Kenza eBookz

Halysaah by khaleesat hydar - Chapter 33

Complete book: Halysaah by khaleesat hydarChapter 33 of 34RomanceBy Khaleesat Hydar

Halysaah by khaleesat hydar - Chapter 33

Halysaah by khaleesat hydar Chapter 33: Halysaah by khaleesat hydar Chapter 33. [6/26, 9:27 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Khaleesat na fitowa parlor suka…

18,290 words

[6/26, 9:27 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Khaleesat na fitowa parlor suka hada ido da Ummu dake kokarin kiran Alhaji Musa da wayarta cikin bacin rai, sunkuyar da kai Khaleesat tayi tana goge hawayen dake ta zuba idonta, Ummu tace "Zo ki zauna tukunna diyata" Khaleesat tayi shiru bata ce mata komai ba don har cikin ranta bata ji zata iya zama a parlon ba kamar yanda Ummu ta umarceta, amma kar tayi disrespecting matar duba da tsaya mata da tayi sanda Abdul ke ci mata mutunci yasa kawai ta duka kasan carpet kanta a kasa, Sau uku Ummu na kiran wayar Dad din Abdul, daga karshe ya daga kiran, cikin fushi ta fara koro masa abubuwan da ta zo gidan Abdul ta tarar da kuma abinda Abdul ya aikata daga karshe, Alhaji Musa dake ta sauraronta ya jira har ta gama, sannan yayi gyaran murya yace "Ai ina ganin Muhusina wannan ba issue bane da zaki shigar da kanki farat daya, ke da ba ma a kasar kike ba zuwa kawai kika yi, i don't think it's proper kiyi involving kanki sama ta ka, it's not done that way, alright? kuma tunda kika ga ya saketa definitely yana ganin hakan shi ne dai dai so meye zaki damu kanki, ko mu iyayensa we are not in the rightful place to question his act, okay? decision dinsa ne, so just stay out of what u know nothing about Muhusina, ba naji kin ce flight din karfe biyu gare ki ba? Ko kin daga tafiyar taki ne?" Kasa cewa komai Ummu tayi tsabar mamaki, kana ganinta kasan she is speechless, ita dai Khaleesat kanta na kasa don ba handsfree Ummu ta saka wayar ba balle ta san abinda Dad din Abdul ke cewa, a hankali Ummu tayi ending call din ta ajiye wayar a gefen kujera don ba ma ta da amsan da zata ba ɗan uwan nata, sosai jikinta yayi sanyi, yanxu dama Family din Alhaji Musa basu canza ba daga yanda ta san su tun tale tale, don ita sai tayi shekara aru aru ba a ganta a Nigeria ba in ba muhimmin abu bane ya kawo ta, Momy ce ta bude kofar parlon fuskarta a murtuke, ashe all this while tana kofar gida tana jiran ganin Khaleesat ta fito ta bar gidan amma shiru shiru bata ga ta fito ba, Momy na kallon Khaleesat tace "In dai ba gidan ubanki bane ko na uwarki nan din tunda har ya furta ya sake ki ai kya fito ki kama gabanki, ko zaman ubanki kike yi har yanxu? Da wani abinda kika zo gidan da shi ne kika yi waya a zo da mota a kwashe maki ko yaya?" Ummu ta kalli Momy tana girgiza kai cike da takaici tace "Ki ji tsoron Allah Hajiya, ki ji tsoron haduwar ki da Allah, ke ma fa kina da yaran nan mata...." A mugun fusace Momy ta karaso cikin parlon ta dakatar da ita tana nunata da ɗan yatsa tace "Kin ga wannan family issue ne ki cire bakin ki a abinda bai shafeki ba Muhusina don ke bare ce a wannan ɓangaren, kuma ba ke kika haifar min Abdul din ba da kike neman cusa kai abinda ya shafi rayuwarsa, who are you to even interfere? Ko Musa kin zata ya isa ya hana Abdul abinda yayi niyyar zai yi ne? To wallahi ki cire bakin ki da idonki akan abinda ya shafi zuri'ata, 'ya ya mata kuma dama ko wani shege ya haifa ai, meye a ciki" Momy na kai wa nan ta kalli Khaleesat cikin daga murya tace "Baza ki tashi ki san inda dare yayi maki ba ko sai na kira su Meemah sun fitar min da ke daga gidan nan??" Mikewa Khaleesat tayi bata bari sun hada ido da Momy ba ta nufi kofa tana tafiya a hankali, Ummu ta kasa cewa komai tana kallon Momy tana girgiza kai, sai da Khaleesat ta fita daga compound din gidan gaba daya sannan ta fara share hawayen dake sauka idonta, tunanin yanda zata koma gida bata da ko sisi ta fara yi, tafiya me nisa tayi har ta iso titin da zata samu abun hawa, daga karshe bayan jiran kusan minti sha biyar ta samu wani adaidaita sahun da zai kai ta Mariri a dubu biyu da dari biyar, in taje gida sai ta basa kudinsa, har Khaleesat ta isa gida hawaye ya ki tsaya mata a ido, ita kanta bata san yanda take ji a ranta ba game da abinda Abdul yayi mata, farin ciki take ko akasin haka har sannan ta kasa ganewa a zuciyarta, but she was deeply hurt and pained, daurewa kawai take kar ta fashe da kuka a adaidaita sahun, bayan ya tsaya dai dai kofar gidansu ta sauka tace "Za a kawo maka kudin yanxu, nagode" Daga haka ta shiga cikin gidansu, a tsakar gida ta tarar da kishiyoyin Ummanta sun gama abincin siyarwansu na yamma yara za su fita da shi talla, ta gaishesu ba tare da ta bari sun hada ido da su ba direct ta nufi dakin Ummanta, duk suka bi ta da kallo, Aunty Farida da fitowar ta daga bandaki kenan zata yi alwala don lokacin sallan La'asar yayi ta ajiye butan hannunta ta bi Khaleesat da kallo ita ma duk da Khaleesat bata ganta ba, Khaleesat na shiga dakin Ummanta ta fada jikinta ta fashe da kuka a hankali, Kasa cewa komai Umma tayi tana kallonta da mamaki, sai ga Aunty Farida ta shigo dakin ita ma, sosai gabanta ya fadi ta tsaya nan bakin kofa tana kallon Khaleesat, da kyar Umma ta dago kanta cike da karfin hali tace "Me ya faru?" Khaleesat ta kasa cewa komai tana kuka sosai, Umma da nan da nan ita ma hawaye ya cika idonta ta rungumeta bata sake ce mata komai ba ta bar ta tayi kukan me isarta, cikin sanyin jiki Aunty Farida ta karasa cikin dakin ta zauna gefen katifa tayi shiru, Umma ta goge idonta tana patting Khaleesat a baya a hankali trying to calm her amma bata hanata kukan da take ba, sun fi minti biyar a haka sai ga Mama Zubaida ta dage labulen dakin tace "To ɗan sahu dai na ta jira a mika masa kudinsa a kofar gida" Magana take amma idonta na kan Khaleesat da Umma, tsabar gulma yaron makota me adaidaita sahun ya aiko cikin gidan amma tayi karaf ta mike bayan yaron ya sanar masu ta nufo dakin Umma taki barin yaron ya karasa, don tun shigowar Khaleesat suka baza kunnuwa ko za su ji wata magana amma shiruu basu ji ko tari ba a dakin Umma, Aunty Farida ta dau handbag dinta ta fita daga dakin ta sake labulen daga hannun Mama Zubaida dake rike da shi, sannan ta fita zuwa gun mai adaidaita sahun, sai a sannan Umma ta iya daga kan Khaleesat, suna hada ido Khaleesat ta sauke jajayen idanuwanta, Umma tayi karfin halin cewa "Me ya faru Jiddah?" Khaleesat ta sauke idonta wasu hawayen na zuba idonta tace "Yace ya sakeni" Hawayen dake makale idon Umma ya zubo tana kallon Khaleesat babu ko kiftawa, Khaleesat ta rufe fuskarta jikin Umma ta fara wani sabon kukan, Umma ta rungumeta sosai, cikin rawan murya tace "Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi a gare ki, kiyi hakuri kin ji?" Kai kawai Khaleesat ke gyada mata tana shesshekan kuka, a haka Aunty Farida ta dawo dakin ta same su, Aunty Farida ta zauna gefen Umma tana kallonsu, Da kyar Umma ta kalleta tace "Wai sakin ta yayi" Ƙasa cewa komai Aunty Farida tayi tsabar yanda ta girgiza, ta dinga kallon Umma babu ko kiftawa, nan da nan ita ma hawaye ya cika idonta, after a while ta goge hawayen dake zuba idonta ta fita ta dau buta tayi alwalanta ta dawo ta tada sallah, Umma ta dago Khaleesat da tayi shiru a jikinta, sai taga bacci take, Khaleesat ta bude ido a hankali, Umma tace "Kin yi sallah ne?" Girgiza mata kai Khaleesat tayi, Umma tace "Ki je kiyi alwala kiyi sallah" Khaleesat ta mike tana tafiya a hankali ta fita daga dakin. Khaleesat na idar da sallah Aunty Farida na kallonta tace "A zubo maki abinci?" Khaleesat ta girgiza mata kai cikin sanyin murya tace "Na koshi" Daga haka ta mike ta hau saman gadon Ummanta ta kwanta, nan da nan bacci me nauyi ya dauketa, daga Umma har Aunty Farida babu wanda ya iya cewa komai a dakin, suna ta zaune har kusan karfe shidda, ita dai Aunty Farida tana rike da Al-qur'ani tana karatu silently a ranta, su Islam suka dawo hadda wanda suke zuwa har ranan friday, Umma ta sa su je su hura gawayi su dora girki, muryar Nenne suka ji a tsakar gida tana cewa "To Zubaida sai ki dau na annabawa don kin tafka asara lafiyayye yau, almajirai na mugun wasa suka hamɓare Suwaiba tallan da kika dora mata ya kife a kasa, su kuma suka tsere, sanin azaban da zaki mata ta taho ta sameni tana kuka kamar ranta zai fita, yanzu haka tana can gidana nace tayi zamanta, ga robobin tallan da faranti nasa an kwaso maki kayanki, ko roba daya bata siyar ba suka hambare farantin" Mama Shatu ta saki salati tana kallon Mama Zubaida da ta nemi waje ta zauna jin abinda Nenne ke cewa, Nenne ta kwashe da dariya har da kyakyatawa tace "Yaran layi kuwa duk suka wawushe abincin da ya zube a kasa suka loda ma cikin su" Daga haka ta nufi dakin Umma ta dage labulen tace "Zahra'u kina da er kuka ko kubewa ki tsam inje in ƙada miya" Umma bata yarda sun hada ido da Nenne ba tace "To bari in duba maki, Ina wuni" Nenne tayi mitsi mitsi da ido tace "Wacece wancan kuma a kwance kan katifarki?" Umma dai bata ce komai ba ta tashi zata dauko ma Nenne kubewa busasshe, Aunty Farida ta gaida Nenne ba tare da ta kalleta ba, Nenne na kallon Khaleesat tace "Wai wa nake gani kamar Khaleesah a kwance?" Aunty Farida ta ajiye Qur'anin hannunta still bata kalli Nenne ba tace "Ita ce" Nenne ta shigo dakin tace "Wato ni dai shikenan kun nuna mata banda matsayi da har zata shigo unguwan nan ta karasa gidana ta gaisheni ko? In ma bata je ta gaisheni don Allah ba ai sai tayi don ubanta Ali tunda ni na haifesa har ya haifeta" Daga Umma har Aunty Farida babu wanda yace ma Nenne komai, Nenne tace "Mijin ne ya kawota? Shi ma ai shegen ne tunda ba karasawa yake yi gidana ya gaisheni ba, banda kaddara a ina za mu san sa har mu aura masa Khaleesat mutumin da baya ganin mutuncin mu, kana masa magana yana amsa maka cikin gadara da yanga wai shi ɗan Alhaji Musa, waye bai san satan da ubansa ya zabga a gwamnati ba kafin ya koma kasuwanci, ko don muna kauda kai?" A takaice Aunty Farida tace "To sakin ta yayi..." Nenne ta juya ta kalli Aunty Farida na en sakwanni, can tace "Ban ji me kika ce ba Parida?" Aunty Farida da har hawaye ya kawo idonta tace "Sakinta Abdul din yayi" Nenne ta kasa motsi a inda take tsaye, a hankali tace "Sakin aure ko sakin me?" Aunty Farida dai bata tanka ta ba, ita dai Khaleesat na kwance tayi backing din Nenne bayan surutunta ya tasheta daga baccin da take, Nenne ta saki wani salati muryarta na rawa tace "Wato dai ɗan nawa ne ba a son a ga ya zauna lafiya a gidan duniya kamar yanda kowa yake zaune" Fita tayi ta koma tsakar gida ta rushe da kuka sosai tace "Allah ya isa tsakanina da Zahra'u da er ta, babban burin su a duniya su ga Ali ya tagayyara, babban burinsu su ga Ali cikin mawuyacin hali cikin tashin hankali, banda haka ko dukanta da zaginta Awdul ke yi a gidan bazata hakura ta zauna ba albarkacin ubanta? Shi ne har zata amshi sakin da yayi mata hannu bibbiyu ta dawo mana gidan nan domin shari'arsu da Ali ya dawo sabo?" Mama Zubaida da Mama Shatu tuni suka mike tsaye jin abinda Nenne ke cewa, cikin kuka Nenne tace "Ban taɓa ganin er da burinta taga ubanta a walakance ba, kun ga ai ta dawo taga yanda za ayi da uban nata ko furson din za a mayar da shi ko hukuncin rataya za a yanke masa, ni dai na shiga uku na lalace, Allah ya hada Ali da mata da 'ya yan da basa tausayinsa kuma su za su yi ajalinsa, yanxu in Khaleesat er arziki ce da yace ya saketa ba sai tace babu inda zata je ba tunda bautar Allah take??" Malam Ali ne ya shigo gidan da er taliyar Hausa da ya siyo cikin Bacco bag, Nenne na ganinsa ta rushe da sabon kuka tace "Wallahi ta kashe auren ta dawo taga yanda za su yi da kai Ali" Malam Ali ya tsaya yana kallon Nenne, Nenne na fyace majina tace "Ga ta can dakin uwar a kwance tana jiran taga da wace motar za a zo a kwashe ka, dama wallahi tun da muka je gidan da parida nasan za a samu babban matsala don babu alkhairi a ran Parida, kuma in bata yi hankali ba daga ita har Zahra'un sai dai su koma kasar su, duk wanda baya son kwanciyar hankalin ɗa na to kwanciyar hankalina ne baya so wallahi" Malam Ali dai ya nemi tabarma ya zauna ya kasa cewa komai, Mama Zubaida tace "Ikon Allah, kuma abinda ya faru kenan ni Zubaida? Aure wata daya da yan kwanaki amma har an yi saki? Yanxu zawarawa har biyu garemu a gidan nan kenan?" A fusace Nenne tace "Ta zauna tayi ma uban wa zawarci a gida? Ai ko taki ko ta so sai naje na ba Awdul hakuri ya maidata dakinta don kaf zuri'armu babu wanda ya taɓa zawarci sai in mutuwa mijin yayi, to ko bakin halinta bai isa ya sa ya korota ba bai shirya ba, Khaleesah ce duk wani mummunan bakar maganar da ya zo bakinta take yaɓa ma mutum, ko kuma in ka gaya mata abinda bai gamsheta ba tayi maka wani kallon walakanci da kaskanci da tula tulan idanuwanta, wani lkcn kana mata magana tayi maka banza wannan duk mun san halinta ne ba wai sharri ba, ga nukurci kamar er sarkin kutare, to ai ba ko wani namiji bane zai dau wannan, don haka zan je in basa hakuri ya dubi girman Allah ya maidata dakinta..." Mama Shatu tace "Toh ko samun sa kika yi ai sai yayi niyya zai maidata Nenne, in zai iya ai bazai fara sakin ta ba" Wani zagi Nenne ta kundumo mata a fusace, dai dai nan aka rafka sallama a kofar gida, Malam Ali ya mike tsaye yana kallon hanyar fita gidan, Nenne tayi tsit zufa na keto mata, can ta fara kuka a hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, Zahra'u dai bata zo mana pamily da alkhairi ba, kun ga har an zo tafiya da shi" Mama Zubaida ce ta yafa gyale ta nufi hanyar fita daga compound din, wani mota taga anyi parking a kofar gidan, mutumin dake tsaye kusa da motan ya nufota yana kallonta, Mama Zubaida ta gaishesa har da risinawarta, ya amsa yace "Mai gidan na ciki kuwa?" Mama Zubaida tace "To Allah ya sa dai lafiya Malam" Mutumin yace "Eh to, ni Dreban Alhaji Musa ne, an bani sako ne in kawo ma mai gidan" Mama Zubaida tace "To ni mai dakinsa ce, ni ce uwar gidansa, ko zan iya karba in mika masa, don baya jin dadi ne" Mutumin yace "To ba damuwa" Hannu yasa a aljihu ya ciro Envelope ya mika mata, ta amsa yayi mata sallama ya koma zai shiga mota, Mama Zubaida ta koma gidan tana juya takardan ita kanta sai da gabanta ya fadi don irin wannan in an kawo ai sammaci yake nufi, Nenne na ganin Envelope din hannun Mama Zubaida ta rushe da matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, shi kenan Ali a haka zai kare kenan ni Zainabu? wani takardan kotun aka sake kawo masa kenan?" Malam Ali ya amshi Envelope din hannun Mama Zubaida ya yage ya ciro takardan ciki ya warware, "Ni Abdallah Musa, na saki er ku Hauwa saki daya, biyu, uku" content din dake jikin takardan kenan, Shatu ta amshi takardan hannunsa tun da tayi karatun primary, tana duba takardan ta karanto abinda ke jiki amma fa da kyar tana in ina, Nenne ta tsaida kukan da take bayan taji Shatu ta karanto rubutun jikin takardan tace "Ji tsinanne la'ananne matsiyaci? saki har uku kamar warce ta kashe ubansa ko uwarsa? To Allah Ubangiji ya tsine masa albarka, dama banda kaddara uban me Khaleesat zata ci da ɗan barawon Gwamnati? ubansa barawon gwamnati shi kuma ɗan daba, Ai mu wannan sakin abun farin ciki ne a gare mu gaba daya tunda ba na'am muka yi da auren ba, kuma ko yau Khaleesat ta fita sai ta samu mijin nuna ma tsara da ya fi sa komai wallahi, bakin cikinmu daya zawara da ya maida ta, dama kullum da fargaban aurenta da shegen nake don har raina bana son sa babu yanda na iya ne kawai, banda jarabawa wasu iyayen kwarai ne za su dau er su su ba tsinanne irin Awdul? Khaleesah sai dai kawai tayi hakuri don cuta kam Ali ya cuceta, ya cuci Rayuwarta, don duk shi ya ja mata wannan masifa, da suka ce maka er ka suke so bayan an fito da kai furson in kai uba na gari ne sai ka cije kace sam baka yarda ba sai dai a maida ka furson din ka mutu a can, amma saboda tsoron azaban duniya ba na lahira ba ka zabi ka sadaukar da erka don samu encin kanka, to gashi nan bayan ya rabata da budurcinta ya sako mana ita, dama auren sha'awa kawai yayi da ita, Allah ya isa bamu yafe masa ba wallahi" Nenne na kai wa nan ta fashe da kuka ta jawo kujera er tsugunno ta zauna tana rera kuka sai kuma tace "To yanxu ko zuwa za muyi mu basu hakuri ya dubi girman Allah ya maidata tunda malamai sun ce saki uku a madadin daya yake" Wajen karfe goma na dare Aunty Farida ta zauna gefen Khaleesat dake zaune da cup din kunun da Umma ta dama mata tunda ta kasa cin abinci, Aunty Farida tace "Baki shanye kunun bane?" Khaleesat ta dau cup din ta ci gaba da shan kunun a hankali, Aunty Farida tayi shiru bata sake cewa komai ba tana kallon buhun abubuwan da ita da Umma suka hada zata kai ma Khaleesat gobe, don da gobe zata je wajenta, tun daga dakakken yaji, kubewa busasshe, kuka, kanwa, su citta da kanumfari, gyadar miyar, har da garin danwake da sauran abubuwa da yawa duk su ne a cikin buhun, ga turaren wuta da suka siya mata masu kyau, Aunty Farida ta sauke boyayyen ajiyar zuciya ta kalli Khaleesat da ta kasa shanye kunun hannunta, a hankali ta jawota jikinta, soothingly tace "Kiyi hakuri Daughter, Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu baki daya, kar ki saka komai a ranki kin ji?" Khaleesat ta gyada mata kai, Aunty Farida bata sake ce mata komai ba don ita bata ma son ta tambayi abinda ya hadasu don mayar da maganar bacin rai kawai zai kara masu, Ita dai Umma na zaune kan darduma Islam na bacci a jikinta, Maman Salame ce tayi sallama ta shigo dakin tana kallon Umma tace "Wani labari ne wannan nake ji a garin nan Zahra'u?" Umma dai tayi shiru tana kallonta, Maman Salame ta zauna kan tabarma tana kallon Aunty Farida da Khaleesat dake gefenta tace "Farida" Aunty Farida ta ɗan yi murmushi tace "Ina yini Maman Salame" Maman Salame tace "Wai da gaske ne? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Aunty Farida tace "A ina kika ji Maman Salame?" Maman Salame tace "Ga labari nan ya baza Mariri? Dawowata daga Wudul kenan kusan mutane biyar suke gaya min haka a hanya tun ban karasa gida ba, wallahi buhun hannuna kawai na ajiye bayan na shiga gida na yo nan" Aunty Farida tace "To Allah ya sa mu dace" Maman Salame tana kallon Khaleesat cike da tausayinta tace "Garin yaya haka Khaleesah?" Khaleesat ta sauke idanuwanta bata ce komai ba, Maman Salame tace "To Allah Ubangiji ya sa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu baki daya, in kuma auren bai kare ba Allah ya kaddara za ki koma sai ki ga an koma" Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tace "Ai saki uku ne Maman Salame" Maman Salame ta kasa cewa komai tana kallon Aunty Farida, kana ganinta kasan sosai jikinta yayi sanyi, ita dai Umma babu abinda tace a dakin, bayan kusan minti goma Maman Salame ta mike a sanyaye tace "Toh Allah ya sa mu dace, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu duka, sai na shigo da safe in sha Allah" Umma tayi mata sallama, Maman Salame ta fita daga dakin rai babu dadi, sarai Umma tasan kishiyoyinta ne suka baza labarin a garin, don ko Nenne bazata gaya ma kowa wannan labarin ba ita da ta tsani tonan asiri, Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya don exactly tunanin da Umma take yi ita ma shi ne a ranta, Khaleesat ta kalli Aunty Farida a hankali tace "Aunty kina da number Safiyyah?" Aunty Farida tace "Ina da shi" Khaleesat tace "Ina son zan kirata ne" Aunty Farida tace "Babu kati a wayar, kuma yanxu dare yayi, ki bari gobe da safe sai kiyi magana da ita" Khaleesat ta gyada mata kai sannan ta mike tayi kwanciyarta saman gadon Umma, yaron Mama Shatu ne yayi sallama bakin kofar dakin Umma ya daga labulan yace "Wai Babanmu yace Khaleesat ta je" Umma da Aunty Farida dai sai kallon yaron suke, ya juya ya bar bakin kofar, Khaleesat ta mike zaune bayan taji abinda step brother dinta yace, tun dawowarta gidan ita ko haduwa da baban nata bata yi ba, ta sauka daga saman gadon tana gyara hulan kanta ta fita daga dakin Umma ta bi ta da kallo taji hawaye na taruwa idonta, Khaleesat na tafiya a hankali ta karasa har bakin kofar Babanta don yana zaune kan tabarma shi kadai a bakin kofar nasa, dukawa tayi daga gefen tabarman ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya ta gaishesa, maimakon ya amsa sai taji a hankali yace "Kiyi hakuri Jiddah, i failed you as a father, i caused you all this, but everything happened because I am a nobody, everything happened because...." Shirun da taji yayi ya sa ta daga kai ta kallesa taga hawaye a idonsa, bata san sanda ta fashe da kuka ba, yace "I am sorry for failing you daughter, albarkacin biyayyan da kika min baza ki taɓe ba in sha Allah, my wish for you since u were born was to give you the best of everything i could amma Allah bai nufa hakan ba kaddara ta fada min...." [6/27, 8:51 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Washegari da safe har karfe goma saura Khaleesat bata tashi baccin da take ba, daga Umma har Aunty Farida babu wanda ya tasheta don duk sun san bata yi wani baccin kirki ba daren jiya, daga wayewar gari zuwa lokacin mutanen da suka shigo dakin Umma yi mata Allah ya kyauta da abinda ya faru sun fi goma, don gaba daya labarin ya gama bazuwa garin, Aunty Farida ta kalli Umma bayan wata makociyarsu da ta shigo jajen ita ma ta fita, a fusace tace "Don Allah ki dena tanka masu Umma, ki nuna ke baki ma san jajen uban me suka shigo yi maki ba, wallahi banda ke in ban ci kaza kazan mace ba ta sake shigo mana dakin nan ace ba ni ba, wannan ai iskanci ne" Umma tace "To ya kike son inyi Farida? kinga ai muna mutunci sosai da su shine har ya sa suke shigowa, duk warce kika ga ta shigo dakin nan to muna mutunci sosai ne da ita, kin ga ai bazan masu rashin mutunci ko wani abu ba, wanda ya yaɗa labarin a garin ai shine vabvan munafuki ba wanda ya shigo jajenta maka ba, kuma naga dai ba kan Khaleesat farau ba mutuwar aure" Aunty Farida ta mike tace "Ban taɓa ganin inda ake shigo ma mutum jajen mutuwar aure ba sai a garin nan, kuma wannan ba komai bane banda salon gulma da munafurci" Daga haka ta fice daga dakin zata duba ruwan zafin da ta dora kan wuta, Umma ta kalli Khaleesat da tayi backing dinsu tana bacci, ta kai hannu ta dafata, tayi kasa da murya tace "Har yanxu baccin dai Khaleesat?" Juyowa Khaleesat tayi tana murza ido, sai kuma ta mike zaune, Umma na kallonta tace "Jiya da daddare baki ci abun kirki ba, ki je ki wanke baki ki zo ki karya, ga wainar shinkafa na sa an amso maki tun daxu, kar ya huce" Khaleesat ta jawo hijab dinta ta saka sannan ta sauka daga kan gadon, ta tafi gun akwatinta da ta dawo da shi daga America ta duƙa ta bude jakar ta ciro Shower gel dinta da sponge, sai toothpaste da Brush, Umma dai kallonta kawai take har ta mike zata fita daga dakin Umma tace "Tunda wanka za kiyi kice Farida ta juye maki ruwan zafin, tana waje" Khaleesat tace "To Umma" Daga haka ta fita daga dakin Umma ta bi ta da ido, Khaleesat bata ko kalli inda kishiyoyin Ummanta suke ba da dukun dukun din zannuwan jikinsu kamar masu yin kuli kuli, ta jira Aunty Farida ta juye mata ruwan zafi a bucket ta surka mata sannan ta kai mata har bandaki, bayan ta shiga wankan Aunty Farida ta dora wani ruwan ta koma dakin Umma, Mama Zubaida ta taɓe baki tana murmushi ta kalli Mama Shatu tace "To kuma yanxu ko da uban me za ayi mana takama?" Mama Shatu ta kwashe da dariya tace "In kin tambayeni in tambayi wa? Ba ke kike kokwanton maganar Malam ba da yace auren karkari ayi wata daya ya sakota, to kin dai ga kwalliya ta biya kudin sabulu, sai ki dena cewa kinyi asaran kudin ki, ji yanda hankalinki ya tashi ranan da muka je gidan da Nenne kin ga katon gida ta shiga dakin can ta fito ta shiga wancan ta fito kin zata watayawa take a gidan, ni dama ina kallon kwayar idonta nasan ubanta take ci a gidan, sam ban ga alamar kwanciyar hankali ba don duk a firgice na ganta" Mama Shatu ta sauke ajiyar zuciya ta rike haɓa tace "Ohhh.... Ba karatu a Amurka, ba Miji, ga zawarci, wannan asara da yawa take ni Aisha, wannan shi ne ga koshi ga kwanan yunwa, an ga samu an ga rashi, ina Zahra'u zata saka ranta ta ji dadi" Mama Zubaida tace "Ke baki ga haka ya korota daga ita sai kayan jikinta ba, ko er jakar hannu da ake saka waya fa bata taho da shi ba, dama a haka ya dauketa, kuma kinga ko tsinke ba a kai mata ba dama" Duk suke kwashe da dariya har da kyakyatawa, Mama Shatu tace "Sai a dawo a ci gaba da alalan da aka watsar, don ita kanta Faridan Allah ya sa ɗan zaman da ta dawo suka yi ba a cinye jarin nata ba, nan nan a gabanmu aka yi ta hade haden garin ɗanwake da su kuka da kubewa za a kai ma Khaleesat ashe ashe korota zai yi, ni anjima ma zan shiga a tsam min garin danwaken don naga da yawa suka yi" Tana dariya ta kare maganar, Mama Zubaida tace "Ae wallahi ko tsirara zan yi na gwammace inyi da dai Zahra'u taji dadi da 'ya yanta, in ke kin manta irin cin ƙashin da Malam ya dinga mana bayan ya aurota ni ban manta ba, duk muka zama bora a gidan nan, baya ganin kowa sai Zahra'u tunda da asirinsu na buzaye ta shigo gidan, banda dai dama tun asali idonmu ya bude da Malamai ai da tuni ya sake mu tun bai samu karayar arziki ba, hatta kayan dakin da ya siya mata sai da na zaga na koma kasuwa na tambaya aka ce min nata duk yafi namu tsada, gashi yaranta su ne 'ya yan so barin Khaleesat din nan ai mun sha bakin ciki iri iri Shatu, Ita fa har Umra tayi sannan ga Hajji, mu kuwa iya Hajji kawai muka je mu ka yi tsabar ya maida mu 'yan iska" Mama Shatu ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Ki bar tuna min wannan takaicin Zubaida, banda a tsaye muke ai da wani labarin ake yanxu ba wannan ba, haka mu ma muka yi ta hadata da Malam da taimakon asiri, amma shegiyar bata yi zuciya ta koma kasar su ba da ya fara cin ubanta a gidan, in sha Allahu yanxu ta fara ganin bala'i ita da zuri'arta su da jin dadi ko farin ciki har abada, hatta yan biyun nan ya kamata mu fara miƙa sunansu yanxu kar lokaci ya kure, don naga wani farin jinin jama'a da suke da shi, duk inda suka shiga sai an tankasu ayi ta nan nan da su" Shigowar Nenne gidan yasa suka yi shiru, duk suka gaisheta ta amsa ba tare da ta kallesu ba ta nufi dakin Umma da er ledanta a hannu, duk suka taɓe baki suna bin ta da kallo har ta shiga dakin, Umma da Aunty Farida suka gaida Nenne bayan ta shigo dakin, Nenne ta amsa bayan ta ajiye ledan hannunta tace "Ina Khaleesar take?" Aunty Farida tace "Ta shiga wanka" Nenne tace "Atoh dai, dama ina zata tsaya bakin cikin shege ya kasheta, harkar gabanta kawai zata ci gaba da yi kamar babu abinda ya faru, da auren wannan gansamemen mutumin da rashin aurensa ai duk daya, kuma mu muka cusa mata shi ba sonsa take ba wallahi, yanxu banda ni da ku waye yasan tayi wani gantalallen aure ko da wani ya fito yana son ta, banda dai gulma tayi ma jama'ar Mariri katutu, ai kawai ce ma Ali zan yi ya siyar da gidan nan da nawa gidan mu koma ko Rijiyar Lemo ne" Dukawa tayi ta kwance ledan da ta ajiye tace "Gashi nan, kasuwa na aiki almajirina ya siyo min kayan ciki me kyau nayi mata farfesu ta sha ta mance abinda ya dameta, saki ai ba kanta farau ba, mu ma duk ai an taɓa sakin mu, uban Ali saki nawa ne bai min ba, sai da igiya daya ya rage mana sannan muka nutsu muka zauna har mutuwa ta raba" Wata mata ce tayi sallama bakin kofar dakin Umma, Umma ta amsa mata, matar ta shigo tana gyara yakunannen gyalenta, ganin Nenne ta duka har kasa ta gaisheta, Nenne ta amsa tana rufe farfesun da ta kawo ma Khaleesat kar matar ta barbade farfesun da gyalenta, Bayan matar sun gaisa da Umma tace "Ashe abinda ya faru kenan Ummansu Khaleesah?" Nenne ta juya ta kalleta tace "Me ya faru?" Matar ta langwabar da kai cikin rashin jin dadi tace "Mutuwan auren Khaleesah Nenne" Nenne ta mike tsaye tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, mutuwar auren wace Khaleesar? A ina kika ji auren Khaleesah ya mutu? Na shiga uku na lalace, wato matan Mariri baza ku canza halin ku na tsugudidi ba ko? To daga ke har wanda ya gaya maki kun ci kaza kazan ku yan iska kawai shegu, tashi ki fita ki ba mu waje, sai dai ki ga mutuwar aure a dakin ki ko na uwar ki, kaji min mata dai munafuka, uban mutuwan auren Khaleesah, fita ki bamu waje" Da sauri matar ta fita daga dakin ta saka takalmi wari da wari ta bar bakin kofar, Nenne na huci ta kalli Umma tace "Ke kuma Las spika ki ka dauka kike shelan an saki Khaleesah?" Aunty Farida ta tabe baki tace "Ina fa Nenne, mu ma kawai gani muka yi ana ta shigo mana tun da gari ya waye, wai an zo Jaje, wa enda suka fitar da labarin ai su ne babban munafukai" Nenne na share zufan goshinta tace "Shatu da Zubaida kenan, babu me fitar da zancen nan sai su" Tana kai wa nan ta fice daga dakin, kafin ta fito dama su Mama Shatu duk sun shige dakunan su da sauri bayan sun ji abinda Nenne tayi ma matar da ta fita daga gidan, nan tsakar gida Nenne ta tsaya babu abinda ta manta bata gaya masu ba, zagi kam sun sha har sun gode Allah, Allah ya isa shima tayi masu kwando kwando, daga karshe tace "Kuma in har Ali ya dawo gidan nan anjima bai dau matakin fitar masa da sirrin gida da ku ka yi ba wallahi sai dai ya zaba ko ni ko ku, da dai in zauna da surkai magulmata munafukai gwara in sallame ma duniya Ali in shi bazai sallama maku ba, to ai ita Khaleesar ta samu mashinshini har tayi auren ta fito, ku kuma da naku 'ya yan ke zube kaman gwanjo babu mataya fa? Dama nace ma Ali in har bazai bada su sadaka ba to ni a dena nuna su ace jikokina don kunya nake ji, ko kuma in tattara in bar masa Maririn in har bazai samar ma narka narkan 'ya yanku mafita ba, yanxu in na Jera da Labeebah ba sai ace ita ta haifeni ba, sannan kwata kwata basa wuni a gidan nan ban san inda suke zuwa ba, sai mutum ya shigo sau dari bai gan su sau biyu ba" Khaleesat ta fito daga bandaki tana rike da Shower gel dinta ta nufi dakin Umma, Nenne ta bi ta a baya tana cewa "Kin fito Khaleesah, mu je ga farfesu can na maki" Sai da suka shiga dakin sannan Khaleesat ta gaida Nenne, Nenne ta amsa tace "Kar fa ki ce zaki sa damuwar shegen a ranki kin ji? Allah ne ya dubemu ya rabu dake cikin aminci bai maki wata illa ba, dama kuma ance min uwarsa har tsafi take yi, kinga hada zuri'a da irin wannan mutane ai abun tsoro ne, kar ki saka komai a ranki, rabuwan shi ne mafi alkhairi a gare ki dama an gaya min" Khaleesat dai ta zauna gefen gadon Umma tana shafa cream dinta, Nenne na kallon Umma tace "Ke kuma duk wanda ya shigo maki jaje baki koresa ba Allah ya isa kema, ai mutum daya na shigowa kika rufe ido kika koresa komawa zai yi ya sanar ma sauran, shikenan babu wanda zai sake shigo maki, ni kin ga tafiyata inje in nemi abinda zan ci da rana" Daga haka ta fice daga dakin. Bayan Azahar Khaleesat na zaune kan darduma da qur'ani a gabanta tana karantawa a zuci, sai ga Safiyyah ta shigo dakin Umma da sallama, Khaleesat ta rufe Al-qur'anin ta daga kai tana kallonta tana murmushi, ji tayi kamar all her worries are gone ganin Safiyyah, Safiyyah ta ajiye handbag dinta ta zauna edge din katifar dakin tana kallon Khaleesat a sanyaye, gaba daya ta kasa ce mata komai, Khaleesat ta mayar da Al-qur'anin Aunty Farida gefe sannan ta mike ta koma kusa da Safiyyah ta zauna tana kallonta har sannan murmushin fuskarta bai ɓace ba tace "I miss you so much" Hawaye ne ya zubo ma Safiyyah a ido don kawai ta kasa daure hakan, Khaleesat ta sauke idonta kasa, sai ga hawayen ita ma a idonta, rabonta da zubda hawaye tun jiya a gaban Abbanta, bayan kuma ta shigo ta kwanta bata sake yarda tayi kuka ba duk da kusan yanda taga rana haka taga daren ga zafin da zuciyarta ya dinga mata, Safiyyah ta rungumeta tace "It's fine Khaleesat, Allah ya saka maki abinda yayi maki" Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Safiyyah ta goge idonta don taga alamar kukan da take ne yasa Khaleesat kuka, Safiyyah ta dago kanta tana kallonta tace "Su Umma fa?" Khaleesat tace "Sun je gaisuwa ne anyi rasuwa dazu a unguwan" Safiyyah tace "Allah sarki, Allah ya ji ƙan musulmi" Khaleesat tace "Ameen, ya su Mama fa?" Safiyyah tace "Duk suna lafiya lau, tace in gaisheki, bayan mun gama waya daxu tace in kira mata ke, na sake kiran wayar Aunty Farida naji a kashe" Khaleesat tace "Ehh babu caji ne, ta bada a kai mata wajen caji" Safiyyah tayi shiru, bata son yi ma Khaleesat maganar da zai kara sa taji ciwo a ranta, amma duk da haka calmly tace "Saki nawa yayi maki?" Khaleesat ta buda manyan idanuwanta tace "Kawai ce min yayi ya sakeni" Safiyyah taji bakin cikin ba saki uku yayi mata ba, don ita ba kukan bakin cikin sakin da yayi take ba, a'a bakin cikin mayar mata kawa bazawara da yayi ne babban bakin ciki da takaicinta shi ne yasa har ta zubda hawaye, a gida ma kukan da tayi kenan don taji ciwon abun sosai, Khaleesat ta kalli inda Aunty Farida ta ajiye Envelope din da Drivern gidan su Abdul ya kawo tace "Ga ma can takardan ya aiko" Safiyyah ta juya ta kalli Envelope din, mikewa tayi ta dauko ta dawo ta zauna ta ciro takardan ciki, ita dai Khaleesat kallonta kawai take don har sannan bata duba abinda ke jikin takardan ba, daga Aunty Farida har Umma babu wanda yace mata saki uku ne, jiya kuma da Nenne ke ta hayaniya a tsakar gida bayan an kawo takardan Khaleesat na kwance duk bata san abinda ake ba don abubuwan da suka dameta daban, Safiyyah ta kalli Khaleesat da sauri tace "Saki uku ne ai a takardan" Khaleesat ta amshi takardan a hankali tana dubawa, after some seconds ta kalli Safiyyah tace "Wannan ai ba rubutun sa bane" Safiyyah ta hade rai tace "Do we care?? Ba dai shi aka kawo mana ba, kinga ai da shi za mu yi aiki, don da kika ce saki daya ne sai da gabana yayi mummunan faduwa don matsiyacin zai iya dawowa yace ya maida ke mu shiga uku, amma tunda ga takarda an rubuta saki uku a jiki shikenan an wuce wajen, Alhamdulillah" Khaleesat dai kallon Safiyyah kawai take, Safiyyah ta ajiye takardan ita ma tana kallonta, can a hankali Safiyyah tace "I don't understand you Khaleesat, ko dai bakin ciki da sakin da Abdul yayi maki ki ke? Kin yi give up kan cewa zaki zauna zaman har abada da shi ne? Pls let me know first so that i will watch my words" Khaleesat tayi murmushin takaici tace "Dukan yau daban, na gobe daban, zagi, hantara cin mutunci, living with hunger...." Kasa ci gaba Khaleesat tayi ta fashe da matsanancin kuka tana girgiza kai, Safiyyah ta rungumeta tace "Allah ya saka maki, Allah ya saka maki cikin gaggawa, in sha Allahu sai yaga karshensa tun ba aje da nisa ba, in sha Allah sai hakkin ki yayi tormenting dinsa har karshen rayuwarsa, komin lalacewan gidanku baza a doke ki ba balle a zage ki ko a hantare ki, uwa uba a bar ki da yunwa, In anyi duniya don manzon Allah sai Allah ya nuna ma Abdul iyakansa, wato punching bag ya mayar dake a gidan, kalli yanda kika rame kalanki ya disashe kamar ba ke ba, dubi yanda duk kika fita hayyacin ki, wallahi hakkin ki bazai taɓa barin Abdul ba, ki kwantar da hankalinki ki cire ko wani damuwa a ranki ki dau hakan a kaddarar rayuwarki" Kai kawai Khaleesat ke gyada mata hawaye masu zafi na zuba idonta, Sosai Safiyyah ta dinga bata words of encouragement tana kwantar mata da hankali, har Khaleesat taji sanyi sosai a ranta, taji ta samu relieve din abubuwan da suka tunkushe mata a rai tun jiya, a haka Umma da Aunty Farida suka dawo suka samesu, Umma ta ajiye masu ɗanwaken da ta siyo a makota sanin Khaleesat na son ɗanwake, ba laifi Khaleesat ta ci ɗanwaken me yawa tare da Safiyyah, dama duk yau ta kasa cin komai, ko farfesun da Nenne ta kawo mata kaɗan ta iya ci, amma sai ga shi ta ci ɗanwaken sosai, sai kusan karfe shidda na yamma Safiyyah ta bar gidan, with the relieve that tayi consoling kawarta tunda gashi har tana dariya ta baro ta, sallan magrib kawai Safiyyah tayi ta jawo wayarta tayi dialing number Housemate, wanda rabon su yi magana tun sanda ya gaya mata abinda Khaleesat tayi masu shi da Ajay. [6/30, 11:27 AM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Jay na zaune dakinsa wajen karfe tara na dare yana rike da mug din coffee da yake ta stirring for almost 5 minutes now ya kasa sha, ya daga kai jin an bude kofar dakin, Ajay ne ya shigo ya nufi inda Laptop dinsa yake, shi dai Jay kawai bin sa yayi da ido har ya kunna laptop din ya duka yana dube dube a cikinsa, after almost 2 minute ba tare da Ajay ya kallesa ba yace "Resend me those files u sent yesterday via Email" Jay bai ce masa komai ba, hakan yasa Ajay ya juya yana kallonsa, mikewa yayi ya nufesa, ya cire masa head warmer din kansa ya saka a nasa kan yace "Hey is everything Okay? Me yasa baka fito ka ci abinci ba?" Jay ya mike ya fixge Head warmer dinsa sannan ya koma ya zauna yace "Kai dai ba ka ci ba, cire min Jacket dina Ajay, I can't remember dashing you the Jacket...." Ajay na gyara Jacket din jikinsa ya koma ya ci gaba da abinda yake yi a laptop din Jay, after a while Jay ya ajiye Mug din hannunsa, speaking slowly yace "I spoke to Safiyyah not long ago" Ajay ya kallesa yace "Wacece haka?" Jay yace "My Housemate's friend" Banza Ajay yayi masa ya ci gaba da duba abinda yake yi a laptop, calmly Jay yace "And she...." Ajay ya dakatar da shi sounding pissed off yace "Plss Jay, i am not interested, do not provoke me this night, banda file da nake nema a laptop dinka baza ma ka gan ni a dakin ka da daddaren nan ba" Jay ya mike yace "Whether you are interested or not, Safiyyah ta gaya min gayen ya saki Halysaah" Ajay ya juya ya kalli Jay babu ko kiftawa, after some seconds ya maida idonsa kan laptop din gabansa sai dai bai ci gaba da operating laptop din ba, Jay ya karasa kusa da window din dakinsa ya bude drape din ya rungume hannunsa yana kallon tiny snow din dake zuba kasa, Ajay yace "What did you expect? Were you expecting less? He's satiated his craving, and that is all that he is after, yayi satisfying Lust dinsa" Yana kai wa nan ya rufe Laptop din kawai ya nufi kofa ya fice daga dakin, shi dai Jay da ido ya bi sa kawai, can ya sauke wani ajiyar zuciya ya karasa ya rufe kofarsa da Ajay ya bari a bude. Khaleesat na zaune gaban Coal pot wajen karfe sha biyun rana tana ta fifita gawayin da ta hura zata dora girkin rana at the same time tana gyara waken farantin dake cinyanta, Ummanta ce zata dora girkin don Aunty Farida ta fita kasuwa shi ne ta amshi girkin tace zata yi, shinkafa da wake da mai da yaji ne za su yi da rana, babu kowa a gidan sai ita da Umma don su Mama Zubaida da Mama Shatu sun tafi gidan biki ko girkin siyarwa basu yi ba ranan, Umma ma gidan Nenne take shirin zata je ta kai mata kubewan da ta tambayeta ranan friday, ɗaga kai Khaleesat tayi jin sallaman Safiyyah a compound din su, ta dinga kallonta bata ko kiftawa don bata ce mata zata dawo yau ba, Safiyyah tayi murmushi ta karasa har inda take sannan ta dau kujeran tsugunno da ta gani a tsakar gidan ta zauna tana kallon Khaleesat tace "Sannu da aiki" Khaleesat ta ɗan bude ido tana murmushi tace "You didn't tell me you were coming today Safiyyah" Safiyyah tace "Eh nima ban zata zan zo yau ba, dama ranan Monday ko Tuesday nace maki zan dawo ai" Umma ce ta fito daga dakinta, Safiyyah ta gaisheta da ladabi, Umma ta amsa da fara'a tace "Ya su maman ku?" Safiyyah tace "Sun ce in gaishe ku Umma" Umma tace "Allah sarki, to ina amsawa, bari in je gidan Nenne in dawo yanxu" Safiyyah tace "To sai kin dawo Umma" A haka Umma ta fita daga gidan, Khaleesat ta dora ruwan girkin ta ajiye waken da ta gyara sannan suka shiga dakin Umma da Safiyyah, Safiyyah na kallonta tace "Don Allah ki daure ki dinga cin abinci Khaleesat, kin ga yanda kika rame kamar ba ke ba kuwa" Murmushi kawai Khaleesat tayi tace "To ni dama kiba gareni Sophie?" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Even though, yanxu raman tayi yawa wallahi, ji fa sai idanuwa da dogon hanci kawai" Dariya kawai Khaleesat tayi bata ce mata komai ba, Safiyyah na kallonta tace "Ba dadewa zan yi yau ba Khaleesat, aikoni aka yi wajen ki" Da mamaki Khaleesat ta dinga kallonta, sai kuma tace "Wajena kuma? Wa ya aiko ki" a hankali Safiyyah tace "Ur Housemate" Sosai gaban Khaleesat ya fadi ta dinga kallon Safiyyah babu ko kiftawa zuciyarta na bugawa, Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya ta kamo hannunta tace "Sai dai kiyi hakuri, ni dai na gaya masa abinda ya faru, And...." Sai kuma Safiyyah tayi shiru, Ita dai Khaleesat kallonta kawai take don ta kasa cewa komai tana jin hawaye na taruwa gradually a idonta, a hankali Safiyyah tace "He sent me money for ur flight ticket back to America, and you tuition fee for this semester, ya ce zai samar maki wani apartment din for the one year that is remaining for us...." Hawayen dake makale idon Khaleesat ya zubo, ta kasa ce ma Safiyyah komai, bata san sanda ta fashe da kuka ba sosai, ita dai Safiyyah tayi shiru tana kallonta cause she wasn't expecting less, sai da Khaleesat tayi kukanta me isarta sannan tana girgiza kai muryarta na rawa tace "I don't think za a bari in koma in ci gaba da karatu Sophie" Safiyyah tace "Ban gane ba? Saboda me baza a bar ki ba?" Khaleesat na goge idonta da kyar tace "Saboda Abdul ma da aka bari ya kai ni karatu babu yanda za mu yi ne hakan ta faru, we had no choice then, dalilin haka har sai da Ummata ta samu hawan jini, kin ga yanxu kuwa ai babu wani hujjan da zai sa a sake barin wani ya ci gaba da sponsoring dina a wata kasar" Safiyyah tace "I don't understand Khaleesat, yanxu me kike nufi? So kike kiyi asaran shekarun da kika yi a makarantar kenan?" Hawaye na zuba idon Khaleesat ta girgiza mata kai tace "A'a Sophie, but iyayena za su ji tsoron sake yarda wani ya dau dawainiyata try to understand me" Safiyyah tace "Zan jira har Umma ta dawo daga gidan Nenne in mata magana, ke kam bani da sauran magana dake, cause haushi zaki ci gaba da bani idan na biyeki, banda haka ta yaya ga dama ta samu amma kina neman misusing opportunity din, did you even know what you are saying?shekara daya kacal fa ya rage maki Khaleesat? Dropout kike son ki zama ko me? Ai wani abun mutum ba shi yake bargaining ma kansa hakan ba, you never bargained for all this Khaleesat, situation ne kawai, kina tunanin har a tashi duniya akwai ranan da Yaya Jawwad zai bude baki yace ai ya dau nauyinki a makaranta? Kina ganin Jawwad yayi kama da mutumin da zai maki gori wataran? Ai wallahi daga shi har Cousin dinsa sun girmi hakan, they are too classy for that, Kin zata kowa mahaukaci ne mara aikin yi kamar Abdul? Haba wallahi har kin bata min rai, ban taɓa tunanin zaki nemi kiyi turning down din offer dinsa ba, shi fa taimako kawai yayi saboda yana da halin yin hakan, duba da kin kusa gamawa kuma yasan duk abinda ya sameki, amma sbda rashin tunani irin naki kina neman gwalesa, i was thinking zaman da kika yi da Abdul zai sa ki ɗan canza wasu tunaninki marasu ma'ana, ko kuma in ce Childish tunani" Ita dai Khaleesat hawaye kawai take sosai ta kasa ce ma Safiyyah komai, tasan duk bayanin da zata mata bazata taɓa fahimtar ta ba, Safiyyah ta ciro wayarta ta fara dannawa bata sake ce ma Khaleesat komai ba don da gaske ta ɓata mata rai, after a while Khaleesat ta mike zata je ta wanke wake ta zuba a ruwan da to dora kan wuta, bayan ta gama wanke waken ta zuba ta rufe tukunyar tayi tagumi tana zaune gaban Coal pot din, a haka Umma ta shigo gidan ta sameta, Khaleesat ta sauke hannunta daga tagumin da tayi tana kallon Umma da ta nufota, tace "Umma kin dawo" Umma tace "Na dawo, ina Safiyyar?" Khaleesat tace "Tana ciki" Umma tace "Shi ne kika bar ta ita kadai" Khaleesat tace "Yanxu na fito in zuba wake ne" Aunty Farida ce ta shigo gidan da abubuwan da ta siyo a kasuwa, Umma tayi welcoming dinta sannan ta karasa dakinta ta shiga ciki da sallama, Safiyyah ta amsa tana mata sannu da zuwa, Umma ta cire Nikab da hijab dinta ta linke tace "Bata baki ko ruwa ba?" Safiyyah tayi murmushi tace "Umma ni ke nake jira ma tafiya zan yi" Umma ta zauna tana kallonta tace "To gani Safiyyah, lafiya dai ko?" Safiyyah tace "Lafiya lau Umma" Kafin Safiyyah ta ce komai Aunty Farida ta shigo dakin, Safiyyah ta gaisheta tana murmushi, Aunty Farida ta ajiye kayan hannunta tana amsa gaisuwan Safiyyah da fara'a, Umma dai kallon Safiyyah take tana jiran jin abinda zata ce, Babu bata lokaci Safiyyah ta fara yi ma Umma bayanin duk yanda suka yi da Housemate din Khaleesat, ita dai Aunty Farida na tsaye ita ma tana sauraron bayanin Safiyyah, Umma ta ɗan yi murmushi bayan Safiyyah tayi shiru tace "Allah sarki, mun gode sosai da kulawan sa, amma dai ki maida masa kudinsa Safiyyah, don ko babanta ma bana jin zai yarda, Abdul ma da ya kai ta karatun ba mu da yanda muka iya ne Safiyyah, Allah ya amfana abinda ta samu" Safiyyah was speechless, Aunty Farida ta dinga kallon Umma jin abinda tace, can tace "Allah ya amfana abinda aka samu kuma Umma? Shikenan fa tayi asaran karatun gaba daya idan bata karasa ba, kamar ka fara gini ne fa ya ruguje har kasa ya rage Foundation, ai kin ga kuwa baza kace Allah amfana abinda aka samu ba" Umma ta kalli Aunty Farida tace "Farida kin fi kowa sanin ban taɓa goyon bayan fitar Khaleesat karatu waje ba tun asali, daga ni har mahaifinta babu yanda muka iya ne, don haka Khaleesat bazata koma Amurka da sunan karasa karatu ba, ashe ma bamu dau darasin abinda ya faru a baya ba kenan" Aunty Farida bata sake ce ma Umma komai ba ta hau fiddo abubuwan da ta siyo a kasuwa, Ita ma Safiyyah tayi shiru don bata ma san me zata ce ba, Umma na kallon Safiyyah tace "Ki masa godiya kawai ki mayar masa da kudinsa Safiyyah, Allah ya dubi niyyarsa na alkhairi ya saka masa, ba wai ni kadai ba, hatta Mahaifinta ma ba yarda zai yi ba Safiyyah, cutar da ita da muka yi da farko ma da muna da wani dubaran da baza ayi haka ba, kin ga in mu iyayen arziki ne ai baza mu yarda ayi na biyu ba" Aunty Farida ta mike tace "To shi Umma ce maki yayi da wata manufa zai biya mata kudin karatun har kike tunanin za ayi na biyu? Shi fa Abdul duk abinda yayi yana da manufar yin hakan duk mun sani, ba haka kawai ya dauketa ya kai ta karatu ba...." Umma ta dakatar da ita tace "Ban ce shi wannan bawan Allahn yana da wata manufa ba amma dai kam Khaleesat bazata koma Amurka ba Farida" Aunty Farida bata sake tanka Umma ba ta fitar da albasan da ta siyo zata je ta shanya a bakin kofa, Safiyyah ta sauke boyayyen ajiyar zuciya a hankali tace "Toh shikenan Umma, ni zan koma gida, dama abinda ya kawo ni kenan" Umma tace "To ki gaida mutanen gidan Safiyyah mun gode kwarai, shi ma ki yi masa godiya don Allah" Safiyyah tace "To Umma" Jiki a sanyaye ta mike ta fita daga dakin, Aunty Farida ta dau hijab dinta da ta rataye a igiya tayi ma Safiyyah alamar su je waje, ita dai Khaleesat na zaune inda take bata tashi ba don duk taji conversation din Safiyyah da Ummanta, Aunty Farida na fita kofar gida da Safiyyah tace "Safiyyah kar ki yarda ki gaya masa abinda Umma ta ce, ki bari Babanta in ya dawo anjima zan samesa in yi masa magana" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya tace "To Aunty, don Allah ki yi convincing dinsa shi ma, It will be very sad idan aka ce bata karasa karatun nan ba, shekara daya fa kawai ya rage mana" Aunty Farida tace "In sha Allah zan yi bakin kokarina, kuma Khaleesat zata ci gaba da karatun ta" Safiyyah tace "To Aunty, gobe da safe zan kira ki sai inji yanda ku ka yi da Baba" Aunty Farida tace "To babu damuwa, ki gaida gida" a haka suka rabu Aunty Farida ta juya ta koma cikin gida... Khaleesat ta gama girkin da take bayan ta kashe gawayin tayi alwala ta shiga dakin Ummanta, tana idar da sallah ta kwanta, gaba daya taji damuwarta ya dawo sabo fil maganar Housemate dinta da Safiyyah ta kawo mata, Umma na kallonta tace "Baza ki ci abincin bane yanxu?" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "Sai anjima" Ita dai Aunty Farida linke kayan su Islam take don tun bayan tafiyar Safiyyah bata ce ma Umma komai kan maganar da Safiyyah ta kawo ba sanin Umma bazata taɓa fahimta ba. Bayan Magrib Aunty Farida ta samu Malam Ali yana zaune kofar dakinsa, bayan sun gaisa yace "Amma ba Lagos kika zo gaya min zaki koma ba Farida?" Murmushi kawai Aunty Farida tayi don in akwai abinda ya tsana zamanta Lagos yayi fadan har ya gaji, ta kauda tambayar da yake mata tace "Magana na zo mu yi kan Khaleesat" Yayi shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace "To ina sauraron ki" Cikin nutsuwa Aunty Farida ta sanar masa batun da Safiyyah ta zo da shi daxu da rana, Malam Ali ya girgiza kai yace "Ashe ban daddara ba kenan Farida, na yi tunanin duk mun dau darasi kan abinda ya faru wanda duk nafi kowa laifi a ciki...." Aunty Farida ta kwantar da murya tace "Ae wancan issue din da wannan ba daya bane Malam, shi fa Abdul da isa da gadara ya turata karatu Amurka kuma babu yanda muka iya haka duk muka sallama masa domin zaman lafiyanmu da naka, Abdul da manufarsa na tura ta karatu, shi ko wannan bawan Allahn babu wata manufa a ransa, saboda Allah zai biya mata ta karasa karatun kar tayi asaran shekarun da tayi, iya shekara daya fa ya rage mata Malam, ka san muhimmancin karatun nan balle ka kushe komawarta America ta karasa, in kowa zai kalubalanci haka ai banda kai Malam, don Allah ka duba wannan lamari, kuma shi wannan bawan Allahn da ya ce zai dau nauyin shekara dayan da ya rage mata su ne fa suka dau maka lauya har aka wanke ka a kotu aka kashe maganar bashin ka da Baban Abdul...." Malam Ali yayi murmushi yace "Ai nayi appreciating hakan da suka min kuma kullum ina saka su a addu'ata, amma babu zancen komawar Jiddah America karatu Farida, kiyi hakuri a bar batun nan gaba dayanta, we shouldn't be a bad parent for the second time saboda son abun duniya, tayi hakuri in Allah ya hore min sai in biya mata tayi Jamb ta nemi ko BUK ko Northwest, duka duka shekarunta nawa suke? Ai lokaci bai kure mata na karatu ba Farida, kuma ko aro ne zan nema in biya mata in sha Allah, don haka bana son a sake tada zancen ci gaba da karatun ta a America" Aunty Farida tayi shiru bata sake cewa komai ba, after a while tace "To shikenan, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi" Yace "Ameen" Mikewa tayi ta bar wajen rai babu dadi. Washegari wajen karfe tara Aunty Farida ta gama shirin da take, Umma dake kallonta tace "Ina za ki ne?" Aunty Farida na dora Nikab dinta kan Hijabin jikinta tace "Ba nace maki zan je gidan Abida ba shekaranjiya" Umma tace "Shi ne zaki mata sammako?" Aunty Farida tace "Jiya tace min bata da lafiya ne, kuma ina son in dawo da wuri in wanke kai na" Umma ta tabe baki tace "To sai kin dawo" Ita dai Khaleesat juya kokon gabanta take a hankali tana sha ga dumamen tuwo shi ma a gabanta, da kyar take shan kokon, dumamen kuwa ta kasa ci, dama jiya da daddare ma bata wani ci tuwon ba, Aunty Farida tayi ma Umma sallama ta fita daga dakin. Nenne na gyara daurin dankwalinta tayi kasa da murya tace "To ke banda abun ki ai Zahra'u Jahila ce Parida, matar da har yau bata da wayewa kanta a murfi yake kamar matar kauye, ita ta wani san maki muhimmancin karatu kina ganin mata haka kara zube, gashi sai yanda kazaman kishiyoyi suka yi da ita sun mayar da ita Bora? Ai bari ki ji Parida, Zahra'u a yanxu dai ita daga tuwo sai bautan Allah kawai ta saka a gaba, babu ruwanta da wani ci gaba na duniya ko kyale kyalin duniya, ta riga ta amince ta kare rayuwar ta a haka in dai zata ci tuwo tayi bautar Allah, shi yasa kullum zaki ganta rike da carbi a kuturin dakinta da ko Ceiling din arziki babu, ni bana ma jin Zahra'u na yi ma Ali addu'an Allah ya dawo masa da arzikinsa don in tayi hakan gani zata yi kamar ta butulce ma Allah, duk tunaninta fa haka Allah ya so ganinsu cikin baƙin talauci, gani zata yi in tayi ta ma Allah magiyan ya yaye masu talauci kamar butulci tayi bata gode da ni'imarsa ba tunda tana samun tuwo ta ci, to irin tunanin yayarki kenan Parida, in ba haka ba ta yaya zaki dinga yi ma er cikinki bakin cikin karasa karatu ta taimake ku a rayuwa ta cire ku daga kangin talauci? shikenan kuma don kai jahili ne sai ka rasa sanin abinda ya kamata? Har wani kwambo fa take da jahilcin ta da rashin wayewa, ki bar ni da su kawai zan yi maganinsu daga Alin har Zahra'un, da can uban me yasa suka bari aka kai ta Amurkan in har da tsoron Allah a lamarinsu daga ita har Alin? Wato sai yanxu suka zama iyayen kirki masu tsoron Allah ko? To zan yi maganinsu gaba daya, in dai karatu ne kamar Khaleesah taje Amurka ta karasa in har ina numfashi, Allah ya kai mu anjima da yamma, Alin ai zai dawo daga zaman kashe wandon da yake yi a kasuwa, zan je har gidan in samesa inji ko na tauye masa karatunsa duk da talauci na, in de ni na amince taje to ko wani ɗan iska ma kar ya amince" Nenne na kai wa nan ta mike ta jawo kofar dakinta ta kulle da kwado, sannan ta dau mayafinta sabo dake rataye saman igiya ta yafa, ta dau handbag dinta ta saka makullin kofar a ciki, ta zura takalmanta ta nufi kofar fita daga gidan tana taku dai dai don sabuwar atamfa ce a jikinta, Aunty Farida ta bi ta da kallon mamaki tace "Wai fita zaki yi ne Nenne?" Ba tare da Nenne ta juyo ba tace "To me zan maki, anguwa har uku zan je yau da kika gan ni, bazan zauna a banza ki bata min lokaci ba, in ba gulma ba ganinki nake yi a gidana, ni dai in kin gama zaman kin fito ki ja min kyauren gidana kar almajirai su shiga su min sata" Daga haka Nenne ta fice daga gidan, murmushi Aunty Farida tayi ta mike ta nannade mata tabarmanta ta ajiye sannan ta daura nikab dinta, bin bayanta tayi da sauri don jadadda mata kar tace ita ta zo ta gaya mata maganar don tasan tsaf sai yayarta ta kullace ta. [6/30, 6:59 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Wajen karfe shidda na yamma Khaleesat na zaune bakin kofar dakin Ummanta tana yanka mata alaiyahu a cikin roba, stepsisters dinta Labeebah da Lamisah na can zaune su ma daga bakin kofar dakin Mama Shatu da kawayensu sai hira suke suna shewa duk sun cika tsakar gidan kai kace gidan biki ne, Mama Shatu da Mama Zubaida su ma suna tsakar gidan don da su ake hiran da kawayen 'ya yan nasu, magana daya biyu sai su kwashe da dariya, yawanci kuma duk habaici suke jefa ma Umma da Khaleesat, ita dai Umma tana zaune gaban Coal pot tana kwashe tuwon masara da ta gama tukawa, Aunty Farida kuma ta tafi Hotoro tun bayan la'asar da su Noor, Nenne ce ta shigo gidan rataye da jakarta a kafada, lkci daya gidan yayi tsit, a takaice Nenne ta amsa gaisuwan da su Mama Zubaida da Lamisah da kawayensu ke yi mata ta nufi gun Umma tace "Zahra'u Alin ya dawo ko be dawo ba?" Umma ta gaida Nenne sannan tace "A'a bai dawo ba tukun Nenne, sannu da zuwa" Nenne tace "Kin gan ni nan daga Sheka nake daga can na tafi Ɗan Agundi, ni ce har Na'ibawa yau, tun safe na bar gida sai yanxu nake dawowa 'yan adaidaita sahun kano dai sauransu yawo da bindiga kawai...." Murmushi kawai Umma tayi tana ci gaba da kwashe tuwon da take yi, Nenne ta jawo kujera ta zauna tace "Gidan Katime me Aya na tafi a Sheka, in gaya maki me Aya dai kafafuwanta sun mutu murus Zahra'u, ko tashi bata iya yi, babu yanda ban yi da matar nan ta rage cin nama ba amma taga kamar bakin ciki nake mata don mijina baya kawo min, to yau ni da ban ci nama ba gani da kafafuwana biyu rass, ita kuwa duk sun mutu, wai tana ganina ina taku dai dai na shigo gidan sai ta fashe da kuka, ni dai bata ban tausayi ba wallahi, sai kinga yanda take mana fafa da nama lokacin, kullum kya ji kamshin tafashen nama a gidanta, mu sai dai mu watsa er daddawa a miya" Umma na girgiza kai tace "To Allah Ubangiji ya bata lafiya" Nenne tace "Ba batun Allah ya bata lafiya ba, ai duk kafafuwan sun rube, da kyar in baza ace za a yanke mata su ba tunda ko motsa su bata iya yi " Su Mama Zubaida gaba daya kunnuwansa na kan labarin da Nenne ke ba Umma, Malam Ali ne ya shigo gidan da sallama, Nenne ta juya tana kallonsa, can ta mike ta nufesa tace "Yanxu Ali baza ka hakura da fita kasuwar nan ba tun da ba wani abu kake yi a can ba sai zama cikin rana da iska? Ka dubi yanda duk kayi bakikirin kamar baka taɓa haske ba a rayuwarka Ali, tunda ba aikin fari gareka ba balle baƙi a kasuwar ka hakura da zuwa mana" Gaisheta kawai yayi ya dau buta zai debi ruwa ya fita waje ya zauna ya jira Magariba, Nenne ta tabe baki tace "To wajen kai da matar ka Zahra'u na xo" Umma ta juya tana kallon Nenne jin abinda tace, Shi ma ya tsaya yace "To lafiya dai ko?" Nenne tace "A ina lafiyar take, ba sai kun nemi zaman lafiyar za a zauna lafiya ba, labari na samu wai masu kare hakkin 'yan Adam sun zo gidan nan sun ce za su ci gaba da daukar nauyin karatun Khaleesat a Amurka saboda tausayin abinda tsinannen mutumin nan Awdul yayi mata, to amma wai saboda kai da Zahra'u yan bakin ciki ne sai ku ka gwalesu ku ka koresu, da wanne ku ke son yarinyar ta ji fisabilillahi? Da mayar da ita bazawara da aka yi tana da karancin shekaru ko kuma da asaran karatun ta da kuke kokarin yi mata? In ita Zahra'u jahila ce bata yi karatun boko ba kai ma Jahili ne Ali? Ina ne ban shiga nayi aikatau ba don kayi karatu? To wallahi ko karshen bangon duniya ne sai Khaleesat ta koma ta karasa karatun ta tunda har aka ce za a dau nauyinta babu ko sisin ku, to ina ma ku ka ga ko sisin" Malam Ali dake ta kallon uwar tasa yace "A ina kika ji wannan zancen Nenne?" Nenne tace "Labarin duniya na buya ne dama? Ina zaune yan Mariri suka zo suka tsegunta min har unguwan da naje yau...." Mama Shatu ta kalli Mama Zubaida da ta saki baki tana sauraron Nenne, Mama Zubaida ta kasa daurewa ta gyara zama cikin kwantar da murya tace "Amma Nenne na farkon ma ba a wanye lafiya ba shi ne za a sake na biyu? Dama gashi duk garin nan kallon makwaita masu son abun duniya kawai ake mana, ko ina sai zaginmu ake tun da aka samu labarin sakin walakancin da aka yi ma Khaleesat, ana ta cewa ubanta ne ya ja mata, A rayuwar nan yanxu fa in ba iyayenka ne za su yi maka dawainiya ba duk wanda yace zai dau dawainiyar ka sama ta ka to da wani abu da yake hangen zai samu a gare ka ne, Khaleesat fa 'ya mace take ba namiji ba Nenne, kuma ba komai ke rudar maza akanta ba sai kyanta da kalan fatar ta sun ga buzuwa, shi kenan saboda son abun duniya sai a zuba ido har sai yarinyar nan ta lalace tukunna, Abdul ya gama nasa ya samu abinda yake so ya sako mana ita sai kuma yanxu ace ga wani ma ya zo wai zai ci gaba da daukar nauyinta? Haba sam batun nan babu tsari a cikinta, shikenan ita kuma haka ta zama kamar Tasi...." Nenne ta kundumo wani zagi tace "Toh duk wanda ya fasa fadin abinda ke ransa akan Khaleesah Allah ya tsine masa albarka, kuma in de karatu ne kamar tayi ta gama sai dai bakin ciki ya kashe duk wani shege wallahi, ko ma ina za a kai ta a kai ta ni na amince ta je, ai ita tasan tarbiyyar da muka yi mata in ma ta gantalar da tarbiyar ita da Allah, kuma gobe gobe zan sa a kira min baƙar kawar tata ta zo in gaya mata uban Khaleesah ya amince koma waye zai dau nauyinta ya dauka, taje can ta ci gaba da karatun ta, ai gwara tayi nesa da mu ko bakin cikin dake damunta a rai zai ragu, mu kanmu in tana ganinmu takaici da bakin ciki take don ba mu da wani babanci da Awdul a wajenta tunda mu muka ja mata komai, gwara ta koma ta gama karatunta ta dawo da kwalinta don bazata tashi a tutar babu ba, shi kansa Awdul din yana samun labari an samu wanda ya maidata Amurka ta ci gaba da karatu sai bakin ciki ya kusa kashe shegen, a nan kuma zai san ba a banza Khaleesah take ba farin jininta ya shahara" Nenne na huci ta juya ta kalli Umma tace "Ke kuma Zahra'u halan tallan alalen ki ke da niyyar dora mata da kike mata bakin cikin komawa ta karasa karatun? To kamar yanda kike takama kina da iko da ita nima haka tunda ni na haifi ubanta, ban ga shegen da ya isa yace bazata koma ta karasa karatun ta ba" Ita dai Umma bata ce ma Nenne komai ba, Malam Ali dai na tsaye rike da buta a hannunsa yana kallon uwarsa, can dai yace "Amma dai Nenne sam babu tsari ace mun sake barin yarinyar nan ta bar kasar nan da sunan wani zai dau nauyinta bayan duk abinda ya faru, me kike son jama'an gari su ce a kaina? Sannan nace duk sanda na samu kudi zan nema mata Jami'ar garin nan tayi, ba wasu shekaru gareta ba balle ace lokaci zai kure mata" Nenne ta kallesa da sauri tace "A gidan uban wa zaka samu kudin? Mutanen garin in sun fasa fadin abinda za su fada a kanka Allah ya tsine masu albarka, kai bari kaji Ali bana bukatar ra'ayinka ko shawararka a yanxu saboda kai ma sanda ka bi ra'ayinka ka yarje ma Awdul ya kai ta kasar waje babu wanda ka saurara ko kaji shawaransa, don haka ni ma yanzu wallahi bazan saurare ka ba Amurka ne sai Khaleesat ta koma ta karasa abinda ta fara in sha Allahu, in kuma nuna ma duniya zaka yi ni er banza ce a gareka to Bismillah" Kofar gida kawai Malam Ali ya fita da butansa a hannu, Nenne ta kalli Khaleesat tace "Maza ki hada akwatinki ki tsaya cikin shiri, in sun biya maki kudin jirgin ki kama gabanki kije kiyi abinda zai taimaki rayuwarki, zama gidan nan kadai ya ishi mutum ya fada cikin mummunan damuwa, gida kamar na 'yan sansanin gudun hijira, ga lafta laftan mata suna yawo suna doyi a cikinsa, ai ko mutum matsiyaci ne ya kasance dai yana da tsaftarsa dai dai gwargwado, amma gidan nan ga talauci ga kazanta, ina bawa zai iya rayuwa a nan idan ba dole ba" Nenne na kai wa nan ta kama hanya tayi tafiyarta, Khaleesat ta daga kai ta kalli Umma da ta bi Nenne da kallo, Mama Shatu ta mike tana kallon Umma tace "Muddin kika ce baza ki bude baki kiyi magana ba to kina ji kina gani za a mayar maki da er ki karuwa Zahra'u, wata birkitacciyar tsohuwa can kamar Nenne ce zata yanke ma er da kika haifa hukuncin abinda ya shafi rayuwarta? Ita ta tsugunna ta haifar maki er? Mu meyasa ba a mana iko akan namu yaran ba? Saboda an san baza mu dauka ba mu ba yan iska bane, to kuwa wallahi Nenne na dab da kai ki ta baro ki, mata me tabin ƙwaƙwalwa zaki yarda ta yanke hukunci akan 'er ki? ai in ita Khaleesar ta bude baki tace bazata je ba babu uban da zai tilastata ta je wallahi, waye bai san Nenne da kwadayi da son abun duniya ba kamar tayi sata?" Muryar Nenne suka ji ashe tana makale bata tafi ba tana jiran jin abinda za a ce, Nenne ta dinga kwalo ma Malam Ali kira, sai gashi ya shigo da sauri yana kallonta yace "Lafiya Nenne? Ai magana ta wuce yanda kika ce haka za ayi" Mama Shatu tayi wuri wuri da ido daga inda take tsaye, Mama Zubaida ta mike ta lallaba ta dau kwandon kwanon wanke wankenta ta shige daki ta sako labule, Nenne ta rushe da matsanancin kuka tana kallon Malam Ali tace "Ali yau sai dai ka zaba ko ni ko Shatu a gidan nan, kawai ka zaba ko ni ko ita, ni Shatu zata kalla ta kira me tabin ƙwaƙwalwa wato mahaukaciya er macukule? Ni zata ce ma me kwadayi da son abun duniya? Tunda nake me na taɓa zuwa gun almajirin ubanta dake bara a bakin danja nace ya bani? Me na taɓa rokon uwarta me shanyayyen kafa? Bata san ina labe ban tafi ba duk ina jin abinda take cewa, cin mutunci da zagi sai wanda ta manta ne bata min ba Ali, har tana gaya ma Zahra'u ni na haifar mata er da zan yanke mata hukunci akan ta? Me nayi ma Shatu da har zata yi mugayen kalamai haka a kai na? Naga dai kullum ci gabanka da na iyalan ka shi ne burina, fadi tashi babu wanda bana yi akan kai da iyalinka, amma daga karshe sai zagi da cin mutunci ya biyo baya, tsofe tsofe da ni Shatu tace min me son abun duniya?" Kuka sosai Nenne take tana share idonta da gyalen jikinta, Malam Ali na kallon Mama Shatu da tayi tsuru tsuru yace "Shatu ki tafi gida, sai na neme ki" Mama Shatu ta gwalo ido tace "Ban gane in tafi gida ba Malam, wani gidan zan tafi?" Malam Ali yace "Gidan iyayenki, ki je na sake ki" Mama Shatu ta zabura tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ka sake ni fa kace Malam, na shiga uku na lalace" Labibah ta mike tana huci tace "Gaskiya Baba sai dai mu bi Baabarmu mu ma" Nenne tace "Shegiya ku bi ta mana, yunwar cikin ku kadai ma ya isheku ai" Malam Ali na kallon Mama Shatu dake rusa kuka yace "Kar in dawo in sameki a gidan nan" Daga haka ya fice daga gidan, Nenne ta bi bayansa tana goge idonta ita ma ta fita, sai a sannan Mama Zubaida ta fito tana salati tana kallon Mama Shatu dake kuka wiwi, Umma tsabar yanda jikinta yayi sanyi ta ma kasa cewa komai daga inda take zaune, Mama Zubaida na kallon Umma tace "Ke kam kinyi asara wallahi Zahra'u, ko wani bala'i ta dalilin ke da tsinannun 'ya yan ki yake faruwa a gidan nan, gashi yau saboda ke da er ki an saki Shatu, sam babu alkhairi a tare dake da zuri'ar ki Zahra'u" Umma ta juya tana kallon Mama Zubaida sai dai bata ce komai ba, Khaleesat ma ta daga kai tana kallonta, Mama Shatu na kuka sosai tace "Kuma in sha Allahu asirin da kike yi zai kare maki a gidan nan Zahra'u, yanda kika yi sanadiyyar tsinkewar igiyar aurena daya ke da er ki wallahi sai nayi sanadin naki igiyar kema, ko tsirara zan yi yawo kuwa, Ni saki daya aka min ke ukun gaba daya za a maki, kuma kamar Ali ya maida ni ne don yanxu na fara auren sa wallahi" Don mamaki Umma ta ma rasa abun ce masu ganin yanda suka juya zancen lokaci daya, yau ga fadan karfin hali tana gani kiri kiri, biyesu ma bata lokaci ne kawai a wajenta ga makota na jin su, tsam ta mike tayi shigewarta daki, Khaleesat ta mike ta bi bayanta. Washegari da sassafe Umma da Aunty Farida suka fito tsakar gida suka tarar da Mama Zubaida da Mama Shatu a tsaye suna jiran fitowarsu za a je ba Nenne hakuri, ko wanne da Hijab dinsa har kasa don sanyi ake sosai, duk abinda suka yi ma Umma jiya hakan bai sa tace bazata bi su zuwa gidan Nenne ba, Su ma din sun san ta dalilin Umman sai Nenne ta iya hakura ta sa Malam Ali ya maida Mama Shatu shi yasa Mama Zubaida da kanta ta samu Umma ko kunya babu tayi mata magana wajen karfe biyar din asuba, Mama Shatu dama a makota ta kwana ranan don sae da Nenne ta dawo ta korata har da watsi da en tsummokaran ta, sae kusan hudun asuba Shatu ta dawo gidan daga inda ta kwana, a haka duk suka kama hanya zuwa gidan Nenne da asuban. Ranan Thursday da safe Khaleesat na zaune dakin Umma tana kallon Aunty Farida dake ta jera mata kayanta da aka amso wajen guga a cikin akwati, ita dai Khaleesat har sannan ta rasa gane me take ji a ranta, farin ciki take ko akasin haka duk ta kasa ganewa, babban damuwarta yanxu bata san da idon da zata kalli Housemate dinta ba idan ta koma America, sannan gani take kamar babban burden kawai zata zame masa a can din tunda ita ba komai gare iyayenta da za su tallafa mata da shi ba idan ta koma, ɗan kudin dake account dinta ba wani kudin kirki bane kuma da shi ta siya sabon waya with new sim card, sai few abubuwan da tasan zata bukata a can kasar, sauran kudin dake account dinta ko dubu dari da hamsin bai karasa ba, duk wannan tunanin yasa take damuwa sosai a ranta, Aunty Farida ta daga kai tana kallonta kafin ta rufe zip din jakar tace "Baki manta komai ba dai ko?" Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Aunty Farida tace "A Airport din za ku hadu da Safiyyah goben?" A hankali Khaleesat tace "Eh" Aunty Farida ta kulle zip din tace "Gwara ki saki ranki kiyi abinda ke gaban ki Khaleesat, ki cire duk wani damuwar dake ranki kar ki je ki samu matsala a karatun ki, shi kuma Jawwad Allah ya saka masa da mafificin alkhairi...." Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, lkci daya taji hawaye ya cika idonta, Aunty Farida ta mike ta dauko daya akwatin don hada few foodstuffs din da suka siyo mata da Umma wanda zata iya shiga Amurka da shi, a hankali Khaleesat tace "Toh Aunty ta yaya za a maida masa kudinsa dake account dina?" Aunty Farida ta daga kai ta kalleta, can tace "Kudin wa? Ko Abdul?" Khaleesat ta gyada mata kai, Aunty Farida ta saki baki, can tace "Wai dama har yanxu kudaden nan nasa na account din ki?" Khaleesat ta gyada mata kai, shiru Aunty Farida tayi kamar me nazari, after a while tace "Ki ci gaba da ajiye kudin kawai Khaleesat, duk sanda ya dawo ya bukaci kayansa sai a basa, ko Umma kar kiyi ma maganar kudin for now, bana son a samu delay a tafiyarki don yanxu sai su iya cewa sai an maida masa kudadensa, kuma hakan zai iya ja maki delay...." Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, Aunty Farida ta ci gaba da hada foodstuff din da take a akwati. [7/1, 1:11 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Wajen karfe uku na yamma Khaleesat na zaune bakin kofar dakin Umma Aunty Farida na combing din mata dogon gashinta bayan ta wanke mata shi da Shampoo da Conditioner, har wani sheki baƙin gashin nata yake yi bayan Aunty Farida ta shafa mata man gashi, tun daga wajen wanke gashin Aunty Farida ke ta mata fadan ta bar gashinta ya kakkarye saboda banzan da tayi da shi ta dena kula da shi, ita dai Khaleesat bata ce mata komai ba don har sannan basu san irin zaman da tayi a gidan Abdul ba, don ma abun ya tsaya iya kakkaryewan gashi, har bata son tuna experience dinta a gidan Abdul hakan yana traumatizing dinta, su Mama Zubaida da Mama Shatu dai na bakin murhu suna girka abincin siyarwansu na yamma, suna yi suna kuskus a bakin murhun, lkci lkci sai su kalli direction din su Khaleesat, ita dai Aunty Farida dama ko kallo basa isanta a gidan, a da dai ta biye su har dambe sun sha yi amma yanxu bata da wannan time din, kallon stark illiterates kawai take masu, wasu mata biyu ne suka shigo gidan babu ko sallama, sun yi shiga ta alfarma sun sha gwala-gwalai suna taku cikin isa, at the same time suna bin ko ina na gidan da kallo cike da kyama gashi dama su Mama Zubaida sun yi gaje gaje da ruwa a tsakar gidan ranan, Khaleesat ta dinga kallonsu haka Aunty Farida da ta ajiye comb din hannunta, Mama Zubaida ta mike tace "Sannun ku da zuwa ko dai batan hanya ku ka yi ne, in gidan Hajiya Samira matar Alhaji Bala ku ke nema can karshen layi za ku karasa sai ku yi tambaya a nuna maku gidan, amma ba nan bane" Momy ce ta shigo gidan tana tafiya gansan gansan da Drebanta a bayanta yana biye da ita, mayafin nata ma ko yafa shi bata yi ba, gashi ta sha wani tsadadden baƙin glass no respect, Khaleesat ta dinga kallonta babu ko kiftawa, lkci daya taji gabanta ya fadi sosai, ta juya ta kalli Aunty Farida, sai ga Meemah ita ma ta shigo gidan tana yatsine fuska, ita ko mayafin ma babu a hannunta, Aunty Farida ta dake tace "Bayin Allah lafiya? Daga ina haka, babu ko sallama" Daya daga matan da suka shigo da farko tana ma Aunty Farida wani matsiyacin kallo tace "Ba shi ya kawo mu ba, a irin wannan bolan za ayi maku sallama?" Umma ta fito daga dakinta don tana jin duk abinda ake cewa, tsaye tayi bakin kofa tana kallonsu, Mama Shatu da Mama Zubaida dai sai zazzare ido suke kamar wa enda suka yi ma sarki karya, Momy ta karaso har tsakiyar compound din tana tafiya cikin isa da gadara, fuskar nan nata babu ko digon mutunci tace "Zuwa nayi in ji ko shegiyar er ku tana da gadon Abdul ne, Ko kuma shi ma satan da ku ka yi ma ubansa kuke da niyyar za ku yi masa, in kuwa babu gado to yanxun nan ba sai anjima ba a maido mana kudadensa dake account din er ku..." Umma ta kalli Khaleesat nan da nan hankalin Umma ya tashi sosai, Aunty Farida tace "Ikon Allah, shi ne sai anyi wannan zuga haka kamar za ayi yaki?" Meemah ta matso har gaban Aunty Farida tana mata matsiyacin kallo tace "Yakin ne ai, ko kin ga alamar da sassauci muka zo? sanin halin familyn na ku na sata wanda ku ka gado a gun Malam me dattin hula ya sa mu ka yo tattaki a mayar mana da kudaden mu tun wuri, ai kowa yasan sata da cin amana shi ne tambarin gidan nan, don haka tun wuri ba a jiyo kan mu ba a maido mana Miliyan goman Abdul, kun zata bulus za ku ci ga banza ta fadi ko? To Sponsoring din matsiyaciyar er ku da ya dinga yi da kudinsa ma ai ba yafewa yayi ba sai kun biyasa a lahira wallahi, kawai babban farin cikin dake saka ni nishadi idan na tuno shi ne karewar da zata yi as dropout din John Hopkins university, don ko kaf zuri'arku za ku siyar baza ku samu kudin biya mata ta ci gaba da karatun a kasar Amurka ba, da yau ta gama John Hopkins sai bakin ciki ya kasheni, amma Alhamdulillah a dropout zata kare, Abdul kuma ya yar da kwallon mangwaro ya huta" A fusace Momy tace "Ke Meemah tsayuwa cikin kangon bolan nan ne ke burge ki da baza kiyi abinda ya kawo mu mu fita ba, ko so kike Cholera ya kama mu? Ina ke ina cacar baki a irin wannan gida" Aunty Farida tayi wani murmushi tana kallon Meemah tace "Sai dai kuwa bakin cikin nan ya kashe ki don kina ji kina gani Khaleesat zata gama karatu a makarantar da kike fada, Allah ya ji ƙan ki in Advance" Cikin tsawa Meemah tace "Keee, ki iya bakin ki, kar ki gan ni tsaye a wannan bolan gidan a gabanki kiyi zata ni sa'ar yin ki ce, don wallahi inda na bi da kafata ma baki isa ki bi ba har duniya ta nade, ni ba sa'ar ki bace ta ko wani angle, banda Abdul yayi downgrading dinmu ya kaskantar da darajan da Allah yayi mana ina mu ina hada hanya da matsiyata talakawa irin ku balle har aje ga auratayya? Ke ki duba irin wajen da ku ke rayuwa wanda ko karen gidanmu baza mu bari yayi rayuwa a cikin wannan hali ba, To wallahi ki iya bakin ki ni ba sa'ar yin ki bace, ba karamin aikina bane in sa a shafe babin ki a duniya" Tun kan Aunty Farida ta mayar ma da Meemah amsa Umma ta hanata, cikin fushi Aunty Farida tace "Kamar yaya in yi shiru Umma, gidanmu fa suka zo suka same mu kuma ki ce inyi shiru? ashe ma karyar arziki suke in don saboda miliyan goma za su yi wannan uban zugan kamar masu bibiyan miliyan 50 har su tsaya suna kumfar baki suna tada jijiyoyin wuya akan 10M, uban wani ya saka ya tura mata kudin a account dinta da har za su zo nan suna gaya ma mutane maganar banza, ko kuma rokonsa tayi ya saka mata kudin, su arzikin ma wallahi da gani taka haye suka yi, da can su ma matsiyata ne" Meemah ta mika ma Momy handbag dinta tana huci zata cakumo Aunty Farida, Momy ta dakatar da ita tace "Ke me ya kai ki, ki taɓa ta ki ce kin taɓa wa? Salon ta goga maki ƙashin tsiyarsu kike kokarin dambe da ita? Yanzu wannan har Class din damben ki ce in ba rashin wayo irin naki ba Meemah? Ai ba a dambe da talaka matsiyaci" Umma ta kalli Khaleesat tace "Ta yaya za ki fiddo kudaden a account din ki Khaleesat?" Khaleesat ta sauke idonta tace "Sai naje banki, bani da Atm card, kuma kudin bazai fita lokaci daya ba...." Momy na mata matsiyacin kallo tace "Sai ki tashi ki tafi bankin ai don wallahi kudaden nan baza su kwana a account din ki ba yau, da niyyar ki kin ci bulus tunda ubanki ne ya nema masa kudin ba" Khaleesat ta daga kai ta kalleta, ita har sannan ta kasa daina mamakin matar nan, kai tunda aka haifeta ma ita ba a taɓa shayar da ita ruwan mamaki yanda mahaifiyar Abdul ta shayar da ita ba, yau sati daya da sakin da Abdul yayi mata amma kullum in ta tashi sai ta zauna tayi mamakin uwarsa ganin abun take kamar Drama, ba ayi ranan da zai zo ya wuce da Momy bazata fado mata ba, bata taɓa san akwai mutane irin Momy a rayuwar nan ba, muryar Mama Zubaida taji tace "Ai ba zama zaki yi kina zazzare ido ba kamar barauniya, tashi za ki yi ki kama hanya ki tafi banki ki fiddo masu da kudadensu tunda ba gadon Abdul din gare ki ba kuma ba kudin tsohon ki bane, duk wani abu na rashin gaskiya dake da uwarki da kanwarta gaba ku ka basa ba baya ba, banda haka ta yaya za kuyi shiru da makuden kudadensa har Miliyan goma a account dinki? So ku ka yi ku danne kudin ko yaya? Don ma kun samu masu hakuri da kawaici da wasu ne idan ba a zo da motar yan sanda an tafi da ku ba ku ce bani ba, wannan ai rashin gaskiya ne da rashin tsoron Allah kiri kiri, duk kun yi mukus da bakin ku za ku cinye miliyan goma ga banza ta samu" Aunty Farida ta juya tana kallon Mama Zubaida, sai kuma ta nufeta tana cewa "Zubaida idan ban zubar maki da hakora a gidan nan yau ba ki ce bani ba, don kaza kazan ki akwai tsinannen da ya sako bakin ki? Uwarki muka yi ma rashin gaskiya ko ubanki?" Mama Zubaida tayi wani shewa tana tafe hannu tace "To yau kika saba Farida? Ai ke fitsararriya ce dama mara mutunci mara kunya shi yasa ga ki har yau duk kyan ki kin rasa mashinshini sai dai kiyi tuwo tuwo a garin legas kina hadawa da karuwanci, waye bai san wannan ba?" Aunty Farida zata cakumo Mama Zubaida Mama Shatu ta shige tsakaninsu tace "Ke yanxu Farida Zubaida sa'arki ce zaki dinga zaginta haka ta uwa ta uba don kawai tana kishiyar yayarki? Daga dai ta fadi gaskiya banda ɗan Adam baya son gaskiya?" Aunty Farida tayi wani wurgi da Mama Shatu sai ga ta a kasa timmm, tuni Mama Zubaida ta shige dakinta ta kulle kofarta da sakata tana cewa "Haka kawai ki shafa min bakin jini irin na ku? Allah ya sauwake in yi dambe dake Farida, ku je can ku ji da rashin sa'ar ku a rayuwa, ku kenan daga wannan iftila'in sai wannan bala'in, ko wani fitinar duniya a kan ku ya kare, daga wannan sai wannan, Allah kadai yasan laifin da ku ka tafka a kasar ku, kilan ma ta zina aka sami ke da yayar taki, ga bakin jini da rashin sa'ar ku ya shafi Malam ya talauce" Da kafa Aunty Farida ta hambare uban miyan da Mama Zubaida ke yi na abincin siyarwanta, miyar duk suka malale kasa, shinkafar ma dake cikin kwando ta kifar da shi a kasa tana zagin Mama Zubaida ta uwa ta uba, Mama Shatu ganin yanda aka yi watsi da kayan sana'an Mama Zubaida ya sa ta ja bakinta tayi shiru ta tafi gun nata miyan ta zauna tana cewa "Hakuri kawai za kiyi Farida, hakan ba dadi kam" Momy ta rike haɓa tace "Alhamdulillahi da na yi iya bakin kokarina na ganin ban hada iri da gayyar tsiya ba, ku kuga wannan tsiya haka kamar 'yar tasha, ga talauci ga tashanci, Abdul ya so ja mana abun fade a dangi Allah ya takaita min abun, kuma ba dai kun ce kudade na banki ba, to zuwa yau da daddare in ga alert din Miliyan goma, in kuwa ba haka ba gobe da sassafe za ku gan ni a gidan nan ba kuma zuwan lumana zan yi ba, ai shi ramin karya kurarre ne, kuma ko kwabo daya yayi ciwon kai a kudaden nan wallahi sai an daure er ku..." Momy na kai wa nan ta bude handbag dinta ta ciro takarda dauke da account details dinta ta jefa ma Khaleesat sannan ja tawagarta suka yi waje tana cewa "Haka kawai Meemah zata ja min bala'i ta hada ƙashi da wannan iri na fitina, irin tsiya, to kiyi dambe da ita ki ce kin yi dambe da wa? Kina ganin yarinya kamar mahaukaciya, A'a wallahi Allah ya maki tsari" A haka duk suka fita daga compound din, Khaleesat taji hawaye ya cika idonta, Umma komawa dakinta tayi tayi tagumi ranta ba dadi, ita kam ta gode Allah da jarabawa iri iri, daga wannan sai wannan, Khaleesat ta dau takardan da Momy ta jefa mata ta juya ta shiga dakin Umma hawaye na zuba idonta, Aunty Farida kuwa bata fasa zage su Mama Zubaida da Mama Shatu a tsakar gida ba, Mama Zubaida taki fitowa kuma taki tanka Aunty Farida, Mama Shatu kuwa tayi tsit kamar bata san da wa Aunty Farida take ba, daga karshe bayan Aunty Farida tayi masu wankin babban bargo ta shige dakin Umma tana huci, Umma ta daga kai tana kallonta tace "Yanxu ban isa ince ki bari ki bari ba Farida?" Aunty Farida ko tanka Umma bata yi ba ta dau Hijab dinta ta saka tana kallon Khaleesat tace "Ki tashi ki shirya mu tafi bankin" Mikewa Khaleesat tayi tana goge idonta ta dau hijab dinta ta saka, a haka suka kama hanyar banki da Aunty Farida, amma suna isa bankin suka tarar an tashi aiki sai ran Monday don karfe hudu har da rabi a lokacin, Aunty Farida na kallon Khaleesat bayan sun fito bankin tace "Goben karfe nawa ne tafiyar naku?" A hankali Khaleesat tace "Flight din karfe daya zuwa Abuja, daga Abuja kuma jirgin yamma ne" Aunty Farida tace "Kuma bazai yiwu a daga tafiyar ba Khaleesat? Kinga banki dole fa sai Monday idan Allah ya kai mu" Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, ita kanta she is just confuse bata san yanda zata yi ba. A haka suka koma gida kusan karfe biyar da rabi, Umma na kallonsu tace "An tashi a banki ko?" Aunty Farida bata ce komai ba ta cire hijab dinta ta nemi waje ta zauna, Khaleesat ta zauna tana kallon Umma tace "Banki sai ranan litinin, sun tashi yau" Umma tayi shiru bata ce komai ba, can tace "Kema kin san bai amshi kudinsa ba me yasa zaki yi shiru har na sati daya Khaleesat? Yanxu da kinyi magana tun yaushe za a san yanda za ayi a cire kudin a mayar masa kayansa, yanxu rashin mutuncin da suka zo suka mana makota na ji ina amfanin sa?" Aunty Farida tace "A'a ta min maganan kudin fa ranan Alhamis, a lkcn ma tayi zaton yau ne tafiyar ashe gobe ne, kuma kema kinsan Khaleesat bazata taɓa ko biyar a kudin nan ba tunda ba nata bane, kawai dai dama matsiyata ne yan iska daga Abdul din har iyayensa" A hankali Khaleesat tace "In ma an cire kudin an basu bazan iya tafiya babu kudi a account din ba, don baza a bari in shiga kasar ba, they wilk see i am not financially capable idan babu kudi a account dina, shi yasa ma ya bar kudin a account din all this years" Aunty Farida tayi shiru don bata ma san me zata ce ba, haka ma Umma da ta rafka tagumi tun shigowarsu, after a while a hankali Umma tace "Ni tsorona kar su dawo goben da suka ce bamu san kuma da me za su zo mana ba" Aunty Farida ta mike tace "Sai su zo su amshi babu tunda su yan iska ne" Daga haka ta fice daga dakin, Khaleesat taji hawaye ya cika idonta, Umma na kallonta a hankali tace "Kiyi hakuri Jiddah, wataran duk hakan zai zama labari, Allah ya bamu ikon cin jarabawan mu, in ma kin koma makarantar in ma baki koma ba duk yanda Allah yayi dai dai ne" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata ta mike ta dau tsintsiya zata yi gyaran dakin Umma tana goge hawayen dake sauka idonta.... [7/2, 6:55 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Khaleesat har ta fara bacci wajen karfe goma da rabi Aunty Farida ta tasheta tana mika mata sabuwar wayarta dake vibrate, mikewa tayi zaune tana gyara hulan kanta ta amshi wayar taga Safiyyah ce ke kiranta, ɗagawa tayi ta kai kunne, daga daya bangaren Safiyyah tace "Ko har kin fara bacci ne" Khaleesat tace "Um, da wuri na kwanta ne" Safiyyah tace "Ayya sorry for waking you up, dama Housemate din ki ne yace in tambayeki wani account zai maki funding, cause nasan definitely Abdul ya amshi kudinsa dake account din ki ko?" Khaleesat tayi shiru ta kasa ce ma Safiyyah komai, har sai da Safiyyah tace "Hello" a hankali Khaleesat tace "Ina jin ki Sophie" Safiyyah tace "To naji kin yi shiru" Khaleesat ta daga kai ta kalli Aunty Farida dake kallonta, goge hawayen dake makale idonta tayi cikin sanyin murya tace "Daxu Mom dinsa suka zo za su amshi kudin, ni kuma bazan iya transfer ba kuma bani da Atm card, shi ne ta ajiye min account number wai in tura masu kudin yau, and today is Friday, mun je banki sun tashi, yanxu tace zata dawo gobe da safe idan ban tura mata kudin ba" Safiyyah dake ta sauraron Khaleesat cikin bacin rai tace "Allah ya sauwake, ke kiji wani tsiya don girman Allah, akan miliyan tara ne ko goma uwar ta kamo hanyar gidan ku da kanta? Can you imagine fa? A'a gaskiya sai yanxu nake sake tabbatar da su Abdul were once poor in this life, all of a sudden kawai Allah ya basu arziki sama ta ka, nobody can change this my perspective wallahi, banda tsiya meye kuma miliyan Goma a irin yanda suke show casing arzikinsu, what is 10M to them? wannan ai abun kunya ne a garesu, Ke kuma maimakon ki kirani tun daxu ki gaya min shi ne kika yi shiru? Yanxu ba don Housemate dinki yayi reason cewar dole sai da sufficient fund a account dinki za ki iya tafiya ba da shiru zaki yi kenan sai gobe da za mu tafi ki gaya min? Allah ya sauwake, ita kuma uwar Abdul wallahi matsiyaciya ce er wahala, har ta iya kamo hanyar Mariri akan kudin da ba ita ta bada ba, in kin bibiya ma ɗan nata bai sani ba ta kamo hanya, ki min sending shegen account din nata da ta bar maki" Daga haka Safiyyah ta kashe wayarta, Khaleesat ta jawo handbag dinta tana goge hawayen da ya taru idonta, ta bude jakar ta ciro takardan account details din da Mom din Abdul ta bar mata, tura ma Safiyyah account din tayi ta message sannan ta mayar da jakar ta ajiye ta koma ta kwanta, ita dai Aunty Farida bata ce komai ba don duk ta fahimci conversation din nasu. Washegari Khaleesat na idar da sallan asuba kiran Safiyyah ya shigo wayarta, tayi picking call din ta kai kunne, a hankali tace "Good morning Safiyyah" Safiyyah tace "How was ur night?" Khaleesat tace "Alhamdulillah" Safiyyah tace "Na tashi yanzu naga Housemate dinki ya tura min receipt din 10M da ya tura a account din da kika turo min jiya, he sent the receipt via my WhatsApp, ba ki yi activating WhatsApp dinki ba da sai in tura maki ki tura masu, sai su san su ne matsiyata" Kasa cewa komai Khaleesat tayi hawaye ya fara sauka idonta, Safiyyah tace "Ko kuma bari in tura ma Aunty Farida receipt din kawai since she is on WhatsApp" Khaleesat ta gyada mata kai da kyar tace "Nagode" Safiyyah tace "Kuka kike yi ko? Kina da aiki, ni dai sai anjima, make sure ki fito gida da wuri kin san Flight dinmu zuwa Abuja karfe daya ne" Daga haka Safiyyah ta katse wayar, Umma na kallon Khaleesat tace "Wai me ya faru?" Khaleesat na share hawayen da yaki tsaya mata tace "Ta ce ya tura masu kudin ne, zata tura ma Aunty Farida receipt" Shiru Umma tayi ta rasa abun cewa, kana ganinta kasan jikinta yayi sanyi sosai, Aunty Farida dake zaune kan darduma tace "Allah Ubangiji ya saka masa da alkhairi ya kare sa sharrin masu sharri, Allah ya mayar masa da dubban abinda ya kashe maki, yanda ya rufa maki asiri Allah ya rufa masa shi ma" a hankali Umma tace "Ameen ya Allah" Mikewa Khaleesat tayi don dama ta gama azkar din da take yi, ta kwanta kan gadon Umma har sannan hawaye yaki dena sauka idonta. Da safe wajen karfe tara Aunty Farida na bude WhatsApp dinta taga Receipt din da Safiyyah ta tura mata, tana kallon Khaleesat tace "Yanxu ta ya za a tura masu receipt din su gani Khaleesat?" Umma tace "Ba kina da number Abdul din ba? Ki tura masa ta WhatsApp din kawai" Khaleesat dake cin wainar da Umma ta sa aka siyo mata ta daga kai ta kalli Umma, sai kuma ta girgiza kai a hankali tace "A'a Umma kar a tura masa, ba sun ce za su zo da safe ba, in sun zo sai a nuna masu receipt din" Umma tace "Saboda me? Ba kudinsa bane kuma shi ya aiko su karbar masa?" Aunty Farida ta kalli Umma tace "Suka aiko kansu dai Umma, don Abdul dai a yanda yake ji da kansa bazai ce a zo a amsar masa miliyan goma ba, dama sun san da kudin kuma kilan sun san bazai ce zai amsa ba shi yasa suka taho su amsa" Khaleesat tace "Shi yasa nace kar a tura masa receipt din, don nasan ba shi yace su zo ba" Umma tace "To ko ma dai yaya ne ai kudinsa ne, ni bana son su sake dawo mana nan su mana tijara makota na ji shi yasa nace a tura masa kawai, idan yaso sai yayi ma uwar tasa magana tunda zai ga a account dinta aka tura kudin ai, tonan asirin bai ishe mu bane da har za mu sake yarda su dawo gidan nan" a hankali Khaleesat tace "Umma ni bana son abinda zai sake hadamu magana da shi balle har yace zai dawo da wata magana kuma" Aunty Farida tace "Ya dawo da wani magana? Saboda ba shi da hankali zai dawo da wata maganar? Ai yanxu ba mu da abinda zai sake hadamu da shi da ya wuce kudin nan nasa, saki uku ya aiko maki balle ace zai dawo da wata magana" Khaleesat ta sauke idonta kamar bazata ce komai ba sai kuma cikin sanyin murya tace "Aunty ba fa shi ya aiko da takardan sakin nan ba, ba rubutunsa bane, iya saki daya yayi min" Daga Aunty Farida har Umma kallonta suka dinga yi, a hankali tace "Shi yasa bana son a tura masa receipt din balle har hankalinsa ya dawo kan mu..." Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya bayan kusan minti daya tace "To Allah ya kyauta, yanxu su suka rubuto takardan suka aiko kenan? To su dai suka sani Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gare mu da ke baki daya, idan sun kwaso kafa sun sake dawowa sai a nuna masu receipt din" Umma dai bata ce komai ba don bata ma san me zata ce ba. Meemah na bacci Momy ta shigo dakinta wajen karfe goma na safe ta tasheta tana mika mata wayar hannunta, Meemah ta amshi wayar tana kallon screen din, sai kuma ta kalli Momy tace "Kudin suka sako?" Momy ta tabe baki tace "Gashi kuwa kina gani, nima yanxu naga alert din ashe tun daren jiya aka sako" Meemah tace "To a gidan uban wa ta samu ta turo bayan tace bata yin transfer kuma bata da Atm card" Momy tace "Ke baki ga sunan wanda ya turo kudin ba? Ai ba ita bace ta turo" Meemah ta kara kallon wayar da kyau taga sunan namiji, taɓe baki tayi tace "To wai ke Momy da nake ce maki iskancinta ta dinga yi da maza a Amurka kin zata wasa nake? Ai ba abun mamaki bane don kin ga ta samu wanda ya turo miliyan goman, harkar iskancinta kawai ta dinga yi a Amurka da 'ya yan masu kudi, kuma karya take babu miliyan goman nan a account dinta wallahi, to dai gashi nan daya daga farkanta ya turo kudin nan take" Momy tace "Oho dai koma wa ya turo kudin ta matse masu can, ni dai ba na amshi kudin ɗa na ba, da ban yi haka ba har a tashi duniya in dai Abdul ne wallahi bazai yi maganar kudin nan ba, kin ga da shikenan sun ci bulus, to ni da na haifesa ba asararriya bace da zan yarda ya bar masu makudan kudaden nan" Meemah tace "Wallahi Momy ni so nayi mu ce sai sun biya kudin sponsoring dinta da Abdul yayi, ke kinsan nawa Abdul ya kashe akan yarinyar nan kuwa? Wallahi idan na fara maki lissafi sai kin rike baki don mamaki, kudade ne ba na wasa ba da, duk kanta dukiyarsa ya dinga tafiya kamar kin masa baki, yaushe rabon kiji Abdul ya siya wani asset nasa ya ajiye? Tun da ya hadu da tsinanniyar yarinyar nan ya dena yi ma kansa komai sai dai yayi mata, ranan a gabana ya siya mata Abaya har biyu ko wanne dubu dari da hamsin, nayi masa magana ya nemi ya min rashin kunya cikin jama'a, handbag din nan shegiya sai Abdul ya siya mata na dubu kusan dari har fin haka, komai designer yake siya mata, suturu kam yayi mata ba iyaka, to wai ko monthly allowance da yake tura mata a kasar Amurka in kika ji sai hankalin ki ya tashi, uwa uba a zo kan kudin makarantar ta da House rent" Momy tayi mitsi mitsi da ido cikin bacin rai tace "Don Allah ki bar wannan maganar don raina baci yake Meemah, su je kawai Allah ya isa, ni da nake uwarsa ma sai ya ga dama yake siya min abu, to yanxu ko ce masu muka yi su biya a ina suka ga kudin biya Meemah? Ko gidan da suke ciki suka ce za su siyar wallahi karkari yayi dubu dari biyar, kai ni dubu dari biyar din ma bazan siya wannan kangon ba wallahi, kin ga kuwa gwara a bar zancen kawai, baki ji yanda raina ya baci ba wallahi, kawai Allah ya isa zan ta ja masu a kan uban kudin da Abdul ya kashe ma yarinyar kuma ba wai don bani da kudin maka su kotu ba...." Meemah tace "Ko kuma mu je duk mu kwaso kayan da ya dinga siya mata da jakunkuna masu tsada" Momy tace "Ki ci uwar me da su? Kema dai wallahi, shekara 38 ban san yaushe zaki yi hankali ba Meemah, Allah ya isan dai shi ne dai dai su, don babu abinda za mu ci da kayanta, tunda muka samu miliyan goman ma ai mun gode Allah" Meemah ta tabe baki ta koma ta kwanta tace "Kuma kin san wani abu Momy, da Abdul yana kasar nan har yanxu zai fa iya waiwayanta idan asirin ya sakesa, don wallahi masifaffen so yake ma shegiyar ke har yanxu baki gane ba, ji fa kafin su bar kasar yanda ko magana baya yi ma mutane a gidan nan, kullum zaka gansa babu walwala" Momy ta hade rai tace "Ni kuma ga er iska sai in sakankance har asiri ya sakesa ko? Ai da gangan na sa uban ya tafi da shi business trip din da za shi china, da biyu na takura uban su tafi tare don naga take takensa, ga sabon tijaran da na lura zai fara mana, kuma ko ba komai ai kinga za su dade a can kan su dawo, ni kuma kafin nan na sa anyi aiki sosai ya mance da wata shegiya wai ita Khaleesat a duniyar nan, sai kuma in tanadar masa mata er gidan mutunci, yana dawowa sai biki kawai" Meemah tace "Da dai yafi kam, yana dawowa yayi aure, ki sama masa yarinya dai dai class dinsa ba er talakawar da ya nace ma ba, ni wallahi ban zata talaucin iyayen yarinyar nan ya kai haka ba, har muka dawo gida na kasa cire view din gidan a idona, wannan ko karen gidanmu aka ajiye a gidan nan ai sai yayi rashin lafiya a bar mu da kashe makudan kudi zuwa veterinary balle ace mutum, to yanxu da bai rabu da ita ba haka wataran abu zai kama ki kwashi kawayenki da abokan business aje gidansu yarinyar? Misali ace ubanta ko uwarta wani ya mutu, haka za a kwasa aje masu gaisuwa wannan gidan?" Momy tace "Ai Abdul ya so ja min abun kunyan da bazai taɓa goguwa ba, ya so tona min asiri a idon duniya amma Allah ya rufa min asiri ya takaita abun, da irin rainin da Abdul zai ja min sai Allah wallahi, to ni dai tunda na samu aka rabu lafiya ai sai su bi wani sarkin kuma" Meemah tayi dariya tace "Kuma da bai saketa ba fa sai ya iya canza masu wani gidan don ba hankali garesa ba, tunda don yayi ta ma shegiyar yarinyar bauta Allah ya halitto sa" Wani shegen kallo Momy tayi mata sannan ta juya ta fita daga dakin. Khaleesat na durkushe gaban Umma dake mata addu'an Allah ya kai ta lafiya, ya bata sa'an karatun ta, ita dai Khaleesat kanta na kasa duk jikinta a sanyaye, a hankali Umma tace "Ki kula da kanki don Allah, duk da na yarda dake Jiddah amma ki kara taka tsantsan, kar ki mance tarbiyar da muka maki, kuma ki rike addu'a da azkar, Allah ya kare min ke ya tsare ki duk inda zaki shiga..." Nenne ce ta bude labulen dakin a fusace tace "Yau naga jaraba wajen Zahra'u, sai me motar yayi zuciya ya ja motarsa ya wuce ne ko yaya? Duk daren jiya da wayewar garin yau baki sakata gaba da duk wani zancen da zaki mata ba sai yanxu da motar da zai kai ta iyapot ya iso, haba Zahra'u ya ki ke haka ne? Ko dai maidata ciki za kiyi?" Aunty Farida ta wani kalle Nenne tace "To kyauta zai kai ta airport din da bazai jira ba, naga dai kudi zata basa Nenne" Nenne tace "Ai ba motar ubanta bane da zata shanya sa a rana don zata basa kudi, kuma shi ba boyi boyinta bane da zai ta tsayuwa yana jiranta a rana kamar ɗan iska, tunanin ku kenan 'yan Adam, don zaka ba mutum kudi sai aka ce ka walakantasa? Ka ki darajasa?" Aunty Farida taki tanka Nenne, Umma na kallon Khaleesat tace "Tashi ki je Jiddah, Allah ya tsare ya kai ku lafiya" A hankali Khaleesat tace "Ameen Umma" Daga haka ta mike ta dau handbag dinta don duk an fitar da akwatunan ta kofar gida, Nenne na kallon Umma tace "In ji dai duk an saka mata doya da dankalin da na kawo mata a akwatin nata?" Da sauri Aunty Farida tace "An saka komai" Nenne tace "Wake da su albasa da garin masara da na alkama fa?" Aunty Farida tace "Har su an sa" Nenne tace "To mu je" Khaleesat ta bi bayan Nenne suka fita daga dakin, Aunty Farida ta kara tura doya da dankalin da Nenne ta kawo da su garin alkama da Masara a bayan kyaure ta boye yanda Nenne bazata gani ba ko ta dawo dakin, daga nan ta bi bayan su, kasa daurewa Umma tayi ta mike ita ma ta fita, su Mama Zubaida da Mama Shatu na tsaye tsakar gida duk suka bi Khaleesat da kallo, Kana ganin fuskokinsu kasan babu farin cikin komawa Amurka da Khaleesat zata yi, Yaron Mama Zubaida ya nufo Khaleesat da gudu yana mika mata kudin hannunsa yace "Wai gashi inji Ummanmu da Mama Shatu ki sha ruwa a hanya" Nenne ta karbe kudin a hannun yaron ta kirga taga dubu biyu ne, sokesa tayi jikin haɓar zaninta tace "Ta gode" Daga haka ta kalli Khaleesat tace "Mu je" Khaleesat tayi ma kishiyoyin ummanta sallama sannan ta bi bayan Nenne suka fita daga gidan Aunty Farida na biye da su, a kofar gidan Khaleesat ta kara sallama da Babanta don bai fita kasuwa ba ranan yana jiran tafiyarta, kasa hada ido tayi da shi yana mata addu'a da fatan alkhairi, Nenne ta bude mata bayan motar tace "Ni dai shiga don Allah, tun jiya basu san da addu'an su ba sai yau da kike sauri salon jirgi ya tafi ya bar ki" Khaleesat ta shiga motar Nenne ta kulle, haka kawai Khaleesat taji hawaye ya cika idonta, ta daga masu hannu kawai sannan drivern ya ja motar suka bar kofar gidan. Ko da Khaleesat ta isa airport ta tarar Safiyyah na ta jiranta don tun daxu ta iso airport din, Khaleesat ta amshi boarding pass dinta suka nufi Departure Lounge, bayan minti ashirin jirginsu ya tashi zuwa garin Abuja, inda a nan za su hau jirgin da zai kai su kasar America.

Chapter notes and social links

Readers Also Read