Halysaah by khaleesat hydar - Chapter 31
Halysaah by khaleesat hydar Chapter 31: Halysaah by khaleesat hydar Chapter 31. Next update at night in sha Allah. [6/2, 8:30 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: A…
35,437 words
Next update at night in sha Allah. [6/2, 8:30 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: A hankali Khaleesat ta ɗan bude curtain din dakin Aunty Farida tana leko cikin parlon ta hada ido da su gaba daya, sauke idonta tayi ta shigo parlon walking slowly ta tafi ta zauna kan kujera kanta a kasa, tun da taji sallama ta tashi ta tafi dakin Aunty Farida don saka Hijab dinta, gaishesu tayi still not looking at them, Jay ne kawai ya amsa yana kalllonta calmly yace "How are you feeling now Housemate?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa a hankali tace "I am much better now" Kallon Ajay tayi suna hada ido ta sunkuyar da kanta tace "Ina yini?" Yana danna wayarsa yace "Fine" Aunty Farida ta shigo parlon daga kitchen ta ajiye masu tray din Can drink da ruwa da taje dauko masu, sannan ta zauna kan kujera tana kara gaishesu, Jay yace "Ya me jiki" Aunty Farida tace "Da sauki, abinci ne dai bata ci har yanxu" Jay ya daga kai ya kalli Khaleesat, sauke idonta tayi ta dau plate din abincin da Aunty Farida ta zuba mata not long ago, ta bude murfin ta ajiye sannan ta dau spoon ta fara cin abincin a hankali, Aunty Farida na kallonsu tace "Bari in kawo maku abinci" Ajay ya kalli Jay, Jay yace "A'a mun yi breakfast Aunty, mun gode" Aunty Farida tace "To ai rana tayi yanzu" Bata jira taji me zai ce ba ta tafi kitchen zata zubo masu abincin, ita dai Khaleesat a hankali take cin abincin hannunta, mikewa Ajay yayi, Jay ya sa hannu a aljihunsa ya ciro wayarsa, Ajay yace "Zan yi waya a waje" Daga haka ya fita daga parlon kafin Aunty Farida ta fito daga kitchen, Jay yayi murmushi bai dai ce komai ba, bude wayarsa yayi yaga miss calls din Safiyyah har shidda, yayi dialing number dinta ya saka handsfree, yana fara ring Safiyyah ta daga kamar jira take, yayi kasa da murya yace "Can you hear me Safiyyah?" Tace "Ina jin ka, plss ba a san inda Khaleesat take bane tun ranan asabar, kuma ni nasan bata da inda zata je a garin kano" Yace "Where are you at now?" Da sauri tace "Nima a kano nake ai, jiya da yamma na dawo daga Maryland shi ne na zo gidansu yau nake samun labari she is away from home tun ranan Saturday after receiving the news of her marriage with Abdul, wai Abdul fa aka daura mata aure da" Safiyya na kai wa nan ta fashe da kuka, Jay yace "I mean are you at home or where?" Cikin kuka tace "A'a yanxu na baro gidansu, ina bakin titi ma haka, i am just confuse, Khaleesat bata da kawaye bata zuwa ko ina, i don't know where she will be now, i am disturb don Allah in kasan inda take kar ka boye min plss Ya Jawwad trust me" Calmly yace "Look, this should be confidential Safiyyah, i trust you are saying nothing to anybody about this...." Da sauri Safiyyah tace "Na rantse babu wanda zan ce ma komai Ya Jawwad, trust me, i am also not in support of the fruitless marriage" Jay yace "Ohk, here is ur frnd speak to her....." Mikewa yayi ya mika ma Khaleesat wayar, ta amshi wayar tana kallon screen din dama tun jiya take wishing ace Sophie na kusa da ita ko ba komai zata dinga Consoling dinta tana karfafa mata gwiwa da bata assurance, lkci daya hawaye ya cika idonta cikin rawan murya tace "Sophie" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Khaleesat, i am so happy you are safe and sound, dama fatana kenan, plss kina ina haka yanxu in taho don Allah" Khaleesat ta girgiza mata kai cikin sanyin murya tace "Bana kano Sophie" Da mamaki Safiyya tace "To kina ina?" Khaleesat ta daga kai ta kalli Housemate dinta dake kallonta, sauke idonta tayi da kyar tace "Ina Lagos" Safiyyah tace "Lagos wajen wa? Ko wajen Aunty Farida?" Khaleesat tace "Um" Safiyyah tace "Amma Umma bata san kina nan ba" a hankali Khaleesat tace "Bata sani ba" Safiyya ta sauke wani ajiyar zuciyar tace "Pls kar ki tada hankalinki kinji kawata, i know ur Housemate won't allow u do that, kuma in sha Allah babu zaman aure tsakaninki da Abdul don bai yi deserving din ki ba, i can't imagine what he will turn you into, in Allah ya yarda bazai ci nasara akan ki ba, Allah zai raba auren cikin gaggawa, shi kadai yasan mugun Intention din dake ransa akan ki shi yasa yayi haka, amma Allah ya fi sa" Khaleesat dai gyada mata kai kawai take hawaye na sauka idonta ta kasa cewa komai, Housemate dinta ya mike ya nufeta ya amshi wayar a hannunta ya koma ya zauna yace "Safiyyah" A sanyaye Safiyyah tace "Na'am Ya Jawwad, Please kawata bata da wanda zai tsaya mata akan issue din nan, ba da intention me kyau ya saka aka daura auren ba wallahi, mugu ne azzalumi, har abusing dinta yana yi" Jay dake sauraronta yace "In sha Allah we will try our very best ki taya mu da addu'a" Safiyyah tace "In sha Allah, but how can i be reaching her?" Yace "Don't you have her aunt's number" Safiyyah tace "Sure ina da shi, i will be calling her ta wayar Aunty Farida" Jay yace "Keep this confidential pls Safiyyah" Safiyyah tace "Trust me Ya Jawwad, i now have rest of mind knowing my frnd is safe" Da haka suka yi sallama ya ajiye wayar, Khaleesat ta ajiye plate din abincin hannunta don ta kasa ci, iya spoon uku kawai ta iya yi, tuni Aunty Farida har ta ajiye ma Jay abincin da ta zubo ta nemi waje ta zauna, sai da ta jira suka gama waya da Safiyyah sannan ta kallesa tace "Ina Junaid din ga abincin na zuba maku" Jay yace "Aunty bamu dade da cin abinci ba da gaske" Aunty Farida tace "Ai ko in baku ci ba bazan ji dadi ba, haka jiya ku ka bar min abincin ku ka ki ci, yanxu fa karfe biyu da rabi ake nema kuma breakfast kace kawai ku ka yi" Jay dai murmushi kawai yake, can yace "Toh zan ci Aunty" Tace "To ko kai fa, ina Junaid din kayi masa magana ya shigo ku ci" Jay na shafa kansa yace "Ai shi ya ci snacks a mota bazai ci abincin ba na sani, bai fiye cin abinci da rana ba" Aunty Farida tace "Ikon Allah to saboda me?" Jay yace "Haka yake, iya breakfast da Dinner kawai yake yi" Aunty Farida tace "Iko sai Allah" Jay na kallon abincin da Khaleesat ta rage ya mike ya dauko yace "Zan ci wannan kar mu bata abincin Aunty" Aunty Farida tace "Don Allah ka ajiye ka debi abinci ga plate nan Jawwad" Yace "Aunty wannan fa ya isheni ba iya cinyewa zan yi ba ma" Spoon din ya dauka ya fara cin abincin, Khaleesat dai kallonsa kawai take, Aunty Farida tace "Ai shikenan" Karfe uku da yan mintuna Ajay da Jay suka bar gidan, Jay ne ke driving din idonsa akan titi yace "To ya ku ka yi da Lauyan?" Ajay yace "He said we should meet in kano" Jay ya ɗan kallesa yace "Zuwa gobe kenan?" Ajay yace "Sure, tomorrow in the morning za mu tafi kano" Jay bai sake cewa komai ba har suka isa gida, yau dai traffic din da ɗan sauki, bayan Jay yayi parking ya juya yana kallon Ajay yace "Please since gobe za mu tafi kano ka bar maganar hotel da kace zaka koma" Ajay yace "Ai matar ne ta fiye takura da sa ido" Jay yayi dariya bai dai ce masa komai ba suka sauka zuwa cikin gidan, Ummi na zaune parlon Hadeeyah na kwance kusa da ita da daura kanta a saman cinyar Ummin, ba tare da Ajay ya kalleta ba ya gaisheta a takaice zai wuce sama Hadeeyah ta gaishesa ya amsa yana haura stairs, Jay ya zauna parlon ya gaida Ummi ta amsa tace "Sai yanxu? Ko dai ba Bar beach din ku ka je ba?" Jay ya ɗan buda ido yace "Mun fasa" Yana magana ne yana kallon Hadeeyah da ta hade rai tana danna wayarta kamar bata gansa ba, Ummi ta kalleta tace "Ke baki ga yayanki bane" Hadeeyah na ci gaba da danna wayarta tace "Oh, ok, Good evening" Jay yace "Ya hanya?" Tace "Lafiya lau" Ummi na kallonsa tace "Mami tana sama" Jay ya mike yace "Ohk" Sama ya wuce, Hadeeyah ta bi sa da kallon gefen ido har ya fara hawa stairs, bayan ya tafi Ummi na kallon Hadeeyah tace "Fadan ku ka sake yi kenan?" Hadeeyah ta ɗan yatsine fuska taki cewa komai tana danna wayarta, Ummi ta kyabe baki tace "Kun fi kusa dai" Jay na bude kofar dakin da yasan Maminsa na ciki ya sameta zaune tana waya, ya karasa ya zauna kusa da ita yana kallonta yayi mata side hug ya jinginar da kansa a shoulder dinta a hankali yace "Mami" Mami tayi ma warce suke wayar sallama ta ajiye wayar hannunta tana kallonsa tace "Ina ka je tun safe Son? I was thinking zaka zo airport kayi picking din mu" Jay ya ɗan kalleta yace "Karfe nawa ku ka iso Mami?" Tace "Karfe sha daya da rabi na safe" Jay yace "Mun fita ne da Ajay, Ummi bata gaya maki ba" Mami tace "Kaga da ubansa ne zai sauka Lagos duk abinda yake yi barin sa zai yi ya tafi ya taro sa, amma kai uwarka ta sauka Lagos ya ja ka kun tafi gantali" Jay bai ce mata komai ba, Mami na kallonsa tace "Duk karatun ne yasa ka fada haka? Are you okay?" Jay yace "Stress din tafiyar da nayi zuwa Nigeria ne" Mami tace "Nasan shi zai zugaka ku dawo Nigeria kar ka biyo min ta UK" Jay ya ɗan hade rai yace "Ya fa riga ni dawowa Nigeria Mami, ni ba jiya na dawo ba, shi kuma ai tun last week yake Nigeria" Mami ta tabe baki bata ce komai ba, Jay ya mike ya nufi kofa yace "Zan je inyi wanka" Mami tace "Dama gobe ka shirya mu tafi Bauchi ban san gantalin da yake jan ka ku ke yi a Lagos ba, kai da ko ance ka sauka Lagos baka taba yarda sai gashi saboda Junaid na lagos kai ma ka zauna a lagos, to gobe za mu tafi Bauchi kuma Hadeeyah ma a can zata yi hutu" Jay ya juya ya kalleta yace "Mami ni ban gama abinda nake yi ba, kawai ku yi tafiyar ku" Bai jira me zata ce ba ya fice daga dakin. Wajen karfe biyar da rabi Jay da Ajay suka sauko downstairs, dakin dake kasa suka nufa don Mami na ciki tare da wata bakuwarta warce suka hadu da dadewa a Saudia suna zumunci sun zama kaman en uwa, jin Mami ta shigo Lagos sai matar ta taho gidan gaida Mami tunda ita ma a Lagos din take, Ajay ya zauna kan 1 sitter dake dakin ya gaida Mami sannan ya gaida frnd dinta, Jay ma ya zauna ya gaida kawar Maminsa, matar me suna Hajiya Batula ta amsa da fara'a tana kallonsu sai kuma ta kalli Mami tace "Wanne ne son din naki a ciki Hajiya?" Mami tayi pointing Jay tace "That is my son" Matar na kallon Jay tace "Maa sha Allah, ai kuwa ga kama na gani" Shi dai Ajay danna wayarsa kawai yake bai dago kansa ba, Jay ya mike yace "Mami za mu je Gym ne" Mami ta kallesa tace "Da yamman nan ga uban traffic din Lagos ne zaka je Gym?" Jay yace "Ai ba nisa Gym din" Hajiya Batula tace "Nan Area din ma ai da Gym ba sai sun je da nisa ba" Jay ya kalli Ajay yace "Mu je" Mikewa Ajay yayi ya nufi kofa Jay ya bi bayansa suka fice daga dakin, Hajiya Batula tace "Amma ɗan uwansa ne wannan din ai ko, naga suna yanayi sosai" Mami tace "Eh Cousin dinsa ne" Hajiya Batula tayi kasa da murya tace "Ko dai shi ne ɗan sarkin dai?" Mami ta tabe baki tace "Shi ne" Hajiya Batula tace "Ya sunansa?" Mami tace "Sunansu daya Ahmad amma Junaid ake kiransa" Hajiya Batula tace "Ikon Allah, shi kam Jawwad babu ruwansa..." Cike da takaici Mami tace "Ni babban bakin cikina yanda har yanxu Jawwad bai san ciwon kansa ba, hakan na ci min tuwo a kwarya wallahi, controlling dinsa kawai yake yana bin sa, ko a America din ma Junaid din ne ke juyasa" Hajiya Batula tace "A'a gaskiya bai san ciwon kansa ba naga alama, shi ko kishi baya yi, kuma gaskiya Mai martaba ya nuna son kansa a fili karara nada ɗan sa da yayi Yarima me jiran gado a maimakon Jawwad, ina ce Jawwad din ya girmi ɗan sa?" Mami tace "Ya basa watanni har uku" Hajiya Batula ta rike haɓa tace "Amma in tambayeki mana Fulani, bayan rasuwan mahaifin Jawwad wato me martaba Sarki Ahmadu Yusuf shi brother din nasa wanda shi ne sarkin yanxu bai nemi rikon Jawwad a gabansa ba?" Mami tayi shiru, can tace "Cikin Jawwad na da wata bakwai mahaifinsa me martaba ya rasu aka nada kaninsa wato mahaifin Junaid, dama su uku ne gun babansu Sarki Yusuf Ibrahim, daga Mahaifin Jawwad wanda shi ne babba sai Mahaifin Junaid sannan Maimuna warce nake gidanta yanxu suna kiranta da Ummi...." Hajiya Batula tace "Ikon Allah, to amma...." Shigowar Ummi dakin ne yasa Hajiya Batula tayi saurin canza topic din tace "Yanxu goben za ki koma Bauchi kenan Hajiya?" Mami tace "In sha Allah" Ummi ta ajiye plate din hannunta tace "Sannun ku, gashi nan kaza na tsaya gasa maku" Hajiya Batula na murmushi tace "Allah sarki, sannu da aiki" Ummi tace "Bari in kawo maku drinks din, a can parlor mai aikin ta ajiye" Daga haka ta fita daga dakin, Mami tace "Da ma kin ci gaba da maganar ki, ita ma ai bata so Junaid din da aka nada Yarima me jiran gado ba" Hajiya Batula tace "To ke sai kika zuba ido aka yi hakan Fulani? In uban Jawwad din bai mutu ba a ina kanin nasa zai samu har yayi sarauta? Kuma shine bazai yi kara ya nada ɗan yayansa da ya mutu ya bar masa sarautan Yarima me jiran gado ba sai ya nada ɗan cikin sa?" Mami tayi wani murmushi tace "Ni fa ko a jikina hakan da aka yi, Jawwad is doing fine beside shi mulki ma baya gabansa, as far as my son is okay, i think da a nada sa Yarima da kar a nadasa duk daya..." Hajiya Batula tace "To halan Junaid din kadai sarkin ya haifa?" Mami tace "Wani Junaid? Amaryarsa da suke kira da Aunty na da ɗa me shekara 29, ita in son samu ne ma a nada ɗan ta Yariman ai" Hajiya Batula ta rike haɓa tana kallon Mami. Ajay yayi parking kenan bayan sun dawo gida wajen karfe bakwai na dare ya kalli Jay zai yi magana wayarsa ya fara ring, ya dauka yana duba me kiransa ganin number wani abokinsu ne da kamar bazai yi picking ba kawai sai kuma ya daga ya kai kunne, after few seconds of listening to what the frnd was saying ya zaro ido yace "What???" Kallonsa Jay yayi da sauri don intonation din da yayi using ya nuna ba lafiya ba, Da kyar Ajay ya cire wayar a kunnensa yana kallon Jay dake kallonsa shi ma babu ko kiftawa, Nan da nan Jay yaji hankalinsa ya tashi don babu inda mind dinsa yaje immediately sai gun Khaleesat, Ya fixge wayar hannun Ajay yace "What's happening plss?" Ajay ya kasa cewa komai tsabar yanda ya girgiza, Jay ya shiga call logs din wayar da sauri yaga Adams abokinsu ne ya kira nan yaji hankalinsa ya ɗan kwanta don yasan ba abu bane da ya shafi Khaleesat, dialing number yayi amma har ya gama ring ba a daga ba, a hankali Ajay yace "Salim aka harba" Jay bai san sanda ya ajiye wayar hannunsa ba yace "What? Harbi kuma? Is he dead?" Ajay ya dau wayarsa shi ma ya kara dialing number Adams amma har ya katse bai daga ba, available flight to kano ya fara dubawa immediately..... [6/3, 9:01 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Washegari sai da rana Ajay da Jay suka samu ganin Salem a hospital din da aka yi admitting dinsa, iya kafadarsa ne kadai aka nannada ma bandage alamar a nan aka harbesa amma duk kamanninsa ya canza alamar ya ci duka ba na wasa ba, Jay ya zauna kujeran dake kusa da gadon yana kallon Salem that was in pain yace "Hasbunallah, How did this happen Salem?" Shi dai Ajay na tsaye ya rungume hannu shi ma yana kallon Salem ganin yanda aka canza masa kama, ya ma kasa cewa komai, Salem dake kishingide jikin pillow da kyar don ko iya motsa kafadarsa daya baya yi ga duk jikinsa yayi tsami yayi karfin halin cewa "Ban san su ba suka yi attacking dina" Jay yace "Har gida suka same ka?" Salem ya girgiza kai yace "I stayed out late yesterday in wudil naje gurin wani abokina, he insisted i stay till the next day amma saboda ina da abun da zanyi washegari da safe a kano sai naki kwana a garin muka yi sallama da shi, bayan na kusa unguwan da nake da zama sai na lura da wata mota na biye dani a baya amma ban yi tunanin komai ba na zata ya shigo layin ne bai san hanya ba shine yake bi na ko nima fita zanyi daga unguwan mun fita tare, bayan na shigo layin mu babu kowa saboda dare yayi tun kan ma in sauko daga motata in shiga gida in bude gate sai nake ma motar alama da hannu ya tafi gaba zai samu hanya, sai kawai matukin motar ya fito ya nufo ni, duk da haka ban wani damu ba na zata direction zai tambayeni, na tsaya har ya iso dai dai gabana ban ankara ba kawai sai jin saukan naushi nayi ta ko ina a fuskata ina kokarin defending kai na sai sauran mutane ukun dake cikin motar suka fito su ma suka hau dukana ta ko ina at the same time they were asking me about a girl i know nothing about, wai inyi providing dinta ko su kashe ni" Da wani expression Jay ke kallonsa, sai kuma ya mike da sauri ya dafa gadon da Salem yake kai yace "A girl?" Salem ya gyada kai da kyar yace "Wai Khaleesat, ni ban ma taba jin sunan ba wallahi, suka yi ta dukana wai sai na fadi inda take ko su harbeni" A tare Ajay da Jay suka kalli juna, Salem yace "Kashe ni suka yi niyyar yi banda Allah ya rufa min asiri kururuwan da nake yi wani soja dake kusa da gidanmu ya fito da bindiga, da wani makocina da ya fito da adda, kafin makota na su fito ne suka min harbi har biyu daya ya sameni a kafada daya kuma bai sameni ba ya sami gate, sojan da makoci na suna fitowa suka shige motarsu suka tsere, ni wallahi ban taba jin sunan yarinyar da suka ambata ba ma" Aunties din Salem biyu ne suka shigo ward din da sallama, Ajay ya gaida su sannan ya fita daga ward din ya tafi haraban asibitin ya zauna, after almost 10 mins Jay ma ya fito, inda Ajay ke zaune ya nufa ya zauna bai dai ce masa komai ba, Ajay yayi breaking silence din yace "He is tracking me, ni yake nema ba Salem ba, but tana da number Salem a wayarta ne?" Jay ya sauke wani ajiyar zuciya yace "Yawanci shi take kira ya bani waya if there is anything she wants to tell me, ko number ka ma ai Salem ne ya tura mata, instead cewa zaka yi he is tracking the both of us tunda nima ta kira layina ai ranan, but how did he get Salem's line?" Ajay yayi murmushi yace "Definitely layinta ya sa a duba masa numbers din wa enda take waya da, and he is using that to track us" Jay ya mike yace "We need to take down our sim card AJ, decidedly zai samu information mun shigo kano since we are in his list, sannan i think before anything ya kamata mu fara fighting for her innocent father's release tunda ita Halysaah yanxu bai san inda take ba and she is safe where she is, but the Man needs help" Ajay yace "No, i don't think she is safe with her aunt, although aunt din tace bai san inda ta koma ba amma as far as yana da number wayarta zai iya sakawa ayi tracing din inda take ita ma" Jay ya juya yana kallonsa yayi shiru, he just realize of course hakan zai iya faruwa cause ya daina underrating Abdul yanxu, Jay ya sauke wani ajiyar zuciya yace "That guy is something else Ajay, duk wata salon mugunta ya sani adding it to his career skills, ina jin kawai a duba mana if there is flight zuwa Niger republic a biya masu kawai su tafi can da aunt dinta har zuwa sanda za mu gama da Case din dad dinta, in the other hand shi kuma mun yi sue dinsa requesting for divorce for her" Ajay yayi shiru, can yace "But what if she is needed in court?" Jay yace "For now her lawyer will represent her, in ma an bukace ta a court we will sort that out" Jay yace "I think that's cool, amma ya kamata mu je gidan su gun mahaifiyarta" Ajay dai kallonsa kawai yake, can yace "Is that necessary?" Jay yace "Of course, kasan aunt dinta tace mana the mother is not medically fit, kada wannan damuwar yayi weighing dinta down" Ajay yace "Sai mu je a matsayin su wa?" jay ya mike yace "Human right" Abdul na tsaye rike da takardan da mahaifiyar sa ta mika masa daga shigowar sa parlor idonsa na kan takardar yana karanta content din jiki, Meema yayarsa ma na zaune parlon tana kallonsa fuskarta dauke da bacin rai karara, wani murmushi Abdul yayi ya cukuikuye takardar ya jefar kan kujera, Mahaifiyar sa dake ta kallonsa ta tabe baki tace "To yanxu menene amfanin wannan tozarcin da kaskantar da kai da ake yi? Sam kace kai baza ka ji maganata ka dau shawara ta ba Abdallah?" Meema ta katse ta tana kallonta a fusace tace "Haba Momy ta yaya kike son ya ji maganarki bayan uban kudin da ya kashe ma tsinanniyar shegiyar yarinyar? Ai jin maganar ki ba nasa bane wallahi, kuma don an kawo masa sammaci ba shi ke nufin ya hakura zai saketa ba, kotu ce kawai za a shiga ayi ta gwabzawa, kuma in sha Allahu duk inda kafafuwana za su shiga sai na shigar da su don Abdallah yayi nasara a wannan case din, bazan taɓa bari a tozarta min kanina ba ga mari ga tsinka jaka bazai taɓa yiwuwa ba wallahi, alamar koma waye ya zugata ta yarda aka yi karansa zai iya biyan ko nawa aka ce ya biya a kotu, kai jama'a amma yarinyar nan anyi babbar er iska butulu, dama ni tun asali ban goyi bayan da yace zai kai yarinyar nan Amurka ba ina jiye masa tsoron kar idonta ya bude, to gashi nan bayan karatun har da karuwanci ta dinga yi da manyan kasar nan tunda gashi har ta samu wanda zai tsaya mata da lauya ya biya makudan kudin da aka kashe mata kilan yace har da miliyan 100 da ubanta ya salwantar, abun arziki dai bai amshe mu ba a family din nan, ban ga laifin ki da baki son talakawa ba Momy, shi yasa nima bana son su na tsane su" Momy dai girgiza kafa kawai take tsabar takaici da bakin ciki ta kasa cewa komai, Meema ta kalli Abdul daka safa da marwa a parlon yana ɗan murmushi tace "Ka kwantar da hankalin ka Abdul, as far as ina numfashi kuma uwar mu na numfashi ko don ka rama duk abinda yarinyar nan tayi maka za mu shiga mu fita har sai kotu ta baka ita, in sun san wata ai basu san wata ba, koma waye ke taka mata baya daga karshe kashe kudadensa kawai zai yi a banza don sai ta shigo gidan nan mun ci ubanta da izinin Allah, banda kaddara me ma zaka yi da er gagurumin barawo kuma makaryaci, daga basa dukiya ya kai Lagos yace an kwace mota" Sama Abdul ya wuce kamar zai tashi sama, Momy ta bi sa da kallo cikin bacin rai tace "Kai Allah Ubangiji ya tsine ma mutanen nan albarka, yanda suka sa ɗa na a damuwa Allah ya saka duk zuri'arsu a damuwa, ita kuma yarinya Allah ya kasheta ma duk mu huta, tun da lamarin nan ya faru ko abincin kirki Abdallah yaki ya zauna ya ci a gidan nan, in ya fita tun safe sai dare muke ganinsa gaba daya ba shi da sukuni akan er talakawa, wannan wani irin iftila'i ne ya same mu" Meema tace "Tashi tsaye kawai za mu yi ayi abinda ya kamata Momy, gidan nan ai kamar ta shigo sa ne in sha Allahu, da bakinta zata ce ita ta hakura a kai ta gidan mijinta kawai, kuma ta shigo nan ta same mu muna jiranta" Daga haka Meema ta mike ta bi bayan Abdallah. Jay na zaune tare da Ajay a office din lauyansu suna sauraron sa, lauyan yace "He is trying to re-litigate a case already resolved in court, don an riga an rufe case din a kotu tunda yace ya yafe, har lauyoyinsa sun yi filing notice of discontinuance kuma kotu tayi approving sannan ta kulle case din ta yi releasing debtor dinsu from any further liability, but like seriously ban san wani irin lauya bane ɗan sa, don har da written confirmation of debt forgiveness da suka yi a kotu duk yana nan, why let them arrest the man again? Ko dai ɗan nasa bai gaya masa consequences din hakan da yayi bane cause this is pure abuse of process and malicious prosecution" Jay yace "To yanxu meye abun yi Barrister?" Lawyern ya ajiye pen din hannunsa yace "Za mu yi Filing motion to dismiss the already forgiven case, and we will plead abuse of process, sannan muyi Raising estopped from pursuing the debt again in near future, just that za mu yi presenting documentation of the original debt forgiveness and court records to the court, wannan ma ai sun yi breaching court order ne kuma hakan laifi ne me zaman kansa" Ajay yace "That is because suna ganin ba shi da wanda zai tsaya masa ko shekara nawa zai yi a kulle, his family have no voice to do so, that was why the breached the court order for their selfish interest" Lauyan yace "Babu matsala in sha Allah za mu shigar da kara kotu, and the man will be bailed out while the case is going on, they will even have to pay him damages...." Bayan la'asar Ajay yayi parking a kofar gidansu Khaleesat, dai dai inda yayi parking ranan da suka yi dropping dinta da daddare, a bayansu kuma wata mota ce ita ma tayi parking, Guard uku ne suka fito daga cikin motar dukkansu suka yi tsaye jikin motar da suka sauka, shi dai Jay kallon unguwan kawai yake, Ajay ya bude mota ya sauka, ya jingina da motar ya rungume hannunsa, Jay ma ya sauko sannan ya zagayo inda Ajay yake tsaye yace "Where is the house?" Ba tare da Ajay ya kallesa ba yace "Gashi nan kana kallo" Jay ya kalli gidan dake opposite dinsu, wani almajiri ne ya zo wucewa Ajay ya kirasa, yaron ya taho da sauri Ajay yace "Shiga cikin gidan can kace ana sallama da Maman...." Sai kuma ya kalli Jay alamar ya fadi sunan, Jay na kallon almajirin yace "Kace ana sallama da Maman Halysaah" Almajirin yace "Toh" Da sauri ya nufi gidan, Ajay yace "Meye kuma Halysaah? How is that even a name? In zaka kira sunanta na asali kawai ka kira" Jay na kallonsa yace "Meye sunan nata na asali?" Ajay bai kallesa ba har sannan yace "Ka fi ni sani ai, tunda ka fi kusa da ita" Jay ya ɗan yi murmushi bai sake ce masa komai ba, Nenne ce ta leko kofar gidan tana zazzare ido kuma bata yarda ta fito waje ba, tana yin ido hudu da su Jay sannan ga wasu samudawa da ta gani har uku tsaye jikin wata motar ta juya ta koma cikin gidan da sauri har tana tuntube, sai ga Mama Zubaida tana gyara gyalenta da ta yafa akan daurin kirjin da tayi, Mama Shatu na bayanta tana kokarin saka hijabinta ta bai bai, tsaye duk suka yi daga cikin gidan suna leko su Ajay da samudawan dake jikin mota a tsaye, Mama Shatu tayi karfin halin cewa "Ina wuninku?" Jay ne ya karasa har inda suke tsaye, shi dai Ajay na rungume da hannunsa yana kallon ikon Allah, Jay ya gaishesu duk suka amsa kamar munafukai suna gwale ido, Jay yayi kasa da kai yace "Mahaifiyar Halysaah mu ke son gani" Da sauri Mama Zubaida tace "A'a to ku shigo mana, Bismillan ku ai tana ciki, fakewa kawai suka yi da cewar bazata iya fitowa ba bata da lafiya, lafiyarta lauz ku shiga har dakin ku sameta" Duk tunaninsu an zo tafiya da Umma ne kamar yanda aka zo aka tafi da Malam Ali, Jay ya juya ya kalli Ajay dake jin duk conversation din su daga inda yake tsaye, ko ba a gaya masa ba yasan stepmom din Khaleesat ne matan, ya kulle motarsa yana kallon wa enda ke tsaye jikin mota yayi masu alamar da cewar za su fito in 5 mins sannan ya karasa har inda Jay ke tsaye yana jiransa su shiga gidan, su Mama Zubaida kuwa har sun koma tsakar gidan sun tsaya cirko cirko suna jiran su ga yanda za a shigo a fitar da Umma, da hannu suka nuna ma Jay da Ajay hanyar dakin Umma, Jay ne yayi sallama bakin kofar dakin, shi dai Ajay na tsaye a gefe yana kallon white t-shirt dinsa to be sure ruwan taɓon da yayi gaja gaja a compound din bai fallatsar masa a jiki ba, Mama Shatu da Mama Zubaida a tsakar compound din suke zubar da duk wani ruwan da suka yi aiki haka ma yaransu, sun maida compound din kamar na mahaukata, gashi simintin da aka masa duk ya dagargaje ya kusa komawa kasa, shi yasa in suka zubar da ruwa sai ya cabe, kudaje sai safa da marwa suke ta ko ina, ga kwanuka gaja gaja, igiyoyin gidan kuwa duk an rataye kaya, Ajay na ganin Jay ya shiga dakin Umma shi ma ya shiga ciki da sallama, dukawa Jay yayi daga bakin kofar ya gaida Umma da Maman Salame dake dakin, Ajay ma yayi hakan ya gaishe su, ganin haka Maman Salame ta tashi da sauri ta shimfida masu darduma a kan ledan dakin tana masu sannu da zuwa, duk tunaninta ita ma zuwa aka yi za a tafi da Umma amma sai bata ga alamar hakan a tattare da su ba duba da yanda suka yi gaisuwa cikin girmamawa, Jay ne kawai ya zauna kan darduman Ajay kuwa ya kasa zama ga wani zafi da yake ji a duk jikinsa, ya ciro handkerchief dinsa yana goge zufan goshinsa, Mama Salame ta dau mafici ta mika masa, ya ɗan yi murmushi ya amsa yace "Nagode" Mama Salame ta dage labulen dakin tana cewa "Yau mun fi sati biyu basu kawo wutan ba, ance tiranspoma tayi bindiga" Nenne dake makale kofar bandaki rike da buta ta dinga leka dakin Umma bayan Maman Salame ta daga labulen, haka su Mama Zubaida da suka ji shiru ba a taso keyar Umma an fito da ita ba, Jay na kallon Umma dake zaune don ko ba a gaya masa ba yasan ita ce mahaifiyar Khaleesat duba da kalan fatarta sannan babu ta inda Khaleesat ta bar ta, ba karamin kama Khaleesat ke yi da mahaifiyarta ba a nan ta samo asalin kyanta, Yayi kasa da murya yace "Ya jikin Umma?" Cikin sanyin murya Umma tace "Alhamdulillah da sauki" Ajay ma yayi mata ya jiki ta amsa tana kallonsu gaba daya don jira kawai take taji me ke tafe da su, in ma cewa za su yi tafiya suka zo yi da ita dama a shirye take tunda hijab dinta na jikinta, shiru ne ya biyo baya a dakin, don Jay bai san ta inda zai fara introducing kansa ba ma, haka ma Ajay da yayi shiru zafi na neman hallaka sa, after few seconds Ajay yayi karfin halin breaking silence din a hankali yace "Makaranta daya mu ke tare da Jidderh a can America, so kawarta ta sanar mana abinda ke faruwa shi ne muka nemi ta bamu address mu zo nan duba ki" Sosai hankalin Mama Salame ya kwanta jin abinda Ajay yace, Mama Salame tace "Allah yayi maku albarka, kuma mun ji dadi mun kuma gode da zuwan da ku ka yi" Jay ya kwantar da murya yace "Kiyi hakuri Umma kuma ki kwantar da hankalinki, muna tabbatar maki in sha Allah komai zai wuce nan ba da dadewa ba, don za ayi duk abinda ya kamata, mahaifinta ma in sha Allahu za mu yi abinda ya dace a sakesa a yan kwanakin nan, ita kanta Halysaah zata dawo gida in sha Allah" Maman Salame ta daga hannu sama cike da farin ciki tace "Alhamdulillah ya Allah, gaskiya mun ji dadin jin hakan daga gare ku, don bamu da wanda zai tsaya mana sai Allah, Alhamdulillah" Ita dai Umma kanta na kasa hawaye na zuba idonta, Ajay yace "Zuwa gobe da safe in sha Allah za mu shigo" Mama Salame tace "To Allah Ubangiji ya kai mu goben lafiya, mun gode, mun gode" Mikewa Ajay yayi ya kara yi ma Umma sallama sannan ya fita daga dakin kar yayi suffocate, heat wan finish prince, don in akwai abinda baya shiri da shine zafi, baya son zafi ko yaya yake, Nenne na ganin Ajay ya fito daga dakin Umma ta sake komawa cikin bandaki da sauri, su Mama Zubaida da Mama Shatu suka bi sa da kallo har ya fita daga compound din, to su waye wannan kuma su da suka baza ido da kunne su ga an fito da Umma tana kuka, bayan fitar Ajay da few minutes sai ga almajirai suna shigowa gidan da buhun shinkafa biyu, carton din taliya biyu, carton din indomie biyu, manyan gallon na manja da mangyada, da carton din maggi duk kuma aka dinga dire su a kofar dakin Umma, daga Nenne har su Mama Zubaida haka suka saki baki suna kallon ikon Allah, Maman Salame ta taso zuwa bakin kofa tana kallon kayan abincin da mamaki tace "Ikon Allah, har da uban hidima haka??" Jay ya ajiye ma Umma 100k yace "Gashi Umma ayi cefane da wannan, in sha Allah gobe za mu shigo da izinin Allah" Bai jira cewar Umma that was speechless and shock ba ga hawayen dake sauka idonta kawai ya fita daga dakin..... [6/6, 5:08 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Jay na fitowa dakin Umma, Nenne dake tsaye tsakar gida bayan ta fahimci ba yan sanda bane ta rushe da matsanancin kuka ta nemi er kujera ta zauna tana kallonsa tace "Da wannan uban kudaden da ku ka kashe na siyo kayayyakin abincin nan ai da belin ɗa na ku ka yi, wallahi maraya ne ba shi da kowa, in ba wani ikon Allah ba sai dai ya rube a can, wancan karan ni kadai nasan wahalan da na sha na ganin an sako sa, babu inda kafata bata shiga ba wallahi, na dinga bi gida gida ina neman taimakon kudi" Jay ya kwantar da murya yace "In sha Allah za mu yi bakin kokarin mu na ganin an sako sa kaka, ki kwantar da hankalin ki" Nenne na matsar kwalla da gefen haɓar zaninta tace "Ɗan nan ina hankalina zai kwanta ɗa na na can furson? In dai daga gidan radio da talabijin ku ke ni dai na amince ku zo ku dau muryata da fuskata in nemi taimakon al'ummar musulmai ku watsa ni duniya ta gan ni ina jawabi, kilan gwamna ma in ya gani yaji tausayina ya saka baki a sakar min ɗa na" Jay yace "Ba sai anyi haka ba Kaka, ina tabbatar maki nan ba da dadewa ba zai dawo gida in sha Allah" Nenne tace "To daga ina ku ke? Ko dai kungiyar kare haƙƙin en Adam ne" Jay ya ɗan yi shiru, Mama Zubaida da Mama Shatu dai sun yi cirko cirko a tsakar gida suna gwale ido suna kallon Jay, Jay yace "Makarantar mu daya da Halysaah a can Amurka, shi ne muka samu labarin abinda ya faru mu ka zo" Nenne ta mike da sauri tace "To ai yau kusan sati daya kenan ana neman ta ko sama ko kasa, wallahi bamu san inda take ba, ita uwar ta na daki tana jimamin ta, ni kuma ina nan ina jimamin ɗa na, haka muka raba abun, amma tun da yarinyar nan ta samu labarin daurin aurenta da annoban nan Awdul ta shiga duniya, wallahi bakina da nata tace min bata son sa bazata iya auren sa ba, tun da uwata ta haifeni ban taɓa ganin inda ake auren dole ba" Nenne na kai wa nan ta fasa sabon kuka, Jay dai ya ma rasa abinda zai ce mata, beside baya ma son yayi magana gaban su Mama Zubaida da suka wangale kunnuwa suna saurare, kawai ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu ashirin din da yayi saura, yaje har gaban Nenne ya mika mata da ladabi yace "Ga wannan Kaka, in sha Allah za mu shigo gobe" Nenne ta daga hannu da sauri tace "A'a, gwara ku hada kawai ku kai furson a sako min ɗa na, don yafi min ko wani kudi a duniya" Jay yayi murmushi yace "Ki amsa kaka, na maki alkawarin za a sako sa nan ba da dadewa ba in sha Allah" Nenne ta amshi kudin da hannu bibbiyu tana sa masa albarka cikin rawan murya tace "In ma Allah ya sa kun zo gobe ba ku sameni a nan ba ku sa a raka ku gidana babu nisa daga nan" Yana murmushi yace "In sha Allah Kaka" Daga haka yayi mata sallama sannan ya fita daga gidan su Mama Zubaida suka bi sa da kallo babu fara'a ko wacce da abinda ke yawo a ranta, Nenne ta kulle kudin a habar zaninta ta soke tace "Dama gobe da asuban fari zan je gun Malam Na ta'ala, Allah ya sa in samu kwale kwalen da zai tsallakar da ni da sassafe" Dakin Umma ta nufa tace "To ke Salame kike ko wa? Ki fito mana ki shigar mata da dukiyar nan dake bakin kofa kar a faki ido a sungume mata wani abun, kayan abinci ai dukiya ce me zaman kanta a yanxu, Allah kadai yasan dubu dari nawa suka kashe wajen siyo kayan abincin nan...." Maman Salame ta fito daga dakin Umma ta fara shigar da kayan abincin ciki, Mama Shatu ta shige dakinta fuska a murtuke, Mama Zubaida ma ta tabe baki ta shige nata dakin ta sako tsumman labulenta dake rataye da kyauren dakin. Jay na fita waje ya tarar da Ajay cikin mota yana zaune a kujera me zaman banza ya kwantar da seat din kujeran idonsa a lumshe, Jay ya bude driver seat ya shiga yana kallon Ajay jin yanda ya kure AC din motar gaba daya, Ajay ya gyara zamansa yana kallonsa, Jay dai yayi murmushi ya fara driving motar Ajay ya nuna masa hanyar da suka bi suka fita ranan da yayi dropping Khaleesat, motar dake bayan su ma ya bi su, Ajay sai sake kare ma unguwan kallo yake with distress har suka isa main road, bayan sun hau saman titi ya kalli Jay yace "In za a samu gida ko na 30M zuwa 50M ne a siya pls su bar wannan vicinity din" Jay yace "I think that will be okay idan anyi releasing mai gidan but not now" Ajay yace "Duk daya ne Bruh, plss kayi ma Salisu magana a fara duba gidan daga yau zuwa gobe, that house isn't healthy for a living thing, ta yaya me rai zai dinga rayuwa a gida irin wannan? This is so pathetic, or am i exaggerating pls?" Jay yace "But haka kawai baza mu yanke decision without the release of the head of the House ba, so kake mu kara triggering saurayin nata bayan har yanxu ba mu yi achieving ko abu daya ba, we are following everything step by step Ajay, we will reach der in sha Allah" Ajay bai sake cewa komai ba, amma da gaske hankalin sa ya tashi kwarai ganin condition din cikin gidan most especially the compound, in ba dole ba shi kam babu abinda zai sake kai sa gidan nan, it's not about the house structure or where it's located but the hygiene of the house, sai kace cikin prison, ji yake kamar har ya kamu da cholera don har wani zazzabi zazzabi ya fara ji, ya kai hannu ya rage Ac din motar, shi dai Jay driving dinsa kawai yake. Washegari da yamma haka nan suka sake komawa gidan bayan Lauyan su yayi requesting su tambayi matan Malam Ali ko da akwai wani written debt forgiveness document kuma original one din da kotu ta bashi bayan masu karansa sun janye karar, cause in dai babu takardun to sai dai ayi case din biyan bashin da yake bin Alhaji Musa amma ba dai su yi karan sa ba, Bayan Ajay yayi parking ya juya yana kallon Jay yace "Zan jira ka" Er dariya Jay yayi yace "Toh ai da baka biyo ni ba kayi zaman ka a gida kawai" Bai jira cewar Ajay ba ya sauka daga cikin motar ya nufi cikin gidan, yau ma dai kamar jiya ba su kadai suka zo unguwan ba don securities da suka biyo su har sun fi na jiya tunda basu san ko Abdul na da Spy a unguwan ba, infact bazai ma rasa ba, definitely za a basa labarin wasu sun zo gidan su Khaleesat jiya, so they are not loosing guard by any means, and they are never going to let him take them unaware, A takaice Jay ya gaida Kishiyoyin Umma dake zaune tsakar gidan sun yi rashe rashe da su, yau ko murhu basu kunna ba don dawowar su kenan daga wajen Malamai, tun asuban fari suka bar gida sai yanxu suke dawowa, duk suka bi Jay da kallo, Jay dai yana tafe yana kallon Islam da Noor dake ma Umma wanke wanke a tsakar gidan don ko ba a gaya masa ba yasan siblings din Khaleesat ne duba da pheomelanin din su, a tare suka gaishesa ya sakar masu murmushi yace "How are you?" Murmushin kawai suka yi basu ce masa komai ba Islam na wanke wanke Noor na mata dauraya, Jay ya isa har kofar dakin Umma yayi sallama, Umma da ta gama gyara dakinta kenan ta saka turaren wuta na tsinke ta amsa sallaman sa, a kullum in zaka shigo dakin Umma a haka zaka tarar da shi fes fes, duk da ba komai bane a dakinta don ta siyar da komai nata amma kullum a gyara zaka same dakin da turaren tsinke, Jay ya shiga dakin Umma na kallonsa tace "Sannu da zuwa" Tabarma ta dauko ta shimfida masa don bata yi tunanin zai dawo yau kamar yanda yace mata jiya ba, Jay ya zauna yana murmushi ya gaisheta, Umma ta zauna kan dardumanta ta amsa gaisuwar sa, har a sannan zaka ga damuwar dake tare da ita alamar karfin hali kawai take, sai kuma ta mike tace "Bari in kawo maka ruwa" Ruwa ta debo masa a cup din stainless ta karaso ta ajiye masa a gabansa sannan ta koma ta zauna, yace "Nagode Umma" Ɗan murmushi kawai tayi, Mama Zubaida da Mama Shatu suka yi tsit a tsakar gida ko wacce ta kasa kunne ko zata ji abinda ake cewa a dakin Umma, Ajay ne ya shigo gidan duk suka zuba masa na mujiya, sau daya ya kallesu ya dauke kai ya nufi dakin Umma, yau dai tsakar gidan a bushe yake bai yi gaja gaja da ruwa ba da yake basu yi girkin siyarwa ba, Islam na tsaye bakin kofar dakin Umma bayan ta shiga da kayan wanke wanken da suka yi da twin sis dinta, Ita kuma Noor na share inda suka yi wanke wanke, Idan Ajay ya kalli Noor sai ya kalli Islam, ya amsa gaisuwar da Noor ke masa tana rike da tsintsiya, yana isa bakin kofar dakin Umma ya ja dogon hancin Islam don ita ce ke mugun kama da Khaleesat har bakinsu iri daya ne, murmushi tayi tana kallonsa yace "How are you?" Ta sauke idonta bata ce komai ba yanda dai Khaleesat ke yi, da sallama ya shiga dakin Umma, Jay ya daga kai yana kallonsu don bai yi tunanin zai shigo ba, Umma ta amsa sallamansa, ya zauna daga gefen Jay sannan ya gaisheta, Umma ta amsa da murmushin karfin hali tana masa sannu da zuwa, after some seconds Jay ya fara magana a hankali yace "Umma akwai wasu takardu na yarjejeniyar kotu na yafiyan bashin da aka yi ma Mai gidan nan, Allah yasa kun san in da takardun suke ana bukatarsu ne" Umma tayi shiru, can tace "To, amma wallahi ban sani ba sai dai ko a duba dakinsa ko suna nan" Jay yace "Eh a duba Umma, Allah ya sa a gani" Umma tace "Ameen" Mikewa Umma tayi ta fita daga dakin, Mama Zubaida da Mama Shatu suka bi ta da kallo har ta shiga dakin Malam Ali, after almost 8 mins sai ga Umma ta fito da wasu takardu wanda bata san ko na menene ba dai zata kai masu su duba ko akwai wanda ake nema a ciki, a haka ta wuce Kishiyoyinta da idanuwansa duk ke kanta, ta koma dakinta ta mika ma Jay takardun sannan ta koma kan dardumanta ta zauna, Jay ya dinga duba takardun daya bayan daya, yaga har da takardun makarantar Malam Ali, ashe har Degree garesa a Agriculture, kafin nan kuma sai da yayi diploma, yana ta dai duba tulin takardun har daga karshe yaga wasu takardun da yake saka rai na yarjejeniyar yafiyar da aka yi ma Malam Ali a kotu na biyan bashin Mahaifin Abdul ne, ya mika ma Ajay shi ma ya amsa yana duba takardun, Jay ya kalli Umma yace "Ina jin wannan ne takardun da muke nema" Umma tace "To Alhamdulillah" Jay yace "To za mu koma, duk yanda ake ciki za mu dawo in sha Allah" A hankali Umma tace "To Allah ya saka da alkhairi, amma sai dai akwai wata uwar dakina da bata ji ba bata gani ba yan sanda suka tafi da ita shekaranjiya har yanxu ba a ma san wani caji ofis din aka kai ta ba" Ajay dake kallonta yace "Ko Baabar nan ta Hotoro?" Cike da karfin hali Umma tace "Ita, wallahi bata ji ba bata gani ba aka je aka tafi da ita" Ajay yayi shiru yana kara mamakin stupidity din Abdul, he don't think that guy is okay in anyway, after some seconds ya kalli Umma a hankali yace "Za mu bincika inda aka kai ta mu yi bailing dinta in sha Allah" Umma ta share hawayen da ya kawo idonta ta kasa cewa komai, Jay yace "Ki kwantar da hankalin ki Umma, in sha Allah komai zai wuce da izinin Allah" Cikin rawan murya Umma tace "Allah ya sa" Jay ya kalli Ajay, tsabar tausayin Umma kawai yaga gwara su gaya mata gaskiyar inda Khaleesat take ko zata ɗan samu sukuni a ranta, Jay ya sauke idonsa a hankali yace "Sannan Umma akwai maganar da zan gaya maki yanxu, amma don Allah kar ki gaya ma kowa har zuwa sanda za mu gama abinda muke" Ajay ya juya ya wani kallesa don har ya gano maganar da Jay zai gaya ma Umma, Umma na share idonta tace "To in sha Allah" a hankali Jay yace "Halysaah na Lagos, amma don Allah ba ma son kowa yasan hakan Umma, ko makusantan ki kar ki gaya ma tukun....." Umma da zuciyarta ke bugawa tace "Lagos kuma? Wajen wa a Lagos?" Jay yace "Tana wajen sister din ki ne, amma mun ce mata kar ta nuna maki tana wajenta har sai sanda komai ya dai daita, shi yasa ma har yanxu bata gaya maki ba" Umma tayi shiru, amma fa ji tayi wani nutsuwa ya zo mata, lkci daya kuma taji hankalinta ya kwanta kamar an yaye mata kashi saba'in na damuwar da take ciki, Umma tace "In sha Allahu babu wanda zai ji hakan daga gare ni, yanda ku ka tsaya mana ku ma Allah Ubangiji ya tsaya maku haka, Allah ya saka maku da alkhairi..." Umma ta kasa ci gaba hawaye masu zafi na sauka idonta, A haka Ajay da Jay suka fita daga dakin Umma za su koma Office din lauya din su da takardun hoping shi ne kotu zata bukata, yau ma dai Ajay ji yayi kamar zafi zai kashesa a dakin Umma amma haka ya dinga daurewa har suka fita daga dakin sannan ya ciro handkerchief dinsa yana goge zufan da yayi, ya kalli Islam dake zaune bakin kofar dakin Umma da takardan makaranta a hannunta alamar karatu take, Noor kuma na hura gawayi a can gefe, ya saka hannu a aljihu ya ciro kudaden da bai san ko nawa bane ya mika ma Islam yana kallonta yace "Ku raba ke da er uwarki" Islam taki amsan kudin, ya hade rai yace "C'mon collect it" Jay dake kallonta shi ma ya sakar mata murmushi yace "Karba mana cutie" Islam ta kalli Noor amma still taki amsan kudin, Ajay ya zare mata ido yace "Kee, amsa nace" A hankali ta kai hannu ta amshi kudin, Ajay da Jay suka fita daga compound din, Kishiyoyin Umma suka dinga kallon uban kudin da aka ba Islam kamar idanuwansu za su fito ko kiftawan kirki basa yi, Islam ta tashi ta shiga dakin Umma da kudin a hannunta, Mama Zubaida ta mike ta ma Mama Shatu alamar su shiga daki, duk suka shiga dakin Mama Shatu sannan suka sake labule, Mama Zubaida ta rike haba tace "Anya kuwa Shatu baza mu san yanda za mu yi Abdul ya samu labarin abinda ke faruwa a gidan nan ba? Ni wallahi ban yarda wa ennan samarin basu san inda Khaleesat take ba, kina fa ganinsu kin ga 'ya yan masu kudi, dubi suturan da suka sa wa, ji motocinsu, sannan kalli fatarsu kalan ta yan hutu, in fa muka yi sake Shatu bakin ciki ne zai kashe mu a gidan nan muna ji muna gani" Mama Shatu tace "Ke ma dai wallahi kin fiye gaggawa, sai kace kin manta me Malamin yace mana, duka duka ba yau muka kai masa kudin ba, to mu zuba ido ya fara aiki mana tukun" Mama Zubaida tace "Duk da haka dai gwara mu ma mu dinga yin namu ta bayan fage Shatu, kada mu sakankance mu bar malami da aiki shi kadai, ya kamata tun wuri mu san yanda za mu yi mu ankarar da Abdul abinda ke faruwa a gidan nan, don gaskiya na sha jinin jikina da wa ennan zaratan samarin, ke ki ga tulin kudin da suka ba Islam, sannan kalli uban kayan abincin da suka jibge jiya daga karshe don walakanci aka biyo mu da kwano uku uku da taliya bibbiyu da man gyada da manja, sai maggi leda bibbiyu ga mayunwata, ke kiji wai yau Zahra'u ce da tsam mana kayan abincin da aka jibge mata, bayan haka Allah kadai yasan nawa suka bata a daki tunda ba gaya mana zata yi ba, ga Nenne ma a gaban mu aka bata rafar kudi yan dubu dubu, anya bamu shiga uku ba Shatu? Ni fa jikina yayi sanyi hankalina ya tashi, meye hadin su da Khaleesat din da har suke wannan hidima haka a kanta, mu ga 'ya yanmu a zube har yau babu mataya sai talla suke, ni fa wallahi ko tsirara zan yi yawo gwara inyi da dai Zahra'u da zuri'arta su ji dadi a duniya" Mama Shatu tace "Yanxu dai Gwaska za mu samu ya raka mu gidan su Abdul din tunda yace yasan gidan uban sa, nasan Abdul din zai taka ma yan iskan burki har ma ya bamu makudan kudi fallasa asirin abinda ke faruwa da mu ka yi" Mama Zubaida tace "Atoh dai tun wuri my gaya masa abinda ke faruwa, zuba ido ba namu bane wallahi, amma sai dai jibi kenan za mu je gidansu Abdul din don Gwaska ya tafi dambatta daxu uwarsa ke gaya min yaje kai kaya can" Mama Shatu tace "Ai jibin kamar gobe ne, kin ga gobe dama mu gama girkin mu da wuri mu tafi inda wannan matar ta mana kwatance daxu a gidan Malam" The next day wajen karfe biyar da rabi na yamma Sha'awa tayi sallama bakin kofar dakin Umma dake yi ma yan biyun ta gyaran gashi, babu kowa gidan don duk yan matan gidan basu dawo talla ba, kananun yaran kuma sun tafi gantali, tun Sha'awa bata shigo dakin Umma ba take cewa "Umma yanxu Ladingo ke sanar min an sako Gaje, wai daxu taje unguwan taga ana ta shiga gidan yi mata jaje" Umma ta sake gashin Noor ta mike da sauri tace "Da gaske Sha'awa?" Sha'awa tace "Wallahi kuwa Ladingo bazata min karya ba Umma, tace Gaje dai ta dawo gida ga yan unguwa na ta tururuwan shiga yi mata jaje tun daxu" Umma ta jawo Hijab dinta tace "To bari in je gidan Allah ya sa da gaske ne dai" Sha'awa tace "Da ina da kudin mota ai da mun je tare Umma, kusan kwanan ta biyar fa a kulle, don ma akwai kanwarta da zata kula da jikokinta tunda uwarsu na can Libiya ta tafi aikatau, ubansu kuma yayi watsi da su, banda haka da yaya makomar jikokin nan nata fisabilillahi?" Umma bata tanka ta ba ta gama saka hijab dinta ta daura nikab ta dau purse zata fita, Noor da Islam suka marairaice wai za su bi ta, ganin in ta tafi su kadai zata bari a gida yasa tace su saka hijab gaba daya, haka nan duk suka saka Hijab suka fita daga dakin Umma na biye da su, kusan kullum sai Umma taje gidan Gaje sau biyu ta duba ko ta dawo amma sai taga akasin haka sai dai ta samu kanwarta Iya a gidan, jiki a sanyaye take juyawa ta koma gida don Iya na ganinta take fara masifar ita ta saka er uwarta a uku, Umma zata fita gidan tare da yan biyunta sai ga su Mama Shatu da Mama Zubaida sun shigo wujiga wujiga da su, kana ganin fuskokinsu kasan a gajiye suke likis, ga wuyan hijabinsu duk yayi jagab da zufa, kafafuwarsu kuwa kamar wa enda suka dawo daga gona, Umma dai tayi masu sannu da zuwa kawai ta fita daga gidan su Islam na biye da ita, ai ko tana isa gidan Gaje taga da gaske an sako Gaje, Gaje na ganin Umma tayi kamar bata taɓa saninta ba a duniya, yanda take amsa gaisuwa da jajen masu shigo mata haka ta amsa ma Umma kamar ranan ta fara ganinta, ita dai Umma na zaune tayi shiru ta ma rasa me zata ce, su Islam na zaune gefenta, Gaje bata sake kallon direction dinta da yaranta ba, duk wanda ya shigo haka take sanar masa yanda Maman Fu'ad ta ci amanarta tace ma yan sanda ita bata taɓa ganinta ba ma balle wata Khaleesat, In tayi bayanin sai ta rushe da kuka tace "Ban taɓa tunanin Sadiyah zata min butulci haka ba duk alakar da ke tsakanin mu wai bata taɓa gani ba, kaji tsoron Allah kaji tsoron mutumin yau kawai, duk kyautata ma yarinyar nan da nake amma ta barni ni kadai raina a cikin matsalar da na tsoma kaina" Ita dai Umma tayi tagumi tana sauraron duk abinda Gaje ke cewa. [6/9, 7:26 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Sai bayan da aka yi sallan Magrib Umma ta bar gidan Baaba Gaje da yan biyun ta, kuma har ta bar gidan Gaje bata nuna ta taɓa saninta ba don casually ma take amsa mata kamar yanda take ma kowa da ya shigo mata jaje, Umma dai a sanyaye ta baro gidan, tana isa gida taga mutane tsattsaye a kofar gida kowa da abinda ke fitowa bakinsa, sosai taji gabanta ya fadi gashi ta kasa fahimtar akan me ake ta surutu haka, can dai ta dubi wata makociyarsu dake tsaye wajen tace "Munnira me ke faruwa?" Munnira tace "Wallahi Umman su Khaleesah nima fitowa ta kenan da naji hayaniyar tayi yawa, amma wai kamar wasu mutane ne da ba a san ko su waye ba suka shiga gidan naku suka yi aika aika, ance a katuwar mota suka zo...." Umma ta kasa cewa komai tana kallonta, da kyar take jan kafa tana rike da su Islam ta shiga gidan har sannan gabanta bai daina faduwa ba, Su Mama Shatu da Mama Zubaida ta gani tsaye da 'ya yan su duk sun yi cirko cirko a tsakar gidan da makota ana ta maida magana, tsakar gidan dai cike yake da jama'a kowa na fadin albarkacin bakinsa, Umma ta dake tace "Wai me ke faruwa ne a gidan?" Mama Zubaida ta wani kalleta a walakance tace "Ina kuwa za mu san me ke faruwa tunda mu dai muna zazzaune sai ga wasu kattin gardawa sun kusa goma babu annuri a tare da su sun shigo mana gida da makamai suna tambayar dakin Malam, basu tsaya iya dakin Malam ba hatta sauran dakunan gidan nan sai da suka shiga..." Sai a sannan Umma ta lura da bakin kofar shiga dakin Malam Ali, gaba daya yayi kaca kaca da takardun da ta mayar daxu bayan su Jay sun dau wanda za su dauka, har kayan cikin dakin sai da aka watso su waje har da er katifarsa da akwatin kayan sakawan sa da butar alwalansa, Umma ta juya tana bin tsakar gidan da kallo taga har dakinta an fito da kaya an yi watsi da su waje, da kyar Umma ta karasa kofar dakin Malam Ali ta leka ciki taga basu bar komai ba, dama ba wasu abun kirki ke cikin dakin ba, can ta juya tana kallon Kishiyoyinta amma ta ma rasa me zata ce, Mama Shatu ta kyabe baki tace "Ni takaicina dakunan mu da suka shiga wai ina takardun da Malam ya ba mu ajiya, ni ko nace mu muka san wasu takardu mu da bamu yi karatu ba ta yaya Malam zai bamu takardu mu ajiye ai sai dai ko ya ba er sa da aka kai turai karatu daga karshe tayi ma wanda ya kai ta karatun butulci wai bata son sa kuma, amma ina mu ina ajiyar takardu mu da muke jahilai" Umma bata tanka ta ba ta duka tana tattara takardun dake watse bakin kofar su Islam suka je suna tayata, a haka duk ta maida kayan Malam Ali cikin dakinsa, su Mama Zubaida sai hararanta suke, can Mama Shatu ta kyabe baki tace "Mu dai mun san ko ma wani takarda suke nema bazai wuce yana da alaka da er ki ba kilan kotu za a shiga, tun da kika haifi yarinyar nan muke shiga jarabawa munana a gidan nan, ko kuma muce tunda aka auro ki, mu da bamu san wani talauci ba balle wahalar rayuwa, daga auro ki karayar arzikin da ba a taɓa yin irinsa a tarihi ba ya samu Malam, sannan gashi sanadin er da kika haifo ga abinda ya samu Malam a karo na biyu, daga ke har 'ya yanki babu wani abun alkhairi a tare da ku sai masifa, ina ma Malam zai yada kwallon mangwaro ya huta mu ma mu huta ki tattara ki koma can kasar ku ki auri buzu ɗan uwanki" Sha'awa dake tsakar gidan wanda tana daga cikin mutanen farko da suka shigo bayan Mama Zubaida da Mama Shatu sun kurma ihu, amma fa sai da gardawan suka fita sannan suka samu bakin ihun neman agaji su da yaransu, Sha'awa tace "Haba Mama Shatu, wannan wani irin magana ce kike yi haka don kin ga Ummansu Khaleesah bata tanka ku a gidan nan, wannan ai cin fuska ne, kar fa wataran ku kureta ayi dauki ba dadi a gidan nan, don mai hakuri bai iya fushi ba wallahi" Wani zagi Mama Shatu ta kundumo mata a fusace, Sha'awa ta rama tace "Wallahi ba dai ubana ba, sai ko in naki uban me gyaran keke dake kabari" Ganin fada na kokarin kaurewa a tsakar gidan Umma da wasu mata suka fitar da sha'awa dake kunduma ma Mama Shatu zagi ta uwa ta uba, ga su Labeebah na kokarin dambe da Sha'awa dake zagar masu uwa su ma duk aka rirrike su, a haka dai aka fitar da Sha'awa dake gyara daurin zaninta da ya kusa faduwa gashi babu komai kasan zanin, tana huci take cewa "Shegu en kutumar uba masu bin bokaye, ko jiya sai da aka bani labarin kun je wajen wani boka na kuma san warce ta raka ku, kun ga kuwa Umman Khaleesah ta fi ku ko a wajen Allah tunda bata san hanyar zuwa gun Malamai ba" A haka dai aka fitar da Sha'awa daga gidan, Umma dai jiki a sanyaye ta tafi kofar dakinta ta tarar su Islam suna ta maida kayan cikin dakin da aka watso waje bayan sun kunna er fitilar dake ba dakin hasken, Noor na kallon Umma tace "Umma kinga babu kayan abincin a inda suke" Umma ta kalli inda Maman Salame ta ajiye mata kayayyakin abincin da su Jay suka kawo taga wayam, tsayawa tayi tana kallon wajen babu ko kiftawa tsabar mamaki yasa ta kasa cewa komai, muryar Nenne taji a tsakar gidan cikin fushi tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, meye haka aka cika gidan nan kamar ana taron farin ciki? Ku yan unguwan nan tsabar munafurci da gulma bakwa tashi shigowa sai iftila'i ya faru sannan ku bi ku cika ma mutane gida ko wacce da warin jikinta, farin cikin iftila'in ku ke ko menene haka? Doo Allah duk ku fita ku ba mutane waje mu ji da daya, ai ba kanmu farau ba, en iska kawai magulmata" Rai bace ta nufi dakin Umma hannunta rike da jarkar manja daya hannun kuma rike da tocilan ta, ta tsaya daga bakin kofa tace "Zahra'u me suka dauka a dakin Alin da suka zo?" Umma da ta zauna gefen katifar ta tace "Shigowa ta kenan nima Nenne, na je gidan Baaba Gaje an sakota daxu da yamma" Nenne ta kalli kayan da su Islam ke shigarwa daki tace "Har dakin naki suka shiga ne? To ni Usama ce min yayi iya dakin Ali suka shiga suka watso kayan ciki, ke kuma wa ya watso naki tsummokaran waje?" Mama Shatu tace "To shi da ya sulale ya gudu ya bar gidan ta yaya zai ce iya dakin Malam suka shiga? Ai babu dakin da basu shiga ba a gidan nan yau, mu ma duk mayar da namu kayan mu ka yi, hatta babban jarkan mangyada da na siya jiya sun dauke, iya shi suka dauka a dakina, Ita kuwa Zubaida kwashin adashin da aka kawo mata suka dauke" Nenne ta fara matsar kwalla cikin rawan murya tace "Lallai na ga abinda ya isheni bai ishi Ubangijina ba, to yan fashi Awdul din ya aiko mana wannan karan? Don dai duk mun san yafi karfin wani kudin adashin da bai taka kara ya karya ba balle wata jarkan mangyada, Allah mun gode maka da wannan rantsattsiyar jarabawan da mu ke ciki mun gode maka Allah, Alhamdulillahi ya Allah, Ina ga in ba tattarawa muka yi muka hakura da zaman birni mu koma kauye gaba daya ba muna cikin mummunan hatsari a Mariri gashi ba mu da gata, kar wataran cikin dare mun saki baki muna bacci su babbake mu, su babbake banza tunda babu me tsaya mana" Ita dai Umma tayi shiru bata ce komai ba, Nenne na kallonta tace "Su kuma samarin da suka sha uban fararen kaya suka zo mana nan suna kwambo dama yaudarar mu suka zo yi bamu sani ba, sun zo nan sun gama cika mana baki sai gashi tunda suka karkade wandonsu suka fita bamu sake ganin keyar su ba, to ina amfanin karya? har da ce min za a saki Ali kwanan nan ashe duk yan iskan gari ne makaryata bamu sani ba" Umma dai kallon Nenne kawai take, Nenne ta mika ma Islam jarkan manjan hannunta tace "Ba ruwana, wahalan da nake ta sha kan Ali ko shi ya halittoni duniya ai sai haka, kai kenan kullum ayi ta garkame ka kamar kasungumin barawo, sai kace wanda yayi ma Allah wani saɓon da bamu sani ba, saura kadan kwale kwalen da na hau jiya zan je nema masa taimako ya kife da mu banda Allah ya tsare, to ina dalili bayan ba shi kadai na haifa ba, in ya kasheni sauran su yi yaya? ke ungo amsa ki mika ma uwarki ta tsiyaya min manja, nawa ya kare" Islam tace "To ai an kwashe kayan abincin gaba daya Nenne" Nenne ta gwalo ido tana kallon direction din da aka ajiye kayan abincin taga wayam, bude baki tayi tana kallon Umma tace "Zahra'u ina kayan abincin? Ko kasuwa ki ka kai kika siyar? Fatarar taki ta kai haka Zahra'u?" Umma tace "Saboda me zan kai kayan abinci kasuwa in siyar Nenne, daga zuwa gidan Baaba Gaje in dawo nima na tarar an kwashe kayan abincin" Nenne ta ajiye jarkan hannunta a kidime ta saki salati tana tafe hannu tace "Baki kulle dakin bane Zahra'u?" Umma tace "In zan fita ai ina sa ma dakina kwado, to fasa kwadon aka yi, ga makullin ma a jakata" Nenne ta juya ta fita daga dakin dai dai shigowar Usama wani almajirin Malam Ali dake tare da shi tun yana da arzikinsa, kuma har yanxu dai yana tare da shi, Nenne na haska sa da tocila tace "Yauwa Usama kace iya wani daki mutanen suka shiga a gidan nan?" Usama yace "Iya dakin Alhaji kawai suka shiga" Nenne bata sake cewa komai ba ta nufi dakin Mama Zubaida don yafi kusa da ita, tana dage labulen dakin ta fara haske hasken tocila, sai kuma ta duka karkashin gadon karfen dake dakin ta hango carton din indomie biyu an tura su can ciki, ta kwalo ma Usama kira ya karaso da sauri tana haska masa karkashin gadon tace "shiga ka jawo min kwalayen taliyar yaran can" Ai ko ya shiga ya kwaso su ya fito da su, Nenne ta shiga cikin dakin tana duba bayan kyaure nan ma taga Babban jarkan man gyada ta sa Usama ya fiddo waje, ta gama duba dubenta a dakin bata ga wani kayan abincin ba sannan ta nufi dakin Mama Shatu, a bayan kyaure taga buhun shinkafa daya da quarter an lullube da zani, ta kwalo ma Usama kira shi ma ta saka ya kinkimo su ya fitar waje, a dakin Mama Shatu still taga kwalayen taliya da na maggi da jarkan manja duk ta sa Usama ya fiddo su waje, Nenne na kallonsa tace "Kwashe su ka mayar dakin Zahra'u Usama" Yace "To Nenne" Sai a sannan Nenne ta juya tana kallon su Mama Shatu da suka yi wuki wuki da ido ko wacce na kokarin diban ruwan alwala a buta, Nenne tace "An dai yi asara duniya da lahira, barayin banza barayin wofi, tirrr da halin ku, wato ga sabon jarin kayan abinci kun samu ko, tunda Zahra'un ta maida kanta er wahala warce bata san ciwon kanta ba, da ban ce a tsam min manja ba shiru zata yi maganar ta bi rariya ta bar ku da haram, ko zama da ku kadai ya isa ya dinga jefa Ali a masifa iri iri, ai ba kyau zama da jahilai shine kawai bai gane ba" Daga haka ta juya ta koma dakin Umma. Khaleesat na bakin pampon dake compound din Aunty Farida tana wanke wanke, ita kadai ce a gidan gaba daya don duk sauran tenant dake gidan sun fita aiki, Aunty Farida kuma ta tafi kasuwa, juyawa Khaleesat tayi jin an bude gate, ta mike tsaye tana kallonsa, murmushi ya sakar mata ya rufe gate din ya karaso cikin compound din shi ma yana kallonta, ta sauke idonta a hankali tace "Sannu da zuwa" Yace "Good morning Halysaah" Ɗan murmushi tayi ta sunkuyar da kai ta gaishesa sannan ta juya ta tafi ta bude masa kofar shiga parlon Aunty Farida tana kallonsa, yace "Aunty fa? ina ta kiran wayarta no response" Khaleesat tace "Eh ta bar wayar a gida ne ta tafi kasuwa" Ya kalli plastic chair dake veranda din Aunty Farida yace "Let me seat here ba sai na shiga ba, i just came to check on you" Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "I really appreciate Housemate" Yace "To ki zauna mana" Ta kalli second chair din dake wajen sannan ta zauna, sake gaishesa tayi da ladabi tana kallonsa, yace "Lafiya lau Halysaah, how is ur body?" Tana wasa da gefen karamin veil din jikinta tace "Naji sauki" Yace "To amma naga kin rame, baki cin abinci ne?" Tayi shiru, yace "Baki ci ko?" Ta ɗan yi murmushi tace "Ina ɗan ci kadan" shiru ne ya biyo baya for almost 30 seconds, ta ɗan daga kai ta kallesa taga kansa a kasa, ajiyar zuciya ya sauke calmly yace "Everything will be alright soon in sha Allah Housemate" Nan da nan hawaye ya cika idonta, da kyar tace "But i don't know my mom's condition, i am really worried" Jay yace "Don't worry, Umma tasan kina nan, mun je can gidanku da Ajay, i assure you everything is fine back home do not worry ur self pls, yanxu dai we are working on clearing ur dad first before anything, soon in sha Allah he will be free from the debt" Hawaye na sauka idonta tace "To amma ni bazan iya zama da Abdul ba tsoron sa nake wallahi, kawai torturing dina zai yi yayi revenging abinda nayi masa, i am afraid" Jay yace "Do not be Housemate, we won't allow that happen in sha Allah, we will go to any extent na ganin hakan bai faru ba" Khaleesat dai tayi shiru tana share hawayen idonta, after some seconds yace "Baki tambayi Ajay ba?" Ta daga kai tace "Na zata tare ku ke yana waje" Jay yace "Not at all yana kano, bai ma san nayi tafiya ba, i took an early morning flight, zuwa 12 noon kuma zan koma kano in sha Allah, i just came to check on you" Khaleesat na kallonsa cikin sanyin murya tace "Nagode sosai, kuma naji dadi" Ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna karfe sha daya saura yace "I will be leaving for the airport now kar inyi missing flight dina, kafin Ajay yayi noticing i am not home ya fara damuna da kira" Khaleesat tace "Ko ruwa baka sha ba, ko in kawo maka shayi? Kilan ma baka yi breakfast ba ko?" Da damuwa tayi tambayar tana kallonsa, Yace "No i am okay Housemate" Wayarsa ne ya fara ring ya ciro yana kallon screen din yayi murmushi sannan ya nuna mata screen din taga Ajayn ne ke kiransa, mayar da wayar yayi aljihunsa sannan ya fiddo 100k ya mika mata yace "In case you need anything Halysaah" ta girgiza masa kai tace "A'a Nagode, bana bukatar komai wallahi" Mikewa yayi ya ajiye mata kudin a kafarta ya fita daga balcony din yace "Take care of ur self Housemate, idan na sake samun lkci ko zuwa nan da few days ne zan dawo in sha Allah, my regards to Aunty Farida" Khaleesat ta mike tana kallonsa ta kasa ce masa komai wasu sabbin hawayen suka cika idonta, ya daga mata hannu kawai ya nufi gate don bai ma son ganin hawayen nata, tana kallonsa har ya fita sannan ya rufo gate din, parlon Aunty Farida ta shiga ta zauna kan kujera ta rufe fuskarta tana rera kuka tana shessheka..... Bayan few weeks na zirga zirga a cikin garin kano, da kuma zuwa court lauyan su Jay yayi Succeeding na amsan Bail din Malam Ali, afterward suna sa ran kotu tayi dismissing claim din Alhaji Musa saboda previous debt forgiveness dake kasa, a kuma yi masa imposing monetary sactions for abuse of process, all this weeks Jay da Ajay where so cautious of der movement in kano and they were at alert In case of necessity ko kadan basu ba Abdul chance din yi masu ba zata ba cause sun san bazai rasa informant a unguwan ba, ranan da suka yi dropping din Malam Ali a gida bayan kotu ta bada bail dinsa farin ciki gun iyalinsa da wasu yan unguwan ba a cewa komai barin ma Umma, sai shigowa gidan ake ana taya sa farin ciki, shi ko Malam Ali har kasa ya duka cikin ladabi yana gode ma Jay da Ajay, shi dai Ajay ya juya ya koma jikin motarsa ya tsaya ya rungume hannu, ga motar escort dinsu a bayan motar tasa, Jay har ya gaji da ce ma Malam Ali ya dena masu godiya, Calmly yace "Don Allah Baba ka dena mana godiya, mu saboda Allah muka yi..." Malam Ali na gyada kai yace "To... to...to wannan gaskiya ne, Allah Ubangiji ya maku albarka, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara daukaka, Nagode Nagode" Duk a birkice yake godiyan, Mama Shatu ta dauko tabarma ta shimfida tace "Taho ka zauna ka huta ko zaka dawo seti Malam, naga duk a firgice kake" Nenne ce ta shigo unguwan bayan wani almajiri yaje har gidanta ya sanar mata Malam Ali ya dawo, mayafin nata ma a baibai ta yafa ga dankwali da ta kima a kan mayafin tana hade hanya ta taho gidan ɗan nata, bata kula da Ajay a kofar gidan ba ta shige ciki da sauri, Ajay ya ciro wayarsa dake vibrate a aljihunsa yana duba me kiran sa, gyara tsayuwarsa yayi yana kallon screen din wayar babu ko kiftawa ganin Aunty Farida ke kiransa, haka kawai yaji zuciyarsa ta harba don Aunty Farida bata kiransa all this while, in ma da wani abu shi ne ke kiranta, ya kalli Jay da ya fito daga cikin gidansu Khaleesat, har sannan ya kasa daga kiran Aunty Farida. [6/10, 6:29 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Jay ya karasa har inda Ajay ke tsaye yace "I think we can take our leave now, nan da friday sai a basa makullin sabon gidan, we just hope he will accept it" Shi dai Ajay bai ce masa komai ba don bai ma san me yake cewa ba, ganin yanayinsa Jay yace "Are you alright Bruh?" Jin Ajay bai basa amsa ba ya kalli wayar hannunsa that was still vibrating yace "Who is calling you?" Ajay ya sake kallon screen din sannan yayi picking dab da kira na biyu zai katse, kunne ya kai wayar yayi shiru yana sauraron yaji abinda Aunty Farida zata ce, muryar Khaleesat yaji a hankali tace "Good evening, Plss can i speak to my Housemate?" At first shiru Ajay yayi, can babu yabo babu fallasa yace "About?" Khaleesat ta girgiza kai murya can kasa tace "Ba komai, kawai dai ina son zan masa magana ne" Jay dai kallon Ajay kawai yake don bai san da wanda yake wayan ba, a takaice Ajay yace "Don't you have his digit?" Bai jira cewarta ba ya katse wayar ya mayar aljihu, Jay yace "Who is that?" Banza Ajay yayi masa ya bude driver seat ya shiga ya tada motar fuskarsa a daure, Jay ya daga shoulder sannan ya zaga ya shiga gaban motar shi ma bai sake kulasa ba, Ajay ya ja motar suka bar anguwan motar bayansu na biye da su. Bayan sallahn magariba Malam Ali na zaune tsakar gida tare da Nenne da duk matansa sai yaran gidan gaba daya, Nenne ce kadai zaune kan kujera er tsugunno, sauran duk kan tabarma suke a zaune kowa na jiran jin dalilin zaunar da su da Nenne tayi, Umma dai na kusa da bakin kofar dakinta da su Islam da Noor a jikinta, Nenne tayi gyaran murya tace "Da farko dai nayi farin ciki ainun da dawowan ɗa na daga furson a karo na biyu, ina rokon Allah ya sa iya bakin wahalarsa kenan sannan muna fatan yayi zuwan karshe kenan, wa ennan samari da suka zo suka tsaya mana kuma har suka kubuto da Ali Allah Ubangiji ya masu albarka don da farko na zata makaryata ne kawai en neman suna, duk da dama inda naje ance min za a roki Allah ya kubutar da ɗa na, nafi tunanin ma rokon Allahn da aka yi ne kawai hakan ta faru ba wai don samarin nan ba, mun dai gode koma ya ya ne, sannan shawaran da zan bada shi ne muyi bulaguro mu koma kauye gaba dayanmu na en shekaru kafin komai ya lafa, mu ma hankalinmu zai fi kwanciya da hakan don Alhaji Musa da tsinannen ɗan sa ba barin mu za su yi mu zauna lafiya ba, duk da kotu ta wanke Ali amma Allah kadai yasan wani sharrin za su billo da shi don mutane ne wa enda babu Allah a ransu, wallahi sai su iya sa wa duk a kona mu cikin dare muna bacci, kunga ance zaman lafiya yafi zama ɗan sarki shi sa cikin rufin asiri mu tattara komatsanmu ko zuwa gobe da magariba ne Ali ya mana shatan katuwar tirela mu koma kauyen mu" Mama Zubaida da Mama Shatu da suka saki baki suna kallon Nenne kusan a tare suka ce "Kauye kuma Nenne?" Nenne na kallonsu da kyau tace "Kwarai kuwa kauye, don dama can ne asalinmu, na gaji da tsallaka kogi cikin kwale kwale zuwa neman ma Ali taimako wataran inje in kife, gwara tun da sauran mutuncinmu mu bar garin nan" Mama Zubaida na girgiza kai tace "Inaaa, ai bazata saɓu ba gaskiya, sai dai ni a bar ni a nan in ci gaba da kasuwancina ina rufa ma kaina da 'ya ya na asiri, akan matsalar da buzuwar matarsa da er ta suka jawo baza a cucemu a mayar da mu riga ba, bazai ma taɓa yiwuwa bane gaskiya" Mama Shatu ta cafke tace "Sai dai ya tattara matarsa da 'ya yanta su kuma kauye Nenne, amma mu kam muna nan tunda ba mu ko 'ya yanmu muka jawo magana ba, dama mu ke ciyar da kan mu balle mu ji tsoron zamu rasa abinci" A fusace Nenne tace "A yaushe ku ka fara ciyar da kan naku munafukan Allah? ba sai bayan da ku ka tsiyace sa da fararen kafafuwan ku ba tukun? Ai ko Alhamdulillah kowa zai ma Ali shaidan kula da iyalinsa banda jarabawan shegun mata da Allah ya hadasa da, ku ne nan ku ka ja masa karayar arziki, dama ance min dukkanin ku babu alkhairi a tare da shi gwara ma Zahra'u, wallahi ce min aka yi in dai zai rabu da ke da Zubaida to arzikinsa zai dawo kaca kaca har fin na ɗa, Zahra'u ce kadai matarsa ta arziki aka ce min, da zai ji ta nawa ma duk ya sallameku in ga inda za ku koma idan ba kauyen ba, ke Zubaida kin manta kauyen da uwarki da ubanki suke sai sati sati ake kawo ruwan pampo? Kin manta ko wutar lantarki ba a ja maku har yau a kauyen ba? Kauyen da muka je na dawo ina ta amai da gudawa watana daya a asibiti amma har kina da bakin kushe namu kauyen da babu abinda babu? To wani ɗan iskan ne ma yace Rano kauye ce tukunna? Sannan ke shatu baza ma a kira garin iyayenki da kauye ba sai dai ace daji, haka nan muka dawo kano maguzawan mayu suka kamani da kyar aka samo kaina ba don Allah yayi da sauran shan ruwana a duniya ba da tuni na rasu wallahi" Shi dai Malam Ali yayi tagumi yayi shiru bai ce komai ba don tun kan Nenne ta kawo wnn shawara dama yake jin gwara ya koma garinsu don bai san da me Alhaji Musa da ɗan sa za su billo ba kuma, shi dai bai yarda kotu zata wankesa akan kudaden nan masu yawa ba gani kawai yake dadin baki su Ajay suke masa, Nenne tace "Yau ga samun waje kai, ita Zahra'u me yasa bata kushe shawarata ba sai ku masu fararen kafa, ko da yake ita ta guduwan er ta da ta shiga duniya ma take, mu bar ta taji da wannan ma" Mama Shatu tace "Wace er ta? Ai wallahi ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba Zahra'u tasan inda er ta take, mu dai ne kawai aka rena ma wayo aka raina mana hankali" Mama Zubaida tace "To ai ba ma sai kin rantse ba Shatu, kwarai kuwa Zahra'u tasan inda Khaleesat take" Nenne dai sai kallon Umma da ko kallon kishiyoyin nata bata yi ba take, a hankali Nenne tace "Lallai biri yayi kama da mutum, na kuma yarda da maganarku don Zahra'u da na sani da har yanzu tana nan kan darduma sanye da dogon hijabi tana rike da carbi tana kuka ba dare ba rana duk ta fita hayyacin ta, kawarta Uwar Salame da makociyarku sha'awa me daddawa su yi ta shigowa suna dannarta su zazzauna kusa da ita kamar me takaba, amma ina lura da ita yau kusan sati uku kenan tana ta harkar gabanta kamar babu abinda ya faru, nima dai ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba tasan inda Khaleesah take" Malam Ali ya gyara zama yana kallon Umma cikin lallami yace "Kiyi ma girman Allah Zahra'u ke da er ki ku rufa min asiri yanda Allah ya rufa maku, duk inda er nan ta tafi kiyi masu waya ta dawo ta amshi auren mijinta hannu bibbiyu, dama Allah ya riga ya kaddara Abdul ne mijinta mu din banza ne za mu canza hakan? don girman Allah ta rufa min asiri, ina cikin tashin hankali har yanxu wallahi don ban san kuma da me Alhaji Musa da ɗan sa za su dawo min ba, rufin asirina shi ne na damka masu Khaleesah kawai, in har suka kasheni wallahi banza kawai za su kashe tunda ba galihu ne da ni ba, tunda aka maida ni furson din nan nake rashin lafiya me tsanani, yanzu haka maganar da nake yi kirjina kamar an aza min katuwar dutse, ku yi min rai ke da er ki" Kamar zai yi kuka ya kare maganar, Nenne na matsar kwallan da babu tace "In wani abu ya same ka dama da Zahra'u da er ta zan yi kuka wallahi, don su ke kokarin salwantar min da kai ta karfi da yaji" Umma da hawaye ya cika idonta tace "To wai ta yaya zan san inda Khaleesah take ni ba waya ba balle ku yi tunanin tana kirana? Ko kun ga ina zuwa wani waje daga cikin dakina ne?" Mama Zubaida tace "Na rantse da wanda raina ke hannunsa Zahra'u kinsan inda makirar er ki take, don haka sai dai ki rena ma wani hankali amma ba mu ba, duk abinda ya samu mijinmu dama har karshen duniya mun yi ta ja ma ke da 'ya yanki Allah ya isa kenan, banda samun waje ita Khaleesah har tana da ta cewa da har zata bude baki tace bazata zauna da Abdul ba? Da me tafi Abdul din banda rufa mata asiri da yayi zai aureta? Mutumin da ya maida ta fess ya maida ta mutum ya kashe mata dukiya babu adadi don butulci da samun waje tace ita bata son sa kuma a ina aka taɓa tafka wannan iskancin? Wallahi ba a samu wanda zai ci ubanta bane shi yasa ta samu waje da yawa" Umma tace "Tun da har kuke tunanin nasan inda take kuma baza ku rasa sanin inda take ba ai, kilan ma za ku fi ni sani, don haka sai ku je ku fito da ita ku kai ta gidan Abdul din" Umma na kai wa nan ta mike ta shige dakinta, Mama Shatu tayi kasa da murya tace "Al-qur'an tasan inda take, da bata san inda take ba wallahi da har yau bata dena koke koke ba kilan har sai tayi rashin lafiya, kuma ni na ma fi zargin tana wajen kanwarta ne a garin Legas wallahi, in da ba haka ba ai da tuni mun ga Farida a gidan nan kamar an jefota amma gashi kusan sati uku har yau shiru Farida bata zo ba" Mama Zubaida tace "Ahaf ai mu ba yara bane" shi dai Malam Ali sai zazzare ido yake, Nenne tayi kasa da murya tace "Gaskiya na yarda da maganarku, don nima ina ta mamakin me yasa har yau farida bata zo ba, ita da ko tari yayarta tayi zata hawo mota ta kamo hanyar kano, amma ace an rasa Khaleesah yau sati uku shiru bata kamo hanya ba, ai da alamar tambaya" Malam Ali ya share zufar goshinsa duk da sanyin da ake shi ma yayi kasa da murya yace "To yanxu meye shawara? Ko ni zan shirya in tafi Lagos din ne?" Sosai hankalin Umma dake tsaye bakin kofarta daga cikin daki ya tashi don duk tana jin abinda suke cewa, Mama Zubaida tayi kasa da murya tace "Ai ban ma yarda da shiga dakin da tayi ba kilan er uwar zata kira, ko da yake bata da waya, kawai ina ga a gaya ma...." Mama Shatu ta ɗan tsunguli Mama Zubaida alamar tayi shiru, lkci daya Mama Zubaida tayi tsit, Nenne ta mike tana kallon Malam Ali tace "Mu je daga gefe mu yi shawara Ali" Mikewa Malam Ali yayi ya nufi can hanyar fita daga compound din Nenne na biye da shi, Mama Shatu ta mike tayi ma Mama Zubaida alamar su shiga ciki, suna shiga daki Mama Shatu tace "Ke ya muna neman maganar auren nan ya rushe gaba daya ko zai hakura yace a basa Labeebah ko Lamisah amma kike basu shawaran su je Lagos?" Mama Zubaida tace "Wallahi gaba daya na sha'afa kinsan kwakwalwar tawa, kuma kece kika kawo maganar Khaleesah, tun asali ma bai kamata mu ce komai ba gashi yanxu mun karkato da hankalinsu zuwa Lagos, sai fa Malam ya iya shiryawa ya kama hanyar Lagos wallahi" Mama Shatu tayi shiru, can tace "Ai ko in yaje lagos din nan shikenan tsarinmu ya lalace don taso keyarta zai yi su dawo kano ya mika ma Abdul ita, kinga shikenan mun tashi a tutar babu mun kai ba malamai kudadenmu a banza, tunda duk mun san Abdul din na sonta kuma hannu bibbiyu zai amsheta su fara rayuwar aure" Mama Zubaida tace "Toh kuwa ina ga da kaina zan kira Farida ince mata in har tasan Khaleesah na wajenta to tayi maza maza su bar gidan don Malam zai kama hanyar lagos tare da Abdul" Mama Shatu tace "A'a bari in shiga dakin Zahra'u in gaya mata hakan, tunda ga Nenne da Malam can sun kebe bamu san maganar da suke ba" Bata jira cewar Mama Zubaida ba ta fita zuwa dakin Umma, Zaune ta tarar da Umma bakin katifarta abun duniya ya isheta gashi babu waya hannunta, kuma in tace ta fita daga gidan ta amshi waya a makota tasan dole za a zargeta, kuma daxu da safe suka yi waya da farida ta wayar Mama Salame take sanar mata jibi za su Nijar da Khaleesat, Mama Shatu na kallon Umma tayi kasa da murya tace "Zahra'u, ga can Nenne da Malam suna shirya yanda za a tafi legas wajen Farida gobe da asubar fari, in dai kinsan Khaleesah na wajenta wallahi kiyi maza ki buga mata waya su bar gidan su tafi wani wajen, a ajiye batun kishi a gefe abinda baza ka so ma danka ba kar ka so ma ɗan wani, don duk mun san Abdul ba mutumin kwarai bane, kuma a zamanin nan an dena auren dole, mu ma ba a mana dole ba don haka baza mu yi ma 'ya yan mu ba" Mama Shatu na kai wa nan ta juya ta fice daga dakin, Umma ta mike gabanta na faduwa ta ɗan leka tsakar gidan taga Nenne da Malam Ali tsaye a can lokon tsakar gidan suna magana kasa kasa.... Jay ya fito daga kitchen hannunsa rike da mug din shayi yana juyawa a hankali, Step Mom din Ajay ce zaune parlon cikin shiga ta alfarma, a ranan ta sauka gidan tare da jakadiyarta sun dawo daga kaduna, Jakadiyarta na dinning area tana yanka mata fruit, Jay ya tsaya dai dai inda yake don bata san ya fito daga kitchen din ba, da wani kallon tsana kawai yaga take bin Ajay dake haurawa sama hannunsa rike da laptop dinsa, after few seconds Jay ya ci gaba da juya shayin hannunsa yana kallonta, tana jin sound din cokali ta juya da sauri tana ɗan murmushi ta hau canza channel din TV, shi dai Jay ya karasa cikin parlon bai sake kallonta ba, Jakadiyarta ta taho ta ajiye mata fruit din da ta gama yankawa cikin ladabi take sanar mata ga kayan marmarin, Cike da isa Aunty ta dau Apple ta fara ci, ta ɗan kalli Jay ganin sama zai wuce shi ma tace "Gobe Abbanku zai shigo wani taro" Jay yace "Mun yi waya da shi" Daga haka shi ma ya wuce sama, ta wani taɓe baki ta bi sa da kallo, Jakadiyar da ta zube gefenta cikin girmamawa tayi kasa da murya tace "Ranki shi dade, Allah ya ja zamaninki, daxu na jiyo mana wani labari Allah ya sa zaki yi maraba da wannan labarin" A takaice Aunty tace "Labari akan me?" Jakadiyar ta gyara zama tace "Akan Yarima" Aunty ta ajiye Apple din hannunta ta ba jakadiyar gaba daya attention dinta tace "Me kika jiyo?" [6/11, 8:28 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Har mahaifin Abdul ya gama bambamin da yake yi a parlon Momy kamar zai ari baki bata ce masa komai ba illa rungume hannu da ta yi tana zaune kan kujera tana girgiza kafa fuskarta babu fara'a, Meemah dake zaune parlon ita ma dai bata ce komai ba fuska a murtuke, Alhaji Musa yayi bala'in sa me isarsa sannan ya juya zai bar parlon a fusace, sai kuma ya sake dawowa yana huci yace "Ina wawan Abdallan yake? Ina yake yaga abinda rashin tunaninsa da rashin daukan shawarar sa ya ja min" Momy ta tabe baki ita ma cike da takaici tace "Ai Alhaji yau kwana uku curr rabonsa ma da gidan gaba daya, kuma ba a samun sa a waya, ya kashe wayar" Rai bace Alhaji Musa yace "Duk shi ya ja min wannan bala'i ina zamana, wa yace masa dama ana harkar arziki da talaka? Sam ai ba a shige ma talaka duk yanda yake kuwa, tun asali zuri'ar da yake son in hada da wancan barawon mutumi ba wai nayi na'am da hakan bane, kawai bani da yanda zan yi da Abdallah ne" Momy ta gyara zama zuciyarta na tafarfasa tace "Atoh dai, har na gaji da nanata wannan sentence din da kayi Alhaji, ai ba a abun arziki da talaka don tun asali dama a tsiyace ya zo duniya kuma a tsiyace zai koma, kana zaman zaman ka gashi Abdullah ya ja maka asaran makudan kudi har da su taran kotu, wai kai da aka zalunta kai ne kuma da biyan tara saboda rashin adalci, ai Abdul bai kyauta mana bai duba mana ba, ace shi bazai dau maganata a matsayina na uwarsa ba? Babu yanda banyi discouraging dinsa kan tsinanniyar yarinyar nan ba na nuna masa ba ajinsa bace yaki saurarata wallahi, kyanta ne kawai ya rudesa wato kyan ɗan maciji, har tayin er aminiyata nayi masa amma firr yaron nan yaki, to ga dai abinda ya ja mana" Meemah tace "Ni duk ba wannan ba Momy, kawai so nake in san wasu 'ya yan shegun ne suka tsaya mata haka har suka maida case din kotu? Sannan ga auren ma suna kokarin kotu ta rabasa ta karfi da yaji, kun ga kenan mun tashi a tutar babu, kuma babu tantama duk yanda aka yi ma su suka boye yarinyar, su waye en iskan nan ne?" Alhaji Musa na safa da marwa a parlon yace "Don kotu ta kori karar nan ba shi ke nufin na bar wannan mutumi da ya salwantar min da dukiya ba, mu zuba mu gani da shi, sai na lahira ya fi sa jin dadi wallahi" Daga haka ya bar parlon kamar zai tashi sama, Momy ta sauke wani ajiyar zuciyar takaici tana girgiza kai tace "Abdallah bai duba mana ba wallahi, ya kaskantar da mu a idon duniya kawai, wai yau talaka ne ya ci nasara a kan mu a kotu, this is a big slap to us, kuma ko uban menene dalilinsa na dinga kashe waya ba a samun sa oho? Ni taran da aka ci Alhaji ne ma yafi ƙona min rai wallahi, ga mari ga tsinka jaka, ki sake kiran wayarsa kiji ko zai shiga" Meemah tace "Baza fa a samesa a waya ba Momy, mu da ganin Abdallah sai ya cika burin dake ransa kema ai kin san halinsa, gwara ma ki saka ma ranki salama mu bi sa da addu'a kawai" Momy ta kalleta tace "Wato kin san inda yake kenan?" Meemah tace "Ke dai kawai ki bi sa da addu'a Allah ya basa nasaran abinda ya saka a gaba Momy, amma shegiyar yarinyar nan ai kamar ta shigo gidan nan ne babu me hana hakan, don baza mu yi biyu babu ba" Momy ta tabe baki tace "Har ga Allah ni so nayi kawai ya hakura da er matsiyatan nan Meemah, kada tsautsayi ma yasa a hada iri da ita mu shiga uku, hada iri da talaka ai ci baya ne Meemah, don ni har cikin raina naki jinin talaka wallahi balle in hada zuri'a da su" Meemah tace "To ai dama bama fatan a hada iri da ita Momy, personally bazan ma bar hakan ya faru ba trust me, kawai ta shigo gidan ta gane Allah daya ne, ke kuma ki fara masa fafutukar wani auren da wuri wuri" Momy dai tayi shiru, can ta tabe baki tace "Allah ya sa ya saurareni to" Meemah tace "Haba dai zai saurareki, da kaina zan masa magana, a samar masa yarinya dai dai class dinsa" Momy tace "To ai shikenan, yanxu tracing din matsiyaciyar yarinyar ya sa a masa kenan?" Meemah tace "Ko ma dai menene mu dai mu zuba ido mu bi sa da addu'a kawai Momy" Mikewa Momy tayi tace "Bari in je in lallaba babanku, na dade ban ga ransa ya baci irin haka ba, haba ai abun da bacin rai, wai ace talaka yayi nasara akan ka a kotu bayan kai ne me gaskiya ai abun da ciwo" Daga haka ta wuce sama, Meemah ta dau wayarta tayi dailing number da take samun Abdul da shi ta tashi ta shiga dakin dake parlon. Da asuba ko sallah ba ayi Malam Ali ya fito da er jakar da yake tafiya da shi bayan ya mulke jikinsa da basilin saboda sanyin da ake, bin dakunan matan nasa yayi duk ya kwankwasa masu kofa, Mama Zubaida da Mama Shatu suka fito suna kallonsa da mamaki suka ce "Lafiya Malam?" Mama Zubaida tace "Ko tafiya kauyen ne ya taso?" Shi dai bai tanka su ba ya dinga goge takalminsa da yayi ƙura, Umma ce karshen fitowa ita ma ta tsaya tana kallonsa ta kasa cewa komai don tasan manufarsa, ko baccin kirki bata yi ba daren jiya tsabar yanda hankalinta ya tashi, Nenne ce ta shigo gidan yafe da zaninta tana ganin Malam Ali tace "Yauwa ko sallah kar ka jira kayi idan kaje tashar kayi a can Ali, ga er soyayyiyar nama da gurasa na kullo maka ka ci a hanya" Mama Shatu tace "Tafiya zai yi ne Nenne?" Nenne tace "Babu ruwan ku, ku dai ku yi masa fatan Allah ya kiyaye hanya" Malam Ali ya amshi kullin nama da gurasan da Nenne ke mika masa, yana kallon matan nasa yace "Toh sai Allah yayi min dawowa" Mama Shatu tace "To ai shikenan, Allah Ubangiji ya tsare Malam" Mama Zubaida ma tace "Allah ya tsare duk da muna da hakkin ka sanar mana inda zaka je da asuban fari Malam" Nenne tace "Bazai sanar ba Zubaida, uban me sanin inda za shi zai kara maki?" Mama Zubaida ta juya ta koma daki, Mama Shatu ma ta tabe baki ta koma dakinta, Nenne ta kalli Umma tace "Wato ke ce isasshiyar da bazata yi masa Allah ya kiyaye ba ko Zahra'u" Shi dai Malam Ali tuni har ya fice daga gidan, Nenne na nuna Umma tace "Mugun abun ku zai kare maku da ke da er ki wallahi, babu wanda ya isa ya salwantar min da ɗa na lokacinsa bai yi ba" Daga haka ta bi bayan Malam Ali da sauri zata rakasa bakin titi ya samu adaidaita sahun da zai kai sa tasha. That same day bayan an idar da sallahn asuba Jay ya shigo parlorn Mai martaba da sleepy face ta dalilin kiran da yayi masa, ganin irin zaman da Abba yayi kamar yana fadarsa ya gane serious issue Abban zai yi discussing da su kenan, ya kalli Ajay dake parlon zaune shi ma alamar kiran sa Abban yayi, Aunty ma na zaune parlon, Jay ya sauke kansa ya karasa kusa da Ajay ya zauna kasan lallausan carpet din parlon, dabi'ar Abba ne sai ya iya minti biyar zuwa goma kamar me nazari kafin ya fara magana in ya tara ku, Jay ya sunkuyar da kansa ya lumshe ido, Ajay ya ɗan kallesa sanin sai ya iya bacci a haka, ai ko yaga baccin yake, Ajay ya ɗan tunkudesa da elbow dinsa, Jay ya bude ido da sauri yana gyara zama, shi dai Abba kallonsu kawai yake, At last Abba yayi gyaran murya cikin nutsuwa yace "First of.... Ina son sanin zaman me ku ke har yanxu a garin nan baku karasa gida ba?" Duk suka yi shiru babu wanda yace komai kansu a kasa, Calmy Abba yace "Ohk take ur time, amma kuyi kokari ku je gida kafin hutun ku ya kare, Secondly.... maganar da nayi da ku a Maryland naji babu wanda yace min komai a kai har yanxu, ga lokacin da na baku ya cika, nayi maku uxurin mantuwa shi yasa nake tunatar da ku yanxu..." Nan ma duk suka yi shiru babu wanda yace komai, shi ma Abban yayi shiru yana kallonsu yana jiran amsa a duk sanda suka shirya, sun san shirun da Mai martaba yayi amsarsu yake kira ko da zai dau 10min ko fin haka ma kafin su basa amsan he won't mind zai jira su patiently, sanin halin Abban nasa yasa Ajay ya daga kai, Softly yace "Ayi hakuri ranka shi dade ba mantawa muka yi ba, in sha Allah we are working on that very soon" Mai martaba yace "Is that so?" Ajay ya sauke kansa don kalman Abba na nufin bai gamsu da abinda yace ba kenan, Shi dai Jay yaki dago kai, a hankali Ajay yace "A gafarce mu a ɗan kara mana lokaci Abba..." Aunty da har ta fahimci maganar da ake ta ɗan yi gyaran murya ta nemi permission din magana gun Mai martaba, ya gyada mata kai alamar ta fadi abinda zata fada, cikin nutsuwa tace "In na fahimci maganar da ake ranka shi dade, magana ce akan su fito da matan aure duba da yanda shekarunsu ke gaba ba baya ba, wannan magana kuma ba sabuwar magana bace don an fi shekara 3 ana yin ta amma babu wani progress, a takaice basa daukar maganar da muhimmanci, to amma dai ina ga ka ɗan sha'afa ne ur Highness, don shi Jawwad ai akwai maganar sa da Hadeeyah a kasa duk da ba wai maganar tayi karfi bane kuma wannan hadi, hadi ne me kyau da zai kara karfafa zumunci don mahaifiyar Hadeeyah jininka ce kuma ita ta kawo wannan shawara duk da Fulani wato mahaifiyar Jawwad uwar dakinta ce tun asali, shi kuma Junaid a yanda na lura da shi zai fi maraba da zabin ka garesa duba da nature dinsa da rashin choice dinsa, don haka shi Jawwad a tsaida maganar sa da Hadeeyah kawai ina ga hakan zai fi, shi kuma Yarima i think we should get him a princess from neighbouring states, ko ni zan iya jagorantar hakan don arranged marriage zai fi suiting dinsa duba da nature dinsa, kuma ina son a bar komai a hannuna ranka shi dade..." Ajay ya daga kai ya kalleta zai yi magana mai martaba ya dakatar da shi, Ajay ya sauke kansa, Speaking Calmly Mai martaba dake kallon Ajay da Jay yace "Za ku iya tafiya, Allah yayi maku albarka" Sai a sannan Jawwad ya dago kai ya kalli Aunty dake ɗan murmushi ganin Mai martaba yayi na'am da shawaranta, tuni Ajay har yayi disappearing daga parlorn fuska a murtuke, Jay ya mike shi ma ya bi bayan Ajay yana tafiya a hankali, bai taɓa sanin baya son Hadeeyah da aure ba sai yau da Aunty ke bada shawaran a tsaida ranan aurensu da ita, yasan kuma duk abinda Aunty tace kamar Abba ya aikata hakan ya gama ne, kawai yaji hankalinsa yayi mugun tashi yaji wani zufa na keto masa, dakinsa ya shige ya kulle da makulli ya jingina da kofar ya lumshe ido zuciyarsa na bugawa, Ajay na shiga dakinsa shi ma ya kulle da makulli ya zauna gefen gado ya dafe kansa da hannu biyu, this is not the first time da Aunty ke kasalanda akan duk abinda ya shafesa gashi Abbansa baya basa listening ears ko me Aunty tace masa kawai haka za ayi abun nan komin munin abun, at this point he felt he is of no importance to his father, he felt dejected, and it's been like this for so many years, he have no one to stand for him, a hankali ya juya yana kallon wayarsa dake vibrate, Number Aunty Farida ya gani a gaban screen din wayar, ya kalli agogo yaga karfe shidda da minti biyar na safe, request din Khaleesat na jiya da ta kirasa ya tuna, hakan yasa har kiran ya katse bai daga ba knowing she might be the one calling, kiran ya sake shigowa ya kalli screen din nan ma bai daga ba har ya katse, sau hudu kiran na shigowa continuously, hakan yasa ya maida attention dinsa kan wayar ya ɗan yi jim with different thought running his mind, ganin kiran ya katse an sake kira making it the 5th time of calling yasa ya dau wayar ya daga ya kai kunne yayi shiru waiting to hear who is on the line, a hankali ya mike jin abinda Aunty Farida ke ce masa ta wayar, bai san sanda ya zame wayar daga kunnensa ba rate din heartbeat dinsa na karuwa, da sauri ya nufi kofarsa ya bude ya fice daga dakin ya murda kofar dakin Jay yaji a kulle, knocking ya dinga yi non stop kafin Jay ya bude kofar da mamaki yana kallonsa yace "What is it?" Ajay ya shiga dakin yana shafa gashin kansa da wani expression yace "He tracked her to Lagos" Still Jay yayi a inda yake tsaye ko kwakkwaran motsi baya yi yana kallon Ajay, Ajay ya ja numfashi sannan ya zauna kan kujeran dakin ya lumshe idanuwansa ya jinginar da kansa jikin kujeran trying to calm himself, Jay was speechless and shock at the same time, da kyar ya ja kafa ya zauna gefen gadonsa ya dafe kansa da yaji yayi masa nauyi, kamar an tsikare Ajay ya mike yace "Book us ticket to Lagos" Daga haka ya fice daga dakin. [6/12, 8:02 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Aunty Farida ta share hawayen da yaki tsaya mata tana kallonsu Ajay da kyar tace "Wallahi ban san ko har su nawa bane a motar, ban ma san ya motar take ba tunda ina cikin gida sanda abun ya faru, yaran makota dake diban ruwa a bakin rijiyar tare da ita ne suke cewa kawai suna diban ruwa sai ga motar ta shigo street din, wasu mutane suka sauka a motar suka ja ta zuwa cikin motar suka tafi da ita, a sannan an idar da sallahn subahi kenan kun ga gari bai waye ba ai" Ajay was speechless, bai taɓa zama confuse haka a rayuwar sa ba don ya ma rasa abun cewa, likewise Jay dake jingine jikin mota tun da suka iso unguwan dama shi bai ce komai ba, Ajay ya daga kai after some seconds ya kalli Aunty Farida a hankali yace "Amma yana da number ki ne Aunty?" Aunty Farida tace "Ba shi da wannan number tawa gaskiya sai tsohon layi na, kwanaki Maman Khaleesat tayi rashin lafiya sai na tafi kano dubata to a hanya na yar da wayata, da na zo kano sai na siya sabon layi kafin inyi welcome back din tsohon layin, to har yanxu ban yi welcome back din ba" Ajay yayi shiru yana nazari, Aunty Farida na hawaye tace "Tsautsayi yasa ta fita deban ruwan yau, amma tunda ta xo wallahi ni ke diban ruwana bana barin ta dibar min tunda har yanxu gata nan ne dai bata dawo dai dai ba, wani lkcn ma da daddare idan na dawo kasuwa nake yi tunda ana wahalar ruwa a season din nan don yawanci rijiyoyi kafewa suke yi sai ana bari ruwan na taruwa sannan a diba, gashi ba a samun wuta balle a samu ruwan pampo, a jiyan nayi girki me yawa ne na wani biki duk sai na gaji ban deba ruwan da daddare ba, da na tashi kuma sai nake jin zazzabi, kun ji dalilin fitarta ta debo mana ruwa kenan" Ajay ya jingina da motarsa ya lumshe ido ya bude, gaba daya ƙansa ya gama kullewa, bai yi zaton Abdul ya wuce yanda yayi zatonsa ba, the guy is really something else ko wani salon tactics na mugunta ya san sa gashi har yau yaki kunna wayarsa balle a san inda yake, ko by mistake baya kunna layin, shi dai Jay dama bai taɓa underrating Abdul ba dai dai da rana daya duba da irin actions din da ya dinga portraying, kawai dai tracing din Halysaah har zuwa Lagos is the least thing da yayi zaton Abdul zai yi, tunda bashi da access da Aunt dinta, but like seriously how did he even find his way, bayan bashi da active line din Aunty Farida sannan bai san unguwan da take ba, ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya yana tunanin ta inda za su fara billo ma wannan lamari, tunda dai babu ta yanda za su ce yayi kidnapping Halysaah da ke a matsayin matarsa ta sunna. Khaleesat na zaune at the far end of the large room ta hade kanta da gwiwa, zuwa sannan ta hakura da kukan da take don ba ma ta da strength din kukan amma tana jin zuciyarta na mata zafi ga wani azababben ciwon kan da take ji da kishin ruwa da ya dameta, tafi awa sha biyu zaune a dakin ba ci ba sha, don tunda aka shigo da ita har zuwa sannan babu wanda ya sake zuwa dakin, infact bata ji motsin kowa a gidan ba alamar ita kadai ce a ciki, bandakin dake cikin dakin take shiga tayi alwala ta fito tayi sallah duk da ba sanin lokaci tayi ba kawai tana amfani da instinct dinta ne, at this point in time tasan bata da wani sauran gata sai wajen Allah, domin kuwa tasan Abdallah ne kawai zai sa a zo ayi mata irin wannan daukan, wasu hawaye masu zafi suka zubo idonta tana tausayin rayuwarta, all she could remember vividly was that tana bakin rijiyan dake kusa da gidansu Aunty Farida tana diban ruwa wasu mutane biyu suka zo a mota, lokaci daya kuma suka yi leading dinta zuwa motar tasu, at first turje masu tayi ta fara kokarin raising alarm tana ihu, yaran dake bakin rijiyan duk suka gudu suka shige gidajensu, tana kururuwa daya mutumin ya rufe fuskarta da wani Handkerchief da sauri, taji ta shaƙi wani abu kamar dust, lkci daya kuma ya cire handkerchief din a fuskarta, daga nan kuma ko kokarin ihun bata sake yi ba cause she became weak, ita dai tasan all through the ride she was conscious but not fully, gashi ta kasa tabuka komai don duk jikinta ya mutu, kanta yayi mata nauyi idonta suka dinga juya mata.... Da sauri Khaleesat ta dago kanta ta mike tsaye jin ana ƙoƙarin bude kofar dakin ta waje da makulli, gabanta ya dinga bugawa da karfi idonta na kan kofar har ya bude ya shigo, she wasn't expecting anyone but him dama, ta sauke kanta bayan sun hada ido, wasu sabbin hawayen suka fara zuba idonta, muryarsa taji ya daki kunnenta cike da isa da gadara yace "Har yanxu Body guards din naki basu biyo bayanki bane? Ai yaci ace sun iso zuwa yanxu don naga It's almost 12 hours now, how comes basu zo cecen ki ba duk capacity din su" Sai a sannan Khaleesat ta daga kai ta kallesa cikin rawar murya tace "Ka ji tsoron Allah...." Kasa ci gaba tayi ta fashe da matsanancin kukan takaici, shi dai yana tsaye yana kallonta da wani murmushin mugunta kwance fuskarsa, ta dago kai da sauri jin yana takowa har zuwa inda take tsaye, mannewa tayi da bango tana jin kamar bangon ya tsage kawai ta shige gabanta na bugawa da karfi, sai da ya zo dab da ita cikin kwantar da murya yace "Me kika ce?" Ta girgiza masa kai da kyar gabanta na ci gaba da faduwa muryarta na rawa tace "Kaji tsoron Allah Ya Abdul, kaji tsoron...." Bata rufe baki ba taji saukan lafiyayyen mari a fuskarta wanda sai da taga taurari, ta dafe kuncinta tana kallonsa babu ko kiftawa, cikin husky voice dinsa yace "You still have the guts to repeat what u just said saboda baki da kunya ko? Ni zaki gaya ma in ji tsoron Allah? To tsoronki zan ji ko tsoron uban ki dake Mariri idan ban ji tsoron Allah ba?" Da kyar Khaleesat ta dake tace "Ka zageni amma kar ka sake zagar min uba" Still bata rufe baki ba ya sake sauke mata wani wawan marin a other side of her face, this time around sai da dakin ya juya mata don ba marin wasa yayi mata ba, ya fixgota yana mata wani irin kallon da ya gigitata don tuni idonsa yayi jajur yana huci yace "Ina magana kina mayar min how dare you poor wretched girl?" Ta fashe da matsanancin kuka tana jin dama Allah ya dau ranta kawai ta huta a wannan lokacin, zata durkusa kasa ya hadeta da bango yace "Yau ina body Guards din naki dake goya maki baya kina min iskanci? Tell me where they are today? Da aurena a kanki kike hulda da wasu banzayen gardawa saboda ke jahila ce warce bata san me take ba" Tana kuka sosai bata san sanda tace "To wai ana aure dole ne dama Abdul? Nace bana son auren, bana son ka, gwara kawai ka kasheni duk mu huta" Da karfi ya bugata da bango har sai da taji numfashinta ya dauke na few seconds, yana mata wani mugun kallo yana huci yace "Dama ke baki san aurena wajibi ne a gare ki ba ko kina so ko ba kya so? Dama shi ubanki bai gaya maki hakan ba ko mantawa kika yi saboda kin fara bin maza? Wallahil Azeem kin ji rantsuwar musulmi ko? Duk ranan da kika sake yunkurin guduwa ko kuma yin wani silly act to rayukan twin siblings din ki za su zama fansar aurena idan kika kuskura kika min jakanci, ko kina so ko baki so lallai dole ki zauna da ni ko kuma in salwantar da ran kanninki i am promising you this Billahil Azeem, kuma babu abinda zai faru don tamkar na kashe banza ne daga ke har iyayenki babu abinda za ku yi, su kansu Body guards din naki ba kyalesu nayi ba don sai na dau revenge din intruding da suka yi a sabgata, i will teach them a lesson kina ji kuma kina gani" Khaleesat ta kasa cewa komai don sama sama kawai take jin numfashinta kalmansa na cewa zai salwantar mata da siblings dinta ya sa jikinta ya fara rawa, ya juya cike da isa ya tafi ya bude closet din dakin wanda duk kananun shegun kaya ne yace "All this are your wears, in kin yi sallah kin shirya ki zo ki sameni a dakina which is 3 rooms away from this, ina jiranki at exactly 7pm and this is just 6:30pm" Yana kai wa nan ya fice daga dakin yana rike da key din dakin, a hankali Khaleesat ta sulale kasa tana sauke numfashi tana jin wani abu ya tsaya mata cak a zuciya, gashi ba ta ma da strength din da zata yi kuka sosai ko zata ji relieve don tun jiya rabonta da abinci, she was just weak and helpless, ga idonta da taji ya fara ciwo saboda marin da yayi mata don dama ba warkewa idon yayi gaba daya ba lkci lkci tana jin yana damunta, tsoro da fargaban kada ya sake dawowa dakin yayi mata fiye da abinda yayi mata yasa Khaleesat tayi karfin halin mikewa da ɗan sauran strength din ta da ya rage tana tafiya da kyar ta shiga bandakin dake cikin dakin ta tara ruwan pampo tana sha ko zata ji saukin abinda take ji a zuciyarta, bayan ta sha ruwan ta dinga kallon fuskarta da yayi ja ta madubi, a hankali ta zame kasan bandakin ta jingina da tile din bangon hawaye masu zafi na zarya a fuskarta, tafi minti goma a haka lokaci daya ta yunkura ta mike bayan ta tuna time din da ya bata kar ya sake dawowa, she wish akwai makulli a jikin kofar bandakin don da kulle bathroom din kawai zata yi in ma mutuwa ne tayi a haka don yafi mata kasancewa da Abdul, cikin rashin kuzari ta cire hijab dinta da kayan baccin dake jikinta ta fara wanka da shower gel din dake bandakin, komai na bukatar mace akwai a banɗakin everything is just set, after a while ta gama wankan ta wanke bakinta ta fito sanye da dogon hijab dinta with different thoughts running her mind, tunda ya bar kofar dakin a bude ko dai ta samu ta lallaba ta fita and find a way for her self, duk da tasan Abdul will never be that stupid da zai bar kofa a bude har ta samu ta fita, infact in ma ta fita daga building din gidan tasan definitely akwai mai gadi a bakin gate kuma babu ta yanda zai bar ta ta fita, kilan ma Abdul din ya sanar masa in zata fita kar ya bude mata gate, but still ita dai burinta ta samu ko daki me makulli ne ta shige ciki ta kulle kofar sannan ta bar key din a jiki yanda ko spare key idan aka saka za a bude kofar bazai budu ba sbda key din da ta bari a jiki, da wannan tunanin ta nufi kofa gabanta na faduwa ta bude kofar dakin a hankali zata fita suka kusa cin karo da shi, rikicewa tayi ta juya da sauri zata bar bakin kofar ya fixgota, bakinta na rawa tace "I am very thirsty" fuskarsa babu wani rahama yace "Follow me" Bata iya ta masa musu ba tunda taga kiris yake jira ya mareta a ko da yaushe, at every slight opportunity marin ta kawai yake, tana biye da shi zuciyarta na bugawa suka shigo Main parlor din gidan, karshen haduwa gidan ya hadu amma ita ko lura da hakan bata yi ba don ta kanta kawai take, tana biye da shi ya kai ta har kitchen din gidan, ya juya ya kalleta a takaice yace "Gashi nan ki dafa abinda zaki ci don bani da time din fita in siya maki komai tunda kina da hannun girki, after that ki dafa min lipton ki kai min dakin da nace" Ita dai Khaleesat na rakube jikin kofar kitchen din gaba daya hankalinta baya jikinta, taga yayi ficewarsa ya bar mata kitchen din, ta bi sa da kallo har ta dena ganinsa, ta zame kasa ta hade kanta da gwiwa cikin rawan murya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace" ta kusa minti biyar a haka kafin ta yunkura ta mike tana goge hawayen da yaki tsaya mata, tana tafiya a hankali ta nufi kofar parlon ta murda taji a kulle kuma babu makullin a jiki she wasn't surprise don tasan dole zai kulle gidan, haka duk sai da ta bi dakunan dake gidan ta murda su taji a kulle kuma babu makullansu a jiki, a sanyaye hawaye na bin fuskarta ta koma kitchen din, duk da rabonta da abinci tun jiya amma ko yunwan bata ji tsabar tashin hankali, kawai jikinta ne yayi weak taji strength dinta duk ya kare, wnn yasa ta ɗan hada shayi kadan a cup zata sha, shi ma dai ta kasa sha don bata da appetite, haka nan ta zubar ta dau black tea din da yace ta dafa masa ta fito daga kitchen din, dai dai san da ya shigo parlon, sunkuyar da kai tayi rate din heartbeat dinta na karuwa cause he is just wearing short and singlet, cike da karfin hali tace "Ga tea din" Babu yabo babu fallasa taji yace "A nan nace ki bani tea?" Ita dai bata ce komai ba amma kana ganinta kasan a mugun tsorace take, tana hade hanya ta nufi inda yace ta kai masa shayin yana biye da ita a baya, da ace tashin hankali da fargaba na kashe mutum ya ci ace ya kashe Khaleesat a wnn moment din, a bakin kofar dakin ta tsaya cikin rawan murya tace "Ga tea din" Wani tsawan da ya kidimata yayi mata don bata ma san sanda ta shige dakin ba ta je ta ajiye masa Mug din tea din a kasa tana waige waige, ya shigo dakin ya tura kofar fuska a daure yace "Cire Hijab din nan, kuma yau ya zama first and the very last day da zaki min yawo da Hijab a gida" Ta durkusa kasa ta fashe masa da kukan tashin hankali tana kallonsa, ya mata tsawa yace "Are you daft?" Cikin kuka tace "Wallahi sallah nake son inyi ne kayi hakuri" Darduma ya nuna mata a takaice yace "Je kiyi" Jiki na rawa ta mike ta tafi kan darduman ta fara sallah jikinta na rawa, tayi raka'a ya fi sha biyar ita kanta bata sani ba, kawai daga bayanta taji ya fixge hijab din, tun bai karasa cirewa ba ta fara kokuwa da shi ta rike hijab din gam tana kiran Ummanta cikin rikicewa, amma da yayi mata wani riko da hannu daya sai da ta gane Allah daya ne, don ko kwakkwaran motsi kasawa tayi, tana ji tana gani ya fixge hijab din ya jefar da ita kan gado rokonsa ta dinga yi da duk kalman da ya fito bakinta tana cewa "Ina rokon ka da girman Allah kayi hakuri Yaya Abdul, don Allah ka min rai kayi hakuri, in kana yi ma darajan iyayenka kayi hakuri, wallahi ban gama sallan da nake ba...." Ya gama kare mata kallo at the same time yana surveying every bit of her beautiful and breathe taking body, komai yayi masa yanda ya kamata, ashe asalin kyanta na boye all this while bai sani ba, yayi tarayya da mata iri iri amma bai taɓa ganin mace that is so beautiful while naked kamar ta ba, iya haskenta kadai ya isa ya rikita mutum, tuni idanuwansa suka sauya launi ya cire singlet dinsa yana kallonta kasa kasa yace "In ma kika yi taurin kai kece a wahale don that isn't stopping me in anyway Baby gal, just relax and i won't be rough" Kara gigicewa Khaleesat tayi tana rokonsa at the same time tana kokarin sauka daga kan gadon ya fixgota ya mayar da ita saman gadon yana kallonta cikin husky voice dinsa yace "Do not allow me give you a dirty slap...." Bata ma san me yake cewa ba still zata sake sauka taji ya danneta kan gadon, roughly ya fara exploring dinta kamar ya samu er hannu.... [6/13, 9:19 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Ko minti uku Abdul bai yi da fara taɓa ta ba Khaleesat taga ya koma gefe lkci daya, da sauri ta mike tana komawa baya har sannan bata dena kukan da take tana basa hakuri ba cikin rikicewa, after some seconds ya juya ya kalleta da rinannun idonsa, suna hada ido ta kara rikicewa muryarta na rawa cikin kuka take cewa "Don girman Allah kayi hakuri, i am begging you please kayi hakuri" Ya jefa mata wani kallo ya mike kamar zai tashi sama ya nufi kofa ya fice daga dakin, ganin hakan tayi kamar a mafarki ta kasa ko kwakkwaran motsi, kamar ance ta sauke kanta taga jinin da ya ɓata farin zanin gadon da take kai, ta dinga komawa baya a hankali tana kallon jinin babu ko kiftawa zuciyarta na bugawa at the same time, and she realize daga jikinta yake fita, lokaci daya ta tuna rabonta da period tun a Maryland almost a month and some days, from nowhere taji relieve ya zo mata, ta jingina da jikin gadon hawaye masu zafi na sauka idonta, tafi minti biyar a hakan ganin zata ci gaba da soiling zanin gadon ta sauka ta dau hijab dinta ta rungume, har sannan jikinta bai daina rawa ba, tana ta tsaye a dakin tana tunanin yanda zata yi, ta kalli kafarta jin period din yana gangaro mata, ajiye hijab dinta tayi ta shiga bandakin da ke cikin dakin, after few minutes ta fito ta dau hijab dinta ta saka, tana kallon zanin gadon da ya baci ta fara ƙoƙarin cirewa a hankali har ta cire gaba daya, bude kofar dakin taji anyi ta mike tsaye da sauri zuciyarta na bugawa tana kallonsa, ya wani harareta yace "What are you using that for?" Bakinta na rawa tace "A'a wankesa zan yi ne" Yace "Ajiye bana so, zo ki fitar min a daki" Ta sunkuyar da kanta babu musu ta ajiye zanin gadon a gefen gado ta nufi kofa a tsorace kamar munafuka, amma ta kasa bin gefensa ta fita daga dakin saboda fargaba, gashi he is blocking the way, ta fi 30 seconds tsaye zuciyarta na bugawa ta kasa fita, shi dai kallonta kawai yake babu yabo babu fallasa, da kyar tace "Zan wuce" Ganin kallon da yake mata bata sake cewa komai ba haka nan ta raɓa ta gefensa ta fita daga dakin, kallon inda ta tsaya yake don nan din ma dai sai da tayi staining dinsa da jini, ita dai tuni har ta shige dakin da aka fara ajiyeta ta tafi bandaki da sauri tana jin maranta na kullewa, ita da ko ciwon mara bata yi sai dai wani lkcn tayi ciwon baya ko kafafuwanta su rike shi ma kawai na 'yan awanni ne, ta samu dai ta wanke jikinta ta fito tana dukawa sbda ciwon da take ji a mara, a haka ta bude closet din da ya nuna mata tana duba ko zata ga pad, amma taga babu alamarsa, ta fara tunanin yanda zata yi gashi tana jin alamar saukan period din nata a jikinta, ita ko da kyalle ne idan ta samu zata iya manage da shi, amma duk dube dubenta bata ga alamar akwai kyalle ko dankwali a closet din ba, duk kananun kaya ne, she was so confuse and in pain at the same time, ta rasa yanda zata yi, sai da tayi sahu ya fi a kirga zuwa bandaki ta wanke jikinta ta sake fitowa, kuma a haka ba heavy flow take ba a ranan farko, ko zama ta kasa yi ciwon mara ya addabeta, hawaye ya fara sauka idonta ta karasa kusa da gadon dakin ta durkusa ta daura kanta saman gadon ta lumshe ido trying to endure the pain she is feeling, tafi 20 mins a haka taji budewar kofar dakin, da sauri ta dago kanta daga gefen gadon har sannan tana duke, ta kallesa gabanta na faduwa, ya shigo dakin ya ajiye ledan hannunsa yana mata kallon sama har kasa a takaice yace "Me ye ma'anar hakan?" Muryarta na rawa tace "I am having cramps" Yace "Yaushe kika fara cramps? Is this also among ur lies?" Ta sunkuyar da kanta wasu sabbin hawayen na sauka idonta, yace "Bazan sake fita gidan nan da daddaren nan ba saboda ke, after all mate din ki ne ke enduring labor pain" Ita dai bata ce masa komai ba har ya fita daga dakin, sai a sannan ta dago kanta with tears rolling down her face, ta kalli ledan da ya ajiye, rarrafawa tayi zuwa gun ledan ta bude taga Sanitary pad ne, daya ledan kuma abinci ne da ya siyo mata a eatry da bottle water, ta daure ta mike tsaye da kyar bayan ta cire pad daya ta bude closet ta dau sabon underwear dake ciki ta tafi bandaki, bayan ta gyara jikinta ta wanke hijab dinta da yayi staining a bandakin sannan ta fito, rigan bacci wanda ya ɗan fi sauran mutunci ta dauka ta saka, ya saukar mata har kusa da gwiwa, kasa cin abincin da ya siyo mata tayi, haka nan ta bude ruwan goran ta sha sannan ta dau pillow ta ajiye a kasan dakin ta dau duvet din saman gado ta kwanta tana jin ciwon cikinta na tsananta, ita rabonta da ciwon mara tun ranan farko da ta fara period, haka nan hawaye yayi ta zuba idonta, har ta samu bacci ya dauketa taji budewar kofa, taki bude idonta tayi lamo a inda take bugun zuciyarta na tsananta, ya zagayo har inda take ya duka gabanta, hannu ya kai forehead dinta hakan yasa ta bude ido da sauri, magani ya mika mata da ruwa a hannunsa ta sauke idonta sannan ta daure ta mike zaune ta amshi maganin da ruwan hannunsa ta sha, ajiye sauran ruwan tayi a gefenta har sannan ta kasa kallon idonsa, taji yace "Meye da gadon da baki hau ba?" Kai kawai ta girgiza masa yace "Get on the bed now" Tashi tayi ta koma gefen gadon ta zauna, kana ganinta kasan a tsorace take, ya dau pillow da duvet din ya ajiye mata saman gadon, kwanciya tayi ta lulluba da duvet din ta kulle idonta, tana ji ya fita ya kullo mata dakin, ta bude idonta da sauri taga ya kashe mata wutan dakin, hawaye taji na gangarowa ta gefen idonta, gradually taji ciwon maran ya fara subsiding after almost an hour of taking the drug he gave her, daga nan kuma bata san sanda bacci me nauyi ya dauketa ba, wajen karfe ukun asuba yunwa ta farkar da ita, ta mike zaune tana bin dakin da kallo har wani rawa jikinta yake saboda yunwa don rabonta da abinci tun shekaranjiya ga kuma maganin da ta sha babu komai a cikinta, zamowa tayi daga kan gadon tana laluba ledan abincin da ya kawo mata taga ya dauke, rasa yanda zata yi tayi, tana ta zaune a haka kawai taji ya bude kofar dakin hannunsa rike da wayarsa da ya kunna fitila, shigowansa na uku kenan zuwa dakin amma duk bata sani ba tana bacci, haskata yayi da wayarsa ya karaso cikin dakin ya kunna switch din fitila, ita dai ta sunkuyar da kanta kamar munafuka tana jin zuciyarta na throbbing, yace "Me kike yi a nan?" Sai a sannan ta daga kai da kyar ta marairaice amma bata ce komai ba, ya daure fuska yace "Nace me kike yi a nan?" Da kyar tace "I am hungry" Yace "Me yasa baki ci abincin da na kawo maki jiya ba?" A hankali tace "Na kasa ci" Juyawa yayi ya fita daga dakin, ta lallaba ta koma saman gadon ta kwanta tayi lamo, after almost 10 mins sai gashi ya dawo dakin da abincin bayan yayi microwaving din mata, nan kan bedside drawer ya ajiye mata abincin da ruwan gora, bata jira yace mata komai ba ta mike zaune tana sunkuyar da kai kamar mara gaskiya ta kai hannu ta dau abincin, shi dai yana tsaye yana kallonta, a hankali ta fara cin abincin har sai da ta ci rabi sannan ta kallesa cike da karfin hali tace "Na koshi" Yace "Cinye sa" Bata masa musu ba ta ci gaba da cin abinci har sai da ta cinye, amma fa da kyar ta dinga turawa, ta ajiye plate din a saman beside drawer, juyawa yayi ya fice bayan ya kashe wutan dakin, Khaleesat ta koma ta kwanta tayi lamo kan pillow, ta ma rasa wani tunani zata yi at this point, ta goge hawayen da taji yana gangaro mata, ba ita ta koma bacci ba sai da aka yi sallan asuba. Wajen karfe bakwai na safe ta fito daga wanka daure da towel tana tafiya a hankali ta bude closet din dakin tana tunanin abinda zata saka, kana kallon fuskarta kasan tana cikin damuwa me tsanani, fargabanta yanxu idan ta gama period ya kenan? Ta ina zata fara nema ma kanta solution yanxu, what next? ta fashe da kuka a hankali tana jin kirjinta na mata zafi, ta jingina da closet din tayi kukanta me isanta tana tausayin rayuwarta, daga karshe ta goge hawayenta a sanyaye ta dau wata riga wanda har kasa ne amma it's transparent, ajiyewa tayi gefen gado ta cire hair net din dake kanta tun shekaranjiya, tana tafiya a hankali ta karasa gaban madubin dakin, turarurruka iri iri ne da mayuka, da man kai, ta dau turaren jiki kadan ta shafa sannan ta shafa ma kanta man gashi don tana barin sa ya kara kwana daya a haka bata shafa mai ba duk tangling zai yi barin dama cukuikuyesa kawai tayi cikin Hair net din Aunty Farida, ita ma Aunty Farida haka gashinta yake, infact dukkansu har Umma da su Islam duk texture din gashinsu daya, tana cikin shafa ma gashinta oil aka bude kofar dakin, still tayi a inda take gabanta ya fara faduwa, taki yarda ta kalli direction dinsa, da kyar ta ajiye oil din hannunta ta dau Hair net zata mayar da gashinta ciki, taga ya amshe net din a hannunta ya juyo da ita yana kallonta, ta sunkuyar da kanta kirjinta na heaving shi dai kallonta kawai yake, short ne kadai jikinsa shi ma da alamar he just took his bath, ya jawota jikinsa ya daura goshinsa saman gashinta at the same time yana shafa dogon baƙin gashinta a hankalin, Khaleesat ta runtse ido zuciyarta na bugawa, murya can kasa taji yace "Why did u change ur mind abou me? It's all my fault right?" Jin bata ce komai ba ya dago kanta yana kallonta, kawai jin bakinsa tayi a nata bayan ya lumshe idanuwansa, tsoron turje masa take yi don bata san me zai biyo baya ba idan tayi hakan, jikinta ya dinga rawa kamar me zazzabi hawaye na sauka idonta tana girgiza masa kai amma ta kasa cewa komai kar ya mareta kamar yanda ya saba, a haka ya ja ta zuwa saman gadon dakin yana sarrafata, he made sure he romanced her deeply to the extent that sai da ya birkice mata kamar ba shi ba, daga karshe kuma ya kyaleta kar ya kasa controlling kansa gashi tana period, amma fa sosai ya iya kai zuciyarsa nesa kafin ya kyaleta ya koma can edge din gadon yayi rub da ciki tare da lumshe idonsa, everything about Khaleesat is just perfect for a Man, laushin jikinta kadai ya isa ya kara gigita mutum, Khaleesat ta koma daya side din gadon a hankali take kukan takaici faduwar gabanta ya tsananta, juyawa yayi ya kalleta after some minutes yaga yanda dogon gashinta ya rufe duk fuskarta tana kuka, sai kuma ta zamo a hankali daga saman gadon ta kife kanta da jikin gadon tana shessheka, ji tayi ya dafata ta juyo a firgice tana komawa baya don bata san sanda ya zagayo ba, ya sa hannu biyu ya maida duk gashinta zuwa gefen fuskarta yana kallonta, tuni ta daina kukan da take saboda tsoro, ta sunkuyar da kanta kirjinta na heaving, jawota yayi jikinsa ya rungumeta ya lumshe ido, ita dai tayi tsit tsabar firgici, a haka ta dinga jin bugun zuciyarsa tana jikinsa, they were like that for 3 mins daga karshe taga ya mike a hankali ya fita daga dakin ta bi sa da kallo tana share sabbin hawayen dake sauko mata a fuska, throughout ranan haka Khaleesat tayi ta zama a daki sai dai ya kawo mata abinci, da ta tuno abubuwan da Abdul yayi mata daxu sai ta firgita, sai ya zama kamar tana hallucinating ne, hakan ya dinga sa mata ciwon kai taji kamar zazzabi zai rufeta, saura kadan panic attack ya kamata a dakin banda Allah ya takaita mata, gaba daya yanxu tunanin menene makomar rayuwarta take, shikenan haka zata hakura tayi zaman aure da Abdul ta ci gaba da shanye duk bakin cikin da zai kunsa mata a zaman aurensu bata da me tsaya mata tunda shi din mijinta ne? Did she even have a way out with the way things turn out to be all of a sudden? Is this going to be the beginning of a new era a rayuwarta? Shikenan irin rabuwar da zata yi da su Housemate dinta kenan? Kilan ma ba lallai ta sake ganinsu ba a rayuwarta? Shikenan haka Abdul zai ci gaba da caging dinta a gidansa ga threatening din kashe mata siblings da yayi idan taki zama da shi? Duk wa ennan tunanin suka sa ta dinga kuka tana tausayin sabuwar rayuwar da take kokarin fadawa, don tasan Abdul na gane ta gama period bazai daga mata kafa ba and that is the end of her, kuma shikenan dole ta zauna tayi zaman aure da shi ko da yankan naman jikinta zai dinga yi kuwa don azabtarwa, tunda Ummanta ta haifeta tana jin bata taɓa shiga irin wannan tashin hankalin da take ciki ba a wannan lokacin, tana jin alamar zai shigo dakin take goge fuskarta ta langwabe a zuwan ciwon ciki take.... Cikin wannan yanayin Khaleesat tayi kwana uku a gidan tare da Abdul, a wannan kwanaki ukun kuwa duk da halin da take ciki a haka yake sakawa taje tayi masu girki a kitchen wai shi baya son abincin restaurant, Khaleesat bata taɓa fatan kar period dinta ya dauke ba kamar irin wannan lokacin, she wish she will keep on flowing continuously like the woman with the issue of blood amma tasan dole ya dauke nan da kwana biyu don bata wuce 5 days in tana period, sosai hankalinta ke kara tashi idan ta tuna hakan, yau tunda gari ya waye tayi wanka ta saka pad take kwance kan gado saboda azababben ciwon kan da take, all these pass days bata wani samun baccin kirki da daddare tsabar damuwar da ta saka ma kanta da tunane tunane, daga karshe dai haka ta daure ta fita zuwa kitchen da kyar don dora breakfast kafin ya fito daga dakinsa kamar yanda yayi mata umarni 2 days back, tana fita parlor ta leka compound din gidan taga babu motarsa alamar ya fita, ta murda kofar parlon taji a kulle kamar yanda tayi tunani, Zaunawa tayi kan kujera ta dafe kanta hawaye masu zafi na zuba idonta, after a while ta mike tana shesshekan kuka ta wuce kitchen din, tana cikin hada breakfast taji alamar shigowar motarsa gidan, after a while aka bude kofar parlon, ƙasa kunne tayi jin kamar muryar mace take ji a parlor, can kuma taji tsit, ita dai ta ci gaba da abinda take yi jiki babu kuzari har ta gama ta tsaftace kitchen din sannan ta juya zata fito ta kusa cin karo da wata mace in her late 30's zata shigo kitchen din, daga sama har kasa matar dake tsaye kofar kitchen din take mata wani irin kallo da za a iya kira da kallon kaskanci, ita dai Khaleesat tunda ta kalleta sau daya ta sunkuyar da kanta ita kanta bata san sanda ta gaisheta ba don duk ta rude gashi kuma taga suna kama da Abdul duk da bai taɓa nuna mata wani nasa ko da a hoto ba, a walakance matar tace "Da ban kwana ba zaki gan ni munafukar Allah, Er gidan matsiyata ma ci amana.... A gidan ubanki kika san ni da zaki gaisheni?" Sai a sannan Khaleesat ta sake daga kai tana kallonta da mamaki cause kalmomin matar kawai a bazata suka zo mata, bata san sanda tace "Ki zageni amma banda iyayena...." Bude baki Meema tayi da mamaki tana kallonta ganin guts dinta, kafin tace komai Khaleesat ta bi gefenta zata fice daga kitchen din wanda saura kiris ta bangajeta wajen fitan, cikin zafin nama da bacin rai Meema ta fincikota ta dawo da ita gabanta sannan ta sauke mata wani wawan mari ta shakota tana kokarin kai ta kasa ta nakadi banza, Khaleesat ta kwala wani kara, dai dai isowan Abdul wajen, lkci daya yanayinsa ya canza don a kan idonsa yayar tasa ta sauke ma Khaleesat mari sannan ta shakota tana kokarin dukanta, cikin daga murya yace "Zo ki fita ki bar min gidana Amina, how dare you? Me tayi maki zaki mareta haka? Baki da hankali ne? Get out of my house pls, fita ki bani waje" Sake baki Meema tayi tana kallonsa babu ko kiftawa, cikin zafin nama ya tafi ya bude kofar parlon kirjinsa na sama da kasa yace "Ki fita nace Amina kar in rama mata" Cikin karfin hali Meema ta dafe kirjinta da hannu daya tace "Abdallah ni kake cewa in fita a gidanka?" Ya jefar da wayar hannunsa yana huci ya nufeta kamar zai kai mata duka cikin daga murya yace "Na ce ki fita din ko gidanki ne? Get out of this house before i loose my control Amina, gerrout" Ita dai Khaleesat makalewa tayi jikin kofa jikinta na rawa, sum sum sum Meemah ta karasa ta dau handbag da karamin travelling bag dinta don dama daga airport yaje ya daukota saukanta garin kenan, ta nufi kofar fita parlon sannan ta juya tana kallonsa da mamaki tace "Abdallah ni kake daga ma murya kake cewa in fita in bar gidanka akan wancan matsiyaciyar? Har kake ikirarin zaka kai min hannu? Ni din Abdallah?" Da karfi yace "Duk nayi, fitaa ki bar min gidana malama" Fita tayi daga parlon ya bi bayanta kamar zai tashi sama ya tafi ya bude mata gate din gidan, ta fita yayi banging gate dinsa ya kulle, har ya dawo parlon Khaleesat na makale jikin kofa ita tsabar yanda ta tsorata ma ko digon hawayen marin da Meemah tayi mata babu a idonta, ya karasa kitchen din yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi, sai a sannan taji hawaye ya fara zuba idonta. [6/14, 9:16 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Juyawa Abdul yayi ya fice daga kitchen din ba tare da yace mata komai ba ya dau wayarsa ya nufi dakinsa, Khaleesat ta bi sa da kallo tana goge hawayen dake zuba idonta har ta dena hango sa, jingina tayi da kofar kitchen din ta kai hannunta fuskarta dai dai inda Meemah ta mareta don sai a sannan ta fara jin zafin marin, fashewa tayi da kuka tayi me isarta kafin ta fito daga kitchen din tana tafiya a hankali ta tafi ta zauna kan 1 seater dake parlorn tana share hawayen da yaki tsaya mata, abubuwan da Abdul yayi ma Meemah ne suka dinga dawo mata a kai don hakan yayi mugun shock dinta, but she just don't want to believe senior sister dinsa yayi harrassing haka har da koranta, to ko dai ita ce Aunty Aminan da suke ce ma Meemah don taga sosai suke kama da ita, tana ta zaune parlon bayan wani lokaci sai gashi ya fito daga dakinsa, sunkuyar da kanta tayi tana wasa da fingers dinta, ya karaso cikin parlon yace "Kin yi breakfast din ne?" Da Authoritative voice yayi tambayar yana kallonta, hakan yasa ta ɗan rikice kamar mara gaskiya ta girgiza masa kai with fear all over her face, sai kuma ta mike da sauri ta nufi kitchen ya bi ta da kallo har ta shiga ciki, shayi rabin cup ta hada sannan debi Irish kadan a plate don tension yasa ta rasa appetite dinta gaba daya , sai kuma ta tuna shi ma bata basa breakfast din ba, tunanin ko ta kai masa parlor ta fara yi don a kwanaki ukun nan Bedroom dinsa take kai masa breakfast din kamar yanda ya umarce ta, kamar munafuka ta makale jikin kofar kitchen din tana kallonsa tana son tambayarsa ko ta kawo masa breakfast din nasa parlorn amma ta kasa don bata san me zai ce ba kar yayi mata masifa, wayarsa kawai yake dannawa bai ma san tana wajen ba, juyawa tayi a hankali ta koma kitchen din a sanyaye ta hada masa breakfast din ta fito da shi parlor, jikin kujera ta tsaya a hankali tace "Ga breakfast din nan" Daga kai yayi ya kalleta, gabanta ya dinga faduwa ta sauke idonta daga kallonsa, jin bai ce komai ba yasa ta karasa har gabansa ta duka ta ajiye masa breakfast din, yace "Ke ina naki?" Taki barin su hada ido tace "Yana kitchen" Yace "Dauko" Mikewa tayi ta tafi ta dauko nata ta dawo tana kallonsa, yace "Ajiye ki ci a nan" Bata masa musu ba kanta a kasa ta zauna gefensa da ya nuna mata ta fara tuttura irish din kamar dole tana satan kallonsa ta gefen idonta, a hankali taga ya jawota jikinsa taji gabanta yayi mugun faduwa, calmly yace "I am a monster to you right?" Da sauri ta girgiza masa kai zuciyarta na bugawa, yace "Gashi nan, kin maida ni dodonki" Ita kanta bata san sanda hawaye ya cika idonta ba, yayi kasa da murya yana zame hulan kanta yace "Now tell me what u want from me, tell me what's on ur mind.... amma before then ki sani bazan taɓa rabuwa da ke ba saboda ina son ki Khaleesat, rabuwa dake will be the last thing i will do on earth no matter what, You know i love you genuinely from onset, i loved you wholeheartedly and i gave u the best of everything I could, i loved you even before you become the woman you are today, i love you since when u were just a 15 year old teenager tun baki girma ba, yea i know about my flaws but loving you is all that matters, not in the sense that abubuwan da nake yi are right, i am obsessed with you Baby, may be you can change me in ur own way...." Khaleesat ta rufe idonta tana jin kamar ta fashe da kuka, jin kalamansa take kamar ana soka mata mashi a kirji, Ya dora forehead dinsa a nata murya can kasa yace "Why not give me a chance and forgive my flaws Khaleesat?" Bude idonta tayi hawaye suka hau zarya a idonta, har cikin ranta taji bata son jin maganganun da yake mata, a hankali yace "Forgive me, i know i wronged you in all ways, but don't forget ina sonki, ina kuma sonki ne saboda Allah, they are many beautiful ladies out der buh i chose you Khaleesat" Lokaci daya gaba daya tunaninta ya tafi kan Housemate dinta, kasa daurewa tayi ta fashe da matsanancin kuka, ya daura kanta a saman shoulder dinsa patting her softly, ta dinga kuka kamar an aikota, shi dai bai ce mata komai ba, sai da tayi kukan me isarta sannan ta hakura don kanta tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, ya daga kanta yana kallonta taki yarda su hada ido, breakfast dinta ya ajiye mata a kusa da ita, ba musu ta fara ci a hankali da tunani iri iri a ranta, muryarsa taji ya daki dodon kunnenta "Yaushe zaki gama period?" Gabanta yayi mugun faduwa, ta ajiye cup din shayin dake hannunta ba tare da ta kallesa ba, a hankali tace "Ai ban dade da farawa ba" Yace "Yau kwana hudu da farawan ki" Da kyar ta dake tace "A'a, uku ne.... first day din ai bana yi sosai..." Yace "Saura kwana nawa ki gama kenan?" Sosai gabanta ke bugawa, ta sunkuyar da kanta cike da karfin hali tace "Kilan nan da kwana uku ko hudu" Jin bai ce komai ba ta daga kai a ɗan tsorace ta kallesa, taga kallonta yake without blinking, sauke idonta tayi tana wasa da karamin cokalin dake cikin mug din shayinta, ya dauke shayin ya mayar gefe, taga ya kai hannu shoulder dinta zai sauke siririn hannun rigar dake jikinta, sosai hankalinta ya tashi amma bata ce masa komai ba gabanta na ci gaba da faduwa, ya sauke rigan gaba daya yana kallon bare chest dinta, hawaye ne ya cika idonta taki yarda su hada ido, can dai tayi karfin hali muryarta na rawa tace "Toh baka sha shayin ka ba zai huce" Yayi kasa da murya yace "Wa ennan zan sha... " Momy ce tsaye parlor tana kallon Meemah dake rusa kukan bakin ciki uwa er yarinya, ga trolley dinta a gefenta, bacin rai ne karara kwance fuskar Momy da idanuwanta suka ƙankance tana huci, mai aikin gidan ce ta shigo parlon rike da bowl din pepper soup din da tayi ma Momy, cikin ladabi ta risina tace "Hajiya ga farfesun nan ya kammala" a fusace Momy ta figi throw pillow ta jefa mata tace "Don ubanki wuce ki ban waje ke da farfesun, baki ga magana nake bane zaki shigo min parlor kai tsaye, yau ga jahilar mata kai" a tsorace mai aikin ta juya da sauri ta bar parlon ta koma kitchen ta kullo kofar, Momy tace "Na kusa daina daukan tsinannun masu aikin nan don sun isheni haka kuma, na kori wancan shegiyar da ta shigo min parlor da yan uwan Alhaji da suka zo daga kauye babu izinina yanxu kuma an kawo min wannan jakar da ko kwana biyu bata yi ba ta fara nuna halayyan dabbobi" Ita dai Meemah kuka kawai take tana fyace hancinta da handkerchief, tsabar kuka idonta har sun suntume, Momy ta kara kankance idanuwanta tana kallon Meemah tace "Shi Abdallahn ne yayi maki haka Meemah?" Meemah ta hadiye wani abu da ya tokare mata wuya don bakin ciki tace "Momy da kin ga tijaran da Abdallah yayi min akan yarinyar nan ko, hmmm, ki bari kawai Momy, Momy kare bazai ci abinda Abdul yayi min ba, bayan zagi da cin mutunci wai ni ya kora a gidansa, kora irin ta walakanci" Momy ta zauna kan kujera with disbelief, duk da AC dake aiki a parlorn sai zufa take yi dama ga ta narkekiya, tana gyara zama tace "Ko dai ya sha wani abu ne Meemah??" Cikin rawan murya Meemah tace "Babu abinda ya sha wallahi Momy don lafiyan Allah ya dauko ni a airport muna ta hira, tare fa da ni duk aka yi tracking yarinyar nan tunda akwai wani tsohon saurayina wanda aikinsa kenan, amma wai yau akanta Abdallah zai min irin wannan tijara haka tun ba aje ko ina ba, duka duka fa kwananta yau hudu da shiga hannunsa, amma ya rufe ido ya zazzageni ya ci min mutunci ya koreni" Momy tayi wani murmushin takaici tana girgiza kafa tace "Kin ga abinda nake ta gudu kika kasa ganewa kenan ai ko? Dama ance duk abinda babba ya hango yaro ko uban me zai hau bazai taɓa hangowa ba wallahi, ba ya kwana da ita ba dole ki ga abinda yafi haka ai, babu yanda banyi in lalata batun auren nan ya hakura ba amma sam Meemah kika ki bani hadin kai ki ka koma bayan Abdallah, har da bin wasu malamanki da basu taka kara sun karya ba duk don yarinyar ta shigo hannunsa, to ai ta shigo kuma kin ga abinda ya biyo baya daga shigowarta, to wallahi zai kai ya kawo wataran Abdallah yace bai san mu ba akan yarinyar nan, ni na haifesa ba wani ya haifar min shi ba sarai nasan abinda zai iya aikatawa" Meemah ta dinga kallon Momy babu ko kiftawa don ita sai yanxu ta kara fahimtar dalilin Abdul nayi mata irin wannan mugun tijara kan yarinyar da yake ta ikirarin zai koya ma lesson idan ta shigo hannunsa, sarai kuwa ya kwana da ita dole ya birkice haka ya haukace kanta, dama buzaye da aka sani da mugayen asiri, Meemah tayi wani murmushin takaici tace "To kuwa yanda nayi ruwa nayi tsaki har sai da yarinyar nan ta shiga hannunsa to haka zan yi har sai ya rabu da ita a kwanan kuwa ba da jimawa ba" Momy ta kwado ma sabuwar me aikinta kira, matar ta taho a guje har sai da tsantsin tiles ya kwasheta sbda ruwan dake kafarta sai ga ta a kasa timmm, A fusace Momy tace "Wallahi tallahi kika kuskura kika illata min tiles sai na cire cikin kudin albashinki, yau naga er iskar mata kawai, kullum na kiraki sai kin azabtar min da tiles saboda kauyanci? Wannan wace irin mata Adama ta kawo min haka da sunan me aiki?" Har kasa mai aikin ta zube tana ba Momy hakuri, cikin tsawa Momy tace "Miko min wayata dallah ki fita ki bamu waje, er kauyen banza" Mai aikin ta kalli wayar dake kan center table dab da inda Momy ke zaune, ta karasa da sauri ta dau wayar ta mika ma Momy, Momy ta warce, mai aikin ta bar parlon, Momy ta mika ma Meemah wayar tace "Dubo min lambar Godiya, glasses dina yana daki" Meemah ta amshi wayar ta dubo number aminiyar Momy sannan tayi dialing ta mika mata, a kashe suka ji wayar, Momy tace "Tayi tafiya me muhimmanci kenan, bari zuwa anjima in sake kiranta" Meemah da kanta ya gama kullewa tace "Tabddi jam, lallai nayi babban kuskuren da ban taɓa yin irinsa ba Momy, sai ma fa kinga kayan dake jikinta da naje gidan, tana kitchen tana soye soye" Momy dai tayi shiru tana girgiza kafa don bakin ciki da takaici, can tace "Dauko min gyale da jaka a daki, ina zaman zamana kin janyo min kashe kudin da banyi budgeting ba Meemah, duk ke kika ja min wannan masifa da kika ki jin maganata wallahi, in hada iri da matsiyata akan wani dalili? A farko dai na hakura na zuba masa ido da yaki jin maganata, amma yanxu kuwa wallahi sae ya rabu da yarinyar nan, babu dalilin da zai sa in hada zuri'a da ita, ga kuma rashin adalcin da aka yi ma Alhaji ga asara ga biyan tara" Tashi Meemah tayi ta tafi dauko ma Momy gyalenta da handbag, all this while dama ita ke ta shiga malamai don Khaleesat ta shiga hannun Abdul Momy ko bin ta kanta bata yi tunda dama ba son auren take ba, Momy na ficewa daga gidan da driver dinta Meemah ta tafi dakinta da wayarta tayi dialing number Malamin da tasa yayi mata aiki. Runtse ido Khaleesat tayi bayan taji duk maganganun da Abdul yayi, yana rungume da ita saman gadonsa kamar zai maidata jikinsa, it's past 8pm na dare, jin taki cewa komai s hankali yace "Khaleesat" Bude idonta tayi wasu hawaye masu zafi suka silalo fuskarta tace "Um" Yace "Say something" Still tayi shiru hawaye na zuba idonta don bata ma san me zata ce masa ba at this point, ya dago kanta yana kallonta yayi kasa da murya yace "Say something pls" Da kyar muryarta na rawa tace "Ban san me zan ce ba" Yace "Say anything" Shesshekan kuka ta fara yi masa tana jin zafi a zuciyarta, me kuma yake son ta ce masa, tunda yace bazai taɓa rabuwa da ita ba ko me zai faru, meaning dole ko tana so ko bata so haka zata ci gaba da rayuwa da shi a matsayin mijinta, so me yake son ta ce, ta dai dake da kyar har sannan muryarta na rawa tace "Kawai alfarma daya zan nema wajenka" Murya can kasa yace "Say it Khaleesat" Tayi karfin halin cewa "I don't want you to hurt anyone because of me...." Kasa ci gaba tayi tana kuka a hankali, ya dinga kallonta don sarai yasan su wa take nufi, Calmly yace "Ohk u mean ur Body Guards that sue me?" Ita dai kuka kawai take, Ya ɗan yi wani murmushi yace "I don't think i will leave dem cause they started everything first, they intruded in what wasn't der business, basu baki labarin harbin da aka yi ma wani dake da alaka da su ba, I mean Salem..." Khaleesat ta daga kai da sauri ta kallesa hawaye na sauka idonta gabanta na faduwa, lkci daya ta tuna sanda Aunty Farida ke sanar mata Ajay yace mata an harbi wani abokinsu a kano, yana wani murmushi yace "To su ma ana nan ana targeting din su, amma in kince in kyalesu i will do that under 2 condition..." Khaleesat dai kallonsa kawai take ta kasa cewa komai duk jikinta yayi sanyi, yace "The first condition is that.... zaki yi magana ta waya da su ki gaya masu ke za ki zauna da mijin ki they should back off, sannan ki gaya masu su janye karan da suka kai kotu..." Bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka ba, ya dinga kallonta sai kuma yayi murmushi yace "Baza ki yi ba kenan?" Muryarta na rawa tace "Ban ce bazan yi ba" Wayarsa ya dauko ya mika mata yana kallonta, da kyar tace "Bani da number ai" Yace "Amma aunt dinki na da shi ai... Call her and ask her to send you the number" Ta girgiza masa kai tana jin kamar numfashinta zai dauke sbda rikicewan da tayi bayan ya fadi conditions dinsa, cikin kuka tace "Bani da numberta offhand" Yace "Ni ina da shi, i will call her now sai ki gaya mata ta turo maki number daya daga cikinsu, and mind you kada ki kuskura ki ce mata komai, number kawai zaki yi requesting ta turo maki" Ta fashe masa da kuka sosai tace "Why are you doing this plss Ya Abdul" Yace "Ohk, i will revenge and nothing is gonna stop me, i promise you this, shi abokinsu da aka harba ai yayi surviving, i hope they survive too....." Tana kuka sosai tace "No plsss..." Wayar ya dauka yayi dialing number din Aunty Farida yana fara ringing ya mika mata yana kallonta. [6/17, 7:43 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Har Aunty Farida ta ɗaga kiran Khaleesat bata amshi wayar da Abdul ke mika mata ba hawaye na zuba idonta, lkci daya ya hade rai yana mata wani irin kallo, babu shiri ta amshi wayar hannunta na rawa, a sanyaye tace "Aunty" Cikin rikicewa Aunty Farida tace "Khaleesat?" Khaleesat ta sauke idonta tayi shiru, hankali tashe Aunty Farida tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Khaleesat kina ji na? Don Allah kiyi magana, Hello Khaleesat" Khaleesat ta kasa ce mata komai hawaye masu zafi na sauka idonta, kiris ya rage ta fashe mata da matsanancin kuka a wannan lokacin, Abdul ya fixge wayar yayi a hannunta ya katse yana mata wani mugun kallon da ya tsorata ta sosai yace "Are you daring me?" ta fashe masa da kukan da take dannewa tana girgiza masa kai, a fusace yace "Ohk then, since abinda kika zabar masu kenan to ina me tabbatar maki zan aikata hakan nan ba da jimawa ba kuwa, sannan bayan nayi zan sanar maki, don bani da imanin kyale duk wani mahalukin da yace zai shiga hurumina, i don't mind sending that person to his early grave, and mind you.... i will so deal with them yanda in their next life baza su kara shisshigi akan abinda bai shafesu ba, if you think i am bragging watch and see, bani da conscience...." Khaleesat ta girgiza masa kai cikin karfin hali tace "Duk ba sai ka masu komai ba, zan yi abinda kace" Wayar ta amsa a hannunsa ta cire a Flight mode din da ya saka sannan ta sake dialing number Aunty Farida, yana fara ringing Aunty Farida ta daga da sauri tace "Khaleesat, kina ji na Khaleesat?? Hello" Khaleesat ta dake ta hadiye sauran kukanta cike da karfin hali tace "Na'am Aunty" Cikin tashin hankali Aunty Farida tace "Kina ina Khaleesat?" A hankali Khaleesat ta daga kai ta kalli Abdul taga ya wani murtuke fuska yana kallonta kamar bai taɓa fara'a ba a rayuwarsa, ta sunkuyar da kanta wasu sabbin hawayen na zubo mata cikin sanyin murya tace "Aunty Number Ahmad za ki turo min yanxu plss" Aunty Farida da duk ta rude tace "Ahmad kuma Khaleesat? Wanene Ahmad? Kina ina ne yanxu?" Shi dai Abdul wani devilish look kawai yake mata, tayi kasa da murya tace "Aunty Number Junaid zaki turo min" Da sauri Aunty Farida tace "To bari in turo maki yanxun nan" Katse kiran Aunty Farida tayi cikin rawan jiki ta tura ma Khaleesat number Ajay, number na shigowa Abdul ya amshe wayar a hannunta yana kallon number for almost 5 seconds, can yayi wani murmushi ya mayar mata da wayar, cike da isa yace "Kirasa ki gaya masa abinda nayi instructing din ki" It took Khaleesat almost 30 seconds kafin ta iya dialing number Ajay, shi ma saboda irin kallon da Abdul ke mata ne, exactly irin kallon da yake mata in zai gaura mata mari, cikin muryarsa dake tsoratata taji yace "Kika kuskura kika yi magana da wata muryar da ba normal voice dinki ba zaki sha mamaki wallahi, and immediately he picks just go straight to ur point, do not give him a breathing space to say anything to you, go straight and tell him kin hakura zaki zauna da mijinki, kin ji me nace maki?" Ita dai bata ce masa komai ba hawayen takaici na zuba idonta, sai da kiran ya kusa katsewa Ajay ya daga, ta ɗan kalli Abdul da bai fasa mata wani irin kallo ba, da kyar ta daure tace "Hello, good evening....." Mikewa Ajay yayi jin muryarta, bata jira ya gama processing ba ta ci gaba a hankali tace "Dama ina son in ce maka ni na hakura zan zauna da mijina, and i appreciate all what you've done for me kai da Yaya Jawwad, thank you so much" Ajay ya juya ya kalli Jay da shigowar sa dakin kenan, as if counting his words yace "Come again!" Yana fadin haka ya saka wayar a handsfree sannan ya nufi Jawwad yana kallonsa, Khaleesat ta kalli Abdul, sai kuma ta sunkuyar da kanta tace "Cewa nayi ni na hakura yanxu, zan zauna da mijina, and thank you for all what you've done for me...." Wasu sabbin hawaye suka hau zarya a fuskarta tana ji kamar ta fashe da kukan dake cin ta, Abdul ya fixge wayar a hannunta ya katse sannan ya kashe wayar gaba daya, Ajay ya kalli Jay that looks speechless and shock at the same time, lkci daya ya jefar da wayarsa saman gado, cikin nutsuwa yace "Nayi da na sanin bata lokacina akan yarinyar nan, i regret wasting my very precious time...." Jay ya ma rasa me zai ce, walking slowly ya karasa gaban window din dakin yana kallon Ajay that was boiling from inside, a hankali yace "Look Ajay, i think those words are not coming from her heart, sakata yayi ta fadi hakan pls mu yi mata uzuri, she is forced to say all what she said, ba mu san situation din da take ciki ba let consider that plss" Ajay ya masa wani kallo yace "Billah na cire hannuna a lamarinta kaji na rantse Jay, i have nothing to do with her case again, after all i was just doing it just for the sake of humanity not because of her, ko kasheta yake ya kamata ta gaya mana haka? Mu zata dauka for granted? Beside she spoke confidently meaning she is okay with what he asked her to say, i am leaving this state first thing tomorrow morning, so unfortunate i waste my time on the brat, don taga mun yi stooping kan mu so low shi yasa ta dauke mu for granted" Yana kai wa nan ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, Jay ya lumshe ido ya bude don bai san me zai sake ce masa ba da zai sa ya sauraresa, kuma tunda har ya rantse magana ta kare, ya zare hannunsa kenan babu abinda zai sa ya sake involving kansa, zaunawa yayi gefen gado ya dafe kansa da yaji ya masa nauyi, at the same time letting out a sigh, kalmomin Khaleesat ne suka dinga dawo masa kai, he felt really disappointed in her too, but can kasan zuciyarsa tausayinta ne ya mamayesa ya kuma yi mata uxuri, ya rasa menene yasa shi shiga yanayin da ya shiga a wnn lkcin, da kyar dai daga karshe ya mike ya fita daga dakin yana tafiya a hankali. Daren ranan nan Khaleesat bata yi baccin awa biyu ba cikakke, da bacci barawo ya saceta zata farka a firgice, bata taɓa jin abu ya tsaya mata a rai irin abinda Abdul ya sa tayi ma su Housemate dinta ya tsaya mata ba, gashi ko digon hawaye yaki fita idonta, her heart is just heavy, but did she have a choice? In bata yi hakan ba yayi ma su Housemate dinta wani mugun abu ai bazata taɓa yafe ma kanta ba, tunda har yake ikirarin ba shi da imani babu abinda bazai iya aikatawa ba, tasan kuma sarai zai iya aikatawa din, tunanin sabuwar rayuwar da take kokarin fadawa take, is she going to survive this at all? Is this not going to be her end? A ranta taji kilan lokacin mutuwarta ne ke tinkarota, sai a sannan taji hawaye masu zafi for the first time a idonta, ta kai hannu a hankali tana sharewa ta juya tana kallon Abdul dake baccinsa hankali kwance, dai dai nan alarm din wayarsa ya kada, ta juya da sauri tayi backing dinsa tana goge hawayen da ya fara zubo mata sosai, after some seconds taji alamar ya tashi yana karanto addu'an tashi bacci, ita dai hawaye kawai take, sai da taji yayi sallah ya fita daga dakin sannan ta mike zaune tana kuka a hankali. Nenne ta bude hannu tana kallon su Aunty Farida cikin nutsuwa tace "To kun ga ai baza mu shiga hurumin Allah ba, ko akwai me tsaurin idon da zai shiga a cikin ku? Allah Ubangiji ne kadai yasan daliliin da ya maidata hannun mijinta cikin ruwan sanyi babu tashin hankali, to don me za mu shiga hurumin da ba namu ba? A'a gaskiya banda ni tunda ni dai nasan wanene Allah, kuma shi kadai yasan hikimarsa ta yin hakan, da yasan Khaleesah zata cutu hannun Awdul da bazai fara basa sa'ar sungumeta ba don bamu fi sa sani ba, ko ba komai ɗa na zai samu kwanciyar hankali ya ci gaba da sabgogin rayuwarsa kamar ko wani ɗan adam, mu mun yarda da kaddara mummuna ko kyakkyawa tunda mu musulmai ne, kuma duk abinda Allah yayi mu din banza za mu ce don me, domin haka nake cewa Allah ya bata zaman lafiya da mijinta, ɗan halayyarsa da yake yi mara kyau Allah ya gyara sa ya dena, ai babu wanda bai da taɓon wani mugun abu a rayuwar nan, in sun dawo kano mu kuma sai mu je ganin daki mu sa albarka, duk sanda ya bar ta ta zo ta gaida mu a Mariri sai ta zo bakinta alekum, shi kuma Ali Allah ya sa karshen wahalarsa kenan a duniya" Wani irin kallo Aunty Farida ke ma Nenne zuciyarta na tafarfasa, Umma dai kanta na sunkuye bata ce komai ba amma ita kadai tasan abinda take ji a zuciyarta, Mama Zubaida tace "Amma dai Nenne ai ya kamata a bibiyi halin da take ciki, an taɓa tarewa haka kawai a zo a sungumi yarinya a mota da asuba ba a san ko shi din ne ba ko ba shi ba amma duk a rasa me bibiyar hakan, wannan ai abun dubawa ne, tun da mu dai har yanzu bai ce mana shi ya dauketa ba" Nenne tace "To er bakin ciki, shi din ne ya sungumeta ba kowa ba aniyarki ta bi ki, kuma ai halaliyarsa ya sunguma ba wata ba, duk wanda ya sake cewa zai bada shawara a wannan lamari idan ban sa Ali ya sallamesa ba shegiya uwata da ubana suka haifeni, kwata kwata bakwa neman ma ɗa na sauki a rayuwar nan, burin ku kawai tashin hankali ya kashe Ali ku huta ni kuma in shiga uku, ita uwar da ta tsugunna ta haifi yarinyar bata da bakin magana sai ke me baki kamar ta dorinar ruwa?" Mikewa Mama Zubaida tayi ta shige dakinta, Mama Shatu ta kyabe baki tace "To Allah ya kyauta, in ya dawo mana da gawar ta ai sai mu zauna mu yi zaman makoki ba shikenan ba" Nenne tace "Sai dai ki ga gawar er ki Labeebah amma ba Khaleesah ba, kuma bakin cikin da ku ka kasa boyewa ne zai kashe ku ke da Zubaida" Mikewa Umma tayi hawaye cike idonta ta shiga dakinta, Nenne ta kyabe baki ta mike tana kallon Aunty Farida tace "In Ali ya dawo ki ce masa nace ya zo ya amshi tuwo da miyar taushe zan ajiye masa, wallahi wata guda zan yi ina masa girki ya marmaro" Daga haka ta fice daga gidan, Aunty Farida tayi tagumi hawaye cike idonta. Meemah ta shigo parlon Momy ta zauna tana ɗan murmushi, ta jira har Momy ta gama wayar da take yi da aminiyarta godiya sannan tace "Momy na samesa a waya" Da sauri Momy tace "Ya daga kuma?" Meemah tace "Eh ya daga bayan yaga text din da na tura masa kenan" Momy na gyara zama tace "Toh Alhamdulillahi nagode ma Allah, sai yace maki me?" Meemah tace "Kema kinsan dole zai taho ai, amma tsorona daya kada ya kira Daddy kuma ya daga waya yace masa ba haka ba" Momy tayi wani murmushi tace "Bazai daga ba, tunda na riga na gaya masa abinda ke faruwa ai" Meemah ta sauke ajiyar zuciya tace "Alhamdulillah, in ya samu flight yau za mu iya ganinsu a gidan nan" Momy tace "Me zai hana ya samu jirgi, ai da sauran lokaci dole zai samu" Mai aikin Momy ce tayi sallama tana makale jikin kofar parlon duk da a bude yake amma bata shiga ba, hannunta rike da tray me dauke da plate din gasasshen kaza da lemon kwali biyu, Meemah ce ta amsa sallaman tana mata wani kallo tace "Tun da kika ga kofa a bude ba sai ki shigo ba, kin wani raɓe jikin kofa kamar munafuka, don Allah ki dena wannan kauyancin yana damun mu a gidan nan" Momy ta hade rai tana kallonta har ta karaso ta ajiye plate din, cikin ladabi tace "Ga kazar ta kammala Hajiya" Momy tace "Kalan Hijabin nan naki na daga min hankali a gidan nan, kar ki sake saka min shi, in yar wa zaki yi to ki yar bana son shi kwata kwata yayi kalar talauci" Mai aikin ta dukar da kai tace "Toh Hajiya in sha Allah bazan sake sa shi ba, kiyi hakuri" Fita tayi daga parlon da sauri, Momy ta dau plate din tulin kazar da aka ajiye mata ta fara ci tana cewa "Ai dama tunda aka ce min zai taho da ita hankali na ya kwanta, don dama taho da ita shi ne me wuyan...." Meemah tayi murmushi ita ma ta dau yankan kaza daya tana ci tace "I trust you Momy" Khaleesat ta saka Hijab dinta har kasa tana harhada wasu daga kananun kayan dake cikin closet din dakin kamar yanda Abdul ya umarceta tayi, absentmindedly take aikin don tayi nisa a tunanin da take, bude kofar dakin yayi ya shigo, ita dai bata juya ba tana ci gaba da abinda ya sakata, ya karasa har bayanta ya tsaya, taki juyowa gabanta na faduwa, juyo da ita yayi yana kallonta ta sunkuyar da kanta, yace "Me ya sa baki son ki saki ranki har yanxu? Always looking worried" A hankali ta daga kanta ta kallesa amma bata ce komai ba, yace "Kin gama hada kayan ne?" Girgiza masa kai tayi, yace "To gama" ta juya ta ci gaba da abinda take, shi dai yana tsaye yana kallonta, pad ta dauko a karshe zata saka cikin karamin trolley din yace "What are you using that for? Ba yau zaki gama ba?" Taki kallonsa zuciyarta na bugawa tace "Amma ban gama ba ai" Bata jira me zai ce ba ta saka a akwatin sannan ta kulle ta mike tsaye, kamo hannunta biyu yayi yana kallon cikin idonta, speaking slowly yace "Promise me you won't act silly har mu isa kano Khaleesat" Ta rasa dalilin da hawaye ya cika idonta, shi dai kallonta kawai yake, after some seconds yace "If you try anything silly, zaki yi matukar mamakin abinda zan yi, i promise you" Da kyar tace "Toh, amma plss ina son inyi waya da Safiyyah, i am missing her" Yace "Baza ki yi waya da Safiyyah ba, amma idan muka isa kano zan fara kai ki gidanku ki gaishesu sannan mu tafi gidanmu" Ita dai bata ce komai ba hawaye na zuba idonta, a haka suka bar gidan zuwa airport tunda yana da hoton National ID dinta a wayarsa. Da yamma suka sauka garin kano, driver din gidansu har ya iso airport din yana jiransa, Drivern ya bude ma Khaleesat back seat bayan ya gaisheta, kanta a kasa ta shiga motar, kana ganinta kasan tana cikin damuwa sosai gashi ta kara zagbewa gaba daya, Abdul ya shiga ta daya side din, sannan drivern ya shiga motar ya tada suka bar airport din, sai bayan da suka fita daga cikin airport Abdul ya gaya ma drivern inda zai fara kai su, sun yi nisa sosai da tafiyar Abdul ya juya ya kalli Khaleesat da tayi nisa cikin tunanin da take, hannunta ya saka cikin nasa wanda hakan ya dawo da ita reality, ta ɗan kallesa, yayi kasa da murya yace "Are you hungry?" Girgiza masa kai tayi, ya jawota zuwa jikinsa yana kallonta, ita dai bata ce masa komai ba zuciyarta na bugawa, a haka suka isa Mariri wajen karfe biyar da rabi na yamma, Drivern na parking daga opposite din gidansu Khaleesat Abdul ya bude motar ya sauka, jiki a sanyaye Khaleesat ta sauka daga motar, ta ma rasa ko farin ciki zata yi ko akasin haka ganinta a kofar gidansu, Abdul ya bi ta da kallo har ta shiga cikin gidan sai a sannan hawaye suka cicciko mata ido, Noor ce ta fara hangota tana hura gawayi ta taso da gudu ta rungumeta, sai a sannan sauran en gidan duk suka juya suna kallon Khaleesat, Umma dake zaune bakin kofar dakinta ita ma ta dinga kallonta, Mama Zubaida da Mama Shatu suka taɓe baki suna kallon juna, Aunty Farida dake gyara dakin Umma ta fito da sauri jin sunan wanda Noor ta kira, Khaleesat ta tafi ta rungumeta ta fashe da matsanancin kuka, Farin ciki wajen Aunty Farida ba a cewa komai don duk tunanin su Ajay ne suka dawo da ita gida, sallaman Abdul yasa duk suka juya suna kallon hanyar shigowa gidan da mamaki, nan da nan fara'ar Aunty Farida ya bace, su Mama Shatu ne kawai suka amsa masa sallaman, ya karaso cikin compound din, Aunty Farida ta saki Khaleesat ta tafi ta zauna kusa da Umma fuskarta babu yabo babu fallasa, Mama Zubaida ta mike da sauri ta shimfida masa tabarma ita da Mama Shatu na masa sannu da zuwa, ya zauna kan tabarman yana kallon Umma ya gaisheta, Umma ta amsa tace "Sannu da zuwa" Aunty Farida ta mike ta shige dakin Umma, Abdul ya gaida su Mama Zubaida dake ta washe baki, duk suka amsa da fara'a, Ita dai Khaleesat na durkushe kusa da Ummanta kanta a kasa, Abdul ya kalli Umma yace "Baba baya nan ne" Umma tayi karfin halin cewa "Eh bai dawo ba" Ko rufe baki bata yi ba sai ga Malam Ali ya shigo gidan da rabin buhun dankalin Hausa a hannunsa, ajiyewa yayi ganin Abdul da Khaleesat, yace "A'aa, ikon Allah, baki mu ka yi yau a gidan" Abdul ya tashi ya tafi har inda Malam Ali ke tsaye ya gaishesa, Malam Ali ya amsa yana kame kame, ya tafi da sauri ya dauko tabarma ya kara shimfida ma Abdul yace "Yi zaman ka a nan, bari in zubo mana ruwa a buta lokacin Magariba yayi" Da sauri ya tafi ya dauko butoci biyu ya tafi zai debo ruwan, Umma ta mike ta shige dakinta, Khaleesat ta bi bayanta, Nenne ce ta shigo gidan da sallama tace "Allah me hikima, sannunku da zuwa Awdul" Abdul ya gaisheta, ta jawo kujera ta zauna tana facing dinsa tace "Lafiya lau wallahi, ya iyayen naka, ina kokarin daura sanwa kenan sai ga wani almajiri da gudu ya zo ya sanar min ai kun zo, kasan ɗan albarka ne almajirin nan duk wani abu da ke faruwa a gidan Ali kamar kiftawan ido yake rugowa ya sanar min, ni kuma in ina da er dabino kwara uku in basa la'ada, nayi farin cikin ganin ka wallahi, ina matar taka, in ji tare ku ke?" Yace "Tare mu ke" Sai ga Malam Ali da ruwa a butoci yace "Ai ina jin tana dakin uwarta" Nenne tace "Kai kuma lafiya? ina zaka da butocin ruwa ko karfe shidda bai yi ba?" Malam Ali yace "Au? To to bari a ajiye, na zata magariba ta yi" Da sauri ya koma ya ajiye butocin ya dawo, Nenne tayi kasa da murya tana kallon Abdul tace "To Awdallah, ka dubi girman Allah ka rike amanar da muka baka, yanxu kai ne uwarta kai ne ubanta, duk ta kuskure maka ka kawota wajena ni zan san yanda zan yi da ita, kuma albarkacin auren da ya shiga tsakaninka da jikata ka kara ba Mahaifinka hakuri ya yafe ma Malam Ali komai ya wuce a wajensa don girman Allah, don yanxu kam duk mun zama daya tunda ga aure har ya shiga tsakani, Allah Ubangijin ya baku zaman lafiya ya kauda duk wata fitina ya kawo zuri'a dayyaba" Abdul yace "In sha Allah Kaka" Nenne na murmushi tace "To madallah, gashi ko tuwon dare ban yi ba balle in zubo maka" Yace "Ba komai, can gidanmu za mu wuce yanxu yamma tayi" Nenne tace "Gaskiya kam, bari in fito maka da ita ku tafi, go slown hanyar nan bata da kyau" Tashi Nenne tayi ta nufi dakin Umma, kuka kawai Khaleesat take Umma tayi tagumi tana kallonta ta ma rasa abun cewa amma daurewa kawai take ita ma hawayen bai zubo mata ba, don bakin ciki Aunty Farida na jingine jikin bangon dakin ita ma ta kasa cewa komai, a haka Nenne ta shigo dakin ta same su, taɓe baki tayi tace "Ta so ki fita mijinki na waje na jiranki" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba tana kuka kamar ranta zai fita, Nenne tayi kasa da murya tace "Wato a yanda kanwar uwarki ke zube ba mashinshini shekara da shekaru haka kema kike son ki zauna mana tunda kyau kawai gare ku amma babu farin jini, banda samun waje ki samu miji zankadede kamar Awdul amma son zuci irin taki da na uwarki da kanwarta bazai sa ku yi farin ciki da hakan ba, in a baya Awdul ɗan iska ne dama Allah ya taɓa halittar da bai shiryar ba in yayi niyya? Daga yanda Awdul ke magana a kintse na gane ya shiryu wallahi, to ko kawota da yayi ta gaishemu kadai ya isa mu shaida shiriyarsa, wallahi ku dinga jin tsoron Allahn da ya halicce ku, duk wanda burinsa ya raba aure to tsinuwar Allah ne zai tabbata a garesa, kuma in sha Allahu Khaleesat tayi aure kenan mutuwa kadai ne zai rabata da mijinta tunda duk mun san yana sonta, tashi ki fita gun mijinki ku tafi munafuka kawai, duk da can baki san baki son shi ba sai da ya aika ki kasar turawa idonki ya bude a can" Cikin kuka Khaleesat tace "Ni wallahi bana son sa, bana son sa, bazan iya zama da shi ba" Nenne tace "Aikin banza, to uban me ya rage kuma bayan ya kwana da ke? Ai duk rashin son da kike masa dole ki zauna da shi tunda ya kwana dake yau kusan satin ki daya a gidansa ba kuma ajiye ki zai yi yana kallo kamar hoto ba tunda shi ba ɗan iska bane, kuma gidan Ali ba Obalande bane da za a tara masa fararen zawara har biyu a gida, Farida ma kadai ta ishemu, tashi ki fita ki bani waje ko in tafi in kira maki Ali yanxun nan ya fitar min da ke, tun da uwata ta haifeni ban taɓa ganin er da bata son kwanciyar hankalin ubanta ba sai ke" Umma ta share hawayen dake zuba idonta tana kallon Khaleesat tace "Ta shi ki je Khaleesah, Allah ya maki albarka, Allah kuma ya baku zaman lafiya" Mikewa Khaleesat tayi tana kuka sosai ta fita daga dakin Ummanta, Nenne tace "Atoh dai, iya addu'ar da za mu yi mata kenan a matsayin mu na rikakkun musulmai, tun da muka ga haka to Allah ne kadai ya san hikimarsa nayin hakan, kuma dama an gaya min aurenta da Awdul aure ne me kyan gaske in har zata kwantar da hankalinta, gashi mun shaida yana son ta, kuma ta dalilinta arzikin ubanta duk zai dawo har ma ya fi na da, wallahi haka aka ce min, kawai dai babba ba a son yayi ta surutu ne shi sa nake jan bakina nayi shiru" Har suka bar gidan da Abdul hawaye ne kawai ke zuba idon Khaleesat, dubu talatin ya ba kishiyoyin ummanta ko wacce 15k, ya ba Islam 50k, Nenne ya bata 20k, Malam Ali kuwa bai amsa kudinsa ba sai ajiye masa Abdul yayi kan tabarman dake bakin kofar dakinsa, babban tashin hankalin Khaleesat yanxu period dinta da ya dauke, don kafin su taho kano a dari dari tayi sallahn Azahar kar ya shigo ya ganta, tasan yau dai ƙaryar ta ya kare kawai, a haka suka iso gidansu Abdul bayan sallan magrib, Driver na shiga babban compound din da mota Khaleesat taji gabanta ya tsananta faduwa, bayan yayi parking a space din parking Abdul ya sauko daga motar yana kallonta, da kyar ta iya saukowa daga motar zuciyarta na bugawa sosai wanda ita kanta bata san dalilin hakan ba all of a sudden, ya fara tafiya tana bin sa har suka isa entrance din shiga parlorn gidan.... [6/18, 7:34 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Khaleesat na tafiya a hankali ta shiga parlon tana karanto addu'o'i a ranta don irin faduwar da gabanta yake yi isn't normal, ga tsikar jikinta sai tashi yake, she was so uncomfortable and restless at the same time, Abdul ya kulle kofar parlon ya kalli mahaifiyarsa dake zaune cikin parlor ita da kanwarta Aunty karima da Meemah, ko wannensu da bowl cike da farfesun kayan ciki a hannu, Khaleesat ta sunkuyar da kanta ganin gaba dayansu zubo mata ido suka yi suna kallonta fuskarsu babu yabo babu fallasa, amma kana kallon kwayar idanuwansa babu abinda zaka gani sai tsantsan kiyayyarta, da kyar ta karasa tsakar parlon kamar zata harde ta fadi, ta duka kasa cikin sanyin murya ta gaishesu gaba daya, instead Momy sai ta dauke kai tana kallon Abdul tace "Flight din sai na dare ka samu kenan Babana, bayan tun sassafe Meemah tayi maka text" Aunty Karima ta hau kwalo ma mai aiki kira ta zo ta karo mata farfesu, Abdul bai ce ma Momy komai ba ganin babu wanda ya amsa gaisuwar Khaleesat cikinsu ya kalleta yace "Ta shi mu je" Khaleesat ta ɗaga kai ta kallesa amma bata tashi ba ga zuciyarta sai bugawa yake, Momy tace "Ta tashi ku je ina? Wacece ita din tukunna?" A takaice yace "Matata ce" Aunty Karima ta gyara zama da mamaki tace "Ikon Allah, ita ce er gidan barawon da yayi ma Alhaji sata har na miliyan dari kenan?" Meemah tace "Kwarai kuwa gashi kin gane ma idonki, ita ce dai er matsiyatan da Abdul ya makale ma saboda rashin sanin darajan mahaifinsa bai dubi rashin kirkin da aka yi ma Daddy a kotu akan hakkinsa ba ya koma ma yarinyar, dama yawon ta zube uwarta ta shigo yi Nigeria shi ne ta hadu da ubanta bayan sun yi watsewarsu ya aureta...." Katse ta Abdul yayi a fusace yace "Idan kika ci gaba da voicing gibberish zaki sha mamakin abinda zan maki a nan Amina, bridle ur tongue" Aunty Karima ta bude baki da mamaki tace "Amina kai tsaye? Ko ka fara shaye shaye ne Abdul? Akan shegiyar yarinyar nan kake nema kayi ma yayarka rashin kunya?" Abdul ya kalleta yace "Kar ki sake sako min baki tunda ba dake nake ba, stay out of anything that concerns me, Momy ce dolen ki ba ni ba" Momy tayi wani murmushi tace "Rabu da su Babana, take her inside ta huta, sannunku da zuwa" Tana fadin haka ta tashi ta taho kusa da Khaleesat ta dafa ta tace "Welcome my daughter, ku je sama kin ji" Da kyar Khaleesat ta mike tsaye duk jikinta a sanyaye ta bi bayan Abdul, Momy ta koma ta zauna ta bi ta da kallon gefen ido, har ta ga sun haura sama sannan ta kalli su Meemah tayi kasa da murya tace "Sam baku da hankali baku da tunani, haka muka yi da ku daxu?" Meemah da ke huci tace "Ni matsala ta kinsan ban iya pretending bane Momy, wallahi ban iya ba ko nace zan yi" A fusace Momy tace "To in kin san ruguza min plan za ki yi ki ja min asara to tun wuri ki tattara ki tafi gidan Suwaiba bana son hauka, duk ba ke kika ja mana wannan bala'i ba? da sa hannun ki fa abubuwan nan suka faru, ai wallahi sati daya yayi ma yarinyar nan yawa a gidan nan in dai ni na haifi Abdallah, don haka duk wanda bazai iya abinda nace yayi ba to ya bar gidan nan kawai kar ya ja min asara" Aunty Karima tace "Toh Momy kar kuma fa yace zai koma can gidansa da ita, kin san babu me sa shi babu me hanasa idan yayi niyyar yin abu" Momy tace "Ku dai ku zuba min ido kawai ku ga ikon Allah, ance maku ni mahaukaciya ce warce bata san abinda take yi ba irin ku? Ai ni ba yarinya bace nasan me nake yi" Mikewa Momy tayi tana tafiya gansan gansan ta nufi staircase, Meemah ta kyabe baki tace "Wallahi ji naki zuciyata bazata iya wani pretending ba akan shegiyar yarinyar nan me kamar sadaka yalla, ban taɓa jin tsanar mutum a duniya irin yanda na tsaneta ba, Abdul bai taɓa min kalan tijaran da yayi min akan ta ba, kuma fa a gabanta yayi min haka tana ji tana kallo" Aunty Karima ta sauke ajiyar zuciya tace "Nima ba gashi yayi min ba Meemah, fatan mu kawai komai ya zo karshe cikin gaggawa, mu yi yanda Momy tace kawai" Khaleesat ta dinga bin dakin da Abdul ya kawota da kallo wanda babu tantama dakinsa ne, a hankali ta zauna saman kujeran dakin tana kallonsa yana cire agogon wrist dinsa alamar zai shiga bandaki yayi alwala, abinda aka yi mata a parlor ne kawai ke yawo a kanta, tayi nisa tunanin da take yi sai gashi ya fito daga bandakin yana kallonta yace "Shiga kiyi alwala" Sosai gabanta ya fadi ta daga kai tana kallonsa, ta dake tace "Ai ban gama ba" Wani tsawan da ya gigitata ya daka mata, yana mata wani mugun kallo yace "Kar ki raina min hankali, is it going to take u forever to finish ur period? Karya kike yi kin gama" Tsabar yanda ta tsorata jikinta har bari yake ta ma rasa me zata ce masa, yace "Idan na dawo masallaci i will check for my self" Daga haka ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, hawaye ya fara zarya a idonta, wannan moment din take ta tsoro gashi ya zo kuma babu yanda ta iya, shesshekan kuka ta fara yi cikin tashin hankali, bayan ya fita da kamar minti biyu taji an bude kofar dakin, ta juya da sauri gabanta na faduwa, Momy ce ta shigo dakin ta sakar mata murmushi ta nufota tace "Ya sunanki daughter? Mu sai yace mana Khaleesat, ni dai nace Khaleesat ai ba sunan yanka bane" Khaleesat ta sauke idonta zuciyarta na bugawa a hankali tace "Sunana Hauwa" Momy tace "Maa sha Allah, ashe uwata ce, welcome to the family my dear, taso mu je kiyi sallah" Khaleesat felt a bit relieve da gesture din Momy toward her, ta mike tsaye Momy ta kama hannunta suka fita daga dakin, can bangarenta ta tafi da ita har cikin Bedroom dinta sannan ta nuna mata bandakin dake dakinta tace "Ki shiga ciki kiyi alwala, amma kafin nan let's do a mother and daughter talk first my dear" Khaleesat ta daga kai tana kallon Momy, Momy ta nuna mata kan kujera tana mata murmushi tace "Get sitted Mamana" Khaleesat ta zauna kan 2 seater dake dakin Momy ta zauna gefenta tana facing dinta tace "Kar ki boye min komai mamata, ki daukeni tamkar mahaifiyarki, ki gaya min gaskiya wani abu ya shiga tsakaninku da Abdul ne tun bayan da ya dauke ki?" Sosai Khaleesat taji tambayar yayi mata nauyi a kai, hakan yasa ta kasa kallon Momy ta sunkuyar da kanta kawai, Momy ta kwantar da murya tace "Akwai dalilin da ya sa nake tambayarki haka ne Mamana, kar ki ji kunya ki boye min komai, open up to me" Girgiza mata kai kawai Khaleesat tayi ba tare da ta bari sun hada ido ba, Momy ta kamo hannunta tace "Kar fa ki ji kunyata ki boye min komai mamana, gaskiya zaki gaya min" a hankali Khaleesat tace "Gaskiya na gaya maki Momy" Momy ta dinga kallonta kamar dai bata yarda ba, can tace "To saboda me? Anya kuwa gaskiya kike gaya min Mamana?" Khaleesat bata dago kanta ba tace "Period nake yi ne" Momy tace "Toh kin gama yanxu?" A hankali Khaleesat tace "Daxu na gama" Momy ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "To naji dadin jin hakan mamana, don nasan irin daukan da Abdul ya tafi ya maki bayan dawowar ki daga makaranta, hakan bai ba iyayenki daman yi maki duk abubuwan da ya kamata su maki ba a matsayinki na budurwa kafin ki tare gidan mijinki, basu samu daman yi maki shirin xuwa gidan miji ba, amma tunda ya kawo ki nan in sha Allah zan maki duk abinda ya kamata diyata...." Ita dai Khaleesat tayi shiru har sannan bata dago kanta ba, Momy ta mike tace "Ta shi mu je bandaki ki ga...." Khaleesat ta mike tsaye ta bi bayan Momy har zuwa bandakinta, Momy ta nuna mata wani babban flask tace "Kin ga wannan flask din? To zaki dinga tsiyayan ruwan ciki ki sirka da ruwan zafi a pampo ki dinga tsarki da shi" Momy ta dauko wasu ɓakakken sabulai dake nannade a leda ta mika mata tace "Sabulan nan su ma tsarki zaki dinga yi da ko wannensu, in kin yi sai ki ajiyesa inda kika ga na dauko yanzu don naki ne" Momy ta nuna mata wani roba dake rufe a bandakin shi ma tace "Wannan ma diba zaki yi kiyi tsarki da shi, kin ji?" A hankali Khaleesat tace "Toh Momy" Momy ta dauko wani kwalba dake boye a cikin bandakin, Khaleesat dai bin ta kawai take da kallo ta bude flask din ta tuttule abinda ke cikin kwalban, sannan ta mike tace "Yauwa mamana, duk ki tabbatar kinyi amfani da su yanda nace, sai kiyi alwala ki fito" A hankali Khaleesat tace "Toh Momy" Daga haka Momy ta fito daga bandakinta ta shimfida ma Khaleesat darduma, sannan ta zaune kan kujera ta jirata har ta fito daga bandakin, Momy ta mike ta nuna mata darduman tace "In kin idar da sallan kar ki fito, kiyi zamanki zan kawo maki abinci" Khaleesat tace "To Momy" Daga haka Momy ta fita daga dakin ta kulle da key ta tafi da makullin tana ɗan murmushi, a corridor ta hadu da Abdul ya taho daga dakinsa bayan ya shiga bai ga Khaleesat a ciki ba, Momy tace "Har ka dawo masallacin Babana?" Yace "Na dawo, tana ina ne Momy?" Momy ta ja kunnensa tace "Yanxu abinda kayi ma yayarka ya kamata Babana? Kasan ta fa wani lokacin ba hankali ya ishi yayar taka ba, da sai kayi hakuri ka kyaleta da halinta kawai" Ya hade rai yace "Dukanta fa take kokarin yi Momy? A ina ta san ta ko kuma me tayi mata da zata zageta kuma ta nemi ta doketa??" Momy ta kama hannunsa suka shiga dakin baƙin dake kusa da su tana kallonsa tace "Ai na mata fada sosai Babana, yanxu ma haushin abinda kayi mata ne yasa tayi abinda tayi a parlor amma kayi hakuri kaji Babana" Yace "Naji, ina Khaleesat din take?" Momy tace "Bazan fa baka matar ka ba sai zuwa jibi in ma zaka cire ido a kanta ka cire, tun da baka bari iyayenta sun gyarata yanda ya kamata ba to ni zan gyarata" With confusion Abdul yace "Gyarata kamar yaya Momy?" Momy tace "Ka taɓa ganin inda aka dau mace budurwa aka kai ta gidan miji haka nan? To fin karfin iyayenta da kayi kuma suna shakkar ka shi yasa suka baka ita haka babu yanda suka iya maka, amma a al'adar mu ta Hausa babu inda ake yin haka, ni kuma kaga bazan baka ita ba sai nayi mata duk abinda ya kamata na gyarata, in kuma rashin kunya zaka yi min to yi Babana, Khaleesah dai bazan baka ita ba sai zuwa nan da jibi in sha Allah, zan mata duk abinda ya kamata a matsayin ta na 'ya ta" Abdul ya kasa cewa komai yana kallon Momynsa, Momy tace "Mu je ka ci abinci" Bata jira cewarsa ba ta fita daga dakin, bin bayanta yayi ya fita amma duk tsaurin idonsa sai yaji nauyin ce ma uwar tasa komai, haka nan Momy ta dauko masa abincinsa da ta hada masa da kanta ta jera masa su a dinning sannan ta koma kitchen zata hada abincin Khaleesat, Abdul ya zauna kujeran dining amma ya kasa cin abincin, shi fa bai yi niyyar ma kwana gidan da Khaleesat ba don irin burin da ya ci a kanta yau ai sai Allah, nan da nan yaji ransa ya baci, ya mike ya shiga kitchen ya samu Momy ta sa mai aikinta ta jera ma Khaleesat abinci a tray, don irin abin da ta hada mata har ya fi na Abdul, Momy na kallon mai aikin tace "Tafi ki kai mata bangarena ki jirani ina zuwa" Mai aikin ta fita daga kitchen din da tray din, Abdul na kallon Momy a fusace yace "Toh wai menene yasa Meemah zata ce min Daddy ba shi da lafiya critically bayan ma ashe baya kasar?" Momy tace "To ai ganin likita yaje a Amurka, ko bai gaya maka bane? Karfe hudu na yamma jirginsu ya tashi, shi yasa kaji nake cewa baka taho da wuri ba don duk zatona zaka tarar da shi" Abdul yayi shiru yana kallon Momy, Momy tace "Ni dai bari in je wajen diyata, kar ka wani huce kan Meemah don ba ita ta hanaka matarka ba" Daga haka Momy ta bar sa tsaye a kitchen din, tsaye ta tarar da Mai aikinta a bangarenta tana jiranta don kofar a kulle yake, Momy ta bude mata suka shiga ciki, Mai aikin ta ajiye abincin gaban Khaleesat, Momy na kallon mai aikin wanda ranan ne ranan farkon da ta shigo mata daki tace "Toh fita ki ban waje...." Mai aikin ta fita da sauri ta kullo kofar, Momy tayi murmushi tana kallon Khaleesat tace "Ga abinci nan Mamata" Momy ta tafi ta dauko handbag dinta ciro wani kulli ta dawo kusa da Khaleesat ta bude kullin ta barbada mata abinda ke ciki a farfesun kayan cikin dake cike a bowl tace "Maza ki shanye har romon kin ji" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Momy ta tafi ta zauna kan kujera tana murmushi ta dau remote ta kunna TV din dakin, a hankali Khaleesat ke shan farfesun tunani iri iri na yawo a kanta, to yanxu kenan hakuri kawai zata yi da auren Abdul, since gaba daya family dinta sun nuna sun yi accepting auren, sannan ga Mum dinsa ma ta ga tana sonta, kilan zaman aure da Abdul a kaddarar rayuwarta yake, she should just accept it with good faith, most important of all gashi mahaifiyarsa na sonta, his sister won't be an issue tunda mamansa na sonta, kawai ta saka ma ranta salama ta amshi auren tunda haka Allah ya kaddara mata, Housemate dinta ne ya fado mata, lkci daya taji hawaye ya cika idonta, da sauri ta sunkuyar da kai kar Momy ta gani cikin dubura ta dinga goge hawayen tana jin wasu masu zafi na sakkowa, sai da Momy ta tabbatar ta ci abincin sosai, sannan ta umarceta da taje tayi wanka ta tabbatar ta sake tsarki da duk abubuwan da ta nuna mata a bandaki, kafin Khaleesat ta fito Momy ta dauko mata kayan bacci da inner wears, Khaleesat ta shirya tayi sallan isha'i, Momy bata tashi barin dakin ba sai kusan karfe tara da rabi, bayan ta sa Khaleesat ta kwanta kan gadonta sannan ta kashe mata wutan dakin ta bata remote din Ac a kusa da ita, tayi mata sai da safe ta fita daga dakin, har ta kulle kofar ta sake budewa ta shiga tana kallon Khaleesat tace "Ko tashi kika yi zaki kama ruwa cikin dare kiyi tsarki da abubuwan nan fa Mamana kar ki manta" Khaleesat tace "Toh Momy" Momy ta kara mata sai da safe sannan ta fita ta kulle kofar da makulli ta sauka downstairs, Abdul kadai ne zaune parlor yana kallon kwallo amma kana ganinsa kasan ransa a bace yake, Momy tana kallonsa tace "Sai da safe Babana" Ciki ciki ya amsa mata, ta juya ta koma sama zuwa dakin da su Meemah suke, duk suka dinga kallon Momy bayan ta shigo, Aunty Karima tace "Ya dai Momy duk ta yi?" Momy tayi wani murmushi tace "Tun yaushe kuma" Meemah tace "Alhamdulillahi, shi Abdul din fa?" Momy tace "Shi ai dama a miyar shinkafa aka ce na zuba masa maganin, sai ruwan lipton, na kori mai aikin taje bakin pampo tayi wanke wanke shine na samu duk na zuba masa nasa" Meemah tayi murmushin mugunta tana gyara zama sanin Momy bata bin malaman banza, kai in malami yace zai amshi kasa da 1M a wajenta ma bata yarda da ingancin aikinsa ba, inda ake aikin da gaske take zuwa, ko da kuwa miliyan biyar zata kashe bata kyashi don tasan aiki na gaske ake mata. [6/19, 8:55 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Washegari da safe bayan Khaleesat ta shirya cikin tsadadden Abayan da Momy ta bata, Momy ta gama hada mata shayin da take yi cikin cup tace "To zo kiyi breakfast din kar ya huce Mamana" Khaleesat bata ce komai ba ta karasa ta zauna kan darduman da aka jera mata breakfast din, Momy tayi murmushi tace "Idan farfesun bai isheki ba sai ki bude warmer ki ƙara, dankalin ma akwai saura a warmer in bai ishe ki ba" Ita dai Khaleesat kai kawai ta gyada mata, tana juya shayin gabanta a hankali da spoon din ciki, Momy ta koma kan kujera ta zauna tana kallonta tace "Duk da ma ina lura jiya baki wani ci abincin da aka kawo maki da yawa ba, ko maganin cin abinci zan sa a samo maki mamana" Khaleesat tayi murmushin karfin hali bata dai ce komai ba ta dau shayin tana kallon ciki, sai tayi tunanin lipton din ne kilan ya fashe a cikin ruwan shayin, sipping din shayin tayi kadan ta ajiye sannan ta fara cin irish din, Momy dai kallonta kawai take kasa kasa, Bude kofar dakin aka yi Momy ta juya, ganin Abdul tace "Sai yanxu ka tashi Babana" Bai ce mata komai ba ya karasa ya zauna saman kujera, Khaleesat ta ɗan kallesa taga kallonta yake, sauke idonta tayi a hankali tace "Ina kwana" Ya kauda kai yace "Lafiya" Momy tace "Ka tashi kaje kayi breakfast din ka" Yace "Momy za mu je shopping ne, bata zo da kaya ko daya ba" Momy na kallonsa tace "To wanda ka gani a jikinta yanxu kai ka siyo mata?" Shiru Abdul yayi yana kallon Momy, Momy tace "To har na tura ma Meemah kudi su je su yi mata siyayya ita da Karima tunda kai baka da ƙara" Mikewa Abdul yayi ya nufi kofa ya fice daga dakin, Momy ta bi sa da kallon gefen ido, sai da Momy taga Khaleesat ta gama cin abinda zata ci na breakfast din sannan ta mike ta fita ta kira mai aikinta ta fitar da sauran abubuwan da Khaleesat ta rage, bayan mai aikin ta fita Momy ta bude bayan labulenta ta dauko wani karamin jarka ta kawo ma Khaleesat tace "Wannan tsumi ne Mamana, daga yanxu har zuwa dare nake son ki shanyesa gaba daya" Ita dai Khaleesat kallon jarkan take, Momy tace "Kin ji ai ko?" Khaleesat ta gyada mata kai tace "Toh Momy" Momy ta dauka ta mayar bayan labule sannan tace "In zaki yi kallo sai ki kunna TV abun ki, bari in je zanyi bakuwa ban san ko ta iso ba" Khaleesat tace "Toh" Momy ta fita daga dakin ta kulle da makulli tana rike da makullin ta sauka downstairs don aminiyarta godiya ta kirata ta sanar mata tana hanya, tana shigowa parlor taga Abdul zaune dinning area da breakfast din da Khaleesat ta rage a gabansa, da karfi Momy ta kwala masa kira, ya juya yana kallonta, ta karasa wajen da mugun sauri tace "Banda abun ka ba ga naka a kitchen ba Abdul me zaka yi da wanda aka rage? Ko har kaci wannan din ne?" Abdul dake kallonta yace "Ban ci ba, amma menene idan na ci?" Momy ta kwalo ma mai aikinta kira, Mai aikin ta taho da sauri Momy ta kunduma mata wani ashar tace "Nan nace ki ajiye sauran abincin er iska kawai er neman jidali? Me yasa ke dakikiya ce? Wallahi zan kore ki fa a gidana na gaji da maganar da kike sa ni kamar kanwar uwarki, yau ga shegiyar mata kawai" Abdul ya kalli Momy yace "Ni fa nace ta kawo min nan, beside what is wrong with the food da bazan ci ba?" Momy ta mata tsawa tace "Dauka ki wuce ki ban waje guntuwar banza kawai" Mai aikin na ba Momy hakuri ta dauke jiki na rawa ta tafi kitchen da breakfast din, Momy ta kalli Abdul dake kallonta, yace "I want to understand meye da abincin da bazan ci ba Momy?" A takaice Momy tace "Kayan gyaran mata mana? Ko kai na mace ne?" Bata jira cewarsa ba ta bar wajen ta shige kitchen ya bi ta da kallo, Tuttular da shayin tayi a sink sannan ta juye sauran irish din da kwai da farfesun duk ta cakudesu waje daya tace "Gasu nan ki kai ma karnuka, in kuma kwadayin ki ya ja ki kika ci ke kika jiyo" Mai aikin ta risina ta amsa tace "Toh Hajiya" Sai da Momy ta jirata har ta dawo bayan ta kai ma karnukan can cage dinsu sannan Momy ta dau breakfast din Abdul ta kai masa kan dining din tace "Ga naka nan" Daga haka ta juya ta bar wajen, dai dai shigowar Godiya gidan, da fara'a Momy ke mata sannu da zuwa Abdul ya dauke kai kamar bai ganta ba don ya tsani matar with passion, tun asali dama baya gaida ta, Haka Momy ta ja ta zuwa sama tana cewa "Mu je ki ga surkar tawa ku gaisa" Da ido Abdul ya bi su har suka haura sama, Momy na isa kofar dakinta ta bude da makulli suka shiga, Khaleesat dake gyara gadon Momy ta mike tsaye tana kallonsu, Momy na murmushi ta kalli godiya tace "Kin ganta" Da fara'a sosai Godiya tace "Maa sha Allah, ai ko ga ta kamar balarabiya Maa sha Allah, sannu amarya, ya sunanki?" Momy na murmushi tace "Sunan Baabata gareta, Hauwa sunanta" Khaleesat ta zame kasa ta sauke idonta ta gaida Godiya, Godiya ta karasa kusa da ita ta dafata tare da ɗagota ta zaunar da ita gefen gadon Momy tace "Lafiya lau diyata, ya bakunta?" Khaleesat bata ce komai ba kuma bata dago kanta ba, Momy na kallon Khaleesat tace "Kin sha tsumin da nace ki sha kuwa?" Khaleesat ta gyada mata kai tace "Na sha" Momy tace "To maa sha Allah, Allah ya maki albarka Mamana, zuwa anjima sai ki kara sha kin ji" Khaleesat tace "To" Bayan few minutes Momy da Godiya suka fita dakin, Momy ta sake kulle kofar da makulli sannan ta cire makullin suka tafi wani daki dake sama, bayan sun shiga Momy ta kulle kofar tana kallon Godiya tayi murmushi tace "Duk tayi amfani da abubuwan babu gardama godiya, iya na jarkan nan ne kawai ya rage yanzu" Godiya ta zauna gefen gado tace "To madallah, shi ma Abdul din duk kinyi yanda aka ce kiyi da na sa?" Momy tace "Kwarai kuwa" Godiya tayi wani murmushi ta bude handbag dinta ta ciro wani babban laya bakikirin da shi ga er karamar kwado a jiki ta mika ma Momy tace "To aikin karshe kenan wannan Hajiya, Malam ya ce ki samu inda kika san baza a taɓa tono sa ba ki binne a cikin gidan nan" Momy ta zauna gefenta tana murmushi ta amshi layan tace "To laya nawa na binne gidan nan ba a tono ba godiya, ai wannan karamin aiki ne a wajena don ba sabon abu bane" Godiya tace "Yauwa, bayan kin binne Malam yace ki basa yarinyar kawai, wallahi yace min in har ta wuce sati biyu Abdul bai rabu da ita ba to bazata wuce sati biyar ba a gidansa" Fara'ar fuskar Momy ya bace tace "Har sati biyar Godiya? Ni da yace min sati daya kacal a waya" Godiya tace "Halan bai gaya maki irin abubuwan dake ƙan dan ki bane? Da yaya ma aka samo kansa har asirin nan yayi tasiri? Ai abubuwan ƙan Abdul sun fi karfin wani asirin wallahi kiji in gaya maki" Momy ta sauke ajiyar zuciya tace "An taɓa gaya min haka da dadewa wallahi, don ni akwai malamin da yace min ma yanda asiri ke cin ubansa shi sai an wahala asiri zai ci sa" Godiya tace "To wallahi Malam sai da ya tura masa aljanu don ma ki ji Hajiya, aikin nan sai da Malam ya hada da wasu malaman don aiki ne me wahalan gaske yace min wallahi" Momy tace "To ni fargabana kada fa in mika masa yarinya ace asirin nan bai ci ba abinda muke gudu ya afku mu shiga uku Godiya" Godiya tace "Sai kace yau Malam ya fara maki aiki? Ai da aikin bai yi ba kinsan bazai boye mana ba, sai dai ya kara mana lokaci yayi wani sabon aikin fa, dama yace in na yarinyar ya ci shine zai sa na Abdul din ma yayi tasiri sosai" Momy tace "Haka ya ce kam" Godiya tace "Don haka zuwa gobe ki basa ita kawai su tafi an gama aiki sai jiran result, kuma ina me tabbatar maki zaki sha mamaki" Momy na murmushi tace "Toh shikenan godiya, nagode sosai, zan tura masa cikon dubu dari biyar dinsa anjima" Da yammacin ranan bayan Momy taga Abdul ya fita gidan tayi maza ta aiki mai aikinta kasuwa saboda tayi amfani da daman ta haƙa rami a garden din gidan ta binne layan da Godiya ta kawo mata, bayan mai aikin ta tafi Momy ta zaga zuwa garden din gidan ta samu spot me kyau ta fara haƙa rami da wuka, bayan ta haka yayi zurfi yanda take so sannan ta jefa layan ta mayar da ƙasan wajen ta dau wani dutse ta dora dai dai wajen don kada a ga alamar an tono kasa, tap ta bude don wanke hannunta da wuƙan da tayi using, Khaleesat ta karasa bakin window din dakin Momy jin ƙaran bude ruwan pampo, in ta gaji da zaman dakin dama jikin window take zuwa ta tsaya tana kallon waje, ta tsaya jikin window din tana ta kallon Momy dake ta wanke hannunta bayan ta wanke wuƙan, bayan ta gama ta kara komawa kusa da dutsen tana seta sa da kyau ta yanda ko da wasa baza a ga tonannen ƙasa ba, sai kuma ta mike ta fara tsinko doddoya dake Garden din, sannan tayi using wuƙan hannunta ta yanki pumpkin leaves isasshe bayan ta gama ta bar garden din tana rike da ganyayyakin hannunta, babu abinda Khaleesat ta kawo a kai don tunaninta ganye Momy taje diba a garden din, Momy na kai ganyayyakin kitchen sai ga su Meemah sun dawo daga shopping din da ta aikesu su yi ma Khaleesat, dariya Momy ta dinga yi a parlor ganin wasu shegun abayoyi masu saukin kudi da suka kwaso ma Khaleesat irin wanda ake dinkawa a kano, ga wasu shegun dogayen riguna su ma masu arha, hatta inner wears da suka siyo duk very low quality ones ne, babu wani abu na arziki da suka siyo ma Khaleesat, Momy na ci gaba da dariya tace "Duk maida su cikin ledojin kawai na yafe ganin wannan tarkace haka karima, amma baku da kirki yaran nan" Aunty Karima na dariya ta maida kayan cikin leda ta kulle tace "Su ne dai dai er talakawa ai Momy, da so kika yi ki ga abayan dubu hamsin zuwa sama? Ai ita Meemah ma en gwanjo ta so mu je muyi selecting mata kawai" Dariya kawai Momy take, ita kuwa Meemah danna wayarta kawai take don duk wani abu da ya shafi Khaleesat ko kadan baya bata dariya, she just can't wait taga irin rabuwan da Abdul zai yi da Khaleesat don shine babban abinda ke gabanta yanxu. Wajen karfe takwas da rabi Momy na zaune parlor da Abdul tana ta yi masa hira, shi dai wayarsa kawai yake dannawa baya responding kamar ma bai san me take cewa ba, Momy ta kwalo ma mai aikinta kira, Mai aikin ta taho da gudu tace "Na'am Hajiya?" Momy tace "Zaki ga Kankana da na yanka a kitchen ki dauko ki kai ma Mamata a sama" Mai aikin tace "To Hajiya" Juyawa tayi ta koma kitchen sai ga ta ta dawo rike da bowl din kankanan tana kallon Momy cikin ladabi tace "Amma Hajiya dakin a kulle yake" Momy tace "A'a a bude yake tun daxu, ki je ki kai mata" Bayan mai aikin ta tafi ta kai water melon din ta dawo ta tafi kitchen ta ci gaba da aikin da take, Momy ta dau wayarta tace "Bari in inyi waya da Alhaji, daxu na ga kiransa ina kitchen wallahi" Shi dai Abdul bai ce mata komai ba har ta shiga dakin dake downstairs ya bi ta da kallo... Bayan minti biyu ya mike ya nufi stairs direct ya tafi bangaren Momy, yana bude kofar dakin Khaleesat dake zaune saman darduma bayan ta idar da sallah ta gama duk addu'o'in da zata yi ta juya ta kalli kofar, sosai gabanta ya fadi bayan sun hada ido da Abdul, ya karasa cikin dakin babu yabo babu fallasa yace "Ta shi mu je shopping...." Khaleesat da gabanta ke faduwa ta nuna masa ledan da Momy ta kawo mata daxu duk da bata duba kayan ciki ba cikin sanyin murya tace "Ai Momy ta sa an min shopping din, ka gan su can ma" Ya hade rai yace "Kee... Get up nace, i am not asking for ur opinion" Ta sauke idonta ta mike tsaye da kyar ta dauke darduman tana linkewa, sosai taji hankalinta ya tashi, a ranta ta dinga addu'an Allah ya kawo Momy dakin immediately, fixge darduman hannunta yayi ganin it's taking her a whole eternity to fold, ya ajiyesa saman kujera sannan ya kama hannunta suka nufi kofa fuskarsa a daure suka fita daga dakin, Khaleesat dai bin sa kawai take a tsorace, downstairs suka sauka har sannan yana rike da hannunta, babu kowa a parlorn sai mai aiki dake goge goge a dining area, ya dau makullin motarsa da ya bari kan center table, Khaleesat ta marairaice masa cikin rawan murya tace "Ya Abdul Momy fa bata sani ba, kar ta shiga dakinta taga bana nan, kaga babu dadi haka" Wani kallon da yayi mata yasa tayi shiru zuciyarta na bugawa, bata sake gigin ce masa komai ba har suka fita parlorn gidan zuwa parking space, Khaleesat taji hawaye ya cika idonta bayan ya sa ta shiga motarsa ya shiga driver seat, mai gadi ya bude masa gate ya fice gidan da motar. Momy ta fito parlor tana kallon Mai aikinta tace "Naji kamar fitar mota, waye ya fita?" mai aikin tace "Alhaji karami ne ya fita" Momy tace "Shi da wa?" Mai aikin tace "Shi da matarsa" Shiru Momy tayi don bata yi tunanin zai ce zai tafi da Khaleesat yau ba, don so tayi taga yanda za su kwashe, shi yasa ma ta basa hint din dakinta a bude yake, ta zata can din kawai zai bi ta ko kuma ya kai ta dakinsa, Momy ta sauke ajiyar zuciya, ganin mai aikinta sai kallonta take ta hade rai tace "Lafiya kike kallona haka munafuka?" Da sauri mai aikin ta juya ta bar wajen, Momy ta juya ta koma daki amma fa zuciyarta ya kasa nutsuwa sam sam, gani take kamar Abdul zai yi tarayya da Khaleesat, duk da malaminta bai taɓa mata aiki bata ga result me kyau ba amma a wnn case din sai take ɗari ɗari kada abinda suke gudu yaje ya afku dama ga Godiya tace aikin me wahala ne, ai kuwa da ta shiga uku ta lalace, number Godiya tayi dialing ta zauna gefen gado tana jiran tayi picking. Hawaye kawai Khaleesat take tana dafa shayin da Abdul ya sa ta dafo masa a kitchen, ita ta ma riga tayi give up yau don bata da wani dubaran da ya rage mata in ba so take ta fusata Abdul ya doketa ba, she will just accept her kadr with good faith, gwara tayi accepting dinsa kawai a mijinta tunda haka Allah ya kaddara mata, goge hawayenta tayi tana tafiya a hankali ta tafi kai masa lipton din dakinsa, tana bude kofar ya ajiye wayar hannunsa yana kallonta, kanta a kasa ta karasa har inda yake ta duka ta ajiye masa black tea din, ta mike zata bar wajen ya jawota ya zaunar da ita gefensa yana kallonta, ita dai bata bari sun hada ido ba zuciyarta na wani irin bugawa, ya dago kanta suka hada ido, sauke rigar baccin jikinta yayi slowly yana kallonta babu ko kiftawa, ta sunkuyar da kanta bugun zuciyarta ya tsananta sosai, tana ji tana gani ya cire duk abinda ke jikinta yana kare ma each and every part of her body kallo, bata sake yarda sun hada ido ba, a hankali ya kwantar da ita, ta runtse idonta da sauri jikinta na rawa ganin inda yake kokarin kai bakinsa, after some seconds Khaleesat ta bude idonta a hankali tana kallonsa jin bai yi abinda yayi niyya ba, taga wani wajen daban yake kallo babu ko kiftawa, after some seconds ta ga ya mike ya nufi kofa ya bude, fuska daure yake kallonta babu yabo babu fallasa yace "I need my privacy....." Khaleesat ta mike zaune da kyar tana kallonsa, lokaci daya jikinta yayi sanyi, ta jawo Hijab dinta da ya cire tun zuwansu gidan ta saka sannan ta dau kayan baccinta ta nufi kofa, bata bari ta hada ido da shi ba ta fita daga dakin taji ya kulle kofar da makulli, juyawa Khaleesat tayi tana kallon kofar.....