Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 27
Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 27: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 27. Karfe 8 na safe Aleey ya aiko mota aka…
4,476 words
Karfe 8 na safe Aleey ya aiko mota aka maidasu asibiti inda ta tarar da mahaifinta yanda ta barsa tamkar babu rai a jikinsa yayi fayau yayi Wani irin haske ya qarasa bushewa sosai babu Sauran kowace albarkar jiki a tattare dashi.
A sanyaye babu kuzari ko kadan a jikinta ta zame gefensa ta zauna idanuwanta na cikowa da hawayen da basu gangaroba ta saka hannunta cikin nasa ta sake hadewa ta qanqamesa cikin wani irin sanyi dayake tabbatarda kaunar datake masa a shirye take da mutuwa tareda shi.
Haka ta wuni a dakin batareda kowa Yazo ba aka bata damarta sbd jikin nasa a yanda suke gani ba Sauran hope dan haka aka barta ta kasance dashi a lokutan da suka rage.
Kwana biyu da zuwansu asibitin bai farfado ba se a ranar na ukun tsakiyar dare kusan karfe biyu da mintina ya farfado dan haka cikin gaggawa asibitin suka kira waya suka sanar da NUAB Wanda a cikin Daren ya sako babbar jacket din fendi Akan Kayan jikinsa ya fito da hular sanyi Akan gashinsa suka nufo asibitin.
Suna isowa Kai tsaye dakin suka isa wanda doctors biyu ne da nurses hudu a dakin yana shigowa dukkaninsu suka jiyo suka kallesa cikeda tausayawa.
Takowa yakeyi a hankali zuciyarsa na tsinkewa a Karan farko dayake Jin tsananin tsoro na saka kafafunsa rawa da nauyin daya sakasa kafe Abaas din da idanuwansa da sukai ja yana Jin wata irin kauna me karfin gaske da tsananin so da fatar ya tashi daga ciwon sbd ya basa rayuwa me kyau da nutsuwa da kwanciyan hankali da kaunar da batada sirki.
Abaas dayake kwancen kamanninsa sun gama sauyawa daga dukkanin lafiyar da babu ko daya a jiki da jininsa bude idanuwansa Yayi ahankali cikin yanayin daya saka kafafun NUAB sake sarewa yaji kirjinsa yayi nauyin daya sakasa qarasowa da kyar,
Akan NUAB Abaas ya kafe idanuwansa masu tsananin Laushi yana Jin dukkanin baqin cikinsa da damuwarsa na yayewa a lokutan sa na karshen rayuwa dan haka Lumshe idanuwansa yayi tareda motsawa a tsananin sanyi ya bude tafin hannunsa na dama da NUAB din yake tsaye,
Zaunawa NUAB yayi a natse tareda Dora hannunsa ahankali Akan nasa din tareda kamawa ya riqe cikin nasa cikeda kulawa da kauna mara sirki.
Numfashi mara karfi Abaas ya sauke cikin rashin karfi ko kadan ya saka hannunsa daya ya zare oxygen dinsa Wanda NUAB yayi saurin riqe hannunsa shi da aleey a lokaci daya amma Abaas din ya girgiza musu Kai tareda bude baki cikin karfin Hali yace
‘Inason Ayanah tasan labarina a bakina kafin barina duniya idan Allah yasa na tashi zan fada mata da bakina idan ban tashi ba Ka gabatar mata da rayuwar da Abaas dinta yayi sbd kada tarihinmu ya zama ba qarasashe ba a tarihin duniya.’
Aleey baya yaja ahankali tareda fidda iPad dinsa da babu inda yake taba zuwa bada ita ba koman emergency kuwa,
Recording na video ya saka tareda tahowa ya ajiyeta a setin gadon Abaas din Wanda hannunsa yake cikin na NUAB yana jinsa har ransa sbd Jin yakeyi kaman hannun Ayanarsa ce a cikin hannunsa hade dan haka baida Sauran regret na rayuwa.
Juyawa aleey yayi waje inda securities suke yace suje su dauko BAHAR sbd ganawa da mahaifinta.
Yana dawowa wayar sa ya fice da ita dan fara hada tafiyar da zasuyi da asubar komai tsanani suna buqatan dagawa da Abaas din tinda ya farfado sbd likitocin su na gaggawa da suka hada suna can suna jiran isowansu.
Kafin Abaas ya fara cewa komai sake qanqame hannun NUAB yayi da dan karfin daya rage masa mara kuzari ko kadan dan ya bude baki ahankali ya furta ‘AYANAH BAHAR’
dago jajayen idanuwa NUAB yayi ya kalli Abaas din Wanda tin daga qasan zuciyarsa sunan ‘yar tasa ya fito harya manta da ita sbd aleey ne yake tsaye Akan kulawa dasu.
Ajiyan zuciya me sanyi Abaas din ya sauke kafin ya Lumshe idanuwansa a hankali sbd rayuwar komai ta farko data fara dawo masa radadi da baqin cikin na budewa yana famawa Wanda gashinan dashi zai mutu yabar duniya.
Asalin tarihinsu da rayuwar da sukai a qarqashin kulawa da kaunar iyayensu ya fara jerowa ahankali cikin nutsuwa da Wani irin ratsa zuciya da yanda kusrawa suka tarwatsa rayuwarsu suka sauya tarihinsu da kaddararsu zuwa mara dadi da kyau,
Yanda rayuwarsu ta sauya ne daga ranar da suka bar garinsu zuwa tafiya qangin bauta yafara zayyana wa Dayan bayan daya daki daki batareda ya boye ko kalma daya zuciyarsa na Kina da radadi me tsananin ciwo da baqin ciki,
Yana zuwa daidai inda aka lalata rayuwar Nurat wadda akai komai a cikin kunnuwansu qanqame hannun NUAB yayi cikin wani irin mafi zazzafan baqin cikin da har yanzu sautin kukanta bai fita kunnuwansa da zuciyarsa ba shiru ya dan yi jikinsa na rawa idanuwansa na rufewa cikin azaba…
Rawa jikin NUAB yakeyi sosai yana wata irin jijjiga a hankali ya qanqame hannun Abaas din da karfin daya saka Abaas bude idanuwansa yana sauke su Akan NUAB din Wanda yake hango Wani irin radadi da baqin ciki me tsananin karfi a cikin idanuwansa,
Rintse ido shima ya sake yi yana cigaba da bada labarin mutuwarta da abinda yaci gaba da biyowa Bayan nan har zuwa inda aka rabasa da yan uwansa,
Cigaba yayi da cewa,
‘Bayan an rabasa da yan uwansa anan kasuwar kwana yayi a daure a Wani ice tamkar dabba haka ya kuma wuni a rana babu ruwa babu Inuwa har saida karfinsa ya qare ya dunqule guri daya yana fita hayyacinsa sbd azabar rana da kishirwan dayake fatar ta dauki ransa dan kuwa bazai iya rayuwa babu su Ayanah a tareda shi ba dan haka duk duka da azabar da aka ringa gana masa Qin cin komai ko ruwan da aka basa yayi sbd yunwa yake sonta kashe sa ya huta.
Ganin taurin kansa ya saka sukuma suka siyarwa wasu marasa imani shi da niyar zasu je dashi su huta a tinaninsu mace ce gashi yaqi cewa komai dan Alkawari ne bazaiyi magana ba da yayiwa Ayanah harsai rayuwarsa ta kubuta dan haka bazai taba karya wannan Alkwarin ba.
Akan kudi ba masu yawa ba aka siyar dashi take wainda suka siyesa suka tafi dashi zuwa gurin hutawarsu,
Koda suka tafi dashi mummunan abinda suka fara aikata masa shine dukansa suka ringa yi har saida ya Dena motsi yayi mummunan illatar da baida Sauran amfani a duniya tukuna suka yaga Kayan jikinsa gabaki daya Akan zasu masa fyade sai suka tarar dashi namiji ne dan haka baqin cikinsu ya tsananta take suka qarasa kashesa da dukan tsiya suka tattara shi suka Kai bakin ruwan suka yar suka Tafiyarsu.
A wannan Daren gap da asuba wasu suka tsincesa suma maimakon su taimaka masa sai suka duba suka ga yanada Sauran rai dan haka suka wankesa tas suka sake saka masa Kayan mata sbd ganinsa da yan kunne a kunne harma da abin hanci,
Gari na fara wayewa kafin rana ta fito suka kallaba suka siyarwa Wani matafiyi shi a matsayin baiwa mace sbd anfison bayi mata a Kasuwan yanzu Shiyasa suka fi tsada.
Matafiyin raya siya bawan asalin balaraben shemali ne Wanda yayiwa ‘yarsa kwalli daya alkawarin siya mata baiwa mace da zata zama tamkar kawarta sbd debe mata kewan rashin uwa da kawayen datake fama dashi dan haka har zai tafi ya samu baiwar duk da taji jiki tana cikin wani mummunan Hali sosai amma hakanan bai damu ba ya siye sbd jirgin ruwa zaibi zuwa komawa qasar sa bazai jira gari ya waye a fara cin kasuwan bayi ba.
Hakanan ya karbi Abaas ya wuce dashi Bayan ya biya kudin jirginsa na ruwa ya biya kudin kayansa da bawansa Wanda zaa saka guri daya da Kayan sbd haka akeyi bayi da kaya guri daya ake sakasa kaman wasu dabbobi dan haka babu komawa jirginsu yabar qasar.
Tafiyar wuni da kwana daya sukai suka isa qasar wadda take cikeda nata kalar arzikin,
Boukar shine sunansa hakama shi din mai arziki ne sosai a gurin yan uwansa dama garin nasu Wanda yake na qasar larabawan shemali ne,
‘Yarsa tak daya a duniya wadda mahaifiyarta bata jima da rasuwa ba tabarta da kadai cin daya saka ya siyo mata baiwa sbd ta fita daga kewan datake cikinta,
Baya tareda yan uwansa sosai sbd akwai Hassada da qyashi sosai a tsakaninsu dashi, Duniyarsa ta tsone musu ido sosai, Tsananin hanyar da zasu rabasa da dukiyar suke nema dan haka basa rabarsa ko kadan sbd rayuwarsa suke dako dan hakanne ma yake tsananin kiyayewa Akan yarsa da ita kadai garesa bai hadata da komai,
AYSHAHH ne sunan yar tasa wadda take balarabiya gabanta da bayanta sbd uwa da ubanta duka yan asalin shemali dinne dan haka da kyau da gata da nutsuwa ta taso tareda gatan da kusan a garin babu Wanda ya keda irinsa. #MAMUH
HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070
Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali*_HAYATEEM_* Mamuhgee
66 Koda boukar ya kawowa yarsa ayshahh baiwa tayi farin ciki sosai sbd tana tsananin buqatar Abokiyar debe kewa dan haka tayi kaunaci kyautar baiwar musamman ganin kusan kansu daya kila ma ba Wani sosai baiwar ta girmeta ba dan haka taimaka mata sukai sosai da magani da ruwa da Sauran abubuwan da abinci ta samu a cikin kwana biyu ta dawo daidai hayyacinta ya dawo Wanda a hakan bata tana magana ba dan haka ran boukar ya baci ganin Ashe Murna aka siyar masa dan haka yayi alkawarin sake siyo mata wata idan yayi tafiyar kasuwancinsa.
Sosai Abaas yayi jinya tukuna ya dawo tsaye a kafafunsa ya fara aikin bautar da aka siyosa yayi batareda har lokacin ya fara magana ba,
Bauta yakeyi a gidan da rayuwar masu gidan dan kuwa kaf hidima da wahalar aikin gidan shine yakeyi Bayan hutawa babu abinda sukeyi se idan boukar ya fita ke yake Zaunawa da Ayshaah dan debe mata kewa kuma har lokacin basu taba sanin shi namiji bane a haka a hakan harya dauki kusan shekara bakwai dasu yana bauta sun samu Wani irin sabo dashi sosai gaske sbd kaf rayuwarsu babu kowa a cikinta baya su kadai uba da ‘ya sai maqota da yan uwan mahaifiyarta dake zuwa akai akai dan haka shine mutum na farko da suka sabo dashi fiyeda kowa da komai duk da har lokacin shi din kurma ne hakama bai taba fita daga qunci da tsananin baqin cikin da zuciyarsa take ciki ba amma daidai gwagwado sbd babu mugunta ba azaba ba tozarwa ba hantara ba qyama a tsakaninsu dashi ya saka suka samu matsayi a zuciyarsa musamman ayshaah dayake kallo kaman yar uwarsa sbd sosai take kaunarsa.
Shi Kansa boukar sosai yake da nutsuwa da kwanciyan hankali idan yabarsu tare sbd ya yadda da yarsa zata samu samu kulawa tamkar yananan koma fiye a gurin Nurat kaman yanda ya fada musu sunansa kenan a rubuce da larabci.
Bayan sabo shekarun suna dake nitsawa shaquwa me karfi ta shigesu sbd a yanzu ya koma tamkar Wani bangare ja rayuwarsu dan haka a yanzu tamkar ahalin mutum uku suke jinsu duk da haryanzu har gobe shi bawan su ne amma akwai kauna da kulawa tsakaninsu sbd tsananin biyayyarsa da rashin hayaniyarsa.
Saida yayi shekara kusan goma a hannunsu tukuna sukasan asalin jinsinsa da tintini boukar ya fahimta amma bai nuna masa ba sbd son qure lamarin Wanda baisan ina ze tsaya ba dan haka ya fuskunci hukunci me tsanani a gurinsa kafin kuma daga karshe ya barsa a macensa cewa shine hukuncin sa haka zaici gaba da zama tamkar dan daudu.
Baiji ciwo da Zafin hukuncin ba sosai sedai Ka quncin sa daya dawo sabo na rashin yan uwansa a rayuwarsa dayake ganin batada Sauran amfani a gurinsa,
Yanayin alaqar sa da ayshaah sauyawa tayi sbd jinsinsu daya bayyana ba daya ba dan haka ta rage shige masa sosai hakama ta Dena bayyanar da inda be kamata ba a jikinta indai suna tare sbd kiyaye dokar addini.
A hakan sukaci gaba batareda sun sauya masa tako wace hanya ba ko kadan, Kaf garin sun San Nurat a matsayin bawan ahalin da shine bawan da zai zama na ahalin me zuwa dan kuwa idan har boukar ya mutu Nurat yana cikin gadon da zaa raba maana shi Kansa abinda Wani ze iya gada ne a gurin rabon gadon Wanda yan uwansa keta lissafi sbd arzikinsa yayi wata irin sake habbaka ya tara dukiya ke yawan gaske data saka yarsa taje rayuwa tamkar sarauniya a fada,
Da farko Bayan angane Nurat namiji ne ba mace ba mutan gari sun so korarsa sbd jifansa da ihu aka ringa yi masa daga kasuwa da aka aikesa Wanda Koda ya iso gida sun masa mummunan illar data sauya masa kamanni sosai sbd jifar ta fasa Kansa da fuskarsa amma a hakan ya iso gidan baya ko gani sosai sbd jinin daya rufe idanuwansa.
Da karfin dukiya boukar yayi amfani ya hana a kori Nurat din amma kuma tin daga wannan lokacin Nurat ya zama abin qyama da hantara tareda jifa a cikin mutane a duk lokacinda zai fita gashi har lokacin shigar mata yakeyi,
Tsananin tsana da qyama tareda hantarar dayake fuskanta a rayuwarsa tsawan shekara kusan uku ya saka rayuwarsa gabaki dayanta komawa asalin baqin ciki da qunci dan haka sai abin ya fara taba zuciyarsa da daman bata taba fita tsananin qunci ba.
Wasu bayin boukar ya siyo guda biyar masu karfi dan gadin gidansa da ako Yaushe ake kokarin kawo harin Kai karshen rayuwar Nurat din Wanda kaf garin suke ganin mugun abu ne a cikinsu zama da zabgegen namiji a cikin Kayan mata dan haka koda be bar garin ba to zasu kashesa dan zamansa a garin tamkar zunubi ne.
Cikin wannan fitinar dake tashi koyaushe yan uwan boukar dake harin rayuwarsa suka shige sbd samun biya da cimma burinsu na shekaru masu yawa akansa sbd a yanda Nurat ta zama rayuwarsa da ‘yarsa bazasu iya rabuwa dashi ba dan haka suna samun ya fara shirye shiryen barin garin da Nurat dan komawa Wani garin suyi rayuwa hankali kwance tinda yanada dukiyarsa me yawan gaske.
Ana cikin wannan halin rana tsaka kwatsam cikin dare kawai aka cinnawa bangaren abincin boukar dake gidan wuta inda tarin dukiyar abincin sa take me yawan gaske buhuhuwan hatsin da dukiya ce me tsananin gaske,
Fitowa boukar din yayi cikin duhu da hayaqin daya gauraye gidan har Baka ganin komai yana kokarin isa bangaren idanuwansa da kunnuwansa sukai masa mummunan ji da ganin daya tabbatar masa da halin yan uwansa dayake zargi na shekaru masu yawa dan haka da sauri ya juya cikin hayaqin jikinsa na rawa zuciyarsa na Wani irin radadi da firgici sbd lamarin Yazo masa a bazata.
Fada ne ya fara kaurewa da hayaniya tareda ihu a gurin kashe wutar wadda duk da tsakiyar dare ne amma take mutane da suka cika gurin da sunan kashe wutar da kuma son qaddamar da nufinsu a cikin hayaniyar kashe gobarar na kashe Nurat su kuma yan uwan boukar kashe sa dan hakanne ma suka fada sun tada wutar yanda zaa hargitse ana ihu da hayaniyar kashe wuta su kuma sukuma su aikata aikinsu tareda sace dukiyarsa dan haka basu taho da shirin barin ko ‘yarsa ta rayu ba bare bawansa.
Fada aka fara tareda sare sare Ana fidda jini me yawa sbd bayin dake tsaron gidan da sukaga alamar fitina a tattare da kashe wutar dan haka suka fara hanawa sedai ko gama rufe baki na farkon beyiba suka rufu a Kansa suka sassarashi suna cewa shi bawa ne bai isa ya basa umarni ba sedai su su basa.
Jin hayaniya da Ihun kashe karshen daya dauki gari ya saka boukar daya dauko makaminsa dakatawa ya juya ahankali ya kalli kofar dakin ayshahh sai kawai yaji tinaninsa ya sauya ko yayane yanason ‘yarsa ta rayu dan haka ya nufi kofar dakin da Nurat yake kwana yana zuwa Kai tsaye shiga dakin yayi ya tadashi da karfi tareda dagosa daga kwancen batareda yace komaiba ya riqo hannunsa da karfi suka fito tsakar gida yana sake shiga tashin hankalin hayaniyar da Ihun daya qarasa gauraye gari.
Abaas na fitowa yanda wutar take ci da Ihun da akeyi ya sakasa jin Kansa na Juyawa zuciyarsa na bugawa da karfin gaske komai na yanda ya faru garinsu yana dawo masa sabo.
Wani irin Zafi da tiriri yaji yana tasowa daga zuciyarsa yana gauraya jininsa komai na sake dawo masa tin daga gawar magaifiyarsu da suka fara rasawa.
Rawa jikinsa keyi kowane irin radadin daya dandana a baya yana dawowa yana zama kuzari da fushinsa dan haka dagowa yayi idanuwansa jajir da wasu irin hawaye a cikinsu sbd bazai taba yadda ya sake shiga hannun kusrawaba koda zai rasa ransa gurin cetan Kansa da ayshahh da boukar sbd har abada bayason su dandana baqin cikin daya dandana shi da yan uwansa musamman ayshaahh datake mace,
A baya rauni da rashin karfi ya sakasa zamowa nace yana kallo baida abin yi Bayan kuka aka tarwatsa rayuwar yan uwansa aka kashe masa Nurat dan haka wannan Karan a yanzu daya zama namiji ya zabi mutuwa Akan tafiya wannnan mummunan rayuwar.
Takobi da adda boukar ya basa yana kallan Zafin dayake bayyana a cikin idanuwansa yace
‘Ka tabbatarda Ka bawa Kanka da Ayshaah kariya’
Wucewa gaba boukar yayi da dan gudunsa na fuskantar komai ai kuwa yana fita take fadan ya dawo Kansa amma dayake yanada nasa karfin sosai haka ya ringa fadan dasu.
Shima Abaas baisan lokacinda ya fado cikin fadan ba idanuwansa a rufe komai na abinda ya faru dasu kawai yake gani dan haka kusrawa kawai yake gani a idanuwansa ya ringa fadan bayaji baya gani.
Fin karfinsu fadan ya fara yi sbd kusan duk bayin biyar an kashesu hakama suma anfara musu rauni dan haka boukar da jini sosai yake fita jikinsa kallan Abaas yayi cikin tsananin galabaitar daya fara yace
‘Ka tafi Ka dauki ayshahh da jaka na nan gefen gadonta na ajiye ku bar nan kuje garin neruji ku tsallaka ruwa zuwa kiyoje ku jirani anan,Ka tafi da sauri….
Kasan Juyawa Abaas din yayi yana kallan boukar din tamkar yanda Abaa dinsu yayi musu hakan ce yake sake faruwa Ayau din dan haka zaiyi musu boukar damqi hannunsa da karfi yace
‘Idan ban taho ba zuwa gobe to bana duniya Ka dauki Ayshaah Ka tafi da ita inda zata samu rayuwa me kyau ita amana ce gareka duniya da lahira, Hakama idan ranar goben ta fadi ban bayyana gareku ba na ‘yantaka Nurat, Ka zama gatan ‘yata ka zama gatanta da dukiyarta’
Cikin tsananin baqin ciki da radadin zuciya a Karan farko Abaas ya bude bakinsa Bayan shekaru ya furta
‘ABAAS GHAZ’
Kallansa boukar yayi da Wani irin yanayin karyewan zuciya batareda yaddarsa akansa ta girgiza ba ya bude baki idanuwansa na yin jajir yace
‘Abaas ghaz ina fatar Ka zamo gatan ‘yata da bata kariya da rayuwarka har karshen rayuwarta ko taka’
Tura Abaas din yayi da karfi zuwa cikin gida shikuma yana sake bude kofar fita daga bangarensu zuwa bangaren da hatsin zuwa da kuma zuwa kofar ficewa da tini suka shigo.
Da sauri Abaas ya juya yana jin zuciyarsa na yanka da Wani irin yanayin da yake sakasa jin kaman bazai iya tafiya yabar boukar ba amma kuma matiqar zasu bawa ayshahh kariya su tseratar da rayuwarta dole ya tafi. #MAMUH
HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070
Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali*_HAYATEEM_* Mamuhgee
67 Kai tsaye dakinta ya isa da gudun gaske ya banka kofar bai tsaya komaiba ya dauki jakar da boukar yace ya miqa hannu ya damqi hannunta datake tsaye ta miqe cikin tsananin tsoro da fargaba.
Janta yayi da karfi suka fito tsakar gidan Wanda yake hayaqi da ci da wuta take ta riqe hannunsa da karfi cikin tsananin tsoro da tashin hankali tace
‘Meya ke faruwa, Ina Abbu??
Baice mata komaiba ya jata da saurin suka bi ta kofar baya da babu Wanda ya sani sai iya su zasu fice ta qwace hannunta zata koma da gudu tana kwala kiran sunan mahaifinta.
Riqota Abaas din yayi da karfin gaske yana kokarin sake tafiya da ita ta fara fizgewa tana Ihun daya sakasa rufe mata baki da karfi yana kallanta cikin duhun hanyar ya sanar da ita abinda yake faruwa da kuma abinda mahaifinta ya ce akan zuwansu su jirasa.
Kasa iya barin mahaifinta tayi ta fara Wani irin kuka da rawar jiki tana kokarin kwacewa sbd tasan mahaifinta bazai tsiraba kashesa zasuyi batada kowa bazata iya rayuwa ba mahaifinta ba,bazata iya shiga duniyar da tasan bazata taba sake dawowa ba anan ko kabarin mahaifinta ta ziyarta ba dan haka gwara ta mutu a guri daya da mahaifinta.
Rufe mata baki gabaki daya Abaas yayi zuciyarsa na jin abinda take ji sbd shima ya shiga irin wannan mummunan yanayin harma nasa ya zarce nata nesa ba kusa ba dan haka daukanta yayi cak yabar gurin da ita yana sake rufe mata baki da duka karfinsa.
Gudu yakeyi da ita a cikin tsananin duhu da shukokin da sun kusa finsu tsayi dan haka cikinsu kawai yake jefa Kafafunsa da ko takarmi babu yanaji qayoyi manya da qananu suna sukarsa da abubuwa masu laifin da harma sun fasa kafafunsa jini suke fiddawa amma bai tsayaba gudun yakeyi sosai sbd yana jiyo hayaniyar biyosu da akai Wanda hakan ya tabbatar musu su duka biyun da boukar ya fadi.
Kuka Ayshaah takeyi sosai dukkinanin jikinta na sakewa a jikinsa tanajin duniyarta ta gama kifewa da lalacewa kenan har abada dan haka bazata taba dawowa daidaiba.
Shi Kansa jin yakeyi jikinsa na Neman mutuwa da wannan mummunan baqin cikin na rasa Wanda yakeda mahimmanci a rayuwarsa datake a rube Bayan rasa iyaye da yan uwansa amma ganin a yanzu shine gatan ayshahh da kuma zai samu yancin zuwa Neman yan uwansa da sune kadai rayuwarsa ya saka yake sake tattaro karfinsa yana cigaba da Wani irin gudun da kafafunsa ke fidda jini sosai amma bai tsayaba dan basu tsira ba.
Gudu sukeyi har kusan asuba hakama karfinsa ya kare daqyar yake iya daga kafa sbd galabaita da jininsa daya fara qasa da kuma wata irin azababbiyar ciwon kirji amma hakanan yake dagewa yana daga kafa.
Koda suka isa wani garin dayake daga shi sai inda boukar din tace suje anan suka samu suka tsare wa wainda suka biyosu amma duk da hakan bai tsayaba dauketa kawai yayi ya Kama hannunta tamkar wadda bata gani haka ya ringa Janta ba karfi a jikinta ko kadan. Tafiya me tsayi suka kuma yi kafin suka isa garin dayake bakin ruwan da zasu tsallaka Anan dinma basu tsaya ba cikin wata gona suka boye yayi sallah a galabaice kafin suka fada jirgi suka bar nahiyar kwata kwata.
Tafiyar wuni guda sukai kafin suka isa inda zasu din suka fito jirgin tareda barin bodar bakin ruwan wadda sai anan ne Abaas ya gane garin da aka siyosa ne dan haka ya sake riqe hannunta gam suna kutsa mutane suna shiga cikin garin sosai Wanda yake a cike tamkar kasuwa koina hidima akeyi.
Wani qaramin gidan baqi da yan gudun hijira ya isa dasu suka zauna Bayan ya tsaya a hanya ya siya mata gasashiyar fulawa da zuma.
Suna Zaunawa ta cusa kanta cikin kafafunta tareda qanqame jikinta tana fasa wani irin kuka mai tsima zuciya koina na jikinta na jijjiga da tsananin quncin da batasan haka radadi da zafinsa yake ba.
Shiru Abaas yayi a gefenta idanuwansa jajir yana Kurawa ruwan dake mamaye da bakin bodar ido zuciyarsa na yanka shima sbd anan ne aka rabasa da tasa rayuwar, Anan ne ya rabu da wainda suke rayuwarsa, Anan ne komai na rayuwarsa ya qarasa Juyawa harzuwa matakin dayake yau akai na rayuwa da bulayi cikin duniya shi kadai babu kowa acikinta.
Radadin azaba me tsanani kafafunsa keyi Wanda ya ke sakar masa da zazzabi me Zafi amma bai damuba shiru yayi ido jajir Akan ruwan.
Kuka tayi Wanda saida ya qarasa cinye karfinta kafin tayi shiru tana Kurawa hanyar ido itama batareda ta iya cin abinda ya bata dinba.
A gurin suka kwana Zaune cikin mummunan halin daya tsananta yanayinsa dama nata datake wata rawar sanyi dan haka ya cire rigar jikinsa ya rufa mata Akan nata Kayan da babu ko kallabi a kanta gashinta a bude yake a sake sbd yanayin da suka fito.
Koda gari ya waye daqyar sukai sallah a gurin suka tashi Zaune suna sake gadin hanyar da duk masu isowa,
Duk yanda yayi da ita taci Wani abin qi tayi gashi tayi Laushi sosai ta fita hayyacinta kawai mahaifinta take son ganin ya taho din.
Haka suka wuni har rana ta Kuma faduwa babu boukar ba labarinsa,
Zuwa lokacin dagashi har ita daqyar suke Numfashi dan haka Akan dole sukaci abinci sbd suna Neman karfin cigaba da jiransa har ranar daya taho.
Wani wunin suka kuma yi ba labarinsa haka suka kuma kwana, Ahankali ahankali kwanakin suka ringa tafiya ba boukar ba labarinsa su kuma sun kasa cire tsammani dan haka basu iya tafiya koina ba haka su kaita zaman jira a bakin bodar wadda tin baa Ankara dasu ba har aka fara ankarewa dasu Ana musu kallan mata da miji marasa hankali sbd yunwa da wahalar data Kama jikinsu take fara bayyana dan kuwa basa Wani iya cin abinci suna cikin tsananin damuwa da baqin ciki tareda rashin sanin inda zasu.
Ganin an fara saka musu ido ya saka suna cika sati shida a gurin Abaas ya tattarata suka bar qasar sbd Wani jirgin na tahowa Wanda zaiyi gaba binsa sukai sbd a yanzu tafiya Neman yan uwansa zai tafi dan haka a qasar datake gaban wannan zai fara tinda daga nan gaba akai dasu Ayanaah.
Tafiya sukai ta kwanaki a jirgin kafin suka isa qasar dake gaban wadda suka Baro,
Isarsu qasar dole anan bakin boda ya samu aikin wahala Wanda zaa ringa biyansa dan yana buqatar kudin dazai nema yan uwansa bazai taba dukiyar Ayshaah ba a gurin nemansu,
Gida suka samu Wanda ake biyan hayar daki daya ya biya hayar ya saka ayshan a ciki shi kuma yana kwana a kofar dakin.
Rayuwa a qasar qunci tafara yi musu sbd yanda ake qyamarsa ganinsa namiji da Kayan maza amma yan kunnen mata ne a kunnensa wainda ya kasa cirewa sbd Ayanah ce ta saka masa su da hannunta bazai iya cirewaba.
Ita kanta ayshahh tsangwamarta mutane suka fara yi sbd tana tareda shi babu aure a tsakaninsu dan haka rayuwa tayi mata qunci da nauyi bata cikin kowace irin walwala bare farin ciki dan haka suka bar garin suka koma can quryar qasar Wani garin suka fara rayuwa shima ahankali ahankali zaman yakasa dadi sbd qabilanci na qasar sam basason baqi dan haka dole suka tattara suka sake sauya guri Wanda duk inda sukaje kaman mahaukaci haka Abaas ke Neman yan uwansa.