Kenza eBookz

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 2

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 2

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 2: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 2. Lokaci ya tafi sosai kauna da shaquwa me tsafta…

4,500 words

Lokaci ya tafi sosai kauna da shaquwa me tsafta ce a tsakanin dukkanin GHAZ da Asamah wadda kulawa da gabaki daya yaran gidan ta dawo hannunta duk da sun zama yan mata amma itace ke kulawa da komai nasu musamman Abaas Wanda yayi wata irin shaquwa da ita,

Duk tsawon shekarun datai a cikinsu burinta Akan kubuto da mijinta bai taba fita a ranta ba duk da lokuta da dama tana Jin kaman ta hakura da hakan sbd tsoron illar da kusra zasu iya shigowa gari suyi Wanda a yanzu cikin garin ANJOM iyalan GHAZ ne kadai take dasu sbd tausayinta daya zamo kauna me karfi a gareta.

A yanzu da shekaru suka ja kusra hakurinsu ya fara qare wa dan haka ahankali suka fara farautar duk Wanda zai fito daga garin dama hanyar makusanta hanyar dajin garin ta yanda gabaki daya nahiyar ta zama ta gagari kowane dan Adam bi a tahiri sbd duk Wanda ko hanya ta biyo dashi ta nahiyar ko gawarsa baa samu dan haka duniya da dukkanin nahiyar tarihi bin nahiyar ya zama tamkar tarihi sbd gabaki daya zagaye suke da dajin ANJOM Wanda ya koma babu shiga dajin babu fita dan haka rayuwar ANJOM ta fara shiga wani irin halin tsanani da rashin kwanciyan hankali da fargaban ko Yaushe komai ze iya faruwa garesu.

Tin masifar na waje dajin nasu harta fara shigowa sbd kisan yayi yawan da a bakin gari suke samun gawarwakin mutanensu.

Wannan tashin hankalin ne ya saka GHAZ fara tinanin iyalinsa da bazai iya barin wannan masifar dake kokarin afkowa ANJOM ta shafesu dan haka yasa aka fara Ramin fita garin ANJOM ta baya ta inda yake saka ran babu kusrawan zuwa ruwan dazai iya kaika nahiyoyi da dama dan tsira.

************ Zaune suke a wata irin lafiyayyan rumfar hutawarsu kowannensu na Zaune gurin cike da yayan marmari masu kyau sai qatuwar kwaryar dabino da shima yake da daukan ido.

Ayanah ce kadai bata gurin sbd shirinta dayake daukan lokaci dan haka tana fito wa tareda baiwarta daya Sakeena dake biye da ita.

Rumfar ta tinkaro a natse cikin takun dayake bayyanarda tsananin nutsuwarta da mulki yake ciki,

Qarar sarkar hannunta data kafarta me fidda dan sautin daukan hankali ce ta saka Asamah dake sake jere Kayan marmari fara dagowa ahankali ta sauke idanwanta Akan hanyar tana zubawa halittar Ayanah dake daukan idanuwa duk Wanda zai kalleta ido Tana ambatar Masha Allah Masha Allah cikin zuciyar.

Abaas ne ya juya ahankali shima yana kallan Ayanah din yana zubawa kyakkyawan fuskanta ido yana Godiyan Allah ako Yaushe da Ayanah ta kasance jininsa wadda yakejin kaman jinin da suka hada bai ishesa ba yana tsananin son ace ya sake hada wani abu da ita Wanda zaisa ace yafi duka Sauran yan uwansu kusanci da hada jini ita.

Ganin idanuwansa akanta kaman koyaushe yana kallanta cike da kauna me tsanani ta jini bude bakinta tayi wani kyakkawan murmushi ya mamaye fuskanta har saida hakoranta suka dan bayyana ta qaraso gurin tana miqa masa hannunta dayake sanye da fararen azurfa masu kyau da rashin sirki.

Kama hannunta Abaas din yayi cikin kulawa yana sake nasa murmushin me kyau daya qawata tasa fuskar dasuke tsananin Kama dan shi Kansa kyakkyawa ne da ake fadarsa a garin ANJOM Wanda lokuta da dama iyayensa ke tinanin bakin mutane ne ya saka ya kasance me rauni. #MAMUH #ANJOM GHAZ #AYANAH GHAZ #ABAAS GHAZ #BOYEM #BEST ROYALTY/BEST LOVE/BEST ROMANCE

HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070

*_HAYATEEM_* Mamuhgee 09033181070

4 Zaunawa Ayanah tayi gefen dan uwanta tana kallansa Fuska cike da murmushi da sakewa tace

‘Godia nake GHAZ Abaas’

Dariya yayi yana sake hannunta yana cewa

‘Ayanaah….

Katsesa Zuhrah tayi batareda ta Bari ya fara fadar maganarsa da ako Yaushe take ta yanda yake Jin bazai iya rayuwa ba Ayanah bane wadda koyaushe damuwansa wani lokacin ta yanda zatai sure wata ran ta tafi tabarsu.

Dariya dukkaninsu sukai ganin yanda ya juya ya harari zuhrah cikeda kauna itama sbd yanda ta katsesa da cewan sun gaji da maganarsa daya kullum.

Fararen idanuwan Ayanah ta juyo ta sauke Akan fuskan mahaifiyarsu dake Zaune Nurat na kwance jikinta ta bude baki tace

‘Amma Barka da hutawa,kin tashi Lfy?’

Hannu Amman ta miqa ta Shafa fuskan Ayanah din tana Jin tsananin son yarta tace

‘Barka Ayanah ghaz,kin tashi Lfy kema’

Murmushi tayi tana dan Dora tafin hannunta Akan hannun Amman dake kan Fuskanta tana Jin kaman ta hadiye tace

‘Lafiya kalau Amma’

Juya wa tayi tana kallan zuhrah tace

‘Ki Dena damar mun da GHAZ Abaas sbd baya buqatan gorinki tareda dashi zan tafi duk inda zani kokuma na zabi zama a cikin ahalina har karshen rayuwata’

Nurat Baro jikin Amma tayi ta dawo gefen Ayanah ta lafe jikinta tana Jin kaman ma hakan ya kasance a rayuwar su kada suyi aure su rabu su tabbata a tare har abada Bude baki tayi tana kallan Ayanah data kalleta cikin sanyi tace

‘Ayanah inason na tabbata tareda ku duka mu tsufa mu mutu tare banason ko aure ya rabamu, Zan cewa Abaa(mahaifinsu) koda zamuyi aure abarmu da mazajenmu muyi rayuwa a cikin GHAZ batareda munje kowane gida aure ba’

Wani iri Ayanah taji a zuciyarta na Ina ma hakan zata kasance datafi kowa farin ciki sbd yan uwanta sune rayuwarta amma kuma kaman hakan bazai yiyu ba,

Numfashi ta sauke tareda Kai bakinta cikin kauna ta sumbaci tsakiyar kan Nurat din tana Shafa gefen fuskanta tace

‘Nurat babu abinda zai raba mu a duniyar nan Bayan mutuwa sbd kune rayuwata’

Amma datake Jin kaman kada ta taba aurar ‘yayan nata sbd ganin baza su iya kowace rayuwa batareda junansu ba wani irin sanyi jikinta yayi ta Kama hannun Ayanah takai bakinta ta sumbata tana kallanta tace

‘Kece rayuwansu suma musamman a lokacinda zaku samu Kanku ba iyaye idan tsufa ko mutuwa tazo dan haka Ayanah kici gaba da zama uwa kaman yanda kike kaman mahaifiyarsu a yanzu’

Qurawa Amman idanuwa Ayanah tai tana Jin zuciyarta na sake cika da tsananin kaunar mahaifiyata,

Gyada Kai tayi tana kwantawa jikin Amman batareda ta iya cewa komaiba.

Abaas ne dayake Jin a jikinsa shikam da Ayanah baza su taba rabewa ba koda basa a raye sai yana Jin kaman baza su rabu ba dan kuwa tsananin so da kaunar dayake wa Ayanah da aure ya Halasta a tsakanin yan uwa to da bazai taba barin kowa ya dauke masa Yar uwa ba zata zauna a karkashinsa koda ba aure zai killaceta ya Hana kowa koda ganinta sbd kada kowane ido yayi mata illa,

Duk da ba aure tsakaninsu yanada Alkawari da fatar duka yayan dazai haifa a rayuwarsa su hada jini Ayanarsa, idan kuma mace Allah zai basa to adduarsa koyaushe a cikin ibadarsa shine ta kasance tamkar Ayanarsa koda hakan shine burinsa na karshe yana fatar Allah ya cika masa shi koda a ranar mutuwarsa ce.

Asamah da dukkanin jikinta yayi tsananin sanyi da kaunar ahalin GHAZ din da baka gane wane yafi wani kaunar dan uwansa Jin takeyi Inama nata ahalin sunanan da yayanta zasu yi girman su zuhrah da Abaas sbd itama ‘yaya mata biyu ne da ita sai namiji daya kaman Abaas,

Hawayene masu tsananin zafi da radadi suka ciko idanuwanta ‘dacin rashinsu na taso mata Wanda daman a tsawon shekarun nan bata taba manta radadin ba koda na qanqanin lokaci ba,

Hadiye hawayenta tayi sbd kada su bayyana a gabansu.

Juya wa tayi Bayan ta gama jere komai ta kalli kakkaifar qaramar wuqar dake kan Kayan da zata bar gurin dasu ta yanka Kayan marmarin taga yanda take daukan ido,

Zuciyarta ce tahau Kai kawo cikin tsananin qunci da baqin cikin daya taso mata na rashin yayanta da tsananin buqatar son dawowan mijinta gareta Wanda zuwa yanzu tasan azaba ta dade da sauyasa zuwa wata mummunan halittar amma tanason abinda a hakan.

Shedan da zuciyarta dake rufewa idan abin ya taso mata Wanda yake tamkar tabin kwakwalwa batareda sanin kowaba suka saka zuciyarta rufewa tafara taku daya na biyun ta saki gabaki daya Kayan hannunta a jikin Abaas Wanda wuqar ta yanki gefen qafarsa take jini ya fara fito wa Wanda ya saka dukkaninsu miqewa cikin tsananin tashin hankali da damuwa

Asamah ma cikin tashin hankalin da tsoro me tsanani ta zube gabansa tareda rigan kowa saka hannunta a kafarsa tana wani irin rawar jiki da kukan dayake fito wa daga qasan ranta tana basa hakuri cikin kulawa sbd a qasan ranta tasan kofar wata rayuwar ce zata bude wa duk Wanda yake garin ANJOM wadda bata San wace iri bace dan kuwa a gefen rigar jikinta ta goga jinin me yawa daga qafar Abaas batareda lurar kowa ba.

Cikin sauri sakon fitar jini a jikin GHAZ Abaas ya isarwa Abaa dinsu wanda ba bata lokaci ya iso gurin Wanda ya saka duk Sauran bayin dake zagaye da gurin na kowannensu dake rumfar ja baya sosai cikin girmamawa.

Wuqar da jininsa ya taba ya fara bada umarnin a karba hakama take aka kawo ruwa masu yawa a babbar tasa me kyau aka saka Asamah wanke duka hannuwanta da jinin Abaas ya taba kafin take GHAZ Ali din da Kansa yasa aka kawo magani ya karba yana kallan Abaas din Wanda hankalinsa yake son tashi sbd fitar jininsu tamkar hadari ne ga dukkanin ANJOM gabaki daya sbd da jininsu ne kadai ake iya karya komai dake ANJOM dan haka Sam baa taba yadda da kowa ba game da duk wani digon jinin GHAZ. Amma ganin Asamah ce ta raunanasa bada ganganba kuma tamkar ahali take sai hakan na hana zuciyarsa shiga tashin hankali da tsoro sosai.

Kukan da Asamah ke yi ya saka Ayanah rarrashinta tareda Zuhrah

Nurat da Amma kuwa suna jikin Abaas din cikeda damuwa suna kallan yanda GHAZ ya saka masa garin maganin da take jininsa ya tsaya ya Dena zuba.

Ajiyan zuciya GHAZ ya sauke yana dagowa ya kalli Abaas din cikeda kulawa da qara tabbatar masa da tsananin mahimmancin jinin dayake yawo a jikinsu.

Cikin nutsuwar mulkin dayake yawo jikinsa da kulawa tareda tabbatarda kiyayewa GHAZ ya bude baki yace

‘GHAZ Abaas ya koma dakinsa a tabbatarda an kiyaye danyen yankan kafarsa ta warke da kyau batareda ya sake fitowa ba’

Gyada Kai kowa yayi suna amsa wa da cewa

‘Angama’

Juya wa yayi ya bar gurin kowa yayi tsit cikeda damuwa da alhini har saida ya fice kwata kwata kafin Abaas din ya dago ya kalli Asamah kaman zai yi magana sai bai ce komaiba ya maida idanuwansa Akan Ammansa dake miqewa tabar gurin tana bin Bayan GHAZ Ayanah kuma hannu ta miqa masa ya Kama ya miqe suka nufi hanyar dakinsa tana cewa

‘Yankan qaramar wuqar cin tufa bazata girgiza jarumin anjom ba GHAZ din anjom me zuwa’

Yar dariya yayi yana kallan kafar tasa tareda cewa

‘Shekarun nawa basu Kai ba ai tukuna amma insha Allah idan nakai shekaru ashirin a duniya zan fara fita a matsayin jarumin na anjom wata ran harma na zama Garkuwa ga dukkaninku’

Har cikin ranta taji dadin abinda ya fada tana fatan hakan koda kuwa a mafarki ne.

Rakasa tayi dakinsa Wanda acan suka zauna ta tayasa fira sai ga su Zuhrah da Nurat sun taho suma sbd sunsan saiya kwana biyu kafin ya fito koina sbd tsaro da dokar GHAZ din tin asali duk Wanda yake jinin GHAZ yaji rauni har jininsa ya fita to saiya kwana biyu a killace batareda fito wa koina ba sai Raunin ya qame,

Hakan ne ya saka yan uwansa zuwa dan tayasa fira da debe kewa,

Kayan ciye ciye da dafaffiyar madarar raqumi me dumi aka kawo aka ajiya musu sunata firarsu da hutawarsu cikin kwanciyan hankali da nishadin farin cikin kansacewa da juna,

Anan suka wuni dan hatta ibadarsu anan sukayita,

Da yamma ma mahaifinsu shigowa yayi cikinsu cikeda Shakuwa da kaunar juna suka cigaba da farin cikinsu anan cikinsu yayi sallah tareda iyalansa har cikin dare tukuna dukkaninsu suka watse kowa ya nufi makwancinsa.

Ayanah na isa dakinta zare Kayan jikinta tayi ahankali tana rufe jikinta duka ruf da wata kakkaurar doguwar rigar wanka me Kama da alkyabba amma ita ta yadin saka me kyau.

Baiwarta Sakina ce take biye da ita dauke da wutar haskawa.

Gurin wankansu ta Nufa Wanda yake cike da ruwa masu tsafta da kullum ake sauyawa ta zare rigar tana zaunawa gaban ruwan tafara wanka a natse.

Sakina ajiye mata hasken tayi ta koma kofa ta tsaya daga waje tana jiran fitowarta.

Gama wankan tayi ta fito tana qamshin madarar flower me dadi.

Dakinta ta shiga ta zauna Sakina tana tayata goge jikknta harta gama ta shirya ta nufi lafiyayyan gadonta na sarauta ta haye.

Washe gari ma haka suka wuni gurin Abaas tareda iyayensu Wanda kwata kwata GHAZ ayau din bai fita koina ba yana cikin yayansa tausayin Abaas haka kawai yake shige masa zuciya sbd ganin kaman zuciyarsa tayi sanyin da bazai iya mulki ba idan ma yayi wahala zaisha sosai,

Akan ‘yayansa mata ya maida idanuwansa yana kallan yanda suke dariya suna Wasagu da juna sautin dariyarsu na shiga kunnuwansa zuciyarsa na na cikewa da tsananin kaunarsu yanajin kaman ya maidasu cikin Mahaifiyarsu sbd basu tsaro da kariya daga dukkanin wata cutar duniya da wahala.

Akan Ayanah ya tsayar da idanuwansa dariyarta na a bayyanarda asalin zallan Kyan da Allah yayi mata Wanda yasa Sam baa barinta fita daga GHAZ din itama, Ayanah nada zuciya me sanyi da hakuri tareda juriya tareda jajircewa Akan ‘yan uwanta Wanda yasa yakejin kannenta sun dace dan kuwa tamkar uwarsu haka take kulawa dasu,

Akan Zuhrah ya maida idanuwansa yana kallan gashinta dayake sake zube a bayanta Wanda babu namijin da zai kalleta bata fizgi hankalinsa ba dan haka yake killace dukkanin wata al’aurarsu sam baya barin ko yatsar hannuwansu wani na waje na gani sbd a sujjarsa gabaki daya adduar ‘yayansa ne.

Ahankali jikinsa na mutuwa ya daga hannunsa ya miqa akan Zuhrah ya fara tattare gashinta cikin kulawa ya daure mata yana janye mayafinta me ado dayake gefenta ajiye ya rufe gashin nata. #MAMUH #GHAZ #KUSRAH #BOYEM #ROYALTY #BEST LOVE

HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070

Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali

*_HAYATEEM_* Mamuhgee 09033181070

5 Dago Kai Zuhrah tayi ta kalli Abaa din tana Dora hannunta akanta ta taba mayafin daya rufe kanta dashi tana zubawa mahaifinta ido ta bude baki zatai magana ya Dora hannunsa daya akan bakinta ya girgiza mata Kai ya bude baki yace

‘Kanki ya kasance koda Yaushe a rufe Zuhrah ghaz’

Gyada kanta tayi batareda ta dauke idanuwanta daga Kansa ba sbd ganin wani irin kallan tsananin kaunar dayake mata.

Tsakiyar kanta ya sumbata yace

‘Albarkar Allah ta tabbata a rayuwanki Zuhrah koda yan uwanki duka’

‘Amin Abaa’ ta fada tana matsowa sosai jikinsa ta zauna.

Nurat ya maida idanuwansa ya kalla wadda take jikinta yayi sanyi sbd itace tafi kowa saurin kamuwa da yanayin da duk ya sauya,

Ta fisu saurin hawaye da zama emotional sbd tanada qawazuci sosai na iyayensu dan haka hannunsa ya miqa mata ta taso daga gefen Abaas ta dawo gefensa ta kallesa idanuwanta na raurau haka kawai.

Wani murmushi me sanyi da kyau ya dake yana Shafa fuskanta ya girgiza mata Kai yace

‘Jarumar ‘yata Nurat bata barin jikinta yayi sanyi a kowane yanayi’

Murmushi ta sake tana Kama hannunsa qamqam tace

‘Abaa ina fatan na kasance hakan daka fada koba yanzu ba’

‘Insha Allah Nurat zaki zama jajirtacciya dakakkiya bazaki taba gazawaba insha Allah’

Maganarsa ta saka Ammansu kallansa tana dan murmushi batareda tace komaiba.

Qarasa fitar da wunin sukai cikin tsananin kaunar dasuke Jin tafi ta koyaushe musamman da mahaifinsu yaketa yabonsu yana kasa dauke kallansa akansu cikeda kauna hakama Amma Jin takeyi tana sake kaunar mijinta sbd yanda ya tarbiyantar da ita da yayansu.

Da daddare Bayan sunyi sallah ishai Abinci da Kayan marmari aka kawo aka Jere musu tareda fitilun wutar ishen flower masu sanyin kamshi da aka kewaye gurin dasu suna basu haske tareda kamshi.

Dagowa GHAZ yayi ya kalli sakina baiwar Ayanah dake gefensa ya bude baki yace

‘Ina Asamah gabaki daya yau ban ganta ba’

Sunkuyar da Kai sakina tayi cikin girmamawa ta bude baki tace

‘Tin jiya bata fito ba babu Wanda ya ganta a yau sbd damuwan abinda ya faru da GHAZ Abaas’

Kallan Amma GHAZ yayi yana Neman qarin bayanin hakan

Kallansa tayi itama cikin kwantar masa da hankali tace

‘Tashiga damuwa sosai ne har dare jiya tana gurina tana kukan Neman Gafara da Afuwan abinda ya faru dan hakanne yau Kowa ya kyaleta ta dawo daidai’

Shiru yayi sbd bayason nuna damuwa ko fada a cikin iyalansa dan haka baice komaiba sbd duk tsawon shekarun nan bai taba dauke saka Idonsa da saka taka tsantsan sosai akan Asamah ba dan haka tin jiyan da jinin Abaas ya fita yake Jin rashin nutsuwa amma baya iya nunawa sbd yanzu suna cikin wani hali ne na kusrawa dake Neman kawo musu hari kowane lokaci suka samu damar hakan.

Abinci suka ci suna fira da nishadinsu har suka gama nanma suka ci gaba da firarsu har dare sosai kafin Abaa da Kansa ya raka kowacensu dakinta da Kansa kafin ya dawo ya tafi da Amma dakinsu itama tukuna ya fito ya dawo dakin Abaas sosai kafin ya fito ya shige shima.

Tsakiyar dare sosai Nurat dake kwance taba bacci cikin kwanciyan hankali da nutsuwa ta farka da karfi cikin mummunan faduwan gaba sbd mummunan mafarkin datai.

Bude idanuwanta tayi ahankali tana sauke ajiyan zuciya a sanyaye kafin ta tashi Zaune tana Jin rashin nutsuwa,

Shiru tayi tana Dora hannunta kan kirjinta dake bugawa sosai cikin rashin Jin dadi,

Koma wa tayi ahankali tana kokarin kwanciya taji motsi me karfi daga waje dan haka gabanta ya sake faduwa ta zuro kafafunta qasa da sauri tana saukowa gadon tareda daukan mayafi tana Daurawa akanta ta nufo kofa tana bude kofar ta fito Kai tsaye batareda tsoron duhun Daren ba.

Takawa tayi Kai tsaye ta nufi dakin Ayanah sedai kafin ta isa dakin wani irin jan haske taga yana gauraye saman garin na alamar wuta.

Saman ta ringa kalla tana nufar dakin sai kuma hayaniyar tashin qara daga nesa Wanda ya sakata qarasawa dakin da sauri tanajin tsoro na shigarta.

Tura dakin tayi ta shiga da sauri ta qarasa gadon Ayanah ta haye gadon tana shigewa jikinta ta qanqameta.

Cikin bacci Ayanah taji Nurat cikin jikinta wadda tasan itace Kai tsaye sbd itace Kai tsaye take zuwa lokuta da dama cikin dare gurinta idan ta kasa bacci.

Numfashi da ajiyan zuciya Ayanah ta sauke tana Shafa kan Nurat din sedai kafin ta bude baki tayi magana aka sake turo dakin cikin wani irin sauri da karfi.

A tare suka miqe Zaune cikin faduwan gaba da mamaki,

‘Abaa’ Ayanah ta Ambaci sunan mahaifinsu dake shigowa da qaramin hasken wuta a hannunsa.

Nurat ma cikin fargaba tace

‘Abaa’

Qarasowa yayi da sauri batareda ya amsa su ba Amma na gefensa da hasken itama jikinta na tsananin rawan mummunan tashin hankalin da basu taba samun kansu a ciki ba tsawon tarihin GHAZ.

Riga me tsananin kauri ya janyo a cikin Kayan Ayanah ya miqa mata cikin kokarin hana mummunan tashin hankalinsa fita sbd kada su firgita yace

‘Saka wannan Ayanah’

Karba tayi hannuwanta na dan rawa tana sakawa akan kayanta tace

‘Abaa meya faru ne?’

Bai amsata ba ya janyo wata rigar ya saka a hannun Nurat dake sake shiga rikici idanuwanta na raurau

Amma ce ta taimakawa Nurat din gurin saka rigar Abaa ya Kama hannunsu su biyun ya nufo kofa dasu wannan Karan Amma ce riqe da hasken gaba daya.

Dakin Zuhrah suka isa wadda take bacci sosai hankali kwance

Cak Abaa ya tadata Zaune Wanda ya sakata bude ido tana sake lumshewa zata zame ta sake komawa kwance ya miqar da ita gabaki daya yana cewa

‘Ayanah samo mata Riga me nauyi sbd sanyi’

Da sauri Ayanah ta nufi Kayan Zuhrah din ta dauko Riga da sauri ta kawo tana miqa masa

Da Kansa ya sakawa Zuhrah din yana Kama hannunta itama suka fito.

Dakin Abaas suke kokarin nufa wani irin kuka da Ihun mutane mara dadin saurare ya sake tsananta yana gauraye garin tareda qaruwar hasken wutar dake cin garin sosai.

Sai a lokacin bacci gabaki daya ya sake su Ayanah suka shiga tsoro da faduwan gaba me tsanani suna kasa ma tambayan meya ke faruwa.

Abaas ma baccin yake Ayanah ce tayi saurin isa gurinsa ta tadashi da sauri dukkanin jikinta na rawa.

Fitowa sukai Abaa yaja su zuwa kofar baya ta fita gidan ya tura su wani daki tareda dukkanin bayin gidan mata ya kalli Amma batareda yace komaiba ya qanqame hannunta ya kalli Ayanah itama yace

‘Ku kula karku fito saina dawo Idan kuma kunji shiru ban dawoba ku fita ta baya akwai hanyar dana tanadar muku ta barin gari ku bi karku tsaya sai kun fita ruwa gabaki daya kun fada nahiyar yom acan zaku samu rayuwan kwanciyan hankali idan har kuka fadawa sarkin garin ku GHAZ ne.

Shiru sukai dukkaninsu Banda Ayanah da Amma da suka riqe hannunsa suna girgiza kai,

Nurat da Zuhrah tareda Abaas kuwa cikin tsananin tashin hankali da wani irin firgici suka ce

‘Abaa ina zaka? Karka fita dan Allah kazo mu tafi din bama sai mun jira ba dan Allah Abaa’

Girgiza kai yayi yana kallansu da jajayen idanuwansa da suke rine da tsananin ‘daci da baqin ciki yace

‘Ni shugaba ne ta yaya zan tafi nabar mutane na batareda nasan meya ke faruwa a garin ba……..

Katsesa Amma tayi cikin wani irin mugun tashin hankali muryanta na rawa zufa na tsiyayo mata da cewa

‘Koma menene ba alkhairi bane sbd Ihu da kukan da garin gabaki daya ya dauka ya tabbatarda hakan, Masifa ce da balai a garin yau karka tafi dan Allah ka tsaya’

Zare hannunsa yayi cikin nata idanuwansa na sake kada wa jajir.

Cafke hannunsa Ayanah tayi tana fadawa jikinsa ta qanqamesa wasu hawayen tashin hankali me tsanani suna kufce mata a rikice tace

‘Abaa dan Allah karka tafi mu tafi mubar garin tare bazamu iya tafiya koina babu kai ba’

Nurat ma qanqamesa tayi Zuhrah ta fada jikin Amma tana qanqameta Abaas ma Abaan ya riqe yana wani irin rawar jikin tashin hankali da tsoro take ya fasa kukan daya saka Abaan kallansa yanajin tsananin tausayinsa.

Banbare Ayanah da Nurat yake a jikinsa suna qanqamesa Ayanah tayi fashewa da wani irin kukan da bata taba sakewaba a rayuwarta tana ambatar sunan Abaan.

Fincikesu yayi da qarfi yana hana zuciyarsa karyewa ya turasu jikin Amma ya fice da sauri yana janyo marufin dakin.

Rawa da kuka sukeyi sosai Wanda gabaki daya gurin yayi tsit sai sautin kukansu dake tashi ahankali cikin mummunan tsoro,fargaba da tashin hankali.

Masifa,balai da kaddara ne suka saukarwa garin ANJOM a cikin Daren dayake na farko a tarihinsu da wannan masifar ta fadowa garin,

Wuta ce take ci tako ina zagaye da garin Wanda saida kusrawa suka gama cinnawa zagayen garin wuta sosai koina ya Kama sannan suka shigo cikin silalowa suka sakawa koina wuta a cikin garin kafin suka afkawa garin da wata irin mummunan kisan da take jini yafara fesuwa koina na mutane.

Ihun da kukan Neman agaji da ceto mutane suka fara Wanda ya saka gabaki daya garin daukan hayaniyan Data saka kowa fitowa Ana gudun Neman ceto sedai yawa da karfin da kusrawan ke dashi ya saka munin lamarin yayi yawan da komai ya lalace.

Kukan kananun yara dana mata da dabbobi ma dake gudun cetan rayuwansu ne yake gauraye gari da dajin ANJOM dayake amsa wa cikin sauti mara dadi da karya zuciya tareda tsananin tausayi.

Wuta kuwa haka take cin wasu mutane harma da dabbobi sbd gobara sosai garin ya dauka kowane gida sakawa wuta sukeyi sbd kada ma mutane su samu gurin boye dan haka komai ya zama tashin hankali mara misali lokaci daya.

GHAZ da fadawansa da askarawansa koda suka fito dan bada ceto ga jamaar gari lamarin ya gama munanar da babu abinda zasu iya sbd Angama cinye garin ANJOM da wuta da jinin mutane dan haka take suka fara cetan wainda zasu iya cikin azabar wuta da tashin hankalin munin gawawwakin mutane da suke tsallakewa da takawa. #MAMUH #ROYALTY #SLAVERY #BEST LOVE

HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070

Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali

*_HAYATEEM_* Mamuhgee 09033181070

6

*_PRIME SCENT_* 08103155915 Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa? Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents? Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites? Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa? Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT Duniyar kamshin da babu kamarsa, Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba, PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu. 08103155915 ********

********** Wani irin zufane yake jiqa Dukkaninsu zuciyoyinsu kaman zasu fado sbd munin tashin hankalin dasuke ciki,

Cikin duhun hasken wutar daya kusa cinyewa Ammah ta dago Idanuwanta da sukai jajir da hawaye masu karya zuciya ta kalli Ayanah kafin ta maida kallanta kan Sauran ‘yayan daya bayan tana hana hawayenta saukowa fuskanta sbd zuciyoyinsu duka a karya suke batason qarasa karyasu gabaki daya.

Juya kanta tayi ta kalli kofar dakin zuciyarta na kasa jurewa ta juyo ta sake kallan Ayanah wadda tayi saurin riqeta cikin mummunan tashin hankali ta bude baki da wata irin murya mara karfi cikin yarensu tace

‘Aāyi Amma, ātadirigi Amma, dan Allah Amma karkiyi hakan, āyi Amma.’

Hawayen da Amman ke riqewa ne suka gangaro cikin tsananin karyewan zuciya ta kalli Ayanah din tace

‘Ayanah dole zan dubosa sbd da hakan zamu tsira gabaki dayanmu’

Wani irin rikitaccen kukan tashin hankali me tsanani Ayanah ta sake tana rintse idanuwanta tareda sake qanqame hannun Amman tana girgiza akai ko magana ta kasa,

Nurat datake qame tin Bayan biyar Abaansu riqe hannun Amman daya tayi Tana girgiza kai itama hawaye masu tsananin zafi na gangarowa daga idanuwanta.

Abaas dake rungume dashi da Zuhrah saurin fadawa jikin Amman yayi ya rungumeta shima dukkanin jikinsa na rawa yace

‘Amma babu inda zaki tafi’

A rufe murya na rawa Zuhrah tace

‘Abaa ya tafi zai dawo Amma mu jirasa dan Allah karki tafi, Idan kin tafi zan biki mu dubosa tare’

Turesu tayi daga jikinta tana kasa kallan kowannesu tace

‘Ku jira zan dawo, Ayanah ki kula dasu karki Bari kowa ya biyo koda ban gansa ba zan dawo’

Sake riqeta Ayanah tayi Tana girgiza kai hannunta na rawa sosai muryanta na sake mutuwa kukanta na bayyana tace

Readers Also Read