cikin girmamawa,bai amsa mata ba,sai ya duqa a gabanta,wata kima da daraja ta samu farat daya a wajensa,ba ita kadai ba,hatta anni a yanzun yana jinta fiye da yadda take a wajensa a baya,bare kuma ita maimunatun,hannayensa ya zura ta qasan fuskarta,sannan a hankali in a low sound yace

"Kwana na yana gurinki.....get up dear" fuskarta a narke ta tabe baki irin na mutumin dake shirin sakin kuka,sannan ta langabar da kanta gefe guda,ha fahimci tana son ce masa ba zata iya ba,amma baki ya gaza fada,sai kawai ya miqe a hankali,yasa hannu kamar daren jiyan dai a tausashe ya dauketa ya nufi toilet din da ita,yana tafe yana kallonta duk da ta cusa fuskarta a qirjinsa,da zata iya da tace masa ya sauketa,yanzun ma da ranar Allah sake kalleta zaiyi haihuwar daadarta?.

Bai sanyata dole kan cire kayanta ba,amma ya tsaya ya gasata kamar daxun,mai ciwo yaji dadin jikinta,sai ta fara son qwacewa,sai ya kamata suka antaya ciki gaba daya shi da ita,dole tayi luf,tun tana jin zafi har ruwan ya fara mata dadi,ya sake tara mata wani sannan ya fito ya barta don ta qarasa.

Manyan towel guda biyu tayi amfani dasu,daya tayi daurin qirji dashi,dayan ta lullube kanta ruf,baka ganin komai sai kwantacciyar sumar gaban kanta mai salki,yana tsaye gaba mirror yana kurbar coffee din da ya hado a hankali,ya bude idanuwansa a kan fuskarta.

Sosai yaga fuskartan itama tayi fresh,farinta kamar ya qaru ya kuma sirkuwa da jaja jaja,tsigar jikinsa ta zuba gaba daya,ya hadiye sauran ruwan coffee din daya kurba,sai ya dora cup din saman morrow din,ya nufota a inda take tsaye daga gefan qofar toilet din,tana ta karatun ta yadda zata shirya yana cikin dakin,da kuma kayan da zata saka wadanda ba zasu fidda tsiraicinta ba sosai.

Idanuwanta a kansa kamar yadda nashi yake a kanta,wani abu mai qarfi yaji yana fusgarsa zuwa gareta,wani abu mai nauyi da tasiri da bai taba jinsa a ransa ba.

Tsoro ya hanata motsawa daga inda take,gani take kamar wani abun zai sakeyi mata,ya karanci tsoronta tsaf,sai ya saki murmushin gefen baki har ya isa dab da ita,a hankali ya sauke zip din jacket din nasa qasa,ya kuma balle botiran gaban shirt dinsa me kauri,sai ya qara matsawa taqi gaba kadan ya manneta zuwa cikin qirjinsa,a tare suka sako ajiyar zuciya,yayin da yaci gaba da sauraren bugun zuciyarta yadda yake gudu fat fat,da alama akwai tsoro tattare da ita.

A hankali ya zura hannayenta ya zagaya dasu zuwa bayansa ta yadda zata rungumeshi sosai,shima haka din yayi ,ya zagaye hannuwansa ta bayanta abinda ya qara musu kusanci sosai,ta shige sosai cikin rigarsa,wani irin dumi da unique qamshin nan nasa ya sauka a hancinta,sanyin data soma ji bayan fitowarta yayi qaura,sai ya dora kansa saman kafadarsa,bakinsa saitin kunnenta cikin fusgar kalaman bakinsa sakamakon yadda tudun qirjinta ya fara rikita masa lissafi

"Relax, don't scare,am not going to do anything angel" wata ajiyar zuciyar ta kuma saki,a hankali yaci gaba da shafan bayanta kamar yadda akema qaramin yaro duk sanda yake rigima,tsahon wasu mintuna sannan ya jata a hankali,suka dinga takawa kamar me koyon tafiya,saboda yasan akwai mikin ciwo a jikinta.

Gaban mudubi ya tsaidata,sannan yaja mata kujera ya kuma zareta daga jikinsa yace

"Seat here" a hankali ta zauna tana rintse idanunta saboda yadda wajen har yanzu yake mata ciwo,ya lura da hakan,sai ya saki boyayyen murmushi,wani sashe na zuciyarsa kuma na jin tausayinsa kan barnar da yayi mata.

Man shafawarsa ya dauko,ya bude ya dora saman mirror din,ya lakato ya daga tattausan tafukan hannunta da kallo da suke jazur, saboda tsaban fari har wani kwanciyar jini sukayi,ya lakata mata man sannan yace

"Lemme help you" sai ya koma daga bayanta ya fara shafa mata a baya.

Idanunta ta lumshe kawai,zallan mamakinsa suna sake shigarta,kamar ba ja'afar ba,ja'afar din anni da amma,gaba daya kamar wani ja'afar na daban aka sauya mata,dukka ya kwance gaba daya.

Wasu abubuwa taji suna mata yawo dukka jikinta,in a romantic way yake mata shafan man,tana iya kallonsa ta cikin madubin yadda gaba daya yanayinsa ya canza, tsoro ya sake cikata,ta riqe kukanta da kyau wanda ke shirin qwace mata,idan yace zai sake wani abu da ita ta tabbatar mutuwa zatayi,ba zata iya sake dauka ba.

Sosai ya dinga qoqarin controlling kansa,bayan ya gama shafa mata zuwa inda yasan ba zata iya ba sai ya dauko hand drayer, already ya iya wannan,shike gyara ma su amna da amra kai sanda suna raye,harma shaheeda,tunda dukansu suna da yawan suma,mamarsu ce kawai bata kaisu ba,don su shi sukayo wajen yawan sumar,don baya sati baiyi gyaran fuska ba,tunda ba kasafai yake rage sumar kansa ba.

Tsaiwa yayi shi da kansa yana kallon innocent face nata ta madubi bayan ya gama gyara mata gashin ya kuma kame mata shi da band,fuskarta ta fito fayau kuma tayi wani irin fes,idanunta sun sake girma da haske,hakanan siraren labbanta kamar an sake qawatasu,sai ya sunkuya yayi kissing tsakiyar kanta yana lumshe idanunsa.

Dukka kayanta noqewa tayi taqi sakawa,daya fita ya bata option na ta saka kayan da taga sun mata a dakin,har nashi luggage din ya bude mata yace ta zaba.

Wata farar turtle neck shirt nashi ta dauko,tana da dan kauri,sannan itama dogon hannu ne da ita,a sake take,don ba size dinta bane,ita ta saka,ta tsaya tana duban kanta a madubi,rigar tayi mata kuma tayi mata kyau sosai,saidai kuma tana kunyar ya ganta da kayanshi a jikinta,ta lumshe idanu tana shaqar daddan qamshin dake fita daga jikin tattausar rigar,batasan me yasa qamshinsa yake kashe mata jiki ba,bata gama wannan tunanin ba ya buda qofa ya sake shigowa dauke data leda mai kauri,sai ta bude fararen idanuwanta da sauri.

Kamar wani sakarai ko kuma yau ya fara ganinta haka ya saki baki yana kallonta,bai taba ganin kyan rigar ba sai yau data sanyata a jikinta,kallon kallo sukaima juna kafin ta janye kallonta daga kansa,ya tako a hankali zuwa ciki yana ajjiye ledar,zuciyarsa nason ya qarasa gareta amma kuma wani sashen yana masa burki,yana kuma gaya masa

"Dole ka bita a hankali,sai ka rage tsoronka daka dasa mata tukunna, ayanzun a tsorace take dakai,dole kadan nisanceta kadan" da wannan shawarar ya samu waje ya zauna,ya fidda komai dake cikin ledar,breakfast ne da qamshinsa ya cika dakin,da alama wadanda suka tsarashi sun san sirrin girki

"Oya,come and take your breakfast" yayi maganar da mayen kallon nan nasa,qas tayi da kanta,sannan ta fara takowa a hankali,yabi qafafunta da kallo,yadda take tafiyar kawai ya isa ya shaida maka lallai wani abu me girma ya faru da ita.

Suna cikin yin break din wayarsa tayi qara,sai ya duba me kiran,jabir ne kamar yadda ya zata,daga wayar yayi,amma sai ya sanyata a hands free ya dorata saman cinyarsa,idanuwansa akan fuskarta yayi masa sallama

"Yallabai,wai anya kuwa lafiya?"

"Me ka gani?" Ya tambayeshi kai tsaye

"Jiya nayita bugu na baku dinner dinku,yauma da safe haka zamu wuce strolling da fa'eema zata dan ga gari shima shuru" sai da yayi sipping coffee dinsa sannan yace

"To sai akayi yaaya?" Dariyar da yaketa riqewa ce taso fitowa,ya sake danneta

"A'ah wai kada ka mace ma mutane a daki ne,shi yasa nake cigiyarka,kuma jiya da dare naji dakin kamar ba lafiya ba,har zan kawo dauki fa'eema ta hanani" tsaki yaja yana saurin kashe wayar daga hands free din da ya sakata ya karata a kunnensa

"Amma qur'ani cewa yayi idan baku samu kowa cikin gida ba kada ku shigesu har sai an muku izini,idan ma akace ku koma to ku koma,na meye wannan bin qwaqwafin?,ni bazan huta ba?,ko kai kadai ne me iyali?"

"Allah ya baka haquri,daga abun arziqi?" Yayi maganar yana tuntsirewa da dariya,fatima nata mintsininsa da yi masa sign na ya daina don Allah,don shike maganar amma ita kejin kunyar, batasan yadda zasu hada ido da ja'afar ba,tana matuqar girmamashi

"Inda kazo min daki a jiyan ma saina farfashe maka kai,banyi laifi ba"

"Sai ogaaaaa,tuba nake" ya fada dariyarsa na fita gaba daya

"Da anni fa zan kira.....wallahi nace mata ba lafiya ba" ya sake fada cikin wani karsashi tare da son sake tunzuro ja'afar din

"Sai ka bada himma" daga haka ya yanke wayar kit,wani murmushi da baisan daga inda yake ba na fita a fuskarsa, jabir jabir?,dan uwan da babu kamarsa,yasan ya fahimci komai,don yaga gilmawarsa a fitar da yayi,ya kirashi ne kawai ya zolayeshi,kuma sai yayi din sannan hankalinsa zai kwanta,jabir ya masa haka ina ga anni,gardin case kenan,ya fada a ransa. [11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 71

Duk yadda ta zata zai barta ne ta huta ita daya hakan bai samu ba,don hatta da girki a ranar data musu na a abincin dare yana tare da ita a kitchen,waya ce a hannunsa yana duba saqonni,amma kuma ya kasa ya tsare da idanuwansa,gaba daya ya azata mata wani nauyi,baya minti uku cikakke bai dago ya ritsata da idanuwansa ba,duk sai tabi ta rude ta kuma gaza sakewa,dalilin hakan har ta yanke hannunta.

A razane ya aje wayar,ya kuma sauko daga saman cabinet din kitchen din da yake zaune a kai,ya riqe hannun da kyau yana kalla a nutse

"Hold on,ina zuwa" ya fada yana fita a kitchen din da dan sassarfarsa,babu jimawa ya dawo da first aid box

"Zauna anan" ya fada yana nuna mata inda ya tashi dazun,ba musu ta zauna,saidai yana bude akwatin hankalinta ya tashi,ta fidda idanu tana zaton ya iya allura,har ta kasa boyewa

"Don Allah......don Allah kada kiyimin allura" cak ya tsaya da neman cotton wool din da yake,ya daga shanyayyun idanuwansa ya zube a fuskarta,karon farko tunda suke dashi taga murmushi na zahiri saman fuskarsa wanda har yaso ya hadu da qaramar dariya,fararen jerarrun haqoransa suka bayyana,sai taji kamar jinin jikinta ya daskare a wajen

"Haka murmushi ke masa kyau?" Ta tambayi kanta da kanta

"Matsoraciya......kin taba ganin captain yayi allura?" Tambayar tadan sanya mata nutsuwa data tuna shi din ba likita bane,sai kunya ta kamata tayi qas da kanta,shi kuma ya janye idanuwansa yana ci gaba da neman audugar

"Ban san me yasa.....fillon da tayi kiwo da dabbobi masu yawan gaske cikin daji.....babu qawa babu aminiya amma take tsoron allura ba,kin bada fulani fa(niko nace yo dama ai sun jima da baduwa,muggan ragwage ne😏🤨🤨)" cike da mamakin maganarsa take kallon fuskarsa,saidai ko sake daga kai baiyi ba bare ya nuna yasan shi take kallo,maganganunsa sunyi kama da maganganun mutumin da yasan wani abu game da rayuwarta,bai sake tankawa ba haka itama,sai ya kama hannun nata a tausashe ya fara goge mata wajen yankan,ta runtse idanunta saboda zafin da ta danji,sai ya dakata yana duban fuskarta da rufaffun idanuwanta,yaga yadda ta kebe baki ta kuma bata rai sosai

"Na dade ina tunanin auta na aura ko diyar fari......shagwabarki tayi yawa,ashe dukka kika hada.....ga wautar dan fari,ga sakalcin auta" ya qarashe maganar miskilin murmushinsa na subucewa a labbansa.

Wannan karon dole ta bude idanuwanta tana sake kallonsa da kyau,yanata kasheta da mamaki,a ina ya santa haka,sai yayi kamar bashi yayi maganar ba,yaci gaba da wanke mata wajen,har ya gama tas ya bata pain killer.

"Abar girkin nan haka,nidai na yafe" ya fada yana rufe akwatin,sannan ya miqe tsaye,ya qarasa gaban gas din ya kasheshi,ta bishi da kallo,tana son gaya masa ya barta zata iya ta qarasa,amma sai ya tsaya gabanta yana bata hannunsa,dole ta miqa masa nata,ya jata jikinsa suka fice a kitchen din.

Duk yadda yaso dauriya daren ranar ya kasa,dole ya sake kai kansa gareta,saidai yadda ta dinga masa kuka cike da tsoro yasa ya haqura,ya sanyata a qirjinsa yana sauke ajiyar zuciya kamar zai shide,shi da ita dukka sun dauki dogon lokaci kowannensu baiyi bacci ba,saidai duk da haka ta rigashi yin baccin.

^^^^^^^^^Washegari kasa hada idanu tayi dashi,ko sau daya bata yarsa qwayar idonta ta shiga tasa ba,daren jiyan ba qaramin murzuwa tayi a hannunsa ba,duk da baikai ga gaci ba amma jikinta ko ina ciwo yake mata,har cinyoyinta ma basu tsira ba.

A haka ta dinga zuba idanu taji yayi mata zancan ta shirya komawa makaranta amma shuru,ko kadan shima bai sake tunawa da wata maganar makaranta ba,yana shiryawa zai fita gaida su amman wayar anni ta riskeshi,tace yazo shi da maimunatun takeson gani,amsa mata yayi da to,don bai kawo komai cikin ransa ba,gefe daya tun jiya zuciyarsa ke cike da mamakin unaisa?,ina taje?,ita dai ba qaramar yarinya ba bare ace bata tayi ko kuma an saceta,hakanan baiyi da ita zata fita zuwa ko ina ba,saidai duk da haka zaisa a bincika masa ko gida ta tafi.

Sanda yace ma maimunatu ta shirya zasu gidan muraran farincikinta ya gaza boyuwa,nan da nan ta buda kayanta na lefe,ta hada kaya sosai da zata kaima su annin da sunan tsaraba,ana zaune a mota yaga fitowarta,idanunsa suka dinga yawo a kanta saboda mugun kyan da tayi masa,yana zaune harta qaraso,sai ya bude murfin motar,ya zuro qafafunsa waje,ya kama hannunta ya jata zuwa ciki,bata musa ba tabi bayansa cikin fargabar kada dai yace an fasa zuwan,tuni ta narke fuska idanuwanta suka fara tara ruwan hawaye.

Closet dinta ya bude,ya fidda wasu kayan daban,sannan ya fara ware na jikin ta,hannunsa ta riqe gam tana dubansa,sai ya girgiza mata kai sannan ya zare hannunta.

Shi ya sake shiryata tsaf,ya isa da ita gaban mudubin yana tsaye a bayanta,dukkansu shi da ita suke kallon mudubin,ya sakar mata tattausan murmushi yana duban qwayar idanuwanta,yaso ya rage kyau da kaifin kwalliyar data yine,shi yasa ya shiryata da kansa,amma kuma ya gaza yin hakan,wani kyau na daban ta sakeyi.

Da wani irin zafin nama ya juyo da ita suna fuskantar juna,don har ta tsorata tana dubansa,hannunta saman kafadarsa, idanuwansa ya sauke kan jajayen lips dinta,wanda koda bata saka mishi jambaki ba iya man lebe ya wadatar ya fidda kyansa,miyansa ya tsinke,ya hadiye wani abu ta maqoshinsa,sannan yakai bakinsa saman nata a hankali yana lashe lips din nata hade da wani zafafan kisses.

Sai da ya gama kashe mata jiki gaba daya sannan ya dauke bakinsa yana sauke numfashi a hankali,sakinta yayi sai tayi taga taga kamar zata fadi saboda rashin qwarin jikinta,da sauri ya tallafe ta yana kallonta,a karon farko yaga yadda tayi laushi,don har ta cikin idanuwanta hakan sun nuna,sai ya ajjiyeta gefan gado sannan ya wuce toilet dinta a hankali.

Minti.biyu kawai ya fito yana goge fuskarsa,ya miqa mata hannunsa ta dora nata a kai sannan suka fice zuwa motar,cikinsu ba wanda ya sake cewa komai.

Yau kai tsaye sassan abbi suka fara dira,saboda khadim da suka hadu dashi yace amma da ammi duka suna can,tamkar ta nutse haka maimunatu ta dinga ji,sai take ganin kamar kowa yana karanto komai daga jikinta.

A matuqar kunyace ta gaida abbi sannan ammi,amma tana bedroom din abbin tana gyara masa gami da hada masa ruwan wanka,sai data fito ta gansu,sai ta shaidaws abbin ta gama tana qarasowa cikin falon.

Yau fuskarta dauke da wani irin murmushi da farinciki,ta qaraso tana amsa gaisuwar maimunatu gami da sanya hannunta dukka ta dagota,sai kawai ta rungumeta

"Ashe ke din jinin sa'adatu ce maimunatu?,na jima jikina yana bani kamar na sanki,kamar nasan wani da yake da.nasaba dake,ashe diyar matar dan uwana ce ke, alhamdulillah" ta qarashe maganar tana maimaita hamdalarta,yayin da kunya suka yiwa maimunatu qawanya.

Shiko jabir yana zaune qafafunsa harde da juna yana kallonsu,wani farinciki yana ratsashi,shaheeda ta tafi ga wata shaheedan,komai da yake qiyastawa na shaheeda wanda yayi missing nasa ya sameshi a wajen maimunatu,harma abinda ita din bata dashi.

Su laila nata kai kawo suna son samu space suyi hirar yaushe gamo da maimunatun amma kowacce idan ta shigo sai ta wayance da wani abun ta fice ganin ja'afar na wajen,sai da amma ta cikata da kayan ciye ciye a sassanta,amma ta kasa cin komai saboda kunyar amman da takeji

"Maimunatu,diyata ce ke yanzu ba surukata ba, maimakon ki sake sakin jikinki sai kuma ki sake dararewa?" Matsowa gaba kadan ja'afar din yayi,ya buda dukkan abinda amman ta ajjiye ya zuba mata,kafin ma ya gama amma ta miqe ta matsa a wajen.

Shanyayyun idanuwansa ya sauke mata

"Ko sau daya ban taba ganin kinci abincin kirki ba.....oya matso muci" ya fada murya can qasa,narkewa tayi kaman zata saki kuka,a shagwabe tace

"Nafa qoshi" idonsa ya lumshe yana cije labbansa,tana kasheshi.....har baisan iyakar illar da take masa ba idan tayi wannan shagwabar tata,tana jefashi a wani yanayi,har yana jin kamar bazai iya jurewa ba.

Kaman baiji me tace ba ya matso ya dauki spoon ya saka musu a ciki,ya tsareta kuma da idanunsa,dole ta dauka ta fara motsa abincin kafin takai bakinta,a spoon na biyu kuwa hannunta ya kama yakai bakinsa,idanu a waje tayi galala tana kallonsa,bayajin kunya ko tsoron kada wani ya shigo?,saidai shi ko a jikinsa,ci gaba yayi da tauna abincin,yana jin yana masa dadi a baki fiye da kullum,ko don da hannunta ta ciyar dashi?.

Wasa wasa sai gashi sunci abincin shi da ita ba laifi,shigowar anty maama yasa suka fara wucewa sassan anni ita da ita,kafin ya bisu a baya.

A nutse anni tayi mata kyakkyawan kallo guda daya,a take kuma ta fahimci komai ya kankama

"Anzo wajen,haka dama nakeso,zakaci qaniyanka" ta fada a ranta,tana amsa gaisuwa maimunatu,wadda ta duqa gabanta tana duban qafan annin data sake motsawa da ciwo,sannu take mata,tana jin ciwon annin yana taba ranta, tsohuwar nada kima da martaba a wajenta,sai ta karba man da take shafawar taci gaba da shafa mata,annin na tayata murnar na haduwarsu da sa'ade,da kuma maida zancan yadda abun ya kasance,anty maama na saka musu baki,itama har cikin ranta tana jin dadin kasancewar hakan

"Ni kaina na jima ina ganin yanayinta da anty sa'adah da fareeda,musamman fareeda,muryoyinsu kusan daya ne,duk sanda naji muryarta sai na tuna dasu,ashe jini daya ne"

"Ikon Allah kenan,ga abinda kaketa nema ashe yana kusa da kai baka sani ba" anni ta fada rana jin zuciyarta na mata dadi,abu daya ya ragewa maimunatu a yanzun shine bayyanar mahaifinta,wanda shima ta fara shirya yadda zata tunkari ja'afar da maganar,don ya kamata ayi wani abu a kai, lokaci yana dada ja.

Dai dai lokacin da yayi sallama ya shigo,kamar kowanne lokacin idanuwansa suna kan maimunatu,duk inda zaya shiga ita yake fara gani,muddin tana waje.

Qasan carfet yau din ya zauna,dab da anni da kuma maimunatu da jikinta yayi week tun shigowarsa,batason yayi wani abu da zai bata kunya a gaban anni,don haka tana gama shafawan ta ajjiye man ta matsa daga wajen.

Gaida annin ya fara yi yana mata sannu da jiki,ta amsa tana dubansa,kafin ta dauke kai tace

"Sannunku da hanya matafiya,ya gajiyar tafiya"

"Alhamdulillah" ya amsa mata hankalinshi kwance,kamar bai fahimci da gatse tayi maganar ba

"To ma sha Allah,ba wata doguwar magana bace,dama so nake na gaya maka,da Allah kayi da jiki ka maida yarinyar mutane makaranta,tunda dai amana na dauko,kai kuma alqawari ka dauka,to ya kamata ka sauke" ya manta rabon da yaji gabansa ya fadi sai yau,yadan lumshe idanuwansa sannan ya budesu yana duban anni

"Wacce makaranta?" Dubansa take saboda yadda taga zai raina mata hankali

"Makarantar da ubanka marwanu ya bude" dauke kansa yayi daga inda take,yasan anni,zata fadi fiye da haka ma,don haka ya fito mata shima a ja'afar dinsa sak

"Na cireta anni,wata zan canza mata"

"Dalili?" Ta tambayeshi harda riqe qugu tana qare masa kallo

"Kawai" ya amsata yana sassauta daurin agogon dake hannunsa,don a take yaji kamar ya matseshi ma.

"To uban maryamu,to billhuwallazi la'ilaha illa anta baka isa ba,uban kuturu ma yayi kadan ballantana na makaho,kaiiii ja'afaru,kayi ta kanka wallahi,bakasan wace maryamu ba hala,mu zaka mayar qananun mutane?,wanne irin zabine baa baka ba amma ka kafe can zaka kaita?,shine zaka tsire cireta a makaranta kanason yi mata walagigi da karatu?,to kayi qarya ka kwana da yunwa" boyayyar ajiyar zuciya ya saki,yana jin cewa ya shiga uku yau,tijarar anni ta dira a kansa

"Lemme explain you mana anni....."

"Lamma ma taci qaniyarta,kayi ta kanka fa,idan hausa hausa idan fillanci fillanci" hannunsa yasa ya dafe goshinsa da kyau,anni bata da kyau idan ta tubure,gashi jabir baya kusa ballantana ya tayashi,shi kuma bai iya daukan hayaniya da yawa ba har haka

"Relax.....relax,ba daina karatu zatayi ba,inaso ta koma day ne,i mean jeka ka dawo"

"Baka isa bafa,ita ka fara zaba mata ita zata ci gaba da zuwa,idan kaga ta daina saidai idan itace tace bata so....." Maida dubanta tayi ga maimunatu dake zaune,tayi shuru yana sauraren dambarwar tasu

"Ke maimunatu.....kinason komawa makarantarki......ko kin zabi dadi miji ya sauya miki wadda yaga dama?".... [11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 70

Seat din kusa da ita fareeda diyar sa'ade ta barwa maimunatu,dukkansu suna ta kallon maimunatu cike da zumudi a zukatansu,saboda suna da.labarinta sarai,sannan ita fareeda tana dan tuna wasu abubuwa da suka faru,tunda da dan wayonta suka bar gembu.

Cikin tafiyar awannin da suka cur hannun sa'ade yana cikin na maimunatu,kaf maimunatu ta labarta mata dukkan abinda take da buqatar sani,saade ta lumshe idanu hawaye masu dumi suna fita akan fuskarta

"Wata shari'ar sai a lahira,inno taci amanata taci amanar shatu,Allah ya jiqanki 'yar uwata,matsala na samu akan dukka abinda ya shafi bayanaina,aka samu wasu suka dauka sukayi amfani dasu suka aikata laifi,ya zamana ni ake zargi aketa nema,wannan dalili yasa abbansu yayimin kyakkyawan boyo,sannan akaci gaba da bincike,don yasan muddin ya fiddani aka kamani babu mai fitar dani sai Allah,wannan dalilin ya hanani dawowa gareku,saidai duk da haka nayi amfani da abbansu nayi aike gembu,waya kudi da kaya,ina amfani da wani boyayyen layi ina yawaita kiran inno akan yaya kuke ya lafiyarku?,koda yaushe nunamin take kuna nan lafiya,bana jimawa akan waya shi yasa bana samun damar cewa a bani ku,aike nake akai akai na kudi da kaya ashe baya samunku,ashe sun gama shirya abinda suka shirya,ashe sun cutar min da shatu na,sun kuma cutatar dake kema" sai suka sanya kuka gaba dayansu hannuwansu cikin na juna.

Dogon numfashi ja'afar dake daga can bayansu ya saki,tunda suka zauna hankalinsa da nutsuwarsa tana kansu,duk da baijin abinda suke fada amma yana iya fahimtar kuka suke,yana kuma ji a zuciyarsa maimunatun kuka take da gasken gaske,yana ta son ya daure amma ya gaza,yana jin kukan nata yana tabashi sosai

"Please,ka gaya mata ta daina sakata kuka haka" ja'afar ya fada idanuwansa a kansu,kallonsa jabir yayi baki galala

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull